Hot romantic hausa novel complete

RANA DAYA COMPLETE HAUSA NOVELS PAGE 21 to 25

PAGE 2⃣1⃣*

  _Big sis🗣 (Maman Fadeel) where are you? I just want you to know that I’m devoting this entire page to you. Thank you for always trying to put a smile on my face, for treating me as if I’m one of your true little sis, know that your Lily loves you so much. XX 😘_

    Kasancewan jikin Nazeefah a gida Afzal yayi sallah ya jasu tare, bayan sun idar da sallan ne ya shiga shirin office inda tace zata had’a mishi breakfast. Take ya hanata akan ta kwanta ta huta tunda bata da lafiya, he can manage. Haka ya shirya ya had’a breakfast nasa ya ci sannan yayi mata sallama. Kaman yadda ya saba kiran Amal ko wani safiya haka nan ma yayi yau sede har yanzu Amal bata sakewa dashi sama-sama suka gaisa sannan ya katse.

   Da yamma bayan Amal ta dawo daga school ta la6e a d’akinta se hira suke a waya da Abdul not knowing Mami na la6e tana sauraronta tun d’azun. Ashe de har yau bata fasa waya da Abdul ba, shin wai meke damun Amal? Ta tambayi kanta, ace mutum an bada shi ma wani amma ya zauna yana hira da wani na daban? Bata yi mata magana ba ta koma ta cigaba da aikin dake gabanta. Bayan dawowan Papi ne ta zaunar dashi take fad’a masa abinda ke faruwa. Amal d’in ya kira bayan ta k’ariso take mai sannu da zuwa. 

  “Yauwa Mamana ya makaranta?”

  “Alhamdulillah.”

  “Nace yaron nan Abdul ai baku waya yanzu ko? Kuma kin canza sim naki kaman yadda iyayensa suka buk’ata?” Shiru Amal tayi dan ko k’aryan da takeson yi d’inma ta gagara, kum taji bakinta ya kullu. 

  “Baby?” ya kirata. 

  “Na’am Papi” ta amsa. 

 “Baki jini bane? Kode har yanzu kuna waya ne dashi?” Nan ma shiru. “Ba magana ake miki bane Baby?” Mami tasa baki. 

  “Eh Papi” ta amsa murya chan ciki-ciki. 

  “Haka kukayi da iyayensa? Ke bakisan cin amana kike ba yanzu Baby? Taya bayan an bada ke ma wani amma ki tsaya kina hira da wani na daban? Kina ganin kin kyauta wa shi Afzal d’in kenan Baby?” Shiru tayi ta kasa cewa komai yayinda take nazarin rabuwa da Ya Abdul. 

  “Iyye? Kina ganin kin kyauta masa kenan?”

  “A’a” ta kad’a kai a hankali. 

  “Toh kije na baki nan da kwana biyu ki canza sim kuma kar in sakejin kina waya da Abdul d’in kinji?”

  “But Papi-“

  “Ko baki jini ba? Har yaushe kike son ki cigaba da yaudarar sa? Kefa kikace kin amince zaki auri Afzal kodan ki biyasa alkhairin da yayi miki a baya yanzu kuma kice ba haka ba Baby?”

  “Papi bawai dena waya da Ya Abdul d’inne bazan iya ba, naga tunda ba auran Yaya zanyi ba yanzu ai ba laifi idan muna gaisawa da Ya Abdul, Papi dan Allah karkace a’a.”

  “Kaman ya Baby? Ni da na d’au da jimawa ma kin canza layin naki? Ke bakisan alkhairi ne miki ba idan kika rabu da Abdul d’in tun wuri, kema zaki fi samun kwanciyan haka shima a hankali Allah ze yaye masa son da yake miki kuma gaisuwa ne kad’ai kuke ko hirar masoya?”

  “But Papi-“

  “Ya isa haka Baby baki cika sa6awa dokokin da nake kafa miki ba, kar kiyi hakan yanzu nan da kwana biyu bana son in sake jin kina waya da Abdul idan kuma ba haka ba zan yima iyayen Afzal magana dama su basu k’i ko a satin nan a d’aura auren ba, se suzo ayi magana asa rana.”

  “Papi dan Allah kar kayi mun haka.”

  “Toh kiyi kaman yadda nace.” Kai ta gyd’a a hankali tana share hawayenta “Tashi ki fice Allah yayi miki albarka” ko amsawa batayi ba ruga d’akinta a guje ta baje kan katifarta ta shiga aikin kuka. Wayanta ta jawo had’e da shiga photos tana kallon pictures nasu tare da Ya Abdul yayinda kukan yaso yaci k’arfinta. Chan dare kaman yadda ya saba kiranta haka nan ya danna mata kira bata 6ata lokaci ba ta d’aga suka sha firarsu sam bata nun masa wai da akwai matsala a k’asa ba sede ko da yakeson yi mata seda safe tak’i amincewa ya katse wayan ita wai suyita hira kawai. Haka ya biye mata dukda cewan bacci yakeji, wayan suka yita yi har zuwa lokacinda ta zarce bacci se anan yayi mata goodnight yayi hanging call d’in. Washegari bayan ta taso daga school ta wuce Post office ta sai sabon sim sannan ta dawo gida. Video call ta dannawa Ya Abdul shi kansa beyi expecting ba dan tun tafiyansa sau d’aya da sukayi video call basu kuma ba. Haka nan tayita masa hirar shirme har seda kud’inta ya k’are sannan ya kirata suka cigaba har anan bata nuna masa cewan akwai wani abu ba. Da daren ranan ne bayan sun k’are wayan ta karya sim d’in ta sa sabuwa tana kuka haka ta zuba pieces d’in a bola. Ranan ko bacci batayi ba, kuka ta kwana tana yi washegari idanun nan sun kumbura tim ko school ta k’i fita. Dama normally kowani safiya da good morning text messages na Ya Abdul take tashi se gashi yau wayam ba komai. Ba yadda Mami batai da ita ta fito ta karya ba amman tak’i. 

   Shiko Abdul chan da yamma bayan ya dawo daga office yayi tunanin kiran Amal tunda shiru yau bata kirasa ba sede fa switched off layin nata ke ce masa. Be kawo wani tunanin a ransa ba yace ze gwada anjima, sede har zuwa dare Amal bata kirasa ba gashi ko ya kira switched off da wasa da wasa hankalinsa ya soma tashi. Sak’onni da dama ya tura mata amma ba response yau akeyinta! Danne zuciyarsa yayi yace bari ya bari zuwa gobe. Safe bim ya sake trying layin nata amma still baya shiga, hankalinsa idan yayi dubu be tashi ba shin meke faruwa? Wutansu ne ya 6aci kokuwa wayarta ta aka sace? Tunani de ba wanda beyi ba k’arshe da shirun yayi yawa ya yanke hukuncin kiran Maamah. Tana ganin call nasan tasan Amal ta canza sim ne kenan. Allah sarki Ya Abdul. 

   Sam bata so d’aga wayan ba amman gudun kar ya fahimci wani abun seta d’auka bayan sun gaisa yake tambayarta ko ta fita school yau. K’arya ta mai tace bata fita ba. 

  “Toh Amal fa kunyi waya da ita?”

  “A’a wallahi tun shekaran jiya rabon mu da muyi waya.”

  “Ikon Allah I’ve been trying to reach her but it ain’t going through.”

  “Toh kuma? Kasan wuta ya 6aci gabad’aya gari toh se a hankali nakega bata da chargi ne.”

  “Nima nayi tunanin hakan gobe zaki fita school ai ko?”

  “Ka manta gobe Saturday ne? Besides bani da lecture ma.”

  “Toh bazaki je gidansu ki duba mun ita ba?”

  “Ya Abdul ka kwantar da hankalinka mana ai Amal lafiyarta k’alau wuta ne ya lalace wayan nata ba chargi ka gane?”

  “Maamah are you sure?”

  “Dagaske amma sunce nan da sati ma zasu gyara.”

  “Anya kuwa zan iya jure sati banji muryan Amal ba? Ni kawai gobe kije gidansu ki had’amu.”

  “Allah sarki Ya Abdul zan raka Mama gidan biki fa kabari mana zuwa Monday.”

  “Mey zakiyi jibi da bazaki je ba?”

  “Naji Allah kaimu.”

  “Yauwa good girl nagode ko?”

  “Uhumm you’re welcome” hira kad’an suka ta6a sannan sukayi sallama. Wayan ta ajiye had’e da sauk’e nauyayyar ajiyar zuciya gabad’aya ta rasa ya zata 6ullowa al’amarin. Mama taje ta samu ta irga mata halin da ake ciki inda take shawatarta da komin yaya karta kuskura ta basa sabon layin Amal. 

  Kamar yadda Abdul ya shiga tashin hankali haka Afzal ma, barin ma shi da bashida clue sam gameda rashin samunta a wayan ya rasa dalili, layin Mami ya kira itama unavailable yake cemata. Beso kiran na Papi ba akan zuwa gobe zeje ya duba ta yaji ko lafiya. Sosai Nazeefah ta warware, washegari bayan sallan La’asr Afzal ya zarce gidansu Amal. 

  Mami da Papi ya tarar a tsakar gidan bayan sun mishi sannu da zuwa ya k’arisa suka gaisa sannan yake tambayar ko lafiya jiya throughout yana neman Amal amma ya kasa samunta. 

  “Bade bata baka sabon lambar nata ba?” Papi ya furta a hankali sede Afzal ya jiyosa saboda nisan kunnensa. 

  “Na’am?” Ya tambaya. 

  “Bata kiraka da sabon layinta ba?”

  “A’a” ya kad’a kai cike da rashin fahimta. “Sabon layi kuma?”

  “Afzal nasan kana hak’uri amma ka k’ara, kasan Baby yarinya ce tunaninta kad’an ne, bayan nan kuma shi rabuwa da masoyi zafi gare shi, gabad’aya na kasa gane kan yarinyar nan gashi kuma idan akace ta rabu da kai ta koma ga Abdul d’in setace a’a ita bata son abinda ze sake samun lafiyanka ta fita harkan Abdul d’in kuma abun ya gagara. Afzal bazan 6oye maka ba amma idan kasa wasa kana sakaci toh wallahi da k’yar idan zaka iya maye gur6in Abdul a zuciyanta, ban san wani irin makahon so takeyi masa ba. Ka sani yanzu ne kake da daman shiga zuciyarta tunda Allah yayi ta canza layin nata zasu daina waya.”

  Sosai Afzal yaji wa Amal, ba k’aramin tausayi take basa ba, yasan yadda takeji sarai saboda shima he went through such. Tunanin ya ze iya karkato da hankalinta akansa yake amma gabad’aya ya gagara. 

  “Papi Amal ta riga ta tsaneni, tsana har a fuska tana nuna mun, wallahi ina iya k’ok’arina don ganin nayi straightening relationship namu but she’s not willing to give me a chance I don’t know what to do again.”

  “Abba a gani na idan ba aure akayi ma Baby da Afzal ba, yarinyan nan baza ta ta6a amincewa da cewa Abdul yayi mata nisa ba” Cewan Mami. 

  lBut Mami makarantar ta fa?l Afzal yayi saurin tambaya kafin Papi yayi magana “Bana son maganan aure ya raba mata hankali.”

   “Hakane Afzal amma kuma akwai abin dubawa acikin abinda Mamin Baby ta fad’a, idan ba wai har rana taga an sa muku ba bazata ta6a fita daga harkan yaron nan ba tasan yanzu ba ita ba shi.”

  “Tabbas hakane Papi toh zan gwada yimata maganan inji mey zatace duk abinda akwai zan sanar da ku.”

  “Toh shikenan hakan ma yayi amma kam kayi sake haka kana ji kana gani ‘yar nan zatayi maka nisa.”

  “Toh zan wuce ko zan iya ganin Amal?”

  “Bari inyi mata magana” cewan Mami. 

 “Toh zan jirata a waje nagode sosai se anjima.”

  “Ka gaida gida” Papi ya fad’a masa. Da haka ya mik’e ya fice. Koda Mami taje kiran Amal akan cewa Afzal yazo yana nemanta, shareta tayi k’arshe seda Papi ya sa baki. Fuskanta ta fito ta wanke sannan taje ta samesa lokacin har ya gaji da jirarta. 

  “Yaya ina yini?” Ta gaishesa daga chan nesa yayinda yake zaune kan benchin sa na kullum. 

  “Fa bazan amsa gaisuwan nan ba sekace wani bak’o Lily? K’ariso nan mu zauna kinji?” Bata mai gardama ba ta k’arisa ta zauna a gefensa. 

 “Meya faru fuskanki ya kumburo haka?”   

  “Babu” ta amsa tana tare fuskan nata. 

  “Dan ance se kin fito shine kike kukan nan Lily?”

   “Yaya ba haka bane.”

  “Lily I’m sorry for making you hate me if you can’t love me back please tell me.”

  “Yaya wani irin magana kuma kake? Har na isa ince bana sonka ne?”

  “Gashi kuwa sede a bakin Papi zanji kin soya layinki you had zero intention of notifying me koba haka ba?”

 “Jiya fa na canza layin ko Maamah ma ban bata ita ba, ba wanda na kira da ita.”

  “Toh shikenan dama magana nakeson miki.”

  “Ina jinka.”

  “Is it okay with you in turo su Abba for formal introduction?” Wani irin wawan fad’i gabanta yayi bade yanzu Afzal ke shirin auranta ba?  

  “Lily?”

  “Yaya…” se kuma tayi shiru. 

  “Talk to me kinji? Ki fad’a mun ra’ayinki I’ll do only as you wish Lily.”

  “Yaya Nazeefah fah? Yaya bana son shiga tsakaninka da matarka bana son tashin hankali.”

  “And who said by agreeing to marrying me zaki shiga tsakani na da Nazeefah? Ke daban ita daban karki damu da ita zata fahimci al’amarin namu in shaa Allah.”

  “Yaya what of my studies? Kaifa kace baka son abinda ze raba mun hankali dangane da karatu baka tunanin auran nan will be a great distraction to me? Yaya I’m sorry amma ban shirya da yin aure ba yanzu.”

  “Is this just how much you don’t want to be with me Lily? Yanzu inda Abdul ne yace ze turo ai bazaki ce masa haka ba ko? Shikenan ba matsala dama ra’ayinki kawai nakeson ji saboda in sanar dasu Papi. Kina iya komawa ciki” yayi maganan yana sa hannunsa cikin aljihu, wata envelope ya zaro ya sa mata a hannu. Kafin tace zatayi masa godiya har ya k’arisa cikin motansa yana k’ok’arin tada ita. Seda taga ficewansa sannan ta k’arisa ciki. Ko mutum be tambaya ha yasan ransa ya 6aci, daga yadda yayi magana ma. 

   Kud’in ta mik’awa Mami akan gashi Afzal ya bata. Zaunar da ita Mami tayi “Baby?”

  “Na’am?” Ta amsa. 

  “Yanzu kina ganin kina kyautawa Afzal kenan?”

  “Mami ni kuma mey nayi?”

  “Kisani wallahi koda ba don istikharan nan da kikayi ba, bawanda ya cancanci soyayyarki sama da Afzal ki tuna da kalan hidiman da yaron nan ya miki ba ke kad’ai ba harta ni da Papinki. Be sanmu ba, besan daga ina muke ba amma ya d’au nauyin karatunki, kud’in takardu da handouts tun kafin ki tambaya yana baki amma ace kike wulak’antasa haka Baby? Wallahi samun mutum kaman Afzal a zamanin yanzu se an tone. An sani rabuwa da masoyi da zafi amma yaci ace kin yayyafawa zuciyarki ruwan sanyi be kamata ace har ki bari Afzal ya fahimci cewa bakiya sonsa ba.”

  “Mami ni yaushe nace bana son Yaya? Wallahi ban ta6a furta hakan wa kowa ba.”

  “Amma haka halayyanki suke nunawa abinda nake fad’a kenan. Kuka ne kawai be min ba ranan gabad’aya kin tada masa hankali har yake cewa shi ze hak’ura kawai a dawo maki da Abdul d’in haba mana Baby ki sani fa ba duk abinda mutum keso yake samu ba a duniyan nan. Yanzu gashi duk da kalan rashin mutuncin da kike masa hakan be hanasa baki kud’in k’arshen watan ki ba harda k’arin dubu ashirin akai.”

  “Zan kirasa inyi masa godiya.”

  “Da kin kyauta dan babu dad’i hakan kiyi hak’uri ki sani Abdul ya riga ya miki nisa ki bud’ewa Afzal zuciyarki sanin kanki ne Afzal baze ta6a cutar dake ba.”

  “Mami na sani.”

  “Toh kina iya tafiya Allah yayi maki albarka.”

  “Ameen” da haka ta wuce d’akinta. Wayarta ta d’auka ta kira Maamah se a karo na biyu ta d’aga kasancewar bata san layin ba. 

  “Halo Maamah? Amal ce.”

  “Amal? Ya kike.”

  “Lafiya k’alau ya kwana biyu?”

  “K’alau ai na d’au nima baza a nemeni da sabon layin bane.”

  “Haba Maamah ya gida?”

  “Lafiya k’alau jiya Ya Abdul ya kirani wai baya samun line naki.”

  “Allah sarki Ya Abdul I miss him already please komin ya za’ayi karki basa sabon layi na bana son in cigaba da zolayansa Maamah, ina tausayawa kaina but I pity Ya Abdul the most.”

  “Haka ma Mama tace.”

  “Maamah I’m so sorry for hurting your brother.”

  “Ba komai Amal ai yin Allah ne ba naki ba.”

  “Thank you so much for everything.”

  “You’re welcome.”

  “Toh sekiyi saving numban nawa se mun had’u a school ran monday.”

  “Alright I’ll” da haka sukayi sallama bata kaiga ajiye wayan ba sega call na Ya Abdul. Ko gaisawa be bari sunyi ba ya hau kurareta akan tabar duk abinda takeyi taje gidansu Amal taji ko lafiya haka kawai yana ji a jikinsa ba k’alau ba. Corner-corner tayita masa akan yau bazeyi ta fita ba seko gobe haka nan ma washegarin daya kirata tace ai taje gidan su Amal d’in Mami tace bata gida amma lafiyarta k’alau. Matuk’a hankalinsa ya d’an kwanta na jin lafiyanta k’alau amma rashin jin muryarta hankalinsa ya kasa kwanciya gabad’aya. 

  Amal ko sosai take kewansa sede gabad’aya ta rasa me take ciki, sosai maganan da Mami tayi mata keta yawo mata a kai tun jiya se tunanin magann take gashi har yau bata kira Afzal d’in ba seta d’au wayan zata kirasa se ta fasa. Haka tayita yi har tazo ta kirasa k’arshe. A lokacin suna tare da Nazeefah suna kallo, ya tashi ya amsa yana gudun kar ta fahimci wani abun, yayi rejecting call d’in kuma baze iya ba haka kawai ya rufe ido ya d’auka. 

   “Assalamu Alaikum” ta soma da cewa. 

  “Wa’alaikumus salam” ya amsa sa6anin yadda ya saba kiranta da Lily yau sallamar kad’ai ya amsa ita ko se ta d’au kodan abin da tayi masa ne yake fushi. 

  “Yaya I’m sorry” ta furta chan ciki-ciki. 

  “Ba komai karki damu.”

  “Dama na kira ne inyi maka godiya tun jiya ina trying numbanka baya shiga” tayi mai k’arya. 

  “Ayya bakomai.”

  “Wannan ne new line nawan se kayi saving.”

  “Alright I’ll se anjima” nan ya katse, da mamaki Amal ta tsaya kallon wayanta yau har Yaya ne ya katse waya a kanta? Hmm

   Nazeefah kuwa kallon sa ta tsaya yi tana nazari kode da budurwansa yayi wayan ne? Kud’i ya bata ne take godiya har yake cewa ba komai? Amma kuma ai idan budurwarsa ce baze bari ma ya amsa wayan a gabanta ba, toh ko business colleague tasa ce?

   Kwana hud’u Maamah ta jera tana raina wa Ya Abdul wayo tun be d’auki abun da zafi ba har ya fara zaton wani abun daban. K’arshe da abun ya ishesa Mama ya kira yake ce mata gashi kwana biyu baya samun Amal yayi da Maamah da ta had’asu amma abun ya gagara inda hali please ko ma waye ne asamu a tura gidansu Amal d’in aji ko tana lafiya, Mama bata nuna masa komai ba tace washegari zata tura ayo bincike se anan hankalinsa ya d’an kwanta sede har gari ya waye rana ya sauk’a Mama bata kirasa ba duk yadda ya k’osa haka ya hak’ura ya bari se a jibi sannan ya sake kiranta itama wani hujjan ta nema ta sake basa. Haka suka yita waina sa, suna masa wasa da hankali ba wanda ya iya fitowa fili ya sanar dashi zahirin abinda ake ciki, ta fannin Amal kuwa duk yadda take missing d’insa hakan besa ta d’au waya ta kirasa ba dukda cewan bata k’i hakan ba. So dayawa takan zuba numbansa da niyyan zata kirasa amma idan ta tuna da fad’an Mami na ranan seta fasa. Sosai fad’an ya shigeta haka ko tana kewansa sede ta rufe kanta a d’aki ta sha kukanta amman bade ta kirasa ba. Hotunansu kuwa har yau ta kasa gogewa haka zata zauna tana kalla tana kuka. 

