Aunty Rumaisa Hausa Novel Complete
Aunty Rumaisa Hausa Novel Complete
AUNTY RUMAISA
Aéroport International Blaise Diagne.
Da yake a K’asar Sénégal capital Babban birninsu (Dakar) da mislin karfe Biyar na yamma, Ko ina ka waiga dandazon jama’a ne, matafiya cikin Airport din kowa na jiran lokacin tashin jirginsu yayi. A tsaitsaye suke suna jimamin rabuwa da ita.Matashiyar budurwa ce kyakyawa lumba one tana da wani irin sihirtaccen kyau duk da ita ba fara ba ce amma tana da mutikar, kyaudoguwa ce sam ba ta layin fararen mata haka zalika bata layin bak’ake, wato chocolate colour kenan sanye take da wani yadi na mata irin na Sénégal green colour dinki doguwar riga wanda ya kamata ya mata cif cif surar jikinta mai kyau ta baiyana tana sanye da wani takalmi shima green ne mai tsayi gaske yana da igiyoyi, sai jakarta da take makale a kafadarta ita ma green colour, ta sha kitso mai masifar kyau wani mai wata irin kwana-kwana ta zubo jelar kitson gaba, sauran gaba sauran baya, daga kitson za ka san tana da gashi, ta dan yane kanta da karamin mayafi shi ma green colour, a gaskiya a wannan lokacin duk namiji mai lfy ya ga Rumaisa zai ji yana son ya mallaketa amatsayin matarsa ta sunnah.
Tsaye suke kasancewar an fara sanarwar matafiya Nigeria su shirya, yan uwanta sun baibaye ta, suna kukan rabuwar su da ita dan har yau sun kasa sabawa in dai Rumaisa zata zo Sénégal to idan za ta koma Nigeria cikin kuka su ke rabuwa da dangin mamarta suna koke-koke. Wata dattijuwa ce mai kimanin 60 year, rungume da Rumaisa tana kukan rashin ta da za ta yi na Rumaisa din.Rumaisa ta manne ajikin tsohuwar tana murmushi tana shafa bayan tsohuwar dan Rumaisa ba ta fiye kuka ba, ga shi idan ta ce za ta yi yanzu tsohuwar rikicewa za ta yi.A hankali Rumaisa ta yi magana, da yaran Sénégal, cikin zazzakar muryata, ta ce” grand-mère ki yi hakuri zan dawo shekara mai zuwa in sha Allahu,ki bar kukan, ta kalli Bibata da Umari ta ce”Ku lallaba mun grand mère ai zan dawo, in ko na sami miji sai ku zo biki ko grand mère?”Ta karasa fadar maganar tana ma grand mère chakulkuli.Sai ga ta tana dariya tana dukan Rumaisa, daket ta kwace ta fara gudu grand mère ta bita suna zagaya dan filin da suke tsaye, su Bibata suna musu dariya, jama’a sai kallonsu suke cike da sha’awa, barin Rumaisa yadda jikinta yake motsawa.Saboda akwai ta diri mai kyau da daukan hankali, jigidarta da ta ke daure a k’ungata mai dauke da sinadarai sai cakas-cakas suke, a k’ugunta, Rumaisa doguwa ce chocolate colour dirara mai kirar Coca-Cola akwaita mazauna, masu mutikar daukan hankalin maza, samanta a tsuke k’asanta a bude yake, ba ta da kiba kuma ba ta da rama sosai akwaita da hips na daukar hankali, ga ta da manyan-manyan boobs a tsaye suke cur tandam-tandam, ma su tafiyar da imanin duk wani lafiyayan namiji. Rumaisa tana da doguwar fuska mai dan fada, tana da dogon hanci da manyan idanu farare tas lumsassun idan tana kallonka za ka zaci kallon raini take ma ko kuma tana jin bacci gashin idanunta gazar-gazar ne haka gashin girarta mai kyau ne, sai dai tana da fadin lips sosai irin na yan Sénégal, amma cikin ikon Allah sai ya yi mata kyau mutika lips dinta pink ne, tana da dimple a gefen kumcinta na dama wanda ko magana take lobawa yake bare ta yi dariya, Rumaisa tana da fara’a da son mutane ba ta da raina mutane sai dai ta fiye sanyin hali kuma ba ta cika surutu ba mutum daya yake bata ciwon kai shi ne ya koya mata surutu da masifa. Shekarunta na haihuwa 26 year amma wlh ba za ka taba cewa Rumaisa tayi 20 year, ba saboda Allah yayi mata kyawun diri da kyan fuska ko ta fadi shekarunta na haihuwa mutane ba sa yarda sai su ce karya take ba za ta yi ashirin ba ma dole take kyalesu saboda ko a makaranta haka ta yi ta fama da kawayanta da