GeneralHot romantic hausa novel complete

RANA DAYA COMPLETE HAUSA NOVELS PAGE 16 to 20

*PAGE 1⃣6⃣*

   Rawa bakinta yake tana kakkarwa tace, “Ummi wallahi ban yi mishi komai ba wallahi bani bace.”

  “Da Allah rufa mana baki!” Mummy ta katse ta. “A jinki bama sane ne da kalan rashin hankalin da kikeyi masa a gidan? Tun yaushe yaron nan yake hak’uri dake? Gashi nan k’arshenta kin sanya masa ciwon zuciya amma karki damu komi yazo k’arshe Allah tada kafad’an shi ya rubata miki takardan sakinki ki huta shima ya huta kowa ma ya huta.”

  “Mummy dan Allah kar kiyi mun haka wallahi inason Afzal kuma wallahi ni ba ni bace sanadin wannan rashin lafiyan nasa Ummi you’ve got to believe me” ta juyo tana kallon Ummi a raunane “Ku tambayi D’anladi me gadi wallahi ahaka muka tsince sa a d’akinsa dan Allah ku yarda dani” sede ba wanda yako kalleta a cikinsu ita kanta Ummi kuka takeyi. Mummy ko ta had’a tagumi tana tunanin yadda zata fara sanar da Daddy wannan labari me d’aci. 

  “Dr dan Allah kuyi duk abinda ya kamata ku tabbata d’ana ya rayu shi kad’ai gareni bazan iya rasa saba dan Allah kuyi mun rai.”

  “Karki damu Hajiya we’ll keep him under an intensive care da ikon Allah ze samu sauk’i sede ku sanya sa a addu’a abu da zuciya ba guarantee, Allah de ya bashi lafiya.”

  “Ameen amma Dr dakata dan Allah, shin baku gano ko mey ya jawo masa wannan ciwo ba?”

  “Tukuna muna kan jiran sauran sakamakon su fito amma ina da tabbacin cewa tunani ne yayi masa yawa dake BP nasa ma ya hau, tabbas akwai abinda yake damunsa na tsawon lokaci wanda ya rik’e a ransa yake kuma bi da zuciya.”

  “Ai na fad’a” Mummy tasa baki “Bin duk kalan halayya da rashin hankalin da fand’ararriyar ‘yarnan keyi masa ya jawo mai wannan ciwon zuciyan. Kinyi asara wallahi Nazeefah kinyi asara.” Banda kuka ba abinda Nazeefah ke iya yi, k’iri-k’iri tasan ba ita bace da laifi amma ake blaming nata ya zatayi idan wannan labari ya iske Daddy? Wayyo nata ya k’are. 

  “Nagode Dr zan iya shiga ganinsa?”

  “Sosai ma kuwa excuse me.” Yana ficewa Ummi ta shige d’akin Afzal a karo na farko da idanunta suka sauk’a akansa ba se hawaye ba, kuka ta shiga yi na sosai da k’yar k’afafunta suka iya takata izuwa gefen gadon nasa. Hannu ta aza akan oxygen supply da aka sanya masa sannan ta koma gashin kansa tana shafawa a hankali yayinda take zubda hawaye sosai. 

  “Afzal Ummi ce” ta furta yayinda kuka yaci k’arfinta. “Afzal Baba na Allah tada kafad’anka in shaa Allahu zaka samu sauk’i sede na rasa dalilin da zaisa kana da uwa a raye amman ka gwammaci ka rik’e damuwanka wa kanka kai kad’ai. Meyasa Prince? Idan Nazeefar ce bakaso a yau ka sanar da Abbanka wallahi mey hana raba auren nan se Allah why do you have to do this to yourself?” Rungumosa tayi tana kuka na hak’ik’a se chan ta iya ta fito daga d’akin ta nufi inda Mummy ke zaune itama ta zauna. Nazeefah dake tsaye daga gefe ne ta k’araso ta durk’usa gabanta. 

  “Ummi dan Allah kiyi hak’uri kibar kukan nan haka.”

  “Mey kika ma Afzal Nazeefah? Na d’au da kikazo kika sanar dani halin da kuke ciki zaki canza al’amuranki ne ku soma zaman lafiya a gidan meya faru?”

  “Ummi wallahi bani bace, duk abinda nasan ze 6ata wa Afzal rai ina k’ok’arin dainawa, wallahi ba nice sanadin rashin lafiyarsan nan ba. A sume haka muka samesa a d’akinsa da D’anladi daman tun jiya daya dawo gida ya rufe kansa a d’aki ban kuma jin motsinsa ba you have to believe me.”

  “Hmmm I wish I could Nazeefah” amsan da Ummi kad’ai ta bata kenan sannan ta kau da kanta. Gun Mummy takeso ta nufa amman bata shirya shan wata marin ba dan haka ta tattara kanta taja gefe. Satan idonsu tayi sid’ak-sid’ak ta shige d’akin Afzal d’in. A hankali ta k’arisa gefen gadonsa ta tsuguna yayinda take zubda hawaye sosai. Hannunta dake kakkarwa ta d’aga ta sauk’e akan fuskarsa tana shafawa a hankali yayinda wani irin so da tausayinsa yake sake shiga zuciyarta. 

  “Afzal?” Ta kirasa a raunene tana shafa gashin kansa. 

  “Afzal wai nice sanadin rashin lafiyarka? Wai nice na janyo maka wannan ciwon? Dan Allah ka farfad’o ka fad’a musu ba ni bace. Afzal suna shirin rabani da kai, Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba dan Allah ka tashi ka musu bayanin komai Afzal I love you, I love you so much and I’m not willing to let you go, I’m here, I’ll always be by your side dan Allah kar ka bani kunya ka tashi.” Kanta ta sauk’e akan k’irjinsa a hankali tana me cigaba da kukan tsuma zuciya. Ta dad’e a hakan badan tana so ba ta tashi ta fice se don kar azo a kamata. 

   Abba dake Morocco Ummi ta kira ta sanar dashi halin da ake ciki. A karo na farko kan ma yak’i amincewa don yadda kansa ya d’aure. Ciwon zuciya de? A dalilin mey? A iya zamansa da Afzal be ta6a sanin Afzal nada zurfin ciki ba toh meya faru? Kode zancen Ummi gaskiya ne, Nazeefah ce ke k’untata masa shiko yake bi a rai har abun ya kai ga haka? Aiko ya zama dole a d’au mataki dan akan zumunci baze rasa ran d’ansa guda ba. Ba shiri ya shiga booking flight of return. 

  Wajajen k’arfe takwas na dare likita ya dawo ya duba Afzal sede har yanzu ba cigaban da aka samu hak’uri ya basu kan su bari zuwa gobe. Ummi kam ba aikinta se kuka, har da Daddy yazo dubata ya tafi bata bar kukan ba. Ran Daddy ya matuk’ar 6aci, ya sani duk hakan na faruwa ne saboda laifin daya ta6a aikatawa, alhak’inta ne ke binsa shiyasa Allah ya basa ‘ya gagararriya kamar Nazeefah. Oh Allah! Ko kallon Nazeefah da ke ta faman rantsuwa beyi ba ya fice. Sauk’a har k’asa tayi gun tana kuka me tsuma zuciya. 

  Wajajen k’arfe goma Mummy tace zata tafi, Ummi na jiran tafiyan Nazeefah amma shiru koda ta tambayeta se yaushe zata tafi kuwa tace mata ita anan zata kwana sede Ummi ta hanata bata son ko cikin dare idan Afzal d’in ya tashi ganin Nazeefah akansa kuma hakan ya sake haifar masa da wata rashin lafiyar dan su duk sun gama yarda cewa Nazeefah ce sanadin komai. Haka badon tana so ba aka sa driver ya dawo da ita gida, ko abinci ta kasa ci sallah kawai tayi ta kishingid’a jikin sallaya tana kuka har bacci yayi awon gaba da ita. 

  Washegari Mummy ta shirya breakfast ta kai wa Ummi haka Nazeefah ma, sede har izuwa wannan lokaci Afzal be farfad’o ba basu Ummi kad’ai ba harta shi kansa likitan ma jikinsa yayi sanyi har ya soma tunanin ko Afzal d’in ya shiga state of comma ne. Sultan da se a yau labari ke iskesa ne ya shirya ya taho. Ko daga jin batun yasan ba komai bane ze jawo wa abokin nasa ciwon zuciya banda tunanin Amal. Sosai ya tausayawa Afzal da yaga irin critical condition da yake ciki yayinda yake jin haushinsa kuma, ai dama seda ya fad’a masa ba inda zurfin ciki ze kaisa banda halak’a amman yak’i ji. Yana zaune a d’akin ne shida Ummi da Mummy Nazeefah tayi sallama zata shiga don ajiye masu basket na abincin ranan data dafa. 

  “Ban ce miki kar na sake ganin kin tako k’afar ki cikin d’akin nan ba? Duk abinda kikayi masa be isheki ba nan d’in ma sekin biyosa kin k’arasa sa?” Mummy ta kurarata. Magana ma ta kasa kawai maida k’ofan tayi ta fice ta nemi gu ta zauna ta shiga kuka, shin yaushe ne zasu amince akan cewa ba ita bace sanadin wannan rashin lafiya?

  Sultan da kansa ya d’aure ne ya juyo yana kallon Mummy da tayi maganan “Aunty me kuma had’in Nazeefah da condition na Afzal? Bade ita kuke zargi ba?”

  “Da wa kakeso a zarga idan ba ita ba Sultan? Abokin naka be ta6a baka labarin kalan zaman da sukayi da ita a gidan bane?” Ta tambayesa. 

  “Sure yana bani kawai de I don’t think itace ta janyo masa wannan ciwo besides ai zatto ma zunubi ne kamata yayi ku jira ya farfad’o ya sanar daku da bakinsa kafin ku hau tsagwamanta haka.”

  “Ko wa kakeso mu zarga? Idan ba Nazeefah ba to waye ne? Dan Allah ka sanar dani idan ma mutanen office ne I am ready to deal with them tell me Sultan” cewar Ummi. 

  “Ba mutanen office bane.”

  “Then waye ne?”

  “Nima bansani ba amma kam ba Nazeefah bace.”

  “Allah farfad’o da Afzal d’in koma wanene ze sanar dani” cewar Ummi had’e da cigaba da shafa gashin kansa. Sallama yayi musu akan yana zuwa ze dawo anjima. Yana fita ya kira numban Amal wanda ta d’auka bada dad’ewa ba. 

  “Assalamu alaikum.”

“Wa’alaikumus salam” ya amsa. 

  “Ya sultan ina yini?”

  “Lafiya ya kike? Kina gida?”

  “Eh lafiya?”

 “Ki jirani ina zuwa” batayi musu ba tace “Allah kawo ka” ta sauk’e wayan. Anya kuwa lafiya? Yau Ya Sultan ne bashida fara’a haka ko kad’an?? Numban Afzal data gaji da kira ne ta sake gwadawa sede kaman yadda take tsammani haka ya gama ringing be d’aga ba toh meke faruwa ne? In minutes like 30 sega Sultan ya iso k’ofan gidansu. Fitowa yayi ya mata waya kan gashi bata 6ata lokaci ba ta sanya hijabinta ta fito. 

  “Ya Sultan yau kaine a gidan namu?”

 “Eh Amal dalili ya kawo ni” ya sanar da ita straight forward. 

  “Toh ina jinka.”

  “Kin ko san Afzal ba shida lafiya yanzu haka as we speak? Yana kwance a gadon asibiti rai na a hannun Allah.”

  “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” tasa salati yayinda ta nemi duk wani nutsuwarta ta rasa. “Ka ce mey????” Ta tambaya bayan tsawon lokacin data d’auka. 

  “Afzal na gadon asibiti haka as we speak fighting for his life” ya sake nanata mata. Take idanunta suka ciko da hawaye ashe dalilin daya sa ko ta kira baya d’agawa kenan toh meya samesa? Meya samu yayanta? Innalillahi!

  “Ya Sultan dan Allah ka fad’a min wasa kake hatsari yayi ne? Meya samesa?”

  “Wasa kuma Amal? Ana wasa da rashin lafiya ne? Ko baki gwada layinsa bane tun jiya?”

  “Wallahi kona gwada baya d’agawa se nayi tunanin ko yayi fushi dani ne.”

  “Mey ya had’aku? Fad’a kukayi ne?”

  “Ya Sultan ni ba wannan ba meya samu Yaya? Hatsari yayi ne?”

  “Ko d’aya yasamu heart attack ne.”

  “Ciwon zuciya??” Ta nanata had’e da zaro idanunta waje. “Me ya had’a Yaya da ciwon zuciya Ya Sultan dan Allah kace wasa kake.”

  “Ba wannan a tsakanin mu Amal and bazan 6oye miki ba kece nan sanadin wannan rashin lafiya nasa.”

  “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un ni kuma Ya Sultan? Dan mey zaka ce nice sanadin rashin lafiyan Yaya bayan kasan nafi kowa damuwa da lafiyarsa da kuma farin cikinsa, dan Allah ka rufa mun asiri” kuka ta shiga yi sosai. 

  “Na k’aryata hakan Amal so kike kice har yanzu baki fahimce komai ba?”

  “Komai game da me fa?” 

  “Taya zakice har yanzun baki gane cewa Afzal na son ki ba? Tayaya Amal?” Wani irin sara kanta yayi mata yayinda jiri ya d’ibeta daba don Sultan da yayi saurin tareta ba da tuni ta sha k’asa, k’aryata zancensa ta shiga yi tana kad’a kai yayinda take kuka na hak’ik’a. 

  “Ya Sultan baka gane bane, baka gane ba Yaya ba sona yake ba. Yaya baze ta6a sona da wata manufan ba, dan Allah kabar fad’in haka.”

  “Dalili? Kibani k’wak’k’warar dalilin da ze hana Afzal sonki Amal, kin d’au duk hidimar nan da yake miki a banza ce? Ko mey yakeyi muddin ke kika kira bari yake and be at your service you think it shall go in vein just like that?”

  “No amma kuma idan har dagaske ne Yaya yana sona da ya sanar dani idan beyi hakan ba kuwa ko Papi ne ze samu ya fad’a mishi baku gane bane Yaya ba sona yake ba.”

  “Sosai yana da niyyan yin hakan sede baya son ya raba miki hankali ne daga karatu Amal, so yake se idan lokacin yayi ya sanar dake kwatsam se gashi kin samu wani har kun daidaita taya kike tsammanin zeji? Taya ciwon zuciya baze kama shi ba?”

  Salati kawai Amal ke ta nanatawa bayan nan ta kasa furta koda uffan. Meyasa bata gane cewa sonta Yaya yake ba?

  “Nide na fad’a miki kuma ina sa ran zaki d’au mataki ki ceto mana ran Afzal ke kad’ai keda ikon hakan.”

   Taya ya Ya Sultan? Ta tambayesa cikin kuka sosai “Ya za’ayi nayi hakan? So kake in je in samesa a matsayina na mace in ce masa ina sonsa bayan banji daga bakinsa shi yana sona ba?”

    “I’ve said my own amman duk abinda ya samu abokina bazan yafe miki ba.”

  “Ya Sultan ya kake magana haka? So kake in haukace in rasa raina? Kafi kowa sanin yadda farin cikin Yaya yake da matuk’ar muhimmancin a rayuwata. I’m willing to sacrifice everything for Yaya amma Ya Abdul fah? Meyasa Yaya be sanar dani tun wuri ba har ya bari soyayyan wani ya shiga zuciyana?”

  “Ban sani ba nima Amal, Afzal nada wani irin hali ko abu na damunsa bai son nunawa ko ni nan da nake miki wannan magana bawai shi Afzal d’in ya sameni ya fad’a min hakan bane, ni na karance sa har na gano hakan. Afzal na sonki Amal, idan har da zakiyi adalci kuma kema kin sani ba wanda ya kamanci soyayyar ki kaman shi. Rai ne kawai Afzal be d’auka ya baki ba, is about time kiyi repaying all the kind gestures da ya miki, nasan da ciwo amma ya zama dole ki rabu da Abdul naki kibawa Afzal soyayyar ki it is the only thing that can save his life.” Shiru tayi tana share hawayenta, “Shin bazan iya zuwa in duba sa ba? I want to see him, I want to see him so badly.”

  “Hakan zeyi wuya amma zanyi iya k’ok’ari na inga kin samu ganinsa.”

  “Are you free yanzu? Zaka iya kaini?”

  “Sure let’s go.” Asibitin suka koma inda ya barota acikin mota ya fito ya samu Ummi yake ce mata taje gida ta huta ze cigaba da kula da Afzal zuwa lokacinda zata dawo bata masa musu ba ta kira driver ya kaita gida. Dama ba Nazeefah ba Mummy don haka ya shigo da Amal ya tsaya daga bakin k’ofa yana guarding nasu. Rawa jikinta yake sosai yayinda ta k’arasa cikin d’akin nasa ta zauna kan kujerar dake gefen gadon nasa. Wani irin mumunar tausayinsa ne ya kamata, ina ma ace zata iya kar6e rashin lafiyan nasa ita tasha wahala a maimakonsa. Sam wannan rashin lafiya be kamace sa ba, “Yaya?” Ta kira sunansa a hankali. 

  “Yaya dagaske ne? Dan Allah ka tashi kace musu k’arya ne. Yaya in har abinda suke fad’a gaskiya ne meyasa baka sanar dani ba? Yaya kafi sanin kowa yadda nake sonka, I’ll sacrifice everything for your happiness mesa baka sanar dani da jimawa cewa wannan ne k’udurinka akaina ba har kabari na shigo da Ya Abdul cikin rayuwata? Kana tunanin da kaina zan gano hakan ne? Tabbas yaci ace na gane hakan amma banyi ba, I’m so sorry for every pain Yaya please forgive your Lily” tasa k’asan hijabinta tana share hawayenta. Tafi minti biyar zaune a gun tana aikin kuka akansa kawai taga alaman yayi blinking idonsa. 

  “Ya Sultan!” Ta k’wala masa kira ba shiri ya shigo ciki yana tambayarta ko lafiya. “Yaya ne yayi motsi get his doctor” a guje ya fice dan nemo likitan. “Yaya please open your eyes it’s me your Lily, I’m right here kaji? You can do this” kalamun kwantar da hankali tayita furta masa a hanakli ya shiga bud’e idon nasa har ya bud’esu duka had’e da sauk’esu akanta. 

  “Yaya you’re alive! You’re alive” tasa ihu tana share hawayen farin cikin dake sauk’o mata. Kallonta kawai yake amman ya kasa cewa komi ahaka ne har Sultan ya dawo da Dr’n Afzal inda ya masa wasu gwajin ya tabbatar da cewa condition nasa is stable sannan ya fice. 

   “Yaya baka gane ni bane? It’s me your Lily.” Maida kallonsa akan Sultan yayi idonsa suna d’auke da d’imbun tambayoyi gano hakan Sultan yayi saurin cewa “bari in kira Ummi ina zuwa” nan ya fice ya barsu su biyu a d’akin. 

  “Yaya?” Ta kirasa sede ina yak’i koda juyawa ya kalleta. “Yaya I’m sorry, I’m so sorry dan Allah ka juyo ka kalleni” nan ma shiru. “Yaya I’m so sorry dan Allah ka dena fushi dani kayi hak’uri” sede fa duk had’asa da Allahn da tayita yi yak’i koda kallonta. Haka ba yadda ta iya ta mik’e tabar masa d’akin. 

  “Ya haka?” Sultan daya ga yadda take kuka yayi saurin tambaya. 

  “Yaya yak’i ya kalleni balle ma yamin magana, Ya Sultan ban san ya zanyi ba dan Allah ka basa hak’uri.”

  “Yak’i ya miki magana kaman ya?”

  “I told you Yaya ba sona yake ba kune baku gane ba, I can’t do this anymore ni zan tafi kawai.”

  “Ah’ah ki tsaya tukuna” d’akin Afzal ya shiga ya zauna gefensa. 

  “Ya jikin naka?” Ya tambayesa. 

 “Meyasa ka kawo ta nan? Ina su Ummi?” Abinda ya soma cewa kenan. 

  “Abinda kad’ai zaka iya cewa kenan?Ka lek’a lahira ma bazaka zubar da wannan halin naka bako?”

  “Ba abinda na tambaya ba kenan ina Ummi? So kake su ganta? Mesa kake abu baka tunani ne kam Sultan? So kake se sun ganta sunyi zargin wani abun?”

  “Ai ko basuyi zargeta bama ni zan sanar dasu komai.”

  “Komai kaman ya?”

 “A tunaninka baki na zeyi shiru ne? Na riga na sanar da Amal gaskiyan al’amarin cewa kana sonta sauran idan su Ummi sun iso suma in fad’a musu haka kawai ina ji ina gani bazaka cigaba da punishing Nazeefah ba bayan ita batayi komai ba.”

  “Kayi meh kace?” Afzal ya tambayesa cike da tashin hankali yayinda zuciyansa ya tsinke da sauri ya rik’e wajen daya fara yi masa zafi. “Gara ka kwantar da hankalinka kabi komi a hankali dan idan wani attack d’in ya sake kamaka se lahira yanzu.”

   “Amma me na fad’a maka? Ni na fad’a maka ba son Amal nake ba don mey zaka sameta kace mata ina sonta? What is the meaning of this Sultan?”

  “Aww har yanzu bazaka yi admitting son da kake yi wa yarinyar nan ba?”

  “Sultan just get out idan har kasan suratan banza zaka cigaba dayi ka tashi ka bar min d’aki.”

  “Yanzu kai fisabilillahi baka tausayawa kanka da ita Nazeefah harda Amal d’inma? Wallahi girman kan nan ba inda ze kaika illa halaka Nazeefah bata san hawa ba bata san sauk’a ba aka d’aura mata laifin komai, Amal na da wanda takeso amman ya zama mata dole yanzu ta rabu dashi saboda kai duk hakan be isheka ba bazaka hak’ura ka amince da komai ba?”

  “Ni ban rok’eta tabar wanda take so ba Nazeefah kuwa ni bani na fad’awa su Ummi suyi blaming nata ba saboda haka nima kadena blaming d’ina.”

  “Da kyau” yace dashi had’e da mik’ewa yabar masa d’akin kafin ya fita har Amal ta tafi nemanta ya shiga yi chan sega Nazeefah shigowa. 

  “Ina yini?” ta gaishesa. 

  “Lafiya Nazeefah ya hidima?”

  “Alhamdulillah wai Afzal ya farfad’o?”

