JAMB ta fitar da sabon mafi karancin makin shiga Jami’a Poly da FCE a Najeriya
Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta fitar da sabbin mafi karancin maki (makin yanke) don shiga manyan makarantun gaba da sakandare a zangon karatu na 2022/2023. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa JAMB ta karbi maki 140 zuwa sama a matsayin mafi karancin maki na shiga jami’o’in Najeriya na shekarar 2022/2023. Halatta aikawa. Shugaban JAMB na kasa Farfesa Is-Haq Oloyede ya bayyana hakan ne yayin da yake magana game da shiga makarantar gaba da sakandare a taron tsare-tsare na 2023 a Abuja ranar Asabar. Farfesa Oloyede ya kara da cewa kwamitin ya kuma amince da maki 100 a matsayin mafi karanci don shiga Kwalejin Kimiyya da Fasaha (Poly) da Kwalejojin Ilimi (FCE) a fadin kasar nan. Ya bayyana cewa wannan maki da JAMB ta kayyade shi ne mafi karanci, ba wajibi ne makarantu su bi ba, kuma suna da ikon karawa fiye da haka amma ba kasa da wannan ba. Daga ISYAKU.COM https://ift.tt/XkBngTavia IFTTT