  Ta fannin Afzal kuma tun kan amsan da Amal ta basa ranan akan cewa ita bata shirya auransa ba gabad’aya ya rasa walwalansa ko kiranta be sakeyi ba, a gida kuwa ba yadda Nazeefah batayi da shi ba amman yak’i sanar da ita halin da yake ciki haka ya bari abin yayita chin sa har seda wani attack d’in yaso kamasa. Daga fitan Nazeefah d’auko masa ruwa dawowan da zatayi kawai ta tarar da shi zube a k’asa se birgima yake yayinda ya rik’e saitin zuciyansa inda yake masa k’una sosai, se wani sama-sama numfashinsa ke masa. Salati tasa yayin da yasar da goran ruwan a k’asa ta nufi kansa da gudu tana k’walla masa kira. 

  Kafin ta tashi tace zata nemi mai gadi dan yazo ya d’aukesa su kaisa asibiti ya rik’e hannunta. “Don’t call Ummi..” ya furta da k’yar yayin da ya shiga yin tari. 

  “Afzal so kake ka mutu ne? Barin kira D’an ladi stay calm kaji?” Ta buk’acesa a rud’e “Don’t call Abba too please” ya rok’eta kai tayi saurin gyad’a mai sannan ta kira D’anladi nan da nan ya cicci6esa suka yi mota. Akan cinyarta ta ajiye kansa yayinda take ta kuka ganin yadda yake wasu irin abubuwan wane wanda ake cire ma rai. 

   Sintiri ta rink’ayi bakin k’ofan nasa gabad’aya ta rasa me take ciki gashi yace mata karta kira su Ummi shin ta biye masa ne ko ta kira sun? Amma kuma tasan halinsa sarai ba k’aramin aikinsa bane idan ya farfad’o ya gansu akansa yayi mata fushi. Haka nan ta rasa me take ciki chan da likitan nasa ya fito ta nufi kansa tana tambayansa ya jikin nasa. 

   Ya buk’aceta ne da ta kwantar da hankalinta Allah yaso an samu an kawosa asibitin da wuri tun kafin heart d’in yayi failing, an kuma basa immediate treatment yanzu sauran a jira farfad’owansa nan da kaman minti ashirin haka. Hamdala ta saki yayin da ta shiga yi masa godiya. Bayan sa tabi ta shige d’akin Afzal inda ta tsince sa kwance kan gadon, wane wanda k’wai ya fashewa a ciki haka sid’ak-sid’ak ta k’arisa ta zauna kan kujerar dake gefen gadon nasa yayinda hawaye ya ciko mata dam a ido. Sunansa da tace zata kira kawai se hawaye. Kuka sosai ta sha wajen ta rasa me ke janyo masa bugawan zuciyan, komi da ta sani baya so tana iya k’ok’arin dainawa amma ace ciwo yak’i ci yak’i cijewa? Ita abu d’aya take gudu ranan da zuciyar nasa zata buga gabad’aya tak’i aiki tasan ko sama da k’asa zata had’a ba wanda ze ta6a amincewa akan ba ita ce sanadin ciwon nasa ba. Tana cikin kuka ba makawan ne Afzal ya shiga kyafta idanunsa har ya bud’e su gabad’aya. Da mamaki ya tsaya yana kallon yadda take kuka gabad’aya se ta basa tausayi.

   “Afzal” ta kira sunansa a hankali ko amsata ya kasa. “Dan Allah idan wani abun nake maka wanda ka kasa furta mun please tell me I’m tired of seeing you collapsing everyday like this idan wani abun nakeyi maka wanda baka jin dad’insa please tell me.”

  “Nazeefah” ya kira sunanta cikin dashasshiyar murya. 

  “Please tell me Afzal I promise zan yi iya k’ok’ari na inga na kiyaye.”

  “Bar kukan haka kinji?” Yayi maganan yn neman share mata hawayen nata. Fuskan nata taja baya “Not until you tell me mey ke jawo maka attck haka please tell me idan nice.”

  “Bake bace bar kukan haka.”

  “How can I? Bazan iya ba Afzal so kake se idan ka mutu kowa yace nice na kashe ka? Dan Allah ka tausaya mun ka fad’a mun matsalar.”

  “Nazeefah nima han sani ba all I want is ki kwantar da hankalinki baki da alak’a da rashin lafiya na kuma ko a gaban waye me zanyi defending naki kinji? Stop bothering yourself like this.”

  “Then mey ke jawo maka?”

  “Nazeefah I’m sorry but I can’t tell you.”

  “Afzal nasan ba wani jituwan kirki bane a tsakaninku nasan nayi maka laifuka da dama I know I’m not the perfect girl for you, amma matarka nake kodan wannan matsayin please tell me.”

  “I can’t Nazeefah” ya sanar da ita. 

 “Saboda ban kai inji damuwanka ba?”

  “Sam, saboda nima ban san meke damuna ba, I have no idea why.”

  “Ban yarda da hakan ba Afzal tun ba yau ba nasan kana 6oye mun damuwanka zan cigaba da addu’ har izuwa rananda zaka fara fad’amun damuwanka I believe mey hak’uri shi kan dafa dutse ya sha romo, I love you Afzal I’ll do everything to stay by your side this’s how much I love you.”

  “Thank you Nazeefah, come here” hannunsa ya bud’e mata a kasalance, a hankali ta shige jikinta dai-dai saitin k’irjinsa ta aza kanta yayinda ya rufeta da hannayensa yana mey shafa bayanta a hankali. “Forgive me for hurting you this much? I’m so sorry.” Kai ta gyad’a masa a hankali yayinda ta sake shigewa jikinsa tana mey cigaba da kukan da takeyi. A nitse ya d’agota had’e da share mata hawayen ta “Kin kira su Ummi?”

  Kai ta kad’a “Kace kar na kirasu.”

  “Very good thank you so much Nazeefah Allah miki albarka.”

  “Ameen” kafin tayi wani k’wak’k’waran motsi wayanta ya shiga ruri dubawan da azatayi taga Mummy ke kira. “Waye ne?” yayi saurin tambayarta. 

  “Mummy” ta amsa cike da fargaba. 

  “Ki d’auka.”

  “What if tana gida taje duba mu ne fah?”

  “D’auka kice mata mun fita.” Hakan ta d’aga Mummy take ce mata gata da Khhaleefah bakin gate sunata honk amma ba kowa. Kaman yadda Afzal ya buk’ata haka tayi tace mata sun fita ne D’anladi kuma yaje duban gida. 

   “Can I use your phone to call Sultan?” Ya tambayeta bayan da ta kammala wayan. 

  “Sure” tayi maganan tana mik’a masa “Amma banida numbansa.”

  “Don’t worry I have it off hand.” Numban Sultan d’in ya zuba ya kirasa. 

  “Halo Sultan?”

  “Triple A?”

  “Yes Sultan kana ina?”

  “Office ina ka ajiye wayanka inata kiranka baka d’auka.”

  “Kazo TH please.”

  “Subhanallah bade jikin naka bane?”

  “Yes but da sauk’i and please don’t tell Umma banason su Ummi suji ina asibiti nima yanzu zance suyi discharging d’ina come quickly.”

  “Alright I’m on my way.” 

  Be 6ata lokaci ba ya kar6i excuse a office ya kama hanyan TH saidai kafin nan ya kira Amal yasan sarai itace sanadin komai. Tana d’agawa yake sanar da ita ai Afzal ya sake samun wani attack d’in yanzu haka ma yana TH an rik’e shi. Sosai gabanta ya fad’i salati kawai ta shiga yi har Sultan ya ajiye wayan. Yanzu mey zatace wa su Ummi? A banza tana neman kashe musu d’a. Bata jira lectures d’in ya k’are ba ta tattara jakarta ta fice kasancewar university da TH ba nisa kusan a tare ita da Sultan suka isa tana sauk’a a napep se gashi yana k’ok’arin shiga shima. K’arisawa tayi cikin motan nasa suka shiga tare. A waiting room yace ta jirasa gudun kar kuma suna shiga suci karo da Nazeefah. Bayan ya k’arisa d’akin Afzal suka gaisa da Nazeefah sannan ta basu waje. 

   “Amal ce har yanzun?” Sultan ya soma da tambayansa. 

  “Sultan haka so yake?” Ya tambayesa a raunane. “Tunda nake ban ta6a son wani mahaluk’i sama da iyayena a duniyan nan ba, ban san haka so yake da sharri ba da nayi duk abinda zan iya na hana son Amal shigewa zuciyana.”

   “Triple A…”

  “Sultan I’m tripping” ya katsesa, “Ban san ya zanyi da son Amal ba, ina sonta amma kona second d’aya bata sona, bata da niyyan bani daman in kasance masoyinta. she disperses me Sultan help me out please, ina jin idan ban samu Amal ba ina iya rasa rayuwana.”

  “Calm down Afzal, meya faru?”

 “Komai ma ya faru ni yanzu nakega kawai zan hak’ura ne zan nemi transfer in d’au Nazeefah mu bar nan kawai maybe by doing so Allah ze rage mun sonta a zuciya, gar da gar ta nuna mun she can’t marry me ya kake tsammanin zanji? I’ve tried my best to forget it but I can’t, da kalamunta kullum nake tashi nake yini, I’m mad over her. And to be frank, I’m tired of seeing Nazeefah like this, gabad’aya ta d’au laifin komai ta d’aura wa kanta, na gaji I don’t know what to do again.”

  “Mun taho tare da Amal” ya sanar dashi.

  “You what?” Ya tambayesa cike da d’umbun mamaki. 

  “Yes tana waiting room, kana kirana itama na kirata se muka k’ariso tare.”

  “Why? Meyasa ka kirata? So kake su had’u da Nazeefah? Maza why?”

  “Saboda tasani idan ta cigaba da abinda take yi maka tana iya jefa rayuwarka cikin matsala.”

  “And? Ba wai kaman ta sona bane bale idan rayuwan nawa ya shiga matsala hakan ya dameta.”

  “Taya zakace Amal bata sonka Triple A? Ai zuciya bata ta6a k’in me kyautata mata ya kamata ka gane cewa Amal na duk abinda takeyi ne saboda haushinka da takeji na shiga tsakaninta da Abdul amma bayan nan wallahi ko ita bata isa ta buga k’irji tace bata sonka ba.”

  “Wai kam bakaji me ta fad’a mun bane? Amal bata sona.”

  “Amal na sonka Afzal she’s just too broken to realize that, gabad’aya soyayyar Abdul ne ya rufe mata ido aikinka ne ka maye gur6insa a zuciyarta idan ko kayi sakaci kana iya rasata har abada amma so kam akwai shi achan k’ark’ashin zuciyarta.”

  “Ko meyasa kace haka?”

  “Da bata sonka da baza tabar duk abinda takeyi ta iso nan atake da na kirata ba, and you know the funniest part? Ta jirani a waiting room d’inma tak’i wai sam semun k’ariso tare, kallo d’aya mutum zeyi mata yasan tana cikin tashin hankali. Gabad’aya ta rasa natsuwarta a haka zaka ce bata sonka? Yanzu that aside, ya za’ayi in shigo da ita?”

  “I don’t know nide bana son su had’u da Nazeefah ban shirya ma wani masifan ba.”

  “Kasan ya za’ayi? I’ll call Nazeefah se kace mata kana jin yunwa taje tayi maka girki kafin ta dawo de nasan Amal harta tafi.”

  “Sultan nifa bana son su had’u.”

  “Trust me” yana fad’in haka ya fice ya kira Nazeefah akan Afzal na nemanta. 

  K’arisowa tayi ta tsaya a kansa tana shafa kansa a hankali “Kana buk’atan wani abu ne?” Ta tambayeshi a maraice. 

  “I’m hungry” ya sanar da ita. 

  “Mey kakeson ci?” A farko yayi niyyan cewa stew tuna akwai stew a gida seyace spaghetti. 

  “Toh bari D’anladi ya zo ya kaini gida inyi sauri in had’a maka, shikenan ko kana buk’atan wani abu?”

  “Shikenan.”

  “Alright I’ll be right back.”

 “Thank you.”

  “Don’t mention” murmushi kad’an ta sakar masa sannan tayi sallama da Sultan ta fice. Nan suka samu suka shigo da Amal. 

  Tana shiga ciki tayi kan gadon nasa a guje had’e da rushewa a gabansa tana kuka sosai sede ko kallonta Afzal beyi ba. Kukan tayita yi chan ta d’ago kanta ta shiga basa hak’uri. “Yaya I’m so sorry please kar ka mutu.”

  “Bakiya son ya mutu kuma kike wulak’antasa haka Amal? Afzal d’in? Bari in kira su Mami in sanar dasu halin da kika jefasa daga nan se asan nayi idan ma rabaku za’ayi toh don da shi zefi alkhairi ma because bazan iya jure ganinki kina destroying min life na amini ba, Amal baki san idan kika cigaba da hakan ba kija iya zamewa sanadin mutuwansa ba?” 

  Kuka take sosai tace, “Ya Sultan please don’t call Mami wallahi tana iya kasheni da duka kuma ya kake magana haka? Sanin kanka ne Yaya yafi k’arfin in wulak’antasa.”

  “Kuma shine kike wulak’antasa hakan?”

  “Ni ban wulak’anta Yaya ba, sanin kanka ne ina son Yaya, Yaya please say something.” Sede ko kallonta Afzal be juya yayi ba. 

  “Toh ai ba haka ake so ba Amal kowa ya sani rabuwa da masoyi da ciwo amma ya zamo dole ki hak’ura tunda an riga an bada ke wa Afzal ko ba haka ba?” Kai ta gyad’a a hankali. 

  “Yanzu haka iyayensa basu da labarin yana asibiti saboda baya son ya had’a kanku amma still kina wulak’antasa haka? Sanin kanki ne Afzal na sonki I don’t have to tell you.”

  “Ya Sultan I’m sorry dan Allah kayi hak’uri.”

  “Ni baki yi mun komai ba Amal, Afzal zaki bawa hak’uri let me excuse you two” daga fad’in haka ya mik’e ya fice tare da ja musu k’ofan. Shiru ne ya rufesu a d’akin Afzal yak’i yayi magana itama Amal tayi shiru bata sake cewa komai ba. Chan ta numfasa had’e da kiran sunansa. 

  “Yaya please ka juya ka kalleni kaji? Yaya I’m sorry please look at me” ganin har yanzu be juya yako kalleta ba ai seta rushe da kuka wajen. Kuka sosai take tun Afzal na iya jure sautin kukan nata har abun ya gagara, be san a lokacinda ya juyo yana kallonta ba don kukan Amal ba k’aramin tada masa hankali yake ba. 

  “Yaya I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri please don’t go and leave me, I’m here please don’t go.”

 “You’re not here Lily, you’re never here. You don’t love me, you don’t even care about me baki damu dacna rayu ko na mutu ba. Lily nasan ni mey laifi ne but I’m sorry, bazan kuma gaji da baki hak’uri ba but please ki amince ki aureni, Lily bazan iya rayuwa ba ke ba you’ve become a part of who I am that I can’t do without, you complete me, I feel so incomplete and lost without you. Lily idan baki kasance mallaki na ba ina iya rasa rayuwa na. I’m sorry but I love you, I love you morethan life itself, your love runs in my veins duk yadda naso 6oye soyayyarki hakan ya gagara, duk yadda na so cireki daga zuciyana nakasa, Lily I was created for you. Nazeefah might be my wife but you’re my home, my soul, my happiness and life, please don’t let me go astray.”

  By now kuka Amal take sosai. A hankali kalamun Afzal suke shigewa jikinta suke kuma tasiri, tabbas ba k’arya ko d’aya acikin kalamunsa tasani batada masoyi sama da shi abu d’aya yake hanata sakewa da shi idan ta tuna yadda ya rabata da Abdul sede kuma da ta zauna tayi tunani, seta gano komi na faruwa ne saboda dalili. Allah nada dalilin daya ya turo Abdul rayuwarta ya kuma ciresa a lokaci guda, dalilin kuwa itace ta sani cewa ba duk abinda mutum yakeso yake samu ba a rayuwa. Hawayenta ta shiga sharewa a hankali ta soma da cewa;

   “Rana d’aya Allah ya kawo ka cikin rayuwana Yaya, acikin k’azanta da yarinta ka ganni ka kuma ce kana sona, baka sanni ba, baka san daga ina na fito ba, bakasan suwaye dangi na ba ka nuna min so da k’auna ka kuma ja ni jiki tamkar k’anwar ka ta jini ka k’ara bani daman kiranka Yayana. Rana d’aya bayan na cira ran zan sake komawa boko ka dawo mun da mafarki na ka nuna min everything is possible with you and God, ban ta6a neman abu na rasa a k’ark’ashinka ba Yaya. Damuwa na tun kafin in furta kake yaye minsu, baka wasa da sha’ani na komai nakeso shi kake mun taya bazan so ka ba Yaya? Idan nace bana sonka wallahi na zama mak’aryaciya but I love Ya Abdul too, ina sonshi amma bawai hakan na nufin ina shirin rasaka bane. Ina iya sadaukar da raina maka Yaya, batun maganan mu na ranan kuma ina sake neman gafararka kayi hak’uri na baka amsa bisa rashin tunani da shawara da nayi. Yaya idan har aurena ne ze farinta maka rai then I’m ready to be your wife, ko a yau kakeson in kasance matarka na amince zan aureka but please ka dena tada hankalinka a kaina haka bana son abinda ze ta6a lafiyanka bana son a sanadi na ka rasa rauwanka, dan Allah ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi ka sani I’m only yours and no one else’s.”

   *PAGE 2⃣2⃣*

      Har cikin ransa yaji dad’in kalamunta dukda cewan ya san ta fad’i komai ne don kawai yaji dad’i bawai don har cikin zuciyanta tana nufin hakan ba, yasani tausayinsa kawai takeji bawai sonsa take ba. 

  “Yaya why are you not saying anything?” Ta tambayesa a sanadin shirun da yayi. “Dan Allah kayi hak’uri.”

  “It’s okay Lily you should get going thank you.”

  “Yaya fushi kake dani har yanzu?”

  “Sanin kanki ne komin mey kikayi mun bazan ta6a iya yin fushi dake ba Lily.”

  “Shine ko kallona bazaka juya kayi kace ka hak’ura ba?”

  “Will it change anything?” 

“Please Yaya kayi hak’uri Wallahi bazan iya jure fushinka ba.” 

  “Toh na hak’ura” ya fad’a had’e da juyowa yana kallonta kaman yadda ta buk’ata. “Bar kukan haka toh” hannu tasa ta shiga share hawayenta. 

  “Thank you so very much, barin koma toh Allah k’ara sauk’i.”

  “Ameen thanks too bari inyi ma Sultan magana ya kaiki gida.”

  “A’a no need daga school nake zan koma I still have one lecture to attend” tayi maganan tana duban agogon hannunta. 

  “Are you sure?”

  “Yes Yaya” ta amsa had’e da sakar masa k’aramin murmushi. 

  “Alright you take care” a waje ta tarar da Sultan tayi masa sallama sannan ta fice. 

  Bada dad’ewa ba Nazeefah ta kawowa Afzal abincin, bayan ta basa ya ci ya buk’aci Dr’n da ya sallamesa. 

****

   Ta fannin Abdul kam k’aramin hauka ne kawai beyi ba, yau ko fita office ya kasa, banda tunanin Amal ba abinda yakeyi, gabad’aya ya rasa mey ke masa dad’i yau kwana nawa amma a rasa wanda zeje ya duba masa lafiyar Amal? itama Amal d’in kwana nawa yau amma bazata nemesa ba? Anya kuwa lafiya? Tunani de ba wanda beyi ba. Toh kode su Mami sunyi mata miji ne a gida suka hanata yin waya dashi suka amshe mata wayan ma gabad’aya? But ai bazasu ci amanar sa haka ba bayan seda ya tura su Baba da su sanar dasu shi yayi kamu then what could be the problem? Kwana yayi yana nazari, washegari da yamma ya kira Maamah. Har tsoron picking call d’in take amman haka ta d’aga don ba yadda ta iya. 

   “Maamah what is going on?”

  “Game da mey Ya Abdul?” Ta tambayesa tamkar bata fahimci inda ya dosa ba. 

  “Please tell me meke faruwa meyasa line na Amal baya shiga?”