  “Eh yana ciki kije ki samesa.”

  “Toh ya naga kaman kana neman abu? Lafiya?”

  “Ko kinga wata yarinya da farin hijabi a hanya?”

  “Wata doguwa hakan nan?”

  “Eh ita.”

  “Ina shigowa naga tana tsaran napep.”

  “Toh shikenan thank you.” Da haka ta wuce d’akin Afzal knocking tayi sannan ta shige. Basket na abincin ta ajiye akan table sannan ta k’arasa ta zauna a gefensa. 

  “Afzal ya jikin naka?”

  “Da sauk’i” ya amsa k’asa-k’asa. 

  “Thank you for staying alive, Allah k’ara maka lafiya.”

  “Ameen thank you” ya amsa. 

  “In sa maka abinci?”

  “I’m not hungry.”

  “Afzal kaman ya baka jin yunwa? Rabonka da abinci tun yaushe? Dan Allah kayi hak’uri in sa maka koda kad’an ne kaji?”

  “Nace bana jin yunwa” bata sauraresa ba ta d’iba ta d’au ruwa tazo ta zauna gefensa. “Tashi ka zauna kaji? Please don’t say no.”

  “Afzal magana fa nake maka dan Allah kayi hak’uri ka tashi” kaman wanda baze motsa ba ya shiga mik’ewa sede hakan ma ya gagara k’arshe seda ta taimaka masa. Abincin ta d’aga ta mik’a masa “Zaka iya ci ko in baka?” Beko kalleta ba ya amshe plate d’in bayan da ya k’are wa abincin kallo ya maido da kallonsa a gareta. 

  “Afzal lafiya?” Ta tambayesa saidai still kallonta yake. “Afzal tunanin ko wani abun na sa maka aciki kake? Dan mey zan cutar da kai? Wallahi ba komai aciki ina iya d’ibawa inci a gaban ka idan baka yarda dani ba” ganin ta mik’e yayi saurin cewa “Don’t bother ki zauna” komowa tayi ta zauna yayin da ya shiga ci a hankali. 

  Murna kenan zan so kuga farin cikin daya bayyana a fuskan Nazeefah rabonta da tayi farin ciki irin na yau a rayuwarta har ta manta. Finally Afzal ya d’and’ana girkinta yau. Zama tayi tana kallonsa yayinda yake ci a hankali dududu beci ya kai rabi ba yace ya k’oshi. Ita a hakan ma ta gode. 

  “In had’a maka ruwa kayi alwala ko?” Nan ma kai zalla ya gyad’a mata bata kai da mik’ewa ba sega Ummi ta shigo. Da gudu tayi kansa had’e da rungumosa yayinda hawaye ya ciko mata a ido. 

  “Prince you’re back! Alhamdulillah! Alhamdulillah!” A hankali ta sakesa ta shiga shafa fuskansa “Prince na d’au zaka tafi ka barni.”

  “Come on Ummi, I’m here.”

  “I missed you.”

  “I missed you too bari inyi sallah.”

  “Haka fa kafin nan kaci abinci? Barin aika driver yaje ya siya maka don miyan kuka akayi a gida.”

  “Karki damu Nazeefah ta taho da abinci.” Ita bata ma lura da presence na Nazeefah ba seda ya ambaci sunanta. 

  “Nazeefah?” Ta juyo da mamaki tana kallonta. 

  “Na’am Ummi?”

  “Prince?” Ta juya tana kallonsa shima. 

  “Yes?” Ya amsa. 

  “Kana lafiya? Ko a kira ma likitan ka?”

  “Why wani abu ne?”

  “Prince mun d’au ai idan kaga Nazeefah ciwon naka ze tashi ke Nazeefah ba ance ki kiyayi shigowa d’akin nasa ba kar wani abu ya samesa” Shiru Nazeefah tayi dan ko bata san me zata ce ba, tsana k’iri-k’iri both mahaifiyarta da surikarta suke nuna mata. Idanunta ta d’ago a raunane tana kallon Afzal tana jiran jin ko zeyi magana dan shi kad’ai yake da ikon wanketa daga wannan daud’a da su Ummi suke ganinta da. 

  “Meyasa?” Ya tambayi Ummi a k’arshe. 

  “Prince meye silar ciwon nan naka? Ba Nazeefah bace?”

  “Waya ce muku itace?”

  “Prince mey kake fad’i wai kam?” Ta tsaya kallonsa da mamaki. 

 “Nazeefah batayi komai ba I’ll ask you to keep her away from this.” Tirk’ashi wai meke faruwa ne? Ummi ta tambayi kanta “Kaje kayi alwalan zamuyi magana idan Abbanka ya iso munyi waya dashi d’azu jirginsu ya tashi.” A nitse ya mik’e ya k’arisa bayin ya d’auro alwala kamin ya fito har Nazeefah ta shinfid’a masa sallaya. Sallolin daya rasa ya shiga ramawa. Ana cikin haka Mummy ta shigo itama suka gaisa bayan da ya idar d’in take sanar dashi abinda ke tafe da ita na cewa Daddy ya turota ne akan idan har ya ga baze iya ba da rashin hankalin Nazeefah ya sawwak’e mata kawai su koma gida yanzu tunda de tace ita bazatayi hankali ba. Kafin Afzal yayi magana Ummi ta rigasa. 

  “A’a shiko Alhaji ai ba haka akeyi ba, zama yakamata shi da Abban Afzal suyi da shi Afzal d’in kansa a dai-daita koma menene koba haka ba?”

  “Dan Allah kibar maganan nan Hajiya Mariam banason ganin ranan da za’ace ga ‘yata nan ta kashe d’an wani kuma idan aka cigaba da tafiya haka tabbas wataran Nazeefah zata aikata hakan tunda gashi ta d’au hanya har ta sanya masa ciwon zuciya.” Shiru Afzal da suke tsammanin zeyi magana yayi. “Afzal?” Ta kira sunansa yayinda da ya d’ago kai yana kallonta “Mey kace kai?”

   “Mummy ni Nazeefah bata yimun komai ba don haka bazan saketa ba kuma ina rok’anku da kudena blaming nata akan laifin da ba ita ta aikata ba” Wani irin sanyi Nazeefah ta jiyo a ranta bata tsamman Afzal ze kareta haka ba. 

  “Wani irin magana kake ne wai Prince? Idan ba Nazeefah ba toh waye?”

  “Ni ba wanda ya d’aura mun ciwo banda Allah, kuma na rungumi k’addara.”

  “Ya kake neman raina mana hankali ne kam Prince? Dama ansan ai lafiya da rashinsa daga Allah ne ko ka ta6a jin jinin mutum ya hau ciwon zuciya ya kamasa ba tare da tashin hankali ba? Wallahi to kar kayi magana Abbanka na nan tafe idan yazo se muga ko wannan silly answers d’in zaka basa Hajiya Fatsuma tashi in raka ki Afzal is not willing to talk.”

****

  Amal ce kwance akan katifarta se aikin kuka take, gabad’aya ta rasa meke mata dad’i tun dawowanta gida bata sake lek’a waje ba. Ba yadda Mami batayi da ita ba amman tak’i fad’a mata ainihin meke faruwa. Toh ma ta ina zata fara? Ta ina zata fara sanar da Ya Abdul wannan zance? Wayanta ta jawo ta shiga viewing pictures nasa da kuma nasu da suka d’auka tare, tana son shi tana son shi na sosai bata jin zata iya rabuwa dashi aman kuma ta d’ayan 6angaren bata son Sultan da shi kansa Afzal d’in da kuma duk wanda wannan labari ya iskesa suyi mata kallon butulu. Sedai har yanzu takasa amincewa da maganganun da Sultan ya sanar da ita, gashi abin haushi sun kasa dena yawo akanta. 

***

   Ba yadda Ummi batayi da Afzal ba akan cewa ya taho gida da ita amman yayi insisting yace shi fa Nazeefah ze bi. Haka nan suka komo gida tare ta tambayesa ko me yakeson ci. A karo na farko kam babu ya sanar da ita. Seda tayita had’a sa da Allah sannan yace indomie ma yayi. Ba tare da 6ata lokaci ba ta wuce kitchen ta shiga girka masa. Nan ya d’auko wayansa dake cikin wardrobe, gabad’aya gani yayi battery d’in yayi draining. Had’awa yayi bayan ya kawo wuta ya soma cin karo da sak’on Amal da sauri ya bud’e ya karanta kaman haka.  

  ‘Get well soon Yaya, my prayers are with you.’

  Duba lokacin da sak’on ya shigo yayi yaga wajajen k’arfe shida ta turo. Maida wayan yayi yayinda ya fad’a duniyan tunani. Yanzu da wannan shirmen da Sultan ya tafka masa da wani idon ze sake kallon Amal? 

  Washegari Abba ya turo driver akan ya taho da Afzal idan kuma jikin nasa baze iya barinsa ba shi da kansa yana iya tahowa su tattauna komai. Wanka yayi ya karya sannan suka fice. Suna is ya zarce parlourn Abba inda yaci karo da Sultan, take gabansa ya fad’i don mey za’a kira Sultan? Yana da tabbacin cewa aikin Ummi ne wannan. A nitse ya k’arisa d’akin ya zauna se kallon Sultan yake ko idonsu ze had’u yayi masa ido komin mey kar ya fad’i komai amman yadda kukasan gunki tun zaman Sultan ko kewaye-kewaye yak’i yi. Gaisawa sukayi da Abban yake tambayansa ya jiki sannan da Ummi bayan nan Abba yayi gyaran murya. 

  “Ina jinka Prince meya faru?”

  “Abba babu” ya amsa kansa a duke. 

  “Idan kun kasa jituwa da ita Nazeefan ne ai seka taho gida kamun bayani amfanin idan iyayenka suna raye kenan bawai ka tsaya kana bin abu a zuciya ba.”

  “Abba ni Nazeefah bata yimun komai ba.”

  “Sorry ban fahimce ka ba.”

  “Nazeefah has nothing to do with this Abba” ya sake nanatawa Ummi dake gefensa ji tayi wane ta hankad’esa don haushi ita ta rasa dalilin da yasa yake rufa mata asiri. 

 “Toh wanene?”

  “Babu.”

  “Nace wanene?” Abba ya sake tambayansa cikin tattausar murya. 

  “Abba matsala muka samu a office wanda nayita bi da zuciya shikenan.”

  “Prince d’ago kai ka kalleni” ba gardama yayi hakan “Yanzu ni zaka kalli cikin idanu na kayi mun k’arya wallahi sam wannan ba d’abi’ar ka bace I’m very disappointed in you.”

  “Abba kayi hak’uri.”

  “Sultan?”

  “Na’am Abba” ya amsa. 

  “Tabbas nasan kana sane da duk wani abinda ke faruwa tunda Afzal ba shida amini sama da kai I’ll ask you to tell me what is really going on idan ko kayi mun k’arya Allah na kallonka.” Shiru Sultan yayi yana nazarin sanar da Abba gaskiyan batun ne koko a’a. Amma ai dan abokinsa besan ciwon kansa ba doesn’t mean shima ya biye masa. 

  “Sultan magana nake maka.”

  “Abba a gaskiya ni ban san mey zahirin maganan ba don ko ni nan Afzal be ajiye ni ya sanar dani abinda ke damunsa ba sede in baka amsa base on yadda na karanci yanayin sa.”

  “Bismillah ina jinka.”

  “Akwai wannan yarinyar da Afzal keyi ma hidima wanda da zama yayi zama na soma ganin alamun son yarinyar a tattare da shi koda na gwada masa magananta akan cewa is about time ya sanar da ita k’udirinsa kuwa se abin ya koma fad’a ransa ya 6aci. Toh kwatsam kawai se mukaji yarinyan ta samu wanin da har sun dai-daita dashi sunyi nisa. A tunani na wannan ne dalilin daya jefa Afzal cikin wannan hali dan tun daga lokacin ban sake gane kansa ba ko office nasu naje acikin tunani nake tsintansa kullum.” Tunda Sultan ya soma bayanin Afzal ya dukar da kansa k’asa amman baze ta6a yafe masa wannan d’anyen aikin daya masa ba. 

  “Ko kasan yarinyar da kuma iyayenta?” Shiru Sultan yayi yana nazarin sanar dasu gaskiya koko a’a sarai ya sani idan yayi hakan Afzal na iya fushi dashi har abada don haka ya kad’a kai “Ban san komi akanta ba Abba banda hotunan ta da nake gani da a wayansa kafin ya goge.”

  “Shikenan Sultan nagode Allah sak’a maka da alheri kana iya tafiya.”

  “Ameen Abba, Ummi ni zan wuce.”

  “Mungode sosai Sultan ka gaida gida” yana ficewa Ummi ta maido da kallonta akan Afzal “Ai dama na sani nasan za ayi haka kai baka san ciwon kanka bane kake neman kai kanka ga halaka akan mace iyye? Macen da kana da tabbacin zata amince da k’udirinka muddin idan ka sanar da ita amman kak’i har wani can ya sace maka ita? Meye amfanin mu Afzal da bazaka zo ka sanar damu damuwanka ba?” Shiru yayi bece komai ba. 

  “Afzal?” Abba ya kirasa. 

  “Na’am” ya amsa. 

  “Wacece wannan yarinya?”

  “Abba ni fa ba wata yarinya ni kaina ban san a ina Sultan ya had’o wannan labari ba ya baku kaman yadda na fad’a maka matsala muka samu a office na kusan rasa aiki na shine nabi a zuciya.”

  “Nace wacece yarinyar?”

  “Abba I’m sorry amman kaman yadda na fad’a maka ba wata yarinya.”

  “Afzal wai meke damunka ne? Kai bakasan zurfin ciki na kai mutum ga halaka ba?”

  “Ya isa Hajiya Mariam bar shi tashi ka tafi Allah k’ara ma lafiya.”

  “Ameen nagode” yana kaiwa nan ya mik’e Ummi ce tabi bayansa tare da k’wala masa kira. 

  “Prince meke faruwa ne? Meya sameka? Prince idan baka sanar dani damuwanka ba mawa zakayi hakan? Wallahi koma wacece wannan yarinya da kakeso kasa zuciyanka a ruwan sanyi dan ka riga ka sameta just tell me wacece ka kuma bani address nata.”

  “Ummi nagode amman ya kamata ki gane cewa ba wata yarinya.”

“Da kyau Prince yau ka nuna min matsayina dake ba ni na tsuguna na haifeka ba dole ina tambayanka abu kana 6oye mun.”

  “Ummi please wani irin magana kuma kike?”

  “No ka tafi nagode” nan ta juya ta shiga tafiya duk kiran da Afzal keyi mata tak’i juyawa har ta k’arasa site nata. 

  Tunanin had’uwansa da Sultan kawai yake a dalilin mey ze fad’awasu Abba gaskiyan al’amarin?

   PAGE 1⃣7⃣

     Yadda yak’i kiran Amal ita ma haka bata sake kiransa ba iyaka sak’on da ta sake masa sending take tambayarsa ya jiki Allah k’ara lafiya. Anan d’inma k’in replying yayi. Kan Ummi ya samu shawo bayan wuyan da ya sha dan sosai tayi fushi da shi amman dukda hakan yak’i sanar da ita batun Amal se musantawa yake sam fa shi ba wata yarinya. Bayan tafiyansa Ummi ta kira Sultan take rok’ansa cewa idan har ya san gidansu yarinyar nan karya 6ata lokaci ya fad’a mata kar ya biye wa abokin sa amman sanin abinda hakan ke iya haifar wa tsakaninsa da amininsa ya busar da ido yace wa Ummi shi sam be sani ba ai idan da ya sani ko basu tambaya ba ze sanar da su a haka ya samu sukayi sallama. 

  Abba kuwa be sake yi takan Afzal ba tunda kusan sau uku yana tambayansa abu d’aya amman yak’i sanar dashi idan tayi tsami shi da kansa ze bud’a bakinsa ba se an rok’esa ba. Sau dayawa Ummi na bawa Abba hak’uri akan ya sake kiran Afzal yayi masa magana k’ila ya amince ya fad’a musu damuwansa amman ina shifa Abba yace ba ruwansa again. 

    Kwana biyu Afzal ya d’auka sannan ya warware ya soma fita office, da safe Nazeefah ta tashi ta had’a mishi breakfast harda coffeen sa a flask da ze tafi da shi, yau kam har da godiya Afzal yayi mata sannan ya fice. Ba k’aramin dad’in hakan taji ba bayan tafiyansa itama ta shirya ta wuce school. A makaranta ne Ummi ta kirata bayan sun gaisa take bata hak’uri game da abinda tayi mata, sosai Nazeefah ta nuna mata komai ya riga ya wuce saboda ko itace a shoes na Ummi abinda zata aikata kenan kawai abinda bata ji dad’insa ba shine damar da ita da Mummy suka k’i bata tayi bayanin kanta. 

   Afzal ne zaune a office gabad’aya hankalinsa ya duk’ufa akan waya yana kallon hoton Amal Sultan yayi knocking bisa k’ofan, kafin yace ze kimtsa har shi Sultan d’in ya sa kai. Da wuri Afzal ya tura wayan nasa k’ark’ashin drawer sede Sultan ya riga ya gansa, kai kawai ya kad’a ya k’arisa ciki. Afzal kam ya sha mamakin ganin Sultan. Zama yayi akan kujera tare da mik’a wa Afzal hannu da ikon Allah Afzal ya kar6a suka gaisa. 

  “Ya jikin naka?” Ya tambayesa. 

  “Da sauk’i I’m fit.”

  “Ma shaa Allah Amal ce ta turoni dama.”

  “Da mey?” Yayi saurin tambaya. Ledan dake ajiye a gefen k’afansa ya d’ago tare da turawa Afzal ta 6angarensa “She’s wishing you a speedy recovery.” Amsa yayi ba musu ya sa a fridge bayan daya lek’a ciki yaga Aldeb ne kaca-kaca da zo60. “I’ll call her up.”

 “Alright ni zan wuce.” Shiru Afzal yayi masa har ya kai ga bakin k’ofa sannan ya kira sunansa, hakan ya sanya sa tsayawa chak. 

  “Thank you” ya furta. 

  “You’re welcome” ya amsa sannan ya fice had’e da ja masa k’ofar. Wayansa ya zaro yayi scrolling kan contact na Amal tare da dialing bada dad’ewa ba se gashi ta d’aga sede sa6anin yadda ta saba kiran sunansa anytime ya kirata yau d’in batayi ba ko sallama ma tak’iyi shi da kansa yayi gyaran murya yace, “Assalamu alaikum” da shirun yayi yawa. 

  “Wa’alaikumus salam Yaya ina kwana?”

  “Lafiya k’alau ya kike?”

  “I’m good ya jiki?”

  “Alhamdulillah yanzu Sultan ya iso min da sak’onki nagode ko?”

  “Ba komai Yaya Allah k’ara sauk’i.” Sede daga yadda take mar magana sama-sama yasan tana fushi dashi kuma yes ya sani she has every single right to act this way. 

  “Ya school yau baki fita bane?”

  “Se anjima banida early morning lectures.”

  “Alright toh.”

  “Toh se anjima” wow ya numfasa a hankali yau har Amal ce ke neman kashe waya a kansa? “Wait” yayi saurin cewa. 

 “Yes wani abu ne?”

  “I’m sorry kinji?”

  “Ni baka mun komai ba Yaya.”

 “Na sani Lily you don’t deserve any of the attitude I’ve been giving you and I’m sorry.”

  “Ba komai Yaya ya wuce.”

  “Ki gaida su Mami toh.”

  “Zasuji” da haka ta katse wayar. Tunani ya shiga yi shi kad’ansa. 

*****

  Haka nan tafiyar ta cigaba ba laifi Afzal ya soma sakewa da Nazeefah sukan zauna a parlour suyi kallon sports ko film tare har abinci ma sun soma ci tare akan dining table. Nazeefah can’t ask for more a duk lokacin da suke tare da Afzal ji take like she’s the most happiest girl on earth, tana son shi, tana sonshi sosai ba tantama akan hakan. Da kansa yau Asabar bayan sallan La’asr yayi tunanin zuwa gun Amal dan gabad’aya ta fita harkansa ko kiransa bata sake ba har yau, abinda ya mata a asibitin ba k’ramin 6ata mata rai yayi ba tace ta yafe amman bazata iya mancewa da shi ba. Shiri yayi tsaf ya wuce gidansu wanda baze iya tuna rabonsa da yin hakan ba, sosai yayi missing nata baze ma iya kwatantawa ba sede isansa ya tarar da exactly motan ranan wanda yake da tabbacin motan Ya Abdul ne. Daga bakin corner’n ya tsaya yayinda gabansa yayi wani irin mumunan fad’i lokacin da ya hango kan Amal cikin motan be 6ata lokaci ba ya juya. Tuk’i yake amman gabad’aya hankalinsa bai kan hanyan shi kansa besan inda ya dosa ba. Zuciyarsa ce ta soma yi masa k’ona yayinda idanunsa suka shiga kakkafewa dan azaba kafin ya hankara kawai ya jisa jikin pole. Da sauri mutanen kusa suka afka kansa akayi saurin kaisa asibiti sannan aka shiga neman ‘yan uwansa. Abba aka samu aka kira ko daya ji beyi mamaki ba dama yasani nan kusa se abu makamancin hakan ya sake faruwa. Kafin ace mey labari ya iske ‘yan uwa gabad’aya nan da nan shi da Ummi suka yo asibitin itama Nazeefah bata 6ata lokaci ba ta wuce a chan sukaje suka had’e. Bayan likita ya fito suka duk’ufa sukayi kansa suna tambayansa ya jikin Afzal d’in. 

  “Idan ban manta ba this was the patient I treated some weeks ago right?” Ya tambayesu. Ummi ce tayi saurin gyad’a kai “Yes Dr.”

  “Haba Hajiya haba! Taya kuke neman halaka d’anku? Shin baku san idan ya cigaba da samun arrest d’innan wataran zuciyar tana iya mutuwa tak’i tashi gabad’aya ba? Yaci ace kun gano inda matsalar take kun magance ta tun wuri don bazan 6oye maku ba rayuwan d’anku na cikin hatsari” ya fayyace masu. Sosai Nazeefah ta shiga duhu toh meke jawo masa tsinkewan zuciyan ne? Gashi nan de a gida bazaka ta6a ganinsa cikin damuwa ba. Kode shida mutanen sa ne na office? Ta tambayi kanta sede bata da amsa.  

  “Yanzu ya jikin nasa?” Abba ya tambaya. 

