littattafan hausa novel complete

RANA DAYA COMPLETE HAUSA NOVELS 6 to 10

PAGE

    “Nifa ka sani acikin duhu, wai meke faruwa ne?” Sultan ya tambayi Afzal dake tuk’i cike da rashin hak’uri da neman k’arin bayani. Shiru Afzal ya masa yana me sa hankali sosai akan tuk’in da yakeyi. 

  “Triple A?” ya kuma kiransa kusan sau goma kenan tun zamar su cikin motar. 

  “Bansan yaushe ka kurmance ba wallahi, referring to abubuwan da kaji na fad’a mata ai yaci kasan auranta mahaifinta yakeson inyi.”

   “Nazeefan fah?” Sultan ya tambaya cike da d’umbun mamaki. 

  “Ask me again” ya fad’a tare da basa d’aya daga cikin mugayen kallonsa sannan ya maida kallonsa kan hanya.

  “How?? Triple A kabani labari please.”

  “Idiot ai labarin nakeson baka yasa nace ka taho.”

   “Asshole” ya fad’a tare da kai masa punch a hannu “Am all ears” nan Afzal yashiga zazzage masa dukannim abubuwan da suka gabata tun daga yinin jiya, a haka har suka iso layin dake kusa da gidansu Amal. 

   “Tsaya maza mey kuma zamuyi anan? Mey ya kawomu unguwan nan? Kode kayi 6atan kai ne?” Sultan ya tambaya nan take. 

  “Nop” ya amsa tare da popping P d’in “Ina yarinyan dana fad’a maka na bugeta accidentally jiya?”

  “Yes” ya amsa tare da gyad’a kansa “Dr ya buk’aci a mayar da ita yau a sake treating k’afan so am here to fetch her” ya fayyace mar. 

  “Toh shine se kai ne zaka kaita? Ai tunda ka riga ka biya kud’in komai se ka bawa mamanta transport fee tana kaita.”

   “No Sultan I cursed this upon them, ganganci na ya kaini kad’eta I have to take full responsibility.”

  “Toh Mr good samaritan jeka ina jiranka” ya amsa shi cike da gatsine. K’aramin mirror dake gaban driver seat Afzal yaja yana duban fuskansa tare da sake daidaita hulansa sannan ya fice. Shi de Sultan baice komi ba illa binsa da kallo da yake. 

  Sallama yayi a hankali alokacin da yake sa kai cikin gidan. Amal ya tarar zaune akan benchin jiya da wani novel na English rik’e a hannunta ta zurfafa ciki tana karantawa. Sanye take da wata atamfa riga da skirt wanda ta mugun amshe kalan skin nata, kanta kuwa ba d’ankwali hakan ya bawa Afzal daman ganin silky gashinta dake nan kaman na bak’ak’en ‘yan India. Kamashi tayi a tsakan kanta tare na nannad’e jelar wanda a sanadin haka Afzal be samu daman gano k’arshen ba. Kallonta ya tsaya yi musamman yadda ta miqar da k’afan nata me targad’e wane wacce ke jiran koda kuda ne ya ta6a ta hau bala’i da k’orafi. 

  “Uhm uhm” yayi gyaran murya wanda hakan yasa Amal tsaida duk wani abinda takeyi ta d’ago kanta domin ganin wanene. Wani irin d’an banzan tsinkewa zuciyarta tayi ganin Afzal tsaye akanta da ratan da befi meters biyu zuwa uku tsakaninsu ba. Da sauri ta dukar da kanta a lokacin da idanunsu suka had’e tana me neman mayafi don lullu6e jikinta sede ba halin yin hakan dan k’afarta. Yadda zama ke bata wuya haka zalika miqewa don haka kawai ta shiga kare k’irjinta dukda cewa bawai ya bayyano waje bane. Shiko Afzal ganin ta soma yin wasu abubuwan yayi saurin juya mata baya totally dan kuwa bega abun gani ba achan da take ta wani faman tarewa. 

  A hankali ta d’ago kanta taga gabad’aya ma baya ya juya mata aiko take ta murgud’a mai baki “Tafi nono fari” ta fad’i can k’asa-k’asa sannan ya k’wolla ma kira. 

   “Mamiiii!” Dan k’ara irin na muryarta seda Afzal ya toshe kunnensa. 

   “Ki fito kinyi bak’o and please ki taho min da hijabi na.”

  “Toh” Mami ta amsa daga ciki, bada dad’ewa ba se gata nan ta fito, ganin mutum kaman Afzal ne yasata sakan murmushi. “A’ah Afzal ko?”

  Se anan ya kewayo nan ta tabbatar shi d’inne “Sannu da zuwa Baba na ina yini?” Ta gaishesa tana mik’a wa Amal hijabin data fito mata dashin. 

   “Yauwa Mami ina yini? Ya gajiya?” Ya amsa cike da girmamawa. 

  “Lafiya k’alau ya kayi tsaye haka? Ka k’ariso ciki mana. Ke Baby haka akeyi ne seki bar bak’o tsaye bazaki ce masa ya k’ariso ba?” Mami ta tambayi Amal data had’e gira gu d’aya. 

  “Yo ba nace ya shigo ba yayi tsaye wajen” ta fad’a cike da rashin kunya. Baki Afzal ya bud’e cike da mamaki yana kallonta wato acikin had’uwa biyu da sukayi ya karance Amal is such a big liar, gashi comfortably take yin k’arya kuma bata d’auki hakan a bakin komai ba. 

  “Toh gaisuwa fa? Kin gaishe shi?”

“Abinda na farayi kenan daya shigo” ta kuma amsawa. Shide Afzal bece komai ba. “Bari in d’auko ma taburma mana ka zauna Afzal ko ruwa ne kasha.”

  “A’a Mami karki damu daga gida nake nazo d’aukan Amal ne ayi dressing k’afan nata kaman yadda Dr ya buk’ata” Kafin Mami tace za tayi magana Amal har ta tsoma baki ta soma k’orafi “Ni wallahi ban komawa asibitin chan in kanayi wa Allah ka koma inda ka fito nagode da kulawarka amman ban sake taka k’ofan asibitin chan.” Har anan Afzal bece komi ba saboda yasan abinda ya tanadar mata. 

  “Yau ina ganin ikon Allah!” Mami ta tsaya kallonta tare da dafe k’irji “Ke da hankalinki? Yanzu ya dace ki fad’awa mutumin da ke nema maki lafiya wannan kalamu? Wallahi karki bari raina ya 6aci in basa hak’uri yayi tafiyansa yaso k’afan naki yayi tsami ya ru6e in kaiki nan gun wanzan a gintile kowa ya huta.” Dariya sosai comment na Mami yabawa Afzal don haka ya shiga gyaran murya don had’iye dariyar sede still seda curves na murmishi suka nuna a fuskansa. Wani kallo Amal ta watsa masa tare da fad’in wasu kalamun chan k’asa-k’asan muryarta yadda ita kad’ai tasan abinda tace. 

  “Maza tashi karki 6ata min lokaci!” Seda ta gama tsiyarta sannan ta amince Mami ta taimaka mata ta miqar da ita. 

  “Toh Allah ya kare Afzal kaikuma Allah ya biya.”

  “Ameen Mami” daga fad’in haka ya fice Amal na k’ingishi tana mara mai baya har suka isa gun da motarsa ke. Kasancewar motar tinted ce Amal bata samu daman gane cewa da akwai mutum acikin motar ba shi kuwa Afzal shiru yayi mata daya ga tana nufan k’ofan gaba. Tsaye yayi yana jiran na aukuwa ya faru. Tana bud’e k’ofan kawai setaga bak’on fuska na kallonta, kunya tajiyo sosai yanzu Afzal yasan da mutum cikin motan yamata shiru har ta bud’e? Yamar kyau. 

  “Ina yini?” Ta gaishe sa cike da kunya tana ja baya a hankali se kace ba ita ba. 

  “Lafiya ‘yan mata kin 6ata ne?” Sultan ya tambaya danko besan itace yarinyan da Afzal ke nufi ba. 

   “Ban san da mutum aciki bane am sorry.” K’ofan ta miyar mishi tare da d’ago kai tana kallon Afzal dake ta faman kallonta shima dariya ya ciko mar dam a baki amman ya dage ya danne. Ba tare da yace mata komai ba ya bud’e motan ya shiga wanda itama tayi hakan. Bayan ya kunna motan Sultan da kansa ya d’aure ya juya ya dubi Amal sannan ya kalli Afzal sam be kawo a ransa cewa budurwa ce Afzal ya buge ba cause yadda Afzal ya basa labarin k’iriniyar yarinyar seyayi picturing nata to be 13-14 years. 

  “Itace yarinyar?” Ya tambaya not believing it. 

  “Wai ba” Afzal ya amsa sa in an I don’t care tone tare da yin reverse suka hau kan hanya. “Kana bani labari” cewar Sultan after a while “Amman Triple A bakada mutunci.”

  “Da nayi meh?” Ya tambayesa yana me miyar da hankalinsa sosai game da tuk’in da yake a yayinda Amal dake baya ta ware kunnuwanta domin jin abinda wannan mara mutuncin yayi da har abokinsa ke mamaki haka. 

  “Kaji kalan kalamun daka fad’awa yarinyan chan mana Nazeefah” ta6e baki Amal tayi, dama tasan za’ayi haka a yayinda ta cigaba da kasa kunne. 

  “She needs to be told the truth” Afzal ya miyar masa ba tare da ya nuna damuwa ba. 

  “Toh kai kasan ka k’yamaceta haka meyasa ka amince da k’udurin auren nata?”

   Aure de? Amal ta nanata a ranta, lallai ta tausayawa ‘yar da zata auri wannan mutumi me uban ji da kai haka, ai kuwa gashi tun ba’a je ko ina ba abokin shi yace baida mutunci be kyauta ba, ko mey ya gaya wa yarinyan se Allah. Shiru tayi tana me cigaba da sauraran hiran nasu. 

   “To make Abba happy” ya amsa sa simply. 

   “Hmm fire on the mountain sunan wani abu, Afzal da Nazeefah a k’ark’ashin rumfa d’aya ai akwai show” jin Afzal be amsa shi ba ya cigaba “Triple A tell me something mana kode dama kanada interest akan yarinyar ne?”

   “Interest?” Afzal ya nanata cike da mamaki yanzu upon all people Sultan ne ze fad’a masa wannan batu? Lallai amman be kyauta ba, ai wannan zagi ne. 

  “Dan Allah ka miyar da kallonka kan hanya kafin kaje ka zubda mu” yace da Afzal daya tsaya yana kallonsa da alama ya manta akan hanya yake domin ko niyyan kau da kansa ba beyi ba. 

   “This is an insult to my face Sultan, ai ko Nazeefah ce autan mata I’ll never learn to love her, she simply disgusts me.”

   “Hmmm nide nayi shiru amm-“

   “Shut up Sultan” yace dashi tare da katse sa. Shirun da Sultan beyi ba kenan ya cigaba da neman tsokan Afzal har sanda suka isa asibitin amman ko uffan Afzal be ce dashi ba, hasali manna mishi yayi. Dukansu uku suka kuguma suka fita inda suka nufi cikin asibitun tun daga harabar Amal ta soma kauce-kauce ita bata so Afzal yayi hak’uri ya maidata gida, ita kad’ai tasan azabar dataji jiya sede ko kallonta beyi ba bale yasan tanayi. Bayan sun gaisa da likitan ya kewayo da fatan ganin Amal se de ya ganta chan tsaye bakin k’ofa ta maraice fuska. Murmushin mugunta ya saki sannan ya dawo da kallonsa akan likitan tare da yin gyaran murya, “Dr ya naga kaman jiya baku ja k’afar yarinyan can kaman yadda ya kamata ba?”

   “Ba’a ja ba kuma Alanguburo? Meyasa kace haka?”

  “Toh gashi k’afan nata yayi tsami ya kumbura-“

  “Wallah bai kumbura ba” Amal da ta kasa kunne tana sauraronsu tayi saurin katsesa “Wallahi be yi tsami ba Dr don Allah karka sauraresa” ta fad’a cike da tashin hankali. Shareta Afzal yayi ya cigaba, “Gashi na kawota yau ina son ku jashi sosai please, a ja sosai saboda kar a samu complications nan gaba.”

  “Toh Alanguburo in shaa Allah ina yarinyan ne? Ke shigo mana” yace da Amal yana maida kallonsa a gareta. Ja da baya ta farayi da niyyan ta gudu. 

   “Don’t even think of running ga nurses da securities kota ina sasu zanyi su kama ki” Afzal ya fad’a cikin tattausar muryar data mugun razana Amal da tuni tasa kuka. Wai don meyasa yake mata haka? Kode don rashin kunyan da take mar ne yayi tunanin ramawa ta nan? Tayi tunanin haka a ranta. Ai kuwa ya zama dole ta basa hak’uri yanzu dukda cewa yin hakan bawai yana nufin bazata kuma mar rashin kunyan bane idan yayi mata abinda be gameta ba. 

  “Afzal- no” tayi saurin kad’a kanta “Ya Afzal dan Allah kayi hak’uri wallahi bazan sake ba.”

  “Yaya?” Ya nanata a yayinda dariya me k’arfi ya ku6uce mar bashi kad’ai ba harta Sultan. “Ni ne Yaya? Guy kanajin yarinyan nan?” ya juya tare da tambayan Sultan nan suka kuma fashewa da wata dariyar barin ma Afzal da yake sark’ewa. Amal ji take kamar ta bisu da mari, ba abinda ta tsana kaman a tsaya ana yi mata dariya amman ya ta iya?

   “Wallahi a kullum kai Yaya na ne ai ko ido ma ma’auni ne” tayi saurin bashi amsa a rud’e. 

  “Kinga karki kaini inda Allah be kaini ba” ya fad’a yana composing kansa, “I don’t have any sibling so am nobody’s Yaya.”

  “Wallahi a’a kai Yaya na ne kuma ai bazaka so a cutar maka da k’anwarka ba ko? Dan Allah ka fad’awa likitan nan karya ja min k’afa da zafi.”

  “Nak’i” ya fad’a a takaice. 

  “Dan Allah Ya Afzal kayi hak’uri bazan sake maka rashin kunya.”

  “Wancan kuma ke ya dama ki shigo suyi miki abinda ya kamata na maidaki gida I have things to attend to.”

  “Dan Allah I’m sorry” ta fad’a tana kad’a kai. 

  “Doctor ka turo nurses su jawota jiki she’s wasting my time.”

  “A’a don Allah zan shigo da kaina.”

  “Then make it quick” ya fad’a tare da galla mata wata mumunar kallo. “Kina fa 6ata min lokaci” ya kuma fad’i ganin bata motsa ba. 

  “Zan shigo zan shigo” ta fad’a a kid’ime sede fiye da minti biyu ta kasa takowa ciki. 

  “Ina nurses d’inne kam wai?” Afzal ya tambaya yana kewaya. 

  “A’a dan Allah zan shigo, wallahi zan shigo.” Da hakan ta k’ariso ciki tana k’ingishi. “Please kace musu kar su ja min k’afan Ya Afzal.”

  “Nak’i” ya sake nanata mata ko d’igon tausayi babu a tattare dashi. 

  “Bazan sake maka rashin kunya ba wallahi na tuba.”

  “Guy pardon her please” fad’in Sultan dake tsaye daga gefe guda sede sanin taurin kai da zuciya irin na abokinsa yasan ba lallai bane ya jisa balle ya sassauta wa yarinyan. 

  “Make me” ya ce dashi tare da basa one of his nasty looks. “Ba ruwanka you better stay out of this, nurses take her in ku ja min k’afan nata sosai don idan yayi tsami ina tabbatar muku da cewa zanyi suing asibitin nan naku duk ku rasa aikinku kuma” ya razanasu. Haka nurses suka taho suka ja Amal se ihu take tana had’a Afzal da Allah amman yayi tamkar bada shi yake ba, idan ba hakan yayi mata ba bazata daina mai rashin kunyar ba. Bayan long draman da aka sha tsakanin Dr, nurses da Amal aka samu akayi retreating ciwon aka sa mata sabon bandage suka kuma jashi sosai kaman yadda Afzal ya buk’ata. Fuskan nan duk jirwayen majina da hawaye gabad’aya ta fita daga hayyacinta. 

  Dariya sosai Sultan ya saki lokacinda shi da Afzal suka shiga d’akin suka tarar da ita zaune bakin gado tana aikin share hawaye. Shima Afzal d’in dariyar ce ta k’eto mar amman kaman yadda ya saba bonewa hakan yayi. 

   “Lets go” yace da ita, da mamaki yaga ta mik’e ba gardama ba suratai. Lallai plan nasa yayi working. 

   “Triple A yaci ace an saya mata koda ice cream ne ta d’anji sanyi a ranta da wannan muguntar da kasa nurses sukayi mata” cewar Sultan lokacin da suka wuce ta downtown. D’ago ido Afzal yayi yana hangenta ta mirror yadda tayi tsit a motan kaman ba ita aciki. 

   “A saya miki kinaso?” Ya tambayeta da gan-gan yana wani murmusawa ta gefe. Idanunta takai inda nasa suke sannan ta kad’a kai a hankali “Karku damu nagode” ta fad’a a nitse ba Afzal kad’ai ba har Sultan yasha mamaki. Wani murmushin ya kuma sakewa sannan ya miyar da kallonsa kan hanyan. U turn yayi suka koma baya inda ya tsaya ya sai mata ice cream d’in. 

   Bayan ya kaita gida ya mik’a mata, jira yake ta amsa ta bud’e ta kwa6ar a k’asa tunda de wanka ta biya kud’in sabulu gashi ya kawota gida se kuwa yaga tana kad’a kai “Nagode ni zan wuce gida” ta sanar dashi kanta a sunkuye. 

    “Haba ‘yan mata, yi hak’uri ki kar6a kinji?” Cewan Sultan cike da dabara. Ba ta kuma yin musu ba tasa hannu ta amsa tare da masu godiya sannan ta bud’e k’ofar. 

  “Sekuma gobe ko?” Cewar Afzal da gan-gan domin jin me zatace. 

  “Eh Allah kaimu” ta amsa calmly. Killer smile nasa ya saki ashede plan d’in yayi working, frankly ko shi be d’au ze iya yin abinda yasa akayi mata ba, but he had to it is the only way da zesa ta dena masa rashin kunya. 

   Tun daga ranan Afzal ya cigaba da d’awainiyar Amal kamar yadda yayi alk’awari. Mostly daga office bayan yaci lunch seya biyo ya d’auketa, wani sa’in sukan taho tare da Sultan mostly kuma shi kad’ai yake zuwa. Amal kuwa tun rana me kaman na ranan bata sake yiwa Afzal rashin kunya ba, cike da girmamawa da ladabi take gaishe sa duk sanda yazo, bata kuma fasa kiransa da Ya Afzal d’in ba, har abin ya zame mata jiki. Shima Afzal kullum daga clinic se sun tsaya a downtown sun sai mata ice cream. Ranan daya kaita dressing na k’arshe bayan ya kawota gida Amal tayita insisting cewa ya shigo ciki suyi final sallama da Mami tunda basu samu daman yin hakan ba d’azu kasancewar Mami bata gida daya taho. Sam baida niyyan shiga ciki again sede kuma yaga Amal nada point idan ba wani ikon Allahn ba kam ai ba abinda ze sake kawosa gidansu, yaci ace sunyi ban kwana da Mami. 

  “Kaji Ya Afzal kashigo ku gaisa da Mami please” ta kuma cewa ganin be ko motsa acikin motar ba. “Pleaseeee Ya Afzal.” Juyowa yayi yana k’are mata kallo seji yake a jikinsa Amal is upto no good, dama chan bawai ya yarda da wannan d’abi’un da take portraying bane ace for the past 6 days ko rashin kunya bata mishi sema ladabi da biyayya. 

  “Amal?” Ya kira sunanta yana k’are mata kallo. 

  “Na’am” ta amsa tare da sunkuyar da kanta tana wasa da ledan ice cream daya siya mata. 

  “Wani abin kike shirin yi ko? Kinsan I don’t trust you not even a single bit.”

  “Haba Yaya har mey yayi zafi haka? Mey zanyi maka? Allah ba komai kawai inason kuyi bankwana ne da Mami kaga ai idan ba wani ikon Allahn ba bazaku k’ara had’uwa ba.”

  Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauk’e “Let’s go” nan ya kashe motan suka fice. Bayan sun k’arisa ciki Amal ta shimfid’a mai taburma tare da yima Mami da Papi sallama, bayan sun fito ta nuna musu ice cream da Afzal ya sai mata. Godiya sosai sukayi mishi sannan suka gaisa, da wayo ta saci jiki ta fice ba tare da sunyi realizing ba. 

  Pins da k’usosin da ta tanada ta ciro sannan ta k’arisa gun motan nasa, tayan baya ta sace dana gaba sannan ta gwada bud’e motar haushi taji datayi confirming a kulle ne if not da tayi niyyan kwa6ar mar da ice cream d’in acikin motar ne next time se taga idan ze sake sa mugayen likitocin asibiti su ja mata k’afa kai bama ita kad’ai ba koda wata ta daban. Seda ta ga tayoyin sun soma tsotsewa sannan ta kama hanyan gidansu Azee inda suka hau shan ice cream suna hira. Afzal kuwa bayan sun gama gaisawa dasu Mami sun d’an ta6a hira kad’an yace ze tafi, har wajen gida suka rakasa sannan suka koma ciki. Yana wasa da makullin motansa yana tafiya har ya isa inda yayi parking motan nashi, sam hankalinsa be kai ga patched tires guda biyun ba seda ya shiga yasa key ya shiga neman yin reverse yaji mota yak’i baya balle yayi gaba. Tirk’ashi, accelerator yata dannawa amman ina mota yak’i motsawa hakan yasa ya fito don duban inda matsalar take to his ultimate surprise yaga tire biyu duk a pache. Da farko yayi tunanin ko ‘ya’yan unguwa ne suka mai d’anyen aikin nan amman tuna yadda Amal ta dage sam seya shiga sun gaisa da Mami yasa ya soma zarginta. 

   Tabbas yarinyan nan bata da kunya, upon duk d’awainiyyan dayayi ta mata da abinda zata saqa masa kenan? Lallai kuwa she’s messing with fire. Ji yake kaman ya shiga gidansu ya nunawa Mami da Papinta abinda ‘yarsu tayi mar amman tuna ba lallai ne su hukunta ta kaman yadda yakeso ba yasa ya fasa, yafison ya hukuntata da kansa, hukuncin da ko akan layi ta gansa seta canza hanya. Murmusawa yayi ya ciro wayansa daga aljihu tare da kiran mechanic nasa. Within 20 minutes ya iso sede ba pachi kad’ai Amal tayi ba, tiren gaban entirely yasamu matsala wanda idan ba ikon Allah ba se an canza shi gabad’aya. Anan de mechanic yamasa concluding cewa mota bazata gyaru a yau ba. Wayan Sultan ya kira don yazo ya d’aukeshi sede switched off yakeji. Be damu ba yashiga neman driver’n Daddy nan ma network yak’i barinsa. Abu fa kaman wasa se trying yake amman network yak’i bari call ya shiga chan kawai service ya d’auke gabad’aya.  Babban magana! Ji Afzal yake kaman ya k’urma ihu bayan nan yaje ya nemo duk inda Amal take a fad’in unguwansun nan ya nad’a mata na jaki. 

  Abu kaman wasa network yak’i dawowa gashi se ci yamma keyi, bayan d’an gyaran da mechanic yayi yakuma cire important parts na motan gudun kar 6arayi suyi gaba dasu dake motan ma se an barta ta kwana anan ya buk’aci Afzal daya bisa cikin keke napep daya taho sesu sauk’eshi a gida. Kallo Afzal ya tsaya yana mishi, wai da shi yake? Shi yake tsammanin ze shiga keke napep? Bawai yana nufin yafi k’arfin shiga bane sede bai ta6a shiga motan haya ba se gashi yau akan ‘yar gudun hinirar can ze soma yin hakan? Lallai kuwa duk rananda Allah ya sake had’a path nasu seta gwammaci kid’a da karatu. 

  “Kayi shiru ranka ya dad’e yamma ne keyi fah” fad’in mechanic d’in. 

  “A’a kayi tafiyanka I’ll wait a bit longer halan network ze dawo se in samu in kira gida suzo su d’aukeni.”

  “Hmmm kana magana sekace ba a Maiduguri kake ba? Kade san idan network ta d’auke to se wani ikon Allah kesa ta dawo a lokacin da de hak’uran kayi muka kaika gida tunda ga keke free ne na yaron gidanmu.”

  “Sekuma aka ce maka gudun kud’in nakeyi? Ni kawai kuje Allah kaimu goben.”

  “Toh shikenan seda safe.” Da haka suka fice a yayinda Afzal ya cigaba da tsayuwa wajen yana jiran dawowan network, can daya gaji ya bud’e motan nasa ya shiga se duban screen na wayansa yake ko network ze dawo amman ko alamun hakan babu. Around biyar da minti sha biyar na yamma 5:15pm Afzal ya soma losing hope, the earlier the better idan de ba so yake ya kwana cikin motan nan ba toh tun wuri ya kama hanya ya nemi a daidaita sahu ya shiga. Shi tunanin yadda ze fita cikin wannan kwamacalan unguwan ma yake, ‘yan unguwa ba manya ba yara duk angle da mutum yabi se sun bisa da ido suna gulma k’asa-k’asa. Cike da takaici ya shiga takawa trying his best not to get distracted. Har bus stop yakai sannan ya soma ganin napep nan ma duk masu passengers aciki ne suke wucewa shi kuma ya rantse saidai dare yayi masa da yashiga me passenger. Yayi kusan minti sha biyar sannan ya samu empty ya shiga, kowani pothole (gargada) aka shiga har cikin k’wak’walwansa yake ji. Se yanzun ya ke sake yima Allah godiya da duk wani abinda ya mallaka masa badon wai yafi sonsa bane akan sauran bayinsa kokuwa don ya kai se don haka yaso abinsa. Isansu gida keda wuya Afzal gabaki d’aya ya galabaita d’ari biyar ya mik’a wa me mashin d’in inda yake tambayarsa ko yanada naira d’ari se ya bashi d’ari hud’u. 

  “Ka rik’e duka ko kayi sadaqa da abinda ya rage” ya sanar dashi rai a murtuk’e sannan ya k’arisa ciki aka bud’e mishi gate. Lokacin har an sauk’o daga sallan Maghrib, Abba ya tarar a waje shima yana shirin fita da driver a gaba yana sauri don bud’e mishi k’ofa. 

   “Ha’a wancan ba Prince bane?” Abba ya tambayi driver’n yana k’arewa figure’n Afzal kallo don tabbatar da zancen nasa. 

   “Shine Alhaji” driver’n ya masa confirming. 

  “Prince ya haka? Ina ka shige?” Abba ya tambaya alokacin da Afzal ya k’ariso inda suke. “Network ya d’auke muna ta neman ka amman bai shiga, ina ka shiga ne? Ina motanka kuma?”

   “Hmm Abba long story motana yayi pachi da keke napep ma na k’ariso gida” ya fad’a tamkar zeyi kuka. Dariya ce ta kauce wa Abba har yana neman sark’ewa, ina irin dariyan nan da alhazai keyi ana yi ana jan nishi? Irin shi Abba yay tayi da k’yar tukun ya samu ya tsagaitar. 

   Lallai ma kuwa Afzal ya furta a ransa yana me mamakin Abba yanzu dariya zeyi masa akan ya tausaya masa? Ai yasan Ummi bazata mishi haka ba. 

   “Ahhh it’s good it’s good” fad’in Abba yana neman kame dariyar da ke sake son kauce masa “Kaga ko a babu yau kayi sabon experience koba haka ba?” Saidai shiru Afzal yayi bece komi ba ga girar nan ya had’esu kum waje guda. “Toh ka kwantar da hankalinka wuyan daka sha yau d’innan tattare yake da alkhairi.”

   Alkhairi de? Ya nanata a zuciyansa. Kallon Abba ya tsaya yi a yayinda ya zira hannu a aljihu tare da ciro wata k’aramar pack. 

   “Gashi open this” ba gardama ya amsa ya bud’e key’n mota ya tarar aciki. Toh fah! Ido ya d’ago yana kallon Abba cike da mamaki da neman k’arin bayani. 

   “Danna security ne kuma baka iya ba Prince?” Ya tambeysa jokingly. Nan ya danna inda d’aya daga cikin motocin da suke fake a parking lot tayi k’ara, da sauri ya maida kallonsa wajen tare da kuma dannawa don tabbatar da wace mota ce tayi k’aran. Sabuwar 2017 Mercedes Benz ce C43 AMG biturbo k’al acikin leda yaga tayi wuta, fara tas an k’ayata ta da black satin and ribbons. 

  “Abba!” Yayi exclaiming cike da mamaki bil adad alokaci guda ya nemi bak’in cikin da Amal ta tusa masa ya rasa. Shi abinda yafi basa mamaki ma  shine yadda Abba yasan wannan ne motan da yake tason ya siya tun watanni uku da suka shud’e wanda yake dai-dai da lokacin da motar ta fito. Kawai tuna lokacin da ya tura wa Sultan pic d’in yake, har yake cemar ga motan da yakeson ya siya toh har yaushe Abba ya shiga zuciyansa yasan sabon mota yake buk’ata when ko shekara biyu ma na wajensa beyi ba?

  “Abba! Mota ka siya min?” Ya sake tambaya full of wonder. 

