MATATA GIMBIYATA COMPLETE HAUSA NOVEL – Hausa Novels
adsense here
(9:09PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦 MATA TA , GIMBIYA TA!! 🌸💦 💘 MY WIFE ,MY PRINCESS 💘Story byJEEDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOHEDITED BYROOKIEY KAXSBamu yarda wani ko wata ya juya muna labari ba yin haka babban kuskure ne, kuma muka kama mutum zai fuskanci hukunci..BISMILLAHI RAHMANIR RAHIM 1⃣➖2⃣ dole sai kin aure shi Attitude miss DEENAH ISMAEEL!! am talking to you right here as a father! Idan da uban ki ne yayi wannan maganar ai babu musu zaki yarda , amma dayake ni kin raina min wayau tunda ba ni na haife ki ba ,shine bari ki nuna min halin ki na y’an duniya ko? Shegiya da ido kamar dattijon biri!!” Uncle Khamis ne ke maganar cikin hasala , daga gani ranshi a b’ace yake. Amma Uncle how can you make such drastic decision without my consent? Maganar aure na fa kuke yi! Kuma hakan ma da mijin da ban tab’a gani ba! That too mai shekaru irin na ubana!” Deenah ta fad’a tana mai d’aga hoton wani dattijo wanda zai yi about 49 yrs ,idanun ta taf da hawaye. Ke uwaki! Kin ci uwaki nace!! Har yanzu ashe baki rufe bakin ki ba? Munafuka ke a yanda kike har wani zab’e zakiyi ? Mutum a kod’e kamar fentin white house. Aure de kamar anyi an gama! In ma zaki mutu a chan ne kije ki karata ,Yarinya ta d’ebo duk munafurcin uwarta, Tashi ki bani waje ko nayi majejewa dake a nan wajen Shashasha!” Cikin tsawa Uncle yayi maganar hakan ya tsoratar da Deenah ba kad’an ba kamar zata kifa ta mik’e da gudu ta fice daga falo idanuwa sharbe sharbe da hawaye.DEENAH ‘ s POV …. Da gudu na shigo d’aki kaina babu abunda yake yi se uban sarawa , fad’awa nayi a kan gado gami da bunne fuska ta cikin pillow babu abunda nake se faman kuka!Shikenan nima haka rayuwa ta zata kasance kenan? Babu y’ancin kai babu sukuni ,tabbas k’unci ya aure ni , a rayuwa ban san lokacin da farinciki zai dawo min ba, gashi ina cikin kadaici babu kafad’ar da zan dafa in yi kuka , babu uwar da zata rungume ni yanda uwata ta fad’i ta mutu a cikin wahala da k’uncin rayuwa haka nima zan kasance. Kuka na ne ya tsananta sosai na mik’e zaune na nad’e kafata gami da d’aura kaina a gwiwa, My dreams are shattered already ! My dreams of being a physiotherapist is no longer trending! Am gonna end up like my own late mother! Married! Becomes the cook of the family , get pregnant, have no time for herself but for the husband and then after some times she end up heart broken by the man she called husband and in the end! Died and left me in the hands of the most wicked step mom! Bayan wannan kuma nima Y’ata ko yayan da zan haifa zasu kasance a hannun wata uwar daban kamar yadda na kasance ,daga nan kuma suma ayi forcing musu auren dole kamar dai ni ,haka abun zaita zagayawa! Tir da wannan rayuwar!” Jin an k’ira sallar azahar yasa na mik’e ina k’ok’arin bud’e kumburarrun idanuwa na da ‘kyar na fad’a bayi ,bayan nayi wanka na dauro alwala sannan na fito direct closet na wuce na d’auko wata long sleeve Anarkaali dress na zira sannan na d’aura hijabi na fuskanci kibla domin gabatar da sallah! Na dad’e sosai a sujjada ina kai kuka na ga Mahaliccin mu ,ina rok’on yasa wannan auren da za’a min in babu khairan cikin sa yayi watsi da shi ya kuma sauya min da alkahairi ” bayan na idar da sallah sannan na koma kan katifa ta na kwanta naci gaba da business d’ina wato kuka” UNCLE KHAMIS POV…….. Deenah tana shiga ya dubi Aunty Hadiza ( his wife) Wallahi ba don gudun bakin jama’a ba! Da sai na batar da wannan yarinyar! Wai yanzu har tana da bakin da zata iya sa in sa da ni? Har zata iya musayar miyau da ni tsabar rainin hankali? Shegiya fuska kamar an silala karas! Lallai seta yaba wa aya zakin ta! Aure kamar an d’aura ” Aunty Hadiza se yanzu tai magana ” ai Alhaji ka barni da ita! Kafin a kaita ma sena sauya mata kamanni! Ni d’in de take ji yanzu zan nuna mata true colors d’ina” Ai nasan zaki yi fiye da haka! Mudai mu tura ta chan ko zamu samu hujjar cin wannan makudan kudaden da yaya ya bari , ni bazan bari wannan kyanwar ta kwashe min dukiyar d’an uwa ba,ai da kika ga ina sassauta mata kwana biyu ai sassautawar ta raka taki gona ce! Kinsan idan muka sake wani abu ya gifta Baba Yaji cewar bata son auren komai zai lalace!” Sosai Aunty Hadiza ta kufce da dariya sannan Uncle ya mik’e domin zuwa masallaci……….. *************** Deenah! Deenah!! Kut amma wannan yarinyar anyi y’ar kwal uba! Shine ina ta kwala mata k’ira kamar bata nan? Ni wallahy satin ma yayi yazo mu tura ki chan! Mu yada kwallon mangwaro mu huta da kuda! ” Da gudu ta shigo kitchen d’in jiki na rawa kamar zata mutu se haki take yi ” kiyi hak’uri aunty wlhy sallah nake yi shiyasa b…..” Ta dakata sanadiyyar wata tsawa da A Hadiza ta yi ,jiki na b’ari tayi gum da baki . ” Sannu sayyada wato zaki nuna min kin fini iya addini ko? Ke gaki musulma! Munafuka kawai ,tsabar renin hankali ni zan d’aura girki a gidan nan yau? Shine har kina son yin k’arya d’a addini ” ta kwada mata ludayi a tsakiyar kai , wannan ya sanya Deenah rik’e kai hannu biyu tana hawaye tsananin sara mata yake yi amma babu yanda zata yi ,don in da sabo ta riga ta saba” Tunkude ta tayi da k’afa ta wuce zuwa falo tana ta banbami ita kuwa Deenah babu b’ata lokaci jiki na rawa ga uban yunwa ga ciwon kai ta mik’e ta hau k’ok’arin daura dinner………,©(email protected)@H F💘J💘R💘(9:10PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦 MATATA GIMBIYATA!! 🌸💦 💘 MY WIFE MY PRIINCESSSTORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOHEDITED BYROOKIEY KAXSNAGARTA WRITERS ASSOCIATION 3⃣➖4⃣ Zaune suke kan brown mahogany wood dinning table yayinda Deenah ke faman serving d’in su , duk idanun su a kanta ne ita kuwa jiki na rawa take faman zuba abincin. Wani dogon saurayi ne ya shigo ak’alla zai kai 23 yrs ya sha kayan thugs harda knuckles ring , ya baje a falo yana kallon su a dining area “Ke”! Ke Munafuka zo nan! sunan kenan da kowa ke k’iran Deenah dashi shima ya k’ira ta , luckily ta kammala zuba musu abincin dan haka ta saka gudu ta nufi inda yake ta durk’usa gaban sa An gaya miki kyau ne dake da zaki wani zo ki zaune min a gaba? Kazama tashi min ki had’o min coffee yanzun nan! Ba b’ata lokaci ta ruga zuwa kitchen su A. Hadiza kuwa se dariya suke yi khairat ma tana ta aika loma ko d’ago kai bata yi ,idan akwai worst mak’iyan Deenah toh bai kai khairat ba.DEENAH’s POV ……. Cikin minti uku na kammala masa komai na d’aura coffee mug d’in a kan saucer sannan na saka teaspoon a gefe na ajiye two cubes of sugar na fito cikin rawar jiki na mik’a masa Kurb’a d’aya kawai yayi kafin na ankara se ji nayi an watsa min hot coffee a jiki Allah yaso bai sami fuska ta sosai ba. Wurgi yayi da kofin in my direction hakan yasa na sunkuya cike da tsoro yayinda cup d’in yaci karo da marble floor a take ya yi dagadaga , ban ankara ba naji anyi Ball dani da k’afa hannaye na biyu duk na dafe su kan fashasshen kwalban ,kuka na ya tsananta naji duk na tsani wannan rayuwar . ke wato kin maida ni sa’an ki ko? Munafuka! Wato ni kike so in zuba sugar a coffee d’in da hannu na? Wannan d’in sabon falli ne ko kuma me? Sa’an ki d’aya yau y’an mutunci na suna nan Amma ai kin sanni sarai! Zan had’u dake anjima! Duk maganganun da Yaya SAEED yake fad’a kawai jin su nake domin na saba ,bayan ya juya ya fice ne na mik’e na d’aure hannu na sannan na fara aikin kwashe kwalaben , ban jima da gama wa ba Aunty ta kwala min k’ira Tana daga zaune kan dining chair tana d’aukar sauran abincin da suka rage a plate ta had’a a plate d’aya sannan ta ajiye a k’asa tayi wurgi da shi da k’afa , da sauri na d’auka na keb’e a lungu ni kad’ai se daka loma nake! Wannan ma yau d’in taga dama ne don wata rana abincin da ake dafawa karnukan gida shi take cewa naci amma duk muguntar ta babu abunda ya sameni har mayya take k’ira na!