  “Ya Abdul ban san-“

  “Maamah we both know you’re lying sarai kinsan meyasa, dan Allah nace please tell me it’s been over a week bana samunta har Mama nasa aje aji mun ya take amma shiru. I can smell it something is not alright.”

  “Ya Abdul-“

  “Ki fad’a mun kinji?” Ya katse ta “Idan ma abu ne yasamu Amal d’in kuke 6oye mun just tell me I promise bazanyi reacting ba.”

  “Ya Abdul ba abinda ya samu Amal, lafiyarta k’alau.”

  “Then meya faru? Meyasa bata picking call d’ina?”

  “Ya Abdul I’m sorry.”

  “Fad’a mun kinji? Kar kiji komai.”

  “Kayi hak’uri amma bazan iya ba.”

  “Meyasa?”

  “Na d’au alk’awarin komin yaya baza aji mutuwan sarki daga bakina ba, kayi hak’uri.”

   “Aure Amal zatayi ko?” Ya tambayeta a hankali daga yadda yake magana mutum zesan zuciyarsa a karye take, sosai ta sha mamakin yadda ya gano hakan ba tare da wani ya sanar da shi ba. 

  “Ya Abd-“

  “Aure zatayi ko?” Yayi saurin katse ta “Just answer me.”

 “Ya Abdul I’m sorry.”

  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” taji ya furta. “Meyasa baki fad’a mun ba Maamah?”

  “Nima labarin be dad’e da iske ni ba.”

  “Ban yarda ba Maamah, dalilin da yasa Baba suka turoni nan dan Amal zatayi aure ne ko?”

  “Ya Abd-“

   “Just tell me yes or no kar kiyi mun k’arya” ya buk’aceta. 

  “Yes” ta furta a hankali “Amm-” be bata daman yin magana ba ya katse wayan. Nan take ta shiga kiransa sede tuni ya kashe wayan gabad’aya. Wajen Mama ta ruga aguje tana mata kuka “Mama Ya Abdul ya gano gaskiyan al’amarin he knows everything.”

  “Kaman ya? Ban fahimceki ba.” Nan ta kwashe duk yadda sukayi da Abdul ta zuba mata. “Jeki ki d’auko mun waya a d’aki yi sauri.” Nan da nan taje ta d’auko ta kawo mata, layin Abdul ta shiga kira duka biyu amma switched off kukeji. Tirk’ashi idan hankalinta yayi dubu be tashi ba. Baba ta kira a office take sanar dashi halin da ake ciki, dama ya sani komin jimawa wataran Abdul ze gano gaskiya don haka ya buk’aceta da ta kwantar da hankalinta zeyi ma abokinsa dake chan wanda ya samowa Abdul aikin da yaje ya dubasa. Har anan hankalin Mama be kwanta ba, Maamah kam se kuka takeyi. 

  Tunda ya kashe wayan nasa ya shiga aikin kuka, kuka yake sosai kaman d’an yaro yayinda zuviyarsa keyi masa k’ona, ji yayi komi ya fita masa a rai, ina ma ba a k’addaro masa da wannan rana ba. Shikenan shi kuma tasa jarabawar kenan? Akan ‘yan matan da yakeso? Until when ze samu sanyin idanunsa tunda gashi Amal da yake sa ran kasancewa da ita har k’arshen rayuwansa ma ta tafi ta barsa. Wai shin meyasa be gane gaskiyan al’amarin bama tun a farko? Ai da abun tambaya yadda duk cikin fad’in gun aikin nasu aka d’aukesa k’walli d’aya tal aka basa appointment letter’n. Da akwai abin tambaya game da yadda su Baba da ita kanta Amal d’in suka nace cewan lalle-lalle seya kar6i aikin. Meyasa be gane cewa aure Amal zatayi ba tun daga kan lokacin da ta soma yi masa kuka a waya haka kawai ba dalili har izuwa ranan daya tafi, kukan da ta keyi yafi k’arfin ace wai kawai na rabuwa da masoyi ne, ashe na zafin rabuwa dashi gabad’aya ne. Meyasa? Meyasa bata sanar da shi ba? Meyasa su Baba suka yita zolayarsa suka k’i sanar da shi gaskiyan al’amarin? Mey yayi zafi da har se sun turosa Canada? Gabad’aya he felt used and abandoned. Ganin kukan baze amfanar dashi da komai ba ya mik’e a raunane ya shige bayi inda ya bud’e shower akansa ruwan na zuba wala Allah hakan zey sanya sa mancewa da d’umbin matsalolinsa. 

   Ranan Abdul beyi bacci ba, se tunanin yadda Amal taci amanansa kawai yake. Saidai kuma da ya nutsu ya zauna yayi tunani yaga haka kawai fa Amal bazata rabu da shi ba, ba tare da wata k’wak’k’warar dalili ba, yana da tabbacin cewa ba a son ranta ta aikata koma mey tayi ba, ze iya rantsewa akan irin soyayyan da Amal takeyi masa, shi kansa yasan Amal na sonsa so kuma na tsakani da Allah ba yadda za’ayi ta amince zata auri wani ba don wani k’wak’k’waran dalili ba, what could be the reason? He need answers. 

*****

   Kaman yadda ta saba yi idan ta tashi kullum da safe hakan yau ma tayi, hotunan Abdul tasa a gaba tana kalla tana kuka, duk yadda takeson mancewa da shi abun ya gagara. Ba abinda takeso sama da ta saurari muryansa, she misses him so much, she wants to know how he’s doing, what he’s doing and all. Bata tsammanin zata iya cigaba da rayuwa ba shi badan tanaso ba ta share hawayenta ta mik’e. Kitchen ta zarce inda ta had’awa Afzal kunun aya da aldeb ta d’ura cikin silver flasks da ta saya da sunansa sannan ta wuce bayi tayi wanka ta shirya zuwa school. A office na Sultan ta tsaya ta mik’a masa sak’on Afzal sannan ta basa nasa shima take rok’ansa idan ya samu dama ya kaiwa Afzal kuma tana gaishe sa da jiki. 

  Bayan Sultan ya idar da sallan Azahar ya zarce gidan Afzal inda ya tarar da Afzal d’in kad’ai a gida kasancewar Nazeefah ta tafi school. Bayan sun gaisa ya mik’a masa sak’on Amal. Sosai Afzal yaji dad’i baze iya tuna when last yayi tasting hand made smoothies na ta ba, he really misses it alot. A fridge ya ajiye, se bayan La’asr Sultan ya tafi. Da Maghrib bayan Nazeefah ta idar da sallah ta wuce dining space dan d’auko ruwa kawai taci karo da flasks har biyu cikin fridge d’in wanda take da tabbacin ba nata bane. Sa idon da zatayi ta tabbatar da cewa ba yau ta soma sa flasks d’in a ido ba sanda take amarya sau dayawa Afzal yakan taho da flasks d’in har akwai lokacinda ta gwada d’aukan d’aya zata sha ya k’wace yake cewa ai wacce ta basa batace ta bata ba. Toh fa wata sabuwa! Shin flasks d’in waye ne wannan d’in? Kode na budurwarsan ce? Amma kuma ai kwana biyu bata jinsa yana waya har yaushe yayi wata sabuwa da zata fara kawo masa drinks? But she’s sure wannan flasks d’in sune na budurwarsa ta da yau ya zatayi? Ina zata sa kanta? A rayuwa in akwai abinda ta tsana shine taga ko kuwa taji Afzal na kula wata. Zata iya jure komai amma banda kishiya, flasks d’in ta zaro ta ajiye akan table tana jiran dawowan Afzal. Be dad’e ba se gashi ya shigo, zuciyarta ta danne tayi mai sannu da zuwa sosai gabansa ya fad’i ganin flasks d’in da yayi a gabanta shin wai meya hanasa sanyasu cikin fridge na d’akinsa yasa key? Tashin hankali. Takawa yayi a nitse ya k’arisa dining table d’in “Zaki sha ne?” Ya tambayeta. Kai zalla ta kad’a. 

  “Then meyasa kika fito dasu? Naga acikin fridge d’in zasu fi yin sanyi.”

  “Afzal?” Ta kirasa “Flasks na waye ne wannan d’in?”

  “Kaman ya na waye kuma?” Mik’ewa tayi ta tsaya “Ba wannan ne ba karo na farko da nake tarar da flasks d’innan a gidan nan am very sure na mutum d’aya ne tambayata itace ta wace ce?”

  “Nazeefah-“

  “Ta budurwarka ce ko?” Tayi saurin katse sa. 

  “Budurwa kuma Nazeefah?”

“Tun da nake amarya ina ganin flask d’innan tana kawo maka smoothies aciki yanzu ma taji batun rashin lafiyanka ne ta kawo maka kenan ko?”

  “Wani irin magana kike haka Nazeefah? Dan kinga flask shikenan seki ce na wata?”

  “Toh na waye ne?”

 “Na Umman Sultan ne” ya had’e mata k’arya nan take. 

  “Umman Sultan?”

  “Baki yarda bane? Ki tambayi Danladi d’azu Sultan ya kawo mun.”

    “Taya tasan baka da lafiya bayan kace kar a sanar da kowa?”

  “Well Sultan told her before I could stop him.”

  “Kana nufin tun fari itake kawo maka smoothies d’innan?” 

  “Nazeefah zan miki k’arya ne? Come here” hannunta ya kama ya jata jikinsa had’e da rik’e k’aramin k’wank’wasonta. 

  “Ba k’arya kake mun ba ko?”

  “Haba in miki k’arya.” Kanta ta kwantar bisa k’irjinsa had’e da kewaye hannayenta a bayansa “I love you so much Afzal, ban tunanin zan iya sharing d’inka da wata, ina kishinka sosai please promise me bakada wata budurwar a waje.” A hankali ya d’agota had’e da rik’o fuskanta cikin hannayensa “What does it matter koda ina da wata budurwar a waje Nazeefah? You’ll always remain the Queen ke bakisan kece uwar gida ba?”

   “Yanzu kana nufin akwai wata a waje kenan?”

  “Ni bance ba” yayi saurin cewa. 

  “Afzal ba k’arya kake mun bako?” Matso da fuskansa yayi kusa da nata had’e da sauk’ar mata da gentle kiss a goshi “Stop bothering yourself okay? In kawo mana cup? Ko bakison ta6a aldeb na Umman Sultan?”

  “Bari in kawo mana” a nitse ya saketa ta zarce kitchen ta d’auko musu cups d’in. Har suka gama cin abincin Afzal se tunanin kalaman Nazeefah yake, ya santa ya san d’anyen aikinta ta ina ze soma sanar da ita batun Amal yanzu after making it clear ita akan kishiya zata iya aikata komai. Hmm!

***

   Kwana biyu iyayen Abdul suka jera suna nemansa amma wayoyinsa duk switched off kaman yasan Baba na iya turo abokinsa yazo ya dubasa ya tattara kayakinsa ya gudu hotel inda yake kwana. Ko fita office baya yi haka ze yini a d’aki yana tunanin Amal tamkar wani zararre ya koma. Se a daren na uku ne ya kunna wayansan, yana kunnawa kiran Mama na shiga kaman wanda baze d’auka ba yayi answering. 

   “Abdul! Alhj Abdul ya d’au wayan” ta sanar da Baba dake gefenta. “Abdul Baba na dan Allah kayi hak’uri.”

  “Mik’o mun wayan” cewan Baba sede tak’i ita se taji muryan Abdul tukuna. 

  “Abdul yi hak’uri kayi mun magana, Mama is sorry.”

  “Mama why?” Abinda ya fara tambayarta kenan. Matuk’a ya bata tausayi har takeji da ma tun farko ta sanar da shi gaskiyan kawai da war haka zuciyarsa ma ta warke. 

  “Abdul kayi hak’uri ka sani we only want the best for you.”

  “Best for me Mama? A ganinku 6oyemun gaskiyan al’amari da turoni Canada shine abinda yadace?”

  “Abdul kayi hak’uri daga ni har mahaifinka ba wanda yake da zuciyan fad’a maka wannan abu, bamu san ta ina zamu fara sanar da kai ba amma kayi hak’uri.”

   “Yaushe ne auran nata?”

  “Muma bamu sani ba Abdul but anytime soon.”

  “Wa zata aura?”

  “Abdul ba amfani.”

  “Just tell me.”

  “Afzal.”

  “Afzal??” Ya nanata da mamaki “Afzal??” Ya sake tambaya. 

  “Eh shi.”

  “How???”

  “Abdul its a long story amma inason ka sani Amal masoyiyarka ce ta hak’ik’a, kuma ko da wasa kar kawo a ranka cewa taci amanar ka.”

  “What happened Mama?” Gyaran murya tayi sannan ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta basa bata bar komai ba. Gabad’aya se ya dena tausayawa kansa ya shiga tausayawa Amal. Tabbas Amal ta cika masoyiyarsa ta hak’ik’a kaman yadda Mama ta fad’a. Inde haka ne toh Allah sa hakan shi yafi alkhairi a garesu duka, ya kuma bawa Afzal ikon rik’e ta da amana sede bai tsammanin ze iya daina son Amal. Sam beso hakan ya faru ba, yaso ace shine mijin da ze kula da Amal, mijin da ze zauna da ita har ila k’arshen rayuwarta, yaso ace shine mijin da zata haifan masa yara rabi masu kama da shi rabi masu kama da ita sede kana naka Allah na nasa. 

  “Ga Babanka nason yi maka magana.”

  “Toh ki bashi.”

  “Baba na?” Baba ya kirasa. 

  “Na’am Baba ina yini?”

  “Ya kake?”

  “Lafiya” ya amsa sama-sama. 

   Hak’uri sosai Baba ya shiga basa amma ya nuna masa shi fa ba komai, abinda Allah ya riga ya k’addara bashida makawa and everything happens for a reason he’s sure Allah nada dalilin shiga tsakaninsa da Amal da yayi, abu d’aya kawai yakeso a taya shi da addu’a Allah yasa rabuwa da Amal d’in shi yafi mashi alkhairi. Sosai Baba yaji dad’in kalamunsa daman yasan d’ansa da tawakkali, albarka yayita sa masa k’arshe yake tambayansa ko ze dawo gida ne? Yaso se a saya masa sabon aiki koma wani iri yakeso. 

  “A’a Baba nagode zan cigaba da zama nan d’in kawai.”

  “Are you sure?”

  “Yes Baba ba amfanin dawowa na, gara inyi zama na anan ko wala Allah a hankali Allah ze yaye min son Amal.”

  “Toh shikenan zamu tayaka da addu’a, so se yaushe zaka zo mana kenan?”

  “After a year or two in shaa Allah nan d’in yafi mun kwanciyan hankali.”

  “Toh Allah yima albarka Baba na, Allah ya mayar maka da wacce tafi Amal kuma, addu’an mu na tare da kai a kullum.”

  “Nagode Baba.”

 “Toh ga Mamanka tana son yima magana.” Itama Mama addu’a tayita masa tana sa masa albarka bayan nan sukayi sallama. Washegari Maamah da Amal suna zaune a makaranta tana bata labarin yadda suka k’aya da Ya Abdul jiya se kwatsam gashi yana kira bata 6ata lokaci ba ta d’aga bayan sun gaisa yake tambayarta ko tana gida ne. 

   “A’a ina school” ta amsa. 

  “Kuna tare da Amal kenan” kafin tayi tunanin yi masa k’arya yace, “Bata kinji? I just want a word with her” batayi gardama ba ta juyo gefen Amal. “Ya Abdul na son yi miki magana” ta sanar da ita. Kai Amal ta shiga kad’awa “I can’t speak with him Maamah bazan iya ba ki basa hak’uri.”

  “Sabida mey?”

  “Maamah naci amanan Ya Abdul , har abada bana tsammanin zan iya sake yi masa magana, kunya baze barni ba. “

  “Ya Abdul tak’i amsa” ta sanar da shi. 

  “Dalili?”

  “Wai she can’t spek to you ever again kunyan abinda tayi maka take.”

  “Sa a handsfree” ba musu ta sanya “Amal?” Ya kirata sede ta kasa amsawa. 

  “Amsa kinji? Kar ki damu” se kad’a kai take yayinda hawaye ya shiga ciko mata a ido amma ta kasa amsan wayan. “I’m not hanging up unless kinyi magana” hakan ko yak’i kashe wayan kud’insa se tafiya yake a iska ganin asaran ya soma yin yawa kawai ta amshe wayan daga hannun Maamah ba don taba so ba tare da miyarwa a headset “Ya Abdul” ta kirasa cikin sauti me rawa. 

  “Amal shikenan idan ban nemeki ba bazaki sake nema na ba? Haka akeyi?”

  “Ya Abdul ba haka bane amma dan Allah kayi hak’uri.”

 “Bade kuka kike ba?”

  “I’m not cryi-” kukan ne yaci k’arfinta tama kasa k’arisa zance nata. Hak’uri yayi ta bata har seda ya samu kukan nata ya d’an lafa. 

  “Meyasa baki fad’a mun ba Amal?”

  “Ya Abdul ta ina kake tsammanin zan soma sanar da kai wannan labari mara dad’i mey uban d’aci? Dan Allah ka gafirceni nasan naci amanarka, naci amanar soyayyarka but I’m so sorry wallahi ba a son raina na rabu da kai ba. Yaya was dying and soyayyata kad’ai ce zata iya ceto da ransa, bazan iya barinsa ya mutu ba inspite of all the good fortunes da yayi mun dan Allah kayi mun kyakkyawan fahimta” ta k’are maganan cikin kuka. 

  “Amal I know ba’a son ranki kika rabu dani ba and I do understand everything, nasani Allah ne ya rabamu and am sure yana da dalilinsa na yin hakan I’m just hurt and broken saboda baki sanar dani ba kikayi ta zolayata for all these while.”

  “Please forgive me amma zolayarkan ce kad’ai mafitar da nake da, banason a sanadin sanar dakai gaskiyan al’amarin wani abu ya samu kafiyarka Ya Abdul I value your life morethan I do value my own, idan har abu ya sameka ban tsammanin zan iya yafewa kaina shiyasa na buk’aci iyayenka da nawa kar su sanar da kai, I’m terribly sorry.”

  “A tunaninki canza layi da kuma daina nema na shine baze cutar dani ba Amal? If only kin sanar dani ko kuwa kin bari an sanar dani da zuciya na baza ta min k’una da ciwon da takeyi mun yanzu ba, I felt used and abandoned.”

  “I’m so sorry Ya Abdul bana son ka d’au naci amananka ne, please forgive me.”

  “Na sani Amal bazaki ta6a cin amana na haka kazai ba. Kuma ba k’aramin lada kike dashi ba na yafe farin cikinki dan ceto ran Afzal ba, only God shall repay you.”

  “But I never wished for it Ya Abdul, gabad’aya rayuwa na da kai nake planning. Na gama sa ran da kai zan raya sunnan manzo, I never wished to be separated from you, please believe me.”

   “Shhh! Na yarda dake Amal kuma nasani Komai na faruwa ne bisa dalili Allah nada dalilin raba mu da yayi fatanmu kawai Allah sa hakan yafi alkhairi.”

  “Please forgive me.”

  “Baki yi mun komai ba Amal, ina iya rantsewa akan soyayyan da kika nuna min and har in mutu bazan ta6a mancewa da hakan ba, ina alfahari da ke Amal, tabbas kin cika masoyiyata na hak’ik’a and I shall never forget that just keep praying kinji?”

  “Ya Abdul I miss you, I terribly miss you” ta sanar dashi cikin tsananin kuka. 

 “I miss you even more my Princess, bazan iya kwatanta zafin rabuwa dake da nake ji ba but God’s plan is the best, Allah tabbatar da alkhairi tsakaninki da Afzal ya sa ya kula mun dake kaman yadda ya saba da a baya.”

  “Ameen” ta amsa a hankali. Kai kuma fa Ya Abdul? Wa ze kula mun da kai? Wa ze baka dukkan farin cikin da ka cancanta?” 

  “Allah, Allah ze ban dukkan ababen da kika k’irga Amal just pray for me.”

  “Ya Abdul you’re one of a kind, kafin a samu irinka se an tona. Allah ya baka mace wacce ta fini da komai wacce zata soka fiye da yadda na ta6a sonka, wacce zata sa kamance da ni a rayuwarka gabad’aya.”

  “Ameen Amal amma bazan ta6a mancewa dake ba, bana tsammanin akwai macen da zata sanya ni in mance da kalan tsaftcacciyar soyayyar da kika nuna mun. Amal kin riga kin zamo 6angare a jikina, I’ll forever cherish our relationship, I’ll forever love you.”

  “I’ll forever love you too Ya Abdul or even more, thank you for understanding me.”

  “My pleasure bar kukan haka kinji? Kinga nima kina sani” yayi maganan yana tare hawayen dake shirin zubo masa. 

  “Na daina please don’t cry” ta amsa tana share hawayenta. 