   “Yes Prince ai na fad’a wa Umminka ta sanar da kai cewa na tanada maka tsaraba fatana de Allah sa tsaraban ya kar6u kuma ya burgek-” Afzal be basa daman k’arisa maganan daya soma ba ya rufe sa da runguma tsan-tsan murna da farin ciki. Da murmushi kwance fal a fuskan Abba ya zagaye hannayensa bayan d’an nasa shima, hugging him back. 

   “Abba thank you so much! I don’t know how to express my gratitude walalhi you made my evening” ya sanar dashi ba tare da ya katse rungumar ba. 

  “Am glad you like it son” se anan Afzal ya sake shi sannan ya juya yana kallon motan. 

  “Nasan so kake kaje kaga cikin motar kaman yadda nima nake son fita yanzu inada conference da colleagues d’ina so ina fatan this year will be convenient for you ko?”

  “For what Abba?” Ya tambaya a takaice da farin ciki kwance a birnin zuciyansa. 

   “Hajj nakeson kaika inason ka zama Alhajin kanka kaima Prince” Dad’i ninkin ba ninkin na d’azu ne ya ziyarci zuciyan Afzal wai kam ya akayi duk abinda yake dashi in mind Abba ke shirin miyar masa dashi reality? Tabbas ranan sunyi hirar nan da Ummi na cewa yanason yayi aikin Hajji wannan shekaran saboda bai ta6ayi ba a kullum yaje Saudi Umarah kawai yakeyi. Ji yake as if duniyan ma tayi kad’an ta d’aukesa don murna. 

   “Abba bazan iya tuna when last nayi kuka ba but with what you’re doing you’re making me want to. Abba this is the perfect time da nakeson yin Hajji har nayi discussing da brand manager namu ma.”

   “Toh Alhamdulillah seka shirya idan Allah ya kaimu lokacin seku tafi tare da Umminka.”

   “Abba thank you so much, Allah miyar maka da gidan aljannah ya k’ara bud’i kuma.”

   “Ameen Prince.” 

  “Saide bansan me nayi dana cancanci kyautuka haka ba.”

  “Prince farin cikin daka sanya ni da ka amince da k’udurin mahaifin y’ar nan kad’an ne daga cikin wanda kakeji yanzu. Nide ba abinda zance se Allah cigaba da yima albarka ya baka ‘ya’yan da zasu kula da kai su kuma farinta maka kaman yadda kake min ko fiye da hakan ma.”

  “Ameen Abba thank you so much.”

  “You’re welcome barin wuce kar na makara.”

  “Toh Abba ka dawo lafiya” bayan motan Abba ya fice Afzal ya k’arisa gun sabuwar motarsa har ya shige ciki seya tuna be d’auke ta a hoto ba, nan ya fito ya d’ad’d’auka sannan ya koma ciki ya shiga dubanta. Ba don yana so ba se don beyi sallan Maghrib ba yasa ya sauk’o ya nufi site na Ummi, alokacin tana bayi tana wanka. Guest toilet ya fad’a yayi alwala sannan yayi sallah, bayan ya idar yayi azkhar nasa sannan ya wuce d’akin ta tare da knocking. Tana amsawa ya shiga inda ya tarar da ita zaune kan stool na dresser side tana kwalya. 

    “Oyoyo my Prince ina ka shige haka? Gabad’aya ka tada min hankali” ta fad’a tare da kewayowa tana kallonsa. 

  “Ummi you can’t believe this!” Abinda ya soma ce mata kenan ko ta kan abinda tace beyi ba balle ya gaishe ta. 

  “An saya wa baby na mota!”

  “Yes!” Yayi exclaiming “So you knew?”

  “Eh mana ai surprise ne so did you like it?”

  “Yes!” Ya kuma exclaiming yana zama daga bakin kan gadon ta inda take zaune akan stool d’in. “Ni nama rasa ya Abba yayi yasan this car in particular nakeso wallahi kinsan tunda ya fito naketa budgeting yadda za’ayi in siya.”

  “Thank your friend then.”

  “Wa kenan Sultan?”

  “Shi de, shi Abba ya kira ya tambayeshi ko yanada masaniya akan abinda idan aka baka shi zakaji dad’i sosai ya bada amsa da wannan AMG.”

  “Allah sarki Sultan, I feel like the happiest soul alive.”

  “Ga kuma zamuje Hajj, it’s a wrap!”

  “Ummi please thank Abba once more.”

  “In shaa Allahu Prince.”

  “Toh tashi muje kiga cikin motan kinga panaromic roof d’in kuwa? Da car radio d’in? My goodness! Wani abun ma sekinga gearbox d’in ga wani k’arar da take badawa kafin engine ya tashi” ya fad’a sounding happy.  

  “Tsaya to in gama jan girar nan se muje.” Jirarta yayi bayan ta gama suka fice inda Ummi ta rik’a sawa motar albarka. 

  Suna cikin cin dinner ne ta tambayesa inda motarsa take kasancewar bata gani a inda ya soma parking ba. 

   “Kede kar ki tuno min da batun motan can kinsan kuwa acikin keke napep na dawo gida yau?” Dariyan da Abba yayi masa haka ma Ummi ta zauna tayi shide ya rasa abin dariya anan, “Wayaga Prince acikin a daidaita sahu” se ta kuma k’yalk’yalewa da wata dariyar. 

  “Seki tayi ai” ya fad’a a fusace tare da jan k’aramar tsuka. Bayan ta gama neman tsokanan nasa kwatsam sak’on da Abba ya bata ta isar masa ya fad’o mata. 

  “Yauwa Prince Abbanka yace in tambayeka.”

  “Me fah?”

  “D’azu Abban Nazeefah na nan ai-“

  “Ni kinma 6ata min mood wallahi” ya katse ta yana mey had’e girarsa. 

  “Toh Prince ka manta ka riga ka amince da auren ne?” Ta fad’a a hankali gudun kar ransa ya kuma 6aci. 

  “Nikam ba yanzu ba” ya amsa a takaice. 

  “Toh se yaushe?” Shiru yayi be sake cewa komi ba se faman latsa wayansa yake yana going through memes da Sultan yayi mentioning nasa a twitter. Hannu tasa ta k’wace wayan “Ummi please give it back” ya fad’a da sauri. 

  “Ina maka magana kana latsa waya wallahi ko ka bani takamammen rana ko in bawa Abbanka duk wanda yayi min.”

  “Toh kiyi mana ni ina ruwana ban damu da yarinyan ba balle aurenta ya zame min matsala ni bani wayana in wuce site d’ina.”

  “Toh fah!” Ta fad’a tare da ta6e baki “Prince ka rufa mana asiri don Allah.”

  “Da nayi mey?”   

  “Bade shirin wulak’anta yarinyan nan kake ba bayan anyi auren nan, don Allah kar kayi haka.”

  “Kekam da assumption Ummi! Allah kyauta. Meyasa zan wulak’anta ta? Just pass me my phone” ba gardama ta miyar mishi “Toh yaushe kakeso ayi bikin? Kaga se su soma shiri suma, idan ranan is not convenient for them kuma se a zauna ayi adjusting koya kace?”

  “Toh why not su suyi fixing date d’in da kansu nifa adena tak’ura min.”

  “Amman kai kam ba a iya maka ba wallahi sam bakada mutunci, naga ai girmama ka mahaifin nata yayi har yace kaine zaka za6i rana kasa amman kake wannan shagantakar.”

  “Toh naji I’m sorry” ya fad’a tare da sauk’e nauyayyar ajiyar zuciya “Bari bayan mun dawo daga Hajj idan Allah ya kaimu rai da lafiya.”

 “Toh ko kai fah? Kaga bayan babbar sallah se a d’aura ko?” Ta tambayesa cike da gastine. 

   “A’a k’ullewa ba d’aurawa ba” ya mayar mata da amsa. 

  “Me dafa maka abinci Prince ni zaka bawa amsa?” kafin tace zata mik’a hannu takai masa bugi har ya mik’e yana mata dariya

  “Shegen dogin k’afa a wajen” gwalo yayi mata sannan yace, “Ni zan wuce site d’ina it’s been a hectic day zanyi Sallah in kwanta idan Abba ya dawo ki sake yi mashi godiya, goodnight I love you.”

  “Sleep like a baby” da haka ya wuce site nasa. Bayan ya gama duk wani abinda zeyi ya d’ale gado ya kwanta dai-dai nan Sultan ya danna masa kira bayan sun gaisa yake tambayansa how went his day. Tsuka yaja sannan yace “Kaide ka barni da ‘yar gudun hijirar can.”

  Bayan dariyan da Sultan ya narka ya buk’aci Afzal da ya basa labarin meya faru. Nan ya labarta mai komi inda Sultan yata dariya kaman zararre yana mamakin guts na Amal, sam idan mutum ya ganta baze ce zata iya yin abubuwan da Afzal ke fad’i a kanta ba. 

   PAGE 0⃣7⃣

     Rana bata k’arya saide uwar d’iya taji kunya. Yau ana sauran sati uku azumi kenan. Afzal ne da Sultan zaune bisa d’aya daga cikin teburan da suke baje acikin office nasu Afzal a ground floor suna hirar match da akayi jiya tsakanin Roma da Barcelona wanda aka sha Barcelona wane ayi musu kuka. Ana cikin haka ne Afzal da hankalinsa ya duk’ufa a waje yana kallon wasu ‘yan mata biyun da suke tsaye da wani d’an saurayi a bakin gate d’in se rashin kunya suke zuba mishi barin ma me d’an haske me maroon hijabi wacce ke tsaye dab gabansa wane zata cukume masa collar. Dukda cewa besan meke faruwa ba alamu sun nuna me marron hijabin na tare wa k’awarta wacce ta kasance me talle fad’a ne. Abu kaman wasa fad’a yak’i ci yak’i k’arewa daga bisani kawai me maroon hijabin tasa hannu ta wafce wani abu kaman kud’i daga hannun saurayin wanda kafin tace zata sa gudu har ya cafko ta, ita ko a garin k’watan kanta ta ture wani glassy sign board me yin wuta-wuta dake gefen gate d’in wanda ke d’auke da sunan bankin aciki. Abu ne wanda ko ba a fad’a ba mutum yasan zeyi bala’in tsada saboda yadda yake a tsare da jan ido. Ba shiri securities sukayi wajen duk anan Afzal na kallonsu daga ciki. 

  “Dude wai meke faruwa ne kam achan?” Sultan da se yanzu hankalisa ya iske su ya tambaya. 

  “Let’s go find out” ya amsa shi inda suka miqe suka nufi wajen. Juyowan da ‘yan matan zasuyi kawai suka had’a ido hud’u da Amal. Ashe itace wacce ke sanye da maroon hijabin, wacce ke ta rashin kunya iya gadaman ranta, lallai kuwa ta shirya biya musu sign board. Idonsu na had’uwa Amal taji cikinta ya d’au ruwa a yayinda zuciyarta ta har6a, for a second ta nemi numfashinta ma ta rasa tuna abinda tayi masa last had’uwansu. Yau shikenan kashinta ya bushe ita a iya tsammaninta bazata sake had’uwa da shi ba se gashi Allah yayi proving nata wrong today.

   “Good day Sir” securities d’in duk suka gaishe shi. Wani har6awa bugun ziciyar Amal ya kuma yi jin securities sun kirasa da sir bade anan Afzal ke aiki ba yau nata ya k’are. 

  “What’s going on in here?” Ya buk’ata cikin tattausar murya a yayinda yayi banza da Amal sam be nuna ya ta6a wayanta ba. 

  “Sir wannan yarinyar ce ta ture sign board d’innan ta biya kud’in kuma tak’i wai sam ba ita ta ture ba bayan kowa shaida ne anan itace ta ture so muna shirin yin police station ne da ita” d’ayan security’n yayi bayani. Take Amal taji cikinta ya sake to the mention of police station, yau ina zata sa kanta? Police station? Gidan yari fa kenan! Danqaree!

  “Wallahi bani na buge ba” ta kuma fad’a. 

  “Bake kika buge ba?” Tambayar securitin itade k’awar nata me tallen gyad’a ko uffan bata kuma cewa ba har yanzun gudun kar suce zasu had’a da ita akai police station d’in. Dama ita tun d’azu tace wa Amal su bar bawan Allan kawai da Allah tunda ya rantse yace shi baze basu kud’insu ba, Allah ze isar musu amman don rigima irin na Amal tak’i. 

  “Eh mana ina wannan ne ya jani baya a garin k’watan kaina se abin ya fad’i wallahi ni bani na fasa muku abunku ba don haka ba abinda zan biya” ta fad’a confidently dukda cewa chan ciki ta gama tsurewa. 

  “Se mu gani, se muga idan mukaje police station d’in sukace ki biya ko zaki fad’a musu hakan” Ganin fa dagaske police station d’in suke son yi da ita don kuwa gashi har sun kawo mota Amal ta soma jin fitsari nan take. Ubanwa zeyi bailing nata idan suka kaita chan d’in yanzu? Tasan ko had’a sama da k’asa zatayi Mami ko zuwa dubanta bazata yi ba Papi kuwa baida kud’in bailing nata. Yau kashin ta ya bushe, ashe da taji maganan Falmata sun ja mar Allah ya isan kawai. 

  “Kai meya faru ne?” Afzal da ya nisanta ya tambayi yaron. 

  “Kud’in gyad’an su nikeson basu suka k’i amsa wai sam suna bina bashin d’ari biyu nikuma banda masaniya akan hakan sharri kawai suke shirin min musamman wannan yarinyar” ya nuna Amal. 

  “Wallahi bawan Allah bazaka gama da duniya lafiya ba, kullum kata cin gyad’an nan a bashi kace bakasan da hakan ba?” Amal data katsesa ta tambaya. 

  “Yanzu akan N200 shine kuka rusar da wannan board d’in?” Afzal ya kuma tambayansa. 

  “Oga ni bani na rusa ba itace agarin wafce hannunta ta ture.”

  “Yanzu ka basu kud’in gyad’an su” yace dashi. 

  “Wallahi ni basu bina kud’i ga kud’in gyad’ansu na yau N50.”

  “Nace ka basu kud’in su” Afzal ya kuma nanatawa. 

  “Gaskiya ni bazan bada komi ba saboda basu bina komi.”

  “Shikenan kayi tafiyanka” hannu ya sa a pants pocket nasa ya zaro wallet nasa tare da miqa wa Falmata d’ari biyar. 

  “A’a don Allah ka bari ni na barshi da Allah dama tun d’azu nike cewa Baby da ta barshi da Allah amman tak’i.”

  “Karki damu amshi.”

  “Toh ai banida canji.”

  “Don’t worry keep it.” Hannu bibbiyu ta miqa ta amsa, “Nagode Allah saka da alheri Baby mu tafi.”

 “Ku tafi? Ku tafi ina?” Afzal yayi saurin tambayarta tare da kewayo da kallonsa akan yaron “Kana iya tafiya kema me gyad’a kina iya barin nan.”

   “Nagode k’awata fah?” Ta tambaya. 

  “Bakiji me securities d’in sukace bane? Police station zasuyi da ita in kuma kinason binta ne fine.”

  “A’a a’a!” Tayi exclaiming da mamaki tana ja da baya, “Baby ki bisu zanyi sauri inje gida in sanar da Mami halin da ake ciki.”  

   Lallai ma Amal ta furta a ranta yanzu tafiya Falmata zatayi ta barta bayan ta sanadinta komi ya faru? Hmm amman ba amana. 

  “Falmata don Allah karki tafi ki barni, Ya Afzal don Allah kayi hak’uri wallahi ba da gangan na buge ba” ta juyo tana kallon Afzal da maraicaccen fuska ko kunya bata ji ba. 

  “Securities ku tafi da ita make sure she pays for this or simply lock her up, Sultan lets get back in” ya yi declaring ba tare da ya kalli koda direction na Amal ba. 

  Da sauri ta shawo gabanshi “Don Allah karka min haka kayi hak’uri na tuba.”

  “Get out of my sight!” ya sanar da ita a tsawace cikin tattausar muryan da yasa ta fashewa da kuka. “Ya Afzal don Allah kayi hak’uri na tuba, wallahi na tuba.” Shiru yayi na ‘yan lokuta sannan ya nisanta, “Na farko, I don’t own this building kinyi 6arna dole ki biya there’s nothing I can do.”

  “Eh nasan ba naka bane amman alamu sun nuna kana da matsayi anan don Allah ka basu hak’uri su barni in tafi kafi kowa sanin cewa Mami da Papi basu da k’arfin bailing d’ina, ba don hali ba amman don Allah ka rufa min asiri Ya Afzal.”

  “Sultan mu tafi mana me kake jira ne wai kam?” Yayi banza da ita. 

  “Ya Afzal don Allah karka min haka kayi hak’uri I’m so sorry” nan ta kuma fashe da wani kukan a yayinda hawaye ke ambaliya a fuskarta sede ko kallonta Afzal beyi ba balle tausayinta ya kamasa. 

  “Guy kayi mata hak’uri please I will settle the bill” fad’in Sultan da Amal ta basa tausayi dukda cewa beji dad’in abinda tayi ma abokinsa da mota ba. 

  “Wallahi tallahi kade ji rantsuwa ko guy? Idan har kayi bailing yarinyan nan ban yafe ba” Afzal ya sanar da Sultan in a serious tone, ai dama ya fad’a seya rama abinda ta yi masa. 

“Let’s go” yace da shi, ba musu Sultan ya shiga binsa ganin yadda ran abokin nasa ya 6aci. 

  “Afzal please pity the girl” Sultan daya matso kusa da Afz ya sanar daahi yadda ba wanda ya jisu. Alokacin har securities sun soma kokuwa da Amal suna k’ok’arin sata cikin mota sede sun garara saboda k’in basu had’in kai da tayi. 

  “Pity her fa kace? Ko ka manta abinda tayi min da mota ne ranan?” 

  “We’ll resolve everything yanzu dan Allah kayi mata hak’uri kar ka 6ata mata future kade san yanzu a cell zasuje su jefa ta har se idan ta biya kud’in abin nan kuma sanin kanka ne iyayenta basuda k’arfin nan” a hankali maganganun Sultan suke tasiri jikin Afzal se de still bai jin ze iya yafe mata. “Ince masu su dakata?” ya tambayesa a hankali, shirun da Afzal yayi ya bawa Sultan daman tsaida securities d’in, ba gardama sukayi hakan. 

    “Wai kam Sultan ka manta abinda tamin ranan ne?” Ya tambaya ransa na tafasa. 

  “Ni? yaushe kuma?” Amal da ta jiyo sa tayi saurin tambaya duk ta kid’ime. 

  “Oww k’arya kuma zaki sake yimin?” Nan ne ya juyo yana galla mata hararan daya sata had’iyan miyau ba shiri. “Guards what’re you guys still waiting for? Kuzo ku jata mana ko sena kira branch manager’n tukuna yayi firing naku duka?” Ya tambaya yana galla musu harara. 

  “No Sir abokin ka ne yace a saketa.”

  “Ni kuma nace take her away.”

  “Dude please kayi mata hak’uri” cewar Sultan again. 

  “Ya Afzal don Allah have mercy on me, na tuba ka yafemin” ta fad’a tana kuka sosai a yayinda securities suka shiga janta. Ido ya musu suka saketa sannan ya kirata. Har tana neman cin tuntu6e ta k’ariso tana mey share hawayenta da k’asan hijabinta. 

  “Me kikayi min da mota ranan?” 

 “Kayi hak’uri don Allah na tuba” ta amsa cike da fargaba. 

  “That is not what I asked me kikayi min da mota ranan?”

  “Na maka pachin taya amman na tuba.”

  “Meyasa? Ni sa’an kine?”

  “A’a don Allah kayi hak’uri na tuba.”

  “Kinsan nawa ne wancan abinda kika rusan?” Ya tambayeta had’e da d’age gira d’aya, kai tayi saurin kad’awa. “It is nothing less than eighty five thousand (85k)” ya sanar da ita. Ido ta zaro waje wane 6eran da aka kama yana sata. 

  “Wallahi Papi baze iya biya ba don Allah ka basu hak’uri.”

  “Hak’uri won’t fix anything the only thing that could fix that mess is ayi replacing da sabo.”

  “Ya Afzal wallahi ko nan da shekara ka bani bazan iya siyan sabo ba.”

  “Then tun da wuri kisan yadda zakiyi hakan kokuma ki shirya zuwa gidan yari.” 

   “Ya Afzal don darajan Allah ka taimaka min ka rufa min asiri ka basu hak’uri.”

  “Kinsan wani abu? Inda wata ce chan ta rusa koda k’awar kice for example da tuni na bada kud’i an sai sabo, kinsan dalilin dayasa bazan taimake ki ba?”

 “Saboda na maka rashin kunya, na 6ata maka mota nayi maka abubuwa kala-kala amman don Allah kayi hak’uri wallahi ban k’arawa na tuba.”

  “Jeki kira k’awarki dake la6e achan” ya buk’aceta. Falmata na ganin Amal na nufo inda take la6e ta shiga neman hanyan gudu da k’yar Amal tasamu ta amince ta biyota. 

  “Gata nan” cewar Amal. 

  “Dude kana cin abin nan ko?” Afzal ya tambayi Sultan yana nuni da soyayyen gyad’an dake kan Falmata wanda ‘yan Maiduguri ke kira da mandawa. 

  “Yes?” Sultan ya amsa sa cike da neman k’arin bayani. 

  “Alright, k’irga gyad’an nawa ya rage duka” ya buk’aceta, nan ta sauk’e tray natan ta k’irga “Na d’ari biyar da hamsin ne N550.”

  “Good amshi tray d’in Amal” ba musu tayi yadda ya buk’ata. 

  “Good inason ki zauna- no ki tsaya anan k’ark’ashin ranan nan ki shiga gyara gyad’an nan kina tarasu cikin leather daban, idan kin gama ki kawo min ciki and mind you ko alaman 6awo na gani aciki aikinki ia ruined zan saki a hannun securities d’innan suyi duk abinda sukayi niyya dake” ya fayyace mata muryansa ko alaman wasa babu bale Amal tace almarai yake bata. Ba ita kad’ai ba harta Sultan da Falmata seda suka sake baki ganin yawan mandawan da Afzal ke shirin sa Amal gyarawa. Mandawan da ko leda d’aya akace mutum ya gyara seya galabaita. 

  “Duka na kan tray d’in?” ta tambaya cike da rashin yarda. 

  “Yes you heard me right, haka ma zakiyi gobe da jibi in fact for a whole month or two only then zan amince in biya kud’in board d’incan da kika rusa. Kekuma Falmata ko?” Ya juyo kan k’awar nata “Daga yau kina ajiye min gyad’an nan naki na d’ari biyar and make sure kin taho tare da Amal, kina ji na?”

  “Eh, eh naji” ta amsa. 

  “Good oya kekuma me kike jira da baki fara gyarawa ba? ga chan tap (famfo) a chan go and wash your hand da akwai sanitizer a gefe kiyi sanitizing hannunki. Securities you can go back to your posts zanyi handling mess d’in.”

  “Alright sir” suka amsa tare da ja da baya. 

  “Toh Ya Afzal amman naga kaman gyad’an d’ari biyar yayi wa Ya Sultan yawa ina laifin in 6are mishi na d’ari??” Amal ta tambayesa cikin best lady like manner nata. 

  “Sauran inga kina tayata kekuma” yace da Falmata totally ignoring Amal, “I’ll be inside duk abinda kukeyi anan zan hangoku daga ciki don’t think of messing with me, guy let’s go.”

  “Mu nemi inuwa toh mu zauna” cewar Amal tana mey neman inda akwai rumfa. 

  “Baki ji me nace bane? Nan k’ark’ashin ranan nakeso ki tsaya kiyi abinda na saki, ko jinguna naga kinyi jikin bango toh zan fasa biyan kud’in in kuma sasu su kaiki police station.”

  Miyau ta had’iye “Allah sarki don Allah ka tausaya min.” Be sake yi ta kanta ba shida Sultan suka wuce ciki. Tun Falmata na iya juran taya Amal tsayuwa k’ark’ashin ranan taga bazata iya ba ta nemi inuwa ta zauna, Amal baiwar Allah se gyaran gyad’a take ko 6awo bata bari kaman yadda Afzal ya buk’ata. Tayi leda shida (6) ta soma jin jiri saboda zafin ranan, ji take kaman ta tsala ihu amman ba daman yin hakan. Haka abin tausayi seda ta kwashi kusan  awa biyu k’ark’ashin rana me tafasar da k’wak’walwar mutum sannan ta samu ta gyara duka. Alokacin har ta gama kod’ewa idanunta sun kad’a sunyi ja, bayanta wane ze 6alle se gumi da zufa take had’awa. Security tasa yayi ma Afzal magana nan ma seda ya gama ja mata aji sannan ya fito da wani saucer a hannunsa kad’an daga cikin gyad’an ya d’iba ya kira Falmata ya mik’a mata ragowan “Ga wannan kici wanda zaki iya ci sauran ki kai wa k’annenki a gida kokuma kiyi sadaqa dashi a layi. hungo kud’in ki.”

   Baki bud’e cike da mamaki Amal ta tsaya tana kallonsa. Yanzu duk uban wahalan nan d’an abinda ze d’iba kenan? Ina laifin ita data sha wuyan gyaran ne ma ze ce mata ta tafi da ragowan amman seya kama ya bawa Falmata??? Ji take kaman zuciyarta zata k’one don tafasar da takeyi. Na farko duk a sanadin Falmata ne wannan abu ya faru se gashi yanzu ta kwashi awa biyu tana aikin sarrafa gyad’a daga k’arshe kuma a bawa Falmata wai taci? Riba biyu fa kenan, ga kyautan sarrafaffen gyad’a ga kuma yanzu ba se tayita yawo a gari tana talle ba lokaci guda za’a siye mata fiye da rabin gyad’anta. Lallai kuwa daga yau tayi hankali wallahi duk wani abinda bai shafeta ba ba ruwanta dashi.

   ***

   Kaman yadda Afzal ya tsara haka Amal da Falmata suka zo ma yau, yadda akayi jiya haka a ka kuma yau, gyad’an d’ari biyar (500) tas ta sarrafa tsaye k’ark’ashin rana me uban tafasa k’wak’walwar mutum, sanin kowa ne yadda ranan Maiduguri yake daban da na kowani gari. Bayan ta k’are ya fito ya bawa Falmata duka mandawan yau kasancewar Sultan baya nan shi kuwa be iya ci ba, itade Amal k’una ne kawai zuciyarta batayi idan taga yabawa Falmata gyad’an dake d’aukanta awa biyu ko fiye tana gyarawa. 

    Anyi hakan na kwana hud’u Amal taga fa idan ta cigaba da haka toh wallahi setafi gawayi bak’i, ga shi tun ba’a je ko ina ba bayanta ya soma mata ciwo, kuma gashi tasan taurin kai da zuciya irin na Afzal ko mutuwa zatayi ta sake dawowa ba canza mind nasa zeyi ba tun akan abinda ya faru a asibiti ranan ta gano hakan, ta sani ras seta cika wata ko watanni biyu da ya yanke matan sede dukda hakan bazata kariya ba zata basa hak’uri. 

    Washegari bayan sun isa ita da Falmata sega Afzal na fitowa daga office da alama masallaci ze zarce yayi sallah, bayan ta jira ya idar ya fito ta taresa ta shiga basa hak’uri harda guntun hawayenta amman kaman yadda tayi tsammani haka ko kallonta beyi ba balle ya tausaya mata yaja baya da wannan punishment. Haka tana kuka ta koma k’ark’ashin ranan ta cigaba da gyaran daga inda ta tsaya. Bayan ta iso gida ta tsaya a shagon Usama ta sai 40 leaves. Bayan sallan Isha ta d’an huta sannan ta d’au littafin da biro ta shiga rubuta, “I’M SORRY YA AFZAL I WILL NEVER DISRESPECT YOU AGAIN” layi-layi tun daga fejin farko har seda ta kai na k’arshe, ko bacci bata samu tayi ba daren ranan se bayan sallan Asuba data gama. 

   Yau bayan ita da Falmata sun isa office nasu Afzal me gadi ya isar mata da saqon da Afzal ya bada a mik’a mata, na cewa baya nan ya fita meeting amman yasa asa mata ido kar ta kuskura ta ko tsuguna bale tayi tunanin shiga inuwa kokuma ta rok’i Falmata data tayata. Bayan kuma ta gama gyarawan ta d’iba rabi ta bawa Falmata rabi ta ajiye masa. Hakan tayi bayan tagama ta had’a masa rabin da littafin data siyan ta bawa me gadi sannan suka fice. 

  Se chan kusan yamma Afzal ya dawo office, bayan me gadi ya miqa masa saqon ya buk’acesa littafin kuma daga gun waye ne? A takaice ya amsa shi yace daga gun ‘yan matan ne. Documents nasa ya tattara ya dawo gida inda ya kaiwa Ummi gyad’an. 

  “Prince mandawa dayawa haka kuma gashi har an 6are an gyara” fad’an Ummi tana k’ok’arin kai amount data d’iba baki. “Gaskia nagode.”

  “You’re welcome lemmi rush to my site.”

  “Kaifa bazaka ci ba? Gashi ya soyu dai-dai be k’one ba.”

  “Nahh ban iya ci ba.”

 “Yo baka ta6a ci ba dama taya zaka iya? Kade gwada kaji Allah da dad’i.”