  “Mude munyi abinda zamu iya sauran mun bar wa Allah.”

  “Dr dan Allah do what you can to save him.”

 “In shaa Allahu excuse me.” Ummi da Nazeefah ne suka shiga ganinsa yayin da Abba ya ke6e a waje yana mamakin halin da Afzal ke neman jefa kansa. Wajajen k’arfe tara na dare Sultan yazo dubansa shi kad’ai ne a lokacin yana mik’e kan gadon nasa da hannunsa a d’aure inda ya samu targad’e sanadin accident da yayi encountering d’azu. 

  “Ya jikin?” Kai zallah ya gyad’a masa nufin da sauk’i. 

  “Afzal me kake shirin yima kanka? It has to stop idan kai baka valuing life naka mu munayi dan Allah ka yayyafa wa zuciyarka ruwan sanyi ka sauk’e girman kan nan ka sanar da Amal kana sonta. Don kayi hakan doesn’t mean zaka mutu amman rik’ewan da kakeyin shine ze iya kashe ka.”

  “So be it idan na mutu Sultan but gaskiya d’aya ce it’s too late for everything.”

  “It’s not Afzal it’s never too late.” Kai ya kad’a da nufin a’a “Amal ta riga tayi mun nisa bazan iya samunta ba.”

  “Ka bani go ahead kawai in sanar da Abba address nata ina da tabbacin su Abba bazasu hak’ura ba har se idan sun shawo kanta da iyayenta ta kasance taka.”

   “Ban tsamman hakan is possible there’s no point of telling Abba and Ummi about her, tana son Abdul bazata iya rabuwa dashi saboda ni ba.”

  “Haka kake gani?”

  “Haka yake I went to visit her d’azu ne ko jiya ne bazan iya tunawa ba achan na gansu tare a motanshi, tana son shi Sultan, da k’yar zata iya yafe sonsa ma wani koda kuwa mutumin ya kasance ni ne.”

  “Toh yanzu ya kenan? Kana nufin ba matakin da zaka iya d’auka?”

  “Babu tunda bata sona I can’t force her into loving me.”

  “Ya kake magana kaman ka sameta kace mata kana sonta tak’i ka ne? Fa Amal bata ma san kana sonta ba wallahi bata sani ba.”

  “Toh what difference will it make koda ta sanin?”

 “What if I tell you itama Amal d’in tana sonka?”

  “Da kace ka sanar da ita ranan, dagaske kake?”

  “Yes Afzal bazan iya juran ganinka a haka ba so I told her you love her.”

  “Mey tace?”

  “Ta kasa yarda amman bata bud’i baki kuma tace bazata iya sonka ba.”

    “Just let her be there’s nothing more I can do.”

 “Kai ke da abunyi Afzal kuma har yanzu ina fad’a maka kana da daman mallakar Amal saboda ba wanda ya cancanci soyayyarta kaman ka.”

 “How?? Dan ina mata hidima shikenan se ya zamanto dole ta soni?”

  “Ba haka nake nufi ba Triple A ina nufin a tsakaninka da Abdul yake kowaye, kai ka dubi k’aranchin shekarunta ne dakuma karatunta dalilin da yasa kaja baya kenan kak’i furta mata k’udirinka ko ba haka ba? Kafi son se karatun nata yayi nisa right?” Kai ya gyad’a a hankali yana mey sauraronsa. “Toh shikuma Abdul d’in be damu da ta cigaba da karatun nata ba koko a’a shi burinsa kawai ya mallaketa ne ko anan aka zauna aka duba ansan wa yafi wani kaifin tunani da kuma wanda ya cancani soyayyarta. Ka riga Abdul saninta, ka riga Abdul fata sonta saboda haka Amal taka ce ba tasa ba, ka sameta ka fad’a mata k’udrinka Afzal ina da tabbacin cewa Amal bazata yi turning naka down ba.”

  “Ka mance da ita kawai Sultan.”

  “Idan nayi kai bazaka iya ba Afzal, Amal ta riga ta zama jinin jikinka bazaka iya rayuwa ba ita ba.”

  “Don’t tell Abba anything about her please Sultan.”

  “Afzal-“

  “Dan Allah nace maka komin yaya ne kar ka sanar da shi komai.”

  “Haka kakeso ka cigaba da zama da wannan ciwo har seta kasheka tukun?”

  “Yafiye mun da inyi forcing Amal lallai-lallai seta soni.”

  “Shikenan Allah k’ara ma lafiya.”

  “Ameen thank you.”

 “Toh ni zan wuce” yayi maganan had’e da mik’ewa. “Sena dawo gobe Ummah ma gobe zata shigo tace.”

  “Allah ya kaimu kace ina gaisheta” da haka ya fice ya ja mishi k’ofan. Sallama yayi wasu Abba sannan yayi tafiyarsa.  

  Washegari shi da Ummansa suka dawo kaman yadda ya fad’a. Bayan sun duba Afzal sun fito Abba ya buk’aci Sultan da ya tsaya don haka Ummah ma ta tsaya jiransa. 

  “Hajiya Aisha?” Ya kirata. 

 “Na’am Alhj” ta amsa “Zamu wuce.”

  “Mungode sosai Allah ya biya amman kafin nan I want to have a word with you.”

  “Toh Alhj ina jinka.”

  “Bismillah kizo ki zauna” ba gardama ta k’arisa gefen Ummi ta zauna. Gyaran murya Abba yayi sannan yace, “Ko ban tambaya ba Sultan nasan kasan gidansu yarinyar nan da take bawa Afzal wuya, ka dubi girman Allah da halin da yaron nan ke neman jefa kansa  ka kaini gidansu in samu iyayenta asan nayi. Idan shi baida wayo besan ciwon kansa ba ai kai a matsayinka na abokinsa kasan hakan ko ba haka ba?”

  “Wai Alhj kana nufin Sultan yana sane da komi yak’i yin magana?”

  “Haka nake zato Hajiya shiyasa nakeson a matsayinki na mahaifiyarsa ki rok’esa kisa baki ya bamu had’in kai mu ceto ran d’an nan baza mu biye masa ba.”

  “Sultan?”

  “Na’am Ummah.”

 “Yanzu kana sane da komai amman ka gwammace kayi shiru saboda rashin lafiyan abokin naka be dame ka ba?”

  “Wallahi Ummah ba haka bane Abba kayi hak’uri nake ganin nafi kowa damuwa da halin da Afzal ke ciki musamman ni dana san kalan hidiman da yake yima yarinyar nan, nauyin makarantarta gabad’aya ya d’auke wa iyayenta. Duk abinda ya dace ayi Afzal nayi mata amman ya furta mata k’udirinsa ya kasa wai sede ita ta gano hakan da kanta ita kuma ta kasa, nayi-nayi dashi abun ya gagara kuma ya had’ani da Allah kar in sanar daku komai akanta komin yaya ne.”

  “Toh kuma seka biye masa ne Sultan? Bakaji me likitansa yace ba? The more yake samun attack d’in wataran zuciyan na bugawa gabad’aya ta daina aiki shikenan kuma k’arshensa kenan ai kamata yayi tun kan maganan yayi nisa haka kazo ka sameni ka fad’a mun abinde ake ciki wallahi banida labari se yau” cewar Ummi. “Meye sunan yarinyar?”

  “Amal” ya amsa. 

  “Amal?” Ta nanata, “Bade Amal da na ke ji a bakinsa ba? Yo Alhj ai nasan yarinyar mun sha gaisawa da ita ta wayan Prince.”

  “Kinsanta fa kikace?” Abba ya tambaya da mamaki. 

  “Ban ta6a ganinta ba amman muna waya itace me kawo mana Aldeb me dad’in nan amman Afzal anyi bahon d’a wallahi yanzu yarinyar nan dake sonsa d’inne ya kasa tunkararta ya fad’a mata yana sonta har abun yayi nisa haka?”

  “Wallahi Ummi bakiga fad’an dana rink’a yi masa ba amman yak’i jina shine kawai na hak’ura na barsa in ga iya gudun ruwansa.”

  “Ita yanzu yarinyar tasan yana sonta ne?” Abba ya tambaya. 

  “Bata sani ba Abba nine nayi gwanintan gaya mata.”

  “Mey tace?”

  “Tak’i yarda sam har kuka tayi mun da hawaye wai sharri nakeyi wa shi Afzal d’in take cewa idan da har dagaske ne ai da ze sameta ya fad’a mata kokuwa iyayenta.”

  “Tabbas tayi gaskiya” Ummah tace. 

  “Yanzu tashi ka kaini gidan nasu” cewar Ummi “Kai Alhj ba seka je ba tunda na riga nasan yarinyar zanyi mata magana in shaa Allahu za’a dace dan idan har itace Amal d’in kaman yadda Sultan ya fad’a toh yarinyar bata da matsala.”

  “Toh Allah kare” basu kai ga mik’ewa ba sega Nazeefah ta shigo da basket na abinci rik’e a hannunta, binsu duka tayi da gaisuwa sannan take tambayarsu ina zasu bayan ga abinci nan ta kawo. 

  “Ermm..” Ummi ta shiga neman dalili “Zan rakasu ne nan in wuce gida in watsa ruwa kiyi sauri ki kai wa Afzal d’in kar yaji yunwa.”

  “Toh Allah ya kare” nan ta zarce d’akin Afzal yayinda su kuma suka fice. Sauk’e Umma Sultan yayi sannan shida Ummi suka k’arisa gidansu Amal. Waya yayi mata akan cewa ta fito bayan ta fito ya sauk’o daga motan ya sameta inda suka gaisa. 

  “Ya Yaya yake? Ya jikin nasa?”

  “Jiki ya sake tashi ai yanzu haka ma yana asibiti.”

  “Innalillahi wallahi banida labari, tun yaushe?”

  “Jiya bayan da yabar nan.”  

  “Nan kuma?” Ta tambayesa cike da rashin fahimta “Yaya bezo nan bafa jiya.”

  “Yazo kede baki gansa ba amman shi ya ganki.”

  “Anya kuwa Ya Sultan? Da yaushe?”

  “Sosai kuwa lokacin da kuke tare da Abdul se be k’arisa ba ya juya. Bisa yadda ciwonsa ya tashi yayi hatsari a hanya amman da sauk’i targad’e kad’ai ya samu.” Mutuwa sosai jikin Amal yayi gun ta ma kasa cewa komai se chan muryarta ta dawo mata. 

  “Ya Sultan-“

  “Ga Umminsa nan acikin mota tazo kuyi magana.” Wani irin har6awa zuciyarta tayi, yanzu take gaskata zancen Falmata, Ya Abdul, Maamah da kuma shi kansa Ya Sultan d’in. Sede kanta ya d’aure, meyasa Yaya ya kasa sanar da ita k’udurinsa akanta? Meyasa yay ta wahalar da kansa akanta? Ko dan bata kai ya furta mata kalaman so bane? Well tasani Yaya ba tsarinta bane amman ai da ko Papi ne ya samu ya sanar da shi, da duk hakan be faru ba. Yanzu ba wannan ba, shin ina yake son tasa soyayyar Ya Abdul nata? 

  “Bismillah ki shiga motar” kai ta shiga kad’a masa da nufin a’a. 

  “Ya Sultan dan Allah ka rufa mun asiri wallahi ni ba nice sanadin halin da Yaya ke ciki, ban san Yaya so na yake ba wallahi da na gano hakan bazan ma fara kula Ya Abdul ba koda kuwa ace be furta yana so na ba please karka had’ani da Ummi.”

  “Calm down Amal tazo ne ta nemi alfarma gunki ba da niyyan tashin hankali ba ki k’arisa ciki tana jirarki” sede ina Amal ta kasa gabad’aya ta rud’e k’arshe seda Ummin ce ta fito da kanta. Bakinta na rawa ta tsuguna ta gaishe da Ummi sannan ta d’agata ta share mata hawyenta ta jata izuwa wani benchi suka zauna. 

  “Baki gane ko ni wace ba ko ‘yata?”

  “Ummin Afzal?” Kai Ummi ta gyad’a mata. “Ya jikin nasa?” Ta tambaya a hankali. 

  “Da sauk’i Alhamdulillah nasan kina mamakin gani na aban haka ba notice ko?” Nan ma kai ta gyad’a a nitse. “Taimako nake nema koma ince alfarma don shi yafi dacewa da k’udurin da nake tattare da shi. Zan iya samu?” Shirun da tayi ya bawa Ummi go ahead. 

  “Amal ran Afzal na cikin hatsari, likitansa yace idan ya cigaba da samun attack wataran yana iya rasa ransa gabad’aya kuma ke kad’ai keda ikon ceto mana ransa.”

  “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un” ta furta yayinda idanunta keta kan cikowa da hawaye. 

  “Kinji Mama na? Nasan da wuya da ciwo da kuma zafi amman dan Allah ki amince ki auri Afzal ki cetosa daga cikin wannan halin da ya fad’a” wani irin mumunan fad’i gaban Amal yayi. Aure gabad’aya? What if she’s not ready? What of Ya Abdul? Shi anyi masa adalci kenan? 

  “Amal baki ce komai ba” Ummi tayi magana bayan shirun da Amal tayi. Baki na kakkarwa tace, “Ummi ban san me zance ba, ina son Yaya, banida kaman shi ban ta6a neman abu gunsa na rasa ba, komi nakeso yana mun, baya wasa da sha’ani na, na d’aukesa a matsayin wa na babba wanda nake da burin zama big aunty ga yaransa not that ni in kasance matarsa, bazan iya auran Yaya ba.”

  “I know how it feels Amal ko ni nan da kike gani banso aure na da Abban Afzal ba, ba nice mahaifiyarsa ba. Ya ta ce mahaifiyarsa, ya ta na k’ut-k’ut mutuwa tayi mana k’atutuwa gashi lokacin Afzal na d’an jariri ko wata be kai ba. Dole aka sani rabuwa da masoyina aka aura min mijin ya ta imagine how difficult it must be for me amman hakan na hak’ura na rungumi k’addara look at where I am today, Abban Afzal shine sanyin idanu na bana jin zan iya rayuwa ba shi. Kema idan kika hak’ura komi me wucewa ne kinsan halin Afzal ba sena irga miki ba muddin yana son abu yana iya k’ok’arinsa yaga ya adana abun ya kuma kula dashi, Afzal will never disrespect or take you for granted dan Allah kiyi la’akari da halin nan da yake ciki ki amince Amal.”

  “Ummi ni idan ta nine bani da matsala, I can sacrifice the entire world for Yaya, zan iya yafe farin cikina saboda na Yaya because he deserves it and kamar yadda kika fad’a nasan Yaya baze ta6a walak’anta ni ba matsalar ba daga ni bace.”

  “Daga ina ne toh Mama na?”

  “Ya Abdul” ta numfasa. 

  “Waye shi?””

 “Shine wanda muke tare da shi, wanda yake da burin mallakata kaman yadda nima nake da burin kasancewa da shi. Ya zanyi? Ta ya kukeson in fara sanar da shi wannan labari? Bazan iya ba his last girlfriend cheated on him nima bazan iya masa hakan ba, Allah ma seya tambayeni” tasa kuka.

  “Shhh!” Ummi ta rungumota tana bata hak’uri “This is not called cheating my dear, ba da son ranki zaki rabu da shi ba and I know, na sani Afzal yayi kuskure amma bazamu iya maida hannun agogo baya ba all we can do now is to make things right. In har Abdul nakin na da tausayi ze fahimci halin da Afzal ke ciki ya yafe son da yake miki masa, Amal bana son in rasa d’ana.”

   “In shaa Allah ba zaki rasa sa ba Ummi.” 

  “Toh ki amince ki aure sa.”

  “Ummi I’m not the one to decide like I told you zan iya yafe farin cikina saboda na Yaya idan Ya Abdul ze iya hak’ura nasan iyaye na ma basu da matsala dan Yaya kaman d’an gida yake  problem d’in kawai Ya Abdul ne.”

  “A’ina ne gidansu ni da Abban Afzal muje muyi musu bayanin halin da ake ciki.”

  “Yana nan Polo.”

  “Zan iya samun layin wayanshi?” Kai ta gyad’a ta d’ago wayanta takai kan contact d’in sannan ta mik’a mata nan take ta kofe a wayarta. “Nagode sosai Amal, thank you so much.” Nan ma kai zalla ta gyad’a “Zan iya komawa ciki?”

  “Sosai mamana ki gaishe Umminki idan kin shiga ina sauri ne da na tsaya mun gaisa.”

  “Bakomai zataji” sallama tayi wa Sultan sannan ta wuce ciki direct se d’akinta. Kuka kawai ta shiga yi a tunaninta shi ze iya magance mata wannan musiba. Wannan wace irin k’addara ce da se an rabaka da masoyinka? Taya zata fara kallon idanun Yaya da wani manufa? Taya zata fara zaman aure da mutumin da ta d’aukesa a matsayin wanta na jini? This’s so wrong bazata iya ba. Meyasa Yaya ya jata jiki haka bayan yasan da wannan manufan a zuciyansa? Oh Allah ga ni gareka. 

**** A gida Sultan ya sauk’e Ummi nan da nan ta samu Abba ta sanar da shi yadda sukayi da Amal. Amsan numban Abdul d’in yayi akan shi zeyi masa magana ko gobe se suje gidan nasu. Har a nan Afzal dake asibiti be san meke faruwa ba, shi de se duba wayansa yake ko zega sak’on Amal tunda daman ta daina kiransa yanzu amman sak’on ma yau babu. Amal nata kanta ko tunawa da shi batayi ba. Wajajen k’arfe goma Ya Abdul ya kirata. Share hawayenta tayi ta gyara muryarta gudun wai kar ya gane kuka take sannan ta d’aga. 

  “My Baby” ya soma da cewa. 

  “My Ya Abdul” ta amsa “Ina yini?”

  “Lafiya ya kike? Ya school?”

  “Alhamdulillah ya office? I missed you.”

  “Alhamdulillah I missed you more my baby.”

  “Shine baka zo ba?”

  “Aiki ne ya rik’eni Baby har ranan sunday ma ban tsira ba.”

  “Ya suke wahalar min da Baby na hakane kam?”

  “Karki damu wahalan is worth it, atleast it comes with money kinga se nayita tarawa in auran mu yazo muyi gaggaruman celebration me hashtag irin na Instagram” dariya sosai ya sata dukda cewan bata mood d’in. 

  “Ko ba haka ba?” 

  “Hakane” ta ce dashi duk da cewan tasan idan ba wani ikon Allahn ba bazata iya kasancewa da Ya Abdul ba. 

  “Ya naji muryan ki k’asa-k’asa haka Baby lafiya?”

  “Lafiya Ya Abdul mura nakeyi.”

  “Shine baki fad’amun ba ni da nace ko cizo sauro ya miki you should call and tell me.” Nan ma bata da niyyan yin dariya amma seda ya sanya ta yi. “I’m sorry forgive your Baby.”

  “Baby ta shirya shan pepper soup gobe se muran ya sauk’a gabad’aya.”

  “There’s no need for that ina shan magani.”

  “Nifa na fad’a miki sauran inzo kik’i fitowa har cikin d’akinki zan shigo in fito dake.”

  “D’ankaren nauyi ne da ni fa bazaka iya ba.”

  “Niko d’ankaren k’arfi ne dani ba abinda bana iya d’agawa.”

  “Toh shikenan da-” se kuma tayi shiru. Haka kawai taji kar tayi saurin sanar dashi abinda ke faruwa tana sa ran wani mu’ujizan ze faru ya zamanto Afzal ya warke ba se an raba ta da masoyinta ba. 

  “Ya kikayi shiru?” Yayi saurin tambaya. 

 “Babu.”

  “A’a fad’i de.”

  “Allah babu.”

  “Baby so kike in taho da bulala gobe ko?”

  “Kuma seka zaneni?” Ta wani zum6uro baki. 

  “Toh tell me menene?”

  “Dagaske babu.”

  “Kinga irin taurin kan naki da nakeso ba? Amal I can’t wait to own you, ki bani go ahead amma kink’i kullum kice ke a’a it’s almost getting to a year.”

  “Kai Babe kai kuma harda zugau 5 months ne fa.”

  “6 ne and it still makes no difference ni ko formal gaisuwa ne azo ayi su Mami de su san sunyi in law.”

  “Ya Abdul I’m sorry” kawai seta rushe da kuka. 

 “Subhanallahi wani abun ne na fad’a? Dan Allah kibar kukan I take it back.” Katse wayar tayi yayinda kukan yaci k’arfinta ta barsa yana ta faman ‘hello? Hello?’ Sosai kan sa ya d’aure ya rasa mene ya fad’a da ze sanya ta kuka haka kode batun turowan da yace zeyin ne? Shikam wasa yake mata he can wait for as long as it takes inde akan Amal ne har se idan ta amince ya turon. Take ya shiga kiran layin tan sede tana gani amman ta kasa d’agawa don kuka. Gajiya da trying layintan yayi kawai ya kira Maamah a waya da ta zo site nasa yanzun yana jiranta. Bata 6ata lokaci ba ta iso take tambayar sa ko lafiya. 

  “Ina wayanki?” Ba gardama ta mik’a masa. Numban Amal ya d’ura ya kira nan ma har ya tsinke bata d’aga ba se a karo na biyu. 

  “Amal I’m sorry” taji muryan Ya Abdul kafin tace zata kashe yayi saurin cewa “Please don’t hang up” hak kawai kuma ta fasa. “Amal abinda na fad’a ne ya 6ata miki rai?” Kai ta kad’a wane yana gabanta “Amal I was only joking dan Allah kiyi hak’uri.”

  “Ya Abdul ba kai bane” ta furta cikin tsananin kuka. 

  “Toh waye ne?”

  “Babu.”

  “Kina kuka haka kice mun babu Amal? please tell me ko so kike in fito cikin daren nan in samu su Mami?”

  “Please don’t.”

  “Then tell me.”

  “Ya Abdul I’m sorry I’m so sorry.”

  “Amal please stop.”

  “Ya Abdul no matter what happens ka sani ina sonka, you’re my first love and I shall die with your love here in my heart. I’ve loved you since day one and I shall continue to love you forever, you’ll always remain close here to my heart please don’t forget this.” Sosai ta sanyasa cikin rud’ani. 

  “I know Amal but why the sudden confessions? Meya faru? Please talk to me.” Ya buk’ata cike da tashin hankali. 

  “Please forgive me seda safe.”