*********** Yau jumma’a yau ake shirin d’aura min aure da mijin da ban san shi ba balle halayen shi, keep maganar ko yana kaunata aside don nasan ba makawa wannan auren ba na soyayya suka had’a min ba, sannan hoton da suka bani dattijo ne mai kimanin 49 yrs who knows mata nawa yake da su? This taught filled my heart to the extend that yau ko kuka ma na kasa yi, tear duct d’ina ya daina zubar da ko d’igon ruwa, babu abunda nake banda dua ina kai kuka na ga mai duka mai kowa mai komai! Yayinda kowa yake murna a cikin gida , ina k’unshe a d’aki na had’a kai da gwiwa. Wata tsohuwa ce ta shigo tare da Aunty , ta inda suka shiga ba nan suke fita ba wai nasiha , ” In har kikayi wani kuskure auren ya mutu toh lallai ki nemi wani wajen ba nan ba!” Kalaman ta kenan na k’arshe daga nan tsohuwar ta d’aga ni muka fita. Wani ikon Allah ban tab’a ganin aure haka ba! Babu kayan daki babu komai daga ni se ni kamar wanda suka bada ni sadaka , daga nan ne kuka na ya karu ban san cewa akwai sauran hawaye a idanuwa na ba se lokacin da ake fitar da ni daga gidan ubana mahaifi kamar ana kora ta! Babu wanda zan yi wa kuka yaji ni! Haka suka saka ni a mota ba tsimi babu dabara Aure de an d’aura! Ango of which i regard to as mr unknown!! K’arfe 3:30 pm At BEN KALIO HOUSING ESTATE DAMATURU YOBE STATE…… Wani makeken gate muka ratsa driver ya yi parking daidai entrace ,jiki na rawa yake yayinda na sako k’afa daga mota ,daga cikin dupatta na ( gyale na ) ina iya hango fuskokin su d’aya bayan d’aya Cikin zuciya nace ” What a family ! Look how happy they seems ! Basu san yadda nake ji ba wlh da sun sani non of them will give such a wide grinn Har cikin main falour akayi leading d’in mu finally na tsinci kaina zaune kan lallausan italian carpet , haka dai suka sani a gaba suna ta surutu wancan yace kaza wancan ma haka Hmmm da kun san yadda nake ji a raina game da auren nan lallai baza ku b’ata lokaci ba! I mean like seriously? Har ma farin ciki sukeyi wanda na kasa fahimtar me yasa , uwar ango harda hawaye. A raina nace ” amma de wannan matar ai d’an nata indai shine nagani a hoto ai yafi ta tsufa!” Maganar mahaifiyar sa ne ya dawo dani daga nannauyan tunani da na tsunduma Y’ata ya kamata ki huta , gobe in sha Allah zaku wuce a kaiki d’akin ki! Na gode miki sosai domin mata irin ku kad’an ne a duniya wanda duk da kunji yanda mutum yake kuke amincewa kuyi abu don Allah! Ni na san in Allah ya yarda Allah zai baki ladan abunda kika yi” Ba tare da na fahimce ta ba nayi murmushi gami da amsawa da Ameen daga nan aka kaini wani d’aki inda nan ne na zauna nida wasu y’an mata biyu muna ta hira har bayan isha muka kwanta!Zan iya cewa yau ne rana ta farko bayan rashin iyaye na da na tab’a kwana cikin dad’in rai da kwanciyar hankali! Amma tunani d’aya tak ya hana ni sukuni! Is it because d’an nata tsoho ne? Ko kuma dan na yi auren dole ba tare da wani musu ba? Or akwai wata matsala ce? Kuma how sure am i, wannan Dattijon shine wanda aka aura min?” Wannan tunani dashi nayi bacci ……………© (email protected)@HF💘J💘R 💘(9:09PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦 MATATA GIMBIYATA!! 🌸💦 💘 MY WIFE MY PRINCESS 💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 5⃣➖6⃣ Kiran sallah ne ya tashe ni , a hankali nake bud’e idanuwa na ina mai k’arewa d’akin kallo wanda yanzu kam duhu ne cikin sa a kasalance na kai hannuna kan switch na bedside lamp ina zaune bakin gado ina tuna abubuwa da dama da suka faru yayinda hannaye na suke shawagi cikin messy gashin kai na bayan nayi alwala nai sallah na rok’i mahalicci ya min jagora a wannan alamari , ban tashi daga sallaya ba wata mata ta shigo d’akin da sallamar ta tace ” Amarya ga abinci nan ki ci sannan ki shirya da wuri don yanzu zaku wuce ” kai kawai na girgiza domin bani da wata ja akan maganar se yanda aka yi dani. Da murmushin ta tafita yayinda na maida dubana ga abincin! Tunda na taso ban tab’a ganin ranar da aka had’a min breakfast irin wannan ba hasalima sedai in ci ragowar yan gida Tsakanin jiya da yau se naji am like free! Yau gashi na wayi gari na tashi cikin nutsuwa babu tsawar Aunty hantara daga yaya Saeed da kuma khairat ! It feels new to me!…… Bayan na kammala breakfast sannan na shiga bayi na sakar wa kaina shower ban d’auki dogon lokaci ba na fito just to find out kaya na yana jira na a kan gado had’e da tsadadun turare guda biyu ga kuma wani simple gold jewelry ajiye a gefe ban san wanda ya ajiye su ba don haka na shafe jiki na da mai na zauna ina jiran shigowar wani, and luckily se ga matar d’azu ta dawo .” Yawwa kin fito ashe?”Tace, “eh nafito” Wad’annan kayayyakin ki ne driver is almost ready ki shirya bari inyi magana da umma kafin nan, nan ma dai kai na girgiza fuska ta d’auke da murmushi sannan ta fice. Doguwar riga ce long sleeve “ja” bodice d’in kuwa black and golden lace ne haka ma boader d’in hannun da kuma borderline na rigar , rigar ba karamin had’uwa tayi ba ni kaina saida nai kauyanci sannan na saka ba wani heavy makeup nayi ba yafa black and gold kashka dupatta nayi sannan na fito zuwa falo bayan yan nasiha da kuma godiya daga mahaifiyar sa wanda ni kaina ban san dalilin yin su ba finally na tsinci kaina cikin wata bak’ar Mercedes Benz muka hau hanyar Maiduguri abun takaicin ma shine daga ni se driver , an saka ni a owners kamar wata matar shugaban k’asa ! To be frank wannan rayuwar bak’uwa ce a gareni……….. Bayan tafiyar Awa d’aya da yan mintina suka iso garin Maiduguri direct Airport driver ya direta , to her surprise wai Abuja za’a kaita thank God i know something about Flight and stuffs ! Abunda ta iya fad’a kenan, cikin minti goma jirgin su ya d’aga zuwa Abuja …………….*************** A yayinda motar ta tsaya idanuwa na rufe suke ina tuna irin abubuwan da suka faru da ni a baya, tabbas nasha wuya gashi kuma an had’a min aure an katse dukkan mafarki na maganan driver ya dawo dani daga tunanin danake yace “Ranki shi dad’e mun iso ” kafin na bud’e k’ofar har ya bud’e min karo na farko a rayuwa ta naci karo da Mansion wanda ya amsa sunan shi Mansion ! Daganan zuciyata ta fara raya min abubuwa guda biyu! Kodai sun aurar da ni don su kwashi arzik’i ko kuma sun aurar da ni don in zama baiwa! Domin ban ga me mai kud’i wanda ya ajiye wannan masarauta in the name of mansion zai yi da low class gal iri na ba! Gaba na fad’uwa ya fara yayinda na juya naga nisan dake tsakanin gate da main House d’in. Gida ne nagani na fad’a tall French windows ne suka fara min sallama ya d’auke ni lokaci kafin na fahimci k’ofar gidan daidai lokacin ne wannan tsohon da ke jikin hoton nan ya fito daga cikin gidan yana washe hak’ora ” Barka da zuwa ranki shi dad’e ! Ki k’arasa ciki master yana jiran isowar ki tun d’azu , kiyi hakuri da kalaman sa, ba haka yake ba kafin yanzu, larura ce, kuma magana d’aya master yake yi bai cika son shishigi ba. Ummmm kiyi hak’uri madam amma dole ne inyi miki sharar fage a kansa domin he’s hard to be with ina son ki kasance mai hak’uri don Allah! Zaki iya shiga..” Like seriously? Wai sharar fage aka yi min akan Master? Wai wane irin game ne wannan? Tsohon da nake tunani shi aka malkala min ba shine miji na ba wani ne daban? Yanzu kam na tabbatar ko daga maganar tsohon nan cewa zaman bauta nazo yi ba na aure ba……. Mahmoud i told you for the last time i don’t need any body’s help! Ni bana son wannan auren! Naji am paralyzed amma kuma i can use my hands banga amfanin kawo min wata mayaudariya a matsayin mata ba! Ko baka gani ba yadda Zeenat ta watsa min ‘kasa a ido? To hell with this married! Now get the hell out of my sight! Ka b’ace min da gani nace!!!” Abubakar SADEEQ IMAM kenan yayi maganar cikin tsaya yayinda ya yi watsi da tray d’in abincin dake gaban shi