  “No thanks” d’iba tayi a hannunta “Bud’e bakin in sa maka kaji” seda tayi dagaske ta samu ya bud’en tasa mishi se kuma ya mishi dad’i ashede for all these he’s been missing alot. A saucer ta d’iba masa ya wuce site nasa dashi. Bayan ya watsa ruwa ya fito da alwala sannan ya shirya yaje masallacin unguwa yayi sallah. Wayansa ya had’a a charging ya shiga viewing Instagram feeds nasa yana jefa gyad’an time to time a baki. Chan ya mik’a hannu ya jawo littafin da me gadi ya basa na cewa Amal ce tace a bashi. First page d’in ya bud’e ya soma cin karo da kalmomin hak’urin data rubuta. Murmusawa yayi tare da flipping next page d’in nan ma haka, tsallakawa yayi ya kai tsakiya yaga har nan hak’urin take basa. Murmushin yake har yanzu ya shiga bi daga farko zuwa k’arshe sannan ya mik’a ya ajiye inda yake keeping important documents nasa. Ashe tasan yin rashin kunyar da take ba kyau amman takeyi, da kyau. 

  A tsammanin Amal washegari idan taje ze ce mata ya yafe sauran punishment d’in ta tafi sede ta tarar da opposite d’in hakan. Sam yi yayi wane saqon nata be iske sa ba, don dad’in da gyad’an ya masa jiya yau har cikin office nasa ya shigo dasu da ta gyara kad’an se ya kwashe yaci, kafin su hankara Afzal ya cinye gyad’an d’ari uku da ashirin (N320) shi kad’ai. Sai the following day ne bayan sunzo ya saye gyad’an har Amal ta fara gyarawa yace masu ta bari su tafi ya yafe mata. Dad’i sosai taji ashe de yana sauraron hak’uri lallai kuwa ta kama kanta kar ta sake yi masa abinda ze fusatar dashi if not itace zatayi bearing consequences. Don ta lura duk wani iskanci da rashin ji da take ji dashi Afzal yana gaba da ita. 

   Tun daga ranan kullum Falmata ke kawo wa Afzal gyad’a wani sa’in Amal kan biyota while most of the times ita kad’ai take zuwa. Anytime kuwa suka zo tare da Amal a bakin gate take la6ewa gudun kar ko kallonsa tayi yace ze bata wani punishment d’in, abu kaman wasa Afzal ya zama addict na gyad’an Falmata har idan gari ya waye beci ba baya jin dad’i. 

   Rana d’aya ko mey ya buga kan Amal kawai ta buk’aci Falmata da ta bata mandawan Afzal, zama tayi ta gyara masa su tsaf ko 6awo d’aya babu sannan ta baiwa Falmata da ta kai masa kaman kullum yau ma ta tsaya bakin gate tana jiran fitowarta. Sosai Afzal yasha mamaki bayan da Falmata ta mik’a mishi gyararren gyad’a cewa kuma daga Amal ne. Lallai yarinyan tayi hankali yayi tunanin haka a ransa kode she is upto something not good again ne? Waya sani ko ta barbad’a masa maganin da ze rud’a masa ciki yasa masa diarrhea (gudawa) amman kuwa idan har tayi kuskuren yin hakan se tayi nadaman shigowa duniya. 

  “Kikace Amal ce ta gyara duka wannan?” Ya sake tambayan Falmata yana mey bin mandawan da kallo. 

  “Eh” ta amsa tana kallonsa. 

  “Yau ma tana wajen ne?”

  “Eh.”

  “Jeki kira min ita.”

  “Toh” da haka ta sauk’a k’asa sede sam Amal tak’i biyota, da k’yar Falmata ta samu Amal ta amince bayan rantsuwan da tayi ta mata na cewa ba abinda Afzal zeyi mata. Ita Amal gabad’aya cikinta ya d’au ruwa gudunta wai kar yace tayi gwaninta yace ze sake bata wani punishmennt d’in. Bayan knocking da Falmata tayi Amal tayi sallama sannan suka shiga ciki. Yau kaman ba Amal ba harda durk’usawa da zata gaishe da Afzal, dama bahaushe yace fad’an da yafi k’arfinka dole ka mai dashi wasa. Yau duk taurin kai da rashin ji irin na Amal ta tarar da wanda yafita hakan. 

   “Ke kika gyara?” Ya tambaya yana tura mata ledan gyad’an gabanta. Kai ta gyad’a a hankali. 

  “Meyasa?”

  “Kawai.”

  “Nace me yasa?” Ya kuma tambayarta. 

 “Allah babu.”

  “Zo ki d’auka kici I don’t trust you.”

  “Wai tunani kake zan cutar dakai in sa maka wani abin a ciki?” Ta tambayesa da mamaki. 

  “Thank god you know.”

  “Wallahi ba abinda nasa ciki.”

 “Then zo kisa a bakinki kici in gani.” Sanin ba abin cutarwan da tasa a ciki ta k’arisa ta d’iba kad’an ta kai baki ta tauna sannan ta had’iye, duk anan kallonta Afzal yake. “Kaga ba komai wallahi.”

  “Thank you” yace da ita. 

  “You’re welcome” ta amsa. 

  “Baki amsa min tambaya na ba har yanzu why did you do it?”

  “Ya Afzal bana son mu zame annabi da kafiri a matsayin mu na musulmai, nasan nayi maka laifi but like I said I’m sorry bamu san wa ze amfana da wani ba wataran kuma ni bana son in mutu sanin cewa wani ya rik’eni a zuciya, ko baka fad’a ba nasan ka tsaneni kana jin haushina but I’m sorry I promise never to disrespect you again.”

  “Hah!” Dariya kad’an ya saki yana mey juya kansa akan office chair’n da yake zaune akai “So kinsan cewa disrespecting na gaba da kai ba kyau?” Ya tambaya had’e da d’age gira. 

  “Eh na sani kayi hak’uri” ta amsa a nitse tare da sunkuyar da kanta. 

   “Meyasa kikeyi then? Saboda mutane suyi miki baki? Kinsan sharrin bakin mutum kuwa?”

   “I’m sorry” ta furta tare da pouting bottom lip nata. 

  “We’re good” ya fad’a bayan tsawon lokacin daya d’auka yana mey wasa da pen da yake rik’e dashi a hannunsa. 

  “Dagaske baka tsane niba yanzu?”

  “I never said I hate you.”

  “Thank you Ya Afzal” ta fad’a wanda yasa sa murmusawa kad’an. Dubu ya zara ya mik’a wa Falmata “Ya Afzal ba canji” tayi saurin cewa. 

  “Ki bawa Amal change d’in ta rik’e in kin samu.”

  “Name nikuma?” Tayi saurin tambaya. Wani banzan kallo ya watsa mata wanda yasa tuni ta shiga yi masa godiya ba tare da tasan tayi hakan ba. Aikin gabansa ya cigaba da yi yana cin gyad’an da Amal ta gyara masa time to time. 

   ****

    Haka nan tun daga ranan anytime Amal is less busy zata d’au lokaci na musamman ta gyara  gyad’a wa Afzal gyad’a rananda batada lokaci kuma haka Falmata ke kawo masa atimes ta gyara mishi most of the time kuma yace karta damu zeyi da kansa. 

  *** GIDAN ALHAJI ABDALLAH ***

  “Ina Nazeefan ne wai kam?” Cewar Mummy tana me lek’an k’ofa ko zata ganta. Bada dad’ewa ba sega Nazeefah tafe, ba shakka tunanin auren da ta sa a gaba ne ya zubar da ita haka dan kuwa har duhu ma tayi sekace ba ita ba. Ga kwana biyu ta rage jin kid’i da sauran rawan kan da ta saba, a takaice de ta sauya halayenta cikin samarukanta befi d’aya zuwa biyu suke huld’a ba yanzu, batun aure kuwa bata sanar da kowa ba banda Rumaysa k’awarta. 

  “Khaleefah be fad’a miki ina kiranki bane kam?” Abinda Mummy ta fara ce mata kenan. 

  “Ya fad’a gani” ta amsa tana neman zama gefen Mummy akan bed bench dake d’akin. 

  “Batun auren naki ne dama kun kusa gama semester’n nan ko?” Kai zalla ta gyad’a. 

  “Good tun last two to three weeks Daddy ya tura saqo wa Afzal amman se shekaran jiya ya bada amsa.”

  “Amsan mey?” Tayi saurin tambaya.  

   “Game da ranan aurenku da Daddy ya buk’acesa yayi fixing, kaman yadda zaki Hajj this year shima Afzal hakan Abbansa ke shirin kaisa so yace bayan ya dawo ze bada specific date kinga by then kuna hutu kuma ko?”

  “Wannan cin fuska da mey yayi kama? Shin keda Daddy kuna son Afzal ya mutuntani ya ganni da k’ima kuwa? Yanzu Mummy ace ko ranar aure na Daddy baze bari inyi deciding da kaina ba komi se abinda Afzal yace, ba damuwa” ta k’are maganan hawaye na ciko mata a ido. 

  “Toh ya muka iya Nazeefah? Ko ni ban goyi bayan shawaran nan ba amman Daddy’nki koni ya dena jin maganata hak’uri ya zama dole, kede kawai ki cigaba da addu’a Allah yasa Afzal ya rik’e ki amana ya kula mana dake.”

    “Da abinda Daddy keyi ko nine shi Afzal d’in bazan rik’e matar da iyayenta ke nunawa batada k’ima kona misqala zarratun da amana ba” ta fad’a chan ciki-ciki sanin sarai Mummy zata jita sannan a fili tace “Ni zan koma d’akina.”

  “Tsaya tukuna kinsan gobe first of Ramadan ko? Daddy yace zan tayaki mu had’a kayan shan ruwa wa Afzal.”

  “Wallahi ni bazanyi ba” nan take ta rushe da kuka. “Wallahi bazan yi ba.”

   “Nazeefah da hankalinki?”

  “Mey hakan kuke shirin min keda Daddy please? Sekace wata bazawara second class slut wacce bata da k’ima da daraja a idanun jama’a. Haba Mummy koda Daddy ya amince be kamata ke ki biye masa ba, saboda farin cikinku na yarda na amince da auren dolen nan da kuke shirin min dukda cewa kun sani wallahi yau idan na kai k’arar ku gun ko wani malami ne a garin nan hana aukuwan auren nan za’ayi saboda ko musulunci ya hane yin auren dole amman duk baku ga k’ok’ari na ba? Haba mana! Yanzu kuma zaku sake tilasta ni in kai masa abinci? Shi waye? Mijina ne shi? Ko nid’in nace muku ina son shi ne da kuke ta nema min gindin zama gun shi haka?”

   “Allah baki hak’uri nide saqon da aka bada na isar miki idan kinga bazaki iya bi ba fine Nazeefah kece da rayuwarki kuma dama kin saba yin abinda kika ga dama ba abinda iyayenki sukeso ba, go ahead sue us to court if that will please you” Mummy ta sanar da ita rai a 6ace sam bata ji dad’in abinda Nazeefah tace mata ba, eh auren dole ba kyau amman ai kuma ita ta janyo komi wa kanta kuma tasani koda ba’a tone zuciyan Daddy ba, tasan bawai da son ransa yake yin abubuwan da yakeyi ba, he is only doing what he thinks is right as a father. 

   “Ki tashi kina iya tafiya” ta sanar da ita ba walwala a fuskanta sam. 

   “Kiyi hak’uri” daga fad’in haka ta mik’e da hawaye na bin k’uncinta ta fice. 

  Washegari Daddy da kansa ya tura Nazeefah kitchen ta samu masu aiki da Mummy suka had’a had’add’en kayan bud’an baki wa Afzal. Daddy ya bari masu aiki su kai mai ma yak’i wai sam se de Nazeefah in kuma bazata kai ba tabar masa gida. 

   Ita Nazeefah ko a mafarki bata ta6a kawowa a tunanin ta cewa Daddy ze juya mata baya haka ba. A da se abinda tace da kuma abinda takeso yakeyi amman yanzu ko damuwa da feelings nata baiyi, abinda ya mishi kawai yakeyi regardless of her feelings. Bayan kukan data dad’e tana yi a bayi ta wanko fuskanta sannan ta fito ta sanya hijabi ta d’au basket d’in ta fice. Wani sabon kukan ta soma yi a bakin gate d’in, seda ta gama shan kukanta sannan ta k’arisa. Site na Ummi ta nufa inda Afzal ke zaune kan two seater ya mik’ar da dogayen k’afafunsa kan centre table se faman latsa waya yakeyi. Sallama tayi ya amsa ba tare da sanin wacece ba, ganin itace yaja k’aramar tsuka tare da kawar da kansa idan da yasan ita tayi sallamar da be amsa ba. Wayansa ya cigaba da latsawa tamkar ba mutum bane ya shigo parlourn. Tafi minti biyu tsaye bakin k’ofan ta na neman koda inuwan mutum ne sede ba Ummi ba masu aiki da alama duk suna kitchen ne suna aiki, taso ta nufi kitchen d’in saidai kuma ba dad’i ka fad’a kan mutane suna ciki aiki. 

   Tsayuwan ta cigaba da yi tana jira 

Ko Afzal zey mata magana sede sam abun ba haka yake ta fannin sa ba. Chan da tsayuwan mutum ya ishesa a ka ya mik’e da niyan zarcewa site nasa. Yazo gab da wuceta ta danne zuciyarta tayi masa magana, “Ina Ummi please?”

  Bayan tsawon lokacin da ya d’auka yace, “In yau kika fara shigowa gidan let me know excuse me” ya sanar da ita cike da gadara ba tare da ya ko kalleta ba. 

  “Gashi inji Daddy a kawo maka” ta kuma danne zuciyarta da take yi mata k’ona. 

  “You can keep it on the table tell him nagode ya sha ruwa lafiya.” Dab ya kaiga fita kenan sega Ummi ta shigo from nowhere. 

  “Ahh ahh Nazeefah kece a gidan namu yau” abinda ta soma cewa kenan a yayinda take sa kai cikin parlourn. 

  “Ina yini Ummi?” ta durk’usa har k’asa ta gaisheta. 

  “Lafiya k’alau Mama na ya kike ya azumi?” Nan de suka gaisa. “Prince shine baka sanar cewa Nazeefah ta shigo ba?” ta juyo tana kallonsa. 

  “Barin je in watsa ruwa it’s getting to Maghrib” ya fad’a tamkar bey ji abinda Ummi ta fad’a ba. Kai kawai ta kad’a ta bisa da kallo yayinda ya fice. Pepper chicken da fruit salat ta d’iba wa Nazeefah kan ta kaiwa Mummy. 

  Bayan an sauk’o daga sallan Maghrib Afzal ya dawo site nasa da shirin cika cikinsa saboda ba k’arya azumin yau ya d’an garasa kasancewar ya kwana biyu beyi azumin Mondays and Thursdays da yake d’anyi ba. Har ya zauna kenan se ya lura da kulolin dake jera akan table d’in ba shakka sune wanda Nazeefah ta shigo dasu d’azu dan kuwa Ummi bata da kalan kulolin nan. 

   “Aikin Ummi” ya furta a fili. Yasan ba wanda zeyi masa kalan d’anyen aikin nan se ita. Sarai da gan-gan tayi hakan, rasa nayi yayi dan kuwa ko za’a had’a sama da k’asa baze ci girkin Nazeefah ba yasan wani concussion d’in tayi ciki? Fridge nasa ya nufa ya zaro wata silver flask daga gun freezer wanda Amal ta basa d’azu. Babban cup ya ciro daga cabinet ya juye kusan rabin zo6on aciki sannan ya shiga kwankwad’a be cire daga bakinsa ba sanda ya shanye nan ya sake cika rabin cup d’in ya kuma juyewa a cikinsa sannan ya d’an jisa da seti. Cookies ya d’aura a kai chan bayan Isha ya fita ya wuce restaurant inda yaci abinci, wanda Nazeefah ta kawo kuwa masu aiki ya kira yasa su suka zauna suka cinye tas sannan suka fita da kwanukan bayan warning daya kashe musu na cewa komin yaya kar Ummi tasan cewa bashi yaci abincin ba. 

   Washegari shi kad’ai ya yini a office kasancewar Sultan yana meeting. Amal kuwa ko mey ya hanata shigo masa yau se Allah if not yawancin kullum tana bin Falmata su taho tare, ko da Falmata ta koma makarantar kwana kuwa Amal bata fasa kawo masa ziyara bayan sati sati ba, se gashi yanzu kusan kullum seta shigo masa ta taya sa hira da wasu k’ananun aikin office wanda baza a rasa ba. Cikin d’an k’ank’anin lokaci suka saba suka soma sakewa da juna unlike Afzal, Amal nada saurin sakewa da sabo da mutum saboda iya zuba surutun ta. Wajajen hud’u Afzal na shirin barin office sega Amal ta shigo, ganinta kawai da yayi se yaji dad’i ya ziyarci zuciyansa atleast zata d’anyi masa lighting mood nasa. 

   Bayan sun gaisa ta zauna a kujeran data saba zama kullum, “Bade shirin tafiya kake ba Yaya?” Ta tambayesa. 

  “I thought you weren’t coming today” ya amsa a takaice. 

  “Mami ne ta aikeni wallahi taji nace zan maka kunun aya shine itama wai senayi musu da Papi ta sake aika na kasuwa” tayi maganan tana ajiye masa wata medium sized silver flask a kan table. “Ka sa a fridge idan ka isa gida don yayi sanyi bamu yini da wuta ba yau.”

  “Duka nawa?” Ya tambayeta. 

  “Nida nake cewa ma yayi kad’an kace bakason sugar so kad’an nasa.”

  “Thank you Amal, ga flask naki na jiya.”

  “You’re welcome yau ina Ya Sultan?”

  “Yana office nasa suna da meeting so ko leqo nan ma beyi ba.”

  “Ayyah, ka gaisheshi in kunyi waya.”

  “Sure” ya fad’a yana k’arisa tattara documents nasa. 

  “Nima bari in tafi toh tunda kana sauri yau.”

  “You want me to stay?” Ya tambayeta. 

  “Banson zuwa gida yanzu markad’e Mami zata tura ni” ta fad’a tana pouting bottom lip nata. Murmusawa yayi kad’an yana duban agogon hannunsa “Bakiya son aike ko?”

  “Wallahi a’a yaron meyin markad’en ne wai sona yake naje kullum ya ta cika min kunne da suratan banza.”

  “Iyye ashe Baby’n tamu akwai farin jini haka” ya fad’a cike da neman tsokana. 

   “Kai ya Afzal” ta fad’a tana kare fuskanta cike da kunya. 

   “Alright let’s spend some time together then.”

  “Yeyy! Amm-” da sauri ya katseta “Yau ba suratan shirmen nan nakeso ba I want to ask you some reasonable questions.”

  “Toh kuma-” ta fad’a tana turo bakinta a yayinda murnan daya ziyarci zuciyarta ya koma ciki. 

  “Ban ta6a jin kince zakije islamiyya ba Amal meyasa?”

  “Kwanan nan na fita.”

   “Meyasa?” Yayi saurin tambayarta. K’eyarta ta shiga sosawa. “Kinyi girma wa islamiyya koh?”

   “A’a ni bance ba.”

  “Toh meyasa kika fita?”

  “Yaya naga kaman na samu na sallah ne” ta fad’a a hankali chan ciki-ciki. 

  “Owww!” yaja numfashi yayinda idanunsa suke k’ok’rain kwararowa waje don mamaki “Dama haka abin yake? Da an samu na sallah se a yanke zuwa?” Ya tambayeta. Shiru tayi bata ce komai ba dan kuwa batada abin fad’i. “Izib naki nawa?”

   “Ashirin da bakwai (27)” ta amsa sa a takaice. 

   “Kuma hadda?”

   “Eh ba a tartil a islamiyyan se hadda zalla.”

   “Masha Allah” ya fad’a sounding impressive. Sam be d’au tanada hadda haka akanta ba. 

   “Toh ina laifin ki koma ki had’a duka Amal? Ko bakiya son kiyi haddan Qur’ani duka? Bakiya son ranan qiyama ayi crowning Mami da Papinki a idanun duniya gabad’aya?”

  “Inaso sosai ma” ta amsa. 

   “Toh ki koma islamiyya.”

  “Yaya…” 

  “I promise you idan har kikayi hadda kika sauk’e zan baki gaggarumin kyauta” ya sanar da ita tare da katse ta. 

   “Dagaske Yaya?” Ta tambaya cike da jin dad’i “Wani irin kyauta toh?”

   “Wanda bakiya tsammani.” 

   “Kaman wani iri kenan?” 

  “Kede ki had’a ki gani mana.”

  “Toh shikenan Yaya in shaa Allah zan koma.”

   “That’s my sis” yayi praising nata had’e da sakar mata murmushi wanda ta mayar masa itama cike da jin dad’i. 

   “Western education (karatun boko) fa?” Ya kuma tambayarta. “A ina kika tsaya? Ko akwai wanda kike zuwa?” 

    “Ko d’aya, tun da na gama secondary school ban sake komawa school ba.” 

  “Meyasa?”

  “Papi baida kud’in sponsoring d’ina” ta fad’a misfortunately, yadda tayi maganan seta basa tausayi shi a cewarsa gabad’ai itace bata son bokon ashe ba haka abin yake ba. “Karki damu, university ko college kikeso?”

  “University idan so samu.”

  “Masha Allah what’s your ambition?”

  “To become a nurse.” 

  “That’s a very good ambition Amal.”

   “Thank you” ta amsa shi ba walwala a fuskarta. 

   “Karki damu kinji? Zakiyi fulfilling dreams naki in shaa Allah cikin satin nan zan shigo muyi magana da Papi muddin ya amince nayi alk’awari zan d’au nauyin karatun ki.”

  “Kai Yaya! Dagaske kake?” Ta tambaya cike da mamaki a yayinda ta kasa 6oye farin cikin data tsinci kanta aciki.  

  “Inade fatan bakiyi tsohuwa wa part one ba” ya tambayeta cike da neman tsokana wanda hakan yasata murtuk’e fuska. “Yanzu Yaya kallon tsohuwa kake min kenan?” Ta tambayesa tamkar zatayi kuka “Ayya I’m just 18 years old fah, 2016 nayi graduating ai kaga its not too late ko?”

  “Yanzu dama duk rashin kunyan nan you’re just 18?” Ya tambaya da mamaki ai ya d’au tayi irin ashirin d’innan contrary to yadda bata jin tsoron idon mutum. Fuskanta ta shiga karewa da hijabin da take sanye dashi. 

  “Ai na tuba bazan sake yiwa Yaya rashin kunya ba.”

  “Kikayi ma zana zaki sha yanzu kinde san yanda Yayu ke discipline k’annensu a gida ai ko? Haka zan miki.”

  “A’a bazan ma yi ba bale ya kaiga zana, kasan wani abu?”

  “Tell me” ya buk’aceta. 

  “You’re such a blessing.”

  “Da nayi me fah?” Ya tambayeta had’e da tattaro hankalinsa akanta yana zuba mata ido. 

  “Da kace zakayi sponsoring karatu na, ba yadda ban yi ba don inga na shiga jami’a amman hakan ya gagara gashi mates d’ina yanzu suna part two yawancinsu.”

   “It doesn’t matter yaushe ka shiga university ko kuwa yaushe kayi graduating Amal, what matters the most is abinda kayi acheiving and albarkan dake cikinsa so ki cire ranki daga damuwa in shaa Allah your delay is for the good kinji?” Kai tayi saurin gyad’awa tana murmushi na sosai “Thank you Yaya.”

   “You’re welcome Lily.”

   “Laa nice Lily?” Ta tambaya tana blushing. 

  “Eh mana you’re my kid sis na chan baya-baya ma kuwa that makes you my lily ko bakiya son sunan?” Ya tambayeta cike da wasa. 

   “Ni wa ince banaso?” Murmushi kad’ai ya sake mata. “Kace ni kid sis taka ce ta chan baya-baya?”

   “Yup baki yarda ba?” Gira ta d’age masa “You’re not looking that old you know.”

  “See this girl o! Na fa girme ki sosai na sosai.”

   “Kai Yaya kaman da shekaru nawa?”

  “Ni zaki ma wayo? You want me to tell you shekaru nawa na baki so that kiyi adding a kan naki ki gano asalin shekaru na ko?”

  “Kai Yaya bade wayo ba wallahi amman yi hak’uri ka fad’a min mana ni baka ga na sanar dakai nawa ba?”

  “Nak’i” yace zalla. 

  “Yi hak’uri.”

  “Kiyi guessing.”

  “Toh let me see…” nan ta tsaya nazari a yayinda ya zura mata ido. 

  “23??” Ta tambaya da gan-gan sanin yafi hakan. 

  “23?” Ya nanata cike da mamaki. “Seriously?”

   “Toh 24?”

  “C’mon I look older than that God this is a slap on my face I’ll be turning 27 by December” ya sanar da ita ba tare da yasani ba. Oops!

   “Yeyyy na ji shekarun Yaya” ta fad’a tare da k’yalk’yalewa da dariya. Jinguna bayansa yayi ya kalmashe hannayensa across his chest yayinda ya k’ure mata ido se faman rawa take kan kujerarta tana masa gwalo. Don kanta tayi shiru “Kin gama?” Ya tambeyeta. 

   “I’m sorry” ta fad’a wani dariyan na neman kauce mata. “But seriously Yaya you look way younger than your age, sam mutum bazeyi tunanin har ka kusa cika 27 ba, wallahi na d’au duk tsanani 25 kake, wai tsaya muga shekaru nawa Yaya ya bani? 27-18. Borrow one from- Wow! shekara tara fah!” Tayi calculating nan take, “Uhm uhm uhm amman gaskiya wawiya nake inyi maka rashin kunya, kayi hak’uri kaji?”

   “Ya wuce Lily don’t worry.”

  “Yaya bakada k’anne ne wai kam? Ban ta6a jin kayi maganansu ba.”

  “Babu sai ke kad’ai.”

  “Iyye Yaya d’an autan daddy nikuma Lilly’n Yaya happy me.” Murmushi kawai yake yana kallonta itade surutu da shirmeh bayi bata wuya “Yaya idan nayi maka wata tambaya ba zaka ji haushina ba?”

  “Go ahead.”

  “Uhm uhmm” tayi gyaran murya “Karfa kace nid’in nan magulmaciya ce.”

  “LOL I won’t” ya amsa yana dariya. 

  “Toh some days back naji kai da Ya Sultan kuna hirar wata Nazeefah senaji kaman har yana ce maka ango, aure zakayi?” Shiru yayi na d’an lokaci “I’m sorry ba seka amsa ba idan kaga ba zaka iya ba, forget it please.”

  “Eh aure zanyi.”

  “Wow! Masha Allah, yanzu Yaya inada Aunty shine baka ta6a sanar dani ba bale ka had’amu a waya da ita kuma kake kirana Lilir ka?”

   “I’m sorry” kad’ai yace da ita don yadda bayison hirar da ta shafi Nazeefah. 

  “Amman ya akayi koda wasa ban ta6a jin kuna waya ba Yaya?”

   “Because she’s not your Aunty with time zan nemo miki Aunt da take da hankali wacce zata sake d’aura ki akan hanya madaideciya ba wacce zata gur6antar min da tarbiyyar ki ba.”

  “Wow! Nikam ka sani a cikin duhu Yaya kode baka sonta ne?”

  Seda ya nisanta sannan yace, “Yes bana son ta” cikin sauk’i. Baki Amal ta bud’e cike da neman k’arin bayani tana kallonsa. “Abbanta ne yakeson in aureta bawai don inaso ba” ya sanar da ita. 

“Allah sarki itace wacce naji kwanakin baya kana bawa Ya Sultan labarinta a mota kenan” tayi reasoning. 

  “Yupp” ya amsa popping the P. 

  “Ka kwantar da hankalinka Yaya in shaa Allah you’re doing the right thing, Allah na tare da kai with time zaka koyi sonta.”

    “Hmm!” yaja nishi “Only if it is that easy.”

   “Why not?”

 “Bazaki gane ba Lily it’s a long story but I promise duk rananda nake cike da labari I’ll give you the whole story yau yunwa nakeji don’t tell me bakiya jin azumin nan?” Da wayo ya samu ya canza topic of discussion d’in. 

    “Laa karde Yaya baya iya juran yunwa?” Ta tambaya da wasa. 

  “Eh mana” ya amsa yana duban lokaci “Wow kinga har quarter to six (shida saura minti sha biyar) tashi in kaiki gida muyi shirin bud’a baki.” Ba musu ta taimaka suka tattara masa documents nasa sannan suka sauk’a k’asa ta lifter. 

    Chan gidan madara yabi da ita inda suka tsaya a Today’s ya sai mata chocolates sannan ya kaita gida sukayi sallama bayan asha ruwa lafiyan da tayi wishing nasa. 

   PAGE 0⃣8⃣

   Haka kwanaki suka ta shud’ewa a yayyinda Afzal da Amal suke sake shak’uwa wane asalin ‘yan uwan jini. Traditional smoothies d’innan ba wanda Amal bata yi mishi, yau ayi Aldeb, gobe Ginger, next day Zo6o. Shima sau dayawa yakan kaita gidan madara ko Sidis su sai mata chocolates, ice creams da makamancin hakan. 

  Ta fannin Nazeefah kuwa Daddy be fasa da abinda ya d’aura ta akai ba, kafin azumi ya fita seda ta kaiwa Afzal abinci kusan sau hud’u ko biyar don haka itama Ummi tayi tunanin ya kamata Afzal yayi wa Nazeefah kayan sallah shima as a token of appreciation saidai ta fanninsa bayida niyyan hakan ko kad’an, Amal tasa kad’ai zai saiwa kayan Sallah ba wata fand’ararriyar Nazeefah ba. Yana cikin shirin zuwa gidansu Amal don kai mata kayakin da yayi niyya ne sega kwatsam Ummi ta fad’a cikin d’akin ko sallama yau babu. 