  “Toh se wataran kuma Amal, take care of yourself-” Katse wayan kawai tayi, ta ma kasa barinsa ya k’arisa abinda yayi niyya yayinda ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Shi kansa Abdul hawaye yake da ya sauk’e wayan he still can’t believe sun rabu da Amal, matar da yake sanyata cikin duk wani plan na rayuwarsa aciki, matar da baya iya d’aukan minti biyu beyi tunaninta ba, “oh Allah you know what is best for me” ya furta a hankali yayinda yake share hawayensa. 

   Har zuwa Azahar Amal bata bar kukan da takeyi ba, Maamah se hak’uri take bata amma abun ya gagara. Suna zaune a masallci bayan sun idar da sallah sega wayanta yana ruri. Maamah ce ta ciro daga cikin jakar had’e da duban wake kira. 

  “Waye ne?” Amal ta tambayeta tana duban yadda fuskanta ya kumbura timm acikin madubi. 

   “Yaya ne” ta amsa. Kaman tace mata ta kashe saidai kuma ta d’au alk’awarin bazata kuma wulak’antansa ba, bata son abu ya sake samun lafiyansa. Haka ba don tana so ba ta d’aga. “Yaya” ta fara da cewa. 

  “Na’am Lily” ya amsa. 

  “Ina yini?” Ta gaishesa. 

  “Lafiya k’alau ya kike ya school?”

  “Alhamdulillah ya jikin naka?”

  “Na warware Alhamdulillah.”

  “Toh Allah k’ara sauk’i.”

  “Ameen inzo muje muci lunch?” Shiru tayi tana nazari har ga Allah bata da niyyan fita dashi yau ba don komai ba kuma se don kukan nan da tayita yi fuskanta ya kumbura, tabbas tasan yana ganin yadda fuskanta yayi timm d’innan ze hau tambayarta dalili. Tsoronta d’aya ne kar ya gane gaskiyan al’amarin k’rashe kuma ciwonsa ya sake tashi. “Lily?”

  “Na’am Yaya.”

  “Inzo? Or are you busy? In baze yuwu ba just tell me kinji?”

  “A’a kazo Yaya I’m free.” Sanyi yaji sosai “Alright I’m on my way.”

   “Toh sekazo” nan ta katse. 

  “Maamah nakega kiyi joining su Aisha kawai Yaya yace zezo muje muci abinci.”

  “Ayyah toh ba matsala adawo lafiya.”

  “Thank you” nan ta mik’e ta bi su Aisha. Yayinda da Amal ta zaro kwalli daga jakarta taja a idonta sannan ta shafa powder duk wai don ta d’an 6oye kumburin fuskan nata amma ina da anganta ansan ta sha kuka, kukan ma mey wuya. Bada dad’ewa ba sega Afzal ya k’ariso kasancewar Nazeefah bata fita school ba yau se yayi tunanin suci abincin a cikin makaranta kawai. Unimaid garden suka k’arisa se anan yake tambayarta meya faru. 

  “Babu” ta amsa sama-sama tana kare fuskarta. Hijabin nata ya janye “Taya zakice babu bayan gashi fuskanki duk a kumbure Lily, meya faru?”

   “K’anwar coursemate d’ita ce ta rasu muka je ta’aziya” tayi mai k’arya saidai take waien ya gano k’arya take. Kukanta baya wuce akan Abdul, tunanin hakan ba k’aramin k’ona masa zuciya yayi ba. Danne zuciyan nasa yayi ya mata ta’aziyya, hira sama-sama sukayi bayan sun gama ci ya d’an zagaya da ita cikin school sannan ya mayar da ita lecture hall nasu ya koma office.

   Nazeefah na kitchen tana had’a girkin yamma taji ringing na wayanta akan dining table. Da wuri ta fito ta d’auka ganin k’awarta Khadijah ke kira. 

  “Halo Khadijah?”

  “Na’am Nazeefah ya kike?”

  “K’alau.”

  Shiru yau baki fito school ba.”

  “Wallahi cramps ne ya rik’e ni d’azu amma da sauk’i yanzun.”

  “Ayyah Allah k’ara sauk’i toh.”

  “Ameen yane toh?”

 “Nace ba wani mota ne kam mijinki yake hawa?”

   “AMG C43 lafiya?”

  “Chab! Wallahi shine! ‘Yan mata shine!” Ta sanar da k’awayenta dake gefenta. 

  “Shine wa?” Nazeefah ta tambaya curiously. 

   “Babe mijinki muka ga tare da wata some minutes ago nan cikin unimaid garden.” Wani irin mumunan fad’i gaban Nazeefah yayi. 

  “Afzal d’in?” Ta tambaya cike da k’in yarda. 

  “Wallahi shine shi da wata suka zo suka ci abinci suka fice duk a idonmu.”

  “Kai k’arya ne ban yarda ba, bade Afzal ba sede ko me kama da shi.”

  “Ki tsaya achan, ana fad’a miki abu kina musu wallahi shi muka ga ni bansan ma mey ya hanani d’aukansu a waya ba da na tura miki an kashe musun.”

  “Khadeejah, Afzal fa kikace? Afzal kika gani da wata?”

  “Tabbas.”

  “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un, Nashiga uku na lalace! Tun ba yau ba nake zarginsa ashe de gaskiya ne, amma ko! Yanzu rashin kunyansa har ya kai yana d’aukan ‘yan mata yana kaisu cin abinci a idanun jama’ah?”

  “Hmm ai na miji ba d’an goyo bane Nazeefah komin dad’inki da shi seya cimiki amana.”

  “Oh Allah nagode sena shigo gobe.”

  “Allah kaimu.” Tana ajiye wayan ta shiga sintiri a dining space d’in har miya ya soma k’onewa bata sani ba. A takaice girkin ranan sam ba hankali a jikinta tayi. Koda Afzal ya dawo bata mai maganan ba duda cewan ji take kaman ta rufesa da duka don zafin kishi. Lafiya k’alau tayi welcoming nasa bayan sallan Maghrib suna zaune a dining zasu fara cin abinci Afzal ya lura da kallon da Nazeefah ke tayi masa kusan tun dawowansa daga office. 

  “Nazeefah are you sure you’re okay? ” ya tambayeta. Kai tayi saurin gyad’a mai had’e da kawar da kanta. Nan da nan tayi serving nasu spoon d’aya Afzal ya kai baki ya harar da abincin waje. 

  “Subhanallahi!” Yayi exclaiming. 

  “Lafiya?” Tayi saurin tambaya. 

  “Ai na fad’a dama ba lafiya ba shin meke faruwa? Kinji uban gishirin dake cikin abincin nan kuwa? Bayan nan ga warin k’una what’s really going on? Jikin naki ne har yanzu? Ai da kin bar girkin” Ji take tamkar ta d’aukesa da mari dan haushi. Bak’in cikin da yakeji yanzu kad’an ne dangane da wanda ya cusa mata. 

  “Mey kajeyi a makaranta yau?” Ta tambayesa. Sosai tambayan nata ya basa tsoro taya ma tasan ya shiga school yau bayan bata fita ba? Allah ya taimakesa bawai munafukan k’awayenta bane suka gansa tare da Amal suka kirata suka yi mata gulma. Shima tun farko mey ya kaisa cin abinci a cikin school? Ai don Nazeefah bata fita school ba that doesn’t mean k’awayenta ma basu fita ba, yayi sakarci. Tabbas su suka had’a komai. 

  “Kayi shiru” ta sake da cewa. 

  “Naje ganin friend d’ina dake lecturing achan ne” ya shirya mata k’arya dukda cewa yasan ba zama zatayi akai ba. Kallon da takeyi masa zalla ma amsa ne game da tambayan da yake yi wa kansa. 

   “Wani abu ne?” Ya tambaya da kallon ya soma yi masa yawa. 

  “Babu kawai dama ance mun anganka a school ne yau.”

  “Ohhh like I told you naje ganin friend d’ina ne” ya amsa saidai yasan k’arya take masa, kaman yadda shima yayi mata k’aryar. Tabbas an gansa da Amal ne aka kira aka gaya mata. 

  “Ya cikin naki ya daina ciwo?” Ya tambayeta yana neman canza topic d’in gudun kar fad’a ya 6arke musu. 

  “Da sauk’i” ta amsa sama-sama. 

  ***

   Tun kan wayan da Amal tayi da Abdul se gabad’aya halinta ya sake sauyawa ya koma na da, no matter how hard she tried ta kasa mancewa da shi, da tunaninsa take tashi da kuma shi take yini. Shima ta 6angarensa hakan ne. Kullum cikin tunaninta yake ba makawa. 

    Haka zata yini d’aki tana kuka. Kwana biyu kenan bata fita school ba ta fake da cewa wai period cramps ke damunta. Shiko Afzal da zaran yaji bataje school ba yasan batun Abdul ne. Hak’urinsa ya k’are, bai jin ze iya jure hakan again he wants Amal to be his alone gashi a gida be san ta ina ze fara sanar da Nazeefah cewan yana shirin k’ara aure ba tabbas yasan baza ta ta6a amincewa da hakan ba, a cikin d’an k’ank’anin lokaci ya gano irin zazzafan kishin da take da shi. Lallai se yayi taka tsan-tsan da d’aukan Amal a mota anyhow tunda yanzu har an soma kawo mata gulma gida. 

   Washegari ya shirya tsaf abinsa ya je gida gun Abba. Bayan sun gaisa yake ce mai shi yana son a tura gaisuwa gidansu Amal a shirye yake ya k’ara aure. Sosai Abba ya taya sa murna had’e da masa nasiha sosai akan yin adalci inda daga k’arshe kuma yake tambayansa ko ya sanar da Nazeefah batun auren ko kuwa tukuna. 

  “A’a tukuna amman ina da niyya nafison idan ku manya kun gama komai sena sameta in fad’a mata abinda ake ciki, kar taga kaman ba neman aure nake ba kawai ina flirting ne a waje.”

  “Kana da point kam amma kana ganin k’in sanar da ita har se idan an sa rana ko makamancin hakan shine dai-dai?”

  “I suppose it is Abba” ya amsa sa. 

  “Toh shikenan Allah shige ma gaba zanyi magana da kawunanka cikin satin da za’a shiga se muje gidansu Amal d’in.”

  “Toh Abba nagode sosai Allah saka da alkhairi.”

  “Ba komai Allah yayi ma albarka.”

  “Ameen bari in lek’a Ummi.”

  “Ai bata gida baka sani bane?”

  “Wallahi no dake ina shigowa site naka na zarce.”

  “Ayya ai ta fita suna wai.”

  “Toh ba matsala ni zan wuce.” Da haka sukayi sallama. Gidansu Amal direct ya wuce yayi mata waya kan ta fito gashi nan bakin k’ofa. Hijabinta ta ja ta sanya ta feshe jikinta da turare sannan ta fice taje ta samesa inda suka gaisa. Bayan nan ya kira sunanta a nitse. 

  “Na’am” ta amsa. 

  “Nace ba izun naki nawa ne yanzun? It’s been long ban ji kina mun zancen islamiyya ba Lily.”

  “I’m sorry kasan jami’a da islamiyyan ne se a hankali idan ba hutu akayi ba bana samun time na karatun kaman yadda nakeso.”

  “Hakane kam, kina ma k’ok’ari ai am very proud of you tunda kika fara karatu baki samu carry over ba.”

  “Thank you Yaya.”

  “So izib nawa kika had’a so far?”

  “Saura goman k’asa in gama had’awa gabad’aya kuma dama chan tun da na ta6ayin biyar d’in k’asan a takaice de izu biyar ya rage mun idan na zauna nayi tilawa.”

  “Masha Allah so ina da Hafizah as a wife to be kenan?” Kai ta gyad’a masa a hankali cike da kunya. “Zaki iya tuna alk’awarin dana d’aukan miki anytime kika gama haddanki?”

  “Eh toh not vividly amma de kace akwai special kyautan da zaka mun idan na had’a.”

  “Very good Umarah nakeson mu tafi tare.”

  “Saudi?” Ta tambayesa cike da k’in yarda. 

  “Eh Lily Saudi.”

   “Yaya are you serious?” Ashe de Allah ze nuna mata ranan da zata kai wa d’akinsa ziyara. Oh Alhamdulillah!

  “I’m damn serious, I would want us two to go together.”

   “Toh Allah nuna mana I really can’t wait.”

  “Ameen but kinsan bazeyi muyi tafiya mu biyu kad’ai ba ko? Tunda ni ba muharraminki bane.”

  Dank’ari se yanzu hankalinta ya buga ta kuma fahimci inda ya dosa a takaice de so yake yace mata aurensu ya kusa. Oh Allah ita bawai auren neba matsalarta, tunanin yadda zata fara zaman aure da Afzal take wai ma zancen kishiya a gefe. Mutumin da duk rayuwarta ta d’aukesa a matsayin yayanta kuma rana d’aya seta fara kallonsa a matsayin mijinta? How is that even possible?

   *PAGE 2⃣3⃣*

         “Lily kinyi shiru” ya fad’a yana kallonta. 

  Kanta tayi saurin kawarwa tare da ambatan sunansa a hankali se kuma tayi shiru. 

  “Lily I’m sorry but I can’t wait any longer, I’ve waited for so long to be with you and to make you mine and now is the perfect time, please kar kice a’a nasan kina iya had’a haddan naki acikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa. Idan har kika samu kika had’a kinga se ayi bikin sauk’an naki dana auran mu at once bayan nan kuma se mu wuce Saudi for our honeymoon, don’t say no please.”

  Excuse ta shiga nema amma gabad’aya ta rasa ta mey zata ce masa. Bata san mey ba amma anytime Afzal yakeyi mata zancen aure gabanta yake tsinkewa yana fad’i, har wani tsoro-tsoronsa ma takeji. K’arshe de ta samu ta 6ullowa zancen ta hanyan sak’alo sunan Nazeefah. “Toh Yaya Nazeefah fah? Ita baza mu tafi da ita ba?”

  “Lily I want you to believe in me, ki sani cewa zanyi iya k’ok’arina don ganin nayi adalci tsakaninki da ‘yar uwarki. Nasan auran mey mata a zamanin yanzu isn’t something easy but I need you to believe in me, ni da Nazeefah cikin kwanakin nan zamu tafi in shaa Allah so that idan munzo tafiya dake bazata ga kaman anyi mata rashin adalci ba. But kafin mu tafi da ita I need your approval please ki amince zaki aureni, I’ve spoken with Abba already a shirye yake suzo su sami su Papi ayi maganan, amincewan ki kawai nake nema Lily.”

   “Yaya I do believe in you, tsoro na d’aya ne” ta sanar da shi a nitse. 

  “What is it? Tell me” ya amsa take. 

  “Nazeefah, Yaya tsoron zama da kishiya nake bansan mey Nazeefah zata iya aikatawa ba, ban san irin kishin da take da shi ba, bansan ko zata amince dani kokuwa a’a ba, banason in zame d’aya daga cikin jeri matan da kishiyoyinsu suke yi musu illa kaman yadda banida niyyan cutar da ita bazan so nima ta cutar dani ba.”

   “You’re safe with me Lily, I’ll do everything in my power to keep you save and kar kiyi tunanin Naeefah is that evil nasani kishi kam dole ne but she’ll never hurt you, I’ll make sure of that and besides banida niyyan had’aku gida d’aya, unguwa ma ba had’aku zanyi ba ni kawai ki amince.”

  “Toh shikenan Yaya na amince da k’udurinka, kana iya turo su Abba but I have one favor to ask.”

  “Ask me anything Lily.”

  “Please kayi hak’uri semun kammala first semester d’in yaso se ayi auren cikin hutu, bana son hidiman bikin ya raba mun hankali.”

  “I’ll do only as you wish Lily se abari idan kin kammalan ba second semester kuke ba?”

  “Eh” ta amsa had’e da gyad’a kai. 

  “Allah taimaka toh.”

  “Ameen.”

  “So will you agree to marry me?”

  “Yaya ba nace eh ba.”

  “I want to hear it again, Lily am head over hills for you, please tell me again will you marry me?”

  “Yes Yaya” ta amsa cike da kunya ko kallon gefensa ta kasa bale cikin idansa. 

  “Thank you Lily ji nake kaman duk duniya ba wanda ya kaini farin ciki, Lily a yau kin cika mun buri da kuma mafarki. I’ve been looking forward to this day and now I shall be looking forward to the day I’ll make you mine, the day you’ll start answering my name and the day I can call you my wife. Lily you don’t have to worry because I’ve promised to take care of you, to love and protect you with my life, I’ve promised to never leave your side. In shaa Allah bazakiyi nadaman aurena ba.”

  “I know Yaya Allah and I’m very grateful Allah ya baka ikon yin adalci tsakani na da Nazeefah.”

  “Ameen Lily kinsan wani abu?”

  Kai tayi saurin kad’awa da nufin a’a . 

  “Guess!”

  “But I can’t ka fad’a mun kawai.”

  “I love you” ya sanar da ita. Har cikin ranta taji nauyin kalamun nasa yayinda kunya me tsanani ya rufeta fuskanta ta shiga karewa. “Kin san wani abu again?” Nan ma kai zalla ta iya kad’awa. 

  “I love you” ya kuma sanar da ita. By now kam Amal ji take kaman zata lume k’asa don kunya, bata san mey ba amma kunyansa takeji kunyan ma me tsananin tsiya bata tsammanin zata ta6a iya sakewa dashi. Wani sa’in tana missing relationship nasu na da dasuke a matsayin Yaya da Lily zallah ba wani abun ba. 

  “Can’t I get an ‘I love you’ back?” Ya tanbayeta tare da had’e girarsa. 

  “Yaya…” se kuma tayi shiru. 

  “Lily I know you’re not comfortable with me, nasan kina tsananin jin kunya na and I respect that alot but please give me the chance to love and make you happy.”

  “Yaya I’m already yours ka daina damun kanka haka.”

  “I feel honored then” ya amsa “Can I ask of a favor?”

  “Ina sauraronka.”

  “Can you please tell me you love me too? I need to hear these words so badly.”

  “Yaya-“

  “Lily I know it you don’t love me-” ya katseta. 

   “Yaya ya kake magana haka?” Itama tayi saurin katse sa. 

  “Na sani Lily, nasani har yanzu Abdul ne a zuciyarki kuma shi kikeso and bawai ina kishi da hakan bane kokuwa ina jin haushi, nasan zafin rabuwa da masoyi nasan ze d’au lokaci kafin ki iya mancewa dashi ki bud’e mun zuciyarki. I just want you to know that no matter what I’ll stand by your side. I’ll provide support and love you regardless, I’ll be here Lily even if you don’t need me.”

  “But Yaya I need you also-“

    “Shhh!” ya katse ta “And also bana son kiyi tunanin cewa banida godiya ne nake tinziraki haka ina gaggawa, ki sani it’s just because I love you so damn much. Bayan nan I’m very grateful for all the sacrifices you’ve made to save my life, I’ll forever remain grateful to you Lily I just need to hear these words koda kuwa you don’t mean them just tell me.”

  “Yaya I-” seta bud’e baki zata sanar da shi kalamun seta kasa ji tayi bakinta yayi nauyi, banda sunansa ba abinda take iya furtawa. 

  “Please try” ya rok’eta. Sede ina duk yadda taso sanar dashi hakan abun ya gagara se gani take kaman Ya Abdul na tsaye a gefen windon yana kallonta. 

  “I’m sorry then” yace k’arshe feeling so sad. 

  “Yaya ni ya kamata in baka hak’uri dan Allah kayi hak’uri Wallahi I’m trying, I really want to forget about Ya Abdul abun ne yafi k’arfina please forgive me” ta sanar da shi cikin sautin kuka. 

  “Its okay Lily ba se kinyi kuka ba, forgive me but ba laifi na bane don hak’uri na ya gaza, you’re just like a drug, so addicting. Ji nake kaman in ban same ki ba ina iya rasa rayuwana.”

   “Yaya dan Allah kabar magana haka I’ll always and forever be yours, kasa a ranka na riga na zama taka bana son inji kana maganan rasa rayuwanka, ya kakeson in rayu in ba kai?” Tunda suka fara hirar se yanzu ne ta juyo tana kallonsa idonta cike da k’walla. 

“Forgive me, but bakiya sona ya kikeson inyi idan ba mutuwa ba?”

   “Yaya I care about you, I care about your existence morethan anything dan Allah kabar cewa haka.” 

  “Anything for My Lily.”

  “Thank you” ta amsa had’e da sakar masa k’aramin murmushi tana share hawayen nata. Murmushin shima ya miyar mata yayinda ta shiga duban lokaci a cikin wayanta. “Maghrib ya kusa ko?” Ya tambayeta. Kai ta gyad’a a hankali “Ya kamata mu soma yin niyyah.”

  “Sure” ya amsa tare da mik’a hannunsa ta back seat ya janyo wata leda. “Here wannan naki ne.”

  “Yaya baka gajiya da bani gifts ne kam kullum?”