yana mai k’ok’arin juya akalar wheelchair d’in shi. Mahmoud PA d’in shi ne , tunda larurar ta samu Sadeeq yake iya k’ok’arin shi don yaga ya samar wa mai gidan shi kuma Aminin shi kulawa ta musamman ,amma with every day temper d’in Sadeeq karuwa yake a yanzu babu kalmar da ya tsana irin ya mace….. Daidai lokacin na shigo falon kenan hasalima tray d’in abincin saida ya kusan fad’o min a fuska domin da iya k’arfin shi ya wurga, ban san lokacin da na saki ihu ba gami da sunkuya wa jiki na yana rawa, ” What the jahannam” Wannan shine master d’in? Allah sarkin Halitta tabbas ko daga zaunen da yake yi bai bani wahala wajen tantance cewa shi dogo ne ba yanayin fuskar sa square shape ne mai d’auke da madaidaitan oval shaped eyes, hanci kuwa kamar zai shige baki, gashin kansa bak’i ne ga dukkan alamu mutum ne wanda yake barin suma a ka ga wani side box bak’in k’irin , gashin idonsa kuwa badon namiji bane zance fixing yayi ga kuma cikar gira daga hannun sa zaka gane cewa maji k’arfi ne kuma ga dukkan alamu baya wasa da nutrition nashi, tabbas Sadeeq yakai namiji ta fannin sura ina ma ace zuciyar shi haka take da kyau? Domin yayin da na had’a ido dashi karo na farko kallon da yayi min ji nayi kamar an jefa ni cikin wuta, a take naji zufa ya karyo min duk da de yaya Saeed mugu ne tabbas wannan ya fishi razanar wa!! Cikin husky voice nashi yace ” Dubi Tray d’in ba kanta yayi ba amma tana cilla ihu wannan ne kake tunanin zata kula da ni?” Oh! For God sake me kake tunani Mahmoud? Mace will remain mace in as much as am concerned so pls before i vomit ka d’auke min wannan dirty figure d’in a gaba na !!” Jiki ba kwari Mahmoud ya nuna wa Deenah hanyar d’akin ta…… Cikin kuka mai tsanani na zube a kan makeken gadon dake d’akin ina zubar da k’walla ga uban yunwa da kishirwa amma sam babu abunda nake tunawa se irin wahalar da zan sha a wannan prison d’in don lallai ba makawa am in a dungeon! Wannan shi ake kira ba’a rabu da bukar ba an haifi Habu!! Kiran sallar Azahar ne ya tasheni daga nannauyan baccin da nake wanda bashida maraba da baccin dole a lokacin ne idona yayi capturing view d’in d’akin Masha Allah shine kalmar da bakina ya fara furtawa yayinda k’afafu na suka saukaa a kan lallausan posh italian carpet ja dake d’akin , daga glass ne dogin French windows ina iya hango had’adden balcony wanda akayi decorating karamin space d’in shi da Arabian lamps da kuma Arabian darduma lallai kudad’e suna inda suke.! Bathroom na shige direct don gabatar da alwala ta amma me? Yayinda naci karo da full length mirrows ga wani chandelier a tsakiya me golden light ,k’ark’ashin sa kuwa jacuzzi ne makeken gaske infact da kyar na iya yin alwala na fito don i prefer the bathroom than the bedroom seriously! Its breathtaking!! And mind blowing!!!………….© (email protected)@HF💘J💘R💘(9:10PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦 MATATA GIMBIYATA🌸💦💘 MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 7⃣➖8⃣ASALIN LABARIN Alh Umar haifaffen d’an damaturu ne yana da mata d’aya mai suna Zainab da yara biyu, Khamees ne babba sannan Ismaeel shine k’arami. Bawani kud’i Alh Umar kedashi ba saidai rufin asiri, amma duk da haka yaba yaranshi ilimi boko da arabiya. shekarar da khamees yagama university Allah yayima mahaifinsu rasuwa ba k’aramin razana sukayi ba kwanan Alh umar talatin da rasuwa Hajia Zainab ta bishi sunyi kuka kamar zasu rasa ransu amma daga baya suka dangana suka barma Allah komai, daga nan Khamees yafara kasuwanci ganin yaba ma d’an uwanshi ilimi, ana haka Allah ya had’a Khamees da Hadiza bai tsaya bincike ba kawai ya aika neman aurenta kuma iyayenta suka amince, cikin kwanaki k’alilan akayi bikin Khamees da Hadiza.. Kulawa sosai suke ba Ismaeel daga Khamees har Hadiza, Ismaeel na 300level Hadiza ta haifi d’an ta mai kama da babanshi sak, zoka ga murna wajen Ismaeel ranan suna yaro yaci suna Saeed, tun daga nan rainon Saeed ya dawo hannun Ismaeel. cikin ikon Allah Ismaeel har yagama karatunshi bai samu wata matsala ba. Tunda Ismaeel yagama makaranta Khamees yabashi dukiyarshi ta gado nan Ismaeel yafara business import and export, ma’ana yana kai atamfofi materilas Ghana, South Africa yana kuma kuma shigo da nasu Nigeria cikin ikon Allah kasuwancin ya karb’eshi saboda yafi yayanshi nan fa Khamees da Hadiza suka fara yimashi hassada amma bai tab’a canja masu ba kuma komai nashi idan yasamu Saeed… Ismaeel ne tafe cikin motarshi saurayin d’an matashi kenan maiji da naira, tsaye suke bakin titi da Alama abun hawa suke jira, har ya wuce yadawo sallama yamasu amsa mashi tayi yace “yanmata ina zaku haka?” Murmushi tayi tace “wlhi kaganmu nan bak’ine mu biki mukazo shine muke neman abin hawa ya kaimu can gidan bikin” kallon su yayi tabbas ba yan garin baneba, daga wane gari kuke? Tambayar da yamasu kenan, Kausar tace “Maiduguri” murmushi yayi yace “toh kunsan gidan?” Girgiza kai tayi amma muna da address d’in, toh karku damu in shaa Allah zan kaiku godia ta mashi, sai a sannan d’ayar tayi magana, haba kausar taya zamu bi mutumin da bamu sani ba? Nikam ba inda zani, murmushi yayi karki damu yanmata niba mugu baneba trust me. Dakyar aka samu ta shiga motar… Tunda suka shiga mota Ismaeel ke masu surutu kausar na tayashi, amma d’ayar k’ala bata ceba, kallon Kausar yayi yace “wai yar uwarki bata magana ne? Ko maganan tsada takeyi” murmushi tayi karkadamu miskila ce haka take dariya yayi yace “aikam yau ta had’u da d’an naci” itadai bata ce komai ba, har suka iso gidan biki godia Kausar ta mashi girgiza kai yayi babu komai fita zasuyi yayi lucking motar juyawa yayi yace “baiwar Allah dan Allah ki daure ki gayaman sunanki” a dak’ile tace mashi “Falmata” lumshe ido yayi yace “nice name” bud’e motar tayi ta fita, exchaging contact sukayi shida Kausar kana sukayi bankwana…. Falmata bata bar damaturu ba saida soyayya mai k’arfi ta shiga tsakaninta da Ismaeel, randa Ismaeel yajema Khamees da maganan auren Falmata nan yace mashi bazai aure ta ba akanmi zai auro yar maiduguri kowa yasansu da mallake namiji, nanfa Ismaeel yace “shikuma baiga matar aure ba sai Falmata” Bai ankara ba yaji saukari mari a kuncinshi dafe kunci yayi idon shi ya kad’a yayi ja kamar an watsa mashi barkono, tab’e baki Hadiza tayi tace “aidama nasan za’ayi haka tunda yace zai auro yar maiduguri komai zaiyi” saboda kowa ya sansu da mugun asiri, girgiza kai Ismaeel yayi ya fita daga gidan…. Fitar Ismaeel bai zame ko ina ba sai gidan yayan babansu, cikin ikon Allah kuma ya sameshi nan ya gaya mashi komai, murmushi yayi yace “ka kwantar da hankalina in shaa Allah anyi auren nan angama” shida ya auro wadda yakeso wani ya hanashi? Gashi tunda ya auro ta ya daina mana abinda yake mana komai daga ita sai danginta, kaje kawai zanzo na sameshi har gida, godia Ismaeel yayi sosai bankwana yamashi ya aje mashi kud’i masu yawa ya tafi.. Har gida kawu ya sami Khamees yamashi tatas, kuma ya shaida mashi aure ba fashi jibi ma in shaa Allah za’a kai kud’in neman aure kuma dashi za’a kai, ba yanda Khamees ya iya dan dole ya amince, kallon kawu yayi yace “Kawu amma dan Allah Ismaeel karyayi nisa dani ya zauna d’ayan part d’in can” Kawu yace “bakomai zan mashi magana Allah yamaku albarka” amsawa yayi da Amin,…© (email protected)@H F💘J💘R💘(9:11PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦 MATATA GIMBIYATA💦🌸💘 MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BY JEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 9⃣➖🔟 Kawu na isa gida ya kira Ismaeel a waya, ba’a jima ba sai ga Ismaeel bayani kawu yamashi yanda sukayi da Khamees saida kawu ya nisa kana yace “Ismaeel Khamees ya rok’eni alfarman ka zauna d’ayan part d’inshi ni kuma na amsa mashi” da sauri Ismaeel ya d’ago, murmushi kawu yayi yace “karka damu Ismaeel in shaa Allah