  “Haba Ummi!” Yayi saurin fad’i “Taya zaki na shigo min d’aki ba sallama idan da kuma ban sanye da kaya fah?”

  “Seka godewa Allah uwarka ce ta shigo ba su Juliet ko Esther ba, speaking of ina shigo maka d’aki ba sallama wani abun kake 6oyewa?” Ta k’arisa tare da tsayawa ta gefen gadonsa. 

  “Me kuma zan 6oye?” Ya amsa yana bin jikinsa da body spray. 

  “Meye acikin leather’n chan?” Sauri yayi ze ja sede dake tafisa kusa da gadon ta rigasa d’agawa tare da zazzagewa akan gadon. Zani ta tarar wanda take da tabbacin super wax ne exclusive ma kuwa, da wata voil lace. 

  “Iyyeehh!” taja numfashi tana binsa da kallo cike da k’in yarda wanda Afzal ya manna mata hasali yima yayi wane be san dashi takeyi ba. 

  “Prince wannan kuma se ina?”

  “Wai kam Ummi ina ruwanki? Haa’a! Ni ki miyar min su cikin leather’n.”

  “Lallai Prince ka girma tunda ka soma 6oye min al’amuranka wato kayi wata sabuwa awaje shine ko a sanar dani ita ko? Da kyau.”

  “Kaman ya sabuwa a waje kuma?” Ya tambaya nan take. 

  “Ai sarai kasan mey nake nufi wannan d’in ina zaka kai?”

  “Gidansu k’anwata” ya bata takaicaccen amsa. 

  “K’anwa?” Ta nanata da mamaki “Kanwa fa kace Prince? Yaushe na haihu ban sani ba?”

  “God help me” ya furta can k’asa-k’asa. “Wai kam se wanda kuka fito ciki d’aya dashi ne ze zamo k’aninka?” Ya tambayeta. 

  “Ni ba abinda nake nufi ba kenan” ta amsa had’e da kare kanta. “Amm-” katseta yayi a hankali “Kinga na farko Amal ba budurwata bace, ina yarinyan nan da na ta6a bigewa days back?”

   “Wacce tayi targad’en nan?”

  “Eh ita she’s the one am referring to my sister” ya fayyace mata. 

   “Ahhh ahhh!” Ta fad’a cike da neman tsokana “Kace tun daga nan ta sace maka zuciya!”

  “Ya Subhanallahi!” Yayi exclaiming a rud’e “When did I ever say that?”

    “Yo gashi alamu sun nuna da de 6oye-6oyen nan ka dena ka rok’eni in tayaka da addu’a.” 

   “Ummi please! Ni ba abinda yake tsakani na da Amal banda dangartakan ya da k’anwa so please kar maganan nan ya isa kunnen Abba.”

  “Hmm Allah sa gaskiya de kake fad’i.”

  “Ya ma riga ya sa don am telling you nothing but the truth” ya amsa ta yana mey manne bakin cuff links na rigansa. 

  “Nide nace Allah ya sa don kuwa gashi har an sai mata kayan sallah ni uwar taka gabad’aya ko d’an kunne ba a sai mi ba.”

  “Oh Ummin tawa akwai kishi, a tunanin ki har zan sai ma wata zani ban saya miki bane?” Wardrobe nasa ya bud’e ya ciro wata leather tare da miqa mata “Gashi open up” Da murmushi kwance fal a fuskanta cike da hanzari ta amsa tare da since bakin, super biyu ta tarar ciki wanda sukafi na Amal ma kyau seda wata had’ad’d’iyar purple lace me torches na white and black. 

   “Awwn Prince duka nawa?”

  “Eh mana you deserve even more.”

  “Gasu duk da torches na purple a jiki my favorite color.”

   “Ummi ai duk wanda yace besan purple ne best color naki ba toh besanki bane.”

   “Thank you so very much Prince Allah yayi maka albarka ya k’ara bud’i ya kuma sa albarka acikin al’amuranka sakallahu bil jannah.”

  “Ameen your prayers keep me moving.”

   “Suna tare da kai a kullum Babana.”

  “I’m grateful bari inyi sauri yamma nayi.”

  “Uhmm Prince nace Nazeefah fah?” Ta tambaya cike da gudun 6ata masa rai. 

  “Ohhhh!” Yayi exclaiming tare da buga k’afansa a k’asa “Ummi please kibar zancen yarinyan chan she’s not yet my responsibility kibari bayan na aureta ban yi mata kayan sallah ba seki min fad’a ki tilasta ni but not now please.”

  “Ayyah Prince ai ko yanzun ma ba tilasta ka nake ba, har na kai insa Prince d’ina aikata abinda beyi niyyah bane? Naga kaman abune da ya kamata kuma ma ai yima kai ne, kana sane de da yadda take kawo maka abinci ba fashi ya kamata kai ma kayi mata wani abun in return kodan iyayenta ma” ta mai bayani a hankali yadda ransa baze 6aci ba.

   “Toh Ummi ni na aiketa? Ko ni nace lalle-lalle se ta kawo min abinci? Abincin da ba ci ma nake ba” ya fad’a ba tare da yasan yaushe ba. 

  “Ba ci kake ba?? Innalillahi Prince!”

  “Ni ba abinda nake nufi ba kenan I mean” nan ya shiga kame-kame. “I mean ni inba girkin kiba ban k’oshiwa ko naci natan sena k’ara da naki a kai.”

   “Da Allah chan! Ni zaka ma zak’in baki? Wato zubar da abincin kakeyi kullum ko?”

  “Itama lace da atamfan kikeso a sai mata kokuwa?” Ya tambayeta deliberately da niyyan canza topic of discussion d’in.

   “Kasan mey za’ayi ne? Tunda zaka fita yanzu kuma gashi yamma tayi why not ka kai mata nawan yaso seka sake siyo min wani ko zuwa gobe? Bana son a samu akasi.”

  “Like seriously?” Ya tambayeta cike da mamaki “Abinda na sai wa mahaifiyata kike son in kai wa wata?”

  “Ai ni nace kayi karka damu all shall be well.”

  “A’a nikam tunda ba firewa zatayi ba gobe idan na fita sena saya mata in tura akai mata.”

  “Prince wai yaushe muka fara jayayya da kai ne? Nifa ban san ka da halin nan ba.”

  “I’m sorry” yayi saurin bata hak’uri. 

    “Ai Prince baya laifi nide alfarma nikeso kayi hak’uri ka kai wa yarinyan kayakin nan.”

  “Duka ukun Ummi? Wallahi lace d’innan ba lalle ne asamu exact irinsa ba kuma ko da za’a samun ma ba exact color d’inba saboda wannan d’inma a online na gani na baiwa me kayan kud’i ya siyo min da ze tafi Dubai.”

  “Ai ko daga ido ma ansan ba k’aramar lace bace wannan kuma nima banda niyyan baida wannan d’in dama atamfofin nike nufi.”

  “Alright keep them aside bari in kira Juliet tazo ta kai mata.”

  “Haba Juliet kuma Prince kai baka ga kullum ita da kanta take kawo maka kayan bud’a bakin ba?”

   “Ohhh! Ummi please.”

  “Yi hak’uri d’an albarka d’an autan Abbansa kuma d’an gaban goshin Umminsa yi hak’uri” shiru yayi bece komi ba “Yau zan yi maka pepper soup na kifin nan da kakeso fah ko kar ayi?”

  “Ni bance ba” yayi saurin amsata “Naji zan kai mata.”

  “Yauwa my charming Prince nagode ko? And please karka manta kace zaka tambaya min yarinyan nan da ta had’a maka aldeb na jiya.”

  “Don’t worry I’ll ask her of it gidansu ma zani ai yanzu.” 

  “Laaa! karde itace Amal d’in?”

  “Toh da waye? She’s the only sister I have.”

  “Iyyeh!” Nan ta shiga yi mai wani irin kallo cike da neman tsokana da magana, shide be ce mata ko k’ala ba hasali bema damu da abinda take tunani akanta tsakaninsa da Amal ba saboda yasan a matsayin k’anwarsa ya d’auketa kamar yadda itama ta d’aukesa a matsayin yayanta. Dressing mirror ya nufa inda ya daidaita hulansa tsab sannan ya shiga feshe varieties na designer turarukan dake jere gaban mirron. 

****

  Daga gefen gate na gidan Alhj Abdallah Afzal yayi parking motarsa inda yasa masu gadi suyi ma Nazeefah sallama, yana zaune cikin motarsa yana going through twitter feeds nasa yaji murya kaman na Daddy na kiransa. D’aga kan da zeyi suka yi ido hud’u. Fitowa yayi daga motar nasa take ya k’arisa inda na Daddy yake, nan Daddy ya bud’e k’ofa suka gaisa. Bayan gaisuwa yake tambayar Afzal dalilin dayasa be shiga ciki ba ya tsaya nan waje sekace wani bak’o. 

   “Wallahi sauri nake ne shiyasa I’m sorry.”

  “Allah sarki ba komai, gun Nazeefah kazo ne?”

  “Eh Daddy saqo nakeson in bata.” Wani dad’i ne ya ziyarci zuciyan Daddy a tunaninsa gabad’aya abubuwa sun soma daidaita ne tsakanin Nazeefah da Afzal not knowing the actual situation. 

  “Kuma shine take 6ata ma lokaci bayan gashi kace da akwai inda zaka zarce?”

  “Eh Daddy amman ba damuwa nima ban dad’e da zuwan ba.”

  “Barin tura d’ayan me gadin ya kirat- yauwa gata nan ma.” Ya sanar da Afzal sanda Nazeefah ke fitowa daga gate d’in tana sanye da bak’in hijab three quarter. “Ke haka akeyi ne Nazeefah seki ajiye bak’onki shiru haka?”

  “Daddy ina taya Mummy aiki ne a kitchen” tayi explaining cike da ladabi kaman ba ita ba. “Sannu da dawowa.”

  “Yauwa sannu ki k’ariso Afzal yana son miki magana” ba musu ta nufi wajen motan Afzal daga baya-baya ta tsaya, ba don tanaso ba sedon idon Daddy data gani a kanta ta gaishe da Afzal harda d’an durk’usawa shima ganin idon Daddy yasanya sa amsa gaisuwan cike da walwala da murmushi seda yaga shigewan Daddy ciki sannan ya azo asalin fuskarsa. Motan nasa ya koma ciki ya fito da ledar “Gashi ki d’au d’aya ki bawa Mummy d’aya” ya sanar da ita ba tare da ya nuna damuwa ba. Mamaki ne ya mamaye zuciyan Nazeefah har ma ta mance yadda ake amsan abu gun mutum. Shiko ganin tana 6ata mar lokaci ya ajiye ledar kan bonnet na motan. 

   Wai Afzal ne ze siya mata kayan sallah? Ta tsaya tana tambayar kanta. Hannu ta mik’a ta janye ledan izuwa 6angarenta tana mey shawaran yi masa godiya kokuwa. 

  “Dont think twice about it” fad’in Afzal yana mey tsamota daga cikin duniyan tunanin data fad’a. “Ummi ne tace lalle-lalle sena kawo miki wani abun kodan bautan kawo min abincin da ban rok’a ba da kikeyi gudun kar ki tashi a tutan babu if not banida ra’ayin hakan sam.”

  Hamdala ta saki na k’in masa godiyan da tayi, dan kuwa da tayi da taji kunya. Numfashi taja tace, “Kaman ka sani there is absolutely nothing in this world daze sani sanya wani abinda ka siyo da hannunka kokuwa kud’inka” ta fad’a cike da gadara da rashin kunya. 

  Murmusawa yayi ta gefe sannan lokaci guda ya tamk’e fuskan nan “Then that makes us even saboda ko wuta da aljannah aka bani bazan iya cin abinda kika girka ba, hannun da sama da maza goma sun rik’e sunyi gadamansu dashi. So idan ma shirin kawo wani tarkacen kike yau I’d better make your work easier for you tun a bakin gate ki tsaya ki rabawa securities because it’ll be more of a westage idan suka shigo site d’ina cause tsab a toilet zan juye kamar yadda na saba inyi flushing.” Duk yadda Nazeefah taso 6oye mamakinta ta kasa, lallai ya cika d’an halas. 

  “You can close back your mouth gudun kar flies su shiga my warmest regards to Khaleefah and Mummy” yana kaiwa nan ya bud’e motansa ya ja yabar gun da d’ankaren gudu har yana neman kad’a mata k’ura. 

  Gidansu Amal ya wuce inda ya tarar da ita da Papi dake shirin fita shima. Taburma Amal ta shimfid’a masa inda duk suka zauna suka gaisa, bayan gaisuwa Afzal ya mik’a wa Papi ledan dake hannunsa. Cike da jin dad’i Papi ya bud’e ledar se ganin kayaki yayi ba adadi, “Wai wai wai Baba na da wahala haka?” Ya tambayi Afzal cike da k’in yarda a yayinda yake fito da kayakin d’aya bayan d’aya. Ashe gogan naku zannuwa biyu ya sai wa Amal sannan da lace nata har ma da takalmi da jaka, d’ankunne dasu sark’a bugu da k’ari harma da d’inkekken hijabin da ze shiga da zannuwan nata. Se kuma atamfa super exclusive wa Mami da babban gezna wa Papi amman ya 6oye wa Ummi saboda yasani da tagani zata hau fassara masa niyya while actually shi bada wata manufar yayi ba illa don k’anwarsa ce. 

  “Kai Afzal mun gode mun gode k’warai wallahi bansan ta ina zamu fara ma godiya ba” Fad’in Papi da se d’aga zannuwan yake yana bi da kallo. Amal kam don yadda mamaki ya mamayeta tama kasa magana banda zuba ma kayakin ido da tayi tana mey mamakin anya kuwa ita zata sa kayakin nan? “Baby bakiga kayaki bane da baza ki bud’e baki ba kiyi godiya?” Papi ya tambayeta. 

   Kai ta kad’a tana mey dawo da kanta asalin rayuwa daga duniyar tunanin data fad’a. 

 “Yaya?! Duka wannan namu?” ta tambaya tana mey nuna kayakin. 

  “Ji Amal” ya fad’a had’e da murtuk’e gira “Kin ta6a jin inda babban yaya yasai wa kansa kayan sallah be yi wa k’anwarsa ba?”

  Cike da kunya ta kad’a kanta “Yaya mun gode sosai Allah k’ara bud’i ya kuma miyar maka da gidan aljannah.”

  “Ameen” Papi ya amsa a fili a yayinda Afzal ya amsa a zuciya. 

   “Gaskiya Afzal ba muda bakin yima godiya sai dai muce Allah ya biya ya k’ara bud’i godiya ba adadi Allah ya sak’a ya shige maka gaba aduk abinda kake ciki kake kuma nema.”

  “Ameen Papi please godiyan ya isa haka ana tare ai.”

  “Toh masha Allah, Baby mai da kayakin ciki kinji kar k’ura ya 6ata” ya sanar da ita a yayinda yake k’ok’arin mik’ewa “Zan fita zani kasuwa sena dawo” ya sanar da Afzal. 

  “Papi idan ba sauri kake ba daman inaso muyi wata magana da kai ne” Afzal yayi saurin tanka shi. 

  “A’a ko kad’an Babana bismillah” nan ya koma ya zauna. 

  “Thank you, dama batun Amal ne munyi magana da ita kuma tace tana son ta koma makarantar boko idan har kaga hakan ba matsala I am willing to provide for her education se tayi sitting jamb muyi mata applying jami’a nan Unimaid.”

  “Jami’ah! Allah sarki babana nauyin baze zo yayi maka yawa ba kuwa? Dan Allah karka damu nima ina kan tara mata kud’i ne ko nan Ramat ta shiga don Allah karka tada hankalinka.”

  “Papi ni izinin ka kawai nake nema karka damu da komai.”

 “Baby zaki deyi karatu baza kisa Yayan ki asaran kud’in makaranta bako?” Ya juyo yana kallon Amal data had’e gira. Lalle ma Papi sekace besan k’ok’arinta ba yake fad’a mata haka gaban Afzal, ai se Afzal ya d’au ita d’in doluwa ce. 

   Daga bisani tace, “Papi da gan-gan ka fad’i hakan donka kunyatani idon Yaya ko? Allah se in d’auko report sheets d’ina tun daga JSS1 in nuna mishi kaima kasan bana wasa da karatu.”

  “Ah ah mamana na kaina yi hak’uri maida wuk’an wasa nike.” Murmushi Afzal ya saki yana mey sha’awan relationship dake tsakanin Amal da Papinta. 

  “Toh Afzal nide ba abinda zance sede muyi ma addu’a Allah ya biyaka. Rashin shiganta babbar makaranta ba k’aramin damuna yake ba a matsayina na mey kula da ita barin ma yadda take da son karatu, tun tana damuna da cewa tanason ta shiga jami’a har tagaji ta dena saboda rashin samu, ba yabon kai ba amman uwata akwai ja inada tabbacin cewa bazata baka kunya ba, kuma nima zan sa ido sosai akanta inga ta cika maka burin ka nason ganin tayi karatun nan, Allah sak’a maka da alheri.”

  “Ameen Papi nine da godiya daka amince da wannan k’udiri nawa zan d’anyi tambayoyi kad’an in shaa Allahu duk abinda akwai zan sanar dakai.”

  “Toh toh Babana mungode mungode sosai Allah kad’ai ze biyaka shikenan ko akwai wata maganar kuma?”

  “A’a Papi kana iya tafiya nagode da ka bani lokacin ka.”

  “Toh madallah madallah” ya fad’a yana mik’ewa. 

  “Toh a dawo lafiya” cewan Afzal. 

  “Allah tsare Papi” inji Amal. 

  “Ameen Afzal ameen uwata, mungode sosai sosai ka gaishe da gida idan ka koma.”

  “In shaa Allah” Da haka ya fice ya rage Amal da Afzal kad’ai kasancewar Mami ta shiga mak’ota. 

  “Yaya wanne ne nawa?” Ta tambayesa cike da jin dad’i tana mey zazzago da kayakin. Murmusawa yayi ganin yadda ta kasa 6oye farin cikinta. Atamfan Mami yaja gefe da kuma shaddan Papi sannan yace, “Duka wannan naki ne.”

  “Dagaske Yaya? Da wannan da wannan da wannan duka?” Ta tambaya cike da k’in yarda tana mey bin kayakin da yatsarta tana nunawa. 

  “Sosai ma.”

  “Yaya you’re truly an angel thank you so much.”

  “You’re welcome Lily” ya amsa yana mey miyar mata da murmushin da take masa. 

  “Toh ni da irin abubuwan nan da kake min dasu Papi me muke dashi da zamu iya baka in return?”

  “Addu’o’in ku kad’ai ya isheni Lily.”

  “Are you sure Yaya?”

  “Absolutely sure Lily.”

  “Toh shikenan Yaya ga addu’o’ina na yau da kullum a gareka; Allah sak’a maka da alheri, ya k’ara maka bud’i yasa ka cimma duk wani burinka a doron k’asa, Allah ya baka mace ta gari da ‘ya’ya nagari ba masu rashin kunya da taurin kai kaman ni ba fa” Dariya sosai Afzal ya tsaya yi a yayinda ta cigaba “Allah sa ka gama da duniya lafiya, ya baka gidan aljannah kuma, kai Allah ya baka duk wani abinda kakeso tun a zuci ba seka furta shi waje ba.” Shiru ta yi don jin yadda Afzal keta dariya tun zamansu dashi bata ta6a ganinsa yana dariya haka ba, ashe de haka dariya yake kar6ansa shine baya yi? Cankwad’i! aikuwa ta rik’a sashi dariya kenan kullum yanayi. 

  “Ka gama dariyar baka amsa da ameen ba.”

  “LOL ameen Lily kema Allah ya miyar miki da duka addu’o’in da kikayi min.”

  “Hmm ameen da babban murya kaga barin surfa waken nan kafin Mami ta shigo ta balbale ni tun d’azun tace inyi na tsaya ina shirme.”

  “Kafin nan Ummi tace tanason ki koya mata yadda akeyin aldeb d’innan Lily na rage mata na jiya bakiga yadda tayita santinsa ba.”

  “Kai Yaya dagaske?” Gira ya d’age mata “Wai yayi dad’i tace?” Ta tambaya zealously. 

  “Sosai ma.”

  “Ai dama nasan na iya girki Mami ce kullum ke kusheni.”

  “LOL that is because tanaso ki k’ara himma ne don’t blame her it’s what mothers do.”

  “Hmm toh kasan me za’ayi? Barinje in kira Mami nan mak’ota tayi hak’uri tayi sirfen waken sena had’a wa Ummi da kai aldeb d’in ai idan nayi a gabanka zaka gane procedures d’in idan ka koma gida se kayi mata bayani ba?” Shiru Afzal yayi yana nazari shi banda dafa indomie, tafasa ruwa, farar shinkafa ko spaghetti da macroni anya akwai wani abinda ya iya?

  “Kode Yayana be iya girki bane sam?” Ta tambayesa cike da neman tsokana. 

  “Waya fad’a miki?” Ya wani 6ata rai yana cin fuska. 

  “Toh naji kayi shiru.”

  “Of course, how do you expect me inje in fara yima Ummi bayanin yadda ake had’a aldeb mace ne ni? Kede yanzu ki bani number’n Mami in naje gida sena had’aku kiyi mata bayanin ta waya.”

   “Haha nide na gane Yaya ajebo ne be iya komi a harkan kitchen ba.”

  “Na yarda fad’i koma mey ba shi zey sa in amince da k’udirinki ba.” 

  “Toh shikenan Yayana na kaina ai ni duk abinda ka fad’a ya zauna se ayi hakan.” Bece da ita komi ba yayin da ta shiga ciro ingredients da zata buk’ata tsakar gidan, tana cikin taran ruwa daga famfo sega Mami ta shigo. Sosai tayi murnan ganin Afzal, bayan sun gaisa Amal ta fito mata da kayakin da Afzal ya kawo musu ta nuna mata, da godiya na kisa kam daya kashe Afzal a wajen saboda kalan godiyan da Mami tayita masa. 

   Bayan ta mai da kayakin ciki ta fito ta tarar da Amal na aiki daban maimakon sarrafa musu waken da zatayi. Ta soma k’orafi kenan Afzal ya shiga bata hak’uri had’e dayi mata bayanin lamarin cewa Ummi ce keson aldeb d’in. Ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga surfen da kanta yayinda Amal ta cigaba da had’a aldeb d’in. Ido Afzal ya k’ura mata yana mey sa hankalinsa sosai game da duk wani abinda takeyi ko da ze iya fahimta yayi ma Ummi bayani ko dan kar Amal tayi underestimating nasa. 

   Abu d’aya daya karanchi tattare da Amal shine kominta tsaf-tsaf take yinsa ba dotti bale k’azanta hakan ba k’aramin burgesa yayi ba, a rayuwa ya washi mutum me shegen daud’a da k’azanta kasancewar acikin tsafta ya girma, mutane har suna cewa tsaftan Ummi yayi yawa, shara idan batayi atleast sau biyu ko uku a rana ba bata jin dad’i. 

   A haka har Amal ta samu ta gama ta d’ura masa cikin manya-manyan silver flasks guda biyu d’aya nasa wai d’aya na Ummi. 

   Kud’i ya k’irga yasa a hannun Mami cewa suyi d’inkin kayakin nasu dashi. Wayyo Mami ta ma rasa ina zata sa kanta, albarka tayita sa masa sannan suka rakasa har inda yayi parking motarsa, bayan ta mishi asha ruwa lafiya ta koma ciki ta barsa shi kad’ai da Amal. 

 “Here press Mami’s number bayan ansha ruwa zan had’aku da Ummi se kiyi mata bayani” ya fad’a yana mey mik’a wa Amal wayansa da ta amsa da ‘Toh.’ Hannu na 6ari ta mik’a ta amsa tana mey fatan Allah ya kawo mata ranar da zatayi wayar kanta me k’aton screen kaman wannan ko shegiyar Bintun ajinsu na islamiyya zata shiga hankalinta ta daina yi musu yanga da wata k’aramar infinix nata da bai iya zama cikin jaka ba sede akan table don a nunawa ‘yan aji ana da waya. Bayan ta zuba ta miyar masa da wayan inda yayi saving. 

  “Toh Lily ba-bye.”

  “Mungode Yaya asha ruwa lafiya.”

  Murmushi kad’ai ya saki mata yayinda ya bud’e murfin motan ya shiga, se da taga ficewansa sannan tabi lungun gidansu ta koma. 

****

BAYAN SHAN RUWA, GIDAN ALHJ AHMAD AMIN. 

   “Ni fa ban yarda ba kuma bazan yarda ba in zaka kira min yarinya kawai ka kira tayi min bayani da kanta dududu banda tafasa ruwa mey ka iya da zaka wani cemin ka iya had’a aldeb me dad’i irin na Amal in yarda” Fad’in Ummi dake zaune a gefen Afzal akan kujera a parlourn site nasa. 

  “Am serious Ummi a ido na ta had’a and I did observed her closely.”

  “Oho nide kiramun ita se naji daga bakinta zan amince, ba ka amshi lambarta kona mahaifiyarta ba? Call her up for me.”

  “Fine!” Ya fad’a aggressively tare da dannawa lamban Mami kira saida ya kusan tsinkewa aka d’aga. “Assalamu alaikum” yaji siririyar muryar data d’aga ta fad’a. For a moment ya shiga duhu yade san muryan Mami ba haka yake ba, na Amal shigen hakan ne seda kuma wannan d’in har yana son fin natan zak’i. 

  “Yaya?” Ta kirasa wanda hakan ya tabbatar masa da kokonton da yake.

  “Na’am Lily” ya amsa yayinda Ummi ta zura masa. 

  “Ina yini? An sha ruwa lafiya?”

  “Lafiya Alhamdulillah ya gida?”

  “Lafiya k’alau ya Ummi?”

  “She’s okay ita ma ke son miki magana kafin nan Lily aldeb d’innan bada tsamiya, sugar, ruwa…” nan ya shiga irgo duka ingredients d’in sannan kuma da procedures d’in, sosai Amal ta sha mamakin yadda ya rik’e komi dai-dai dukda fad’in sau d’aya aka ta6a had’awa a gabansa. 

    “Wow! Impressive kai Yaya na akwai k’ok’ari ai kuwa ka bada procedures din dai-dai sede tsamiyan da ruwan zafi ake jik’a sa kuma sugar’n ma ba raw one ake sawa direct a ciki ba se an narkar dashi.”

  “Ai na fad’a seda na fad’a maka narkar da sugar’n nan ake kak’i yarda Pff” nan Ummi ta shiga yi masa gwalo. 

  “Whatever ai nayi k’ok’ari for goodness sake yau fa na fara ganin yadda akeyi.”

  “Eh sugar’n ma ana iya sa shi direct amman narkekken yafi fita ne” Amal dataji Ummi sama-sama ta waya ta amsa. Gwalo ya shiga yima Ummi shima “Pff to you! Kin deji da kunnen ki a hakan ma ana iya sawa.”

  “Kai Yaya bade gwalo kake yima Ummin namu ba?” Ta tambayesa “D’an bata mu gaisa.”

  “Barshi Amal ‘yata gwalo yake min” Ummi ta amsa tana matsowa kusa da wayan. 

  “Toh bata mu gaisa.”

  “Nak’i, ke bakiji sanda take min gwalon ba itama?”

  “Yi hak’uri toh ka bata” ba gardama ya mik’awa Ummi wayan inda suka gaisa take ta yaba aldeb na Amal wanda har ahakan yasata kunya sosai.

  “Ai da na bi procedures na Prince da nayi kwa6a” For a moment kan Amal ya d’aure karde sunan da ake kiran Yaya dashi kenan a gida Prince? Ta tambayi kanta, lallai kuwa d’an gata ne. “Kai Ummi ai yayi k’ok’ari” ta amsa cike da wasa. 

  “Bani waya na Ummi bani!” Ya fad’a trying to sound serious. Da sauri ta tare hannunsa “Kinsan kuwa banda tafasa ruwan zafi ba abinda ya iya? Taya mutumin da ko jollof be iya dafawa ba ze ce min ya iya had’a aldeb kuma in yarda, ‘yata is it possible?” Dariya sosai Amal tasa har tana sark’ewa Afzal da ya kai har maqora se harara yake dannawa Ummi yayinda take tayi masa gwalo. Taya zata fad’awa Amal bai iya girki ba? So take ta raina sa? 

  “Ai fa ba laifinki bane nine nan na had’aku ai” yace da ita yana girgiza kai. 

  “Kinji Yayanki yamun fushi ko ki basa hak’uri” Ummi tace da Amal dake ta faman yi musu dariya tun d’azu. 

  “Laaa yayi mana hak’uri don Allah ai bamu iyawa da fushin Yaya, Yaya?”

  “Gashi amshi k’anwarka na son yi maka magana.”

   “Nak’i” ya amsa ba walwala “Ni d’agani in mik’e idan kun gama wayan naku ki kawo min wayana ciki ko ki kirani inzo in kar6a.” Kafin ya kaiga mik’ewa Ummi ta danneshi “Haba Prince yi hak’uri mana.”

  “Toh Ummi seda safe, ki sake yiwa Yaya godiya sosai dan Allah munga kaya mun gode Mami tac-” wabce wayan yayi daga gun Ummi da sauri kafin Amal ta k’arisa zancenta had’e da katsewa yana mamakin dogon baki irin na Amal se kace bata san halin Ummi ba. 