malamai kafin su kammala karatunsu na karshe wato law school , wlh har sai da ta fara musu yar masifar da Abdallah ya fara koya mata tukun ta samu kansu, suka rabu da ita suna cewa an kara mata shekaru ne ai.Dole Rumaisa sai dai ta yi dariya ta ce ta ji har suka gama karatun su.Sosai Rumaisa suke zagaya filin suna dariya ita da grand mère, umari sai ya fara hawaye ya tuno da mahaifiyar Rumaisa da ta mutu.Moubarak ne ya isa gurin Rumaisa ya kamota ransa a bace ya ce “wai me yasa kike haka ko baki ga yarda jarababbun maza ba suka zuba miki idanu ko baki san abin na bata mun rai ba wlh dole zan zo Nigeria cikin satinan tunda karatu ya kare Abbie ya bani auranki na dauko abuna mu taho haba ina dalilin jaraba sai kace Rumaisa ce kadai mace.” Ya karasa yana huci.Rumaisa ta kwace jikinta,ta kura masa idanu dan sam ba ta san da zuwan sa ba, cikin sanyin murya ta ce”wai Moubarak me yasa kake da kishi yaushe muka yi da kai zan aure ka wlh har yanzu ban sami kalar namijin da nake so ba in da ina son ire-iren ka da tuntuni ina cikin karatu na yi aure plz ka barni mana mu tsaya zumunci ba wai soyayya tsakanin mu, da wani idanu zan kalli Aliya matarka haba dan Allah.”ta fada tana ja baya.Moubarak kallonta yake cike da mamaki ya ce”wlh a kanki ko sakinta ya kama zan yi wlh idan kika ga ban aure ki ba sai dai wani ikon Allah” grand mère ta fara masa fada ta rungume Rumaisa tace”ki rabu da sakare.”dariya Rumaisa ta yi..za ta yi magana aka fara neman matafiya sai lokacin idanun Rumaisa suka ciko da ruwa ta rungume grand mère suna kuka.Sai da Bibata ta banbare, Rumaisa daga jikin grand mère. Rumaisa ta rungume yan uwan mamarta maza da mata daya bayan daya, Bibata ta ja hannunta ta rakata bakin inda za ta shiga har gun jirgi Moubarak na biye da su hannu ta daga masa dan a rabu lafiya. Haka Rumaisa ta shiga cikin jirgi tana kewar yan uwanta.Tunda Rumaisa ta shiga jirgi ta jingina kanta da kujera ta lumshe idanunta tana safke numfashi tana jin wayarta na ringin ta ki bude idanunta ma bare taga mai kiran, dan ta san bai wace, Abdallah.A can kuwa *Nigeria garin Abuja unguwar Games village* a dai-dai wannan lokacin wani matashin saurayi ne ya fito cike da takun isa da kasaita yake takunsa, yana kalkada makullan mota,yana ciza lips dinsa ya nufi rumfar ajiye motoci da take cikin wannan tamfatsetsan gidan tsarare wanda aka kerasa da kayan zami tamkar a k’asar larabawa babu abin da babu a gidan tsayawa fadar tsarin gidan ɓata lokaci ne, amma ya hadu ta ko ina dan gidan kallo daya zaka masa ka san ya hadu ba karya me shi ya ci ya tada kai da nera.*Abdallah* yana isa rumfar motocin ya yi tsaye jikin wata jibgegiyar Jeep fara kal fuskarsa ba walwala yana latsa zabgegiyar wayarsa iPhone 11 yana jan tsaki da ciza baki.yana sanye da wasu kananun kaya riga da wando masu masifar kyau Ash colour sun yi masifar masa kyau sai zuba uban kamshi yake kayan sun fito da girman kirjinsa saboda yadda kayan suka kamashi, da gan-gan yake zazago wando yayi k’asa amma hakan baya hana kaya su masa kyau, gashin kansa mai tarin suma baka sudik sai walkiya yake iska na kada gashin tamkar na indiyawa harda tilar kunne daya gare shi wacce yasa mata barimar zallar gold sai sheki yake gashin kansa sai walkiya yake saboda bai fiye aski ba shiyasa zaka ga gashin tamkar na wata macan,Abdallah dan kimanin 23 year dogo mai murdaddan jiki mai zubin karfafa yana da faffadan kirji samansa a bude yake yayin da k’asansa yake a tsuke,fari ne tas kyakyawa ajin karshe a kyau yana da manyan idanu dara-dara da gashin idanu da na gyara masu kyau yana da dogon hanci bakinsa dan karami, jajur da shi tamkar na jarirai wanda hakan ya kara masa kyau ba kadan yana da dimple har biyu, ko magana yake lobawa suke uwa uba idan ya yi