ba abinda zai samu matarka” sai a sannan yayi magana yace “to kawu gidan fa da na gina?” shiyasa nace karka damu bawai zaku zauna ba nan har abada ni da kaina zan umurceka da kukoma gidanka, ba yanda Ismaeel ya iya haka yama kawu bankwana yatashi ya fita… Ba a d’auki lokaci ba su Kawu sukaje neman Auren Falmata, gaskia sun ga kara saboda an amshe su hannu biyu, abun har ya dinga ba Khamees mamaki, amma duk da haka tsanar Falmata na nan cikin ranshi bare da yaganta, nan su Kawu suka nemi aure kuma aka basu dangin Falmata suka yanka sadaki dubu hamsin nan take Kawu ya biya, aka tsaida biki sati hud’u da yake ko wane b’angare a shirye suke, kwanan su kawu d’aya suka dawo damaturu cike da karamcin mutan maiduguri…. Tunda Kawu ya gayama Ismaeel an bashi Falmata kuma an biya sadaki yake cikin murna, lefe ya had’a naji da gani yana kawowa gida Hadiza da Khamees sukace yayi yawa dole sai ya rage nan fa suka fara rigima har saida Kawu ya shiga maganan ya kuma hana a rage, a cewar shi kowa rabonshi yake ci dan haka baiga illar dan miji yama matarshi sutura ba, dan dole Khamees da Hadiza suka kyale lefen ba dan ransu ya so ba… Tun da bikin yazo Ismaeel baya zama, Khamees har mamaki yakeyi yanda Ismaeel ke rawan kai a bikin nan Hadiza tace “ba dole yayi rawar kai ba tun da ya auro mana dangin asiri” ba ayi wani event ba kasancewar Falmata bata san wani event ko d’aya ba yanda Ismaeel ya iya walima kawai sukayi, ranan juma’a aka d’aura aure ana gama d’aura aure aka taho da amarya damaturu, kwanan yan kai amarya d’aya dama turu suka juya maiduguri…. Hadiza ce tsaye bakin k’ofa tana kwalama Falmata kira ke! Da sauri ya fito kallonta tayi shek’ek’e tace “wakika aje da zai maki gyaran gidan? Dallah fito malama kifara aikinki kina tunanin hutu kika zoyi to bauta kikazo yi” bata ce komai ba ta bita sharan gidan tafarayi tana gamawa ta d’ora girkin kitchen Ismaeel ya tarda ta nan fa yafara masifa, kallonshi tayi da murmushi tace “karkadamu mijina bautan aure nakeyi dan Allah karka masu magana kaga gaba suke damu dole mu bisu”. Tunda nazo gidan nan nagane Anty Hadiza da ya Khamees basu sona amma kullum burina na kyautata masu harta Saeed sun dasa mashi k’iyayyata, kwantowa yayi bisa jikinta yace “kiyi hak’uri in shaa Allah kwana kad’an zamu koma gidanmu” murmushi tayi ta cigaba da aiki.. Tunda Falmata ta samu ciki take fama da laulayi kullum cikin amai take, amma duk da haka dole sai tayi aiki ba abinda ta dainayi, kullum kuma cikin kwantarma Ismaeel take da hankali akan karya damu.. Wata tara cif ta sankato d’iyarta mai kama da ita, tunda aka haifeta Ismaeel yake cikin farin ciki, a yayinda Khamees da Hadiza ke cikin bakin ciki.. Ranan suna yarinya taci suna DEENAH bayan suna Ismaeel duka k’adarorinshi ya maidasu sunan Deenah, nan fa hankalin Khamees da Hadiza ya tashi, babu yanda basuyi ba dan suga sun kauda Deenah daga dunia amma Allah bai basu iko ba, watanni biyu da haihuwan Deenah Hadiza ta k’ara haihuwa itama tasamu mace ranan suna aka sama yarinya ummul Khairi.. Tunda Deenah ta taso cikin so da k’aunar iyayenta komai suka samu ita da zaran ta fita sai tadawo da kuka saboda Saeed zalintar ta yakeyi kuma ba’a hanashi kullum cikin gallaza mata sukeyi har takai ga bata fita saboda da ta fita sai tadawo da kuka tun abun na damun Ismaeel har yakai ga ya hak’ura, Haka rayuwa ta cigaba da tafiya kullum da azabar dasu Khairee kema Deenah, BAYAN SHEKARA BIYARZaune suke parlor suna fira da gudu ta shigo tana kuka, jawota yayi jikinshi ya rungume yace “Deenah kiyi hak’uri da irin abinda zaki gani gidannan kinji ko watarana sai ya zama labari” hawayenta ta goge tace “Daddy miyasa su Uncle suka tsaneni?” Bafa mai sona cikin su, Falmata tace “ba tsanarki sukai ba kinji ko” daina kuka, tashi mu raka babanki ke yake jira dama kidawo tafiya zaiyi… Har wajen mota suka rakashi, yana shiga mota sai kuma ya fito shafa kan Deenah yayi ya kalleta yace “my dota ki tsaya kiyi karatu in shaa Allah duniya sai tayi alfahari dake” d’aga kanta tayi tana hawaye, kallon Falmata yayi yace “ga amanar Deenah nan nabari a hannunki dan Allah ki bata ilimi” ita kanta hawaye takeyi tace “in shaa Allah saika rayu da Deenah”, girgiza kai yayi ya juya ya tafi bud’e mota yayi sai kuma ya k’ara juyowa shima hawaye ya keyi, hawayen ya share kana ya shiga mota, d’aga mashi hannu sukeyi har saida yafita tunda yatafi Falmata ke kuka wanda ta rasa dalilin yinshi…. Kad’an kad’an Falmata zata duba wayanta, ga bugun k’irji da takeji number d’in Ismaeel tayi try amma sai tajita kashe, k’irjinta ne ya cigaba da bugawa, kamar daga sama taji kuka da sauri ta tashi ta saka hijab taja hannun Deenah suka fita……© (email protected)@HF💘J💘R💘(9:10PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸💘MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 1⃣1⃣➖1⃣2⃣ Suna fita suka ga wasu mutane su biyu sai kuma mutum kwance k’asa, ga Khamees sai rusa kuka yakeyi, matsowa tayi tace “miyafaru?” Babu wanda ya amsa ta, saidai taji d’aya daga cikinsu yace “hak’uri zakuyi accident ya samu kafin ya k’arasa mutuwa shine ya bamu address d’in gidannan” da sauri ta k’arasa dan taga waye… Tana bud’ewa ta ganshi kwance kamar yana bacci idonta ta k’ara murzawa taga kodai mafarki take, tabbas ba mafarki bane ba Ismaeel d’inta ne. Kuka ta fashe dashi tace “haba Ismaeel ya zaka mana haka? Ya zaka tafi kabarmu cikin duniyar nan mai cike da k’unci pls katashi nasan baka mutu ba” kuka take sosa ashe dama mutuwa kakeyi shiyasa kake ban amanar Deenah. Matsawa Deenah tayi inda gawar baban take ta kwanta bisa shi tace “please Daddy wake up nasan baka mutu ba wasa kake mana”, saboda malaminmu yace duk wanda ya mutu bazai dawo ba, kai ko nasan ba zaka mutu yanzu ba baza ka mutu kabarmu wajen su Uncle ba dan zasu cigaba da zalintarmu please Daddy ka tashi, babu wanda Deenah bata saka kuka ba, jawota Falmata tayi jikinta tace “kiyi hak’uri Deenah Daddynki ya rigamu gidan gaskia” yanzu zamu shiga wata jarabawan, d’aga hannu tayi sama tace “Ya Allah kabani ikon cinye wannan jarabawan, ka bani ikon cikama Ismaeel burinshi na ganin naba Deenah ilimi mai amfani… Haka aka shirya Ismaeel suna gani aka d’aukeshi aka tafi dashi gidanshi na gaskia. Yan maiduguri sunzo saida akayi sadakan uku kana suka sami Khamees dan shaida mashi suna so su tafi da Falmata, Khamees yace “ba matsala amma ba zasu tafi da Deenah ba saboda shine babanta” tunda Falmata taji bazata tafi da Deenah ba tace “bazata je ba itama saboda tanasan cikama Ismaeel burinshi” , dan dole suka tafi suka barsu.. Rasuwa Ismaeel da kwana bakwai Khamees yazo ya karb’e duka takardun k’adarorin Ismaeel, acewarshi shine ya dace da ya rik’esu ba Falmata ba, haka Falmata ta bashi ba tare da ta nuna wata damuwa ba, burinta kawai taga ta cika ma mijinta burinshi na ganin Deenah tayi karatu… Haka rayuwa ta cigaba kullum su Falmata cikin k’unci suke sunyi bak’i sun lalace kullum da azabar da ake masu ita da d’iyarta. Abinda yafi d’aga mata hankalin yanda Khamees ya cire Deenah daga private school ya mai data LEA ba yanda ta iya haka ta hak’ura amma abin burgewa tun da Deenah ta taso mai k’ok’ari ce komai da an fad’a mata take d’aukewa sab’anin Khairee da bata gane komai…. Bayan rasuwar Ismaeel da shekara biyu, kwance take k’udundune Deenah ce kusa da ita tana mata fita da kyar ta d’ago ta kalli Deenah kamo hannunta tayi ta matse cikin nata ta kusa rabin awa haka, can ta sake kallonta kiranta tayi da “DEENAH” amsawa Deenah tayi da naam, kiyi hak’uri da duk halin da zaki tsinci kanki, na tabbata Allah na tare da ke ba zai bari ki wulak’anta ba, ki rik’e mutuncinki duk inda kika samu kanki, ki rik’e ibada in shaa Allah zakiyi dariya watarana cikin kuka Deenah tace “Mummy miki keson gaya mani? Kema zaki barni kamar