  “Ya haka Prince?” 

 “Babu d’agani nikam.”

 “Tsaya ma tukun wato ba wa ita kad’ai ka sai wa kayan sallan ba harda iyayenta ko?” Shiru yayi tamkar be jita ba, “Hmm su Prince an fad’a kogin soyayya.”

   “God help me! Ni wallahi saboda irin suratan nan naki nak’i nuna miki kayakin duka baga irinta ba” ya fad’a a tak’ure. 

  “Aww ashe da gaske ne ka sai wa iyayenta kayan.”

  “Eh na sai musu shikenan kin huta?”

  “Prince jokes aside kode son yarinyan nan kake ne amman ka kasa ganewa har yanzu?”

  “Haba Ummi! Taya zan so Amal please? Ai banyi adalci ba kenan.”

   “Kamar ya bakayi adalci ba?”

  “For goodness sake a matsayin yayanta ta d’auke ni, ta na gani na da k’ima da daraja tana girmama ni kawai don ni na kawo rashin halacci da kunya duniya se in hau sonta? It’s not possible.”

  “Kana nufin in ba don wannan dalilin ba zaka iya sonta kenan?”

  “God help me!” Ya furta unbelievably “No that is not my point you know what? Let’s just drop this topic” ya fad’a ransa na soma 6aci. 

  “Hmm tayi tsami maji.”

  “Ummi please kidena blabbing d’innan haka Amal is just my sister there is no any other feeling attatched to it” ya fad’a cikin tattausar murya. Shiru Ummi tayi bata kuma cewa komi ba ganin yadda ransa ke 6aci. 

     Bayan Sallah da k’imanin wata biyu dai-dai da lokacin watan Zul~Hijjah ta kama kenan Afzal da Ummi suka wuce Saudi wanda tafiyansu yazo dai-dai da na Nazeefah, Mummy da Khaleefah. A hotel d’aya duk suka sauk’a inda Khaleefah da Afzal suka had’a d’aki, Mummy, Ummi da Nazeefah ma haka. Kusan kullum tare suke fita suyi Ibadunsu har Allah ya kawo su k’arshen aikin Hajji. Ana jibi zasu juya ne Ummi tayita insisting cewa se Afzal ya kai Nazeefah shopping kar Mummy tayi zaton lallai-lallai tilasta masa akayi batun auren. Seda suka kusan haurawa sama Afzal ya amince. Bayan ya fito daga wanka, ya shafa lotions nasa sannan ya zira d’aya daga cikin expensive jallabiyan daya sissiya ya feffeshe jikinsa jak’ab da turare sannan ya tattara wayoyinsa. 

  “Khaleefah kace bazaka bimu ba? Da Nazeefah zamu fita fa” ya sanar da Khaleefah dake mik’e akan gado se faman buga game na world tip yake. 

  “Friend d’ina zezo za muje muyi playing video game kuje sekun dawo.”

  “Alright make sure you lock the door idan zaka fita.”

  “Toh Uncle Afzal Allah ya kare.” Da haka ya fice ya sauk’a reception a k’asa. Numban Nazeefah da Ummi tayi masa saving about last two weeks yayi scrolling yakai kai amman bai jin ze iya kiranta. Bayan tsawon lokacin daya d’auka yana nazari k’arshe ya yanke hukuncin kiran Mummy. Bayan ta d’aga sun gaisa yake sanar da ita cewa yana reception yana jiran Nazeefah yana son su d’an fita yau, yayita trying layinta amman bai shiga. 

   “Allah sarki halan network ne don gata ma a gefe na bari yanzun nan zata sauk’o sannu ko Babana.”

   “Yauwa Mummy thank you” da haka ya katse. 

  “Nazeefah maza tashi ki shirya Afzal na jiranki a reception.”

  “Mey zey min?” Tayi saurin tambaya had’e da d’ago kanta. 

   “Jimin tambaya yace yana son ku fita go meet him downstairs.”

  “Mummy ni wallahi da kince mishi na fita bana nan.”

  “Dalili? Yanzu har yaro yayi creating time miki ki tsaya kina batun banza?” Itade Nazeefah bata kuma cewa komi ba amman tasan tabbas inma Ummi ce tasa sa na dole kokuwa yana shirin yi mata wani mumunan abun. “Ba zaki mik’e bane?”

  “Ba naji ba” ta amsa a tak’ure. Da haka ta kimtsa ta fice inda ta tarar da shi da wasu yaran larabawa se faman wasa sukeyi. Sallama tayi masa wanda se da ya gama 6ata mata lokacin duniya sannan ya amsa. Maimakon ya sallami yaran su tafi inda zasu, no wasan suka cigaba dayi yabar Nazeefah tsaye gun kaman ta6arya, seda ya tabbata ta gaji sannan ya sallami yaran ya mik’e. Don kanta ta shiga bin bayansa dan kuwa beyi niyyan yi mata magana ba. 

   A mall suka tsaya inda ya d’au trolley tare da ce mata “Pick whatever it is you want I’m doing this because of Ummi so karki kawo tunanin wani abun a ranki.” Daga fad’in haka yaja nasa ya fice ya shiga shopping. Tafi minti biyu tsaye wajen sannan daga bisani taja trolley’n ta shiga kwasan duk abinda yazo hanyarta da abinda zatayi amfani da shi da wanda bata ma san meye shi ba komi kawai d’auka takeyi har Afzal ya gama kwasan abinda ze kwasa Nazeefah bata gama ba se chan ana cikin billing masa abubuwan da ya siya se gata nan cike da trolley tazo ta tsaya bayansa. Murmusawa yayi ba tare da yace da ita komi ba. 

  Kayakin nasa ta leqa ciki sede da mamaki taga yawancin kayan ‘yan mata ya kwasa wanda ta nada tabbacin bana Ummi bane gashi bawai k’anwa ko ya yake dashi ba bale ace nasu ne, toh na waye ne? Kode budurwa yake dashi?? Toh ma ina ruwanta? Kanta ta kawar ta maido da kallonta akan wayarta har izuwa lokacin da billing ya iso kanta. Kud’in abubuwan data siya yayi ninkin na Afzal biyu, da gangan tayi hakan dama, fatanta kawai ace kud’insa ya kasa ta biya wa kanta tasasa jin kunya cikin mutane sede kash! Credit card nasa kawai taga ya zaro ya mik’a wa mutumin inda yayi debiting nasa suka miyar masa da abunsa, har maqora abin ya kai Nazeefah sam ba haka ta so ba. Acikin manya-manyan shopping bags aka sanya musu kayakin nasu suka fito. A bakin k’ofar Nazeefah ta tarar da beggers masu rok’o d’innan tsaye suna neman taimako, ledojin nata gabad’aya ta dank’a musu lokacinda taga Afzal ya kewayo yana kallonta. 

  Ya sha mamaki sosai amman yayi k’ok’arin 6oyewa, taxi d’in ya bud’e ya shiga tare da cewa driver’n su tafi, sa6anin tahowansu a rarrabe suka koma. Ko a babu itama tasan tayi mishi ba dad’i yau, a cigaba a hakan aga wa ze yi surrender. 

   ***

   Afzal ne mik’e kan gadon d’akinsu da Khaleefah se tunanin abinda Nazeefah tayi masa yake yana mey nazarin mey zeyi mata wanda zataji zafinsa haka itama a yayinda wata zuciyar ke cey masa kawai ya barta yaci girma sede yana ganin da k’yar idan ze iya. Ana cikin haka ne wayansa dake kife akan cikinsa ya shiga ruri, duban wa da zeyi ya tarar da Nigerian number, be kawo wani tunanin ba a ransa ya d’aga a tunaninsa gabad’aya ma Sultan ne sede ya tarar da muryar mace, macen ma Amal. 

  Yau akeyinta, bema san ta ina ze fara yi mata bayani ba saboda ko sanar da ita cewa zasa aikin Hajj beyi ba rabonsu tun kafin ya taho Saudi yau kusan sati uku kenan. Ma ya akayi ta samu numbansa? Katse wayar yayi gudun kar kud’inta ya k’are sannan ya kirata back. 

   “Lily?”

  “Na’am Yaya ka kyauta min kenan? Ai kam yanzu na tabbata ni ba Lilir ka bace kamar yadda kake fad’a tunda har zaka aikin Hajji amman baka sanar dani ba.”

   “Lily ba haka bane.”

  “Toh yaya ne Yaya? Kawai sena dena jinka ga layinka kullum switched off hankalina du yabi ya tashi haka su Papi ma gashi ban san gidanku ba, last week naje office naka nake tambayarka sukace kayi tafiya se yau kawai Allah ya had’a ni da Ya Sultan yake fad’a min wai Hajj ka tafi sannan ya bani numbanka truly am very disappointed.”

  “Yi hak’uri kinji Lily? I know I’ve offended you ni kaina bansan meya hanani sanar dake ba but I’m sorry.”

  “Saboda baka damu dani bane mana inda kayi ai da ka sanar dani.”

  “Kema kinsan that’s not true I do care about you Lily.”

“Uhmm” tace kad’ai. 

   “Baki hak’ura ba?”

  “Ai Yaya baya laifi” ta fad’a tana murmushi. 

  “Masha Allah that’s my Lily ya kike toh?”

  “Lafiya Alhamdulillah ya Ibada kun kammala ko? Allah yasa kar6e66iya ce.”

  “Eh Lily ameen, jibi ma in shaa Allah zamu juyo, anyi sallah lafiya?”

  “Lafiya k’alau though I miss having you around.” 

  “I miss you even more Lily yasu Mami da Papi?”

  “Duk lafiyansu suna gaisheka.”

  “Ina amsawa my regards, ya karatu?”

  “Gashi muna ta fama da tilawa.”

  “Allah ya taimaka guess what?”

  “Ameen, tell me Yaya I’m a bad guesser.”

  “Alright digital Qur’an na sai miki na k’ira’a Al~Sudais complete.”

   “Kai Yaya! Dagaske!” Tayi exclaiming yayinda ta tsinci kanta cikin farin ciki maras misaltuwa. “Kaman kuwa kasan k’ira’an Sudais nake bi nake kuma son koya.”

   “Ai kin riga ma kin iya Lily sede kice kina son sake k’warewa.”

  “Kai Yaya! Har yaushe ka sani?”

 “Am serious, there was a day naje gida na tarar dake kina karatu so I stayed back and listened to you as you recite.”

  “Kai Yaya har kasa naji kunya.”

  “Sosai fah Lily nan na gano k’ira’ar Sudais kike bi and masha Allah kin iya sosai.”

  “Thank you Yaya.”

  “You’re welcome karatun boko fa kina d’an tab’awa ko?”

  “Eh wai February zamuyi Jamb ko?”

  “Eh in Allah ya yarda.”

  “Ina d’an ta6awa amman akwai wasu abubuwan dana d’an manta a physics da chemistry kasan it’s been long banbi ta kansu ba.”

  “Don’t worry idan na dawo I’ll help you out.”

  “Toh Allah ya dawo mana da ku lafiya.”

  “Aameen.” 

  “Amman Yaya dama ba commercial class kayi ba?”

  “Waya fad’a miki? I was once a science student.”

  “Shine kuma kake aikin banki?”

  “Ai kowa ma zey iya aikin banki Lily ba se lalle wanda ya karanta accouting ko economics ba kuma kinga ni da bank of agriculture nake aiki.”

  “Agric ka karanta kenan?”

  “Yes se nayi specializing a Horticulture and Agronomy.”

  “Wow! I’m impressed” hira sosai suka tayi se kusan k’arfe goma wanda yake dai-dai da k’arfe sha biyu a k’asar Nigeria Afzal yayi tunanin suyi sallama kodan Amal ta samu tayi bacci, bayan seda safen da tayi masa ya jira tayi hanging sannan ya ajiye wayan a kan side drawer. Daidaita wa Khaleefah dake ta faman bacci blanket yayi sannan ya mik’e ya shiga bayi ya watsa ruwa had’e da d’auro alwalan bacci ya dawo ya kwanta a gefensa. 

 ~•. .•~       ~•. .•~       ~•. .•~      ~•. .•~

    Da dawowansu Afzal da sati biyu kayakin su na Cago suka iso nan yayi sorting out tsaraban da yayi ma mutanen hannun damansa ciki harda na Amal dasu Mami. Na Sultan ya soma kaiwa sannan na colleagues nasa a office. Daga can ya zarce gidansu Amal har ya soma sabawa da ‘yan unguwa saboda yawan shiga da fitan da yakeyi. Parking yayi suka gaisa da ‘yan bakin shago inda suke tambayarsa ko lafiya kwana biyu shiru yake sanar dasu cewa tafiya yayi. 

    Da kansa ya fito da ledojin har zuwa bakin k’ofar gidansu Amal inda ya shiga had’e da yin sallama saidai tun daga bakin k’ofar yake jin hayaniya, kasa kunnen da zeyi ya jiyo muryan Mami da ihun Amal da hanzari ya k’arisa ciki ya tarar dasu se kuje-kuje suke yayinda Mami ke rik’e da tsumagiya tana bin Amal da keta zagaya tsakar gidan. Mami ce ta soma yin tozali da idon Afzal don haka tayi saurin dakatar da abinda takeyi wanda hakan yasa Amal daina ihun da take ta faman yi. 

   “Afzal??” Mami ta kira sunansa cike da k’in yarda. 

  “Na’am Mami” ya amsa. Amal kam don mamaki da kunya tama kasa magana banda raba idon da takeyi. 

  “Wai! Wai! Lale lale mutanen Saudiya sannu da zuwa sannu da zuwa, Baby d’auko tabarma ki shimfid’a masa sannu da zuwa Baba na, sannu da zuwa” Tafiya take wane wanda k’wai ya fashe mata a ciki har ta isa bayan k’ofan d’akin Papi ta d’auko tabaramar. 

   “Zo ki shimfid’a a nan” cewar Mami tana mey mata nuni da inda take tsaye. K’arisawa tayi ta shimfid’a ta kai ga d’agowa kenan Mami dake fakonta ta sauk’e mata tsumagiyan zuwat a baya da iya k’arfin ta, wani irin rkicaccen ihu Amal ta saki yayinda ta shiga susa bayan nata take tana kuka. 

    “Subhanallahi!” Afzal daya zame shedan yadda tsumagiyar ta sauk’a da k’arfi akan bayan Amal yayi saurin furtawa “Dan Allah Mami kiyi hak’uri” be san lokacin da ya sake ledojin dake hannayensa ba a k’asa tare da shiga tsakanin Mami dake shirin sake kaiwa Amal wani zanan yayinda Amal ke ta faman kuka. 

   “Ba zaki rufa ma mutane k’aton bakin nan bako?” Mami ta tambayeta tana neman bin ta gefen Afzal don kuma sauk’e wa Amal wani zanan wanda da sauri Afzal yasa hannu ya k’wace bulalan yana mey bawa Mami hak’uri. 

  “Afzal don Allah ka barni da yarinyan nan yau seta fad’amun waya haifi wani tsakani na da ita a gidan nan.”

  “Kiyi hak’uri Mami beyi zafi haka ba yi hak’uri.”

  “Haba! Wace erin ‘ya ce bata jin magana haka? Ba sa’anninki bane suke aure a k’auye amman don an barki anan kina girman jaki kina abinda kika ga dama zaki soma wuce gona da iri? Wancan ma a gefe amman ace kullum sekin k’ona min miya idan nace ki kula da shi? Kinada kud’in sake min wata cafanin ne?” Shiru Amal dake la6e bayan Afzal tayi se faman share hawayen dake ta faman zubo mata take da hannunta. 

   “Ba dake nake bane?” Nan Mami tayi kaman zata ture Afzal don ta jawo Amal daga bayansa ta gaggaura mata mari saidai Afzal be bar aukuwan hakan ba as da sauri ya janye Amal sukayi baya yana kareta. “Kice mata tayi hak’uri” ya juyo yana kallon Amal saidai ko d’ago kai ta kallesa batayi ba bale tayi yadda yace se faman kukan zucin da takeyi tana hawaye. “Lily ki bawa Mami hak’uri nace” ya sake fad’a mata. 

  “Kiyi hak’uri” ta furta a hankali. 

  “Ni da kene a gidan nan ai ba Papinki yayi tafiya ba? Zan koya miki hankali ma tukunna maza jeki ki tattaro duka novels d’innan ki kawo su nan in cinna musu wuta ba shakka suke d’auke miki hankali ‘yar iska kawai.”

  “Ya isa Mami please kiyi hak’uri bazata sake ba in shaa Allah kiyi hak’uri” Hak’uri Afzal ya cigaba da baiwa Mami yayinda take ta huci, kunde san yadda fad’an itayenmu mata yake idan suka kama basu san suyi shiru ba, da k’yar ya samu ta hak’ura tayi shiru ta janyo hijabi daga kan igiyan shanya tare da d’aukan purse nata akan benchi ta fice don zuwa bus stop ta sake yin wata cafanin. Tana fita Amal ta ruga cikin d’akinta a guje had’e da jan sakata inda ta fad’a kan katifarta tana kuka. Afzal dake tsaye totally out of what to do daga bisani yabi bayanta, k’ofan ya gwada bud’ewa yaji a rufe don haka ya kira sunanta a nitse. 

   “Lily?” Shiru tayi bata amsa ba se k’aran shesshek’an da takeyi yake ji. 

  “Yi hak’uri ki taso ki bud’e wa Yaya kinji?” Nan ma shiru. “Yaya na miki magana bazaki tashi ba Lily? Yi hak’uri kinji? Ina nan ba inda zani sekin bud’e k’ofar nan” Seda yayi dagaske sannan ya samu ta taso ta bud’e masa, ta kai ga juyawa ta koma ciki kenan ya rik’e k’asan rigarta stopping her. Idanunta da sunka kad’a sukayi ja ta d’ago tana kallonsa a maraice. 

 “Come with me” ba musu tabi bayansa inda suka zauna akan benchi. K’aramar gelen abayan daya tsinta a k’asa wanda yake da tabbacin a garin guje-gujen da suka ta6a da Mami ne ta yasar ya d’ago had’e da mik’a mata. “Gashi cover your hair” nan ma batayi musu ba ta amsa ta rufe bak’in gashinta me uban shek’i. 

   “What happened Lily? Kin manta alk’awarin da kika d’au mun na cewa bazaki sake sa Mami surutu ba? Mey kika mata yau kika fusatar da ita haka har ta ta6amin lafiyar jikinki?” Shiru tayi ta kasa cewa komi gudun kar da ta soma magana ta shiga yin kuka. 

  “Talk to me kinji?”

   “Yaya..” ta furta bayan tsawon lokacin data d’auka kafin ta iya furta wata kalman kuka yaci k’arfinta. Tausayi na hak’ik’a ta basa saboda be ta6a ganinta tana kuka me tsuma zuciya kaman na yau ba toh shin meya faru? A kan k’ona girki zalla de Amal baza tayi kuka haka ba kamar yadda itama Mami bazata tayin surutu yadda tayi ba, mey take nufi data kwatanta Amal da ‘yar iska? shin meya faru? 

  Be sake cewa da ita komi ba saboda yasan how badly she needed to cry, ya sani kukan nan da takeyi ne kad’ai ze iya rage mata k’unar da zuciyarta keyi mata don haka ya zauna yana saurronta tanayi badon yanaso ba sedon ba shida wata mafitar. A hankali ta shiga yin shiru, handkerchief nasa ya ciro daga aljihun wandonsa ya shiga share mata hawayen nata a hankali har ya samu tayi shiru. 

   “Yaya-“

  “Shhh” ya katse ta a hankali “Don’t speak.”

  “Yaya but I need to let you know what’s really happening ko Allah zeyi kai zaka yarda da ni kuma bazaka yimin kallon ‘yar iskan da Mami keyi min ba.”

  “Subhanallah Lily! Meya faru?”

  “Yaya Mami tak’i ta yarda dani dan Allah help me out” ta kuma fashewa da wata kukan. “Wallahi ni ba ‘yar iska bace.”

   “Shhh it’s okay I’m here, yi shiru ki fad’a min meya faru.”

  Hanci taja ta share hawayenta sannan ta fara kamar haka; “Ina yaron nan dana ta6a maka hirarsa ranan a office?” 

  “Wanne d’aya? Yaron me markad’en bakin hanyan nan?”

  “Shi” ta amsa tana gyad’a kai.

  “Meya faru?”

  Hawayenta ta share da hanky’n da Afzal ya bata ta cigaba “Yaya sharri yayi mun gun Mami wai kullum ba aikina idan ta tura ni markad’e saidai inyi ta mishi hirar banza ina tatta6ashi.”

  “Subhanallah!” yayi exclaiming cike da k’in yarda. 

  “Yaya ko kai na ta6a shafa koda hannunka ne? Yaya ka yarda zan iya aikata abinda yake tuhumata da shi?” Ta tambayesa cikin kuka sosai. 

  “Ko kad’an Amal you’ll never do such a thing kibar kukan haka kinji? Your Yaya is here.”

  “Thank you Yaya but Mami tak’i yarda dani wai sam ni ‘yar iska ce idona a bushe yake ni munafuka ce, bata sanar da Papi ba tukun amman ta rantse se tayi hakan, shekaran jiya data aikeni markad’e ashe yace mata tabi bayana yanada abinda ze nuna mata bayan ya k’arisa markad’en yace in k’arisa in d’auka, dai-dai na kai inda yake tsaye sauran in d’aga roban kenan na zame na fad’a jikinsa ba tare da na sani ba ashe 6awon ayaba yasa mun don in zame. A sanadiyyar ture ni da yayi naji wannan ciwo” nan ta d’aga bakin skirt nata zuwa idon sahu sega wani babban k’warzani, fatan gun gabad’aya ya d’aye don azaba.

  “Subhanallah” Afzal Yayi exclaiming cike da tausayin Lilirsa. “Me kikayi masa ya za6i yayi framing naki haka Amal?”

  “Wallahi Yaya ba abinda nayi masa.”

  “Tell me the truth Amal bakiyi masa komi ba?”

  “Wallahi Yaya banda cewa da yayi yana sona na nuna masa ko wuta da aljannah ze bani bazanso mutum irinsa ba bakuma abinda ya sake had’amu shine yace min wai zan gani sena lahira ya fini sukuni.” Shiru Afzal yayi ko nazarin me yake se Allah. “Yaya kaima baka yarda dani ba?” Ta tambayesa sabin hawaye na ambaliya a fuskarta “Wallahi ni ban aikata abinda yake tuhumata dashi ba, Yaya please believe me.”

   “Shhh!” ya katse ta “I believe you Lily nasan bazaki ta6a aikata abu haka ba, I’m here bazan tsaya ba se inda k’arfi na ya k’are in shaa Allah yaron nan da kansa zaizo har nan gida ya baki hak’uri ya kuma yiwa Mami bayanin gaskiyan al’amarin da bakinsa.”

  “Yaya how is that even possible?”

  “Trust me okay?” Kai tayi saurin gyad’awa had’e da yi masa godiya. “Girkin da take cewa kullum kina k’ona mata shi kuma fa, haka ne?”

   PAGE 0⃣9⃣

    “Quite alright nasan ina k’ona mata miya but tun kan alk’awarin dana d’aukan maka wallahi ban sake ba se yau, kawai tana neman huce haushi na da takeji ne taketa nanatawa haka nan” ta fayyace mai hawaye na tsiyaya daga idanunta. 

  “Meyasa baki sa hankalinki ba kika bari har girkin ya k’one? Bance idan Mami ta saki aiki ki bar duk abinda kikeyi ba muddin ba sallah bane kisa hankalinki?”

  “Ka fad’a” ta amsa tare da dukar da kanta. 

  “Then what happened?”

 “Yaya duk hankalina baya jikina, na rasa ina zan sa kaina da abinda Abdul (yaron me markad’e) yayi min kuma wallahi ba wani novel d’in nake karantawa ba hasali ma ina zaune cikin kitchen d’in amman banma san miyan na k’onewa ba seda ta shigo ita kuma ta dage sam wai novel nike karantawa shi ya d’auke min hankali.”

  “Shikenan ya isa, bar kukan haka kinji? Am here for you bari Mami ta dawo zan yi mata bayani.”

  Bayan isowan Mami Afzal ya sa Amal ta amshi cafanin ta shiga sarrafawa acikin kitchen yayinda shida Mami suka zauna suna tattauna batun Amal da Abdul. Sam Mami tak’i yarda da abinda Afzal ya fad’a mata a cewarta wai kawai Amal ta tsara Afzal d’inne don ya tausaya mata, ita da ta ga abu da idonta Amal ta kwanta jikin Abdul ne kuma za’a tsaya ana mata wasa da hankali? Daga k’arshe ba don tana so ba se don tana jin nauyin Afzal ta nuna masa ta yarda komi ya wuce. Rok’anta sosai Afzal yayi cewa kar ta fad’awa Papi nan ma de tace taji baza ta fad’a mar ba amman dukda haka Afzal be yarda ba seda yasa ta d’au masa alk’awari. Nan ya zazzage tsaraban daya siyo musun, sosai tayi farin ciki da godiya da addu’a har ta buk’ace sa daya tsaya ya jira abinci amman ya nuna daga gida yake don haka a k’oshe yake. Amal ta kira ta nuna mata kayakin inda itama ta nuna farin cikinta sosai dukda cewa chan k’asa hankalinta a tashe yake. Godiya ba adadi tayi masa itama sannan suka rakosa waje, yau zuwa bakin k’ofa Mami ta rakasa tace su k’arisa da Amal kasancewar miyan dake kan wuta. Wajen motansa suka nufa suka shiga ciki suka k’arisa bakin layi gun markad’en su Abdul. 

   Plan daya shirya yayi ma Amal bayani sannan ya mik’a mata wayarsa bayan ya nuna mata inda zata danna da zaran sun fara magana da shi Abdul d’in. Daga cikin motansa ya zauna yana hangensu yayinda ta k’arasa ta sami Abdul.  

   “Abdul inason magana da kai” tace dashi ba gardama ya mik’e harda d’an guntun murmushinsa ya nufo inda take tsaye. A tunaninsa wai ko tazo ta fayyace mar soyayyan da take masa ne.  Nan Amal ta danna button na play had’e da b’oye wayar k’ark’ashin hijabinta gudun kar ya gani sannan ta fara kamar haka;

    “Yanzu Abdul abinda kayi min ka kyauta kenan?”

  “Mene? Ban fad’a miki cewa na lahira seya fiki jin dad’i ba muddin kika k’i bani had’in kai?”

  “Toh Abdul ana soyayyan dole ne? Ka gane mana bana sonka.”

  “Ni kuwa sekin soni in ba haka ba ki shirya wa tashin hankalin dayafi wanda kika shiga a baya.”

  “Mey kake nufi da hakan?”

  “Ina nufin a shirye nake da inyi komi domin inga na mallakeki.”

   “Kana nufin zaka iya ta6a lafiyata idan banyi yadda kakeso ba?”

  “Sosai ma kuwa har kisan kai zan iyayi a kanki.”

  “Lallai kuwa kasani Allah ya fika kuma ma ranan mey kasa min na zame?”

  “Aww ma tambaya kike? 6awon ayaba na ajiye miki bayan nasa Mami ta biyoki ranan don ta tabbatar da abinda na fad’a mata akanki.”

  “Dukda cewa kasan k’arya ne ni ban ta6a koda rik’e hannunka ba?”

  “Tabbas sharri na miki mana amman ai na ja miki kunne ko ba haka ba? Kuma na baki nan da sati kije kiyi tunani idan har baki amince da soyayya ta ba ina tabbatar miki da cewa gaba abinda zan miki se ‘yan unguwan nan sun k’yamace ki zaman unguwa ya kasa ki ba zaman gidanku kad’ai ba.”

  “Nagode se muga yadda Allah ze baka nasara” daga fad’in haka ta juya ta fice. Tana shiga mota ta mik’a wa Afzal wayan inda yayi stopping ya kuma yi saving sannan yayi playing suka saurara. 

  “Good job Lily kinga da wannan muna iya kai k’arar sa kotu against the crime of misdemeanor but kafin nan I’ll meet him personally to make him go and apologize for you idan har yak’i complying then I’ll have to bring police for him.”

    “Yaya you’re going to do all these for me?” Ta tambayesa a hankali tana mamakin yadda Afzal ke nuna tsananin damuwa duk lokacinda ta shiga matsala. 

  “Wanda yafi haka ma zan miki Lily muddin ina raye kuma inada halin” ya jaddada mata. 

   “Thank you Yaya sakallahu bil jannah.”

  “Ameen don’t worry.”

   “Toh barin koma gida ka gaishe da Ummi in ka isa.”

  “Ki bari in mayar dake.”

  “Haba Yaya nan da gidan ne kuma har seka mayar dani dan Allah ka bari.”

  “Lily-“

  “Please Yaya karka damu” ta katse sa a nitse. 

  “Toh shikenan and please Lily karki sake yin abinda ze fusatar da Mami koda tana miki surutu kiyi mata shiru in har zakiyi magana toh ya zamanto hak’uri zaki bata kinji?”

  “In shaa Allah Yaya nagode.”

  “Gobe ko jibi in shaa Allah zan shigo.”

  “Toh Allah kaimu se anjima” da haka ta sauk’o daga motar tabi lungun da ze kaita gidansu. Isan Afzal gida keda wuya, bayan an sauk’o daga sallan Maghrib Abba yayi requesting presence nasa a site nasa. Wayansa kawai ya d’aga yabi bayan Micheal suka zarce site na Abba inda ya zauna kan kujera. Bayan d’an tambayoyin da Abba yamasa game da aiki da makamancin haka ya buk’aci Micheal daya mik’a masa bak’ar ledan dake ajiye akan dining table. 