dariya, abin da ya ke tafiya da Antynsa Rumaisa kenan tayi ta saka sa dariya tana saka yatsarta ramin tana tabawa. Abdallah ga shi da shegen kwarjini duk girmanka idan kuna magana da *Abdallah* ya tsareka da wannan shanyayyun idanun nasa masu wani sinadari a cikin su na baiwa da ba kowa Allah ya ke ba irin ta ba dole ka ji shakkarsa shiyasa zaka ga har wanda suka girme masa suna shakun sa saboda shi yaro ne jarumin gaske ta ko wane fanni namiji gaske ne shiyasa ko a makaranta abokansa da malamai suke kiransa da Baffa Abdallah babban mutum, shi ko uban son girma sai ya fara bubbude hancin ala dole shi babba ne, Abdallah duk abin nan nasa amma sai ya maida kansa sakare mara wayo a gurin Antynsa Rumaisa ita ko take biye masa tana renonsa tamkar jariri duk da watarana idan ya shakata ta ga iskancinsa yayi yawa fada suke sosai ta yi masa fushi, dan labari dai sai a nan gaba. Kai komo Abdallah ya fara saboda kiran da yake ba’a dauka, ransa a bace ya bude motar ya shiga, cikin daddadan muryasa a yangace can k’asan makoshi ya furta”Wlh My Aunty Rumaisa sai na bata miki rai fiye da yadda kika bata mun yau nine zaki dauka dan iska dan ina miki biyayya wlh sai na saki kuka kamar yadda kika sani sai na daga miki hankali gobe na san maganin ki”ya karasa maganar yana ciza jajayan lips dinsa yama motar key ya fizgeta da karfin gaske ya nufi tamkameman get din gidan yana zuba uban horn, me gadi na sanye da uniforme a guje ya nufi get sanin halin Abdallah yanzu zai bashi hutu,yana wangame masa get ya fice a guje kamar zai tashi sama.Bangaran Rumaisa jin an daina kiran ta ja tsaki ta ciro wayar a jaka wani kiran ya shigo ganin Abbie ne ta zaro idanu ta dafe goshi cikin siririyar muryata mai dadin, gaske ta furta ” oh My God my Abbie dama kaine kake kirana tun d’azu” ta fada tana tsinke kiran, ta ce “Abbie bari na kira ka na zata wannan fitinanan Baby kanina ne shiyasa naki duba wayar” ta fada tana dailing number Abbie.Bugu daya ya daga da sallama murya dattijo mai cike da kamala.Rumaisa ta ce”my Abbie barka da yamma ina yini ya karfin jiki ya mamie, ka yi hakuri na zata Baffa Abdallah ne shiyasa naki picking”daga can bangaran Abbie ya saki murmushi ya ya ce”My love Allah ya shirya ku ke da Baffa abin ya Kai ya kira kiki dauka kanin ki ne fa abokin shawara ki, na ko ga yanzu ya fita cikin fushi yana jan tsaki” murmushi Rumaisa ta yi, ta basar da zancan ta ce” Abbie gamu cikin jirgi zamu taso a mana Addu’a i love u Abbie Allah ya kara ma lfy sai na iso plz Abbie yaya Al’ameen zai je daukata bana son Abdallah ya je….zaman da na ji anyi dab da ni wani daddadan kamshine ya daki hancina shi ya saka na katse maganata nan take ba tare da na sani ba na tsinke kiran dan na tsani takura ga shi ba halin na ce ya tashi tunda jirgin ba na gidanmu ba ne…Cikin cool voice na ji ya mun sallama muryashi mai dadi, ban san lokacin da na dago ba, karaf idanunmu suka sark’e da na juna yana sakar mun murmushi take na ji gabana ya fadi nayi saurin kawar da kaina na sadda k’asa, ina mamakin kyawunsa duk da bai kai Baby k’anina kyau ba, baki ne kyakyawa isasashan namiji na nunawa sa’a zai kai kimanin 32 ma’abucin fara’a.Amsa sallamar nayi daga shi ban sake ko kwakwaran motsin, wayata na kashe baki daya na maida jaka na darma belt na takure a guri gudu na lumshe idanuna.Har jirgin mu ya tashi ban dago ba, murya sa na kuma tsintowa yana cewa”La beauté sannu kin amma ke haifafiyar Nigeria ce ko..? Ya fada yana leken fuska ta.Ban masa magana ba, saboda kusancin mu ya yi yawa ga kamshin sa ya cika ni, ban taba tunanin ana samun namiji mai kwarjini da dadin murya wanda ya hadu ga sansan yan kamshin bayan Baby Baffa kanina ba…Tunanin ya katsemun ta hanyar ce mun “plz mai kyau ki mun magana wlh tunda na ganki a