yanda Daddy yabarni dan Allah Mummy ki zauna dani karki barni” hawaye Falmata ta share tace “Allah bai barin wani dan wani yaji dad’i” da Allah na barin wani da mahaifinki ya zauna damu inaji araina na kusa barin dunia kamar yanda mahaifinkin yabarta, dan ciwon zuciyar nan ba zai barni ba shiyasa nake maki nasiha da ki kula da kanki da mutuncinki dan nasan babu wanda zai damu dake… Kuka Deenah keyi sosai, cikin sheshek’ar kuka tace “ya rayuwata zata kasance babu iyayena a duniya?” Inama mutuwa zata d’aukeni nima dana fijin dad’i, jawotw Falmata tayi jikinta tace “kidaina fad’an haka d’iyata Allah na tare dake kuma yasan halin da kike ciki shi zai kareki”.. Tashi ki d’auko man ruwa, jiki ba kwari Deenah ta mik’e, tana tashi taji mahaifiyarta ta fara kalmatush shahada, da sauri ta k’araso inda take amma kafin ta iso rai yayi halinshi tabbas a yan k’ananan shekarunta tasan mahaifiyarta ta mutu. Kuka ta saki mai tsuma rai tace “shikenan na dawo banda kowa” mutuwa ya zakiman haka kin rabani da iyayena miyasa baki bari na rayu da su ba? miyasa baki had’a dani ba? Haka ta dinga sabbatu, tafiya tayi part d’in Hadiza tana kuka tana isa ta daka mata tsawa dole Deenah ta had’iye kukanta, cikin kuka tace “Mummy ta rasu” da sauri Khamees ya mik’e ya nufi hanyar fita binshi sukayi, yana isa ya tab’ata, tabbas ta rasu abinda yace kenan…. Haka aka shirya Falmata aka kaita gidanta na gaskia, duk wanda yaga Deenah sai ta bashi tausai dangin Falmata sunzo, sunyi sunyi Khamees ya basu Deenah amma haka yak’i amincewa sukayi fushi suka tafi… Tunda Falmata ta rasu Deenah ta koma gidan Khamees da zama… Haka rayuwan Deenah ta cigaba kullum da sabuwar azabar da suke mata, wankin khairat ita keyinshi ga duka da Saeed ke mata, da ta d’anyu mistake zasu fara dukanta… Kullum cikin nacin karatu take saboda burinta ta cikama mahaifanta burinsu, amma ba kullum ake barinta zuwa makaranta ba. Shekarar da sukayi SSCE Uncle Khamees yace aure zai mata dan baiga amfanin karatun ta ba, tayi kuka ta rok’eshi akan yabarta ta cika burin mahaifanta tazama cikakkiyar likita, ranan saida tasha duka dan taron dangi suka mata shida Anty Hadiza saida suka ga bata, motsi kana suka kyaleta, kuma ya shaida mata aure babu fashi, da kanshi ya nuna mata hoton mijin da zata aura, cikin kuka tace “Uncle wannan ai ya girmi babana pls karka aura manshi” dariyar k’eta Anty Hadiza tayi tace “wlh aurenki da wannan mutumin babu fashi” ke ko gawarki ce sai an kai mashi, Tashi tayi ta shiga d’aki tana kuka, cikin kuka tace “naso na cika maku burinku na ganin na zama likita” amma gashi hakan bai yuwa saboda za’a aurar dani ga mutumin da ya girmi mahaifina, Allah ka kawoman mafita…. Tanaji tana gani aka d’aura mata aure da tsohon da bata sani ba.. Abun mamaki tana zuwa taga ba tsoho baneba, amma yanda taga tsanarta a cikin idon mijinta ya d’aga mata hankali dan tabbas tasan wata uk’ubar ce zata shiga…Shin ya zaman Deenah da Abubakar Sadeek Imam zai kasance? Shin zai so ta ko kuma zasu rabu da juna? burinta zai cika naganin ta zama babbar likita? Ku cigaba da binmu in shaa Allah zakuji amsoshinku….© (email protected)@HF💘J💘R💘(9:10PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸💘MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS1⃣3⃣➖1⃣4⃣Back to story…….. A kasalance na fito daga d’aki gabana se dukan uku uku yake duk Allah Allah nake kar in had’a ido da Mr Sadiq Imam , doguwar riga ce ta atamfa wanda na ci karo da shi cikin wardrobe na saka , wani ikon Allah kamar an gwada akayi dinkin. Yayinda nake saukowa daga stairs d’in ina iya hango mutum zaune a dining section na makeken living room d’in, Gosh !! A lokaci guda na kasa d’auke idanuwa na daga gareshi yayinda yake taunar fried potato chips wanda yasha tomato ketchup , the man is breathtaking and charming physically! Allah kad’ai yasan dalilin bacin ransa da mata! Ko me ma ya dawo dashi paralyzed? Oho?……. Ba kamar yadda kike tunani bane cewa am paralyzed! tajiyo husky voice nashi ya doki kunnen ta, ya dawo da hannayen sa kan control na wheelchair d’in ya waigo yana facing inda take yaci gaba da fad’in Zaifi miki sauk’i kada kiyi shishigi! Aikin ki a gidan nan bai wuce shara da goge goge ba! Shima kuma na d’auke miki flat d’ina so all i want from you is stay away from me! Kada ki dinga yin garajen had’a ido da ni, also am not interested in your helping hand, zan iya yin komai da kaina tunda Allah ya hore min hannu i don’t need anybody’s help! Shishigi dai ina dad’a jan kunnen ki akai And don’t worry I’ll pay you, your salary starting from this month idan hakan yayi miki zaki iya zuwa ki karya, and also Young lady for your information akwai kwararriyar Nutritionist a gida ba se kin yi girki ba am not sure ma zaki iya aiki da appliances d’in so gudun karkiyi wa kanki asarar mummunan fuskar nan zai fi miki kar ki yi garajen girki… Na dad’e a tsaye baki a bud’e cike da mamaki, ko da nake zaman wahala ban tab’a ganin mara mutunci irin Mr Imam ba ,shi d’in na daban ne, Wato ma y’ar k’auye ya maida ni? Ai kuwa ban san lokacin da hawaye suka soma gangarowa ba, na koma d’aki da gudu. Fad’awa kan gado nayi nace “daman haka auren yake?” Wannan tozarcin shine sauran mata ke fuskanta? Kodai ni d’in ce kawai? Wannan wace irin kaddara ce?.. Nikima tawa k’addaran haka tazo, lallai rashin iyaye ba k’aramin abu baneba hawayen da suka gangaro man ne na share su, Nasihar Mahaifiyata na tuna “inda take ceman Deenah kiyi hak’uri da duk irin abinda zaki gani a dunia, in shaa Allah watarana zaki dariya….” Toh yaushe ne zanyi dariyan? Tambayan da banda amsar ta, murmushi nayi in shaa Allah zan jure kowace matsala ce daga wajen wanda ake kirana mijina, dan gaskiya banga k’iyayya ta a idonshi ba kamar yanda na ganta a idon su Saeed, akwai dai abinda mace ta mashi yasa ya tsani mata, koma miye a sannu zan sanshi kuma saina kauda mashi tunanin duk mata haka muke, saina canja mashi ra’ayi… Murmushi nayi na tashi dan naje na karya, ina isa downstaire na ganshi yana k’ok’arin tura wheelchair zai d’auko ruwa, da sauri na isa wajenshi na turashi yana d’auko ruwan daidai muna had’a ido wata zabura da yayi ya dakaman tsawa saida na kusa fitsari, ruwan ya watsoman bansan sanda na saki k’ara ba na duk’e k’asa… Wace irin jakka ce ke? Banace bansan taimakon ki ba? i don’t need anybodys help, Angaya maki banda hannu ne? Tun yanzu kenan ba’a je ko ina ba kin fara karyaman doka, hmmmm mata duk halinku d’aya na tsaneku wannan ya zama na k’arshe da zaki shiga harkata, dan haka get out from here, kasa tashi nayi saboda tsabar razana nayi, da k’arfi ya k’ara maimaitawa a said get out da gudu na tashi na haye sama ina kuka… Ina shiga d’aki na banko k’ofa kan gado na fad’a ina kuka, ni kuma haka tawa k’addaran take? Mutuwa bakiman adalci ba, inda iyayena na da rai bazasu barni na tozarta ba, ganin kukan baiman magani ya sa na shiga toilet na d’auro Alwalla nazo na tada sallah ina gamawa na d’aga hannu sama nafara adua neman nasara ina gamawa inda nayi sallah nan bacci ya kwasheni…..