  “Ga wannan wedding invitation cards naka ne Prince na d’ibi wanda zan rabar wa jama’a na haka Umminka ma wannan naka ne.”

 “Duka wannan Abba?” Ya tambaya had’e da zaro idanu waje. Invitation cards sekace wanda za’a rabawa kaf ‘yan Maiduguri!

  “Eh Prince nasan iya adadin mutanen da kake dasu fatana de baza su kasa ba ko?”

  “Baza su kasa ba Abba nagode.”

  “Yauwa Allah yayi ma albarka.”

  “Ameen Abba.”

  “Yauwa nace iyayen yarinyan fa suna son fara yi mata jere tunda biki ya matso kusa ga gininka kuma kusan yanzu ma aka fara ina laifin ka yafe neman gidan hayan da kake seka za6i d’aya daga cikin gidaje na dake garin nan? Kowanne ya maka niko zan baka.”

  “Ayyah Abba karka damu, I don’t want to be a burden to you.”

 “Nonsense ko ka manta d’a kake na cikina? Kai de karka damu ni da niyyan baka kyautan gidan ma nake as my own gift for you on your wedding.”

  “Abba ba abinda zance sede Allah k’ara maka bud’i thank you so much in shaa Allah gobe nida PA’nka zamuje mu duba gidajen zan sanar da kai duk abinda akwai, nagode.”

   “Toh hakan yayi sannu kana iya tafiya.”

  “Toh Abba seda safe” da haka ya koma site nasa inda ya fad’a kan gadonsa had’e da zaro d’aya daga cikin invitation cards d’in yana galla mar harara. 25th December daya bada d’in shi ke rubuce jikin invitation card d’in ba abinda aka canza. Ji yake kaman ya tattara duka IV d’in gabad’aya ya k’ona don haushi, da k’yar ya samu yayi bacci ranan. 

   Washegari kamar yadda yayi promising Abba shida PA’n Abba suka dudduba gidajen Abba dake nan cikin Maiduguri wata bungalow ce a New GRA na layin NUJ yayi masa nan yayi deciding ze d’auka, 6angare biyu ne acikin gidan seda BQ. Na gaban wanda ya kasance master side na da two bedrooms, parlour, kitchen and toilet a ciki se main side d’in kuma wanda ya k’unshi four bedrooms da toilet each, two living rooms, kitchen, dining area da kuma store room. Tun a yinin ranan ‘yan uwan Mummy da ita Mummy kanta suka shiga yiwa Nazeefah jere. 

   Afzal kuwa ranan be samu zuwa ganin Abdul ba se a washegari, shiga yayi cikin k’ananun kayan da suka mugun amsansa sannan yasa nerdy glasses (fararen tabarau) kafin wajen markad’en ya yi parking sannan ya fito ya tarar da Abdul wanda idan yayi shekaru dayawa a duniya shine ashirin. Ashe ma yaro ne, jiransa yayi bayan ya gama markad’en sannan ya k’arisa yayi masa sallama. 

   “Wa’alaikumus salam” Abdul ya amsa yana me zuba ma Afzal ido ko zey iya tuna ina ya wayi fuskan nasa sede ina ya kasa, ba tantama yau ne had’uwansu na farko kokuma halan yana ganin shiga da fitansa cikin unguwan nan. 

   “Abdul ko?” Afzal ya tambayesa wanda yasa sa gyad’a kai cike da neman k’arin bayani. 

  “Tambaya kake yi ne bawan Allah?” Ya tambayesa. 

  “A’a magana nakeso muyi.”

  “Toh ina jinka.”

  “Batun Amal ne” ya fad’a had’e da yin shiru. 

 “Amal wace Amal kenan?” Abdul ya tambaya yana mey nazari. 

  “Baby.”

  “Oh! Wani abun ne?”

  “Game da abinda kayi mata ne nakeson jin gaskiyar batun daga bakinka.” Dariya Abdul ya k’yalk’yale da ita “A dalilin mey kake tunanin har zaka ji wata abun daga bakina? Mey alak’arku? Ina da yak’inin cewa Baby batada Ya so meya kawo ka nan?”

 “To make you go and apologize to her and tell her mother the whole truth” Afzal ya sanar dashi cikin tattausar murya. 

  “Turanci kuma zakayi min? Toh dukda cewa ban fahimci duk abinda ka fad’a ba nadeji kanason in sami Mami in fad’a mata gaskiya, ko wani gaskiya kake nufi?”

  “Ka dena pretending kaman bakasan me nake nufi ba, ko ba kai kaje ka samu Mami ka irga mata k’arerayin banza ba akan Amal don ka 6ata mata suna? And also ka ajiye mata 6awon ayaba don ta taka ta zame koba haka ba? Ce maka akayi ana soyayyan dole?”

  “B’awon ayaba? Kai to na ajiye ayimin abinda Allah beyi min ba aikin banza har waye kai zaka tsaya kana gayamun magana iya son ranka wallahi idan ba aikin ‘yan tasha kakeson gani ba anan zaka d’ibi k’afafunka ka koma inda ka fito yanzun nan.”

  “Zaka je ka bata hak’urin ne kokuwa?”

  “Ba inda zanje ina nan” ya jaddada masa. 

  “Good” Afzal yace tare da ciro wayansa yayi playing mar audio da Amal ta d’auka shekaran jiya. Ido wuru-wuru Abdul ya zaro waje yayin da cikinsa ya d’au ruwa. “Taya ka samu wannan magana?”

   “Wancan be shafe ka ba abinda zan jaddada maka shine ka shirya dan kuwa hukuma zata shiga neman ka.”

  “A dalilin meh?”

  “Because you’ve been found guilty of misdemeanor.”

  “Ko mey hakan ke nufi?”

  “Laifi ne wanda kotu ke tuhumar duk wanda ta kama yana ma d’an uwansa barazanar yi masa illa kokuwa lahani na jiki ya kuma cimma hakan. Na farko na sanya wa Amal 6awon ayaba da kayi dagangan don ta taka is a battery crime, haka takawan da tayi kuma ta fad’i kakuma sake hankad’eta taji ciwo shima battery crime ne sannan barazanar illata ta da kayi na cewa idan batayi yadda kakeso ba rayuwarta zata iya shiga cikin matsala shi kuma assault crime ne don kuwa yanzu duk wani mumunin abin da ya sameta God forbid ala misali ma ace wani ne yayi mata kisan kai, kaine nan kotu zata tuhuma saboda nauyin kalamunka” Afzal yayi masa bayani. 

  “Toh naji nayi dukkanin abubuwan daka k’irga amman waya ganni ina cikin aikatawa?”

  “Smart guy kenan seems like ka mance muryanka ne acikin audio d’innan.” 

  “Murya kace, murya kuwa sama da mutane goma suna iya yin murya iri d’aya kuma nan yanzu naga dama ina iya sauya murya na in k’aryata duk ewata hujjar da kake tak’ama da ita.”

  “Zaka k’aryata fa kace?”

  “Sosai ma kuwa tunda ba fuskata bace murya ne.”

  “LOL a gaskiya nayi mamakin yadda ka kasance baho a matsayinka na d’a na miji” Afzal yayi magann had’e da zaro glasses da yake sanye dasu. Wata k’aramar cable yaciro daga aljuhun wandonsa ya had’a da wayansa da glasses d’in sannan ya shiga yin ‘yan wasu danne-danne. Shi de har anan Abdul kallonsa yake, zuciyarsa bata tashi tsinkewa ba seda yaga fuskansa live a cikin wayan Afzal tun daga lokacinda yake amsa sallaman da Afzal yayi masa har izuwa k’arshen maganan da yayi. Ashe de glasses me CCTV Afzal ke sanye da wanda ya aro daga gun wani abokinsa lawyer, glass ne me camera ta gefe biyu duka wanda yake baiwa wanda ke sanye da ita daman yin video record na duk abinda yake tsaye gabansa. 

  Nan take cikin Abdul ya d’au ruwa gyaran murya Afzal yayi had’e da kashe wayan nasa ya mayar aljihu “Se muga yadda zaka iya kare kanka yanzu a kotu idan na nuna musu wannan don kuwa akasin hakan na iya janyo maka one year inprisonment (shekara d’aya a gidan yari).”

   “Shekara de?” Abdul ya nanata cike da k’in yarda lallai kuwa ya yayyafa wa kansa ruwan sanyi. Ai kafin yasan Baby ma ya rayu se akayi yaya don tace bata son sa? Yaga de soyayya bata kisa. Yanzu bama wannan ba waze na taya mahaifiyarsa yin markad’ai da kula da kuma saiwa k’annensa ‘yan biyu magani idan aka turasa gidan yari? Amman wannan mutumi baze gama da duniya lafiya ba yanzu akan d’an k’ank’anin abinda ya aikata wanda be d’aukesa a bakin komi ne ba har yake neman jefa masa rayuwa cikin had’ari haka? Hmm!

  “Ka shirya gobe polisawa zasu zo nemanka don kaika kotu muddin kayi tunanin guduwa kuma that will be a double offense and kasani cewa duk inda ka shiga a fad’in garin nan me sauk’i ne a kama ka, a word is enough for the wise” Afzal na kaiwa nan ya juya ya shiga tafiya. Daga bisani Abdul da yayi shiru tun d’azu ya rasa na cewa bLe nayi ya k’wala wa Afzal kira had’e da bin bayansa. 

  “Bawan Allan ka tsaya, don Allah ka tsaya kayi hak’uri” ko ta kansa Afzal beyi ba se faman tafiyansa yake. 

  “Dan Allah ka tsaya” Abdul ya fad’a a lokacin da ya iya yasha gaban Afzal causing him to stop. “Dan Allah karka kaini kotu kayi hak’uri, k’annena biyu suna iya rasa rayukansu idan kayi hakan please.”

  “Ashe de bakada kunya? Kasan da hakan amma kai baka tsaya kayi tunanin cewa da abinda kayi wa Amal ka sa ta rasa martabarta da darajarta a idon iyayenta ba?”

  “Na tuba officer don Allah ka rufa min asiri.”

   “Bana magana biyu bana kuma ja da baya, tun wuri ka nemo lawyer’n da ze iya tsaya maka a kotu dukda cewa nasan mey wuya ne yin hakan saboda evidences da nake dasu a kanka are strong.”

  “Wallahi ko kud’in d’aukan lawyer ma banida kuma koda ina dashi ma ni bazanyi fad’a da kai a kotu ba amman kayi hak’uri don Allah.”

  “Matsa min a gaba in wuce.”

  “Naji na amince zan bawa Baby hak’uri in kuma fad’awa mahaifiyarta asalin gaskiyan al’amarin amman don Allah ka ja baya da kai k’arana kotun nan.”

  “Come again kace zaka yi mey?” Sake nanata abinda ya fad’a yayi a rud’e “Wallahi idan kana so yanzun nan ma ina iya zuwa in bata hak’urin ni de kawai ka ja da baya da zancen nan.”

  “Ni kakeson raina wa hankali? In ba wai ka kurmance bane I said to get out of my face ka kuma shirya gobe za’a zo a d’auke ka.”

  “Officer dan Allah kayi min rai ka tausaya min.” Bayan d’an tsawon lokacin da Afzal ya d’auka daga bisani yace, “Shige cikin motar nan.”

  “Dan Allah kayi hak’uri.”

  “Ba wani gun zan kaika ba a idanu na nakeson ka bawa Amal hak’uri saboda in zame sheda.”

  “Ba kotun zaka kaini ba ko?”

 “Kaga alamun wasa a tattare da ni ne?” Da sauri Abdul daya gama rud’ewa ya kad’a kai tare da zagayawa ta passenger’s side ya bud’e murfin motar ya shiga. Dai-dai inda Afzal ya saba parking yayi ma yau suka fito da Abdul dake biye dashi a baya suka k’arisa cikin gidansu Amal. Da mamaki Mami ta kar6esu ta shimfid’a musu tabarma sannan Afzal ya buk’aci ganin Amal. 

   “Tana Sallah” Mami ta amsa sa a takaice “Lafiya dai ko?” Ta tambaya duk ta kid’ime. 

  “Lafiya k’alau Mami ki kwantar da hankalinki” zaman jiran Amal suka shiga yi, bayan ta kammala azkhar nata ta fito sanye da d’aya daga cikin hijaban da Afzal ya d’inka mata chan daga gefen Mami ta zauna ta gaishesa bayan ya amsa ya ta6a Abdul da yayi tsit tun shigowansu ko gaishe da Mami ya kasa da nufin yayi magana. 

  “Bazaka yi maganan bane?” Afzal yace dashi cikin tattausar murya. 

  “Zanyi zanyi, Baby kiyi hak’uri” ya furta yana kallon k’asa. 

  “Ka d’ago kanka tana kallonka kana kallonta ka bata hak’uri don’t make me change my mind.” Kan nasa ya d’ago ya kuma bata hak’urin kamar yadda Afzal ya buk’ata, ita de Mami sosai ta tsinci kanta cikin duhu ko hak’urin mey?

  “Saura Mami.”

  Gyaran murya Abdul yayi sannan ya nesanta yace, “Mami kema kiyi hak’uri ki yafe min wallahi sharri nayi wa Amal bata ta6a aikata koda rabin abinda na fad’a miki tanayi ba duk sanda kika turo ta markad’e, k’azafi nayi mata saboda tun ba yau ba nike cewa ina sonta amman tak’i bani had’in kai senayi tunanin hakan kadai ce mafitar da zeysa ta soni idan nasata na dole amman don Allah kiyi hak’uri.”

  “Abdul? Da hankalinka kuwa? Kasan me kake fad’i?” Mami dake jin al’amarin kamar wata raha ta jero wa Abdul wannan tambayoyi cike da rashin yarda. 

  “Tabbas na sani Mami amman kiyi hak’uri.”

  “Kai d’ago kai ka kalleni ka kuma sake nanata min abinda ka fad’a” ta buk’ata.  Ba gardama ya kuma yi, mamaki ne sosai ya rufe Mami akan kunyan da ta jiyo. Shin yanzu da wani idon zata sake kallon Amal? Amman kam Abdul be kyauta mata ba, take gun ta soma nadamar duk abunuwan da tayi ma Amal barin ma zaneta da tayi gaban Afzal da kuma kiranta ‘yar iska da tayi shi yafi komi ci mata rai. Ita ta tarbiyyarta da Amal be kamata tayi kokonto akan hakan ba koda mey aka fad’a mata akanta face ta tara hujjoji da dama, amman kuma ai itama ba laifinta bane duk mahaifiyar data ga ‘yarta na rungumar wani dole ranta ya 6aci but even still kamata yayi tayi bincike tabi diddigin komi ba wai tayi jumping into conclussion ba. 

   _Gareku iyaye bawai duk abinda aka zo aka fad’a akan ‘ya’yanku zaku d’auka ku zauna akai ba saboda muna zamani ne yanzu wanda munafukai sukayi yawa wanda burinsu bai fi su 6ata wa yara suna a idanun iyayensu ba, mutum ya tabbata  yayi bincike sosai tukunnah saboda kamar yadda yara keda hak’k’i akan iyayensu to suma fa yaran nan haka suke da hak’ki akan iyayensu kuma duk wani iyayen da ya d’au hak’k’in d’ansa toh fa Allah ze tsayar dashi akan hakan, Allah is the best of all Allah kare mana zuri’ah, ameen._

   “Amman Abdul tsakani na da kai sede Allah ya isa wallahi.”

  “A’a Mami dan Allah kar kice haka” fad’in Afzal. 

  “Toh mey zance Afzal? Ka dubi yadda na rik’a d’aukan alhak’in Baby mana Baby?” Ta kirata tare da kewayo da kallonta akan Amal datayi lamo jikin garu tana was da k’asan hijbinta. “Baby ki yafeni nasan nayi miki laifi Baby kiyi hak’uri.”

   “Mami ya wuce Allah yafemu gabaki d’aya.”

  “Baby nima ki yafeni don Allah” fad’in Abdul. 

  “Da Allah chan malam rufa man baki kuma maza ka tashi ka bar min gida kuma in shaa Allahu sena sanar da mahaifiyarka abinda kayi mana da ‘yata tasan cewa bakada hankalin ko kobo.”

  “Mami please calm down tunda har Allah yayi shi Abdul ya sauk’e girman kai ya gane kuransa ya kuma zo ya bada hak’uri kamata yayi ki yi hak’uri ki yafe masa mu kanmu munayi wa Allah laifi amman kuma yake yafe mana so please kiyi hak’uri” Afzal yayi bayani a hankali. 

  “Wallahi darajan Afzal kad’ai kaci in ba haka ba Allah ne kad’ai zai mana hisabi kuma dukda hakan ma se mahaifiyarka taji wannan zance.” Hak’uri da wa’azi akan yafiya Afzal ya tayi wa Mami cewa duk wanda ya rufa wa d’an uwansa asiri toh shima Allah zeyi masa ranan gobe k’iyama, hakan ne kad’ai yasa Mami ta hak’ura daga k’arshe ta ja baya daga alwashin data d’aukan ta kuma jaddada masa cewa ya fita harkan Amal idan har ya sake yi mata wani abun ko ya tinkareta da kalman so toh se inda k’arfinta dana Papi ya k’are. 

   Da yazo tafiya ne ya mik’a wa Mami invitation card na d’aurin aurensa cewa a baiwa Papi. Sosai Mami ta tayasa da murna tare da yi mai fatan alkhairi. Ko bayan tafiyan Afzal kuwa hak’uri Mami tayita bawa Amal amman Amal ta nuna mata ba komai ya riga ya wuce. Alhamdulillah tunda Afzal ya cika mata burinta ya wanke ta daga cikin daud’an da Abdul ya aza mata. Bata san da wata bakin zatayi masa godiya ba. Da daren ranan ne bayan sallan Isha ta ari wayan Mami ta tura masa saqo tana mey masa godiya na sosai tare da yimasa addu’o’i da dama. 

   Preparations na biki ne ya sha gaba sosai ta fannin Ango da Amarya gabad’aya as auren na faruwa ne acikin sati na uku me gabatowa. 

      Afzal yadda kuka san ba ango ba, ba abinda ya d’agashi bale ya nana shi a k’asa d’an shirye-shiryen angoncewan nan ba abinda ya ta6a. Muddin baya tare da Amal ko Sultan toh su uku suna tare ne, sosai yake taimaka mata da karatun jamb nata irin past questions d’innan duk ya sai mata tana bin exercises d’in on her own tana solving. Gashi Allah yayi kuwa Amal is a very fast learner, aya bata k’arya dama malamai sunce duk meh haddan Qur’ani a ka toh karatun boko baya basa wuya, Alhamdulillah Amal na ja sosai ta fannin boko. 

   Ta fannin Nazeefah kuwa dukda cewa ba son auren take ba amman don ta k’ure k’awayenta ‘yan k’aryan nan ta bawa Mummy had’in kai sosai. Sam kuma bata nuna wa k’awayenta cewa auren had’i bane za ayi mata da Afzal, hasali ce musu take ita da Afzal sun jima suna soyayya kawai sun yi deciding to keep it private ne, gyaran jikin nan tun dawowansu daga Saudi wata mata daga Nijar keyi mata. Shirye-shirye de ba inda ba’a ta6o ba. 

   Ana saura sati biyu d’aurin aure Mummy da kanta ta kawo wa Ummi invitation na programmes of events da za’ayi wanda suke nan kusan guda biyar. Ita kanta Ummi shakkan sanar da Afzal take sanin halinsa, tasan sarai yau d’inma se sun haura sama kafin ya amince gashi ko Abba baze tilasta masa cewa lalle-lalle se yayi attending ba tunda ba abun addini bane saidai da mamaki data nuna mishi invitation d’in ko complaining beyi ba illa ma cewa da yayi Allah ya nuna mana. A satin gaba aka soma events wanda duk wanda ake buk’atan halattar Afzal ya samu yaje illa bridal shower da Walima wanda k’awayen amarya ne zallah da family. Bawanda ze ga Afzal da Nazeefah yayi tunanin wai auren dole aka sanya su saboda walwala da farin cikin da suke portraying. A haka ne har Allah ya kawo ranarda aka d’aura auren Afzal da Nazeefah akan sadaki dubu d’ari biyu da sisin gold guda hamsin wanda daren ranan Ummi tayi organizing gaggarumin dinner to welcome Nazeefah into the family. Budiri sosai aka sha gun dinner, ba yadda Afzal beyi ba da Amal cewa tayi attending event d’in amman tak’i a cewarta wai dinner ne bazeyi tasa hijabi ba se gyale ita kuma a rayuwa idan akwai abinda bata so shine ta fita da jikinta a bud’e. 

   Bayan abokan ango sun sallami k’awayen amarya suma bada dad’ewa ba suka tafi ya rage Afzal da amaryarsa kad’ai. Bayan rakiyan da yayi musu ya dawo ciki inda ya zarce kitchen ya d’au goran ruwa yana sha yana tafiya, har ya kaiga bud’e k’ofan d’akin seyaji Nazeefah na magana. Sa hankalin da zeyi ya gano a waya take maganar don haka ya kasa kunne yana mey saurararonta. 

   “Haba Bestie a dalilin mey zan had’a shimfid’a dashi? Ai da in bashi kyautan budurcina na gwammaci wasu ‘yan iskan chan sunyi min fyad’e a kan layi… Hm ai kede bari tunda aka tauye min hak’k’i aka aura min shi I’ll make sure shima na tattauye masa hak’k’i a gidan nan zamuga iya gudun ruwansa, sooner or later ze rubuta min takardan saki na se muga ko shima Daddy d’in ze sake bin gida by gida yana rok’on yaran mutane da su taimaka su aure masa yarinya.”

  Murmushi Afzal ya saki tare da kad’a kai sannan daga bisani ya bud’e k’ofan yasa kai ciki. Nan take Nazeefah ta katse wayar tare da cusawa k’ark’ashin pillon dake gefen hannunta. Ko k’ala be ce mata ba ya nemi waje ya zauna ya kwankad’e ruwan daya d’auko daga kitchen, kazan amarcin da su Sultan suka sanya sa siyan na dole ne ya d’ago daga side drawer’n dake gefensa ledoji biyu ne ciki da alama kowanne da kaza d’ai aciki. D’aya ya d’auka ya tura mata d’ayan side nata. 

   Lek’a cikin tayi ta tabbatar kazan ne a ciki sannan tace, “Kana iya d’aga gabbage d’innan daga gaba na dan kuwa ba a yunwa ka d’auko ni daga gidan ubana ba” ta sanar dashi cike da rashin kunya bako tsoron ido, sede yadda kuka san bada Afzal take ba ko kallonta beyi ba bale yasan da shi take, ledan kazan ya gama bud’ewa ya shiga ci seda ya ci kusan rabi sannan ya kora da juice dake gefe se a nan ne ya dawo da kallonsa a gareta yaga de har yanzu bata ta6a kazan nata ba. 

  “Kina iya bar min d’aki I suppose this is my room and I want to sleep” yace da ita cikin deep voice nasa. Da mamaki ta tsaya tana kallonsa. “D’akinka fa kace? Wallahi idan har kaga nabar d’akin nan to gawa na akazo fita dashi idan kaga you can’t cope with me the earlier the better tun wuri ka rubuta min takardan saki na ba d’akin kad’ai zan bar maka ba gidan in whole” Ba tare da yace komi ba ya zaro d’aya daga cikin ninkakkun kayakin baccinsa had’e da ragowan kazansa da drink nasa ya fice mata daga d’akin. Se yanzu Nazeefah ke bin d’akin da kallo tabbas tasan wannan gado baya d’aya daga cikin wanda ita da Mummy suka siyo daga Dubai bade Afzal bane ya taho da abinsa? Oho! Koma meye anan zata na kwana sede shi ya bar mata d’akin. Rage kayan jikinta tayi ta janyo kazan taci fiye da rabi, tun wayewan garin Allah yau banda tea da tasha seda maltina d’aya bata sake cin komi ba. Bayan tayi nak ta tsiyaye ruwa daga dispenser tasha sannan ta shiga bayi ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallah daga k’arshe ta kwanta. Tun kwanciyanta ba abinda taji wane gawa se bayan dawowan Afzal daga massalaci ne yayi tunanin dubata don tabbatar da ko tayi sallah ko batayi ba. Knocking bisa k’ofar yayi sannan ya bud’e ya kunna wuta inda ya tarar da ita kwance se bacci take tayi. Wutan d’akin gabad’aya ya kunna wanda hakan ya sata bud’e idon dole. 

  “Kina iya tashi kiyi sallah” daga fad’in haka ya mai mata da k’ofan ya fita. Wayewan garin Allah keda wuya Afzal ya bud’e wayansa don going through feeds, mails da messages nasa gabad’aya ma ya mance yau birthday nasa ne seda ya soma cin karo da message na Amal wanda take wishing nasa happy birthday sena Ummi da Abba da sauran mutanensa. Kiransu yayi one by one yana musu godiya, kasancewar Amal ce ya kira k’arshe bayan sun k’are wayan take tambayarsa in ze iya shigowa yau she has a surprise for him. Bayan sun gama wayan ya katse ya fad’a bayi yayi brushing sannan ya zira d’aya daga cikin jallabiyansa ya fice siyo musu breakfast bayan yaci nasa ya zauna a parlour yana replying birthday wishes from followers and friends nasa na social media accounts nasa. 

   Yana cikin hakan ne chan sega Nazeefah ta fito daga d’akinta da alama banda brushing da tayi ko wanka bata d’aura akai ba dan kuwa da sleeping dress nata na jiya ta fito sanye da, kanta kuwa a bud’e yake ta kama sa sakwa-sakwa a tsakan kanta. Dining direct ta nufa tana hamma yayin da ta janye takeaway’n da Afzal ya ajiye mata ta soma ci ba gaisuwa bale godiya. A nitse ya mik’e ya bar mata dining d’in ya shiga d’akin data kwanan, kayanta na jiya, wayanta, charger, ragowar kazanta da wata k’aramar akwatin da yake da tabbacin ba nasa bane ya fito dasu bakin k’ofan ya ajiye sannan ya tattaro kayakinsa daga d’ayan d’akin daya kwanan ya maida su asalin d’akinsa had’e da locking k’ofar ya sa key d’in a aljihunsa dai-dai nan Nazeefah ke shigowa corridor d’in.

   “Ya haka Mallam?” Tayi saurin tambaya ita da take da aniyyar shiga d’akin ta koma bacci. Yi yayi tamkar be jita ba, ta gefenta yaso bi seta tare sa “Wannan wani irin childishness ne? Taya zaka watso min kayaki na waje? Wallahi tun wuri ka bud’e kokuma a kunnen Ummi.”

  “Ummi kad’ai? I thought Abba zaki kira, I told you this is not your room why’re you so dumb to realize that? Zan fita idan na dawo na tarar da kayakin nan anan don’t be surprised idan na wulla su waje” Daga fad’in haka ya bud’e d’akin ya shiga tare da locking again. Bayi ya shiga yayi wanka tsaf ya shirya cikin k’ananun kayan da suke bala’in amsan figure’nsa ya fice gidansu Amal. Nazeefah dake tsaye har yanzu bakin k’ofan ta rasa nayi se binsa da kallo take a ranta tana tunanin abinda zatayi masa ta rama wannan rashin mutunci. Haka ba yadda ta iya ta tsuguna ta tattara kayakinta, sauran d’akunan ta dudduba sannan ta d’au d’aya aciki. Akwatunanta wanda muhimman kayakinta ke ciki ta jawo ta kaisu d’akin da ta tare sannan ta jejjerasu cikin wardrobe d’in. Bayan da ta gama ta fad’a bayi tayi wanka ta shiga bin gidan tana zagayawa har anan Afzal be dawo ba. Da azahar Nazeefah ta soma jin yunwa, tayi girki ne? Ta tambayi kanta. Amman ai amarya bata girki a ranar farkon kaita gidan miji kamata yayi har na wata Afzal yana siyo musu abinci ko ba haka ba? Zama tayi a parlour ta shiga duban channels na DSTV in search of abin kallo. 

   Afzal kuwa fitansa ya wuce gun Sultan daga chan ya zarce gidnsu Amal. Gani yayi an shimfid’a babbar dadduma a tsakar hidan gashi ko ina fefes kake gani fiye dana kullum. Kan daddumar ne aka jera kuloli na abinci daban-daban ga silver flasks kusan kala hud’u da yake da tabbacin Aldeb da su ginger ne aciki. Da murmushi kwance a fuskansa ya k’arisa ya zauna daga gefe chan sega Amal ta fito sanye da purple jallabiyar data sha stone work koba a tambaya ba ansan kaya ne me tsada kuma ba shakka yana d’aya ne daga cikin tsaraban da Afzal ya kawo mata. D’aurin kai me kyau tayi irin na zamanin nan da ake kira Zahra Buhari wanda k’awarta ta koya mata. 

   Cike da kunya da girmamawa ta k’ariso ta zauna daga d’ayan 6angaren da Afzal ke zauna had’e da gaishe sa. 

  “Yaya?” Ta kirasa for the second time jin be amsa gaisuwan ba da tayi mar banda kallonta da yake ko kyafta ido babu. “Yaya?” Ta kuma kiransa se anan ya kad’a kai yana me dawo da kansa asalin rayuwa daga duniyan tunanin daya fad’a. 

  “Lily?” Ya kirata yana me kasa d’auke idonsa a kanta har yanzun. Ba wai wani kwalyan azo a gani tayi ba kwalli zalla da powder ta shafa se lip gloss amman wani kyan da tayi sekace wacce a ka yima bridal makeover. 