waje kuna wasan tsere da kakar ki Allah ya jarabe ni da sonki kai tsaye wlh gaskiya nake fada miki.”ya kara maganar yana dafe kansa idanunsa sunyi jajur kwalla ta taru.Kallonsa na yi na ga kwalla yake,cikin sanyi murya cike da tausayin sa nace”plz kar ka yi kuka ina da rauni ba na son ganin na sanya wani damuwa, ko Baby k’anina ba na bari yayi duk yadda zai bata mun rai shi da yake yaro bare kai babba”ta karasa maganar tana sadda kanta dan bata jure kallonsa gabanta faduwa yake sai ta rika jin wani irin yanayi.Murmushi farin ciki ya saki yace “Alhmdllh na ji logon ki zan dinga miki kuka da zaran kin ki saurara ta, so da farko ni sunana *Shaheed Ghali imam Sara* muna Abuja zaune tare da iyayena, da yan uwana sauran labarina sai mun kebe, plz ki bani gurbi a zuciyar ki wlh yau daya na yarda da ake cewa daga kallo daya ana kamuwa da soyayya.” Ya fada yana sakin murmushi yana leken fuskar Rumaisa wacce take wasa da zoben gold guda biyu, hannunta.Shiru ya mata yana mai jin dadin samun irin macen da ya jima yana nema kamila mai kamun kai ba irinsu Labibah ba kamar tai masa fyade. Haka jirgin su yake lula gudu asararin samaniya, cikin hikima da dubara Shaheed ya saka Rumaisa ta dan saki jikinta da shi har ta fada masa sunanta da unguwar su a Abuja ya mata wayo har da numberta saida ya amsa.A haka har bacci ya dauke ta ganin ta takure ya gyara zamansa ya dora kanta saman kafadarsa ya tallabe ta da hannunsa yadda za ta ji dadin bacci, duk da ya k’age amma bai damu ba,haka jirginsu ke tsula gudu zuwa Abuja,sai muce Allah ya sauke ku lafiya.*Nigeria* Baffa yana fita a guje ya harba motar saman titi gudu yake sosai, yana ciza lips dinsa na k’asa har ya yi wani irin ja ko me ya tuna da karfi ya take burki ya juya kan motar zuwa gida yana sharara gudu.Tun daga nesa ya fara zuba honr, megadi ya bude masa get, tun kafin ya iso.Yana isowa ya shige gidan a guje, ya nufi parking space. Yana shiga ya yi parking ya kashe motar ya fito ko motar bai tsaya kashewa ba ya fara takun sa mai cike izza da karfi yake takawa ya nufi tsakiyar rumfar, kallo daya za ka masa ka san ransa a ɓace yake.Yana zuwa ya bude wata rigar rufe mota wani hadaddan mashin babba mai kyan gaske ya baiyyana green colour ne ajiye rigar yayi ya hau abinsa saboda baya da kura wani bakin glass ne sark’e gaban mashin din Abdallah ya cire farin glass din fuskarsa ya saka bakin ya wa mashin din key ya tayar da shi, wani irin kara yake zuuuuuuuum me dadi ya fito daga rumfar Al’ameen da ya gama parking ya fito daga cikin motarsa ya kalli Abdallah yace”Baffa kai dawo nan” banza Abdallah ya masa ya ma mashin din wuta ya nufi get a guje.Al’ameen ya buga masa tsawa ko a jikinsa tun daga nesa yake honr aka bude masa get ya fice daga gidan a guje.Al’ameen da ransa ya gama baci ya nufi cikin gida gun Abbie yana masifa sai sauri yake kamar zai kifa dan iskancin Baffa ya fara isar sa…………….✍🏻
*+22796515805*
(03/06, 6:27 pm) +234 816 362 6370: _AUNTY RUMAISA_
Page2⃣
Cikin wani tafkeken parlo ƙayatacce, wanda ya gaji da haduwa ya sha kayan alatu Al’ameen ya shigo,ransa amugun b’ace sai hanci ya ke budewa, masifa na cin sa.Kyakyawan dattijo ne farin bafulatani zaune cikin keken guragu, kafafun sa an yan ke, jarida a hannunsa ya na karantawa farin gilashi manne akan fuskasa, zai kai kimanin 55 year.Gefe guda dattijuwa ce yar kimanin 70 year fara kyakyawa, tasbaha rike hannunta ta na Ja, sai wata yar matashiyar budurwa kyakyawa fara tas kallo daya zaka mata kasan sun sha nono daya da Abdallah saboda tsantsar kamar su tamkar an tsaga kara yar kimanin 15 year tana zaune kusan Abbie.Sai ganin Al’ameen suka yi tsaye yana masifa, da kumfar baki ya na cewa “Abbie wlh ka rabani da Baffa akan me zan masa magana amma ya na jina ya kama hanya