  “Amal wait!” Saidai har ta kashe wayan. Hankalinsa ya matuk’ar tashi, ba shi kad’ai ba harta Maamah data kasa fahimtan meke faruwa. 

  “Ya Abdul meke faruwa?”

  “Maamah I don’t know d’auko mun key’n mota na.”

 “Kaje ina?” Ta tambaya da mamaki.  

  “Gidansu Amal.”

  “Ya Abdul shin baka san k’arfe nawa bane yanzun? Dubi pass 10 fa.”

  “I don’t care Amal na cikin damuwa get my car key for me.”

  “Toh iyayenta zaka je ka samu ko wa?”

  “I don’t care I just want to see her and make her feel okay.”

  “Ya Abdul dan Allah ka kwantar da hankalinka kayi hak’uri ka bari zuwa gobe ni ma zan raka ka muje muji meke faruwa amman fita cikin daren nan is not a good idea.”

  “Maamah baki ji yadda take kuka bane?”

  “Naji gobe in shaa Allah zamuje mu dubata dan Allah ka kwantar da hankalinka” hak’uri tayita basa da k’yar hankalinsa ya d’an kwanta ya amince se goben zasu je su dubata. Sede kaman yadda Amal tayi kwana zaune tana kuka tana tuna rabuwanta da Ya Abdul, shima haka Ya Abdul d’in yayi kwana zaune yana tunanin halin da Amal tasa take ciki. Ji yake kaman gari baze waye ba.

   PAGE 1⃣8⃣

  ****

   “Alhj?” Ummi dake zaune a kan gado ta kirasa. 

  “Na’am” ya amsa yana me karkato da kallonsa a gareta. 

  “Nace ba ina laifin mu fara samun iyayen ita Amal d’in kafin mu nemi Abdul nake ga hakan ze fi fasali.”

  “Ko meyasa kika ce haka?”

  “A tunani na hakan ze fi tunda de ita Amal da bakinta tace mun Prince kaman d’an gida yake a gurinsu and kaga ze fi sauk’i mana ma idan har iyayen nata ne zasu sanar da Abdul d’in halin da ake ciki zefi d’aukan maganan shima da muhimmanci.”

   “You have a point.”

  “Thank you so mey kace?”

  “We’ll do it your way gobe in shaa Allahu se muje gidansu Amal d’in.”

  “Yauwa toh Allah kaimu.”

  “Ameen” kammala abinda yake yayi sannan ya k’ariso ya kwanta tare da kashe masu wutan d’akin. 

 Gari na wayewa wajajen k’arfe goma Abdul yasa Maamah a gaba suka wuce gidan su Amal. Kiranta ya tayi amman tak’i d’aga wayar, haka ma da ya gwada da lamban Maamah still tak’i picking don haka ya buk’aci Maamah da ta shiga ta tabbatar masu meke faruwa. Shigan Maamah taci karo da Mami se suratai take ita kad’ai da ta kasa kunne kuwa seta gano regarding Amal ne tana cewa “yarinya tun jiya ake tambayarki meke damunki amman kink’i kiyi magana se aukin kuka ki tayi” 

   “Assalamu Alaikum” tayi sallama hakan yasa Mami kewayowa had’e da amsawa. 

   “Wa’alaikumus salam, a’ah! Maamah?”

  “Na’am Mami ina kwana?” Ta tsuguna ta gaisheta “Lafiya k’alau ya kike ya makaranta?”

  “Alhamdulillah Amal na gida kuwa?”

  “Ga ta chan tana d’akinta tana kuka ki k’arisa ciki halan ke ta gaya miki meke damunta.” Ba gardama ta k’arisa ta tsinci Amal nata kuka kaman yadda Mami ta fad’a gabad’aya ta fita daga kamanninta fuskan nan ya kumburo tum idanunta sunyi ja suma sun tara ruwa a k’asa. Hugging nata kawai tayi tsananin tausayin da ta bata, kukan ta cigaba dayi yayinda Maamah ke bata hak’uri da k’yar tasamu kukan nata yad’an lafa sannan ta shiga tambayarta meke faruwa sede Amal tak’i bata amsar komai. Ba yadda Maamah batayi da ita ba amman banda hawaye ba abinda Amal takeyi. Abdul da ya gaji da jiransu a waje ne ya kira Maamah don jin ko lafiya inda take irga mai ai Amal d’in tak’i sanar da ita komai. Abdul be san lokacinda zuciya ta d’aukesa ba ta diresa a cikin gidansu Amal ba shiri. Sallama yayi da wuri Mami taja hijabinta daga kan igiya ta sanya jin muryan na miji sannan ta amsa tana jiran ganin kowa. Bak’on fuskan data gani tsaye bakin k’ofan ne ya sanyata ja da baya kad’an. Se kuma taga tsananin kama tsakaninsa da Maamah to kode wanta ne? Ta tambayi kanta. Tun daga bakin k’ofan ya durk’usa har k’asa ya gaisheta. 

  “Tashi don Allah tashi kaji?” Amman yak’i seda ta amsa sannan ya mik’e. “K’ariso ciki, wan Maamah kake ko?” Mamakin daya bayyana a fuskansa ne ya sanyata murmushi “Bade mamakin ya na gano kake ba?” Dukda mugun halin da yake ciki hakan be hanasa mayar mata da murmushin ba “Sosai Mami” ya amsa. 

  “Yo ai kama kuke wane an tsaga kara marabanku de hasken data fika shikenan lale k’ariso ciki barin yi mata magana ta fito.”

  “Toh nagode amma dama wajen ki nazo” ya sanar da ita. Da mamaki ta tsaya kallonsa “Gu na kuma?” Ta tambaya. 

  “Eh Mami I’m sorry please.”

  “Ba komai bismillah k’ariso.” Tabarma ta shinfid’a masa ya zauna sannan tayi hakan itama har anan Maamah da Amal dake cikin d’aki basu san meke faruwa ba. 

   “Toh gashi ban ma san sunan ka ba.”

  “Abdurrahman” ya sanar da ita. 

  “Toh Abdurrahman meke tafe da kai?” Gyaran murya yayi tare da dukar da kansa “Mami a farko de ina son in fara da baki hak’uri, dan Allah kiyi hak’uri na shiga gonan ki da Papi da nayi na sace flawanku ba tare da sanar daku ba, I’m sorry.” Sosai Mami ta shiga duhu “Baba na kayi hak’uri amman ban fahimce ka ba.”

  Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauk’e sannan yace, “Sama da wata shida kenan muna tare da Amal amman keda Papi ba kuda labari, what’s worse is ko izinin nemanta banyi ba daga gareku which I know is very wrong of me amman ku gafarceni. Banida niyyan lalata Amal, ina sonta ne so na tsakani da Allah so na aure idan har zaku bani izini. Sau dayawa nakan gwada rok’an kanta da tabani dama in turo magabatana koda formal introduction ne ayi don asan juna amman hakan ya gagara kullum excuses da take bani daban amman ina da tabbacin tana da k’wak’waran dalilin dake sata hakan. Toh kuma se gashi tun jiya na kasa gane kanta, muna cikin waya kawai ta rushe da kuka tun wannan lokacin bata sake d’aukan kira na ko na Maamah ba. Yau na turo Maamah don ta tabbatar mana da me ke faruwa amman shiru Amal tak’i magana dalilin daya sa nayi wannan zuwan bazata kenan amman kiyi hak’uri sam ban so hakan ba nima da magabata na naso fara tako k’afa na cikin gidan nan, my sincere apologies please.”

  Shiru Mami tayi tana assimilating kalamunsa wato har na kusan wata shida suna tare amman shine Amal bata ta6a bud’an baki koda wasa tace mata gashi ba? Sau dayawa takan jita a waya amman kota tambayeta da waye ne setace da Afzal ne ashe saurayi tayi a bayan idonsu. 

  “A gaskiya Abdurrahman bazan 6oye maka ba banji dad’in cewa se yau nakejin wannan batu ba ace na tsawon wata shida kana neman ‘yata amman ba tare da ka nemi izini gun d’aya daga cikin iyayenta ba?”

  “Nasan ban kyauta maku ba Mami and I’m gravely sorry bana son hakan yasaki tunanin da wata manufan nake neman Amal wallahi my intentions are pure ina son Amal ne tsakani da Allah.”

  “Kuma da ba don halin da ta fad’a d’inba bakada niyyan bayyana mana kanka yanzu ko ba haka ba?”

  “Mami bazan gaji da baki hak’uri ba saboda nasan ni me laifi ne amma kisani wallahi nima ba haka naso abunnan ya kasance ba. My apologies please, and ko a yau kukace in turo magabata na zanyi hakan saboda bana son abinda ze rabani da Amal, inason ta sosai.” 

  “Naji bayanunka Aburrahman kuma na gamsu dasu idan Papinta ya dawo daga tafiya zan mai bayani duk abinda akwai zan sanar da kai.”

  “Nagode sosai Mami kuma ina sake baki hak’uri.”

  “Ba damuwa karka damu.”

  “Se kuma batun Amal ko zan iya sanin meke damunta? Nayi nayi ta sanar dani amman tak’i bazan kuma 6oye miki ba hankali na ya matuk’an tashi banason ganin Amal cikin damuwa.”

  “Wallahi bazan 6oye maka ba, yadda baka da masaniya akan halin nan da take ciki nima haka ne, tak’i sanar dani matsalarta se kuka kawai. Yanzu haka jiran Papinta kawai nake shi kad’ai take jin maganansa.” Ya bud’e baki zeyi magana kenan sega k’ofan d’akin Amal ya bud’u Maamah na fitowa bayanta kuwa Amal ce ta rik’e k’ofan tana shirin rufewa. Idanunsu na had’ewa gabanta yayi mumunan tsinkewa barin ma ganinsa da tayi tare da Maami. Yau shikenan ya gama da ita, tasan she’s in a big trouble idan Papi yazo. 

  “Amal!” Ya kira sunanta da sauri ta mayar da k’ofan kai zallah Mami ta kad’a wai kode aljanu ne suka shigeta? “Kafa kwantar da hankalinka yau Papin nata ze dawo koma mey ke damunta zata sanar dashi ko ta fad’a miki abu ne Maamah?” Ta juyo tana kallon Maamah. 

  “A’a wallahi tak’i sanar dani komai.”

  “Toh Mami zamu koma nagode sosai da k’aramcin da kika nuna mun Allah sak’a da gidan aljannah.”

  “Ameen Abdurrahman ba komai gashi har zaka tafi ko ruwa ban baka ba.”

  “Haba daga gida nake karki damu mu tafi ko Maamah?” Yayi maganan had’e da mik’ewa har waje Mami ta rakasu sannan ta dawo ta nufi d’akin Amal tare da bankad’e k’ofar. “Ai Papinki ze dawo wai shin a ina kika koyo wannan d’abi’ar iyye? Har kiyi saurayi ba wanda ya sani a gidan nan? Abinda kikeyi a makarantar kenan ko?” Shiru Amal tayi mata don bata jin ma tana da energy’n yi mata bayanin komi. 

  “Sa’an ki d’aya wallahi yaron nada hankali wato har iyason turo magabatansa amman kike hanasa saboda ke bakison ku gina abinda kuke da shi akan addini ko? Kuma kiji ni kukan nan ya isa haka, ba dukanki akayi ba ba fad’a aka miki ba kawai kibi ki ta da wa mutane hankali haka a banza? Dubi yadda hankalin yaron nan ya tashi da safen nan kika d’agosa duk da hakan kin gansa kin kasa k’arisowa ki gaishesa toh ki cigaba Baby” tana kaiwa nan ta fice. Wani sabon kukan Amal ta rushe dashi a gun haka ta cigaba dayi har izuwa dawowan Papi. Bayan ya d’an huta Mami ta zaunar da shi ta labarta masa ababen da suka faru bayan tafiyansa ta ke kuma yabawa hankalin Abdul. Turata yayi da ta kira Amal bayan sun k’ariso Amal ta tsuguna daga waje-waje tana mey tare fuskarta da hijabinta. 

  “Mama na?” Ya kirata 

 “Na’am” ta amsa. 

 “Daina kukan haka kinji? Ya isa goge hawayenki.” Ba musu ta shiga share hawayen nata “Gaya mun meke faruwa?”

  “Papi babu.”

  “Nace ki gaya mun meke faruwa.”

  “Babu komai.”

  “Kode se kinji bugu ne?” Fad’in Mami. 

  “A’a beyi zafi haka ba zata fad’a da kanta gaya mun kinji keda waye ne?Keda Abdul d’inne?” Kai ta kad’a a hankali “Toh waye?”

  “Yaya” ta furta chan k’asa-k’asa. 

  “Afzal??” Papi ya tambaya da mamaki yayinda Mami ta bud’e baki tana kallonta itama cike da mamaki. 

  “Meya samesa? Wani abun ya miki?”

  “Ba shida lafiya, likita yace yana iya rasa ransa.”

  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” both shi da Mami suka sa salati. “A dalilin mey?!” Mami tayi exclaiming cike da tashin hankali Allah sarki ashe shiyasa kwana biyu baya zuwa kuma bayi ko kiranta ita ko Allah be bata ikon kiransa ba dukda cewan yana ranta ashe beji dad’i bane. 

  “Meya samesa?” Papi ya tambaya finally. 

  “Ya kamu da ciwon zuciya.” Nan ma wani salatin suka kuma sawa. “Allah sarki d’an halak shine baki fad’a mana tun wuri ba Baby? Sede kiyita kuka amman baza kiyi magana muje mu dubasa ba? Haka akeyi ne aka ce miki?” Mami ta kurareta. 

  “Tun yaushe yake jinyan?”

  “Ya d’an kwana biyu Papi” ta amsa tana share hawayenta. 

  “Ya isa kukan haka in shaa Allah ze samu sauk’i ba wanda ze mutu kinji?” Kai ta gyad’a a hankali “Zamu shirya kuma duka muje mu dubasa kukan ya isa haka.”

  “Nagode” bata kai ga mik’ewa ba ya dakatar da ita. 

  “Se kuma batun Abdurrahman ko?” Yayi maganan yana kallon Mami. 

  “Waye shi?”

  “Wan k’awata Maamah ne.”

  “Mey a tsakaninku?” Shiru tayi ba amsa. “Meyasa baki ta6a sanar dani ko Maminki batu akansa ba? Haka aka ce miki akeyi?”

  “Papi I’m sorry kayi hak’uri.”

  “Baki amsa tambaya na ba meyasa?”

“Papi kuskure ne amman kayi hak’uri.”

  “Da yakeson turo magabatansa kuma meyasa kike hanasa?”

 “Papi ba hanasa nayi ba.”

  “K’arya Mamin ki take kenan?” Kallon Mamin tayi sannan ta kad’a kai. “Toh meye dalili?”

  “Na d’au idan akayi hakan zaku hanasa kula ni ne.”

  “A ganinki kula shi da kikeyi ba tare da izinin mu ba shine abinda ya kamata?”

  “A’a” ta amsa tana kad’a kai. 

  “Tun yaushe kuke tare?”

  “About 6 months now” ta amsa chan k’asa-k’asa. 

  “D’an gidan waye ne?”

  “A Zarma na bakin layin polo.”

  “A Zarma me masallacin juma’ah?”

  “Eh shi.”

  “Kina sonshi kuma?” Shiru tayi ta kasa amsawa. “Ke fa Baby kina son shi?”

  “Eh Papi” ta amsa murya a ciki kallonta Mami tayi had’e da turo baki. 

  “Idan nace ya turo magabatansa zaki amince ki auresa?”

  “Eh Papi.”

  “Toh shikenan tashi ki fice amman nan gaba karki sake yin wannan rashin hankali duk wanda kuka had’u dashi ya nuna yana sonki kiyi masa kwatancen gidan nan kice yazo ya gana da Papinki kinji? Bawai kuje chan kuna sha’aninku ba bawanda yasani kin ji?”

  “Naji Papi nagode kuma ka sake yin hak’uri kema haka Mami.”

  “Shikenan ta shi ki fice” da haka ta mik’e ta wuce d’akinta. 

  “Ban yarda wai saboda rashin lafiyan Afzal take wannan kuka ba” fad’in Mami. 

  “Ko?”

  “Sosai ma kuwa Baba kasan tun yaushe take wannan kuka? Da akwai 6oyayyan al’amari a tattare da yarinyar nan.”

  “Nima nayi zaton hakan amman kinga koda k’arya take anjima idan mukaje asibitin zamu tabbatar da gaskiyar al’amarin.”

  “Toh shikenan Allah kaimu.”

****

   Nazeefah ce tayi knocking bisa k’ofan d’akin Afzal sannan ta bud’e ta shiga yana ganin itace ya kawar da kansa. K’arisowa tayi da basket na lunch nasa ta ajiye akan table “How’re you feeling? Kana iya d’aga hannun?”

  “Tukunna amma da sauk’i” ya amsa. 

  “I cooked your favorite Rice and stew” ta sanar dashi tana me bud’e hulunan. Bayan tayi serving nasa ta taimaka masa ya zauna sannan ta zauna a gefensa itama da shirin basa abincin. 

  “Ahhh” ta buk’acesa. 

  “I can manage karki damu.”

  “Come on Afzal open up.”

  “Nace karki damu zan iya ci da kaina.”

  “I know laifi ne don nayi feeding naka? Besides you’re still not fit.” Da k’yar ta samu ya amince ta shiga basa abincin har seda ya k’oshi. Godiya yayi mata sannan ta tsiyaye masa ruwa ya had’iye magunansa yake tambayanta Ina Ummi tun jiya be sake ganinta ba. 

  “Nima tun jiya da na ganta tsaye dasu Sultan da Ummah tace zata masu rakiya ban sake ganinta ba.” Haka kawai seyaji gabansa ya tsinke bade wani d’anyen aikin suke shiryawa a bayan idonsa ba ya tambayi kansa. 

  “Wayyo!” Yasa ihun k’arya. 

  “Lafiya?” Tayi saurin tambaya. 

  “Get my Dr! Hurry! Washhh!”

  “Keep still ina zuwa” a guje ta fice neman likitansa inda ya ciro wayansa ya kira Sultan. A karo na farko ya d’auka. 

  “Sultan meke faruwa?”

  “Kaman ya? Lafiya?”

  “I don’t want to believe ka sanar dasu Ummi batu akan Amal ka tuna ka d’au alk’awarin bazaka fad’a musu komi ba.”

  “Sekuma akace maka na sanar dasu wani abun?” Ya mai k’arya. 

  “I just have a strange feeling.”

  “Ka kwantar da hanaklinka ni ban sanar dasu komai ba.”

  “Yauwa thank you.”

  “Ya jikin naka?”

  “Alhamdulillah zuwa anjima ma zasu sallameni.”

  “Toh madallah ko kun sake waya da Amal?”

  “Nah bata kirani ba nima ban kirata ba.”

  “Alright sena shigo de.”

  “Okay you take care.” Da haka sukayi sallama. Dawowan Nazeefah da Dr seyace ai daya sha ruwan sanyi yaji sauk’i, dubasa sama-sama likitan yayi sannan ya fice. 

   Wajajen k’arfe biyu da rabi Ummi da Abba suka isa gidansu Amal. Sallama suka yi a bakin k’ofar seda aka amsa suka shiga, Ummi ce ta soma sa kai. 

  “Lale sannu da zuwa” cewan Mami lokacin da taga Abba a bayan Ummi ne tayi saurin mayar da hijabinta. “Sannunku da zuwa” dadduma ta shiga ciki ta dau ta shimfid’a musu sannan suka gaisa. “Baki gane ni bako?” Ummi ta tambayeta. 

  “Eh toh wallahi” ta amsa da fara’a. 

  “Ummi ce, mahaifiyar Afzal na gefena ko mijina na ne Abban shi.”

“Wai wai wai ashe manyan bak’i mukayi lale lale sannunku da zuwa bari in kawo muku ruwa.”

  “A’a karki damu daga gida muke” cewan Abba. 

  “Ya jikin Afzal d’in se yau Baby ke sanar damu wai beji dad’i ba.”

  “Jiki Alhamdulillah da sauk’i” ya amsa. 

  “Toh Allah k’ara masa lafiya muma muna shirin zuwa dubasa dama da Kakan Baby.”

  “Ayyah ba komai ko shi kakan nata na gida?” Abba ya tambaya. 

  “Eh barin yi mishi magana.”

  “Yauwa toh” da haka ta shiga ciki ta kira shi yayin da ta lek’a d’akin Amal don tazo ta musu sannu da zuwa sede ta ga d’akin nata ba kowa ko yaushe ta fita ba tare da ta sanar da ita ba? Papi na fitowa suka gaisa da Abba sannan Ummi inda Papi keta sawa Afzal albarka yana fad’a masu irin hidiman da yakeyi wa Amal yake kuma godiya. Sosai shi Abba da Ummi suka ji dad’in halin taimako irin na Afzal. 

  “So Alhj Muh’d ba tare da 6ata lokaci ba bari in sanar da kai meke tafe damu” cewan Abba had’e da yin gyaran murya “Munzo ne batun Afzal.”

  “Toh ina jinka Alhj.”

  “Kaman yadda Amal ta fad’a muku be ji dad’i ba, hakan yake likita yayi gwaje-gwajensa an gano ya kamu ne da ciwon zuciya.”

  “Tabbas haka Baby tace Allah k’ara mai lafiya ya kuma yaye mashi wannan ciwo.”

  “Ameen ya Allah” duka suka amsa sannan Abba ya cigaba. “Sanadin wannan ciwo daya kama sa se kan kowa ya d’aure mun rasa sababin ciwon, ba irin tunanin da bamuyi ba amman ina mun kasa gano dalilin da ze sanya masa ciwon zuciya a k’arancin shekarun da yake da ita. A fari munyi tunanin ko rashin jituwar dake tsakaninsa da matarsa ne kasancewar auran biyayya duka sukayi amman da bincike yayi bincike se muka gano ba hakan bane ciwon son ‘yarku Amal ne da ya kasa furtawa kowa.”

  “Ciwon son Baby?” Shida Mami suka nanata cike da k’in yarda. 

  “Tabbas na tsawon lokaci Afzal na son Amal amman ya kasa samunta ko ku ya fad’a muku wanda har izuwa yanzu bamu san meyasa ba, kwatsam kuma kawai sega wannan shi Abdul ko?” Ya juya ya kalli Ummi inda ta gyad’a masa kai “Yauwa shi Abdul ya fito yace yana sonta har ya zamanna sunyi nisa da ita Amal d’in, toh wannan ne sababin rashin lafiyan nasa. Ganin su da yake kullum tare kuma ba yadda ya iya, gashi yana ganin lokaci ya riga ya k’ure masa se ya zammana ba aikinsa kullum se tunani, yana mey tak’ura wa kansa yana bin abun a zuciya har wannan ciwo yayi nasara akansa. Sau biyu kenan yake samun attack gashi likitansa yace muddin ba a magance masa wannan matsala ba yana iya rasa ransa idan ya cigaba da samun attack d’in.”