  “Yaya lafiya?” Ta tambaya yayinda kallon da Afzal keyi mata ya soma sanya ta tsoro. 

  “I’m sorry” ya furta tare da kawar da kansa. 

  “Wani abu ne Yaya?”

  “Nothing Lily illa kyan da kikayi, kinyi kyau sosai” ya sanar da ita wani murmushi cike da jin kunya ta sakar masa. “Kai Yaya har kasa naji kunya” ta amsa tana kare fuskarta. 

   “Masha Allah ina Mami?”

  “Tana ciki tana fitowa.”

  “Lily wannan kuma fah?” Ya tambayeta yana nuni da kulolin. 

  “Har ka mance yau birthday naka ne? This is my birthday treat for you.”

  “Lily you didn’t have to do all these for me, I’ll appreciate even the little things from you.”

  “Haba Yaya ai you deserve even more, nifa raine kawai zance baka d’auka ka bani ba so kabar damuwa don Allah, Happy birthday.”

  “Thank you Lily, I do appreciate but next time please karki kashe kud’inki a kaina haka save it you’ll need it more yanzu nawa kika kashe anan?”

   “Yaya ba wan-” katse ta yayi gano tana shirin yi mai k’arya “Remember kin d’au alk’awari cewa baza ki sake yimin k’arya ba.”

  “Toh Yaya kabar tambaya na nasan zaka min fad’a.”

  “I promise bazan yi ba.”

  “Ba kud’i na ni kad’ai bane harda na Mami da Papi.”

  “Lily!”

  “Yaya please stop complaining kai nawa ne baka kashe ba akan mu a gidan nan? Ina de fata Amarya bata cika maka ciki ba” da wayo ta canza topic d’in. 

  “Ai ko a k’oshe ma nake I must create room for Lily’s cooking.” Murmushi cike da jin dad’i ta sakar masa sannan ta shiga bud’e kulolin sede duka favorites na Afzal ne aciki, d’ayan flask d’in pepper soup na kifi ne aciki se kuma d’ayan garnished spaghetti wanda yasha sardines kaca-kaca aciki. A rayuwa ba abinda Afzal keso kaman kifi yafi sonsa fiye da kowani irin form of protein. Bayan n ga su spring rolls da samosa abinde ba’a cewa komi. 

  Amal na cikin serving nasa kenan sega Mami ta fito itama tayi wankanta fes cikin wata atamfa d’inkin riga da zani. 

   “Bak’on namu ya iso kenan” ta fad’i tana nufan inda suke tare da zama gefen Amal. “Ina yini Mami?” Afzal ya gaisheta cike da girmamawa, bayan nan tayi masa fatan alkhairi na shiga sabon shekara da addu’o’i da dama. 

  “Thank you Mami da wahala haka kuma.”

  “Haba Afzal ai ka zamo na gida yanzu ina ce de abincin gishiri beyi yawa ba ka de san girkin Baby kullum da k’urak’uri.”

   “Kai Mami! Lily fa ta iya girki ai daba don boko ba se a bud’e mata restaurant.” Gwalo Amal ta juya tanayiwa Mami harda kama kunnenta. 

   “Kade hura mata kunne d’an girkin data iyan ma ta shiga kofsa sa.”

   “Ai sede ta k’ara himma ko Lily?” 

   “Sosai ma Yaya kodan wasu suji kunya” Amal tayi maganan tana nufi da Mami. 

  “Aw taron dangi kuma za’ayi mun? Toh barin baku waje ina d’aki idan kuna buk’atan wani abun.”

  “Toh Mami” Afzal ya amsa, da haka ta shige ciki yayainsa Amal ta rink’a jan Afzal da hira yana cin abincin har seda yayi nak sannan ya kora da zo6onsa me sanyi ta kawo masa ruwa da sabulu ya wanke hannunsa. 

  “Yaya are you free today?”

  “Sure Lily wani abu ne?”

  “Yaya saura sati biyu exams na mun gashi ban gama covering syllables d’in ba ko zaka taimaka min?”

  “Why not Lily? Jeki d’auko books nakin.” Cike da jin d’adi ta shiga ta d’ibo books natan nan ya fara tutoring mata ababen da bata gane ba, mamaki ne sosai ya cika Amal sosai yadda Afzal ke solving questions d’in da ko ita da take fresh gradute ma baza ta iya ba. Sa hankali sosai tayi tana mey d’aukan duk abinda yake koyar mata ahaka har Papi ya dawo ya tarar dasu. Bayan sun gaisa yayi ma Afzal fatan alkhairi na shiga sabon shekaran da yayi shima sannan ya k’arisa ciki ya samu Mami. 

    Se La’asr Afzal ya musu sallama bayan tattara mishi ragowan birthday treats da Amal tayi cikin robobin takeaway daga k’arshe ta rakasa. Masallaci ya zarce yayi sallah inda ya wuce restaurant ya sai wa Nazeefah abinci shikam na Lilirsa zeci zuwa anjima. Isansa gida keda wuya ya tarar da Nazeefah da yunwa ya gama cin k’aniyanta se shar6an bacci take ta bar Tv na aiki da alama ko sallah ma batayi ba. Sauk’e ledojin dake hannunsan yayi akan centre table sannan ya d’au remote ya shiga bubbuga mata har se lokacinda ta tashi. 

   “Ke bakisan lokacin sallah yayi bane?”

  “Ka kama ka barni da yunwa laifin waye don banyi sallah akan lokaci ba?” Ta tambayesa cike da rashin kunya yayinda take adjusting position nata don zama. Ledojin ta shiga bi da kallo daga bisani kawai tasa hannu ta janye d’aya daga cikin ledojin da Amal ta had’awa Afzal wanda ke d’auke da Aldeb dasu samosa da wuri ya mik’a hannu ya wabce har yana neman ji mata ciwo. 

   “Ya haka Malam? Ko abincin ma hana ni ci zakayi?”

  “Yes tunda kika d’au wanda ba naki ba” ya amsa ta a takaice, takeaway’n daya tsaya ya sai mata a restor ya wurga mata “Ga naki.”

  “Lallai ma! D’an wannan zaka bani? Sauran kuma fah? Ka kaisu ina? Ai wannan rashin adalci ne.”

   “See banida lokacin exchanging words da ke in kinga ya kasa miki bazaki iya ci ba kinada mota kina iya fita ki sai abinda ya miki” yayi maganan had’e da zaro wallet nasa dubu uku ya k’irga ya ajiye mata “Here you go amman kam wannan ba naki bane don ko wacce tabani ma tasan da zamanki amman batace in ragar miki da komi ba” yana kaiwa nan ya tattara abunsa ya kai fridge ya sanya su ciki had’e da sa key ya zira a aljihunsa.  Binsa da mumunan kallo Nazeefah keyi yayinda ya zo wuceta ya shige d’akinsa. Mik’ewa tayi ta nufi fridge d’in ta gwada bud’ewa seji tayi ya kulle da key don takaici ji take kaman tasa hannu aka tayi ihu sa’ansa d’aya yasa key da kuwa sede ya tarar da empty goruna next idan ya fito. Kuma wai don rashin kunya har yake ce mata wai wacce ta basa bata ce da ita aciki ba? Hmm wato budurwa ma yake da? Ai kuwa bazata fasa kula samarukanta ba itama face ya dena kula ‘yan matansa. Dry abincin nata ta zauna taci ta kora da ruwa sannan ta zarce d’akinta tayi sallah. 

***

     Wajajen 10:12pm Nazeefah ta ajiye wayarta da take ta faman chatting na asara tun d’azu. Sallan Isha ta idar sannan ta fito parlour don neman abinda zata sa a baki. Afzal ta tarar zaune a parlour da plate na samosa da su spring rolls kusan biyu a gabansa ga kuma flasks da take da tabbacin juice ne a ciki se faman cin abincinsa yake yana kallo. Murmushi ta sakar wa kanta don kuwa a nata tunanin kalan abincin dake gabansa itama ya sai mata. Cike da jin dad’i ta k’arisa dining da mamaki ta tarar da shi empty ko leda d’aya babu akai bale kula to ina abincin nata ita? Kitchen ta shiga ta leqa sede shar ba alaman komi, yau akeyinta. Parlon ta dawo taje tayi tsaye a kansa “Malam where is my dinner I’m hungry” ta sanar dashi cike da gadara kaman wanda bazeyi magana ba yace, “Seki shiga kitchen ki girka abinda ya miki.”

   “Ban gane inyi girki ba ka ta6a jin inda Amarya tayi girki ne?”

   “Aww ashe amarya kike” ya amsa har anan be ko juyo ya kalleta ba balle ya san wani kalan kaya take sanye dashi. 

   “Wallahi Afzal bana cike da rashin mutunci wannan son kai da mey yayi kama? Kai ka sai wa kanka abinci ni kuma kace min inyi girki? Yanzu baka ji kunya ba.”

   “I really don’t know what you use your ears for I told you wannan duka da kike gani anan bani akayi bawai fita nayi na siya ban sai miki ba and don ke kuma bazan fita da daren nan ba da sunan sai miki abinci ko ki nemi abinda da zaki dafa kici or simply kisha ruwa ki kwanta bana son hayaniya kina iya barmin kai.”

   “Kai wai rashin mutunci ka gada ko? Mu zuba ni da kai a gidan nan and see who will surrender first aikin banza kawai!” tana kaiwa nan ta nufi d’akinta Cookies ta k’wak’ulo cikin kayakinta ta zauna taci don kuwa ta gommaci ta kwana da yunwa data aikata abinda Afzal yace mata dan kuwa be isa yayi iko da ita ba. Juice nata tasha akai sannan ta cigaba da chatting nata har se lokacinda bacci ya d’auketa. Kamar jiya yau ma Afzal ne yazo ya tayar da ita sallan Asuba, yana mey mamakin sakaci irin nata ace da girmanta amman bazata iya sa alarm ta tashi tayi sallah ba yaso ta koma baccin. 

     Haka rayuwar nasu ta cigaba da kasancewa ba ci gaban ko k’ala, dai-dai da rana d’aya Nazeefah bata ta6a d’aukan tsinstiya ba da sunan shara iyaka idan d’akinta ya gama baza datti sannan zata d’an share sama-sama. Afzal da bai saba da zama cikin k’azanta da daud’a ba tuni yasa Micheal ya nemo masa me aiki na miji wanda bayan kwana bibbiyu yake zuwa ya share gidan tas ya kuma yi mopping harda goge amman banda d’akin Nazeefah kasancewar dokan da Afzal ya kafa masa. Bugu da k’ari Afzal be fasa siyo musu abinci ba kaman yadda ya d’au alk’awari wa kansa. Abinda ya kama daga kan breakfast, lunch and dinner duk ya d’auke wa Nazeefah ita de aikinta bai fin taci ta sha tayi wanka da bacci sede abinda yake damunta d’aya ne, yawan fitan da Afzal keyi. Ace mutum kullum bai yini a gida? Ya fita tun safe se yamma abinda ke kawosa kad’ai shine delivering abincinta. Bayan tana da tabbacin an basa leave a office balle yace aiki yake zuwa. Shin ina yake zuwa? Toh wallahi itama baza a barta a baya ba. Afzal na fita itama zata d’au wankanta tabi bayansa. Dai-dai da rana d’aya Afzal be ta6a tambayarta ina take zuwa ba koda kuwa ya dawo gida ne ya tarar bata nan harkan gabansa kawai yakeyi idan ta dawo kuwa ko kallonta baiyi bale ya tambayeta daga ina tafito. Tun abun bai damun oganniyan taku har ya soma ci mata rai yana tsaya mata a wuya shin shi Afzal d’innan wani irin miskilin mutum ne? So take yace ze mata magana kan yawon da take wataran amman ina. Rashin hankalin nata har ya kaiga wani sa’in ma mangariba ba a gida take ba amman haka ko d’aga ido ya kalleta bai yi idan ta dawo. Ita ba haka taso abin ba taso ace ya gwada tinkarar ta koda so d’aya saboda su yita ta k’are tayi masa rashin kunya iya son ranta in yaji zafi ya sake ta amman ko shiga harkanta baiyi a gidan. 

   Kasancewar k’arfe bakwai na safe Amal zatayi jamb nata yau tun shida Afzal ya gama shirinsa, yana cikin shan black tea sega Nazeefah da tun d’azu ya tada ita sallah amman tak’i tashi se yanzu ta fito, yanzun ma sabida ishin ruwan daya isheta ne. Da fari da ta gansa tayi tunanin ko office zasa amman seta gansa sanye da half jumper tabbatar mata da cewa ba chan d’in za sa ba. Lallai ma kuwa sabon iskancin daya koyo kenan, wato yanzu sammako ma ze fara yi toh Allah ya taimakesa ya kawo su ranan da zata tabbatar da zargin da take akansa in har ta tabbatar ‘yan matan waje yake bi toh in shaa Allahu zamansu ya k’are don bazata hak’ura ba har seya sake ta, aikin banza kawai. K’arisawa gun fridge d’in tayi ta d’au ruwa ta koma d’akinta shiko yana kammala breakfast nasa ya fice. Already Amal na jiransa lokacinda ya isa, Allah bada sa’a su Mami suka mata sannan tabi bayan Afzal suka fito. Acikin Unimaid tayi jarabawartan, bayan addu’an da Afzal yayi mata ta k’arisa cikin exam hall d’in, Afzal be je ko ina ba zama yayi cikin motarsa kusan na awa biyu da k’ari yana jiran fitowar Amal. Sanin dole zata ji yunwa kaman yadda shima yakeji don kuwa gashi rana ta fito, bayan data gama exams d’in ya wuce dasu restaurant inda suka karya da chips sannan ya sai wa Nazeefah nata. Har gida ya mai da Amal ya komo nasa shima, akan dining ya ajiye wa Nazeefah abincin nata ya k’arisa d’akinsa ya kwanta don biyan baccin da yayi missing. 

   Bayan kwana uku results nasu Amal ya fito. Tunda Amal taji results ya fito hankalinta ya tashi jira kawai take Afzal ya kirata yace mata ta fad’i. Shiko Afzal a ranan da aka saki results d’in ya shiga website d’in ya duba mata inda ya tarar taci…

   PAGE 1⃣0⃣

     Points har 225, damn! Sosai yaji dad’i ya kuma yi alfahari da ita yana me kasa 6oye farin cikin da ya tsinci kansa a ciki. Layin Mami ya kira take, kasancewar itace ke kusa da wayan yasa ta d’aga, bayan sun gaisa ta kaiwa Amal wayar tun kan ya buk’aci hakan. 

  “Assalamu alaikum Yaya ina yini?” Ta fad’a lokacin da ta amshi wayan daga hannun Mami tana mey azawa a kunnenta. 

  “Wa’alaikumus salam Lily, ya kike?” Ya amsa. 

  “Alhamdulillah ya gida ya Nazeefah kuma?”

  “Lafiya Alhamdulillah.”

   “Toh masha Allah.”

   “Hmm” ya numfasa had’e da yin shiru, hakan yasa Amal tambayar ko lafiya. 

  “Results naku ne ya fito” ya sanar da ita cikin wani irin salon daya sa Amal yanke hukuncin ta ma riga ta fad’i exams d’inne. 

   “Innalillahi!” ta furta yayinda zuciyarta ta buga. 

  “Ban ci ba ko?” Ta tambayesa a hankali bayan d’an lokutan data d’auka. 

  “Toh gashi nan de-” ai bata basa daman k’arisa abinda yayi niyya ba ta katse wayar. Ba shiri ta fad’a bayi ta d’auro alwala, tana cikin shimfid’a sallaya wayan ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira wani tsinkewar zuciyarta ta kuma yi ba shakka ta fad’i d’inne in ba haka ba da tun da ya kira ze sanar da Mami. Nata ya k’are yau, shin ina zata sa kanta? Da wani idon zata sake kallon Afzal?? Hmm har ta hango tokari da habaicin da Mami zata yi mata idan ta gano ta fad’i jarabawar nan. Sanya wayan tayi a silent sannan ta shiga kawo nafilfilu. 

    Ta 6angaren Afzal daya san rud’ewa irin na Amal kuwa da gan-gan yayi hakan dama ba don komi ba se don yayi dariya kamar yadda yakeyi yanzu, har picturing fuskanta yadda ta rud’e yake a kansa. Two more missed calls ya k’ara mata har anan bata d’aga ba don haka ya tura mata sak’o;

   ‘Lily pick up that phone.’ Dai-dai lokacin da take sallame sallan sak’on yake shigowa batayi ta kai ba seda ta gama tofe addu’o’inta sannan ta lek’a screen d’in. Bata kai ga bud’ewa ba se ga call nasa n shigowa ta sani muddin bata d’auka ba ransa ze 6aci, ba don tana so ba ta d’aga had’e da yin shiru. Shima shirun yayi don kanta ta soma magana. 

   “Yaya don Allah kayi hak’uri” jin yadda ta rud’e shiko ya canza ra’ayinsa na sanar da ita aslin batun ya soma da cewa, “Lily meya faru?”

  “Tell me Yaya na fad’i ko?” Ta tambayesa cike da tsoro. 

  “Your results…” se kuma yayi shiru. 

  “Yaya don Allah kayi hak’uri wallahi ni kaina ban san ya akayi na fad’i ba please don’t tell Mami.”

  “Am so disappointed in you Lily shin duk abubuwan dana koya miki daman ba ganesu kike ba kokuwa amfani da computer d’inne baki iya ba?”

   “Wallahi ni kaina ban sani ba amman kayi hak’uri don Allah.”

  “Nide nayi asaran biyan kud’in jamb.”

  “Please kayi hak’uri” ta furta a hankali yayin da takejin haushin kanta. 

  “Yanzu Lily ki rasa nawa zaki ci se 225?”

  “Na shiga uku 225!” ta nanata a rud’e tsabagen yadda ta rikice hankalinta be ma bata taci ba se chan abin ya buga mata kai “225 fa kace Yaya?”

  “Eh” ya amsa. 

  “Toh ai naci ko?”

  “Congratulations Lily” ya fad’i yana mata dariya. 

  “Omg! 225! Yaya I made it! Oh Alhamdulillah” take ta sauk’a k’asa tayo sujudush shukur tana meyiwa Allah godiya sannan ta cigaba da ihun, don kanta tayi shiru. 

  “Kin gama ihun? Afzal daya nisantar da wayan daga kunnesnsa ya tambaya. 

  “I’m sorry Yaya ban tsammanin zan iya 6oye farin cikina.”

  “Sure you can’t, ko ni nan na kasa 6oye nawa. Keep it up Lily I’mso proud of you.”

  “Thank you Yaya but the accolades goes to you, kai ka koya min ababe da dama.”

  “Duk da haka Lily kinyi k’ok’ari you know what? Kin cancanci kyauta.” 

  “Kai Yaya dagaske?” Ta tambaya cike da kunya. 

  “Yup kina gida gobe?”

  “Eh” ta amsa. 

  “Good, zan shigo in shaa Allah.”

  “Toh Yaya seka shigo amman fa ka tsinka min zuciya wallahi na d’au na fad’in ne dagaske har na soma tunanin da wani idon zan sake kallonka” ta fayyace mai. 

  “Matsoraciya kawai ashe baki yarda da kanki ba.”

  “Not really kasan shi E exams sa’a ne ba a yi mishi baki.”

  “Da wannan kuma but even still my Lily is such a clever girl.”

  “Thank you Yaya” hira kad’an suka ta6a sannan suka yi sallama. Kan Mami da Papi ta fad’a bako sallama ta soma yi masu wak’an taci jarabawar ta inda suka mugun tayata da murna barin ma Papi. Alwala duk suka d’auro sukayi nafillah raka’a biyu don yima Allah godiya. 

   Washegari kaman yadda Afzal ya d’au alk’awari hakan ya cika yazo ya d’auki Amal ya kaita shopping amman kunya yak’i barinta ta d’au koda abu d’aya a ganinta wai hakan ya zamo rashin godiya taya akan duk d’awainiyyan da yake mata da kuma wanda zeyi mata a nan gaba ace ya kawota shopping ta baje tana kwasan kaya?

   “Lily kina son muyi fad’a ko?”

   “Yaya wallah nida nasan nan zaka kawo ni ma da ban biyoka ba tun farko don Allah karka damu am good.”

  “Lily nifa na kawoki or isn’t wrong for a brother to take his sister shopping?”

   “Not at all Yaya kawai ba abinda zan iya d’auka anan ne.”

  “Dalili? Ba abinda ya miki anan? Kin fi son kiyi purchasing products naki online?”

   “Waye ubana?” Da sauri ta bige bakinta “Ni ba abinda nake nufi ba kenan kawai deh…” se kuma tayi shiru. 

  “Look kin de san rantsuwa ko?” Kai tayi saurin gyad’awa tana mey k’ure masa ido “Toh wallahi Lily muddin baki d’au ko da abu d’aya ba anan believe me anan d’in zamu yini inda hali har ma mu kwana.”

  “Yaya please karka ce haka” tayi saurin fad’i. 

  “Am damn serious” ya sanar da ita cikin tattausar murya. Yana kaiwa nan ya juya ya je ya zauna gun cashier. Tsaye tayi gun jugum totally out of what to do, daga bisani ta juya ta shiga bin store d’in da kallo wanda ya k’unshi kayan kwalya zalla da turare da makamancin hakan. Yau ake yinta kwata-kwata idan za’a k’irga abubuwan data san amfaninsu a shagon basu fi biyar zuwa shida ba toh me zata d’auka don su rabu da Yayanta lafiya? Chan tunani ta fad’o mata gun turaruka ta nufa tuna turarenta ya kusa k’arewa. Bin su ta shiga yi da kallo tana me bud’e kan tana shinshinawa don samun wanda k’amshin zey mata, chan ta d’ago wani da aka rubuta ‘adolfo-dominguez’ a jiki. Ba k’aramin k’amshi turaren yayi mata ba gashi nan d’an tsut d’an k’arami hakan ya sata yanke hukuncin cewa bazeyi tsada ba. A nitse cike da jin dad’in ta k’ure Yayanta ta tako gun cashier’n inda Afzal ke zaune daga gefe hanklinsa ya duk’ufa akan wayansa se faman latsawa yake tayi gyaran mrya wanda hakan ya sanya sa d’ago kai.

  “Yes where is your basket?” Ya tambayeta, shiru tayi bata ce komi ba “kin d’ai san bana wasa dake ko Lily?”

  “Yaya gashi na d’au wannan” ta furta cike da tsoro tana mey fito da hannunta data 6oye a bayanta. 

  “Mey wannan d’in?” ya tambaya yana bin hannun nata da kollo. 

  “Turare” ta amsa a takaice. A tunaninta ze hau mata k’orafi setaga yana murmusawa ko dariyan mey yake? Ta tambayi kanta. “Kawo ayi miki billing” k’arisawa tayi ta bawa cashier’n inda ya d’au pointer don gano price d’in. 

   “N11,765 (dubu goma sha d’aya da naira d’ari bakwai da sittin da biyar)” ya sanar da su. Da idanu na zubewa a k’asa domin mamaki da na Amal sun jima dayin hakan. Dubu goma har da sha d’aya fa taji cashier’n ya ambata kode ya 6ata ne? D’an wannan turare dayake nan kaman a sa a hancin ne har dubu da k’ari lallae se yanzu ta fahimci ma’anar murmushin da Afzal keyi mata ashe de yasan tsadan turaren ne. Ita haushin kanta ma taji shin meya hanata duba price d’in bayan gashi an manna a jiki harda ticket nasa?

  “Akwai abinda zaki k’ara?” Afzal ya tambayeta cike da neman tsokana. 

  “Cashier d’an kawo wannan d’in Yaya zan canza turaren.”

  “Ina wasa dake ne Lily?”

  “Yaya wallahi almubazaranci ne taya turare kad’ai har dubu goma? Don Allah kar ka biya kud’in ni da nasan ya kai haka tsada ma da ban d’auka ba tun farko” Shiru ya mata tare da zaro wallet nasa ya k’irga kud’in ya mik’a masa. Don takaici Amal ji take wane ta kashe kanta, da fesa turaren dubu goma ai gara a baiwa mutum kud’in ya biya buk’atunsa dashi. 

    Godiya sosai tayi masa sanda ya sauk’eta bakin lungun gidansu. Tazo dai-dai da shiga gida kenan sega Ameenatu na fitowa daga gidansu nan de suka gaisa inda Azee ke tayata murnan cin jarabawar da tayi yayinda Amal tayi mata godiya. 

  “Toh daga ina kuma kika fito haka?”

  “Wallahi babu nida Yaya ne muka d’an fita.”

  “Oh Baby! Wannan Yayan naki fa ba k’aramin ji dake yake ba ‘yan unguwa har sun soma cewa saurayinki ne.”

  “Don girman Allah su rufa min asiri ina ni ina Yaya?” Ta tambaya had’e da kwararo idanunta waje. “Wallahi ba komi a tsakanin mu illa soyayyan dake tsakanin Ya da k’anwa.”

  “Toh deh tayi tsami ma ji” ta amsata cike da gatsine. 

  “Wallahi Azee babu komai, haba mana kiyi tunani da kanki ina zan kai na miji kaman Yaya? Kema kinsan yafi k’arfina.”

  “Haka de kikace amman wata soyayyar bata fi wata ba.”

  “Na amince da hakan amman komin taurin kan zuciya still tasan da wa take yi, ba yadda za’ayi zuciyata ta soma son Yaya da wata manufa so tun wuri ku da ‘yan unguwa ku sa hankalinku cikin ruwan sanyi.”

  “Nifa ban ce komi ba, rana de bata k’arya, tukuna me wannan kika rik’e sekace k’wai a hannu?” Ta tambayeta had’e da zuba ido wa ledan da Amal ta damk’e a hannu. 

  “Wannan?” Amal ta d’aga tan nuna mat “Ai wannan yafi k’wai buk’atan adana.”

  “Ko meya saki fad’in haka?”

  “Ke matsalarki bawai a baki labari bane kika tashi sekin k’ara gishirin ki a kai ki baza mutum a unguwa.”

  “Haba k’awas wani asirin kika ta6a bani nayi miki haka?”

  “Kar deh?” Ta watsa mata harar. 

  “Ki yarda da ni wallahi ko Falmata bazata ji batun nan ba.”

  “Hmm kawai Yaya ya kaini wata shago wai in d’auki duk abinda yamin…” nan de ta baiwa Azee labarin abinda ya faru baki wangalau cike da k’in yarda Azee  ta tsaya tana kallon Amal ita kan ma tak’i yarda seda Amal ta nuna mata receipt d’in. 

   “Wai wai wai gaskiya Yayan nan naki dagaske yake, kut!” Tayi exclaiming cike da k’in yarda. 

   “Ai kede ki bari hakan ma wai yana tambaya ta ko da akwai wani abinda nikeso again.” 

  “Gaskiya Yayan nan naki na sonki Baby kuma kikace ba komi a tsakanin ku kai! Da akwai ayan tambaya.”

  “Kinga irin halinki da baniso ko?”

  “Toh afuwan afuwan yanzu de d’an bani in fesa turaren a hammata na.”

  “Shamawai! Ni me shi ban fesa ba se ke?”

  “Yi hak’uri mana ta Yaya Afzal ke inba ke bama har a kaiki siyayya ki tsaya kina plako ai idan baki buk’atan abubuwan kwalyan mu munayi kuma idan ba son kai bama da kikazo siyan turaren ai ko yan dubu ne seki d’aukan mana da Falmata.”

  “Eh naji d’in matso kusa in miki feshi d’aya a hijabi amman ko ba a hammata ba Wallahi don koni ba kazai zanna shafa turaren nan ba se idan ta kama. Chan saman wardrobe m zan ajiye.” Rok’arta Ameenatu ta rik’ayi har seda Amal ta amince ta bata turaren ta fesa a hammatarta, tamkar k’wai haka Amal ke tattalin wagga turare. 

****

   Da auren Afzal da Nazeefah wata d’aya da k’imanin sati biyu kenan Afzal yaga fa baze iya da siyan abinci ba kullum bayan gashi shi ba gauro ba. Wannan ma a gefe, hutun da Nazeefah ke samu ya soma yin yawa, na farko ko shara batayi bale mopping da goge-goge don haka ya yanke hukunci daga yau ze dena siyo abinci ita zata soma yi musu girki tunda Allah yayi ya biya sadaki. 

   Washegari, kamar yadda oganniyan taku ta saba se chan shad’aya saura ta tashi. Tayi brushing ta fito sanye da kayan baccinta gashin kan nan a hargitse wane gidan tsunstu. Dining ta nufa inda ta tarar da shi empty.  Dank’aree! Ta furta a zuciye bade abinci Afzal ya sai ba ita ba yau? Juyowan da zatayi se ga Afzal ya fito sanye da k’ananun riguna se buga k’amshi yake. Hannunsa rik’e yake da wata k’aramar saucer wanda ke nuni corn flakes yasha aciki. Gabansa tasha da wuri lokacinda ya zo shiga kitchen d’in tare da kama k’ugunta “Mallam ya ina breakfast d’ina?” Ta tambayesa cike da rashin kunya ko gaisuwa babu. Banza da ita yayi tare da niyyan bin gefenta ya wuce inda ta sake taresa. 

   “Ban gane ina maka magana ba kana miyar dani ‘yar iska where is my breakfast?” Kaman wanda baze amsa ta ba yace “Tunda dumb head naki ya kasa figuring out miki abinda ya faru, abinci ne na daina siya, starting today ke zaki fara girki a gidan nan.”