ya tafi saboda ya maidani ba kowa saboda mahaifina ya daure masa gindi”ya fada ya na tafiya zai bar parlon.N’aima ranta taji ya soso akan maganar da Al’ameen yay a ganinta meye banbban cinsu.Abbie ya a jiye Jaridar hannunsa, ya kalli Al’ameen ya ce” Al’ameen dawo yau she ne zaka kama girman ka kasan Baffa baya ji rigima ce da shi ba raga maka zai ba kuma a kashi ba kashi zaka iya bashi ba, ba wai ina daure masa gindi ba ne, don Allah ka rabu da shi fushi ne ya ke Rumaisa ba ta daukan kiransa.”dariya Na’ima tayi. Innani tai dariya ta ce” Wlh Kai anyi babban kwabo ban san me Abdallah ya tsare ma ba kullum cikin kai karan sa kake Abdallah ko bashi da gidan da ya fi nan, mutumin banza mai mugun hali kawai.” Ta fada tana hararasa.Dariya abin ya ba Al’ameen yadda innani take masa kallon banza amma sai ya basar ya atsuke fuska ya ce”ni fa ban saki a zan ce naba dama ke ce kike daure masa gindi ajikoki ma son kai ake nunawa”Abbie ya kallesa ya ce”Wai Al’ameen yau me ya zo ma kayi baki haka kai da hayaniya ba damuna ka ta yi ba” wata mata ce mai madede cin kyau da jiki da tsayi fara ce tas yar kimanin 35 year ta shigo da sallama dauke da faranti mai butar shayi ta nufi gurin innani ta duka ta ajiye ta dauki cup ta tsiyaya ma innani shayin ta bata ta zuba ma Abbie ta mike ta kai masa ta duka har k’asa ta bashi ya amsa yana godiya.Mamie ta kalli Al’ameen ta ce”My son waye ya tabo ka halan Baffa ne kayi hakuri”ta fada tana langwabarda kai ta masa kuri da idanu, shima kallonta ya ke, yace “Mamie ai nasan ke daya ce kike sona gidanan tun bayan mutuwar Ummin mu nida Rumaisa ita ana son ta ni ne ba’a so.”ya fada kwalla ta cika masa idanu.Abbie ya ce “Wlh yau kai kam a kwai aljanar da ta kawo maka farmaki, magana ba kan gado Allah ya shirya to”Innani ta ce”munji mun gode Mamie ka dai take sonka ai dole ta soka tunda d’anta ne”murmushi Mamie tayi taje ta tsiyayo masa shayi ta zo ta kamo hannunsa gam ta rike cikin nata tana murzawa ahanakali tana kallonsa ta ce “Muje kasha shayi”Kai Al’ameen ya d’aga suka nufi kujera ta zaunar dashi, ta saki hannunsa, ta bashi shayin ya a masa,ya ce”thanks my Mamie”murmushi tayi,”Abbie ya ce”idan ka gama fushin ka tashi ka tafi Airport ka jira My love tace kai zaka daukar ta.”murmushi Al’ameen yayi dan baya da riko har ya sauka dan idan yayi fushi da Mamie ta lallabashi yanzu zai sauka.Ya ce da Abbie “Abbie tun yanzu baza mu bari sai zuwa dare ba.”Abbie ya ce”Ok ka bari sai bayan sallah magarib”Mamie ta ce “Allah ya kawo dota lfy masu aiki sun gama shirya mata duk abinda take son ci an gyara mata dakinta da komai nata.”Abbie ya ce”Maryam Allah ya miki Albarka yasa ki gama da duniya lfy yadda kike dawainiya dani da yarana da mahaifiyata bamuda abin biyan ki.”Innani ta ce”Ameen gaskiya ba muda Allah ya bar kauna” suka amsa da Amin dan Al’ameen ya saki jikinsa suna hira su, Na’ima ta ce “Bro harda ni za’aje Airport” innani ma ta ce “nima har dani”Abbie ya ce”au ku duka zaku”dariya suka yi atare suka ci gaba da hira.⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐Bangaran Abdallah kuwa ya na ficewa da mashin ya rinka tsula uban gudu saman mashin din,cike da kware wa yake tukin fuskarsa babu walwala amma hakan bai hana tsantsar kyawunsa baiyana ba.Abdallah bai zame ko ina ba,sai paparazzi pack.Lokacin da ya shiga gurin cike ya ke da jama’a samari da yan mata kowa ya zo shakatawa, parking space Abdallah ya shige da mashin dinsa ya ajiye, ya kulle ya sauka, ya nufi farfajiyar gurin. cike da takun kasaita ya ke takunsa kai tsaye Sowimmig pool ya nufa, gurin cike da mata sa ‘ya’yan masu akwai dayawa sun san dan Abdallah, ai kuwa suka nufo gunsa suna ihu, Deena da gudu tayi kansa tana cewa”welcome my Guy i miss u”ta fada zata fada jikinsa ya