  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” Mami ta sake sa wani salatin. 

  “Jiya ina nan ma ai na samu Amal nakeyi mata maganar inda ta tausaya wa halin da Afzal ke ciki ta kuma nuna min zata iya yafe komai saboda ceto ransa dukda cewan bata 6oye mun tsananin soyayyan dake tsakaninta da shi wannan saurayin nata ba amma tace muddin ku iyayenta kun amince ita me iya yafe farin cikinta saboda na Afzal ne. Tabbas mun san Afzal me laifi ne na hadissa duka wannan matsalar, da tun farko ya sanar daku komai da shi Abdul baze ma samu daman shigewa zuciyan Amal ba amma abinda ya faru ya riga ya faru sede ayi tunanin magance ta yanzu haka as we speak Afzal ma ba shida masaniya akan zuwan mu nan. Yanzu haka be ma san mun gano sababin rashin lafiyan nasa ba ma sabida wa amininsa Sultan kad’ai ya fad’awa damuwansa ba yadda bamuyi da shi ba ya fad’a mana meke damunsa amman yak’i da k’yar muka samu abokin nasa ya bamu had’in kai ya kawo mu gidan naku.” Nauyayyar ajiyar zuciya both Papi da Mami suka sauk’e as suna mamakin wannan al’amari ashede kukan da Amal ta yini take tayi kenan tun jiya na zafin rabuwa da masoyinta ne, hak’ik’a tana son Abdul. Shi ko Afzal har yanzu sun rasa dalilin da ya hanasa sanar dasu cewan yana son Amal bayan yasan ba wanda ya cancanci soyayyarta sama da shi kodan hidimomin da yake mata. Sau dayawa Papi kan zauna yayi tunanin nan na cewa anya ba son Amal yake ba shiyasa yake mata wannan hidimomi sede tun yana sa ran wataran Afzal zeyi masa maganan Amal har ya dena saboda koda wasa Afzal be ta6a d’auko masa zancenta ba. Toh meyasa? Meya hanasa? Ko gani yake ko da ya furta masu kud’urina  zasu hanasa Amal d’inne? Ai shima yasan baza a ta6a yimasa haka ba toh meya hanasa sanar dasu?

  “Shine muke neman alfarma a gareku, ku kad’ai keda ikon ceto mana ran d’annan idan har Allah ze baku iko, shi kad’ai ne garemu bama son mu rasa sa kuma munsan yadda tambayan hakan agareku ya nuna tsan-tsan san kanmu amman ina da tabbacin duk iyayan da suka tsinci kansu acikin halin da muke ciki haka zasuyi suma” Ummi ta sake fad’a. 

  “Tabbas haka yake Ummin Afzal” Mami ta nunfasa “Nima koda nice na tsinci kaina acikin halin nan da kuke ciki bazan fasa ba har se inda k’arfi na ya k’are. Abu d’aya ne ya d’aure mun kai, dalilin da ze hana Afzal sanar damu k’udurinsa akan yarinyan nan bayan yasan baza a ta6a hanasa ita ba kuma a fari ita kanta Baby nasan bazata k’i sa ba, yanzu gashi tun tafiyanki jiya ta kulle kanta a d’aki tana ta aikin kuka ko ni tak’i sanar dani meke faruwa harta Papinta ma ce masa tayi babu da aka tak’ura mata ne se take ce mana wai Afzal ne bashida lafiya likita yace yana iya rasa ransa dalilin da ke sata kukan kenan amman dukkanmu ba wanda ya yarda da hakan saboda kukan yayi yawa. D’azu shi Abdul d’inma ya shigo kuma ya nuna a shirye yake da ya turo magabatansa anytime aka basa daman hakan, a gaskiya ban san ya zamu 6ullowa al’amarin nan ba. Yaran nan sunyi nisa ba adalci bane mu raba su, ta fannin Afzal kuwa ya cancanci komi a garemu ko saboda halaccin da yayi mana ko duniya yake buk’ata inde muna da ita ya zamo dole mu basa.” Sosai Ummi suka ji dad’in maganan Mami suka shiga yi mata godiya. 

  “Toh yanke hukunci de ba namu bane” cewan Papi “Mude zamuyi k’ok’ari muga mun karkato da hankalin ita Baby da Abdurrahman d’in idan sun amince zasu iya yin shahada su ceto mana ran Afzal walillahil hamdu amman nikam bazan iya tilasta Baby auran wanda bata so ba, shi auren dole ba shida amfani kuma kun sani.”

  “Wannan haka yake Alhj Muh’d” cewan Abba “Kuma a hakan ma muna godiya sosai and we pray for nothing but the best Allah sak’a muku da gidan aljannah.”

   “Ameen wa iyya kum” ya amsa. 

  “So zamu wuce duk abinda akwai dan Allah ga number na” yayi maganan had’e da zaro card nasa daga aljihunsa ya ajiye a gaban Papi “Ka min waya.”

  “Toh toh shikenan Allah sa mu dace.”

  “Ameen ameen” da haka suka musu rakiya. 

   “Ai dama na fad’a miki iyayen Afzal ne” fad’in Amal dake la6e jikin k’ofansu Falmata tare da ita Falmatan. Tuntuni taso komawa gida amman cin karo da tayi da motar seta fasa gashi kuma kamar yadda ta fad’an ne su Ummi ne. 

  “Yanzu har sunzo sun sami su Papi kenan? Amal ki hak’ura da Ya Abdul kawai nasan da k’yar ki kasance tasa.”

  “Falmata I love him I can’t do without him.”

  “Ya Afzal fa? Kina nufin duk halaccin da ya miki da butulcin nan zaki sak’a masa kenan?”

  “Falmata ban sani ba sun tafi barin k’arisa gida duk abinda akwai zan sanar da ke.”

  “Toh se anjima.” Tana isa gida Papi ya kirata ta k’arisa ta zauna a tsakankaninsa da Mami. “Uwata ina kika shige?”

  “Na jeni gidansu Falmata ne.”

  “Toh tafiyanki iyayen Afzal suka zo suka kuma sanar damu dalilin kukan da kika kwana kinayi a gidan nan tambayata itace meyasa? Meyasa kika k’i sanar dani ko Maminki halin da kike ciki kika gwammace kisha wahala ke kad’anki?”

  “Papi I’m sorry ban san ya zan fara sanar daku bane shiyasa.”

 “Ko tunani kike zamu bada ke ga Afzal d’in ko kink’i ko kin so?” A hankali ta gyad’a kanta. “Ko kad’an Baby se wanda kike so zaki aura kinji? Alk’awari na d’auka tunda Maminki ta haife ki na cewa zan kula dake tamkar nine mahaifinki kuma bazan bada ke ba se ga wanda kikeso.”

   “Papi ina son Ya Abdul bana son rabuwa da shi” ta fad’a yayinda ta shiga kuka. 

   “Shi ko zaki aura in shaa Allah kinji? Se wanda kikeso zaki aura ki kwantar da hankalinki.”

  “Toh Papi Yaya kuma fah? Ya zamuyi da shi? Kana ganin munyi mai adalci kenan bisa ga duk ababen alkhairin da yayi mana a gidan nan? Ace buk’atansa ya tashi amman mun kasa biya masa saboda son kai namu?”

  “Uwata meke tafe a k’wak’walwarki? Kina son Abdul?” Kai ta gyad’a take “Ba kiya kuma son Afzal ya rasa ransa?” Nanma kai tayi saurin gyad’awa “Amma kinsan bazaki iya auran maza biyu ba ko? Dole cikinsu d’aya ya hak’ura koba haka ba?”

  “Hakane Papi.”

  “Toh wa zamu ba hak’uri? Dan ni se abinda kikeso zanyi miki.”

  “Papi ban sani ba nima I don’t want to lose them both.”

  “Amman ya zama dole Baby, hungo Jamila ku shiga daga ciki duk hukuncin da kuka yanke shi zamuyi aiki akai.” Yace da Mami ba gardama taja hannun Amal suka yi ciki kaman yadda Papi ya buk’ata sede banda kukan da Amal keyi ta k’i cewa komi. Daga k’arshe de Mami ta yanke hukuncin Amal zatayi istikharan kwana uku duk za6in da Allah yayi mata shi zata bi. Amal batayi musu ba ta amince da shawarar cikin dare yau ta fara. 

  2 days later…

    “Assalamu Alaikum” Mami ta fad’a tare da sa kai cikin d’akin Amal. Hawayenta ta shiga sharewa da wurwuri sede ina Mami ta riga ta ganta. K’arisowa tayi ta zauna a gefenta had’e da kiran sunanta. “Na’am” ta amsa sama-sama. 

  “Yau kika kammala istikharan ko?” Kai ta gyad’a a hankali. 

  “Wanne cikinsu yafi kwanciya miki a rai?”

  “Mami…” sekuma ta rushe da kuka, rungumota tayi tana shafa bayanta tana bata hak’uri har seda kukan nata ya lafa. “Waye ne ki gaya mun kinji?”

  “Mami it can’t be Yaya it just can’t! What of Ya Abdul? Bana son in rasa sa” ta kuma rushewa da wani kukan. 

  “Afzal?” Mami ta ambata da mamaki “Shi hankalinki yafi kwanciya da?”

  “Mami zan sake yin wani istikharan what of Ya Abdul? Me ze sameshi? Waze aure shi?”

  “Baby za6in Allah shine mafi alkhairi idan har hankalinki yafi kwanciya da Afzal toh shine za6in da Allah yayi miki ya zamo dole ki hak’ura da Abdul nakin.”

  “But Mami I can’t, I love Ya Abdul wallahi ina son sa kuma banjin zan iya rayuwa ba shi dan Allah karki fad’awa Papi wannan za6in zan sake yin wani istikharan.”

  “Baby ai ba ayin istikhara sau biyu akan matsala d’ai kuma ina da tabbacin koda kin sake d’inma still Afzal Allah ze za6a miki.”

  “Mami dan Allah ki bari in sakeyi please don’t tell Papi.”

  “Baby-“

  “Mami please” ta rushe jikinta tana kuka, sosai Mami ta tausaya mata daba don za6in Allah yafi ba da se suyi ma Papin k’aryan cewa Abdul ne yafi kwanciya mata a rai a shafe zancen Afzal. “Shikenan bar kukan haka zan sake baki kwana uku ki k’ara yin wani istikharan tunda abinda kikeso kenan.”

  “Thank you Mami.”

  “Shikenan toh kukan ya isa haka” tayi maganan tana share mata hawayenta. Bayan fitan Mami sega Ya Abdul na kiran Amal, hawayenta ta share ta gyara muryanta sannan ta d’aga. 

  “Halo my princess?”

  “Na’am my Baby good morning.”

  “Morning ya kike?”

  “Lafiya k’alau ya office?”

  “Alhamdulillah baki fita school bane yau?”

  “Eh.”

  “Baby why?”

  “Gobe zan fita in shaa Allah.”

  “Toh Allah ya kaimu, Baby har yau bazaki bani date in turo su Baba ba? Ni ko formal introduction akayi I’m satisfied, bana son wani yazo yayi mun awuf dake.”

  “Bayan kasan ni kai kad’ai nakeso?”

  “Even still my Princess, du da hakan inason iyayena suzo su sami su Papi.”

   “Ya Abdul kad’an k’ara hak’uri kad’an kaji? In shaa Allah very soon zan kasance mallakar ka kaji?”

  “Promise?”

  “In shaa Allah Ya Abdul.”

  “Thank you my Amal, I love you so much.”

  “I love you even more you take care.”

  “You too, bye” da haka sukayi sallama. Kwanciya tayi akan wayan yayinda wasu zafaffun hawayen suke shiga gangarowa akan kumatunta. Tasan 6ata lokacinta kawai take koda ta sake yin wani istikharan still Afzal Allah ze sake za6an mata but why not Ya Abdul? Ta fi son Ya Abdul akan Yaya a tunaninta kodan wannan Allah ze za6an mata shi akan Yaya but why?? Why Yaya? Kuka ta shiga yi a hankali. 

****

   Kwana biyar kenan yau su Abba suna sa ran kira daga gun Papi amman shiru, gabad’aya shida Ummi sun k’osa a fari ma shikam cewa yayi ko zasu sake komawa gidan nasu ne amman Ummi ta ce su k’ara hak’uri su bari zuwa gobe ko jibi idan har basu kirasu ba se su san nayi. Afzal kuwa har yau besan me ake ciki ba, lafiya k’alau suke zama da Nazeefah a gida. Kasancewar be fara fita office ba kafin ta fita school take shirya masa breakfast da lunch idan rana yayi se yayi heating a microwace yaci. 

Washegari…

    Tun shigowan Mami da tayi taga Amal ta baje kan sallaya tana kuka kawai ta yanke hukunci. K’arisawa tayi tare da hugging nata tana bata hak’uri “In shaa Allah Afzal shine za6i mafi alkhairi a gareki hak’uri ya zama dole kinji?”

  “Mami Ya Abdul fah?” Ta d’ago daga jikin Mami tana kuka sosai idanun nata sun kunburo sunyi ja wur. “Shikenan shi ko wacce budurwa yayi ta ringa tafiya tana barinsa kenan? What if shima ciwon zuciyan ya kama sa fa? I’m sure idan ya gano for all these while I’ve been deceiving him ze kamu da ciwon zuciya kokuwa yayi hauka.”

  “Wa yace deceiving nasa kikayi Amal? K’addarace ta rabaku bawai ke kika yi niyyan barinsa ba saboda haka ki kwantar da hankalinki in shaa Allah shi Abdul d’in ze miki kyakkywar fahimta.”

  “No Mami no matter what karku sanar da Ya Abdul zan auri Yaya banason ya rasa hankalinsa a sanadin hakan dan Allah kar ku fad’a mishi.”

  “Toh ya kikeson ayi Baby? Ayita yaudararsa kenan? The earlier the better.”

  “I know amman karku sanar da shi direct I don’t care how you do it amman karku fad’a mishi cewan zan auri Yaya wallahi ina gudun abinda hakan ze iya haifarwa.”

  “Shikenan zan yima Papinki bayani za’a san yadda za’a sanar da shi amma kibar kukan haka kinji?” Kai zalla ta gyad’a. Isan Mami d’akin Papi ta sanar da shi halin da ake ciki da kuma alfarman da Amal ke nema na cewa kar a sanar da Abdul direct bata son wani abun ya samesa. Dabara ce ta fad’o wa Papi bayan ya kira Abban Afzal ya sanar da shi outcome da suka samu bayan istikharan da Amal tayi Abba yayi ta godiya yace zuwa anjima ko gobe ma zasu shigo. D’akin Amal ya nufa ya buk’aceta numban Abdul inda take sake rok’ansu da komin yaya ne ita kar a sanar da Abdul direct cewa Yaya zata aura. Kwantar mata da hankali Papi yayi akan ta bar masa komi yasan yadda ze 6ullowa al’amarin. Bayan ya amshi lamban nasa ya kira sa tare da masa bayanin shi waye, bayan gaisuwa yake ce masa yana son ganin mahaifinsa idan da hali har ita mahaifiyarsan ma. 

   “In shaa Allah zanyi musu magana duk abinda akwai zan sanar da kai Papi nagode.”

  “Nine da godiya Abdul Allah yima albarka.”

  “Ameen” ya amsa “Toh se anjima.” Isanaa gida can yamma ya watsa ruwa yad’an huta bayan sallan Isha ya samu mahaifinsa a site nasa yake sanar da shi halin da ake ciki. Sosai mahaifin nasa ya masa murna tun ba yau ba yake jiran wannan rana da Abdul ze ce masa gashi ya samu wata se gashi nan Allah ya k’addaro masa da ranan ashe da rabon zega auran d’ansa. In shaa Allahu gobe nida mahaifiyarka zamu je gidansu yarinyan kaji?”

  “Toh Baba nagode.”

  “Yauwa d’an albarka ko ‘yar wace gida ne?”

   Ba ‘yar babban gida bane Baba amman she’s from a well respected home.”

   “Madallah, zamu je gobe in shaa Allah ko akwai wata matsalar?”

  “A’a shikenan.” Da haka yayi masa seda safe ya wuce 6angarensa. Amal ya kira yake ta faman yi mata godiya a tunaninsa gabad’aya wai ita tabada daman ayi wannan formal introduction. Itako bata nuna masa komai ba, hira suka shafa kad’an tayi masa seda safe akan gobe tana da school. Washegari iyayen Abdul sukayo gaggarumin shopping na kayan abinci yadda al’ada ya kawo suka iso gidansu Amal har da shi Abdul d’in. Bayan gaisuwa da hiran da suka d’an ta6a Abdul yayi tunanin basu waje su tattauna dan haka ya fito waje ya shiga mota yana jiransu. Anan ne Papi ya samu daman yin magana.  

   PAGE 1⃣9⃣

   Gyaran murya Papi yayi sannan ya numfasa “Iyayen Abdurrahman ku gafirceni, ba abinda kuke sa ran ji daga gareni nake da shirin sanar daku ba” ya ce dasu. Sosai suka shiga cikin rud’ani suka ma kasa cewa komi daga k’arshe de cikin tsan-tsan rashin fahimta Baba ya tambayesa “Ko game da mey Malam Muh’d? Ban fahimceka ba.”

  “Zan fara de da neman gafararku nasan ni mey laifi ne amman ku sani banida wata mafitar ne shiyasa, har cikin raina banso hakan ya kasance ba sede k’addara ta riga faruwa.”

   “Wannan haka yake” Baba ya amsa dukda cewan ba wai ya fahimci inda Papi ya dosa bane. 

  “Tabbas Abdurrahman yaro ne mai hankali da ladabi da biyayya da kuma sanin ya kamata, d’a ne da kowani mahaifi zeyi kwad’ayin samunsa a matsayin surki sede kana naka Allah na nasa. Da mahaifiyar Amal ta sanar dani batun za6in Amal akan cewa Abdurrahman ne wanda takeso take kuma son ta aura, wallahi nakega ba wanda ya kaini yin farin ciki. Sosai nayi murna saboda yadda ita Jamila ta yaba wa hankalinsa, sede wani hanzari ba gudu ba kwatsam sega wannan yaro Afzal wanda tun kamin had’uwan Amal da Abdul suke tare da Amal bawai as masoya ba a’a yadda dey kuka san shak’uwan dake tsakanin wa da k’anwa, tamkar d’an gida haka yake a gidan nan kusan kullum suna tare da Amal da Maminta. Sau dayawa nakan zauna inyi tunanin anya ko ba son ‘yar nan yaron nan yake ba? Amman dai-dai da rana d’aya Afzal be ta6a nuna mana ko ita kanta Amal d’in alamomin da zema nuna cewa yana sonta ba banda hidimomin da yakeyi mata. Sati biyun da suka wuce muke samun labarin cewa ya kamu da ciwon zuciya a sanadin son Amal wanda be ta6a furtawa kowa ba. Na tsawon lokaci ya kasance masoyinta na 6oye amman ba wanda ya samu ya sanar da shi ko iyayensa ya 6oye musu zancen. Haka abun yayita cinsa barin ma idan yazo nan d’in ya tarar da ita Amal da Abdul, sau biyu yanzu kenan yake samun attack wanda shi likitansa ya nuna cewa idan har ba a magance masa wannan matsala ba to yana iya rasa ransa. Satin da ya wuce iyayensa sukazo sukayi mana bayanin halin da yake ciki suke kuma neman alfarma daga garemu na cewa a taimaka musu a had’a shi d’an nasu da Amal don ceto ransa, kar ku manta har anan shi Afzal d’in be san mey ake ciki ba. Da magana ya iske Amal kuwa ta nuna tsan-tsan rashin son rabuwanta da Abdurrahman. A matsayina na me kula da ita yazamo dole ne inyi mata abinda takeso don haka na baiwa iyayen shi yaron hak’uri akan cewa bazan iya tilasta mata auran wanda bata so ba tun farko Afzal d’in shi ya janyo komai da tuni ya d’au mataki akan soyayyar da yake yiwa yarinyar nan da anjima da wuce gurin don ba wanda ze hana sa ita kuma koni na tabbata a fari Amal bazata k’isa ba amman seda ya bari soyayyar wani ya shiga zuciyanta sannan kuma za’a zo a fara tunanin raba masoya biyu? Gaskiya na nuna musu hakan ba mey yuwu ba ne ni iyakan abinda zan iya yi shine in gwada karkato da hankalin Amal da na masoyin nata idan har sun amince zasu iya saudakar da son da suke yima junansu suyi shada su ceto masu ran d’a toh walillahil hamd amman de nikam bazan shiga tsakanin masoya biyu ba. Ita Amal da kanta tazo tayi tunani daga baya ta kuma yi la’akari da kalan hidimomi da d’awainiyyan da shi Afzal d’in yayi mata a baya taga kaman ba a kyuata masa ba idan har ba’a share mai da iyayen nasa hawaye ba. Gabad’aya de ta zamo confused ta rasa me take ciki, gashi bata son rasa Afzal alokaci d’aya kuma bata son rabuwa da masoyinta. Mahaifiyarta nan ce ta kawo shawarar cewa Amal tayi Istikhara duk za6in da Allah yayi mata se ayi amfani dashi. Idan har Abdul ne alkhairi a gareta walillahil hamd dama abinda akeso kenan se a baiwa iyayen Afzal hak’uri idan ko Afzal d’inne alkhairi a gareta se ta rungumi k’addara ta bawa Abdurrahman hak’uri. Yin hakan shine adalci saboda cikin duka 6angare biyu ba wanda zeyi jayayya da za6in Allah. Bayan da Amal ta k’are istikharan ta se za6in ya kasance Afzal amman haka nan yarinyar nan tak’i amincewa da sakamakon ba dan komi ba kuwa se don tsan-tsan son da takeyi wa Abdurrahman da kuma gudun rabuwa dashi. Kuka take tana rok’an mahaifiyarta da a sake bata wani daman ta kuma yin wani Istikharan. Yaushe akeyin istikhara sau biyu akan matsala d’aya inba abunku da yaron da soyayya ya rufe mai ido ba?” Ya tsaya tare da sakin murmushin takaici sannan ya cigaba “Haka nan aka zuba mata ido ta kuma wani istikharan sai dai still za6in d’aya ne Afzal. Gata chan har yau ta na rufe a d’akinta tana kukan rabuwa da Abdurrahman ko makaranta tak’i fita kwana biyu haka nan zata yini a d’aki tana kuka. Yanzu haka ita ta kawo shawaran kar mu sanar da Abdurrahman gaskiyan al’amarin gudun abinda hakan kan iya haifowa gwara idan ku iyayensa ku mai bayani, bata son sanadin hakan wani abu ya samesa. Dalilin da yasa na kira Abdurrahman na buk’aci idan da hali ina son ganinku kenan, nasan ba k’aramin karya muku zuciya wannan labari yayi ba amma dan Allah kuyi hak’uri ku sani bawai nuna banbanci muka soyi ba saboda munga Afzal d’an gida ne ko makamancin hakan kokuwa don kwad’ayin abin duniya muka raba Amal da Abdurrahman, kun deji rantsuwa ba kaffara wallahi da ba don wannan istikharan da ‘yar nan tayi ba da ba abinda ze hanani had’ata da masoyinta don a fili ta nuna tafi son Abdul akan shi Afzal d’in dukda kalan hidima da d’awainiyan da yake yi mata hakan be rufe mata ido ba. Ina fatan zaku san yadda zaku sanar da Abdurrahman wannan labari ba tare da tsinka mai zuciya ba kamar yadda Amal ta buk’ata.”