© (email protected)@HF💘J💘R💘(9:11PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸💘MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 1⃣5⃣➖1⃣6⃣ Ban farka ba sai da aka kira magrib, shima saboda kukan yunwan da cikina keyi ne da sauri na tashi na fad’a toilet nayi alwalla, nazo na kabbara sallah ina idarwa nafara adu’o’i ina nan aka kira isha tashi nayi na gabatar da isha ina gamawa nayi adua tare da neman nasara na nufi k’asa gabana na fad’uwa saboda bansan sake had’a ido da Mr Sadiq Imam… Luckily ina fita palorn ban ganshi ba hamdala nayi ga Allah, kana na k’arasa a daining table, ina zama na bud’e kuloli tuwon semovita ne sai miyan agushi da taji kifi, d’ayar kula kuma pepper soup d’in kayan ciki ne, zubawa nayi naci mai isata nikaina nayi mamakin abincin danaci, koda yake ba abin mamaki baneba cz tunda nazo gidan banci komai ba, sai azaba danake sha… Ina gamawa na dawo palor na kunna kallo na zauna, banjima da zama ba naji anyi sallama, amsawa nayi yayin da yake shigowa, k’arasowa yayi yace “Mrs Sadiq Imam right?” Saida gabana yafad’i jin yakirani Mrs Sadiq Imam, murmushi nayi na sunne kai k’asa, dariya yayi yace “anyway congratz Allah ya baki miji kamili mai ilimi” amma fa saikin yi hak’uri da halin da kika tsinceshi yanzu saboda illar da mace ta mashi, tab’e baki nayi nace “wannan ne kamili? Mugu dai” duk a cikin zuciya nake magana, a zahiri kuma nace “Thanks” in shaa Allah l’ll try my best naga na kyautata mashi kudai tayani da adua, yace “in shaa Allah… Nacika ki da surutu baki san wayeni ba ko? Murmushi nayi nace “bakomai”.. My name is Doctor Bilal, ni Aminin Mr Sadiq Imam ne and also nine doctor d’in dake kula da lafiyarshi, yanzu zamuje d’akin tare dake na dubashi sannan nabashi wasu methods na excersice which will help him recover fast, kuma kece zaki dinga taimaka mashi wajen excersice d’in. Da sauri na kalle shi nace “Ni?” Murmushi yayi yace “yes you” i know it’s deficult amma daurewa zakiyi ina da yak’inin kece zaki canja shi ki daure Allah na tare dake. Ajiyan zuciya nayi nace “shikenan muje”… Da sallama muka shiga d’akin Dr na gaba ina biye, da murmushi ya amsa yace “Bilal na d’auka sai gobe zaka…” Bai k’arasa ba ganina da yayi bayan Dr d’aure fuska yayi kamar bashi baneba mai dariya yanzu… Dariya Dr yayi ya bugi kafad’ashi yace “Sadiq rigima” yanzu dai bari nayi abinda ya kawoni, nan yafara aikin dubashi tare da yan rubuce rubuce, yana gamawa ya kalleni yace “Madam zan tardaki palor yanzu kinji” d’aga kai nayi dama kamar yasan a tsorace nake.. Ina fiya ya juya ya kalli Sadiq d’aure fuska yayi yace “haba Sadiq wai yaushe zaka daina abinda kake?” Kaifa ba yaro baneba yakamata ka san abinda kakeyi kamanta da abunda yafaru ka d’auka k’addaranka ce haka, yanzu kuma Allah ya maka canji da mafi alkairi dan Allah yanzu kaga yanda yarinyar nan ke tsoronka saikace taga zaki wlhi ka canja, dan da ganin yarinyar nan yar mutunci ce… Murya sanyaye yace “please abokina ka manta da komai ka sake sabuwan rayuwa kaji” tunda yafara magana Mr Sadiq baice komai ba kuma har yagama, yafi k’arfin minti ashirin da gamawa amma baice k’ala ba, murmushi yayi yace “nasan dama da fad’a zamu rabu amma kasani gaskia ce ko kanaso ko bakaso sai an fad’ama” yana kaiwa nan yaja briefcase d’inshi yayi gaba…. Yana fitowa ya sameni zaune nayi tagumi, murmushi yaman yace “haba Amaryanmu miye na tagumi” kodai ciwon mijinki ne ke damunki? Dont worry in shaa Allah soon zai warke kinji, ajiyan zuciya nayi cikin raina nace “wannan mugun yanama zaune guri guda yana zalintata inaga ya samu k’afa”… Maganan Dr ce tadawo dani daga tunanin da nake, farar leda ya mik’oman yace “magunguna ne ciki ki tabbata yasha safe rana da dare” kuma kece zaki dinga bashi wannan kuma zaki dinga mashi massage dashi ne shima 3times daily har na tsawon sati guda kinga duk idan zaki bashi magani saiki mai massage, in shaa Allah nextweek zandawo. Karb’a nayi namashi godia bankwana mukayi ya tafi nikuma na kashe kayan kallon nayi d’aki ad’ua nayi na haye lafiyayyen gado na kwanta, banjima ba bacci mai nauyi yayi gaba dani…. Ban tashi ba sai asuba ina idar da sallah na koma kan gado na cigaba da bacci, tara (9:00am) daidai na tashi wanka na shiga ina fitowa na bud’e wardrob d’in nan ma wata doguwan riga na jawo color d’in purple sai stones suma purple nd white ina sakawa ta zauna jikina cif cif dama kamar danni aka d’inkasu, downstaire na nufa cikin ikon Allah baya palorn nan na zauna nayi break fast ina gamawa na d’auki ledan magungunanshi na nufi d’akinshi gabana na dukan uku uku… Sallama nayi na shiga d’akin, bud’e baki yayi zai amsa ganina da yayi tsaye yasa ya zabura laptop d’in dake hannunshi ya wurgoman kad’an ya rage ya samu k’afana, duk ta tarwatse k’asa, niko sai kyarma nakeyi, ubanmi ya kawoki? Abinda naji yace kenan, cikin rawar murya nafara magana dama dama, tsawa ya dakaman wadda tasa na kusa sakin fitsari dama mi? Dama doctor ne yace nazo na baka magani kuma na maka massage a k’afafuwanka har na tsawon 1week kuma 3times daily… Shiru yayi can yace “ban amince ba kuma idan kece zakiyi banaso” dan haka aje magungunan ki ficema daga d’aki, wata zuciya tace mashi “Ah Ah” Sadiq kabari tayi kaga konan ka bautar da ita dama abinda tazoyi kenan gidan kenan… Ina aje magungunan na juya zanfita nakai k’ofa naji yace “dawo kiman” duk’awa nayi na d’auki ledan magungunan na k’arasa cikin d’akin, harara ya wurgaman yace “da kin gama ko second karki k’ara a d’akina kinji ni? D’aga kai nayi alamar “Eh” b’alla mashi magani nayi na mik’a mashi amsa yayi baiko kalli inda nake ba, fridge d’in d’akin na bude na d’auko ruwa bud’ewa nayi na zuba a cup na kai bakinshi, harara ya wurga mani kana ya bud’e bakin, yana saka maganin na bashi ruwa yana gamawa ya wurgaman harara yace “miye kika tsareni da ido?” Nidai bance komai ba na cigaba da yimashi massage a k’afa…. Ina mashi massage ina satar kalllonshi runtse idonshi yayi alamar yanajin dad’in abun saida nagama tsaf na d’ago da niyar nace mashi nagama, ina d’agowa muka had’a ido dashi, kunnena ya murd’e saida nasaki yar k’aramar k’ara yace “banace ki daina kallona da wannan ugly face d’in naki ba, ina cewa nace maki da kingama ki fitarman daga d’aki ko second kada ki k’ara shine kika tsareni da kallo… Ina hawaye nace “dan Allah kayi hak’uri dama zance maka nagama” idan akwai abinda kake buk’ata kafad’aman tsoki yayi “mtchw” mi zan buk’ata wajenki? Aibaki da dashi dan haka get out of my room, kafin ya ida na ruga da gudu…. Dariya ya bushe da ita saida yayi dariya mai isarshi kana yace “matsoraciya” ashe haka take da tsoro? K’afafuwanshi ya kalla yaji duk sun d’an saki, murmushi yayi yace “ashe dai ta iya massage haka?” Dole ta zama mai man massage…. Ina shiga d’aki na maida k’ofa na rufe fad’awa nayi kan gado nace “mugu azzalumi sai Allah ya sakaman, kuma anjima saina maka mugunta tunda kake cutata.”©(email protected)@HF💘J💘R💘(9:11PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦MATATA GIMBIYATA🌸💦💘MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 1⃣7⃣➖1⃣8⃣ Zaman shiru ne ya ishe ni don haka na yanke shawarar zagayawa cikin gidan bak’in mayafi na d’auko na yafa sannan na fice gami da janyo k’ofar. Daidai step d’in k’arshe na d’ago idanuwa na wanda suka sha ado da Mascara by Mary Clair na aza su cikin makeken falon amma me? Idanuwan mu ne suka ci karo da na juna tuni jiki na ya d’au rawa na fara taking steps backwards. ” Ke!! ” ya daka mani tsawa hakan yasa na tsaya chak idanuwa na a rufe . Where did you think you are going? Ya tambaya ” Cikin zuciya ta nace ” Yaushe kuma ka fara karanta minds ? Kuma ma me ya shafeka da inda zani!” Murmushi yayi yace ” Nasan me kike tunani! Yes babu abunda ya shafeni da inda zaki! Kawai de bana son a lokutan da nake having peace a dinga shige man harkoki! Saboda haka go back in bana falon se kiyi abunda ya kawo ki! ” Yanzu don kana zaune a falo tsabar bak’in hali shikenan kar kowa ya shigo? Allah ya sawwak’e !” Ta fad’a cikin zuciya kana ta juya zata koma fuska a murtuk’e kamar zatayi kuka ta koma d’aki ta fad’a kan gado tana ta sak’e sak’e…….. Zaune yake as usual kan wheelchair nashi yana kallon program na The Doctors. Shirun ne ya ishe shi don haka ya k’ira Sadeeya ( Mai girkin gidan ) da sauri ta fito tana goge hannayen ta a jikin kitchen towel , durk’usa wa tayi a gaban shi tace “Gani Sir” ta fad’a kai a k’asa. Ajiye wayar sa yayi kan centre table ya ce ” Ga ATM card nawa kije Shoprite zakiyi min siyayya ga list din a kan kujera ” yana