goce yayi kicin-kicin da fuska ya nuna ta da yatsarsa ya ce”wlh idan kika kuskure kika tab’a mun jiki a yau wlh uwarki sai dai ta haifi wata yar iska marar kamun kai” ya fada yana fucewa gurin wasu korayan kujeru.Jamil ya bishi a baya ya na cewa”haba babban yaro ya zaka mana cin fuska kasan Deena tana sonka saboda kai ta ke zauwa nan kuma kai kace tazo ka rage zafi” Abdallah ko kallon jamil bai ba ya ciro kudi cikin ajihun wandon sa, bai san ko nawa bane ya beka ma, jamil ta baya ya ce”lemo nake buka ta me sanyi ka dai, wannan kudin ya isa kuyi komai bana son takura a yau Ok..? ya fada ya na kallon jamil.Jamil ya ce”Ok Guy”ya fada yana juya wa, Abdallah kuwa ya isa saman kujerun ya zauna ya na kallon ruwan yayi ringeshe ya lumshe shanyayyun idanunsa yana karka da kafafunsa, ya na ciza lips dinsa.Kamar amafarki ya jita a jikinsa tayi kwance a saman kirjinsa ta saki kuka ta rungumesa gam,ta na cewa”My Guy i love u”cike da zafin zuciya Abdallah ya bude idanunsa ya ga Deena male-male saman kirjinsa ta manne sa.Azafafe ya mike tsaye da ita a jikinsa ya ce”dan ubanki har yan zu baki san waye Baffa Babyn Anty Rumaisa ba, baki san lokacin” farin ciki da lokacin bakin ciki ba ya fada ya na sakin ta daga tsaye ta fadi k’asa, ya shakota ya kifa mata wani mahaukacin mari.Cikin tsananin tsoron Abdallah da ya kama Deena ganin yadda kirjinsa ya ke sama da k’asa, bakin ta na rawa ta ce”Babyn… Anty…Rumaisa…ka..yi..ha..kuri…Amma Abdallah bai saurari Deena ba, ya sake wanka mata mari, sai da ta fadi k’asa, hakan bai ishi Abdallah ba ya harbata da kafa sai gata tsumdum ta fada ruwa daman, dab da shi suke Deena ta gigice ga zafin marukan da tasha gashi kan ta dawo haiyacinta ta ji ta cikin ruwa duk da ta iya ruwan ma yau, tsoro ya sa ta kasa ce ton kanta, sai yawo ta ke cikin ruwan har ta fara shan ruwa.Abdallah koma wa yay ya kwanta saman kujera, ya na huci, sai ga Jamil ya iso da gudu ya ajiye ma Abdallah lemon ya na cewa” Haba Babba yaro ya zaka yarfata cikin jama’a , kalli fa kaga idan ta mutu fa”ya fada ya na nufar gun Deena da gudu.Ko kallo bai ishi Abdallah ba, ya tashi zaune ya bude lemon yay bismillah ya kafa bakinsa ya na sha bai sauke bakinsa ba sai da ya shanye tas ya sake daukar daya shima ya shanye, zai dauki na uku ne yaji an damki hannunsa, da sauri Abdallah ya d’ago da kansa, yaga wata yar matashiyar budurwa ta na girgiza masa kai tana murza tattausan hannusa.Can murya a k’asa ta ce”Kyakyawan Guy karka ilata kanka ma wannan manyan…wani matsiyacin kallo ya watsa mata, ai bata san lokacin da ta saki hannunsa ba ta mike a tsorace ta matsa baya, ganin zai mike ta kwasa a guje, baki Baffa ya ciza ya kwanta yana lumshe idanunsa.Jamil kuwa cikin ruwan ya shiga ya tsamo Deena ya fito da ita dama kayan ba abun kirki ba duk sun kame mata jiki haka ya kwantar da ita ya na danna mata cikin ta ruwan da ta dan sha ya fara fitowa daga bakinta, tana nishi ya mata sannu kai ta d’aga cikin wahaltuwa ta ce”Jamil Baffa Abdallah baya sona kalli zai kashe ni wlh ko shine ajalina sai dai ya kasheni bana son kowa aduniya sai shi zanyi yaki da ko diyar uban wacece ta nemi raba mu dashi.Abdallah ya na jin duk abinda Deena take fadi bai dalu ba sanin bashida budurwa sai masu kawo masa hari dan bai taba cewa yana son yar kowa ba, tab’e baki yay ya mike ganin magarib ta kawo jiki, a nutsu ya ke takunsa cikin isa da kasaita yana karkada makullan hannunsa ya bar gurin ko ta kan Jamil bai bi ba, yana zuwa parking space ya hau mashin dinsa ya bashi wuta yaja ya nufi get. Jama’ar gurin kowa kallonsa yake dan mashin din ya masa mugun kyau, a guje ya bar gurin jin an fara kiran sallah magarib.⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐Bayan sallah insha a gagauce Al’ameen ya shirya suka tafi Airport tarbo Rumaisa shi da Mamie da Innani da Na’ima.Da misalin karfe 7:30pm jirgin su Rumaisa ya sauka a Nnamdi Azikiwe international.Har lokacin Rumaisa baccin ta take hankali kwance, Shaheed na tallabo da kanta yadda zata ji dadi.Saida ya ga jama’a an fara ficewa ya tashe suka fito duk kunya ta cika ta dan baccin jiya take ramawa da bata yi ba.Anutse suka fito suna takun su mai cike da aji Shaheed na rike da jakarta da tashi har suka fito bayan sun dauko akwatina su, kowa ya fara raba idanu ya na neman nashi. Shaheed ya hango yan gidansu har mutum hudu da daddy da Ammi da Hamza da Mimi.Cikin farin ciki ya kalli Rumaisa ya ce”My heart kalli family dina pls muje su ganki kinji” ya fada yana langwabe mata kansa.Idanu na zaro cike da mamaki na ce”Haba Shaheed pls kayi hakuri wlh bazan iya ba daga haduwa yau daya gaskiya bazan je ba ni bani jakata…magana ta ce ta tsaya sakamakon hango my bro da nayi da Mamie da innani da Na’ima, cikin murna ina dariya na ce”Shaheed kalli bro na da mamana da kakarmu da kanwata”na karasa maganar ina amsar jakata karama ina jaye da babbar na nufi gunsu Mamie, Shaheed ya biyo bayan ta.Shiko Shaheed yan gidan su cike da mamaki suke kallonsa sai bin Rumaisa ya ke Daddy yayi murmushi ya ce da Hamza”ina ga fa ita ce yarinyar da ya kira ni kafin su taso ya ce yayi matar aure”Ammi ta ce”Wow masha Allah yarinya mai hankali kalli taki zauwa gun mu dan kunya amma shi idanunsa ya rufe ya bita”dariya suka sayi atare suna binsu da kallo su ga iya gudun Shaheed din.Rumaisa da sassarfa ta isa gunsu tayi jifa da jakar ta fada jikin innani ta rungumeta gam tana dariya innani ta ce”ke karki karasa ni mana, sannu da zuwa”kiss Rumaisa tama innani ta saketa ta rungume Mamie ta ce”i miss u Mamie” dariya Mamie tayi ta ce me too dota ya gajiya” Na’ima ta ce”Anty nifa”sakin mamie Rumaisa tayi ta rungume N’aima.Al’ameen ya ce”Rumaisa ni me na kashe miki wai” sakin Na’ima Rumaisa tayi ta nufo gun Al’ameen ta shagwab’e fuska tana bubbuga kafa ta fada saman kirjinsa ta rungumesa gam, ta shagwab’e masa ta ce” my bro kayi hakuri kaji wlh nayi missing d’inka sosai fiye ma da tunanin ka”murmushi Al’ameen yayi ya kara manne ta jikinsa yana buga bayanta.Shaheed ko wani gululun bakin cikine da kishi ya tokare shi duk da ya ga yayanta ne, haka ya iso ya musu sallama, Rumaisa da sauri ta saki Al’ameen ta kalli Shaheed shiko ko kallonta bai ba, ya gaishe dasu innani suka amsa cikin fara’a Na’ima ko idanu ta kura masa.Al’ameen ya bashi hannu Shaheed ya amsa sukayi musabaha, ya musu sallama ya tafi gun yan gidan su.Rumaisa ta bisa da kallon mamaki ko me ta masa yayi banza da ita duk Sai bata ji dadi ba. Al’ameen ya ce”ai sai muje gida ko kanwar ki ce mun kusa shan biki dan naga wani abu”Baki Rumaisa ta zumburo ta sunkuya ta dauki jakar ta karama Al’ameen ya Ja babbar Rumaisa ta kama hannu Innani suka nufi gun mota.Shaheed ya na isa gun iyayan sa ya rungume Daddy Ammi ta ce”wai mun zata can gidan nasu zaka bita” dariya yayi ya ce”Ammi muje gida akwai hira Allah kuwa” dariya suka masa Hamza ya Ja akwatin sa suka nufi gurin mota.Lokacin da su Rumaisa suka isa gida takwas da rabi, na dare, Al’ameen ya na parking Rumaisa ta bude mota ta fito aguje tayi cikin gida tana kiran Abbie.Parlon ta fado aguje, Abbie na zaune cikin keken sa ya ware mata hannunsa, da gudu ta karasa ta fada jikinsa tana murna ta rungumesa tsam ta ce”My Abbie i miss u ya karfin jiki.” Ta fada tana d’agowa ta na kallon sa.Dariya Abbie yayi ya ce”My love Alhmdllh ya gajiya ya yan uwanki da fatan kowa ya na lfy…? Rumaisa ta ware hancin jin kamshin Abdallah na ziyar tar hancin ta, ta ce da Abbie”Alhmdllh Abbie duk suna gaishe ka” ta fada tana sakin sa ta mike tsaye tana raraba idanu, karaf idanunsu