  Shiru kukeji a wajen Mama kanma ta kasa magana tsan-tsan tausayawa situation da d’anta ze shiga kawai da takeyi. Ta sani idan har ya gano gaskiyan al’amarin abun bazeyi kyau ba. Wannan karo na uku kenan da yake yin rashi, jikinsa har rawa yake idan yana bata labarin Amal tsabagen yadda yake sonta yake kuma sa ran finally ya samu sanyin idanunsa kwatsam kuma se gashi. Shi de tasa k’addarar kenan, akan ‘yan mata to ita fatanta Allah yasa rabuwansa da Amal shine alkhairi a garesa. Baba da jikinsa ya mutu ne shima ya numfasa yace, “Mungode Malam Muh’d da har ka sanar damu gaskiyan al’amarin baka bari kwad’ayin abin duniya ya tsole maka ido ba kayita ja mana rai da d’an namu gabad’aya. Fatana Allah yasa rabuwnshi da Amal shine mafi alkhairi a garesa itako Amal da Afzal Allah basu zaman lafiya.”

  “Nagode sosai da kyakkyawar fahimtar da kayi mun dukda cewan nasan hakan da ciwo nima sam ba haka naso abun nan ya kasance ba amman ku k’ara hak’uri abin ne nima yafi k’arfi na wallahi banso sake karyawa d’anku zuciya ba barin ma da Amal take cemun ‘yan mata biyun da yayi a baya ma duka bezo ya k’are dasu ba d’aya mutuwa ya rabasu d’aya kuma abin bezo yayi ba, dan Allah kuyi hak’uri.”

  “Ba komai Malam Muh’d k’addara ta riga faruwa kuma bazamu iya ja da za6in Allah ba in shaa Allahu zamu san yadda zamu sanar da shi. Abdul yaro ne mey tawakkali ina da tabbacin zeyi muku kyakkyawar fahimta ya mik’a komi wa Allah.”

   “Godiya nake Alhj Zarma, Hajiya ina me sake baki hak’uri don Allah” yace da Mama da tayi lamo tun d’azun.

  “Hajiya kiyi hak’uri na gane yanayin da kike ciki amman kiyi hak’uri” Mami da tun da aka fara maganan batace komi ba ta fad’a. 

  “Ba komai Allah sa hakan ne mafi alkhairi ga kowa.”

  “Ameen ya Allah” duk suka amsa.

  “Toh bari zamu wuce sede akwai kayakin da suke acikin mota idan da almajirai kusa sesu shigo muku dasu” Baba ya fad’a. 

  “Kayaki kuma? Wasu irin kayaki kenan?” Papi yayi saurin tambaya. 

  “Kayan abinci de da makamancinsu.” 

   “Ko meyasa Alhj?”

  “Ji Malam Muh’d kuma da wata tambaya, yadda al’ada ya kawo de muka d’an yo cafani sede kuyi hak’uri ba yawa.”

  “Haba! Haba Alhj! Ai idan har muka kar6i kayan nan kuma ya zamo bamuda kunya kenan, baza ayi haka ba yadda kuka taho dashi haka zaku koma dashi mungode sosai da fahimtar mu da kukayi.”

  “Kaya an riga an siyo dan ku taya kuma kakeson mu koma da su? Dan Allah kar kace haka.”

  “A’a Alhj wallahi bazamu kar6a ba ai be ma yi fasali ba, bayan aure baze auku ba kuma a kar6e kayan gaisuwa? A’a dan Allah.”

  “Baka tunanin idan har aka koma da kayakin nan Abdul ze iya fahimtan akwai matsala? Ko ba don wannan bama kaya tunda aka siya da sunanku aka siya idan zakuyi mana adalci ya kamata ku kar6a koda baku so.”

  “Hakane Alhj amma-“

  “Kar kaji komi Mallam Muh’d ai na fahimce ka abu ne Allah ya riga ya k’addara ba yadda muka iya so karka damu dan Allah.” 

  “Toh Alhj amm-“

  “Dan Allah fa nace” ya katsesa. 

  “Toh shikenan Allah saka da alheri” nan suka rakosu waje inda aka nemi almajirai suka sauk’e kayakin daga mota suka jibge aciki. Kayan abinci ne ba abinda babu, shopping kaca-kaca su Baba sukayi. Godiya sosai su Mami sukayi musu har seda motansu ya fice sannan suka dawo ciki. 

  “Abba wallahi sam banji dad’in wannan abu ba” Mami ta fad’a bayan dawowansu ciki “Baka ga yadda jikin mahaifiyar nasa ya mutu ba wallahi sosai na ji musu ba dad’i barin ma shi Abdul d’in.”

  “Tasa jarabawar kenan Jamila se muyi masa addu’a Allah ya basa ikon ci.”

  “Ameen hakane kam itama Baby tana cikin tsaka me wuya rabuwa da masoyi babu dad’i.”

  “Sosai shiyasa ya kamata mu jata jiki mu nuna mata so sosai don ba k’aramin buk’atanmu take ba yanzu.”

  “Hakane bari in shiga daga ciki in sameta.”

   “Toh nima barin d’an fita.”

  “Toh Abba a dawo lafiya.” Da haka ta k’arisa ciki ta samu Amal da keta faman kuka har yanzu hak’uri ta shiga bata tana fad’a mata kalamu masu dad’in da zasu kwantar mata da zuciya akan hakan na daga cikin jarabawanta ne itama idan tayi hak’uri ta kar6a hannu bibbiyu tayi tawakkali komi mey wucewa ne. Da k’yar ta samu kukan Amal d’in ya lafa take sanar da ita yanzun Abdul da iyayensa suka tafi bayan nan kuma sunyi gaggarumin siyayyan kayan abinci sun sauk’e musu dukda cewan Papi beso kar6a ba tunda aure ba yuwuwa zeyi ba amman Baban Abdul d’in ya nuna rashin damuwansa ga hakan ya dage lalle-lalle se sun kar6i kayakin. 

  “Toh yanzu ya kenan? Kun fad’a wa shi Abdul d’in kenan?” Ta tambayeta a nitse. 

  “A’a Papinki de ya buk’acesu da su san yadda zasu sanar da shi kaman yadda kika buk’ata so muna fatan zasu san yadda zasu fad’a mishi.”

  “Mami bana son rabuwa da Ya Abdul.”

  “Rabuwa ya zama dole Baby kede ki dage da addu’a Allah sa za6in nan shine mafi alkhairi a gareki nima zan tayaki da addu’a kinji?” Kai ta gyad’a a hankali had’e da kwantar da kanta akan cinyan Mami tana share hawayenta. 

*****

   Tun isansu Mama gida suke tunanin yadda zasu 6ulloma wannan al’amari tabbas Amal masoyiya ta hak’ik’a ce da har tayi tunanin cewa breaking wa Abdul news d’in haka kai tsaye na iya jefa rayuwarsa cikin matsala. Toh yanzu ya zasu 6ullowa al’amarin? Ya zasu fara sanar da shi Amal bazata iya auransa ba? 

   “Alhj bansan ya zanyi da Abdul ba wallahi ina mugun tausaya masa, bakaga yadda yakeson yarinyar nan ba ko hirarta yake mun jikinsa rawa yake don murna kawai.”

  “Dama kina da labari?”

  “Ai har waya ya ta6a had’ani da yarinyar kuma itama tana sonsa wallahi wannan abu beyi ba.”

  “Tasa k’addarar kenan akan ‘yan matan da yakeso se muyi masa addu’a kaman yadda ya ci na baya ya sake cin wannan d’in.”

  “Hakane Alhj amman gaskiya Amal nada kaifin tunani da tace kar ayi masa breaking news d’in kai tsaye wallahi nima tsoro nake idan kuma shima ciwon zuciyan ta kamasa fa? What of idan ya samu k’aramar hauka?”

  “Subhanallah ya kike magana haka Binta? In shaa Allahu ze fahimce mu.”

  “Gaskiya a’a Alhj bana son abu ya samu Abdul kasan ya za’ayi kawai amman de kar a sanar dashi kai tsaye haka.”

  “Ya kikeson ayi toh Binta? A cigaba da zolayarsa kenan? Har izuwa yaushe? I think the earlier the better.”

  “Yes the earlier the better amman kuma sanar dashi kai tsaye Amal bazata aure shiba ba k’aramin hatsari bane wallahi ni nasan yadda yakeson yarinyan nan I’m very sure news d’innan zeyi devastating nasa ka yarda dani.”

  “Toh Binta ya zamuyi?”

  “Ban sani ba amman we have to think of a way bana son abu ya samu Abdul.”

  “Toh shikenan zamu tsaya muga me Allah ke ciki ko kafin nan da next week 6ullo mana da wata solution d’in.”

  “Yauwa toh hakan yafi.”

****. 

   GIDAN ALHJ AMIN (Abban Afzal)

  “Assalamu alaikum” Afzal yayi sallama had’e da sa kai cikin parlourn. 

  “Wa’alaikumus salam” Abba dake zaune a gefen Ummi ya amsa. “Bismillah k’ariso ciki.” A nitse ya tako ciki ya nemi gu ya zauna had’e da gaishesu duka. 

  “Ya jikin naka?” Abba ya tambaya bayan nan. 

  “Alhamdulillah da sauk’i Monday zan fara fita office in shaa Allah.”

  “Toh Allah k’ara sauk’i.”

  “Ameen Abba nagode.”

  “Dama magana nakeso muyi na turo akira ka.”

  “Toh Abba ina ji.”

 “Kafin nan d’ago kanka ka kalleni inason ina kallon cikin idanunka idan ina ma magana” beyi gardama ba ya d’ago kansa. 

  “Shin wani irin zama kakeyi da matarka Nazeefah a gida?”

  “Lafiya k’alau” ya amsa take. 

  “Kar kayi tunanin yimun k’arya Afzal” ya kirasa da asalin sunansa “Nace wani irin zama kakeyi da Nazeefah? Shin kana kula da ita a matsayinta na wacce take k’ark’ashinka? Shin kana bata hak’k’inta a matsayinta na matarka? Kana kula da tufafin da take sanyawa da kuma kalan mutanen da take mu’amala da su? Shin ka kafa mata dokokin da na miji ya kamata ya kafawa matarsa don kare ma kansa mutunci da ita kanta matar?”

  Shiru Afzal yayi don acikin ababen da Abba ya irgo idan akwai d’aya da yakeyi me kyau shine ciyar da Nazeefah da yakeyi se bata tufafi bayan nan ba komai again. 

  “Da kai nake magana Afzal.”

  “Abba I’m trying, ina iya k’ok’arina don ganin nayi improving relationship namu I just need some space.”

  “Lokaci? Lokaci fiye da shekara d’ai Afzal? Koma me de kasani duk abinda kakeyi a gidan Allah na kallonka muddin idan kai kake toye mata hak’k’i to fa Allah baze barka ba dan Allah baya barin a ci mai alhak’in bawa kaji ka sani idan ko ita ke tauye maka hak’k’i itama Allah baze barta ba.”

  “Na sani Abba.”

  “Bayan nan tun wuri ka zubar da wannan banzan d’abi’ar taka ta zurfin ciki wallahi banda halaka ba inda zata kai ka. Ace ina matsayin mahaifinka in tambayeka fiye da sau uku meke damunka amman ka bushe mun ido kace kai babu bayan soyayyar yarinya ke neman halaka ka? Toh koma me kake 6oyewa kasani munyo bincike kuma mun gano bakin zaren. Kuma wallahi sa’anka d’aya ne na cewa da likitanka yayi idan har ba a magance maka wannan matsala ba kana iya rasa rayuwanka idan ba don haka ba da na barka kasha d’an banzan wuya k’arshe shi Abdul ya aure Amal d’in a idonka muga ko zaka soma yawo tsirara akan hanya. Kana son mutum amman bazaka iya samunsa ka fad’a masa ba chan kuma ka bugi k’irji kace kai na miji ne? A ina aka ta6a yin hakan? Toh ka bud’e kunnuwan nan naka ka saurareni da kyau tun wuri idan kasan bazaka iya rik’e mata biyu ba ka fad’a min kar kazo kayi mun abin kunya.”

  Gabad’aya kan Afzal ya d’aure ya rasa inda Abba ya dosa “Mata biyu kuma Abba?”

  “Eh matar mutum kabarinsa duk yadda Amal da iyayenta suka so kasancewarta da saurayinta Abdul Allah beso hakan ba ya za6ar mata kai a matsayin mijinta na aure bayan istikharan da takeyi har sau biyu just to tell you how much she loves that Abdul. Afzal ka bamu wuya kasa mun nuna son kai a fili na neman raba wannan masoya biyu. Shine tun wuri idan kasan bazaka iya yin adalci ba tsakanin yaran nan ka fad’a mun kar mu fara abinda baza mu iya k’arasawa ba.”

  “Abba ban fahimce ka ba, kana nufin kai da Ummi kunje kun samu Amal da iyayenta akaina?”

  “Ban sani ba ko ka daina jin hausa da yamma.”

  “Abba why? Abba ba lallai bane se Amal ta aureni tunda kaima da bakinka ka fad’a ba yadda ta iya ne, ina amfanin tilasta ta against her wish? A gani na hakan ba shida fa’ida. Nagode da d’awainiyan da kai da Ummi kukayi mun amman a gani na is better a bar Amal ta auri wanda takeso.”

  “Kai kuma se kayi ya da ran naka da kuma son da kakeyi matan?”

  “Zan hak’ura Abba, haka Allah ya k’addara kenan amman banason in zame sanadin k’unci da bak’in ciki a rayuwan Amal.”

  “Na yaushe kuma? Da tun farko da ka gano kana sonta ka tinkareta ka fad’a mata ai da du hakan be faru ba yanzu sede ayi maganan yadda za’ayi ka gyara kuskuren da kayi dan kuskure de kam ka riga kayita saboda haka nakeson gobe ka shirya kaje gidansu ka yima iyayenta da ita kanta godiya ka kuma basu hak’uri musamman ma ita Amal ba k’aramin jarumtaka tayi ba na saudakar da farin cikinta maka kaima ka sani ba sena fad’a maka ba.”

  “Abba I’m sorry amman bana tunanin I can do this.”

  Da mamaki both Ummi da Abba suka tsaya suna kallonsa. “Kana nufin duk hidiman da mukayi maka a banza ze tashi kenan?” Ummi ta tambayesa da mamaki shikam Abba yama kasa magana. 

  “Ummi kuyi hak’uri ba wai zuwa gidansu Amal in basu hak’urin bane bane bazan iya ba.”

 “Mey toh?” Ta kuma tambayansa yayinda Abba ya kafa masa ido. 

  “Ummi bazan iya rik’e mata biyu ba Allah ma shaida ne bazan iya ba.”

  “Kasan da hakan ka kwad’aita wa zuciyarka soyayyan Amal bayan kana da mata a gida?”

  “Ummi inda zan iya hana zuciya na son Amal da nayi hakan da jumawa amman ba daga ni bane, I really tried but abun ya gagara.”

  “Ya zamo dole kenan kaman yadda kowa ma ya hak’ura kaima ka hak’ura ka san ya zaka koyi zama da mata biyu ko a jinka bamu da aikin yine feee se mu d’ibi k’afa mu sake komawa gidansu Amal muce musu gashi kai kace bazaka iya zama da mata biyu ba? Ka sani don lafiyarka muke yin komai Afzal idan ba don haka ba wallahi ko kallonka ma bazanyi ba nide na fad’a maka gobe kaje gidansu Amal ka bata hak’uri da iyayenta tun wuri kuma ka fara koyan zama da mata biyu kana iya tafiya.” Abba yace da shi cike tsiwa. Daga yadda yake magana a san ransa ya 6aci. A raunane Afzal ya mik’e ya fice ko hak’uri ya kasa bawa mahaifin nasa. Ummi ce tabi bayansa tare da kiransa, site nata ta jasa suka wuce inda suka zauna akan kujera. 

  “Prince meyake damunka? Tun da kayi aure ban sake gane kanka ba, ko ka manta ni mahaifiyarka ce da kake gudun gaya mun damuwanka haka?”

  “Ummi ba haka bane.”

  “Toh yaya ne? Kana son Amal ko baka sonta?”

  “Ummi it doesn’t matter.”

  “Yes it does kana sonta koko a’a?”

  “Ummi kema kin sani, I love her, I love Amal.”

  “Meya hanaka sanar damu tun wuri toh da muke tambayanka?”

  “Saboda bansan ya zan fara zama da mata biyu ba I can’t Ummi.”

  “So kake ka saki Nazeefah kenan seka kawo Amal?”

  “Sam ba haka bane Ummi, Nazeefah bata min komai ba idan da adalci be kamata in saketa haka kawai ba don zan auro wata.”

  “Toh seka had’asu su biyu ai dama tun kafin auran naku ma Abbanka yayi maka alk’awarin cewa kowa ka kawo daga baya kace kanaso za’a aura maka ita.”

  “Ummi ina sane da hakan.”

  “Amma abinda kayi ma Abbanka banji dad’insa ba ya kamata ka basa hak’uri.”

  “Ummi I’m sorry amman bazan 6oye miki ba banji dad’in zuwa gidansu Amal da kukayi ba tare da kun sanar dani ba.”

  “Ai ba wai haka kawai aka k’i sanar da kai ba Prince kai kanka kasani idan da mun sanar da kai bazaka yarda ba aje gidan nasu, kasani idan fa kai baka damu da halin da kake neman jefa rayuwarka aciki ba mu nan mun damu da kai. Ko ajinka idan ka cigaba da samun attack d’in zaka rayu ne? Wataran zuciyan na iya bugawa kuma tak’i tashi se lahira kenan. Mey kakeson ace damu? Iyayen da suka kasa magance wa d’ansu tilo damuwa? Abu d’aya nake so da kai Afzal ka rage zurfin cikin nan naka duk abinda yake damunka tell me I’m just a call away komin yaya ne zan san yadda zanyi in share maka hawayenka.”

  “Ummi thank you and I’m sorry.”

  “Ba komai ya wuce bayan nan kuma ina son ka daidaita tsakanin ka da Nazeefah ka sani idan kana tauye mata hak’k’i Allah baze barka ba, a matsayin matarka take dole ne kana biya mata buk’atunta ka kuma bata lokacinta only then Allah ze sa maka hannu acikin al’amuranka ya shige maka gaba.”

  “In shaa Allah Ummi thank you.”

  “Yanzu kaje ka bawa Abbanka hak’uri gobe in Allah ya kaimu seka jeka gidansu Amal d’in kaji?” Kai ya gyad’a a hankali “Very good.” 

  Mik’ewa yayi tare da yimata se anjima ya fice, site na Abba ya nufa ya samesa zaune kaman yadda ya barosa. Durk’usawa yayi ya basa hak’uri se a karo na biyu Abba ya amsa tsabagen yadda ransa ya 6aci. Hak’urin yayita basa amman Abba ya nuna masa ba komai. 

   Isansa gida keda wuya ya shige d’akinsa had’e da mik’ewa akan gado se tunanin abinda Ummi ta fad’a masa yake. Ya sani sarai Sultan ne ya sanar dasu komai bama amfanin kiransa ya tambayesa. Bayan da ya dawo daga sallan isha ne ya tsinci Nazeefah zaune a parlour tana yin assignment nata. Sannu da zuwa tayi masa bayan ya amsa ya k’arisa inda take zaune akan rug yayi tsaye a kanta. Kai ta d’ago da mamaki tana kallonsa amman bata ce komai ba hannunsa biyu ya mik’a mata da nufin ta kama ya mik’ar da ita sede don mamaki tama kasa koda kyafta ido. “Come” ya buka’aceta biron nata ta ajiye sannan a hankali tasa hannayenta cikin nasa ya mik’ar da ita. Da hannunta cikin nasa yayi gyaran murya sannan ya kira sunanta. 

  “Na’am” ta amsa. Idanunsa ya d’ago yana kallon cikin nata idon sannan a hankali ya furta “I’m sorry.”

  Mamaki ne ya rufeta kum tama kasa koda magana da fari ma tayi zaton kode aljanu ne suka shigesa yake bata hak’uri, toh ma hak’urin mey?

   “Afzal” ta kira sunansa a hankali. 

  “I’m sorry kinji? Starting today we’ll be living a happily married life in shaa Allah.” Dan murna tama kasa cewa komai kawai rungumesa tayi yayinda hawaye ya ciko mata a ido, “Afzal I’m sorry too, forgive me also.”

  “Shhh!” ya buk’aceta had’e da hugging nata back sun kai kusan minti d’aya a haka sannan ya zame jikinsa had’e da share mata hawaye “Banda kuka kinji?” Kai ta gyad’a a hankali tana mai murmushi “I’m hungry akwai abinci?” Yayi maganan yana lek’an dining space. 

  “I’m sorry gabad’aya hankali na ya tafi akan assignment d’innan bari yanzu inje in dafa maka macaroni akwai stew na rana senayi heating.”

  “Ki bari ki gama assignment d’in tukuna kinji?”

  “But kace kana jin yunwa.”

  “I can wait finish up first.”