  “Bazan ta6a gajiya da farinta miki ba Lily.”

  “Amma Yaya-“

  “Not a word please” ya katseta. Bata k’ara musu ba ta mik’a hannu ta amsa  had’e da yimai godiya. Seda taga ficewansa ta k’arisa ciki. D’akinta ta nufa inda ta zazzage kayakin gabad’aya designer turaruka ne da man shafawa aciki seda su gel da sauran kayan shafe-shafe. Oh! Idan ta tuna da irin kashe kashen kud’in da Afzal yakeyi akanta setaji kaman ta samu Ummi tace ayi mishi fad’a ya daina. Bata son a sanadinta ya samu kariyar arziki ko makamancin hakan gashi ya dage kullum idan zezo se yayi mata gaggarumun shopping. 

  ***A nitse Afzal ya k’arisa gida sede tun da ya hau kan hanya yake tunanin kalamun Amal da kuma yadda ta kasa furta masa kalaman da kunnensa suke kwad’ayin ji. Be san kuma mey zey sakeyi Amal ta bud’e masa zuciyarta ba ta koyi sonsa, he misses her alot. He misses her smiles and laughter, everything about her he mise. Duk abinda yasan ya kamata yayi ya yi amma ina har yau ta kasa sakewa da shi. Yana isa gida Nazeefah ta taso tayi masa sannu da zuwa jawo hannunta kawai yayi ya rungumeta feeling so lonely. 

  Ta kai kusan minti d’aya tsaye ko motsi babu sannan a kid’ime ta zagaye hannayenta a bayansa hugging him back cike da rashin fahimta. “Afzal is everything okay with you?” Ta tambayesa a hankali har anan be saketa ba yayinda kuma ya kasa amsa ta. “Afzal?” Se anan ya raba jikin nasu. 

  “Nazeefah I feel so alone, shin bayan su Ummi akwai mey sona kuwa?”

  “Wani irin magana kuma kake haka? Meya faru?”

  “Just answer me, akwai?”

  “Akwai mana Afzal, and ina d’aya daga cikinsu. I love you Afzal no matter what, kar ka ta6a tsammanin bakada masoya bayan su Ummi. I’m here and I love you kaji?”

  Kai ya gyad’a a hankali “Thank you Nazeefah.”

  “You shouldn’t mention food is ready taho muje inyi serving naka ko seka dawo daga masallaci? Naga Maghrib ya kusa” Ta tambayesa. Bata kai da juyawa ba ya rik’o hannunta kafin ta fahimci abinda yake shirin yi kawai taji moist lips nasa akan nata, mutuwan tsaye tayi a wajen yayinda ta kasa koda kyafta ido.  A hankali taji large arms nasa yana rufe bayanta yayinda yake matso da ita kusa da shi, deepening the kiss in the process. Wani irin electrification taji yana bin jikinta yayinda taji numfashinta na neman d’auke mata, bata san a lokacin da ta shiga mayar masa da martani ba. A hankali a hankali suke tafiya manne da juna har seda Afzal ya turata jikin bango. Mutum na iya cewa sun mance da duniyan da suke ciki don zafin kiss kawai, gabad’aya sun fita daga hayyacinsu. Chan Afzal ya saketa a hankali yana k’ok’arin kama numfashinsa kaman yadda itama takeyi, goshinta ta sauk’e dai-dai saitin ha6arsa yayinda wani irin zazzafan sonsa yake shiga jikinta. Ji take gabad’aya duniya ba wanda ya kaita murna, ashe de Allah ze k’addaro mata da wannan rana? Oh she can’t get over how sweet, soft and moist his lips were, bata k’i ya sake kissing nata over and over again ba. 

  “I’m sorry” taji ya furta a hankali yayin da minty breath nasa yake fifita hancinta. Shi kansa ya rasa gane meke faruwa. 

  “It’s okay” ta mayar masa har anan ba wanda ya motsa acikinsu. 

  “I’m sorry” ya sake fad’a had’e da sauk’e hannayensa da suke rik’e da kunkuminta “I’m really sorry ban san meke shirin faruwa da ni ba please forgive me” kafin tace wani abun ya wuceta da hanzari inda ya zarce d’akinsa. Key ya sa had’e da manna bayansa jikin k’ofan. Idonsa ya rufe gam amma ya kasa daina tunanin kiss da sukayi sharing da Nazeefah shin meke faruwa? Gabad’aya ji yayi Amal yake kissing, mey soyayyar Amal ke shirin yi masa? Taya zeyi kissing Nazeefah ya d’au Amal yake kissing? Anya kuwa soyayarta ba shi ze halaka sa ba? Yanzu da wani ido ze sake kallon Nazeefah? Oh Allah! Yau yana cikin wani yanayi. Sallan Maghrib da be fita ba kenan ranan wane sabuwan amarya haka ya la6e a d’akin.  Tun Nazeefah na jiransa da ya fito suci abinci har bacci yayi gaba da ita zaune akan dining d’in. Chan wajajen goma ya lek’o waje a sanadin yunwan daya fafarosa. Sid’ak-sid’ak yake tafiya wai kar tajiyo motsinsa ta fito, ba k’aramin tsinkewa zuciyansa yayi ba ganinta da yayi zaune akan dining ta kafa kanta akan dining table d’in. A farko niyyan juyawa ya koma d’akinsa yayi tunda de bata gansa ba amma kuma ya fasa sanadin kukan da cikinsa yayi don yunwa. Matse idonsa yayi ya k’arisa wajen had’e da yin gyaran murya se kuma yaga bata motsa ba. 

  “Nazeefah?” Ya kira sunanta nan ma shiru lek’a fuskanta da zeyi kawai ya tarar bacci takeyi. Allah sarki bade bacci ne ya d’auketa anan ba tun tana jiransa ya fito suci abincin tare? Shin ta ma yi sallah kuwa? A hankali ya shiga tada ita har ta bud’e idonta. 

  “Kinyi sallah?” Ya soma da tambayarta. Kai zalla ta gyad’a masa yayinda idanunta suke neman kafewa. 

  “Abinci fa kinci?”

  “Ba tun d’azu ina jiranka ka fito muci ba kak’i.”

  “Ba wai nak’i bane Nazeefah…” se kuma yayi shiru a bisa rashin sanin abinda ze sake cewa. 

  “Are you ashamed because you kissed me? Are you Afzal?” Ta tambayesa da mamaki. 

  “Ko kad’an ba haka bane.”

  “Toh yaya ne? Afzal I know you don’t love me but I’ll never surrender, zan cigaba da hak’uri ina farinta maka har izuwa ranan da Allah ze sa a ranka kaji zaka iya yafe mun abubuwan da nayi maka da a baya, I really am sorry” ta k’are maganan idanunta na neman cikowa da hawaye. 

  Zama yayi a gefenta a hankali had’e da rik’o hannunta cikin nasa. “Kibar cewa haka please ni baki yimun komai ba.”

  “Ban yi maka komai ba?” Ta tambayesa da d’umbun mamaki. 

  “Ban yi maka komai ba amma auran mu sama da shekara biyu kenan yau baka ta6a tunanin sauk’e mun hak’k’ina da Allah ya d’aura maka ba? Baka ta6a damuwa da wani halin nake ciki ba Afzal. Kana ganin ka kyauta mun kenan?”

  “Nazeefah-“

  “Amma kar ka damu har ga Allah ni na yafe ma komai saboda bana son Allah ya tsayar da kai ranan qiyama akai na” ta sanar da shi had’e da katse sa sannan ta cigaba. “Nasani ni na bud’e k’ofan duk wani tashin hankali da wulak’anci daga gareka, da tun farko na rik’e mutunci na nayi respecting naka da duk hakan be faru ba I just hope it’s not too late to say sorry.” Sosai kalamunta suka shigesa ya kuma tausaya mata. Ya sani tauye hak’k’in bawa ba abu bane me kyau musamman ma na tsakanin mata da miji but shima ai ba a son ransa yake hakan ba. 

  “A tunanin ki a son raina ne nake tauye miki hak’k’in ki? A tunanin ki nid’in zama haka dad’i yake mun ne? Kokuwa kina tunanin ni banida sha’awa ne? As much as you need me as your husband know that I need you as much amma-” se kuma yayi shiru. 

  “Amma mey? Please talk to me Afzal I can’t do this anymore.”

  “I can’t Nazeefah, bazan ta6a iya had’a kwanciya dake ba.l Har cikin ranta taji zafin kalamun nasa ba shiri hawaye ya shiga tsiyaya daga idanunta. 

  “Afzal meyasa? Me nayi da zaka hukunta ni haka? Dan Allah kayi hak’uri, Afzal bazan iya rayuwa ba kai ba, wallahi da in rasa ka gara na rasa komai ciki harda rayuwa na. I love you Afzal I can’t stop saying it no matter what.”

    “Nazeefah I’m sorry.”

  “Ni ba hak’urinka nakeso ba Afzal, ka gayamun dalilin da yasa bazaka iya had’a kwanciya dani ba idan wani laifin nayi in baka hak’uri.”

  “Forget it, just forget it” kafin ya kai ga mik’ewa ta jawo hannunsa tana hawaye sosai “Please tell me Afzal a shirye nake da inyi ta baka hak’uri har se Allah ya huce ma zuciya dan Allah ka fad’a mun.” A da ya d’au alk’awarin komin yaya baze ta6a sanar da ita laifin nan da tayi masa ba amma kukan da takeyi ba k’aramin karya masa zuciya yayi ba. 

  “Please tell me Afzal I can’t do this anymore.”

  “Remember the first day aka kawo ki gidan nan?” Kai tayi saurin gyad’a “Mey kikace wa k’awarki da ta kiraki?” Ya tambayeta, sede ta duba ta duba tayi tunanin gaba da baya amma ta kasa tuna komai. “Afzal wallahi bazan iya tunawa ba dan Allah ka fad’a mun.”

  “I can’t tell you, bazan iya ba Nazeefah saboda kalamun basuda dad’in sauraro zan baki nan da duk lokacin da kike buk’ata ki zauna kiyi tunani idan har kin tuna da kanki then I’m willing to forgive you.”

  “Afzal please tell me I’m so sorry.”

  “I’m sorry as well but I can’t.” Yana fad’in haka ya kuma mik’ewa da niyyan ficewa hannunsa ta sake rik’owa “Nasan kana jin yunwa please ka zauna kaci abinci.”

  “Karki damu.”

  “Please Afzal.”

  “Kefa? Kinci?”

  “Ni idan har zaka ci ma hakan ya isa ya k’osar dani don’t worry about me.”

  “I’m not eating unless with you.”

  “Toh ka zauna please kar ka tafi.”

  “Toh kibar kukan haka” badan tana so ba ta shiga share hawayen nata seda ta bar kukan ya amince ya zauna nan tayi serving nasu suka ci bayan sun gama ta tattara plates d’in takai kitchen. D’akinta ta wuce dan watsa ruwa shima haka, chan yana shirin kwanciya se gata ta shigo daman ita yake jira. Bayan ta kwanta ya kashe musu wutan. Kan pillonta ta bari ta matso kusa da shi had’e da sauk’e kanta a birnin k’irjinsa tana mey zagaye hannunta akan cikinsa. A hankali taji hannayensa yana kewaye bayanta “Goodnight Nazeefah” ya sanar da ita had’e da sauk’e mata peck a kai. 

  “Goodnight Afzal I love you.” Bada dad’ewa ba yayi bacci itako ta kasa, se tunanin maganansu na d’azu take. Shin mey ta fad’a da ya 6ata masa rai haka har ya gommaci ya tauye wa kansa hak’k’i ya sha wuya da ya kusance ta? Se kusan k’arfe biyu bacci ya d’auketa. Washegari wajajen k’arfe hud’u bayan Afzal ya dawo daga office tayi masa sannu da zuwa had’e da amshe jakansa. Har d’aki ta rakasa ta ajiye jakan nasa a mazauninsa sannan ta shiga bayi ta had’a masa ruwa ya shiga ya watsa bayan ya fito ya sanya shorts da singlet sannan suka fito dining inda suka ci abinci. Bayan sun gama ta tattare wajen tsaf. Har Afzal ya shiga takawa zuwa d’akinsa yaji muryan Nazeefah na kiransa, chak ya tsaya had’e da kewayowa. Mik’ewa tayi ta k’arisa ta samesa. 

   “Afzal I’m sorry I’m really sorry.”

   “Why? What for?” Yyi saurin tambaya. 

  “Bayan tunanin da na yini inayi na tuna abinda na fad’a a daren auren mu dan Allah ka gafirceni, I was young and stupid then, yarinta na yawo a kaina bansan ciwon kai na but tuba nake please forgive me for hurting you like I did, wallahi I didn’t mean a word.”

  “It’s okay Nazeefah ya wuce.”

  “Dan Allah ka yafemun.”

  “Na yafe miki komai Nazeefah forgive me also.”

  “You have nothing to be sorry for.”

  “Toh hawayen ya isa haka” ya fad’a had’e da sa hannunsa yana share mata hawayen nata. Hugging nasa kawai tayi yayinda kukan nata ya tsananta “Thank you for forgiving me Afzal, I love you so much.” A hankali ya zagaye hannayensa a bayanta hugging her back. 

   “Its okay” ya sanar da ita yana shafa bayanta a hankali. Be barta ba seda kukan nata ya lafa hannunta ya ja izuwa parlourn inda suka zauna akan kujera. 

  “Yaushe zakuyi exams naku?”

  “Da d’an saura se nan da two months in shaa Allah.”

  “Masha Allah shikenan an zama graduate kuma ko?”

  Ka manta ne? First semester muke ai? Se mun gama second tukuna.”

   “Yesh haka My computer scientist” yayi complimenting nata. 

  “Thank you” ta amsa tana murmushin jin dad’i, har cikin ranta taji dad’in yadda ya kira ta ‘his computer scientist.’

  “I’m so proud of you Nazeefah Allah sanya albarka acikin karatun.”

  “Ameen Afzal thank you.”

  “Ina son mu tafi Umarah tare.”

  “Umarah?” Tayi exclaiming cike da mamaki. 

  “Yes just me and you.”

  “OMG!” Tsalle tayi tare da hugging nasa. “Are you serious?” ta sake tambaya bayan da ta sake sa. “Yes Nazeefah” ya amsa. 

  “Yaushe toh?”

  “I guess se idan kun gama exams naku yanzu kinga ai kina school.”

  “But ba wani serious lectures ma muke ba.”

  “A’a Nazeefah bana son wasa da karatu ai 2 months d’in kaman gobe ne karki damu kinji?”

  “Toh shikenan Allah kaimu I just can’t wait.”

****

   Haka nan tun daga ranan Nazeefah da Afzal suka soma zaman lafiya a gidan. Kullum shi yake kaita school, idan lokacin lunch yayi kuma ya d’auketa suje su ci da ikon Allah basu ta6a had’uwa da Amal ba sannan duk sanda yake gida baya kiranta gudun kar Nazeefah ta gano wani abun. A satin da ya gabato ne su Abba suka turo gaisuwa gidansu Amal inda su Papi suka amince suka kuma bada Amal. Siyayya sosai su Abba suka yi fiye da wanda Baban Abdul sukayi, kayaki se de ace masha Allah. Kaman yadda Afzal ya buk’ata haka Abba ya sanar da iyayen Amal cewa baya son a d’au lokaci kafin ayi bikin so samu idan Amal ta kammala part three nata batun kayan d’aki da gara kuma yace ya d’auke masu nauyin su kawai su amince ayi bikin ba tare da an 6ata lokaci ba. Papi beyi jayayya da hakan ba shima dama bayi da ra’ayin jan bikin idan ma da akwai abinda ze sasu jan bikin shine shirin yima Amal kayan d’aki amma yanzu da Afzal ya nuna zeyi komai sede suyi musu fatan alkhairi. 

   Sati uku Papi ya basu a gaba da su dawo kafin nan Amal da mahaifiyarta sun gama yanke hukunci game da ranar da za’a sanya na auren. Sosai su Abba sukayi godiya inda suka sauk’e dubu ashirin da suka tashi tafiya. 

****

   Haka tafiyan ta cigaba duk da kalan halatayya irin na Amal, Afzal be kariya ba, be fasa kirarta da kuma zuwa gidansu dubanta ba. Gashi duk abinda ya gani me kyau se ya sai mata ita da Nazeefah sosai yake kwatanta yin adalci a tsakaninsu. Nazeefah kuwa har yau bata san meye ake ciki ba. 

  Ta fannin Abdul kuwa sosai yake kewar Amal, rana baya ta6a wucewa beyi tunaninta ba sede kuma bai fasa tashi cikin dare yana rok’an Allah ya kawo masa sauk’i ba. 

  ****

  Yau bayan sallan Isha Afzal da Nazeefah suka shirya tsaf inda suke je sukaci abinci bayan nan ya wuce da ita 3G gallery inda ta sassayi jakukkuna da dama. Bayan ya biya komai sun dawo mota ya sake fita da sunan yayi mantuwa inda ua sai wa Amal tasa itama jakukkunan ya bayar aka sa masa a booth suka k’arisa gida. Project nata ta d’auko suka cigaba da yi mata daga inda suka tsaya jiya, wajajen goma tace su bari haka su kwanta yaso su cigaba gobe. Yau wankan ma a bayin d’akinsa tayi, bayan ta fito shima ya shiga yayi zuwa k’arfe sha d’aya de suka samu suka kwanta. Kaman kullum ta gangara jikinsa sede yau Afzal ya d’au niyyan mayar da Nazeefarsa cikakkiyar mace. Yau fiye da sati biyu kenan tunda ta nemi tubansa amma ba abinda ya shiga tsakaninsu. Tun Nazeefah na sa ran ze nemeta har ta dena saidai ko da wasa bata sake yi masa maganar ba ita de bata fasa da yin addu’an Allah shirya tsakaninsu ba. Kaman acikin mafarki taji ana yi mata wani irin shafa, a firgice ta bud’e ido sede kafin tace zata mik’e zaune ya rik’ota gam a jikinsa. 

   “Shhh!” Ya buk’aceta se anan hankalinta ya d’an kwanta. A hankali cike da dabara ya shiga sarrafata yayin da take basa had’in kai har yaci nasaran raba ta da kayan jikinta. Wannan dare de da Nazeefah ta dad’e tana jira finally Allah ya kawo mata shi, anci kuka anji dad’i duk a lokaci d’aya. A hankali har bacci me nauyi yayi gaba dasu duka sede duk lokacin da Nazeefah ta tuna yadda Afzal ya riga tarerayarta se ta murmusa acikin baccin. Wani irin gobaran sonsa ne yake ruruwa a zuciyarta ji take idan ba shi bazata iya rayuwa ba. 

   Kiran sallan Asuban fari Afzal ya tashi, a hankali idanunsa suka sauk’a akan Nazeefah datake manne a jikinsa se bacci take bayan da ya kunna wutan d’akin. Murmusawa yayi a hankali yayinda events na last night suka soma dawo masa ashe de raguwa take se kurun bakin tsiya. Cike da dabara ya raba jikinsa daga nata had’e da lullu6e jikinta da bargo. Bayi ya fad’a yayi wanka sannan ya d’aura alwala ya had’a mata ruwan d’umi tukuna ya fito. Bayan ya sanya jallabiyansa ya nufi kan gadon inda take bacci har yanzun. 

  Sunanta ya shiga kira a hankali har seda ta bud’e idonta, da sauri ta sake kullesu bayan da suka had’a ido hakan ba k’aramin murmushi ya sanya sa ba, wai kam dama Nazeefah na da kunya? Wai toh idan tana irin wannan kunyan? Amal tasa fah? Amal da ko kalamun soyayya ya fad’a mata bata sake iya kallon cikin idansa. Lallai akwai k’ura a gaba. 

  Gyaran murya yayi yace, “Tashi haka toh kiyi wanka muyi sallah baccin ya isa.”

   “Toh ka daina kallo na” tayi maganan idanta rufe gam. 

  “Yau kuma? Tashi kinga lokaci na k’urewa.”

  “Toh Ya Afzal ka tashi ni idan da hali ma ka fita idan na kimtsa zanyi maka magana” ta sanar da shi. Murmusawa yayi sosai “Yau kuma nine Yaya saboda kinji wuya jiya?”

  “Ya Afzal mana” ta fad’a had’e da jawo pillow tana kare fuskanta. 

  “Toh naji naji, zan jiraki a parlour.”

   “Toh ka tafi” mik’awa yayi ya janye pillon a hankali had’e da sanya mata light peck a goshi sannan ya mik’e ya fice. Seda taji k’aran kulluwan k’ofa sannan ta shiga bud’e idon nata a hankali. Haka kawai ta tsinci kanta cikin tsananin farin ciki, se murmushi wa kanta take barin ma idan ta tuna abubuwan da Afzal ya rink’a yi mata daren jiya, yadda ya rink’a binta a hankali yana kashe mata jiki. She felt like a princess, like a baby and all. Aww she’s madly in love with him, a hankali ta mik’e ta nufi bayin. Shiganta ba da jimawa ba Afzal ya dawo d’akin, bedsheet d’in ya tattara yayi disposing. Kafin ta fito har ya shimfid’a sabo ya zauna bakin gadon yana jirarta. 