ya sark’e da juna ita da Abdallah ya kame saman wata lumtsumemiyar kujera ya dora kafa daya kan daya,kansa ya kauda fuskasa kicin-kicin ya shiga latsa waya, Rumaisa ta saki murmushi ta kalli Abbie ta ce”Abbie yaron nan ya raiwa kansa hankali ya na kallo na shine bazai mun sannu da zuwa ba” ta fada tana nufar gurin Abdallah tana murmushi ta ce”Baby k’anina waye ya tab’a min kai agarin Abuja”ai Abdallah bai bari ta iso ba ya mike tsam ya kara waya a kunnasa ya na takunsa na isassun maza sabon jini ya nufi kofar fita. Baki da hanci Rumaisa ta saki tana kallon sa har ya fice sai taji ta tozar ta dan ta tsani a disga ta har kwalla ta taru idanunta ta iso gaban Abbie ta sunkuya ta rike kafar keken, Abbie muryata na rawa ta ce”Abbiena wa ya b’ata ma Baby Baffa rai, kalli ko kulani bai ba ace wata daya bamu hadu ba amma ya ganin ya mai dani banza”dai-dai lokacin su Al’ameen suka shigo da sallama.Abbie ya amsa musu ya kalli Rumaisa ya ce “My love Baffa ke kika ta boshi ya kira yafi sau dari ba ki dauka ba ya ce ya fita daga harakar ki”abin dariya ya ba Rumaisa ta saki ranta ta ce”au a kan wannan ne wlh tafi nono fari can ya karata nima na huta”ta fada tana dariya ta nufi bedroom d’inta.Dariya Na’ima tayi taja akwatin Rumaisa ta bita ta na cewa”Wa zai shiga tsananin harshe da hakuri”dariya su Mamie suka yi Mamie ta kira Larai da karima masu aiki suka shimfida babbar leda nan saman tafkeken carpet din parlon suka kawo kulolin abunci a ka jera dan mafi yawa haka suke dinner din dare.Rumaisa bayan ta shiga hadaddan bedroom dinta ta cire kayan jikinta ta daura towel ta shige bathroom tayi wanka bathroom din kadai abin kallon ya hadu mutika,Ta jima sosai, kafin ta fito dan saida ta gasa jikinta sosai da ruwan gumi, tayi wanka ta fito.Na’ima tana zaune Rumaisa ta ta fito ta ce”to me kuma kike jira baki fita ba” N’aima ta ce”Anty kiran ki ake tayi a waya shine na d’aga muryar kamar ta wanda muka ganku tare a Airport” Rumaisa ta na goge jikinta da towel ta ce”Ok naji tashi ki fice na shirya jikina”Na’ima ta mike tsam ta fice.Agagauce Rumaisa ta shirya cikin riga da siket yan kanti milk colour wanda suka dan kamata hips dinta duk ya fito rigar ta dan matse ta kirjinta da yake cike dam kamar zasu fasa rigar su fito kayan sunyi mata kyau sosai ta kame jelar kitson ta daure su da ribbon suka koma tsakiyar gadon bayanta batai kwaliya ba turaran ta mai sanyin dadi ta fesa ta dauki wayarta wacce take ta ruri, irin ta Abdallah har kalar ma iri daya ne, bata yi picking ba ganin number ba suna ta nufo parlo.Yan gidan sun jeru a saman carpet suna zazaune suna jiran Rumaisa sai gata,kusan Abbi ta zauna tana murmushi ta riko hannunsa ta ce”Abbie ni zan baka abaki”dariya yay ya ce”My love ki bari kici nima zan ci da kaina”innani ta ce”Rumaisa tashi ki kirawo k’aninki ya fa ki zauwa ya ce baya cin abuncin kinga har marin Na’ima yayi dan ta je kiransa”Rumaisa ta kalli Na’ima tana matsar kwalla kumcinta har yayi Ja abin ka da farin mutum.Rumaisa ranta ab’ace ta ce”ri bar ya ci mana amma meye na dukanta a kan me zai duki mareniyar Allah ko ya manta Amana take a wajansa”ai Na’ima najin Rumaisa ta daure mata gindi ta b’are baki ta fashe da kuka tana cewa wayyo wuyana Yayana ya murde mun wuya bayan marin da ya zuba mun”Rumaisa ranta a mugun b’ace ta mike ta na cewa”wlh ran Baffa sai ya b’aci yau ta “fada tana nufar kofar parlo.Mamie da Abbie da Al’meen suna kiranta ta rabu dashi kar fa suyi rikici dan a sama ya ke ta ce”wlh Abbie sai na wanwanka masa mari yaji idan da dadi ai shima ai ya na da gaba dashi”ta fada tana ficewa daga parlon.Kai tsaye Rumaisa part d’insu Abdallah ta nufa ko ina na jikinta motsi ya ke, tamkar tarwada sai sauri ta ke ta je ta rama ma Na’imah dukan ta.
*+22796515805*