  “Are you sure?”

  “Yes” ya amsa yana mata murmushi. 

  “Alright bari inyi sauri saura kad’an dama.”

  “Okay barin watsa ruwa nima” mik’awa yayi had’e da placing mata light kiss a goshi sannan ya wuce. Mutuwan tsaye Nazeefah tayi gun yayinda farin ciki ya mamaye mata zuciya, ji take tamkar duk duniyan ba wanda ya kaita murna. Nan da nan ta k’arisa assignment natan ta wuce kitchen. 

   Washegari da yamma Afzal ya shirya tsaf cikin half jamfa maroon color ya feffeshe jikinsa da turare ya janyo k’ofar d’akinsa ya fito. 

  “Zan fita” yace da Nazeefah dai-dai lokacin da ya k’ariso parlourn. Sosai gabanta ya fad’i mostly idan yayi wanka haka da yamma gun zance yake wucewa ya zatayi yanzu? Gashi bata son da zaran tayi masa magana hakan ya haifar masu da wani fad’an dan haka kawai ta danne zuciyanta tace, “A dawo lafiya kayi kyau.”

 “Thank you” ya amsa da murmushi sannan ya fice. Gidansu Amal ya wuce direct inda yayi parking ya shige. Mami da Papi ya tarar a tsakar gidan suna zaune. K’arisawa yayi ya tsuguna daga waje-waje had’e da gaishesu. 

  “Kuma ka tsuguna daga chan ka k’ariso ciki mana” Papi yace dashi ba musu ya k’ariso ya zauna daga bakin tabarman inda suka sake gaisawa da kyau. 

  “Ya jikin naka? Ka warware ko?”

  “Alhamdulillah” ya amsa. 

  “Shine ka k’i mu kwana biyu ko?” cewan Mami. 

  “Ba haka bane Mami kuyi hak’uri.”

  “Gashi ka shigo Amal ta fita bata nan.”

  “Ayya dama gunku nazo kafin nan.”

  “Toh toh madallah” Papi ya amsa. 

  “Papi, Mami kuyi hak’uri nasan ni mey laifi ne amma d’an Adam ajizi ne ku gafirceni.”

  “Ba komai Afzal komi ya riga ya wuce Allah sa hakan shi yafi alkhairi kawai.”

  “Ameen nagode, Mami bakice komai ba ko senayi tsallen kwad’o tukuna?”

  “Ai ko abinda za’ayi kenan ace yadda muke da kai amman kana son Amal ka kasa furta mana Afzal? Har seda ciwo ya shige ka? Nakega tsallen kwad’on nan zan saka shine punishment naka.”

  “Yi hak’uri Mami, Papi ka tayani bata hak’uri.”

  “Wasa take maka ta hak’ura da jimawa itama yauwa nace ya batun matarka ta gida?”

  “Lafiyarta k’alau.”

  “Shin tana sane da abinda ake ciki kuwa?”

  “A’a Papi amman idan lokacin yazo zan sanar da ita.”

  “Kana ganin baza a samu matsala bako? Kasan shi rik’e mata biyu ba abu neba na wasa.”

  “Tabbas Papi ina fatan Allah ze bani ikon yin adalci a tsakaninsu.”

 “Toh Allah taimakeka Afzal kasan Amal yarinya ce se anayi ana hak’uri.”

  “Karka damu Papi zan kula da Amal in rik’eta amana se inda k’arfi na ya k’are.”

 “Na amince da kai Afzal dan Allah kar ka bani kunya ga Amal nan mun baka ita kaman yadda kake kula da ita da a baya ina fatan zaka k’ara himma yanzu da ta kasance mallakinka.”

  “In shaa Allah bazan baku kunya ba Papi, you have my word.”

  “Sekuma abu d’ayan da ya d’aure mun kai.”

  “Ina jinka.”

  “Inason jin dalilin daya hana ka sanar damu k’udurinka akan Amal.” Shiru yayi be amsa ba “Afzal?”

  “Papi banason in zame mata distraction ne having that karatun nata beyi nisa ba, dalili na daman in bari idan tayi nisa da karatun se in fayyace mata koma mey ke tafeni kwatsam kuma sega Abdul abinda ya hanani sanar da ita kenan.”

   “Kayi gaskiya amma da ko nine seka sameni ka fad’a mun ba lallai se ita Amal d’in ta sani ba.”

  “Hakane Papi nayi kuskure amman ina sake baku hak’uri, kuyi hak’uri.”

  “Allah sa mu dace.”

 “Ameen bari in fita waje in jira Amal.”

  “Shago ma fa taje bansan meya ajiyeta haka ba” cewan Mami yayinda Afzal ya mik’e. “Toh se anjima.”

   “Ka gaishe da Abbanka.”

  “Toh zeji in shaa Allah” da haka ya fice yaje ya tsaya gun motansa inda yake kallace-kallace chan ya hango Amal daga jikin wani shago. K’arisawa yayi ya tsaya daga bakin k’ofar yayinda take ce da me shagon ya bata pad, dai-dai ya mik’a mata ta juya tana shirin sanyawa acikin leda kenan se kawai sukayi ido hud’u da Afzal dake tsaye a bayanta wane wani aljani. Wani irin ruwa cikinta ya d’ura ga kuma kunyan da ya rufe ta duka atake, yasar da ledan kawai tayi abun nata ya fad’i a k’asa. Dukar da kanta tayi cike da kunya. Kafin yace zeyi mata magana har tabi gefensa da hanzari ta wuce murmusawa yayi gano kunyansa taji sannan ya tsuguna ya d’au abinda ta yasar d’in ya sanya cikin ledar ya shiga binta a baya yayinda take ta hanzari ta k’arisa gida. Taku guda biyar yayi masu kyau ya kamato, hijabinta ya rik’e hakan ya sa ta tsaya ba tare da ta juya ba. 

  “Lily?” Ya kira ta amma tak’i juyawa. Takowa yayi ya k’ariso gabanta tare da tare k’ofar gidan nasu don karta shige, kanta tayi saurin kawarwa. 

  “Lily taya kikeson in fara baki hak’uri tunda ko kallona bakiya son yi? I’m sorry kinji?” Se shiru tak’i koda kewayowa ta kallesa. “I should go down on my knees? I should?” Ya tambayeta nan ma shiru. “Okay” ya furta yayinda ya shiga sauk’a k’asa. 

  “Don’t Yaya” tayi saurin katsesa kafin ya gama sauk’an. 

  “Then turn and look at me” sede har anan d’in ta kasa. Sarai kuma yasan kunya takeji har yanzu na ganinta da yayi tana sayan abin chan. Kawai ji tayi ya d’aga hannunta ta cikin hijabin ya sanya mata ledan aciki “Taho kinji?” Ya buk’aceta. 

  “Ina sauri zan shiga gida” ta furta a hankali. 

  “Lily nasan ni mey laifi ne amma idan kika cigaba da shareni haka ya kikeson in nemi tubarki? Please come down with me” bata sake yin musu ba tabarsa ya jata zuwa kan benchin dake wajen gidan nasu. Bayan data zauna shima ya zauna a gefenta. 

  “I’m sorry, I’m so sorry Lily ban san ta ina zan fara baki hak’uri ba I know I’ve wronged you in so many ways but I’m sorry, I’m sorry for making you pass through all those pains kiyi hak’uri.”

  “Ba komai ya riga ya wuce” ta amsa ba tare da ta kallesa ba.

  “Lily mey zanyi kiyi hak’uri ki kalleni? Yaya is sorry.”

  “It’s really okay” ta amsa had’e da juyowa tana kallonsa. 

  “Thank you, Lily na san yadda kika tsaneni yanzu and I don’t blame you ni na janyo komai, if only I could stop myself from loving you I would have ko dan kar in shiga tsakaninki da Abdul.”

  “Ka dena kawo maganansa.”

  “I’m sorry I really am.”

  “Why didn’t you tell me for all these time Yaya?” Ta tambayesa. 

  “Saboda nasan bazaki amince dani ba” ya amsa take. 

  “Meyasa kace haka?”

  “Saboda kina son Abdul.”

   “Ina nufin kafin mu had’u da Ya Abdul.”

  “Nima ban san mey ya hanani ba Lily but maybe kodan kunya nakeji.”

  “Kunya?” Ta tambayesa da mamaki. 

  “Yes Lily I’m not your Yaya after all tunda har na bari zuciyata ta koyi sonki, ke kin iya kinyi respecting relationship namu ni kuma na kasa yin hakan har na bari soyayyarki tayi nisa a zuciyana, I felt disgusted at myself na rasa da wani idon zan sake kallonki and now I feel so sorry na shiga tsakaninki da Abdul da nayi, wallahi ban san su Abba sunzo nan ba se jiya yake sanar dani. Amal bana son in kasance sanadin k’unci da rashin walwala a rayuwarki if you know you can’t find a place in your heart for me please tell me I can bring back Abdul for you, farin cikinki yafiye mun komai, we marry because of love not pity, ba sekin aure ni ba idan bakiya sona I will understand you.”

 “Lafiyanka kuma fa Yaya? Ko ka manta mey likitanka yace? Bana son in rasaka Yaya, bana son a sanadi na ka rasa raywanka.”

  “Karki damu dani Amal ai ciwo ba mutuwa bace.”

  “In your own case mutuwa ce Yaya, bazan iya ba, bazan iya yafewa kaina ba idan har a sanandi na wani abun ya kuma samunka.”

 “Abdul fa? Don’t you love him?”

  “Yaya I’m sorry” kawai se ta rushe da kuka “But I do love Ya Abdul, I really love him so much” ta sanar dashi cikin tsananin kuka. Har cikin zuciyarsa yaji zafin kalamun nata yayinda sautin kukanta ke tada masa hankali. Mey matakin da ya kamata ya d’auka? Yana son Amal yana son kasancewa da ita amma meye amfanin ajiyeta a gurinsa idan har zuciyarta na tattare da wani daban? Sosai ya tausaya mata barin ma da yaga yadda take kukan cira rai. Ji yayi gabad’aya ya tsani kansa na jefata cikin wannan hali da yayi. Da ya sani da tun farko ya sanar da ita abinda yake zuciyansa kokuwa da ya gano tana da wanda takeso ya tattara ina inasa yabar musu garin inda hali k’asar ma gabad’aya. Sautin kukan ne ya ishesa ya shiga kiran sunanta a hankali. 

  “Yaya I’m sorry but I don’t think I can do this” tana fad’in haka ta mik’e a guje ta wuce ciki ko ta kan su Mami batayi ba ta nufi d’akinta had’e da sa sakata ta kwanta kan katifarta ta shiga rera kuka. 

   *PAGE 2⃣0⃣*

   _My dearest Aunty Sis where’re you? Here’s a page I’m devoting in your honour, know that your daughter loves you hell much, Xx._ 😘

   Sosai kan Mami da Papi ya d’aure barin ma ganin yadda ta shigo a guje da sukayi ko amsa kira batayi, toh kode wani abun ne ya bita? Da wuri Mami tabi bayanta ta lek’a waje don tabbatar da me ke faruwa chan kawai ta hango Afzal zaune kan benchi ya had’a tagumi. K’arisawa tayi ta zauna a gefensa sede har anan be lura da cewa ma wani ya zauna kusa da shi ba. “Afzal?” Ta kira sunansa se a karo na biyu ya amsa a firgice. 

  “Lafiya?” Ta tambayesa. Sam be 6oye mata mumunan halin da yake ciki ba. “Ba lafiya ba Mami” ya amsa tamkar wanda zeyi kuka. 

  “Meya faru? Kai da Baby ne? Yanzu naga ta shiga ciki a guje wani abun ne?”

  “Mami Amal bata sona sam bata sona Abdul take so it breaks my heart watching her cry like this I can’t take it anymore.”

  “Laaa! Bade kukan kai ma zaka yimun ba?” Ta tambaya da mamaki. 

  “Mami no.” 

  “Toh ya kakeson ayi kenan?”

  “Ni zan hak’ura yaso ta auri Abdul d’in kawai, farin cikinta ya fiye mun komai.”

  “Kaman yadda kaima lafiyarka ya fiye mata komai ba.”

  “Mami she’s hurting alot please ku barta ta auri wanda zuciyanta keso.”

  “Yaushe ne zaka gane kaine za6in da Allah yayi mata Afzal? Kuma yanzu da kake biye mata d’in kai kuma ya zakayi da naka ran? Idan ban manta bafa likitanka ne yace rashin magance maka wannan matsala yana iya saka rasa ranka koba haka ba?”

  “But Mami Amal’s happiness comes before anything my life included.”

  “Kar ka kariya Afzal kar ka bari tausayinta ya rufe maka ido tabbas Amal abar a tausaya mata ce amman kai be kamata ka kariya haka gabad’aya ba. Amal na buk’atanka yanzu. Idan har bata sonka ya zame dole kenan ka koya mata. Mu mata munada laushin zuciya garemu, abu kad’an yakan karakato mana da hankali hak’uri zakayi ka nuna mata tsan-tsan so hakan ne kawai zesa ta iya mancewa da Abdul ka kuma maye gur6insa a zuciyanta amma idan ka kariya haka ai kaman ka bata dama ne ta cigaba da kewan Abdul d’in koda yaushe, Amal taka ce Afzal.”

  “Mami bana son ina ganinta cikin k’unci da hawaye haka duk laifi na ne gashi yanzu Amal ke shan wuya.”

  “Ka dena cewa haka Afzal kuskure de an riga anyisa ba kuma amfanin nanatasa kaide yanzu ne ya kamata ka nuna jarumtakarka wajen tabbatar da cewa Baby ta mance da Abdul idan ko kayi sakaci…”

  “Thank you Mami.”

  “Karka damu duk lokacinda kake buk’atan wani abu kar ka 6ata lokaci ka taho ka sanar dani damuwanka ina nan zan kuma yi iya k’ok’arina inga na magance ma wannan matsala kaji?” 

  “Thank you so much.”

  “Ba komai zaka shiga ciki kokuwa?”

  “A’a zan wuce gida but please ki samu Amal ki bata hak’uri tabar kukan haka nan.”

  “In shaa Allah” da haka ta rakasa gun motarsa bayan ya fice ta dawo ciki ta wuce d’akin Amal sede duk suratan da take tayi Amal tak’i tasowa ta koda bud’e mata k’ofar se kuka kawai take, k’arshe seda Papi yace ta hak’ura ta barta kawai. Tambayanta yayi ko meke faruwa inda ta zauna ta zazzage masa komai. Sosai ya tausayawa Afzal d’inma kansa tabbas ya cika masoyi na k’warai shima da har yake tunanin saudakar da rayuwansa gabad’aya saboda farin cikin Amal sede kaman yadda Mami ta fad’a kada ya kariya ya cigaba da nuna mata so a hankali zata koyi sonsa shima ta kuma manta da Abdurrahman. 

  Tun isan Afzal gida Nazeefah ta lura da yanayinsa gabad’aya ba walwala tattare da shi sa6anin yadda ya fita. Ko da tayi masa tayin dinner ma cewa yayi a k’oshe yake baze ci ba ya wuce d’akinsa amma bata sauraresa ba ta d’iban masa abincin ta d’au ruwa a fridge ta nufi d’akinsa. Knocking tayi bayan ya amsa ta shiga ciki. Tsince akan gadonsa ta samesa da wuri ya 6oye wayansa dayake ta faman kallon hotunan Amal k’ark’ashin pillow. Bayan ta k’ariso ta ajiye masa abincin akan side drawer tare da buk’atansa ya tashi ya ci. Beyi musu ba ya mik’e ya zauna. 

  “Wani abun ne yake damunka Afzal?” Ta tambayesa cikin siririn murya. “Feel free to talk to me kaji? I’m here.”

  “Ba komai Nazeefah” ya amsa a sakalce. 

  “Taya zakace ba komai bayan gabad’aya ba haka ka fita kabar gidan nan ba.”

  “Just pray for me kinji? Allah shige mun gaba.”

  “In shaa Allah I’ll ga abincinka kaci kar ka kwanta akan yunwa.”

 “Thank you.”

  “You’re welcome akwai wani abinda kake buk’ata?”

  “Not at all.”

“Alright ina parlour idan kana buk’atan wani abun.” Kai zalla ya gyad’a mata yayinda ta mik’e ta fice. Abincin ya janyo ya shiga ci a hankali yayinda yake ta tunanin Amal. 

  Washegari…

   GIDAN ALHJ A. ZARMA. 

  “Assalamu alaikum” Abdul yayi sallama cikin parloun Baba inda shi da Mama suke zaune. 

  “Wa’alaikumus salam” duka shi da Mama suka amsa. K’arisowa cikin parlourn yayi sannan ya zauna a inda ya saba zama kullum “Sannu Mama”

  “Yauwa Abdul har kun taso?”

  “Eh, sannu Baba ka kirani.”

  “Eh Abdul ya office?” 

  “Alhamdulillah.”

  Gyaran murya Baba yayi ya cigaba “D’azu manager’nku yake mun wata magana akan yana son yi maka transfer zuwa Canada ko ya gaskiyan al’amarin yake?”

  “Tabbas yamun maganan amman ban kar6i transfer letter d’in bama bana so I’m not interested.”

  “Dalili?” Ya tambaya da mamaki. 

  “Baba banason inyi nisa da gida most importantly bana son inyi nisa da Amal.”

  “Ya kake magana haka Abdul sekace idan ka tafi ba za ka sake dawowa ba?”

  “Baba duk da hakan bana so I’m okay with my job in here.”

  “Ka dubi kyan aikin fa Abdul ka kuma sani dama sau d’aya yake zuwa a rayuwa. Shi kansa manager’n naku cemun yayi dayawa sun samesa suna rok’ansa da ya basu aikin amman ya duba zumuncin dake tsakani na da kai ya d’auka ya baka amma kace kai baka so? Gaskiya be kamata kayi wasa da wannan damar ba, aikin tana da kyau albashi hud’u zuwa biyar fa shikenan ka zama DON (mey bala’in kud’i) na kanka ka sake tunani ai idan mu kake gudun yin kewar mu bature yayi video call idan ma Amal takan ce kuna iya yin video call da ita ko ba haka ba?”

  “Hakane Baba amma ai aikin nan nawa ma nada kyau.”

  “Bance batada kyau ba amma sanin kanka ne ai bazaka had’a kyan albashinsa da shi na Canada d’in bako? A gaskiya tunaninkan nan beyi ba koba haka ba Hjy Binta?”

  “Hakane Alhj, Babana Abdul?” Ta kirasa. 

  “Na’am Mama.”

  “Kabi shawaran Babanka kar ka bari wannan dama ta wuce ka this is your chance to build yourself into the millionaire you’ve always wanted zamu baka nan zuwa jibi ka zauna kayi tunani kaji?”

  “Toh Mama nagode Baba zanyi tunani in shaa Allah I’ll get back at you.”

  “Allah yima albarka Abdul.”

  “Ameen Baba nagode zan wuce site d’ina.”

  “Toh ka huta gajiya ko?” Yana ficewa Baba ya sauk’e nauyayyar ajiyar zuciya “A gaskiya keda Amal kunyi gaskiya Hjy Binta yanzu fa saboda yarinyar nan ne bayison tafiya bawai saboda mu ba.”

  “Ai na fad’a maka he’s so attached to her Allah kawo masa sauk’i.”

 “Ameen.”

  “Amma Alhj idan har yak’i amincewa fa? Ya zamuyi? Plan namu beyi ba fa kenan.”

  “In shaa Allah zeyi ai aikin na da kyau.”

  “Toh Allah yasa, kaga idan muka samu ya tafi yanzu se ita Amal d’in ta canza layinta gabad’aya yadda komin ya yakeson samunta baze iyaba ita kuwa Maamah komin ya zeyi da ita akan ta nemo masa new line na Amal zance kar ta basa, this’s the only way nake ganin ze iya rabuwa da Amal cikin sauk’i.”

  “In shaa Allahu wannan shawara taki tayi Hjy Binta Allah sak’a maki da mafificin alkhairi.”

  “Ameen Alhj”****

  Bayan sallan Isha Abdul da gabad’aya kansa ya d’aure ya d’ago wayansa da aniyan kiran Amal. Shi kansa yana son aikin saboda kyansa amman kuma baya son yayi nisa da Amal baya son tafiyansa ya zame sanadin rabuwansu gashi idan ya tafi ze iya d’aukan kusan shekara ko biyu ma halan kafin ya dawo. Kai baze iya ba. A karo na biyu Amal ta d’aga wayan nasa. 

  “Halo Baby na?” Ta soma cewa. 

  “Na’am My Princess ya kike?”

  “Lafiya k’alau ya office I missed you two days.”

 “I missed you even more office na shiga miki hak’k’i ko?”

  “Sosai ma.”

 “Toh ya zamuyi? Gashi na samu promotion a office this time har Canada sukeson tura ni Baby.”

  “Har Canada?” Jin hakan kawai ta gano iyayensa has something to do with this, Allah sarki ta inda suka 6ullo masa kenan so that idan ya tafi a hankali har ya soma mancewa da ita. 

  “Eh Baby kuma idan na tafi I might take a year or two kafin na dawo.”

  “Babe congratulations nayi maka murna sosai this is such a massive promotion.”

  “Yes it is amman ni nak’i amincewa nama k’i kar6an transfer letter’n.”

  “Meyasa Baby?”

  “Toh kuma haka kawai se in tafi in barki har na tsawon shekara Baby? Kina tsammanin zan iya rayuwa ba ke ne?”

  “Baby yanzu danni kakeson barin wannan dama ta wuce ka?”

  “I can sacrifice the whole world for you darling.”

  “Allah sarki Baby please don’t do this, our love for one another is enough balle ma ai zamu na waya har har video call ma idan kana so amma please kar ka bari daman nan ya wuce ka saboda ni.”

  “Baby bana son inyi kewarki.”

  “I’m just a call away my Prince Charming kaji? You don’t have to miss me.”

  “Duk da hakan my Princess nifa bazan tafi ba.”

  “Baby mana yanzu so kake kace zaka bar daman nan ta wuceka?”

  “Ni tama riga ta wuce dan bazan tafi Canada ba tare da ke ba.”

  “Kana nufun idan zan bika zaka tafi?”

  “Mey ze hana ni?”

  “Toh Baby makaranta ta fa?”