   “Ya Afzal” ta kirasa lokacinda ta fito tana tsaye bakin k’ofar d’aure da d’an guntun towel. Kafin yayi magana har idonta ya kai ga sabon bedsheet daya shimfid’a kan gadon. “Awwn Ya Afzal ai ko ni ma zan iya canzawa it doesn’t have to be you.”

  “Don’t worry sanya kayanki muyi sallah” ya amsa. Nan da nan ta shirya ya jasu bayan sun kammala azkhar nasu suka shiga shirin office da school. Yau ma kaman kullum shi yayi dropping nata. Nazeefah fa ji take tamkar duniyan ma tayi kad’an ta d’auke ta dan murna da farin ciki kawai. Tuni ta sanya hoton Afzal a home and lock screen nata, idan ta isa gida ma zata canza na laptop nata ta sanya hoton nasa. 

   Da Azahar lectures nasu ya k’are saidai Afzal baze samu daman zuwa d’aukanta ba don haka ya tura driver’n Ummi da ya d’aukota kasancewar yana da meeting. Bayan da ya d’auketa se tayi tunanin ya wuce da ita gida gun Ummi ya kwana biyu basu lek’a juna ba. Sosai Ummi tayi murnan ganinta daman tana da anniyar kai masu visit this weekend saboda shirun yayi yawa. Hira suka sha sosai sekace ba surikai ba, suna cikin cin abinci ne Nazeefah tayi gyaran murya “Ummi?” Ta kirata. 

  “Na’am Nazeefar Mummy.”

  “Kai Ummi wai yaushe zaki sauk’e sunan nan ne kam?”

  “Ko Nazeefar Afzal ce?”

  “Toh ko kefa? Ai hakan ma yafi dad’i” nan suka k’yalk’yale da dariya. 

  “Ahh lallai soyayya manya wannan kumatu da kika k’ara anya kuwa ba abu a k’asa?”

  “Laaa ji Ummi dan Allah ni kinga har zaki sa in mance abinda nakeson tambayarki ma wallahi.”

   “A’a yi hak’uri tambayan ina jinki.”

  “Shin mey yafi burge Ya Afzal game da mace?”

  “Addini” Ummi ta amsa nan take. “Yana bala’in son mace mey addini.”

  “Allah Ummi?”

  “Sosai ma kuwa.”

  “Ai kuwa ya zama dole in koma islamiyya kodan shi ma.”

 “Toh fa mey Prince yayi har ake neman farinta masa rai haka.”

 Hmm Ummi kenan ai komai ma Ya Afzal na mun jiyan nan ya kaini 3G gallery bakiga jakukkunan dana d’iba ba kuma duk ya biya makaranta yanzu kullum shi yake kaini sede idan banida lectures na safe please ki cigaba da sanyasa a addu’a keda kike mahaifiyarsa, nima inayi masa amman naki daban ne. Allah ya taimakesa ya k’ara masa bud’i.”

  Masha Allahu sosai Ummi taji dad’in kalamun Nazeefah ashe in de haka ne Afzal yaji fad’an da ita da Abba su kayi masa kenan. Madallah gaskiya tayi wa Nazeefah murna sede kuma alokacin da ta fara jin dad’in aurenta a lokacin Afzal yake shirin k’aro mata kishiya. Oh kowa de da tasa k’addarar, Allah de ya sa ta d’au hakan a matsayin k’addararta ta kar6a hannu bibbiyu. 

   “A gaskiya naji dad’in kalamanki matuk’a Nazeefah, naji dad’i yanzu da ke da Afzal kuke zaman lafiya Allah yasa hakan ya d’aure ya kuma cigaba da had’a kawunanku.”

  “Ameen Ummi so bayan addini sey kuma mey yakeso?”

  “Addini de itace babba, kika rik’e addini to kin kama k’afansa kenan, inda so samu wannan gyale ma ki daina sanyasu in ba a gida ba, yana son mace me sanya tufafin da ze rufe mata jiki bayan nan kuma mace mey tsafta, mey kunya. Ki zame mey kunya, mey kuma kamun kai ba kowani na miji zakina huld’a dashi a makaranta ba inba wanda ya zama dole ba.” Se kai Nazeefah keta gyad’awa wane mey d’aukan lectures “Nake ga idan kika kiyaye wannan ababen da na k’irga miki toh fa kin riga kin mallake Prince kin zama uwar gidansa.”

  “Thank you very much Ummi in shaa Allah zakiga canji wallahi ina son Ya Afzal and doing just what he likes makes me happy. A shirye nake da in sadaukar da farin cikina saboda nasa, please ki rink’a samin shi acikin addu’a Allah cigaba da karemun shi.”

   *PAGE 2⃣4⃣*

     “Allah cigaba da baku zaman lafiya Nazeefah ki dage da addu’a, itace komai.”

  “In shaa Allahu Ummi zan wuce girki na jira na.”

  “Toh bari ina zuwa.” Kitchen ta nufa chan bada dad’ewa ba ta dawo rik’e da wasu robobi a hannunta. “Ga wannan spices ne k’awata take had’awa wannan a pepper soup zaki na sawa, wannan kuma ko a jollof ko fried rice yana gyara girki sosai nima ina amfani dasu.”

  “Allah sarki Ummi baki gajiya da mun kyauta kullum idan na shigo?”

   “Jibeki ko kin manta a matsayin ‘yata kike? Hungo kar6i ayi ma Prince girki mey dad’i yaci.”

  “Toh shikenan Ummi” ta amsa tana murmushi “Nagode sosai akwai leda ne se in juye in baki robobin?”

  “Karki damu musamman na sai rabobin dan in zuba miki su aciki.”

  “Kai Ummi da wahala haka? Nagode sosai zan ko nunawa Ya Afzal bari in wuce.” Har wajen mota Ummi ta rakata sannan ta dawo ciki. Driver na sauk’e ta a gida ta rage kayan jikinta ta watsa ruwa sannan ta shiga kitchen bayan ta had’a kan girkin ta d’au wayanta ta kira k’awarta Aisha mey siyar da readymade hijabs akan ta kawo mata tana son siya. 

  Se wajajen k’arfe biyar Afzal ya dawo gida, lokacin Nazeefah na zaune da Aisha tana kan za6an hijaban. Mik’ewa tayi had’e da yi masa sannu da zuwa, bayan sun gaisa da Aisha, ya k’arisa ciki. Nan da nan Nazeefah ta gama za6e three quarter hijabai masu hannu kusan kala goma sha biyu. Duka-duka de ya tashi N21,600 kasancewar N1,800 ne kowani guda amma k’awar nata tayi mata ragi akan N20,000. 

  “Toh nagode zan miki transferring kud’in banida enough cash a wajena.”

  “Ba komai toh zan wuce.”

  “Yauwa nagode” bayan tayi mata rakiya ta tattara hijaban ta wuce d’akin Afzal dasu. A lokacin yana mik’e kan gado yana latsa wayansa. A kan gadon ta jibge kayakin yayin da ya kafa mata ido yana kallonta da mamaki. 

  “Wad’annan fah?” Ya tambaya. 

  “Na wa ne” ta amsa tana jin dad’i. 

 “Toh kuma” ya furta yana mamakin ina zata kai hijabai dayawa haka, inde don na sallah ne kam ai sunyi yawa. 

  “Starting today zan soma sanya hijabi ban sake fita da gyale” ta sanar da shi tana k’ok’arin sanya d’aya daga ciki. Da mamaki cike da jin dad’i ya tsaya yana kallonta ba k’arya kuma hijabin ya mugun amsanta. 

  “Ya mun kyau?”

 “Sosai ma kuwa RABB’ATUL BAIT (sarauniyar gida)” ya amsa yana bata full attention nasa. Sosai taji dad’in sunan dukda cewan bata san meye ma’anar ba amma ta de san abun arziki ne. “Duka wannan kika saya?” Ya tambayeta. 

  “Eh zan zo in k’ara ma daga baya.”

  “Wow! I’m really impressed Nazeefah, Allah yayi miki albarka.”

  “Ameen Ya Afzal.”

  “So duka-duka nawa ne?”

  “N21,600 amma tabar mun akan N20k.”

  “Alright zanyi miki transferring kud’in.”

 “A’a kar ka damu inada enough kud’i a waje na.”

  “You shouldn’t bother as well kiyi amfani da kud’in ki sai wani abu daban zan biya na wannan d’in kinji?”

  “Toh shikenan thank you so much Allah k’ara bud’i.”

  “Ameen my Rabba’atul bait.” Dad’i sosai ta kuma ji sede ta kasa hak’ura taji ma’anan sunan dan haka ta tambayesa. “Ya Afzal meye ma’anar Rabba’atul bait d’in?”

   “Wai ashe matar tawa bata jin larabci” ya shiga neman tsokanarta. 

  “Kaga nifa shiyasa banason tambayar ka abu seka gama yi ma mutum dariyar mugunta tukuna amma karka damu kwanan nan zanyi joining islamiyya zaka sha mamaki.”

   “Dagaske zakiyi joining Islamiyya?” Ya tambayeta cike da k’in yarda. 

  “In shaa Allah idan muka samu hutu, ko baka so?”

  “Taya bazan so matata ta shiga neman k’arin ilimin addini ba? I’m very happy in fact nima zan nemo miki islamiyyan da kaina.”

   “Awwn Ya Azal da gaske?”

  “Sosai ma Rabba’atul bait.”

  “Toh gayan mey ma’anan sa?”

  “It means The queen of my home (sarauniyar gida na)” bata san sanda ta shiga blushing ba. “Am I really?” Ta tambayesa cike da kunya da kuma jin dad’i. 

   “Yes Nazeefah you are.”

  “Awwn Ya Afzal thank you so much I really am in love with the name.”

  “You’re welcome” ya amsa yana mayar mata da murmushin shima. 

  “I feel honored kaima ka jira nan da lokaci kad’an zan nemo maka romantic name in baka.”

   “Toh shikenan ina jira.”

  “Yau baka jin yunwa ne? Naga ko tambaya na abinci bakayi ba.”

  “Ai nasan food will always be ready as long as kina gidan nan so yau mey aka girka mun?”

  “Fried rice ne da pepper chicken.”

  “Wow! Har wani fitinannen yunwa ya kamani, let’s go?”

  “Let’s go” takawa yayi ya k’arisa inda take, da hannunta rik’e acikin nasa suka k’arisa dining d’in inda tayi serving nasa saidai spoon d’aya ya kai baki ya tsaya yana exaggerating girkin wai yayi dad’i murmusawa tayi sirrin Ummi ta fad’a a zuciyarta. Seda suka gama ci take fad’a mishi dalilin daya sa abincin yayi dad’i sosai yau, spices da Ummi ta bata ne. Sosai yaji dad’in zuwa duban Ummi da tayi ba tare da ya sanar da ita ba.

****                  ****

   “Abba ai wannan kaman tonawa Baby asiri ne” Mami tace da Papi yayinda suke zaune a d’akinsa. 

  “Kaman ya tona mata asiri Jameela?”

  “Abba banda ni da kai fa ba wanda yasan 6oyayyan al’amarin nan a tunani na ba amfanin sanar da iyayen Afzal wannan batu, mu rufa wa kanmu asiri kaman yadda Allah yake rufa mana banga amfanin tozarta kanmu wa mutane haka ba.”

  “Ya kike magana haka Jameela? Shin bakisan duk auran da aka ginata akan k’arya bata d’aurewa ba?”

   “Na sani Abba amma gani nake kaman mutuncin mu ne ze zube barin ma naka dana Baby, wallahi da wuya mutanen nan su sake d’aukan Amal da k’ima da daraja ba.” 

   “A’a Jameela, ba wani zancen abin kunya ko kuwa zancen zubewan mutunci anan, ba wanda yafi k’arfin jarabawa da k’addara. Gaskiya kuma ko bamu fad’eta ba wataran zata fito da kanta don haka gara mu fad’a musu komai da bakin mu akan suzo su gano gaskiya wataran, a gani na hakan ne zai zubar mana da mutunci da daraja a idonsu.”

  “Amma Abba yau shekara nawa? Kusan ashirin amma banda mu ba wanda yasan wannan labari, tunda muka baro Askira ba tashin hankalin da ya sake binmu kana ganin ya dace mu sake jefa kanmu acikin wani rud’anin?”

  “Ki kwantar da hankalinki Jameela in shaa Allah ba rud’anin da ze biyo bayan yin abinda ya dace.”

  “Toh shikenan tunda kace haka se a sanar dasu d’in dama ni kawai ina gudun tokarin da za’a zo ana yi wa Baby ne.”

  “Har wa ya isa yayi mata tokarin? Ai ba lalle ne akace se sun aureta ba idan sunga bazasu iya auranta a haka ba walillahil hamd dama tun farko su sukace suna so ba tallar su akayi mata ba, amma kam ba dani za a a gina aure akan k’arya ba. Abinda ka raina kake ganin ba komai ba shi zezo ya zame maka babban matsala nan gaba. Ke zaki gani kaman ba komai bane yanzu koda ba’a sanar dasu ba amma rananda k’wai ya fashe se mutum ya raina ka yaga kaman ka ci mai amana ne ka zaluncesa saboda haka yanzu ne lokacin da ya dace da a sanar dasu gaskiyan al’amarin idan sunga su bazasu iya had’a zuri’a da ita ba shikenan Allah ze kawo mata wani, hannun mutum baya ru6ewa ya yasar.”

  “Tsakani na da Khalifah sede Allah ya isa, Khalifah ya cuceni a rayuwa bansan da wani idon zan sake kallon Baby ba idan har ta jiyo gaskiyan labarinta, Khalifah ya cuceni ya cuceni!” Ta rushe da kuka. 

  “Yanzu kuka kike saboda Baby ta shigo ta tsince ki ahakan ko mey? Kisani Baby baza ta ta6a yi miki mumunan fahimta ba, sanin kowa ne Khalifah ne ya cuceki bawai ke kika cuci kanki ba. Ya auna tunaninki ne da k’arancin shekarunki yayi riba da hakan, shiyasa kika ga koda ‘yan unguwa da dangi suke tsangwamar ki nayi tsaye na kareki, koda wasa ban ta6a baki laifin abinda ya faru ba kuma bazan ta6a ba Jameela ni nasan kalan tarbiyyan dana baki.”

  “Abba banida kaman ka, bazan ta6a iya biyanka kalan halaccin da kayi mun ba a rayuwa fatana kawai Allah ya sak’a maka da gidan aljannah.”

  “Ameen share hawayen naki haka ki shirya abinci wa bak’in namu munyi waya da Abban Afzal d’in yace suna tahowa.”

  “Toh shikenan Abba” da haka ta fice instead ta wuce kitchen seta nufi d’akin Amal inda ta tarar da ita kwance kan katifarta. Tana jin k’aran k’ofa ta 6oye wayarta da take ta faman kallon hotunan Ya Abdul k’ark’ashin pillow. 

  “Bade bacci kike ba?” Ta soma da tambayarta. 

  “A’a nagama tilawa ne nace bari in d’an huta.”

  “Oh dama nazo ne muyi wata magana” A nan Amal ta mik’e ta zauna tana mey baiwa Mami full concentration nata “Ina jinki.”

  “Baby kiyi hak’uri ki yafe mun” ta sanar da ita. Cike da rud’ani Amal ta tsaya tana kallonta “Mami hak’urin mey kuma kike bani? Ai baki yi mun komai ba.”

   “Ko da wasa kar kice haka ‘yata, laifin da na miki har yau ba wanda yayi maki irinsa, Baby na cuceki a rayuwa, nayi miki k’arya gabad’aya rayuwarki, k’aryan da ban san ta ina zan soma wanke kaina ba amma dan Allah ki gafirceni kisani ba haka hali na yake ba, k’addara ce ta riga fata.”

   “Mami ban fahimceki ba dan Allah meke faruwa?”

  “With time zaki fahimci komai Baby ni gafararki kawai nake nema.”

  “Mami baki yi mun komai ba ni don haka nakeson ki daina tambaya na yafiya, you have nothing to be sorry for” k’arisawa tayi tare da hugging nata. “I love you so very mucu Mami no matter what.” 

   “Allah yayi miki albarka Baby, ya cigaba da kare mun ke ya sanya miki albarka acikin dukkan al’amuranki.”

  “Ameen Mami please don’t cry” a hankali ta saketa ta shiga share mata hawayenta sannan suka wuce kitchen d’in tare suka shiga had’a kan girkin. 

   Bayan La’asr Afzal da Abbansa suka duro gidansu Amal. Bayan taransu da su Papi sukayi Mami ta sa Amal fito musu da drinks da aka tanadar musu don Abba ya ganta. Daga baya-baya ta tsuguna ta gaishe sa cike da ladabi da biyayya kanta sauk’e a k’asa bayan nan ta gaishe da Afzal sannan ta k’arisa ta ajiye tray d’in daga gabansu sannan ta tsiyaye musu juice d’in a cup each. 

   ‘A gaskiya Afzal ya iya za6i’ abinda Abba keta furtawa a ransa kenan haka kawai Amal ta shige masa zuciya. Kaman yadda Afzal yake son mace kamila mey kunya shima mahaifin nasa haka ne, kamun kai, fasali da kunyan Amal ba k’aramun burgesa yayi ba, fatansa Allah basu zuri’a d’ayyiba. 

    Bayan Papi ya sanar da su Abba date da Amal ta za6a su Abba suka amince right away, bayanin komi dalla-dalla Papi yayi musu akan cewa ta za6i February d’inne saboda by then ta samu hutu a makaranta kuma da ikon Allah ta samu ta had’a haddan Al~Qur’anin da takeyi. Abba couldn’t ask for more akan fasali da kamilancin nan kuma ga hafizancin Al~Qur’ani madallah nan take yafara shawaran kyautan da ze bata ranan sauk’an nata. Bayan Mami ta mik’e ta basu waje, Papi yayi gyaran murya ya fara kaman haka, “Godiya ya tabbata ga Allah yadda komi yake tafiya lami lafiya.”

  “Tabbas, mune da godiya Mallam Muh’d Allah sak’a muku da alkhairi ya ji k’an mahaifa.”

  “Ameen ameen saidai wani hanzari ba gudu ba.”

  “Toh toh ina sauraranka.”

  “Batun Amal ne, a gaskiya ni mutum ne mey fad’in gaskiya a ko da yaushe komin d’acinta komin kuma ya take.”

  “Tabbas haka wannan yake ni kaina na fahimci hakan a d’an cikin kwanakin nan da muke tare.”

  “Madallah, kasan shi gaskiya komin d’acinsa fad’inta yafi barinta da tayi tsami.”

  “Tabbas Mallam Muh’d.”

  “Ban san ya kai da Afzal zaku kar6i wannan labari ba amma ya zama dole a matsayina na wanda Amal take hannunsa in sanar daku duk wani abinda na sani game da ita baze yuwu don son abun duniya ko makamancin hakan inyi muku k’arya in tauye muku hak’k’i ba saboda son zuciya da gudun abin kunya.”

  Na matuk’a both Afzal da Abbansa suka shiga cikin rud’ani amma ba wanda ya iya bud’a bakinsa ya tambayi meke faruwa, shiru sukayi suna jiran jin k’arshen labarin. 

  “Shi aure abu ne babba wanda ko addininmu ma ya nuna mana fa’idarsa shiyasa bana wasa da sha’aninsa, idan aure yayi kyau toh zuri’ah ma zatayi kyau idan ko ta 6aci zumunci da komai ya lalace kenan. D’aya daga cikin ababen da yake rusa d’aurewan aure kuwa shine ginata akan k’arya.”

  “Wannan haka yake Mallam Muh’d” Afzal de ido ya zubawa Papi yayinda hak’urinsa ya gaza don jin k’arshen wannan labari. 

  “Shiyasa nace tun kafin magana yayi nisa gara in sanar daku wannan al’amarin dake 6oye a gareku. “

  “Ina jinka Mallam Muh’d.”

  “Sanin kanku ne ba nine mahaifin Amal ba, Kakanta nake amma a hannu na ta girma.”

  “Wannan haka yake Mallam Muh’d.”

  “Afzal nasani ko ban tambaye ka ba ze iya yuwuwa Amal ta ta6a maka magana batun mahaifinta akan ya rasu, hakane?”

  “Hakane Papi da jimawa ma kuwa, a kullum addu’an mu na tattare da shi Allah ya jik’ansa ya sa mutuwa hutu ce a garesa.”

  “Ameen” Abba ya amsa. 

 “Gaskiyan al’amarin shine banida yak’inin hakan. Kaman yadda bazan iya cewa eh gashi Abban Amal ya mutu ba haka zalika bazan iya cewa yana raye ba, masani se Allah.”