  Murmushi kad’ai ta iya ta saki yayinda mamaki ya mamaye mata zuciya. Ko k’ala ta kasa ce masa da kanta ta matsa mishi ya shiga kitchen ya ajiye saucer’n ya fice sannan ta shiga ta dafa indomie sharp sharp taci. Wajajen k’arfe uku Afzal ya dawo, ya d’ibo yunwan duniya ya taho dashi da niyyan cin abinci ya tarar da dining empty, banda plate na macronin da ya sha had’i da minced meat aciki dage gaban Nazeefah tana ci, bayan nan ba komai se cup na ruwanta da juice. 

   “Nawa kuma fah?” Ya tambayeta bayan jan ajin da ta gama yi masa daga bisani tace, “Ban girka ba” ba tare da ta kalli direction nasa ba.

  “Mey na ce miki kafin na fita?”

  “Ba zaka iya ba da barazanar siyo abinci? In ba shi ba toh na manta.”

  “Young lady let me make this clear to you muddin kina zaune a cikin gidan nan a k’ark’ashina kike kina ganewa ko? I won’t allow it you disrespect me in my own house.”

   “Hilarious!” Tayi exclaiming tare da k’yalk’yalewa da dariyan daya mugun k’ular da Afzal “Sannu masu gida, nayi maka rashin kunyan me ka isa kayi? Iyaka kace zaka sakeni, please make it quick ko duka na zakayi? Yanzu kai bakaji kunya ba? Ka kalli tsabar cikin idanu na kace wai inyi maka girki? LOL ina gadara da ji da kai d’in ya tafi? Idan ban manta ba bakin da yace ayi mishi girki yau shi ya ta6a cewa baze iya cin abinda hannayena suka girka ba. Now I see you’re not a man of your words” ta k’are tana zuba masa mumunan kallo da dara-daran idanunta. Da k’yar Afzal ya iya danne zuciyansa ya juya ya fice tare da bar mata gidan gabad’aya. Idan yace ze biyewa Nazeefah to k’arshenta zata sanya sa aikata abin kunya ne, amman ko ta guji randa zata turasa jikin bango. 

   Da harara ta bisa yayinda ya ficce tare da furta “Tafi nono fari” k’asa-k’asa. 

  A da yayi niyyan zuwa gida gun Ummi amman gudun abinda hakan ze iya haifarwa se kawai ya wuce gidansu Amal inda ya tarar da ita zaune kan tabarma tana bitan karatu. Sallama yayi a hankali sannan ya shiga. 

  “Wa’alaikumus Salam” ta amsa dai-dai lokacin data kai k’arshen aya jin murya kaman na yayanta . “Yaya!” Ta yi exclaiming cike da jin dad’i bayan ca ta tabbatar da cewa eh shi d’inne. Sede sam ba walwala a fuskarsa har izuwa lokacinda ya k’ariso ya zauna a kan benchin dake gefen taburman da take zaune. 

  “Yaya ina yini?” Ta gaishesa tana mey ajiye Qur’anin da take karantawa a kan mazauninsa. 

   “Yaya meya faru?” Ta kuma tambaya tana me k’are masa kallo. 

  “Lily I’m hungry” ya sanar da ita tamkar wani yaro k’arami. 

  “Yunwa kuma?” Ta nanata “Meya faru? Nazeefah bata gida ne?” Jin yayi shiru tayi saurin mik’ewa ta zarce kitchen Allah yaso yau shinkafa da wake da stew sukayi ba tuwo kaman na jiya ba. Da sauri-sauri tayi serving nasa ta d’auko masa d’aya daga cikin gorunan aldeb dake kula ta ajiye masa. 

  “Gashi Allah sa ka iya cin abincin gidan namu” a nitse ya shiga cin abincin yayinda ta d’ebo mishi ruwa a cikin wata plastic jug. Komawa tayi ta zauna akan taburman had’e da k’ura masa ido tana me mamakin yadda yake cin abincin a hankali dukda cewa yuwa ta addabesa, hakan ba k’aramin burgeta yayi ba. Seda ya cinye tas ya kora da ragowan ruwansa da aldeb d’in sannan ya maido da kallonsa akanta inda idonsu ya had’e, murmushi ta sakar masa “In k’ara maka?”

   “Me kika mayar dani, glutton?”

 Murmushi kad’an tasa had’e da kawar da kanta “Thank you Lily” ya furta wanda hakan yasata maido da kallonta a garesa “Don’t mention Yaya you deserve morethan this” murmushin ya miyar mata “ina Mami?” Ya tambaya. 

  “Ta fita gidan biki.”

  “Papi fah?”

  “Ya fita kasuwa.”

  “Yau ma ked’ai ce a gida?”

  “Eh nima inason in gama bita na ne daman se in fita.”

  “Se kuma nazo namiki ruining schedule ko?”

  “Haba Yaya ko kad’an wallahi karka damu amman meya faru?”

  “Game deh?” Ya tambayeta. 

  “Waya ta6a min kai? Waya hana min ka abinci?” Shirun da yayi tayi zaton ko Nazeefah ce, amman meye dalili?

  “Nazeefah ce?” Ta tambaya a hankali, kai zallah ya gyad’a mata. 

  “Toh meyasa?”

  “I don’t wanna talk about it Lily I’m sorry.”

  “It’s okay na fahimce ka.”

  “All I know is hak’uri na ya kusa k’arewa.”

  “Ayya Yaya se kana had’awa da hak’uri kasan mu mata rauni ne.”

   “Rainin hankalin Nazeefah ya soma yawa ne Lily, she is taking my patience for granted.” 

  “Se hak’uri Yaya wataran se labari kuma ai kaga Nazeefah yarinya ce idan ban manta ba kai ka fad’a mun cewa she’s just 17 years old wasu abubuwan se kana overlooking amman ka sake hak’uri.”

  “Shikenan Lily ya wuce.”

 **** Akan ana gaba zama ya daidaita, tsakanin Afzal da Nazeefah sede abinda ya k’aru. Tun kan rashin kunyan da tayi masa ya daina shiga harkarta kwata-kwata kowa zaman kansa yake a gidan, har rana me kaman ta yau kuwa kwana be ta6a had’asu ba, girki de Nazeefah nayi duk da cewa ba kullum ba amman tanayi na dai-dai bakinta kad’ai, shima Afzal ko da wasa be sakeyi takan kulolinta ba. Gado ba gwaninta ba, munde san hali irin na Afzal idan yayi fushi da abu to ciresa yake gabad’aya daga ransa. Abincinsa yawancin a restaurant yake ci kokuwa gida gun Ummi and atimes gun su Amal. 

   Ana cikin haka ne su Nazeefah suka bud’e makaranta zasu koma second semester kenan. Wayyo ita dad’i kasheta, aga wa Afzal zena fita yana bari a gida yanzu, itama idan ta fita tun safe se shida zata na dawowa abinta. Da safe tsab yau ta tashi ta shirya abinta, bayan ta karya ta leqa parlour taga Afzal bai nan d’akinsa ta nufa ta kwankwasa k’ofa, bayan d’an lokaci ya taso ya bud’e da alama bacci yake don wani kakkafewan da idanunsa sukeyi. Sanye yake da guntun wando zalla wanda hakan ya bawa Nazeefah daman k’are wa k’irar jikinsa kallo. Wai wai wai zalla take furtawa a zuciyanta yayinda ta kasa d’aga idanunta daga kan well visble abs nasa, packs guda shidan nan duk sun bayyano. Ouu la la!

   “Lafiya kinzo kinyi min tsaye bakin k’ofa?” Ya tambayeta yana me tsamo ta daga duniyar tunanin data wula. Da sauri ta kad’a kanta had’e da kawar da kai yayinda ta shiga jin haushin kanta yanzu shikenan Afzal ze soma jin kansa tunda ya kamata tana kallonsa ba ko kyaftawa haka shin meke damunta ne? Mstw! Mozewa tayi tace, “Zani school tunda kayi gwanintan d’aukoni daga gidan mahaifina ya zamo dole ka bani kud’in break bayan nan kuma inason yin full tank wa mota na.”

  Se yanzu Afzal ya bud’e idanunsa da kyau yake kuma k’are mata kallo yanzu da irin wannan shirin ne matar aure zata fita? Lalle yau ya sake tabbatawa Nazeefah batada hankali. Kallonta yake daga sama zuwa k’asa. Na farko d’aurin kanta ma ba me mutunci bane ina d’aurin nan na ture kaga tsiya? Shi ta buga a kanta k’eyar nan gabad’ai gashinta ne a waje data nannad’e, ga kuma kayan da take sanye da, wata matsatssiyar straight gown me tsagu a baya wanda yabi surar jikinta tun daga sama har k’asa gaba kuma k’aramar mayafin data d’auka wanda ya kasance small size na gyalen R&S da ta nannad’e sa gefen kafad’arta d’aya. Be ce da ita komai ba ya juya cikin d’akin ya nufi gun safe nasa had’e da sa password d’in. Bayan ya bud’u ya k’irgo kud’i ya dawo ya mik’a mata amsa tayi cike da walak’anci da tak’ama sekace ba wacce tazo tana tambayar  abu ba. Da sauri ta shiga k’irgawa dubu shida ta tarar kafin ta kawo wata tunanin a ranta yace, “2k kud’in makarantar ki 4k kuma kiyi full tank da ita” yana kaiwa nan ya ja k’ofansa ya rufe ba tare da ya bata daman yin magana ba. 

   Mamaki ne ya mamaye Nazeefah don kuwa ko a mafarki bata ta6a kawowa a ranta cewa Afzal ze bata kud’in kashewa a rana har dubu biyu ba kode yana nufin har da na gobe ne? Amma ai da ya sanar da ita. 

   A gida ma gabad’aya dubu Mami ke bata dama-dama ma Daddy ne ke bata dubu biyu. Lallai kuwa auren nan ya d’an had’u ta wani fannin. 

  **** A makaranta…

   Nazeefah ne zaune da k’awayenta suna cin abinci a restaurant. Nana ce ta ta6e baki tace, “Amarya kenan kinga wani fresh da kika k’ara kuwa? Gaskia angon nan namu na kula dake.”

   “Toh ba dolensa ba” ta amsa tana murmushi. 

  “Amman ya ganki yau da safe kuwa?”

  “Sosai ma ai da shi ze kawo nima nace ya bari kawai yayi baccinsa, wani abu ne?”

  “Babu ai naga wankan da kika d’aukan ne sekace ba matar aure ba.”

  “So kike kice wai mijina baya kishina?”

  “Kusan hakan Babe kinga Hafiz (saurayinta da ake shirin yi masu aure) wallahi ko gyale ya haneni da sawa sena tabbata yayi tafiya nake sa abuna amman yana gari kam ban isa ba, d’an banzan kishi ne da shi.” Sosai kalamun Nana suka tsaya wa Nazeefah a wuya, da biyu dama itama tayi wannan shed’anin shirin taji ko Afzal zeyi magana se gashi kamar yadda ya saba manna mata hakan yayi. Yo dama mutumin da ba sonka yake ba kam ai ba yadda za’ayi yayi kishin ka wai ma tukun meyasa ta damu? Da yayi kishinta da kar yayi duk uwa ubansu d’aya. 

   Dagewa tayi tace; “Ai da dad’ewa na fahimci Hafiz nakin nan d’an zamanin da ne yo me acikin sa gyale? Kuma kinga Baby na ya yarda dani yasan ko tsindir d’ina na fita bazan kula wani a waje ba kede ki binciki Hafiz naki gani nake kaman be yarda dake ba.”

  “Haka dey kikace anyways ga ankon nan fa kunsan abun ya matso” Nana tayi maganan had’e da shiga photos a wayanta don nuna wa k’awayen nata sample. Nazeefah ce ta soma kar6a tana gani “Na farkon lace ce 15k ita zaku sa a pre wedding dinner se atamfar kuma a kamu ita 5k ce, next material d’in kuma na dinner’n ango ne wanda za’ayi a Abuja shi 10k ne altogether is 30k kenan. Kar ku damu da siyan head ango ya d’au nauyin duka biyun tare da makeup wa 3 best friends d’ina.”

   “Awww kice mu soma booking makeup artist tun yanzu” cewar Nazeefah tana mik’a wa Adama wayar. 

  “Manyaaaa” Rumaysa tayi praising nata “Gaskiya na sha wutan lace d’innan bari zuwa anjima zan miki transferring kud’in.”

  “Ni kuma ko zuwa gobe ko jibi haka kunsan Ummi sunyi tafiya banida enough kud’i” cewar Hadiza. 

  “Nazeefah kefa?” Tambayar Nana. 

  “Ai ko a yanzu ma ina iya k’irgawa in baki tunanin barin Baby na nike for this Abuja dinner anya kuwa zan iya?”

  “Su masu baby! Sha wannan iyayi sede kiyi ma su Rumaysa da basu da direction nikam kinga na kusa” take suka rushe da dariya. 

   “Alright zuwa anjima zan miki transferring.”

  Chan da yamma Nazeefah ta dawo gida, ruwa ta watsa ta nemi vest da wata wandon data d’an sauk’o k’asan guiwa da kad’an tasa sannan ta shafa mai a kanta ta kama a tsakiya ta fito. A parlour ta tarar da Afzal yana d’an wasu aikin office d’in, kamar yadda ta saba ba sallama bale gaisuwa ta k’arisa kansa tayi tsaye “Malam ina buk’atan kud’i k’awata zatayi aure kud’in anko 30k, d’inki 15 se kuma na gudumawa 20k.”

  Sai dai yadda kuka san kurma haka ya mata wajen ko d’aga kai ya kalleta ma beyi ba ran Nazeefah in yayi dubu be 6aci ba, a rayuwa ba abunda ta tsana kaman shariya. 

   “Mallam ya ina maka magana kana mai dani mahaukaciya?” Nan ma shirun yayi mata, gabansa ta shawo “Mallam magana fa nake” sede shiru by now zuciyan Nazeefah tafasa yake.  Paper’n data ga yana typing content nasa a computer tasa hannu ta waske se a nan ya d’ago lumsassun idanunsa yana kallonta. 

   “Ban gane ina maka magana ba kana mayar dani yar iska, da ba don kayi gwaninta ba ka aureni you think zan tsaya ina tambayarka kud’i ne har ma ka tsaya kana nuna min isa da tak’ama? Wallahi Afzal kake ko wa ka sani ba’a tsiya ka d’auko ni ba, a gida ban ta6a neman abu k’ark’ashin iyayena ba na rasa saboda haka I see no reaso why zanna maka magana kana manna min. Ka bani abinda nake buk’ata wallahi idan ka bari raina ya 6aci naje gida na tambaya kaine da jin kunya ace mutum ko rik’e mace tal ya kasa.” Tun d’azun jira take yayi magana amman yak’iyi banda idon da ya kafa mata kaman hoto, bayan ya gama sauraronta daga bisani kawai ya wafce paper’n nasa data d’auke had’e da mik’ewa. Laptop nasa ya d’aga ya shiga nufan d’akinsa yayinda take binsa a baya tana k’orafi da surutu tana habaici tana zaginsa. 

   “Ai da fili ka fito kace baka da kud’in da yafi maka ba wai ka tsaya kana nuna isa da tak’ama ba andeji kunya wallahi ace common kud’in da be taka kara ya karya ba ya gagari mutum” har anan be tanka taba, yana kaiwa d’akinsa ya shiga had’e da sa makulli ya rufe. Ganin suratai da buga k’ofan nasa da take ba shi zaisa ya taso ya bata kud’in ba don kanta ta wuce d’akinta.

 Washegari tun 1 ta dawo gida ta dafa indomie taci sannan ta shirya tsaf ita gata me iyaye tunda miji ya hanata kud’i zata je ta amsa a gun su. Tana cikin shan ruwa sega Afzal ya dawo daga office ko meya faru kuma yau? Shi d’inda se yamma yake dawowa kode wata mantuwar yayi? Ta tambayi kanta. 

   “Yauwa Mallam ka dawo a dai-dai zani gidan mahaifina in tambayeshi kud’in daka hana mun, zan nuna maka rijiya ba gun wasan yaro bane keep your damn money” yana gama sauraronta ya shige d’akinsa file nasa daya mance ya d’auko sannan ya fito. Wato kuma yau don munafirci don zata gidansu shine har da sa babban mayafi ta lullu6e jikinta haka, lallai munafiki ya shiga uku a rayuwa Afzal yayi tunanin haka a ransa. Shi bema d’aurata a ka ba bale abubuwan da takeyi su damesa kamar yadda Amal ta fad’i yarinta ke damunta ga rashin wayo da tarbiyya. 

    Isarta gidansu keda wuya se lale masu gadi da masu aiki suke yi mata kasancewar ta d’au kusan sati biyu bata lek’o su ba. Ita da Khaleefah sekace ba karnukan da suka saba haushi ba harda hugging nasu ba k’arya sunyi kewar junansu. Parlour’n Daddy ta shiga inda ta tarar da shi da Mummy zaune. Waje ta nema a k’asa kaman mey hankalin k’arshe sannan ta gaishesu cike da girmamawa. Sosai suka ji dad’in ganinta cikin wannan kamilalliyar shirin, barin ma Daddy. Ina irin manyan gyalen nan na kashka shi ta lullu6e jikinta dashi tun daga kanta. 

    “Ina Afzal ko yau baku taho tare bane?” Ya tambayeta. 

  “Wallahi aiki yayi masa yawa in ba haka ba daman tare zamu taho amman ko yana gisheku barin ma Mummy wai yaushe zaki sake kawo mana kwad’on dambun nan naki mey dad’i.”

Murmusawa Mummy tayi cike da jin dad’i ita kam Alhamdulillah Allah ya bata sirki d’an arziki imagine zuwansu sau biyu nan se yayi ma Khaleefah kyautan kud’i itako na zani. “Kice masa kwanan nan in shaa Allah.”

  “Toh Mummy.”

  “Toh bari in barku tare zan d’an fita” Daddy ya sanar dasu. 

  “Daddy idan ba damuwa ina d’an buk’atan wani abu.”

  “Mene kenan Nazeefah akwai matsala ne?”

  “A’a” tayi saurin amsawa. 

  “Toh madallah ina jinki.”

  “Daddy k’awata ce daman zatayi aure” ta fara a nitse. 

  “Toh masha-Allah Allah ya sanya alheri.”

  “Ameen” both ita da Mummy suka amsa a tare. 

  “Toh Daddy kud’in anko nikeso dana gudumawa.”

  “Toh nawa ne?”

  “Ankon 30k ne se kuma na d’inki 15k dana gudumawa dubu ashirin, Mummy ai zaki iya tuna k’awata data kawo min bedsheets na 40-40k d’innan guda biyu a bikina ko?”

  “Tabbas Allah ya basu zaman lafiya.”

  “Yauwa toh daddy ita zata yi aure.”

  “Toh kin tambayi Afzal kud’in ne kokuwa?” ya tambayeta. Gabanta ne taji yayi mumunan fad’i me hakan ke nufi? Kame-kame ta shiga yi chan de ta amsa da “A’a” k’sa-k’asa. 

    “Toh ai shi ya kamata ki soma tambaya Nazeefah bani ba.”

  “Ban fahimce kaba Daddy” a bak’wance zancen ya isketa. 

  “Nauyin ki ya tashi daga kaina ya koma kan mijnki Afzal, duk abinda kike buk’ata shi zaki tambaya sai idan abin yafi k’arfinsa ne zan iya taimaka miki nan ma sena tambayi izininsa saboda kar a nuna masa rashin isa, ina fatan kin fahimce ni? So kije ki tambayesa tukuna se idan ya nuna baida hali dukda cewa ma nasan hakan baze faru ba amman idan abin ya juya hakan zan tambayesa izini ko nawa kikeso ni kuma na miki alk’awari zan baki.”

  “Allah sarki Daddy se naga kaman hakan yayi sauri I mean da auren mu wata nawa ne da zan soma tambayansa kud’i masu yawa haka banda na makarantar da yake bani. Daddy please ko na yau kawai ka bani yaso zuwa nan gaba mun sake sakewa da juna sena soma tambayarsa banson yayi mun mumunar fassara yayi tunanin kud’insa nakeso cin ko makamancin haka.”

  “Sam Afzal baze miki mumunar fahimta ba Nazeefah, Afzal yaro ne mey hankali da tunani.”

  “Sosai ma kuwa” Mummy ta sanya baki tana mey gyad’a kai. Ji Nazeefah ke wane tasa hannu a kai ta k’urma ihu yanzu bayan gorin iyayen data gama yiwa Afzal ne Daddy keson ta koma ta sake tambayansa? Chab! Yau tana cikin wani yanayi tasani ko sama da k’asa zata had’a Afzal ba bata kud’in nan zeyi ba, menene mafita?

   “Daddy d-” ido Mummy tayi mata da wuri don haka tayi shiru “Toh ni bari in shirya zan d’an fita idan kin koma gida ki gaishe min da Afzal.” Ba don tanaso ba ta amsa da “Toh Allah ya kare.” Daddy na fita ta taso ta zauna kusa da Mummy. 

  “Mummy dan Allah ki taimaka min.”

  “Dame?”

  “Mummy da kud’in please.”

  “Wai baki ji abinda Daddy’nku ya fad’a miki bane? Bawai ana hanaki kud’in bane Nazeefah ki gane mana ba a son nunawa Afzal d’in rashin isa ne, baze ji dad’i ba amman yanzu ki gwada tambayansa muji me zece.”

  “Ni banason in tambayesa.”

  “Dalili?” Mummy ta tambaya da mamaki. 

  “Haba mana Mummy kinde san halin Afzal.”

  “Kode naki ba? Tell me something kin tambayesa kud’in nan da rashin kunya da isa yak’i ya baki shine kikazo nan kina yi mana k’arya ko.”

  “Ni bance ba.”

  “Ja chan har ni zan haifeki ki tsaya kina min k’arya? Toh wallahi ki cigaba.”

  “Toh Mummy laifi na ne? Na tambayesa ya hanani me kikeson inyi?”

  “K’arya kike wallahi, idan har a cikin girmamawa kika durk’usa kika tambayesa nasani tabbas ze baki kud’in nan tunda de Allah yayi yana da hali.”

    “Wallahi yayi kad’an in durk’usa a gabansa” ta furta ba tare da tasan yaushe ba. 

  “Innalillahi! Kika ce mey?” Mummy ta tambaye ta cike da mamaki. “Wato rashin kunya kike yi masa a gidan ko? Toh wallahi ki cigaba ranan da ya illata ki kece da asara.”

  “Mummy please ni in zaki bani kud’in toh in bazaki bani ba ni zan tafi.”

  “Ki tafi kar kuma ki sake dawowa maras kunya kawai a da nayi niyyan baki kud’in nan amman tunda haka ne na fasa. Sani ya rage miki ko kiyi humbling kanki ki basa hak’uri ki tambayesa cike da girmamawa ko kuma kije bikin k’awarki ba anko ba gudumawa kece k’awaye zasuyi gulma a bayan ido bani ba kin ganni nan k’awata ta haihu zani suna in kin tashi tafiya ki gaishe min da Afzal.”

  “Mummy dan Allah karki min haka Mummy kiyi hak’uri.”

 “Afzal zaki baiwa hak’uri bani ba” tana kaiwa nan ta mik’e ko sake kallon Nazeefah dake ta kiran sunanta batayi ba ta wuce d’akinta. Haka idily Nazeefah ta cigaba da zama cikin parlourn totally out of what to do, gashi ba kud’in arziki bane acikin account nata sam be kai N50k ba.  Haka duk su Rumaysa suka sata gaba a bikinta seda kud’in nata ya k’are tas. Mstww! Dan kanta taja motarta ta fice ta koma gida tun isarta take tunanin yadda zata 6ullowa al’amarin nan don a gaskiya bata jin zata iya yin abinda Mummy tace tayi. Ai ma zubar da aji ne, idan ta durk’usa a gaban Afzal ai seya fara jin kanshi ya aza ya kai ne alhalin ba kowa yake ba a idanunta gaskiya no way! Toh kode ta fasa zuwa bikin ne? Gab da lokacin bikin ta soma yi musu k’aryan laulayi na damunta. Kai amman fa k’arya ba kyau don komin yaya ne a k’arshe za’a kamata, haka kawai mutuncinta ya kwa6e. Wayyo Allah menene mafita?

    Share maganar tayi har na tsawon kwana biyu, bayan sati d’aya Nana ta soma damunta da kira tana tambayarta ko lafiya ita da ta d’au Nazeefah ce zata soma siyan anko sekuma gashi. K’arya Nazeefah tayi mata cewa ta mance ne amman right away zatayi mata sending kud’in in shaa Allah da haka sukayi sallama. D’akin nata ta shiga zagayawa tana tunanin ya zata 6ullowa al’amarin sede ta kasa yanke hukuncin komi daga k’arshe de ta yanke hukuncin kirar aminiyarta ko zata iya ranta mata kud’i kafin nan. 

   “Babe wallahi banida kud’i nima da k’yar na samu na had’a kud’in ankon nan na bada d’inki haka ma yanzu bansan me zan kai mata as gudumawa ba wannan shegen saurayin nawa ne ya kod’a ni in gaya miki yace ze turo min kud’i shiru.”

  “Toh bestie yanzu what is the way out?”

  “Hmm mafitar ki d’aya ce Bestie.”

  “Mey fah?”

  “Humble yourself kawai ki tambayeshi da hankali banda rashin kunya.”

  “Haba bestie yanzu wannan itace shawara?”

  “Idiot ai ba cewa nayi ki soma girmamasa ba amman yanzu ki gwada kigani maybe dalilin daya sa ya hanaki don kin tambayesa cike da rashin kunya ne kinde san maza da son a girmama su so ki gwada yin hakan muga ko ze baki.”

  “Kai Bestie anya?”

  “Ki tsaya kina taurin kai karki sauk’e wannan girman kan muga inda ze kai ki wallahi kinsan aikinsu Adama k’iris suke jira suyi chaaa a kanki.”

  “Toh naji zanyi tunani.”

  “Yauwa se anjima Mama na kira na.”

  “Aha bye.” Da haka sukayi sallama. Zama gu d’aya Nazeefah tayi tana nazari ta bisa a hankalin ne ko kuwa? Timing nasa tayi bayan sallan isha dai-dai lokacinda yake kallon sports ta fito ta leqa sa sekuwa gashi kallon yakeyi. 

   It’s now or never ta tunasar da kanta tare da numfasa sannan ta k’arisa parlourn, pack na takeaway’n daya gama ci tasa hannu ta d’aga “Kagama ci zan iya fita dashi?” Ta tambayesa cike da kissa. Kallonta ya tsaya yi na d’an lokaci da tunani kala-kala na tafiya a kansa kode aljanu sun shige ta ne? Kai ya gyad’a mata a hankali nan ta d’aga ta kai kitchen tayi disposing a dawowanta harda d’auko masa ruwa ta tsiyaye a cup ta ajiye masa tare da durk’usawa a gefe shide Afzal banda binta da kallo da yake ya kasa yin komi. 

   “Afzal nace dama kayi hak’uri game da rashin kunyan dana maka ka bani kud’in ankon please.” Da mamaki ya zaro lumaassun idanunsa waje sekuma yayi sauri ya kawar da kansa ba tare da yace mata komi ba. 

   “Afzal?” Ta kuma kiransa. 

  “Nawa kike buk’ata?” Ya tambayeta bayan tsawon lokacin daya d’auka. 

  “30k ne ankon, sena d’inki 15k san-“

   “Nawa ne altogether?” Ya katse ta. 

  “65k” ta amsa k’asa-k’asa.

  “Naji” ya amsa sama-sama. Ganin be kuma yunk’urin cewa wani abu ba ta numfasa, “Afzal yau ne nike buk’atan kud’in.”

   “Da daren nan kikeso inje ATM? Cash da yake wajena bekai sum da kike buk’ata ba.”

   “Toh in baka account details d’ina mana seka min transferring” tayi tunani. Kaman wanda baze amsata ba yace, “Write it down for me” ba gardama ta d’ago wayanta dake kan cinyarta “Ko zaka bani number’nka se inyi maka sending?” Nan ma seda ya d’au tsawon lokaci sannan ya irga mata nan take gun ta yi mishi sending, shima ba tare da 6ata lokaci ba yayi mata transferring sum d’in. Baki bud’e cike da mamaki Nazeefah ta bud’e tana kallon cikin wayarta yayinda ta kasa amincewa da abinda idon ta ke gane mata. “Dubu saba’in?” ta furta a hankali. 

  Kai ta d’ago tana kallonsa yayinda ya mayar da hankalinsa kan Tv’n “Nagode” ta sanar dashi nan ma kaman wanda baze amsata ba yace da ita, “You’re welcome” sama-sama. Mik’ewa tayi ta shiga d’akinta tare da fad’awa kan gado cike da jin dad’i. Aminiyarta ta kira dan breaking mata wagga news. “Babe you won’t believe this!”

  “Ya meya faru?”

  “Dubu saba’in mutuminki yamin transferring.”

  “Like forreal!”

  “I’m telling you wallahi ban d’au ze saurareni ba ma.”

  “Hehe kode so yake kuyi sulhu ne?”

  “Lallai kuwa ze 6ata lokacinsa dan kuwa ni ba sa’ar yinsa bane.”

  “Omo I dey feel my babe anyways congratulations sekiyi maza ki turawa Nana kud’in.”

  “Ai right away, gobe zaki shigo school?”

  “Eh kefa?”

  “Also semun had’u.”

  “Alright ba-bye” da haka sukayi sallama inda tayi wa Nana transferring kud’in.

Leave a Reply

Back to top button