kai wa nan ya maida duban shi ga TV Sadeeya ta mik’e da zummar komawa kitchen ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa where do you think you are going? Sir akwai abinci a kan cooker shine zan sauk’e kum…” Dakatar da ita yayi ta hanyar d’aga mata hannu sannan yace ” Ki dawo ki d’auki abunda na saki ki wuce kafin raina ya b’aci , bana son ki ‘kara koda second biyu! Jiki na rawa ta d’auki card d’in da list ta fice domin kuwa tasan halin sa , a da can ba ita kad’ai bane mai aiki duk shi ya koresu don haka itama dole tayi taka tsantsan in ba haka ba yanzu yayi waje road da ita……….. Ina kwance har k’arfe sha biyu sannan na yanke shawarar dawowa ko ya bar falon amma me? Kaurin k’one wan abinci duk ya mamaye downstairs d’in , zaune na hango shi ko a jikin sa duk warin nan ko a jikin sa , ganin yanda hayak’i yake fita daga kitchen yasa na sa gudu , har nakai bakin k’ofar kitchen d’in yace ” ” Ke wace irin bagidajiya ce? Shin idonki bai nuna miki makunnin ruwa bane a k’ofar ? Toh in baki sani ba yanzu ki sani an saka su ne saboda emergency na fire outbreak kuma automatically yake kunna kan shi ya kashe wutan , no need ki d’auki wata flamingo leg naki kice zaki shiga coz wutan ya mutu! Bak’auyiyar yarinya kawai! jiki a sanyaye na juya zan bar falon yace ” Ina kuma zaki? Wa kike tsammanin zai goge mess d’in kitchen d’in?” Zaro idanuwa nayi Like seriously wai me wannan mutumin yake nufi da ni ne? ” Ba tare da na furta kalma d’aya ba na koma kitchen d’in na fara aiki komai seda na tabbatar ya koma normal nayi mopping sannan na sauya tukunya bani na gama aikin ba se k’arfe biyu hakan ma na je nayi sallah sannan na cigaba, ina fitowa direct na wuce Upstairs na tube kayan jiki na gami da fad’awa bathroom nayi wanka , fitowa na ke da wuya naji ihun mutum, babu shakka muryar Sadeeya ne don haka na fice d’aure da k’aramin towel don ta tsorata ni . a d’akin shi naji tana k’iran suna na ” Hajiya! ( kamar yadda ta saba ) a firgice na shige d’akin only to se Mr Imam a kwance k’asa ruf da ciki ya runtse idanuwa kamar yaji ciwo ga kuma wheelchair a jefe guda. Hajiya nima Nazo kawo mishi orange juice kamar yadda ya buk’ata na same shi a haka” cewar Sadeeya a rikice Ido na mata da cewar ta fita , haka ta fice gami da rufe k’ofar , iya k’arfi na, na ciccibeshi sai nishi nake domin kuwa nauyi ne dashi ba kad’an ba , da ‘kyar na iya jinginar da shi jikin gadon sannan na sake k’ok’arin d’aga shi gami da maida shi kan gadon , Duk nayi gumi gashi k’arfi na duk ya tafi ,ina kwantar da shi na zube a kansa jiki ba kwari duk gashin kaina a fuskar sa numfashin mu na gogan na juna , yayinda ‘kamshin fresh mint na bakin shi ya bugi hanci na lumshe idanu nayi. Ji yayi zan zame k’asa don haka ya yi wrapping hannun shi guda around my back yana shak’ar ‘kamshin Bakhur dake mamaye cikin gashi na , wannan feelings d’in yau kad’ai na taba jin sa , sam ya kafe ni da idanuwa , mun kai mintina biyar a haka kafin na ce ” Excuse me” jin muryata yasa ya hankad’o ni k’asa yana watsa man harara duk jiki ba kwari na fita se kare jiki na nake yi.. Ina fita ya lumshe ido, da sauri ya bud’e sakamakon k’amshin dayaji jikinshi nayi, cire riganshi yayi haryanzu k’amshin na nan, lumshe ido yayi yace “turaren yarinyar nan yana da dad’i how i wish na dingajin shi kullum” wata zuciyan tace Sadiq ka mance matsayin da ka ajeta? Da sauri ya kauda tunanin ya wurgar da riganshi yana huci kamar tsohon zaki…. Ina shiga d’aki na fad’a kan gado wani irin farin ciki na shiga, tunano abinda ya shiga tsakaninmu na dingayi, rintse ido nayi ina k’arajin feelings, da sauri na tashi na shiga toilet nayo Alwalla na tada sallah bayan na gama na nufi downstair… Ina sauka na had’u da Sadeeya har k’asa ta duk’a ta gaidani, cikin sakin fuska na amsa, tambayarta nayi Sadiq yaci abinci? Sadeeya tace “yace dai na kai mashi d’aki a can zai ci” amsawa nayi da “ok” na juya na tafi d’akin cikin tsoro. Ina shiga nayi sallama shiru akayi k’ara sallama nayi cikin zafin rai yace “malama ki shigo idan zaki shigo bansan yawan magana” tab’e baki nayi nace “shi duk yanda ka mashi baka iya ba… Shiga nayi zaune yake yana latsa waya, gaidashi nayi amsawa yayi da lafiya, girgiza kai nayi na d’auko magani na mik’a mashi kallo na yayi yace “a k’auyenku ana shan magani ba’aci abinci bane?” Girgiza kai nayi nace “ai na d’auka kaci” banci ba abinda yace kenan, duk’awa nayi na zuba mashi abinci ina gamawa na mik’a mashi kallona yayi yace “ai yana daga cikin aikinki kibani abinci” da sauri na kalleshi harara ya wurgamani yace “zakiyi ko kuma zaki tsareni da mayatacce kallonki?” zama na gyara na dinga bashi abinci har saida ya k’oshi na bashi ruwa yasha…. magani na b’alla mashi na mik’a mashi, k’in amsa yayi bud’e baki yayi na saka mashi maganin na bashi ruwa, ina gamawa nafara mashi massage saida na tabbatar maganin ya shiga jikinshi sosai kana na mik’e na nufi hanyar fita.. Ina kaiwa bakin k’ofa yace “ke mummuna” cikin b’acin rai na juyo, kallo na yayi yace “wajen takwas zakizo kiman cz zan kwanta da wuri” kuma kika k’ara koda second guda ne wlhi l’ll show u my true color, cikin raina nace “yo akwai true color d’inka bayan wannan?” Murgud’a mashi baki nayi na fice d’akin da gudu… Murmushin mugunta yayi yace “zaki gane kurenki yarinya” zakisan kin murgud’aman baki…©(email protected)@HF💘J💘R💘(9:11PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸💘MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 1⃣9⃣➖2⃣0⃣ Shiru har k’arfe Tara na dare Deenah bata fito ba tun Mr Imam yana daurewa har ya kai mak’ura don haka ya d’auki telephone ya k’ira line na cikin gida luckily Sadeeya ta d’auka , cikin hasala yace ” Tell your Madam in akwai abunda yafi b’ata min rai bai fi delay ba, kada ta kuskura ta k’ara ko da minti d’aya kan hour d’aya da ta tsallake” Jiki na rawa ta fice bata zame ko ina ba sai d’akin Deenah inda ta iske ta a baje kan gado tana sharara bacci da alama duk na sauk’e gajiya ne. Da kyar Sadeeya ta iya tashin ta sannan ta Isar da sak’o ta fice , nan fa mutumiyar tasan cewa dubun ta ya cika Amma mafitar shine ta je kawai don dai masifar sa a wajen ta ba wani sabon Abu bane. Na dad’e bakin k’ofa hannuna ya kasa bud’e k’ofar balle nai tunanin shiga, at last nayi ta maza na bud’e ban shiga ba Sai da na lek’a kwatsam mukayi ido hud’u ,hah! Come see yadda na fara muzurai kamar tsohuwar munafuka shi kuwa ya zubamin na mujiya ko kyaftawa babu, ba tare da ya ce komai ba nayi sallama na shige ko ya amsa ma ni ban Sani ba ,direct na nufi bedside drawer na ajiye tray d’in dana d’auko ruwa da glass ,a kai . har na bud’e ruwan zan 6alli maganin naji muryar shi cikin sigar da bai taba min magana da ita ba tunda na zo gidan shi Indeed the sweetest ever! ” You never listen do you? , nace miki k’arfe takwas and here you are k’arfe Tara da Kusan rabi zaki bani magani , yanzu in na miki fad’a zaki ga laifina ko?” A hankali na girgiza kai nace ” Kayi hakuri I slept in ” Hakuri! Hakuri!! Hakuri!!! Ya daka tsawa sannan ya dawo normal muryar shi yace ” meyasa dukkanin ku hali d’aya gareku? ” Cikin sauri na d’ago kaina na aza idanuwa na cikin nashi tartare da alamar tambaya baki na rawa nace ” Dukkanin mu? Ni da wa?” Da alama bai ma San yayi magana ba don haka ya d’ago yana kallo na kafin yace ” Get lost! ” cikin damuwa nace “Toh maganin fa?” “YOUNG LADY BAKI JI ME NACE BANE? GET LOST !!;” cikin firgici na fice a guje na bar d’akin na fice ma daga cikin gidan zuwa jikin wani window na zauna , wasu zafafan hawaye suka fara tsere daga idanuwa na. Daga kan gadon da yake zaune yana hango ni ta glass na windon shi ,yasan bansan a nan yake ba Amma fuskar shi ya nuna ji yake ya tashi ya bata hakuri and of course give her a warm hug…… Ina nan bakin window har bacci ya