  “Sorry?” Afzal da kansa ya d’aure yayi saurin tambaya. “Kana nufin baku san inda ya shiga ba kawai kukayi assuming ya rasu?”

  “Haka nake nufi Babana. Daga ni har Mamin nata bamu da masaniya akan inda bawan Allan nan yake.”

  “Subhanallahi! Allah ya fito dashi a duk inda yake toh” Abba ya fad’a yayinda Afzal ya amsa da “ameen.”

  “Ina son ku sani cewa ba a haifi Amal da uba ba, Amal bata da uba” kat kuma seya yi shiru. Yadda kuka san anyi mutuwa neither Afzal nor Abba spoke up. Shiru kukeji a wajen yayayinda fuskokinsu ke d’auke da d’imbun mamaki da neman k’arin bayani barin ma Afzal. 

  “No this can’t be possible” Afzal ya shiga k’aryata zancen daga bisani “No I’m not believing this, taya zakace an haifi Amal ba uba bayan ita da bakinta tace mun ya rasu ne please Abba tell him this’s not possible” yayi stating a kid’ime. A lokaci guda ya fita daga hayyacinsa. Taya batin kowa ace Amal tasa ce bata da uba? Wai mey ma hakan ke nufi? So ake ace mai Amal tasa shegiya ce? Bayan duk kamala, kamun kai, addini da hankalinta? No! Baze ta6a yarda da hakan ba. 

   “Afzal kayi hak’uri nasan ni mey laifi ne, yaci ace tun farko na sanar da kai da mahaifinka gaskiyan al’amarin ba se na bari har magana ta kai ga matakin aure ba amma kuma Allah be bani ikon yin hakan ba se yau, ka sani ko da wasa ban so zolayar ka ba. In da kuwa hakane da bazan ta6a sanar daku wannan al’amari ba dukda muhimmancinta se idan ranan da dubu ya cika saboda haka nake sake baku hak’uri idan har duk tsawon lokacin nan kunga kaman na 6ata muku lokaci ne ku gafirceni. Gaskiya de d’aya ce kuma na fad’eta ba a haifi Amal da uba ba tunda mahaifin nata ya samu abinda yake nema daga gun mahaifiyarta bamu sake ji daga garesa ba har yau. Yanzu haka Amal bata san da wannan magana ba saboda ba wanda ya ta6a sanar da ita gaskiyan labarin ta.”

  Shiru ne ya d’au wajen, daga bisani Afzal ya shiga magana “Mey hakan ke nufi kenan Papi?” ya tambayesa cikin rud’ani “Kana nufin zaku rabani da Amal kenan?” Har anan Abba bece komai ba. 

  “Ba wai haka nake nufi ba Afzal shawara ya rage naka da na iyayenka kaman yadda bazan iya tilasta maku auren Amal ba haka bazan iya hana ku ba ni duk abinda kukace shi za’ayi kawai bana son agina aure ne akan k’arya.”

  “Kaman ya Papi? Wani irin magana kake haka? Dan an haifi Amal ba uba shikenan se na k’ita? Laifin ta ne? Ya kake magana haka Papi?”

  “Ba wai abinda nake nufi ba kenan Afzal ka fahimceni, kade san irin zamanin da muke ciki a yanzu, yadda ake tsangwan yaran da suka tsinci kansu a cikin hali irin na Amal. Ni kuma muddin ina raye bazan bari aci zarafinta ba. Amsan ku nake jira idan kunga baza ku iya had’a zuri’a da ita a hakan ba toh kar kuji komai ku sanar dani haka Allah ya k’addara.”

   “Tabbas kayi gaskiya Mallam Muh’d sam ba k’arya acikin abinda ka fad’a ko d’aya kuma ina gode maka na bud’e mana cikinka da kayi har ka sanar damu wannan sirri me uban nauyi. Ina son ka sani cewa sirrinka is safe with us, ba wanda ze kuma yaji wannan magana bale har hakan ya jawo wa Amal matsala a rayuwarta. Ya zama dole in yabawa halinka, a gaskiya samun irinku a zamanin yanzu se an tona. Sai dai ina son ka sani cewa this will not change a fact, kasani baza mu bari wannan labari ya dawo mana da hannun agogo baya ba kokuwa yasa a fasa abinda aka fara. Muddin Afzal yana son Amal kuma yana son ya aureta ko a hakan ni da mahaifiyarsa bamu da matsala saboda ba laifin Amal bane don an haifeta ba uba baza kuma a k’i ta don hakan ba so Afzal” nan ya juyo yana kallonsa “Mey zaka ce game da wannan al’amari? Kasani abinda kakeso shi zanyi maka.”

  “Abba bansan na mey kake tambayan baki na ba, I love Amal and ko a yaya take zan aureta I don’t care ko ta rasa ganinta kokuwa ji. Ko da gurguwa ta koma zan aureta a hakan saboda zuciyarta nakeso ba looks nata ko asalinta ba. I love her and I’ll marry her regardless.” Sosai Papi yaji dad’in kalamun Afzal da Abbansa tabbas sun cika mutanen k’warai sun kuma nuna wa Amal so tsakani da Allah. 

   “Toh Mallam Muh’d kade ji, saboda haka nake son ka kwantar da hankalinka ka sani wannan aure kaman an riga an d’aura ne da izinin Allah.”

  “Toh madallah Allah sanya albarka aciki ya nuna mana ranan.”

  “Ameen ya Allah” Abba ya amsa.

  “Papi ina da alfarma please” Afzal yace. 

  “Ina jinka Babana.”

  “Kace Amal bata da masaniya game da al’amarin nan ko?”

  “Bayan ku da nake sanar ma wannan labari da mahaifiyarta ba wanda yake da masaniya ga al’amarin nan kuma nakega se ‘yan unguwan da suke nan lokacin da abun ya faru a garin Askira.”

  “Papi please kada a ta6a sanar da Amal wannan magana.”

  “Ko meyasa kace haka Afzal?” Ya tambayesa cike da son k’arin bayani. 

“Bana son hakan yasa ta tsani kanta ta fara guje wa mutane ciki harda ni, please kar a fad’a mata komai this should remain as a secret between us kamin alk’awari kai da Mami baza ku ta6a fad’a mata komai game da maganan nan ba. I want her to remain the Amal that she is, with equal right like everyone possesses.”

  “Afzal-“

  “Please Papi, Abba dan Allah ka rok’eshi da kar su sanar da Amal komai wallahi nasan halinta kad’an ne daga cikin aikinta bayan taji labarin nan tace ta fasa auren saboda tunaninta bata zeyi bata kai ta auri d’an halak ba, I love her this way and I wouldn’t wanna be separated from her.”

  “Toh Mallam Muh’d kade ji alfarman da Afzal yake nema inda hali kada a sanar da Amal d’in kaman yadda ya buk’ata dan Allah.”

  “Alhj Amin nifa duk abinda kukace shi za’ayi saboda kun nuna mun halacci kun nuna wa Amal d’ina soyayyan da bayan nida mahaifiyarta bana tsammanin akwai wanda ze sake kwatanta mata irinsa idan har kuna ganin fad’a mata wannan magana ze iya jawo matsala se a fasa Allah tabbatar mana da alkhairi.”

  “Ameen nagode” Afzal ya fad’a “Thank you so much Abba thank you Papi.”

  “Ba komai d’an albarka Allah cigaba da yi ma albarka.”

  “Ameen Papi thank you.”

  “So zamu koma Afzal bismillah jeka fiddo da kayakin toshin.”

  “Wasu kayakin toshi kuma Alhj Amin?”

  “Yadda de al’ada ta kawo d’an akwatuna uku ne da naka guda d’ai dana mahaifiyarta itama.”

  “Shikenan mu kuma aikin mu komai aka kawo hab mun kar6a?”

  “D’aya daga cikin riban haifan ‘ya mace kenan. ‘Ya’ya mata arziki ne.”

   “Hakane kam amma namun yayi yawa ne.”

  “Toh wannan kuma sede kayi musu da al’ada dan ni shi nake bi tashi Prince ga makullin motar.” Afzal da kansa ya shigo da akwatunan da suke guda biyar in number seda kit guda d’aya making it six. Godiya sosai Papi yayi sannan ya rakasu har bakin k’ofa. A hanyan su na komawa gida Afzal ya rok’a Abba da komin yaya karya sanar da Ummi wannan 6oyayyan al’amari ya buk’acesa da maganan da ya zauna a mtsayin sirri a tsakaninsu su biyu kad’ai. Abba beyi jayayya da hakan ba, shi de addu’ansa d’aya ne yadda Afzal ke son Amal da yadda itama ta sadaukar da soyayyarta masa Allah sa soyayyan nasu ya d’aure. 

  Bayan dawowan Papi ciki ya kira Mami inda yake nuna mata kayakin da su Afzal suka sauk’e yake kuma sanar da ita alfarman da Afzal ya rok’a. 

  “Toh Alhamdulillah sede nayi kaud’i na sanar da Baby nifa.”

  “Kin sanar da ita mey? Yaushe?” Ya tambaya cike da k’in yarda. “Da izinin wa?”

  “Bawai na fad’a mata ainihin labarin ba neman tubanta kawai nayi da ta yafemun idan labari ya isketa.”

  “Toh da sauk’i dan Afzal yace baya son a sanar da ita komai.”

  “Allah sarki yaron nan ya cika d’an halas wallahi, tsakani da Allah yakeson Amal Allah yasa son ya d’aure har bayan auransu.”

   “Ameen kira Baby’n ku shiga da kayakin ta duba barin shiga da nawa nima.”

  “Sun amince da ranar da muka d’aukan ko sun buk’aci ayi canji beyi musu ba?”

  “A’a sun nuna komai ya musu yanzu de rana kawai ake jira.”

  “Toh madallah Baby!” Ta k’olla mata kira. 

  “Na’am” ta amsa daga ciki. 

  “Fito mu shiga da kayakin gashi har akwatuna uku kika samu na toshi.”

***** 8:12pm 

  Nazeefah ce a kitchen tana dafa musu  indomie ita da Afzal yayinda yake zaune a kan gado a d’aki yana had’a kan ragowan aikin da ya rage masa a office sega wayansa ya shiga ruri dubanwan da zeyi yaga Amal ke kira wai! Wata sabuwa, baze ma iya tuna rabon da ta kirasa ba. Be 6ata lokaci ba yayi picking, “Se yau aka tuna dani kenan.”

   “Ai kullum kana cikin raina Yaya makaranta ne bayi bari na.”

  “Toh ya kike?”

  “Lafiya k’alau ya aiki? Ya gida? Ya Nazeefah?”

  “Alhamdulillah komai k’alau ya school?”

  “School se godiya.”

 “Madallah Allah taimaka toh.”

  “Ameen Yaya da wahala haka kuma?”

  “Wani wahala ne kuma Lily nifa bana son godiyan nan naki.”

  “Kayi hak’uri amma godiya ya zama dole Yaya, mungode sosai Allah saka da alkhairi ya k’ara bud’i please ka tayani yiwa Ummi godiya.”

  “In shaa Allah Lily.”

 “Toh goodnight kar in shiga hak’k’in Nazeefah.”

   “Toh Lily goodight, I love you” daga nan ta katse. Mayar da wayan yayi ya ajiye yana me tunanin abinda Papi ya fad’a masa. Sede ya kasa yarda da hakan har yanzu gani yake kaman mafarki ne, shi Amal kawai yake tausayawa yasani komin jimawa wataran gaskiya ze fito he can’t imagine the kind of pain Amal will go through idan ta gano gaskiyan labarin asalinta shide ya d’au alk’awari no matter what baze ta6a goranta mata da komai ba he’ll love her until his last breath.

***

  A kwana a tashi kaman gobe ne ga mey rai a haka har su Amal suka kammala exams nasu na first semester daga nan ta mayar da hankalinta sosai ga karatun Qur’aninta dan son samu ta had’a kafin auran nasu, dududu saura watanni biyu ne bikin. 

   Ta fannin Afzal da Nazeefah kuwa sun gama shiri tsaf a yau jirginsu na zuwa Saudi ya tashi amma kafin nan seda suka bi gida sukayi sallama da kowa. Kaman yadda ya d’au wa Amal alk’awari, suna isa Jiddah yayi texting nata akan cewa sun isa lafiya. 

  Nazeefah dan farin ciki fa ji take kaman ma duniyan bazata iya d’aukanta ba. Lafiya k’alau suke zama ita da Afzal duk wani abinda tasan yana iya 6ata masa rai batayi, yi tayi bari ta bari. Ba k’aramin jin dad’in zama da ita Afzal yake ba, ba tashin hankali ba komai se zallan soyayya da kwanciyan hanakli. Haka nan tun sauk’ansu a Saudi kusan kullum se sun fita sunyi shopping sun fita yawo, sede wayon Afzal duk abinda ya sai wa Amal baya barin Nazeefah ta gani, ko da wasa be ta6a kawo abu d’aya daya saya wa Amal a hotel room nasu ba. Wani balarabe mey hankali ya samu wanda yake ajiye kayakin nasa a wajensa. Yau satinsu d’aya kenan amma tun kiran Afzal da Amal tayi don yi mai sannu da zuwa bata sake kiransa ba shima kuma da gan-gan be sake yi ta kanta ba, Allah ma yayi Nazeefah na d’auke masa kewa da idan yayi wasa se wani attack d’in ya sakd kamasa. Sosai yake missing nata amma yayi making mind nasa muddin ita bata kirasa ba toh shima baze sake kirarta ba har se idan sun dawo Nigeria lafiya. 

   Nazeefah na wanka a bayi kasancewan zasu fita unguwa kawai sega call na Amal dan mamaki yama kasa d’agawa seda call d’in ya kusa tsinkewa tukun. 

  “I’ll call you back” ya sanar da ita had’e da katsewa. Mik’ewa yayi ya fice inda ya sauk’a k’asa sannan ya kirata. Bayan sun gaisa yake ce mata “Se yau aka tuno dani kenan ai na d’au bazaki kira ba.”

  “Shine kak’i kira kaima wato ko?”

  “Gani nayi kaman ina damunki ne Lily not as before kwata-kwata yanzu baki kirana ko na kiraki ma Allah-Allah kike mu gama wayan ki huta ko ba haka ba?”

  “Se gashi na baka kunya na kiraka kuwa.”

  “Waya sani ko Mami ce ta sanya ki na dole kaman ma ina jin muryarta k’asa-k’asa.”

  “Kai Yaya banda sharri de ya Nazeefah?”

  “Lafiyarta k’alau tana wanka ma muna shiri zamu fita.”

  “Toh yayi kyau a dawo lafiya se anjima.”

  “Wait!” ya katse ta.  

  “Yes?”

  “Baki fad’a mun mey kikeso ba fa, ko bakiya son tsaraban Yaya?”

  “Ina so mana.” 

  “Then tell me then mey kikeso, name anything.”

  “Anything?” Ta tambayesa tana nazari. Sosai yake jin dad’in hiransu na yau. Watarana Amal ta sake tana hira dashi koda shike yasan ba har cikin ranta take hakan ba kawai de tanayi ne but even still he can’t help but to feel happy. 

  “Anything Lily” ya jaddada mata. 

  “Ni tsarabar kanka kawai nakeso, ka taho mun da kanka cikin k’oshin lafiya.”

 “Shikenan abinda kikeso?”

 “Yes Yaya” ta tabbatar masa. 

  “Toh karki damu dal acikin leda zan kawo miki kaina.”

  “Wani dal acikin leda kuma? Zan de yi maneji da kai ko ka manta kai ba saurayi bane yanzu?”

  “Aww abun kuma gori ya koma?” Dariya tasa ta cikin wayan shima besan lokacinda ya jonata suka cigaba da dariyan ba. Ba k’arya acikin soyayyan da yake yi mata, ita ta daban ce, he’ll choose spending time together with her than anything in this world. Shi kansa ya san son da yakeyi mata bayida k’arshe kaman yadda bayida farko. Da alama Allah ya soma amsa masa add’o’in da yata sauk’ewa akan Amal ne a gaban ka’aba shiyasa ta soma sakewa da shi haka. 

   “A hakan kuma zaki aureni ba.”

  “Don’t get too confident ina iya nemo d’an saurayi na in aura.”

  “Nine nan de d’an saurayin naki karma ki 6ata lokacinki.”

  “Toh Yaya kar na cinye wa uwar gidanmu lokaci je ka tayata shiri se anjima ko? Mami tace in gaishe ka.”

  “Toh ina amsawa thanks for calling baby I love you.” Wani irin bak’on yanayi ta tsinci kanta da yakirata da ‘baby’ dukda cewan sunanta ne na gida amma setaji wani iri kodan tana da tabbacin da wata manufar ya fad’a ne?

  “You take care” da haka sukayi sallama. Afzal ya kasa 6oye farin cikin da ya tsinci kansa aciki, se kallon ckin wayan nasa yake yana cize la66e. Da murmushi kwance fal a fuskansa ya haura sama d’akinsu inda ya tarar da Nazeefah zaune akan towel tana shafa mai. 

   “Ya rouhi (my soul, sunan da take kiransa da shi) ina kaje?” Ta soma da tambayarsa. 

  “Wani friend d’ina ne yazo na sauk’a muka gaisa” ya had’a mata k’aryar nan take. 

  “Ai na d’au tafiya kayi ka barni.”

  “Har na isa in fita ba tare da Rabba’atul bait d’ina ba? Ko de so kike hukuma ta kamani?”

“Har kana tunanin zan bari hukuma ta kamaka?”

  “Toh gashi na d’au kafin in dawo har kin gama shiri sede gashi mai ma kike kan shafawa.”

  “Toh Ya Rouhi ai bazaka had’a tsawon wanka na da naka ba kaifa cikin minti biyu shaa ka yi wanka ka fito.”

  “Ke kuma har sama da minti talatin ba.”

  “Eh mana” ta amsa tana murmusawa. 

  “Toh shirya dai ina jiranki.” Zama yayi akan gado yana kallonta yayinda take ta shafa manta a hankali. A garin mik’ewa bayan da ta gama shafa man towel nata ya kusa sincewa da hanzari ta tattare sekace wacce aka ce mata idan ta bari towel d’in ya fad’i toh wuta za a kaita. Yadda ta kid’ime ne ya sanya Afzal dariya, ba shiri ya shiga dariya har yana neman k’warewa. Har akwai abinda be gani bane a jikin nata da take wannan rawar jikin? Shi bata ma ishesa da kallo ba. 

  “Ya rouhi wallahi mugunta ba kyau” ta sanar dashi tana turo baki. Dariyar yake har yanzu da k’yar ya iya ya tsagaitar sanan ya mik’e ya k’arisa inda take tsayen had’e ca janyota jikinsa yana mey zagaye hannayensa a ‘yar k’ugunta yayinda da ta zagaye nata a wuyansa. 

  “Toh koda towel d’inma ya kunce mene ban gani ba anan d’in Rabba’atul bait?” Ya tambayeta yana yi mata nuni da ido. 

  “Kai Ya Rouhi dan Allah ka dena” ta fad’a cike da kunya, kafin tace zata sauk’e hannayen nata daga wuyan sa yayi sauri ya miyar dasu. A lokaci guda wani zuciyan ya raya masa da ya sanar da ita cewan ya kusa k’ara aure saboda this is the right time da zata yima kanta addu’a ko Allah ze sassauta mata zafin kishinta yayinda wani zuciyan kuma ya hanasa yin hakan yana rinjayansa cewan ai akwai sauran lokaci.

 “Tunanin mey kake haka Ya Rouhi?” Ta tambayesa a hankali bayan tsawon lokacin data d’auka tana kallonsa. 

  Kai yayi saurin kad’awa yana me sake matso da ita kusa da shi, har nishinsu na had’ewa sannan ya murmusa yana mey kallon cikin dara-daran idanunta. “Was I thinking of something?” Ya tambayeta. 

 “Gashi gabad’aya hankalinka baya jikin ka.”

  “Well I’m just happy that you’re happy being with me.”

 “Awwn Ya Rouhi being with you is my absolute pleasure. I love you so much, so much that bazan ma iya kwatantawa ba.”

  “Allah?”

  “Sosai fa wallahi k’awaye na har cemun suke wai nafi sonka fiye da yadda kakeso na kuma Allah na yarda da hakan.”

  “Ko meyasa?”

  “Saboda baka ta6a cemun kana so na ba koda kuwa ni na fad’a maka” ta fad’a sincerely. Sosai ya tausaya mata saboda yasan how she must be feeling anytime yayi mata hakan, shima duk lokacin da yace wa Amal yana sonta amman tayi shiru tak’i mayar masa da amsa ba k’aramin damunsa hakan yake ba, wai a hakan ma shi na miji ina ga Nazeefah ita mace kuma? Murmusawa yayi “Then stop feeling sad about it.”