  “Ai muna iya kar6a miki transfer letter se muyi aure mu wuce chan d’in tare.” Ba k’aramin hawaye kalamun sa suka sanyata ba da wuri ta share kafin ya gane kuka takeyi. Ina ma ace hakan is possible, ina ma ace za ayi musu aure su tafi Canada and start a new life together, tana ganin da duk duniya ba wanda ze kaita jin dad’i amman Yaya fa? Shin ta kyauta masa kenan idan haka kawai ta tashi ta tafi ta barsa da ciwo? Upon all the hidimomin da yayi mata a baya? 

  “My Baby kinyi shiru.”

  “Ya Abdul I want this morethan anything, ba abinda ze fiye mun kwanciyan hankali kamar rananda za’a d’aura mana aure in kasance mallakinka.”

  “Then let’s get married princess let’s do and fly to Canada together zan d’au nauyin komai karki damu kawai ki amince don Allah.”

  “But Ya Abdul su Mami bazasu amince ba.”

  “Meyasa? Ina iya turo su Baba suyi masu magana ke kawai ki amince.”

  “Ya Abdul kasan ina sonka ko?”

  “Yes Baby I do ai kema kin san ina sonki.”

  “Sosai Sweetheart shiyasa nakeson ka kwantar da hankalinka, ina nan ba inda zani har kaje ka dawo ina jiranka, kaga idanma a shekara d’aya zaka dawo by then na kammala part 4 d’ina clinicals kawai ze rage mun idan kuma in two years ne kaga ma na kammala karatun kenan gabad’aya se muyi auren mu cikin kwanciyan hankali ba hanzari ba komai.”

  “Princess why not now?”

  “Baby bana son had’a aure da karatu ne banason school yana shiga maka hak’k’i idan munyi aure.”

   “Princess ni ban damu ba as long as zaki amince ki tafi dani Canada.”

  “Baby please listen to what I told you, ina nan ba inda zani zan jiraka har kaje ka dawo, I’m yours alone.”

  “Meyasa nake ji ajikina bayan tafiya na wani ze min gaba dake?”

  “Kuma har kake tsammanin zan amince in auri wani sama da kai? Baby shin baka yarda da soyayyan da nake yi maka bane?”

  “Of cours not Princess I trust in your love but-“

  “Them you don’t have to worry Baby I will wait for you ko shekara nawa ne zan jira ka kaji? I love only you.”

  “Promise?” Hawaye na d’iga daga idonta tace, “I promise.”

  “Thank you Princess zan yima Baba magana suzo su samu Papi suyi masu bayani ko?”

   “Baby ba amfanin hakan.”

  “Princess what if suka ji shirun nawa yayi yawa sukayi deciding su ba wani ke? I think is better su Baba su samesu suyi musu bayanin ina nan tafe kar su d’ay Princess d’ina suba wani chan.”

  “Toh shikenan Baby tunda kayi insisting seka turo su Baban suzo.”

  “That’s my Princess.”

  “Tafiyan yanzu ne?”

  “Eh baze fi nan da one month ba.”

  “Ayyah I’ll miss you so much.”

  “I’ll do that even the more Princess.” Hira suka sha sosai sannan tayi masa seda safe. Washegari yaje ya samu su Baba ya musu bayanin shawaran da ya yanke, sosai suka ji dad’in amincewan da yayi amman ya nuna masu shi lalle fa se anje gidansu Amal an sanar dasu Papi batun tafiyan nasa kar bayan tafiyansa su aura mata wani. Basu masa musu ba suka amince duk dan son su 6atar da sahun abun. Koda labari ya iske Maamah, bata sha mamaki sosai ba saboda a karo na farko data fara ganin Afzal ta tabbatar da soyayyan da yakeyi wa Amal ita Ya Abdul kawai take tausayawa yanzu na k’arfi da yaji ana son turasa Canada. 

  Washegari kaman yadda Abdul yaso haka iyayensa suka shirya suka sake zuwa gidansu Amal duk se zolayansa suke.    

   A cikin wata d’aya da sati visan Abdul ya fito ya gama shiri tsaf sauran tafiya. Cikin wata d’ayan nan Amal bata ta6a d’aga waya ta kira Afzal ba saidai idan shi ya kirata shima befi sau biyu zuwa uku ya kirata ba don ya gane kaman tak’ura mata yake. Ko daga yadda take mai magana ma. Don haka se be sake kiranta ba haka kuma be sake taka k’ofar gidansu ba amma kullum da tunaninta yake kwana da kuma shi yake tashi. Sau dayawa suna fita tare da Nazeefah se yayi dropping nata a school sannan ya wuce office rananda yake da meeting d’in safe kuwa ita da kanta take tafiya. Lafiya k’alau suke zama a gidan rannam ma a d’akin Afzal ta kwana, suna cikin hira bacci yayi gaba da ita shiko be tada ita ba instead seya gyara mata kwanciyar suka yi kwanciyar su tare. Da Asuba da ya tada ita sallah kawai se ganin kanta tayi cikin d’akinsa, mamaki ne da farin ciki ya rufeta a lokaci d’aya bata d’au har Afzal ze barta ta kwana d’akinsa ba. Lallai idan mutum yayi hak’uri komai ma is possible, aiko hak’urin zata cigaba da yi har se ta gama karkato da hankalinsa akanta gabad’aya. Tana cikin sallan Asuba Afzal ya dawo daga masallaci bayan da ta idar suka gaisa sannan ta d’aga pillonta. “Ina kuma zakije?” Yayi saurin tambayarta. 

  “D’akina” ta sanar dashi tana kallon k’asa. 

  “A ina kika kwana?”

  “I’m sorry ai da ka tadani jiyan.”

  “Ajiye pillonk kinji? You’re sleeping in here.” Dad’i kaman ze kashe Nazeefah mayar da pillon tayi ba musu ta kwanta chan shima yayi joining nata, bargon yaja ya rufesu suka koma bacci. 

   ***

   Ta fannin su Amal kuwa, ba k’aramin shareta Maamah ke ba, se wani kaffa-kaffa takeyi da ita sam bata sakewa da ita kaman da seda Amal ta zauna tayi mata bayanin komi dallah-dallah sannan ta kuma nuna mata how sorry she is Maamah ta amince suka sake dawo da k’awancensu na da. 

   Kasancewar tafiyan Abdul gobe ne yau tun da Azahar ya taho ya d’auki Amal suka wuce yawo ba shi ya dawo da ita ba se chan yamma bayan sun fito daga motan ya sa yara suka shiga mata da ledojin siyayyan da yayi mata sannan ya kira sunanta alokacin idon Amal ya cike dam da hawaye tasani daga yau kuma se idan Allah ya sake had’a su she’s sure kafin ya dawo an yi mata aure da Afzal. 

  “Princess bade kuka kike ba?” Ya tambaya da mamaki. Kanta tayi saurin juyawa yayinda ta shiga share hawayenta. Zagayowa yayi ta gefenta “Princess so kike kisani kukan nima?” Kukan ne yaci k’arfinta sosai kawai ta fad’a jikinsa tana kukan tsuma zuciya. Tasan yin hakan haramun ne amman bazata iya jure rashinsa ba, mutuwan tsaye Abdul yayi wajen ko rik’eta ya kasa yi. Wai Amal da ko hannunta bata barin a ta6a ne ta fad’a jikinsa haka? Tunani ya fara yi anya ko lafiya? Ya yake ji kaman wannan ne had’uwansu na k’arshe? A hankali ya zagaye hannayensa a bayanta yayinda kukan nata ya tsananta, hak’uri ya shiga bata sannan ya d’agota a hankali ya shiga share mata hawayenta da handkerchief. 

   “Princess kukan ya isa haka kinji?”

  “Ya Abdul dan Allah kar ka tafi, I can’t do without you I really can’t” ta fad’a cikin tsakankanin kuka. 

  “Amal I’m sorry but I have to, we’ll keep in touch kinji? Kukan ya isa haka, idan fa kika cigaba nima zanyi” Kalamai masu kwantar da hankali yayita fad’a mata har ya samu kukan nata ya lafa a hankali har ya d’auke gabad’aya. 

  “That’s my Princess smile toh kinji?” Sede ta kad’a masa kai da nufin a’a. 

  “D’an murmushin ma yau bazaki yi mun ba? Sena kira Babana na fad’a mishi” Yayi maganan had’e da turo baki wane d’an yaro. Bata san lokacinda ta fashe da dariya ba, she’ll surely miss him kodan sanyata dariyan da yake yi. Hira suka sake ta6awa kad’an gun sannan ya buk’acesu da suyi last selfie, suyi a wayanta suyi a wayanshi haka suka tayi har seda suka gaji. 

  “Toh Maghrib ya kusa muje muyi niyya ko Baby?” Yace da ita. “Ki gaishe mun da su Mami sosai sosai.”

  “Toh my Baby semun sake waya ko?”

 “In shaa Allah I love you so very much” ya sanar da ita.

 “I love you too baby” ta amsa, a hankali ya mik’a yayi placing mata light kiss a goshi “Keep yourself safe for me okay?” Kai ta gyad’a cike da kunya ta juya ta k’arisa ciki. Washegari da safe kafin jirin su Abdul zuwa Abuja ya tashi ya kirata yayi mata sallama haka itama da suka isa ta kirasa tayi masa sannu. 

  The next day international flight nasu ya tashi tunda ya kira Amal don suyi sallama take faman yi masa kuka a wayan haka har ya ajiye bata fasa kukan ba. Tun Mami na bata hak’uri har tagaji ta barta. Haka nan tun tafiyan Abdul Amal ta koyi sabon sana’an kulle kanta a d’aki tayita kuka. Sau biyu Afzal na kiranta amman bata d’aga wayan nasa, yau bayan ya tashi daga office ya biya ta gidansu. Mami ya tarar a tsakar gida tana surfan wake. Bayan sun gaisa yake tambayarta ko Amal na gida. 

  “Gata chan a d’aki tun safe da ta fito ta karya ban sake jin motsinta ba.”

  “Meya sameta? Bata da lafiya ne?”

  “A’a Abdul d’inne ya tafi.”

  “Ina?”

  “Canada kode baka da labari ne?”

  “Sam” ya kad’a kai. Nan ta basa labarin duk yadda akayi, ashe de dalilin daya sa ko ya kirata kwana biyu bata d’auka kenan, Allah sarki. 

  “Toh ni zan kai markad’e nan mak’ota zaka jira in dawo?”

  “Eh Mami Allah kare.”

 “Ameen” ta amsa tare da ficewa. Nauyayyan ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya mik’e ya nufi k’ofan d’akin Amal d’in tare da placing gentle knock sede shiru tak’i amsawa. Sallama yayi next se ji tayi kaman muryansa shiru tayi ko ze sake magana don ta tabbatar.

  “Lily?” Ya kirata anan ta tabbatar da cewan shi d’inne. “Lily fito kinji?” Manna masa tayi duk suratan da yata yi hakan besa ta fitowa ba daga d’akin, don kansa ya fito waje ya d’auko ledan da ya d’an yi mata sayayya tare da attaching note ajiki ya koma ya ajiye mata dab bakin k’ofan nata sannan ya fita waje ya jira dawowan Mami, tana k’arasowa yace ze wuce, se anjima tayi masa sannan ta k’arasa ciki. Chan da Amal ta tabbata Afzal d’in ya tafi wajajen Maghrib ta bud’o k’ofan d’akin nata inda ta tarar da farar leda tsugunawan da zatayi ta d’aga se note d’in ya fad’i d’agawa tayi ta karanta kaman haka;

   ‘Here’re your favorites to light up your evening, I love you Xx.’

   Lek’a cikin ledar tayi taga favorite ice cream flavors nata ne da har sunyi melting da kuma chocolates, ciki ta koma ta ajiye ledan a d’akinta ta wuce bayi ta d’auro alwala sannan ta wuce kitchen dan ibo abinci. Achan suka had’u da Mami inda take ce da ita “Se yanzu kika ga daman fitowa?” Shiru ta mata bata amsa ba “Ga chan abincin alale na dafa.”

  “Sannu da aiki.”

  “D’azu Afzal yazo ai ko baki sani ba?”

  “Ban sani ba yaushe?”

  “D’azun.”

  “Allah sarki” tayi maganan tana serving kanta. “Seki kirasa.”

  “Toh” ta amsa tare da ficewa d’akinta. Instead ta kirasa kaman yadda Mami ta fad’a, bayan da ta idar da sallah taci abincin seta tura masa sak’o as ‘Thank you.’ 

    Suna zaune da Nazeefah sak’on ya shigo a farko yaso ya kirata amman sanin idan ya tashi a take Nazeefah na iya gano wani abun se kawai yayi replying nata as ‘You’re welcome.’ Da daren ranan Abdul ya kirata suka sha hira kaman ba gobe tasan ya kamatabace ta canza layinta saboda kar Abdul d’in yana samunta kaman yadda iyayensa suka buk’aceta amman ina baza ta iya ba, son zuciya baze barta ba. Bata son rabuwa da shi, shi kad’ai ne idan tana tare dashi take jin dad’i yake kuma sanyata mancewa da dukkan matsalolinta

   Washegari Afzal yayi timing dai-dai break time nasu Amal ya jesa school nasu. A gaban lecture hall nasu yayi parking sannan ya kirata a lokacin wayan na a hannun Maamah tana kallon pictures. “Gashi Ya Afzal na kiranki” ko kallonta batayi ba tace “Bar shi kawai na koma gida zan kirashi.”

  “Haba Amal rashin mutunci de ba kyau hungo ki amsa.”

  “Nace zan kiranshi anjima” Maamah bata saurareta ba ta d’aga wayan tare da manna mata a kunne seda Amal ta watsa mata mumunan kallo sannan tayi sallama. 

  “Wa’alaikumus salam” ya amsa. 

  “Yaya ina yini?”

  “Lafiya Lily, ya kike? Kin fita school ko yau d’inma kina gida?”

  “Ina school.”

  “Toh gani a gaban lecture hall naku.l

  “Yaya zan-“

  Gano neman excuse take yayi saurin katseta “Please come Lily.” 

  “Wai yaya?”

  “Wai yana waje inje in sameshi kinga shiyasa nace ki bari se idan na koma gida in kirasa.”

  “Amal running away from him won’t solve anything, da hak’ura kikayi kika bud’e mishi zuciyarki.”

  “Maamah it’s not that easy, I love Yaya amma ba so na soyayya ba Maamah Ya Abdul kad’ai nakeso.”

  “Na gane Amal but Ya Abdul ya miki nisa kema kin ba iya kasancewa tare zakuyi ba, beside time heals a hamkali zaki koyi sonsa, yanzu ki fita kije ki samesa kinji?”

  “Kefa? Mu je tare.”

  “Ni meya kaini shiga tsakanin masoya? Barni kurum zan wuce hostel yaso semu had’u achan.”

  “Maamah please kar kiyi mun haka mu tafi tare.”

  “Ji min ‘ya fa! Ya Afzal d’in bak’o ne? Abeg in zaki tashi ki wuce toh da ya fi miki.” Haka tak’i raka Amal, books nata ta tattara ta d’an kimtsa fuskan ta sannan ta fice. “Shine se an shanya ni haka za a fito Lily?” Yayi maganan bayan da ta shiga motan. 

   “I’m sorry ina copying abu ne da ka kira.”

  “Alright ya lectures toh?”

  “Alhamdulillah ya office?”

  “Very good only that I’ve been missing you haka jiya naje gida kika k’i fitowa.”

  “Yaya ba haka bane.”

  “Toh Yaya ne?” Yayi maganan lokacin da ya shiga tuk’i. “Are you still mad at me? Lily I’m sorry bazan gaji da baki hak’uri ba.”

  “Yaya komai ya riga ya wuce ka dena damun kanka” be sake cewa da ita komai ba har suka isa restaurant da zasu ci abincin. Beso suci a restaurants na cikin school ba gudun kar suci karo da Nazeefah. Sede sa6anin yadda Amal ta saba sakewa da shi tayita masa hira yau jugum tayi ko uffan bata ce da shi ba. Afzal ya rasa meke masa dad’i besan mey zeyi ba Amal ta kuma sakewa da shi kaman da, gashi da zaran ya gwada d’auko mata maganan Abdul se ranta ya soma 6aci. Haka nan da suka gama ya mayar da ita school sam ba walwala tattare da ita. 

   Haka fa Afzal ya koma tamkar bak’o ga Amal. Sam bata sakewa da shi, kominbyadda yaso su koma yadda suke a da abun ya gagara. Sede kaman yadda Mami tace masa kada ya kariya haka yake danne zuciyansa yana hak’uri. Duk randa he is free yakan d’aukota daga school suje suci abinci a weekends ma idan bashida abunyi ko kuwa idan Nazeefah ta fita unguwa shima se ya shirya ya kawo mata ziyara even though bata ta6a kawo masa hira saidai shine yata zuba ita ko tayi ta basa short short answers. 

  Tun dawowansa gida yau ya karanchi yanayin Nazeefah ya soya tayi lagwai kaman wanda baida lafiya. “Sannu da zuwa” tace dashi lokacinda ya shiga parlourn. 

    “Yauwa sannu” ya amsa. 

  “Your lunch is ready” ta sanar da shi.

  “Thank you lafiya? Ya naga ganki haka?” Yayi maganan had’e da zama gefenta akan kujeran data jingina. 

   “Lafiya nakega stress ne kawai kar ka damu.”

  “Are you sure?” Ya tambayeta yana ta6a jikinta don jin tempreture’nta. 

  “Yes karka damu” ta amsa had’e da yi masa murmushi. D’akinsa ya wuce ya watsa ruwa sannan ya fito yaci abinci sede be tarar da ita a parlourn ba, take ya yanke hukuncin ta shiga d’akinta ne. Shi kad’ansa ya zauna a parlour yana kallon sports har izuwa Maghrib. D’akinta yawuce inda ya tarar da ita tana kwance, k’arisawa ciki yayi tare da zama akan side drawer’n sannan ya shiga kiran sunanta. A hankali ta shiga amsawa “Tashi kiyi niyya lokacin sallah yayi.”

  “Nagode” kad’ai ta iya cewa sannan ya fice. Be dawo gida ba se bayan Isha rashin ganinta da beyi a parlourn ba kawai ya yanke hukuncin jikin nata ne daman tunda ya dawo ya ganta wani iri d’akinta ya wuce ya sameta kwance lamo akan gado. K’arisawa yayi ya zauna gefenta tare da ta6a jikinta sosai tempreture’n nata ya hau. 

  “Nazeefah you’re sick” ya yake hukunci. 

  “I fear I am” ta amsa murya ciki-ciki. 

  “Ya kikeji?”

  “Zazza6i” ta amsa a takaice. 

  “Bakiya fleeting d’akinki kwana biyu har sauro suka yita cizonki ko?” Kai ta gyad’a a hankali. 

  “Yanzu kin huta ai da malaria ya shigeki.”

  “I’m sorry” ta furta a hankali. 

  “Ba magani a gida barin fita in siyo miki.”

  “Ba seka fita cikin daren nan ba kabari ko zuwa gobe.”

  “So kike in zuba miki ido haka? Ina zuwa kinji?” Kai kad’ai ta gyad’a yayinda ya ja bargo ya rufeta da shi sannan yayi adjusting AC’n d’akin. Dai-dai yazo fita ta kira sunansa “Na’am wani abu ne?”

  “Thank you Allah ya kare.”

  “Ameen don’t mention” ya amsa tare da sakar mata da murmushi nan da nan ya d’au key’n motarsa ya fice. A pharmacy’n dake unguwansu ya samu maganin ya sai mata nan da nan ya komo gida ya d’au ruwa ya wuce d’akinta da shi knocking yayi sannan ya shige. Lokacin har tayi bacci zama yayi gefenta ya tada ita had’e da taya ta zama “Sannu ko?”

  “Har ka dawo?” Ta tambayesa. 

  “Eh na samu anan bakin layi kinci abinci?” Kai ta kad’a “Bari in d’ibo miki toh seki sha maganin naki.”

  “Bari zan sha maganin haka kawai bana son shinkafan.”

  “Toh an ta6a shan magani akan yunwa ne Nazeefah?”

  “Afzal ko naci hararwa zanyi shiyasa.”

  “Mey kikeso toh?”

  “Babu.”

  “It can’t be babu tell me , zaki ci indomie?l” Kai tayi saurin kad’awa “quarker oaths?” Nan ma kai ta kuma kad’awa “What of custards?”

  “Dama dama shi ma, bari zuwa anjima idan na d’an samu k’arfi zan had’a thank you so much Afzal.”

  “Bari zan had’a miki.”

  “Ka iya girki ne?” Ta tambayesa da mamaki murmusawa yayi “Halan ke kike mun da nake school.”

  Dariya ta saki kad’an “I’m impressed.”

  “Kwanta ki huta lemmi get it ready for you.” Kwanciyan tayi ya ja mata bargo sannan ya wuce d’akinsa ya rage kayan jikinsa ya wuce kitchen d’in. Nan da nan ya tafasa ruwa a heater ya had’a mata custards d’in ya kai mata. A farko yayi tunanin barinta ta sha da kanta amman tuna yadda tayita masa d’awainiyya sanda yayi targad’e hannunsa yasa ya canza ra’ayinsa. Da kansa ya zauna ya bata custards d’in seda ta shanye tas sannan ya 6allo mata magunan ta ya bata ta had’iye. Bayi ya rakata tayi alwala sannan tayi sallah ta koma ta kwanta. D’akinsa ya koma ya kammala aikin dake gabansa, chan wajajen goma ya watsa ruwa ya sanya shorts nasa ya d’au pillonsa ya zarce d’akin Nazeefah. Ba k’aramin mamaki tasha ba ganinsa da tayi rik’e da pillow. Bade anan yake shirin kwana ba saboda bata da lafiya? Haka kawai ta tsinci kanta cikin farin ciki. Kallon ne yaga ya soma yin yawa yace, “Ko in koma ne?” Cike da wasa. 

  “Ni yaushe nace haka?” Taya saurin tambaya. 

  “Toh naga kin k’i matsa min ne ai” yayi maganan sanda yake tsaye akan gadon. 

  “Gadon ma gabad’aya idan kakeso zan bar maka.” Murmushi ya sakar mata sannan ya ajiye pillonsa daga space da tayi masa providing. 

  “Do you need anything else?” Ya tambayeta kai ta kad’a da haka ya haura gadon ya sameta tare da kashe musu wuta. Jawota yayi a hankali izuwa jikinsa sannan ya furta “Goodnight Nazeefah.”

  “Goodnight Afzal I love you.” Peck yamata placing a hankali da haka har bacci yayi gaba da su duka. 

Leave a Reply

Back to top button