d’aukeni, nice ban farka ba sai k’arfe shida da rabi na safe (6:30am) firgigit na tashi zaune amma abinda na gani yaban mamaki tuni nafara tunanin waya kawoni d’aki nidai iya sanina a waje nake har bacci ya d’aukeni amma gashi na ganni d’aki harda rufeni da blanket da kunna man Ac kodai Sadeeya ce ta maidoni? Haka na dinga ma kaina tambayoyin da nikaina bansan amsarsu ba… Haka na tashi jiki ba kwari na fad’a toilet wanka nayo da yake ina fashin sallah, turare kawai na saka na d’auko doguwar riga ta material na saka. Down stair na nufa ina sauka muka had’u da Sadeeya da sauri ta duka “Ina kwana Anty?””Lafiya lau”Na bata amsa, tashi tayi zata wuce “Sadeeya” “Naam Anty””Dama tambayarki zanyi ke kika kaini d’aki jiya bayan nayi bacci?””Ah ah Anty bani bace ba””To waye ya kaini d’aki?””Wallahi ban sani ba Anty” Juyawa nayi na nufi kitchen zuciyata cunkushe da tunani kala kala.. Abinci na tusa gaba ina kallo ina wasa da spoon, Sadeeya ce ta k’araso inda nake zaune tace”Anty ya kamata kici abincin nan”Murmushi nayi nace “Karki damu Sadeeya nama k’oshi kedai had’oman break din yallabai” Mik’ewa tayi ta nufi kitchen.. Mik’aman tray d’in tayi karb’a nayi na nufi kofar gabana yana dukan uku uku, sallama nayi har sau uku amma ba amsawa kaina na kutsa ciki, tsawar daya dakaman yasa na kusa yada tray d’in hannuna, ke jakar inace? Da zaki fad’o ma mutum d’aki batare da izini ba? Ko an angaya maki idan kai sallama shigowa kake batare da ance ka shigo ba kodayake ba mamaki k’ila bakije makarantar Islamiyya ba… Bak’in ciki yasa nakasa koda d’agowa in kalleshi, cikin tsawa naji yace “Get out of my room”Ba musu na juya zan fita “Ke ugly” Tsayawa nayi amma ban juyo ba dan in akwai abinda na tsana bai wuce wulakanci ba shiko naga mutumin nan bai aje komi ba sai wulakanci.. Zokiyi aikin daya kawoki marar kyau da ke, shiga nayi na samu wuri na aje tray d’in tare da goge hawayen da suka gangaro man.. Gaida shi nayi amma ko kallo na baiyi ba bare nasa ran zai amsa… Plate d’in soyayyen dankali da kwai sai tea na d’auka na isa gabanshi, fara bashi nayi ba musu ya bud’e baki na fara bashi sai da ya k’oshi kana na b’allo magani na bashi had’awa yayi da hannuna da maganin ya taune saida na saki k’ara kana ya sakar man hannuna hawaye na share cikin raina nace kaida Allah mugu Azzalumi kuma indai haka zaka cigaba a zaune zaka k’are rayuwarka bazaka mik’eba…”Idan kin gama zagin nawa sai kiyi sauran aikinki kitashi kiban wuri nagaji da ganin fuskarki tun banyi amai ba..””Ido na zare nace wallahi ba zaginka nayi ba”Ba rantsuwa na tambayeki ba kiyi abinda zakiyi ki b’aceman dagani ugly dai ke..” Massage nafara yi mashi inayi yana lumshe ido sai da na gama mashi komi kana na mik’e da zumar barin d’akin.. Hannuna ya fizgo har sai da na fad’i amma ko kallo ban isheshi ba.”Miya hanaki zuwa jiya da wuri?” “Bacci nayi na bashi amsa a takaice dan na fara gajiya da wulakancin shi..” Kunnena yaja yace “Wakika ma rashin kunya jiya?”Hawaye na farayi nace”Dan Allah kayi hak’uri”Tsawa ya dakaman wadda yasa saida na kusa sakin fitsari”Dake nake ubanwa kikama rashin kunya nace?” Kuka na fashe dashi, kallona yayi yace”Kigama kukan sai kin gayaman ubanda kikema rashin kunya..”(9:11PM, 8/3/2017) +234 806 677 6651: 🌸💦MATATA GIMBIYATA💦🌸💘MY WIFE MY PRINCESS💘STORY BYJEEDDAH JA’OWRITTEN BYFEEDOH DEEDOH (NWA)EDITED BYROOKIEY KAXS 2⃣1⃣➖2⃣2⃣ Shiru nayi ina kuka a hankali, ina jin yadda ya damk’e hannu na nasan bazan iya wafce wa ba don haka na fara tuno dabaran da zan yi ya sake ni. Da gangan na saki k’ara kamar Wanda naga abun tsoro ba shiri ya sake Mani hannu yana fad’i “Me ne?” Ban ko saurare shiba Sai da na isa bakin k’ofa na juyo fuska ta d’auke da exclusive dariya Wanda of course na manta ranar da nayi irin ta a hankali nace “Catch me if you can!!” Sannan na fice ina murza inda ya damk’e d’in Sosai ya dinga dariya shi kad’ai harda rik’e ciki yace “yau na farko you tried to fight back in your own style” ya d’aga gira sannan ya d’auki wayar shi yana danna wa….. Yau haka na wuni tun dana gudo ban sake had’e ido da shi ba, kuma hakan yayi min dad’i sosai don at least na samu peace yau. Horn na mota da naji ne yasa na mik’e na nufi window Matace tare da wata budurwa kyakkyawa kam babu yabo ba fallasa. Matar zata kai shekaru Arba’in plus ta sha liffaya kai kace daga Borno take Amma fuskar nan ba annuri ko kad’an da alama ma masifa take yi gata Masha Allah tana da k’iba Amma ba na tashin hankali ba. Da sauri Sadeeya ta iso inda nake tace “Tab’l yau kam na shiga uku! Yau Hajiya ce a gidan nan?” Deenah ta juyo da alamar tambaya a fuskar ta tace “Kamar ya kin shiga uku? Wacece ita?” “Uwar Ki ce! Nace Uwar Ki ce! Hummp! Wato tsabar tsegumi tun kafin na k’ariso har an gama k’are min kallo, Munafukan banza” Ta juya gefen Sadeeya tace “Toh Munafuka! Sai Ki kai kayan mu ciki ai.” Jiki na rawa Sadeeya ta fice don d’auko kaya ni kuwa k’asa na durk’ushe ina mai gaida su, ba tare da ta amsa ba ta ja tsaki ta wuce tana fad’in”Oh ni Halima! Y’an aiki se tsegumi, munafukai Ke kuma Ramlah je Ki duba yayan Ki don nasan bai San da zuwan mu ba” Tana magana tana nishi kamar Wanda taci gudu wai hakan stairs take hawa….. Tun da muka rabu da su a Falo na dawo d’aki Jiki na rawa a rai na nace “Tab ba’a rabu da Bukar ba an haifi Habu! Wannan wacce irin K’addara ce? Ni Wollah matar nan ma tafi Mr Imam bani tsoro, don Rashin mutunci ma a y’ar aiki ta d’auke ni, like serious? Do I really look like a maid? Ko dai kawai zagi na take yi?” Na dad’e ina sak’e -sak’e ban ankara ba naji an chafko wuya na kamar Wanda nayi wata gagarumar sata idanuwa a waje cike da mamaki na juyo ina kallonta ido cikin ido tana taunar chewing gum kamar y’ar tasha “Uban wa ya baki izinin shigo min d’aki, kina y’ar aiki da Ke har kin samu hurumin shiga min d’aki har kisa min kaya?” Ramlah kenan Zaro idanuwa nayi waje kamar an mahaukaciya baki bud’e nace “kamar naji kin ce kayan Ki? Toh mesa Mr Imam ya barni a Wannan d’akin, koda yake daman shima ba mutunci gareshi ba I don’t blame him” Duk cikin zuciya nake wad’annan maganganun Ban ankara ba naji tayi snapping yatsun ta a fuska na tace “Wake up stupid! Kafin na bud’e ido na Ki cire min kaya kuma Ki bar min d’aki” Gudun janyo magana yasa nayi maza maza na kwashi flamingo legs d’ina na fice ban zame ko ina ba se d’akin Sadeeya , sai a lokacin haushin Mr Imam ya kama ni , don haka na mik’e da zummar zuwa d’akin shi………. Ko sallama babu ta banke k’ofar d’akin ta shiga , idanuwan ta basa ma gani balle taji shakkar sai huci take.. “Hey! I did not remember you asking for my permission kin wani shigo min d’aki babu ko sallama”Ya fad’a kansa a kan laptop screen. “Sallama? Sallama ai a mutanen da suka san ma’anar ta ake yi wa? Kai da you do not ever want to maintain peace dalilin me yasa zan maka sallama? You have humiliated me to the extend that naji na tsani kai na yau! First ka bani d’akin da ba nawa ba sannan na saka kayan da ba nawa ba duk ka Sani ka bari Yarinya tazo ta ci Mani mutunci Wollah ban tab’a jin anyi downgrading d’ina haka ba, yau naji cewa dama an barni a inda nake cikin bauta da takura ko ba komai jini na ne su ,Wollah if you had known da baka b’ata lokacin ka har ka bani d’aki ba, nida na kwana a kitchen, na kwana a filin gida ina ne bazan kwana ba, now I want you to explain this to your sister that I did not wear her clothes Intensionally” Tana kaiwa nan ta fice gami da banko k’ofa har Saida Mr Imam ya tsorata gami da ajiye laptop d’in ya bi k’ofar da kallo cike da mamakin what she just did. “How can I tell you My Darling,Cewar kayan sun miki kyau?, bazan iya cewa Ki cire ba coz they seems like they are meant only for you” Cikin sanyin murya yake magana bai ma San da mutum tsaye a kanshi ba………
adsense 2 here