  “But I can’t.”

  “You have to because I love you too my rabba’atul bait” ya sanar da ita. Har cikin ranta taji dad’in kalamun nasa yayinda suka kwanta a birnin k’irjinta . 

  “Ze iya yuwu wa ban ta6a furta miki ba amman ba wai hakan na nufin bana sonki bane I love you so much.”

  “Dagaske Ya Rouhi? You really love me?” Ta tambayesa yayinda ta kasa 6oye farin cikin da ta tsinci kanta aciki. 

  “Wai tayaya ne ma bazan fara son wannan kyakkyawar yarinyar da bata da burin da ya fi taga ta farinta mun ba? Mace mey ladabi da biyayya, da iya soyayya da kuma sanin ya kamata, macen da ta gwammace ranta ya 6aci da nawa ya 6aci, wacce ta tsani ganin fushi na. Macen da kowani na miji zeyi alfaharin samunta a matsayin uwar gidansa taya ya kike tsammanin bazan so ki ba my rabba’atul bait? Amsa da kanki you think it’s possible?” Kai ta kad’a a hankali cike da kunyan jin dad’i. “I love you kinji? I love you so much my rabba’atul bait.”

  Bata san lokacinda ta soma zubar da hawayen jin dad’i ba “I love you much more Ya Rouhi, my husband, my heartbeat and everything, Allah ya bar min kai ya kare min kai wallahi banjin zan iya rayuwa idan ba soyayyarka.”

  “Shhh!” Ya katse ta yana mey share mata hawayen nata “I’m never leaving your side till eternity bar kukan haka.”

  “Thank you Ya Rouhi” a hankali ya mik’a had’e da sauk’e lips nasa akan nata yayin da ya shiga yi mata wani irin kiss yana kashe duk wani sassa a jikinta. Tuni yasa ta mance da inda take, basu hankara ba kawai suka jisu akan gado. Cike da daraba ya janye towel da take ta faman tare jikin nata da shi ya wullar a k’asa sannan ya shiga sarrafa ta yadda yakeso. Unguwan da basu zo suka fita ba kenan! 

   *PAGE 2⃣5⃣*

   Shirye-shiryen biki kuma aka shiga yi na sosai, kaman yadda akayi bad’ad’in bad’a haka aka kuma. Kyautan gida Abba ya sake yiwa Afzal a matsayin gudumawan da ya bayar. Sosai Ummi take taimaka wa Afzal, kusan komi ita takeyi, duk wani abinda yake buk’ata fa toh tun kafin ya furta zata tambaya masa gun Abba. Akwatuna har guda ashirin da d’aya aka had’a wa Amal sannan na Nazeefah kuma set mey k’waya shida na fad’an kishiya. Kusan duk zannuwan da suke cikin na Amal akwai su a na Nazeefah babancin kawai na Amal sunfi yawa ne. Abinda ya kama daga kan kayan kitchen, gadaje, kujeru, show glasses, rugs, da komai Ummi ne suka siya, ba yadda Mami batayi da ita ba akan ta bari ko wani abu k’adan ne su kawo yaso se a had’a kud’in ayi siyayyan amman Ummi tak’i kasancewar Afzal ya rok’eta da komin yaya karta yadda ta amsa koda kobo ne daga gun su. Sude kawai suyi focusing akan abincin da za’a dafa.

     Mutum na iya rantsewa ‘yar Ummi ce zatayi aure don kalan kayakin d’aki masu tsada da alfarman da ta sai wa Amal. Gida yayi kyau sosai se wanda ya gani. Yau ana saura sati uku d’aurin aure kenan. 

***

   “Halo Yaya?” Tace bayan ta d’aga wayan. 

  “Na’am Baby” ya amsa. 

   “Yaya wai yaushe ka fara kirana da Baby?” Yau kam ta kasa hak’ura seda ta tambayesa. Kusan sati kenan yana kiranta da hakan, kuma da gan-gan yake gano bata so. 

  “Jimin ‘ya da ba sunanki bane?”

  “Ni Amal ne suna na.”

  “Baby’n fah?”

  “Sunan gida ne.” 

  “Ni d’in ba d’an gida bane?”

  “Ni ba haka nake nufi ba kawai na gwammaci kana kira na da Amal ne.”

  “Toh nak’i ni Baby nafi so.”

  “Toh Allah taimake ka, ina yini?” ta gaishesa. 

  “Lafiya d’an fito waje kinji?”

  “Yaya ka fa san an fara yimun gyaran jikin.”

  “Se akace baki sake tako waje?” 

  “Toh ai Yaya idan na rink’a fita muna had’uwa bazaka ga effect na gyaran jikin ba.”

  “Nide fito ina jiranki.” Nan da nan ta janyo hijabinta tasa ta fita taje ta samesa. 

  “Tabarakallah gaskiya Allah yayi halitta anan” ya ce da ita lokacinda ta shiga motan “Masha Allah, Abba yayi gaskiya da yace na iya za6i kin ganki kuwa?”

  “Kai Yaya kadena zolayata mana.”

 “I’m damn serious wai ma yaushe ne auren? I can’t wait any longer.”

   Wani irin ruwa cikinta ya d’auka, ba shiri ta had’iye miyau had’e da tambayansa,

  “Uhm so what brought you here?” Don canza topic d’in. 

  “Is it a crime idan ango ya zo ganin amaryarsa sati uku kafin aurensu?”

  “Ba wai haka nake nufi ba I mean akwai matsala ne?”

  “Ohh wato ma haka kika miyar dani se idan akwai matsala nake tahowa ko?”

  “Goodness! Nifa ba haka nake nufi ba.”

  “Toh yaya ne?”

  “Babu nayi shiru.”

 “Yauwa da yafi kam so jiya kika gama bada haddanki duka wai ko?”

  “Eh.”

  “Congratulations then, Allah sanya albarka aciki yasa idan kika tashi haifo mun yara ki haifa mun hafizai kaman ki Lily I’m so proud of you.”

  “Ameen Yaya thank you” ta amsa tana mey jin kunyansa. 

   “Yauwa wai inji Ummi tunda aka shiga yi maki jere baki je kinga gidan naki ba?”

  “Gida na kuma? Gidan mu de.” Ba k’aramin dad’i lafazin nata yayi masa ba. 

 “Toh gidanmu” ya gyara kaman yadda ta buk’ata. 

 “Eh amma Mami tace cikin satin nan zamuje.”

  “Toh ni nazo in kaiki ne yanzun.”

  “Toh ai ya kamata in sanar da ita kafin nan.”

  “I’ve already done that so don’t worry.”

 “Toh shikenan.”

  “Kafin nan ina fatan kuna waya da tailor’n naki? Idan fa baki tak’ura mata da kira kad’an ne daga cikin aikinta tayi disappointing naki se ranar dinner’n yazo ki rasa kayan sawa.”

  “Yaya ni dole ne se anyi wannan dinner?”

  “Wannan kuma seki tambayi Ummi tunda ita tace zatayi, da kud’in d’inkin ki dana komai ita tace zatayi handling ni karki sani cikin shirgin ku.”

  “Toh ai laifinka ne da kace mata baka buk’ata tunda de Allah yayi wannan ba shine auren ka na farko ba ai zata ji.”

 “Kefa kike gani kaman ba wannan ne aurena na farko ba tamkar sabon saurayin da ze angwance nake jin kaina so be calling the tailor on frequent basis kina mey tuna mata kayan naki, okay?”

  “Toh shikenan.”

  “Sekuma batun wushe-wushe da kamu ko? Lokacin aurenmu da Nazeefah naga su Mummy sunyi mata and I can say I absolutely loved everything about the event inason a naki ma ayi.”

  “Yaya dan Allah kayi hak’uri nifa ban ga amfanin tarukucen nan ba wallahi hanyan kashe kud’i ne kawai, kayan dinner kad’ai kusan dubu d’ari biyu wannan kuma nawa zasu ce? Ni gaskiya banason kashe kashen kud’in haka ya isa.”

  “Toh banda ke da abunki wushe-wushe kam ba al’adanku bane ku shuwa? Ai ya zamo dole kiyi.”

  “Bawani dole d’innan ni kashe kud’i ne bana so.”

  “Laffaya nefa kawai zakisa.”

  “Shi d’in bada kud’i za a siya bane?”

  “Lily wai ni ke miki magana kina jayayya dani?”

  “Ni ba jayayya da kai nake ba Yaya, a matsayina na wacce zaka aura ne nake yi maka gyara.”

  “Toh banaso se anyi wushe-wushen da kamun ga wannan” yayi maganan yana d’auko wata bak’ar leda daga backseat. “Gashi” ya mik’a mata. Amsa tayi ba musu ta bud’e sabon laffaya ta gani me uban kyan k’arshe irin na ‘yan Sudan masu d’ankaren tsadan nan. Yaya!” Tayi exclaiming. 

   “Yayi miki?”

  “Fisabillahi nawa ka kashe a nan?”

  “So kike in fad’a miki kud’in saboda kice baza ki sa ba? Ki kwantar da hankalinki ba tsada.”

  “Mey k’arya…” se tayi shiru

  “Naji mey k’arya d’an wuta bade hakan ze sa in fad’a miki kud’in ba, so yanzu an gama da maganan wushe-wushe se kuma na Kamu.”

  “Ni wallahi 6arna da kud’i ne banaso ga walima ga wushe-wushe ga dinner mey na wani kamu kuma? Kai baka tausaya wa kanka dasu Abba ne kam Yaya? Ni gaskiya ba wani kamun da za’ayi.” 

 “Allah baki isa ba.”

  “Har Allah fa kace Yaya?”

  “Eh baza kiyi auren nan dry ba mey sekace auren dole za ayi miki? Ai ko na Nazeefah da na dolen ne ma anyi celebrating se naki ne zaki wani ce a’a? Ko so kike ki nuna mun auren dole ake shirin miki Lily?”

  “Yaya ba haka bane kashe kud’in ne ya isheni dubi ko tsinke fa ka hana su Papi siya.”

  “Ai ni na d’auke muku ba ku kukace nayi hakan ba kuma ko a addinance ma ya halatta idan miji nada k’arfi ya d’auke wa matar da ze aura da iyayenta nauyin komai so ki daina bothering kanki kinji? Ni naso in d’auke muku kuma ko a ina ma yin hakan ba laifi bane.”

  “Thank you so much Yaya Allah k’ara bud’i, I really like this laffaya, wallahi yayi kyau sosai.”

  “Ameen glad you like it, so kin amince ayi kamun? I’ll just talk to our wedding planner.”

  “Nikam a’a wushe-wushen ya wadatar.”

  “Mey laifin in anyi duka toh Lily?” 

  “A’a gaskiya nikam guda d’aya za’ayi.”

  “Toh wa ze hak’ura cikin mu?”

  “Yaya kai babba bazaka hak’ura ba?”

  “Nak’i hak’uran.”

  “Toh shikenan ni k’arama zanci girma.”

  “Nak’i yarda da hakan.”

   “Toh kuma?”

  “Duka biyu za’ayi.”

  “Wai kam cire kud’i ba amfanin nan baya damunka ne? Wallahi haramun ne ko sena ja maka aya tukun?”

  “Ko ki yarda ko in samu Papi ince mishi gashi tun kafin ayi aurem kina mun rashin kunya ina miki magana sam bakiya ji.”

  “Ni yaushe na yi maka rashin kunya? Sharri zaka soma min tun kafin in shiga gidan naka?”

 “Toh ki amince kai karma ki amincen da kin k’i da kinso se anyi duka hungo wannan” yayi maganan yana d’auko wata bak’ar leda dake ajiye gun k’afansa. “Mey wannan d’in?” Ta tambaya tana warware ledar. Invitation card na programme of events na auren nasu ta tarar aciki, ashe duk surutun nan da yakeyi har ya riga ya sa an buga komai ciki harda kamu da wushe-wushen kawai neman sata surutu yake. 

  “Ashe har ka sa an buga.”

  “Dama in fad’a miki ne kayan da zakisa a kamun already na gun tailorna bada measurement naki.”

  “Ni wallahi har kunyarka nakeji Yaya komai kai kakeyi.”

 “Ba wani abin kunya dama al’adan yarabawa ango shi keyin komai ko cokali mace bata kaiwa gidanta so stop bothering yourself.”

   “I know thank you won’t compensate but thank you so much Allah k’ara bud’i.”

  “Ameen don’t mention so mu tafi?”

  “Eh muje ba kace ka riga ka sanar da Mami ba?” Da haka ya jasu suka wuce gidan nasu wanda yake unguwan Old GRA. Amal seji take kaman komi a mafarki yake faruwa, koda wasa bata ta6awa kawowa a ranta cewan wataran zatayi aure acikin fankacecen gida irin wannan ba, itama 4 bedroom flat ne da parlour biyu se kitchen da store d’aya da kuma guest toilet d’aya. Ita ba abinda yafi burgeta ma kaman yadda aka k’aya kitchen natan, yadda komi yake in purple and white gaskiya ba k’aramin kud’i su Ummi suka kashe ba. Addu’a tayita yiwa Afzal da Ummi dan idan ba addu’ar ba bata tsammanin akwai abinda zata iya yi da ze iya biyansu kalan d’imbum alkhairin da sukayi mata. Gida sekace mutum na aljannar duniya. Bayan ya sauk’eta a gida sukayi sallama sannan ya biya gida gun Ummi. 

   “Kayakin Nazeefan kazo d’auka ko?”

  “Eh Ummi are they ready?”

  “In a moment, amma Prince kace akwati shida be isheta ba se har an yi mata goma? Sekace itace amaryar?”

  “Ummi kinsan halin Nazeefah yanzu haka idan taji na Amal 21 nata shida wallahi ba k’aramin tada mun hankali zata yi ba.”

 “Lallai kam kai kaso amma ban ta6a jin inda akayi kayan fad’an kishiya set goma ba shidan nan da muka had’a mata a farko yayi.”

  “Ayi mata goman kawai kowa ya huta.”

  “Toh shikenan kayaki suna hanya sun kusa isowa.”

  “Alright toh thank you so much Ummi Jazakillahu khair.”

  “Ameen wa iyyaka, ya amaryar tamu? Munyi waya da Mami d’azu tace wai ka d’auki Amal ka kaita duban gidan nata.”

  “Eh wallahi lafiyarta k’alau tana gashe  ki ma.”

  “Ayya ina amsawa, yaya gidan tace wai? Komi yayi mata ko?”

  “Sosai ma, bakiga kalan godiya da addu’an da tayita yi maki ba wallahi.”

  “Allah sarki ‘yar albarka kace mata kar ta damu.”

 “Ai ko na fad’a mata, wai ayi kamu da wushe-wushen da yake kaman al’adansu wai sam baza ayi ba walima ya wadatar ita bata son kashe kud’i dinner’n ma ta amince ne saboda tana jin kunyarki” ya sanar da ita. Dariya sosai Ummi tasa. “Ai ustazancin Amal takan nan kam se a hankali, kuma fa ba komai yake hanata amincewan ba tuna yadda zata fita ba mayafin kirki a idon jama’a ne yake damunta.”

  “Ai kaman kin sani da fari ma cemun tayi wai abaya zata sa zuwa gun dinner’n” Nan ma wani dariyan Ummi ta kuma sawa “Kai!! Amal takan nan drama queen ce, ai nace da tailor’n nata tayi mata decent d’inki, kayan da baze bayyana jikinta ba.”

  “Hakan yayi sosai.”

 “Toh Allah bada zaman lafiya ya nuna mana ranar auren nan.”

  “Ameen Ummi thank you for all that you’ve been through for me wallahi bansan ta ina zan fara biyanki ba.”

  “Ba komai Prince karka damu bayan kai fa ba kowa idan ban yi maka abinda kakeso na lalata ka ba wa zan lalata toh?”

  “Your boy loves you so much.”

  “I love him even more.”

  “So mey Daddy’n Nazeefah yace bayan da Abba ya sanar dashi zan k’ara aure?”

  “Me kuwa zece? Ya taya ka murna mana ai har ya sanar da mahifiyar nata ma don jiya ta kirani take cewa in tayaka murna.”

  “Ayyah Alhamdulillah toh.”

  “Yanzu dey matsalar d’aya ce Nazeefah Allah sa tayi maka kyakkyawan fahimta duk da cewan ka makara, yaci ace ka sanar da ita da jimawa.”

  “Ameen fah wallahi ni har tsoro ma nakeji kinsan kalan zafin kishinta kuwa? Akwai lokacin da Amal ta ta6a kawo mun aldeb sena zuba flasks d’in acikin fridge bakiga yadda hankalin yarinyan nan ya tashi ba da ta ci karo da flasks d’in.”

  “Aikam daga yadda take magana ma mutum ze san tana da zazzafar kishi Allah de sa ta yayyafawa zuciyar tata ruwan sanyi tayi maka kyakkyawar fahimta.”

 “Ameen Ummi” bada dad’ewa ba akwatunan da yasa a k’ara d’in suka iso nan ya had’a dana farkon ya cika goma cus aka sanya masa a booth. Sallama sukayi da Ummi sannan ya fice, se hasbunallai wa ni’imal wakeel yake ta nanata cikin motan yau yasan se gobara ya kusa tashi masa a gida.

   A cikin motan ya baro kayakin ya k’arisa ciki. Mik’ewa tayi tamai sannu da zuwa had’e ba sa light kiss on the lips. 

  “Ya Rouhi ina kaje haka tun d’azu ina jiranka?”

  “Akwai wasu ababen da na kula dasu ne I’m sorry for keeping you waiting.”

  “Ayyah ba komai muje in had’a maka ruwa kayi wanka food is ready.” D’akin nasa suka k’arisa nan da nan ta had’a masa warm water sannan ya shiga. Tana cikin ninke kayakin sa da ya cire dan kaisu laundry room wayan sa dake kan gado ya shiga ruri bata damu ta duba wa ke kira ba ta cigaba da harkar gabanta. Call d’in na tsinkewa meshi ya sake kira se anan ne tayi tunanin bari ta lek’a taga ko waye ne, idan Ummi ce tace mata yana wanka. 

  ‘Lily❤💕’ taga yana flashing akan screen d’in bayan nan ga picture’n Amal da yayi saving contact d’in dashi. Wani irin mumunan fad’i gabanta yayi bata san lokacinda ta shiga yin kakkarwa ba. Tabbas ta wayi fuskan nan amma ta rasa a ina, kode a makaranta ne? Kai da wuya toh a ina ta waye ta? Da hanzari tayi picking kafin call d’in ya tsinke had’e da yin shiru. 

  “Halo Yaya?” Amal ta soma da cewa. 

   “Kina neman waye?” Nazeefah ta tambayeta, Amal na jin muryan tasan na Nazeefah ne bata sake cewa komai ba kawai ta katse wayar. Nazeefah bata kai ga ajiye wayan ba Afzal ya fito daga bayin d’aure da towel a iya kunkuminsa. Kallo d’aya yayi mata yasan ba lafiya ba, idanunsa na sauk’a akan hannunta da ke rik’e da wayan nasa kuwa ya gama tabbatar da abinda ke faruwa. Tabbas Amal ce ta kira Nazeefah kuma ta d’auka. Innalillahi! Meya hanasa shiga da wayan nasa bayi kaman yadda ya saba? Sam ba haka yaso ba, yafi son ya sanar da ita komai da bakinsa ba wai ta gano hakan da kanta ba. Nauyayyan numfashi ya sauk’e sannan ya k’arisa inda take tsayen har yanzu. 

   “Nazeefah-“

   “Da abinda zaka sak’a mun kenan Ya Rouhi?” Ta katse sa. 

  “Meya faru? Mey wayana keyi a hannunki kuma if I may ask?”

  “Kiranka akayi na d’aga” ta amsa. 

  “Kawo muga” ba gardama ta mik’a masa kaman yadda ya k’udura a ransa kuwa Amal d’in ce ta kira. 

  “Wacece ita? Meyasa take ce maka Yaya? Mey ma’anan wannan hearts da suke gaban sunanta?” Ta jero mai tambayiyo a lokaci guda. 

  “Nazeefah calm down.”

  “I can’t calm down Ya Rouhi I can’t! You mean to tell me for all this while dama kana da wata a waje? Wow!” Ta numfasa cike da d’umbun mamaki se ganin al’amarin take kaman raha. 

   “Nazeefah I’m sorry but wallahi inada niyyan sanar dake komai.”

  “Sanar dani mey? Akan kana da budurwa? Seriously Ya Rouhi? Meney bana yi maka a gidan nan da zaka za6i ka k’untata mun haka? Why do you have to flirt behind my back?” By now har idanunta sun soma cikowa da hawaye. 

  “Nazeefah please don’t cry” ya fad’a a kid’ime. Hannun sa tayi saurin cirewa kafin ya samu ya rik’e ta. “I’m not flirting behind your back kema kinsan ba hali na bane hakan, I respect you a lot to hurt you like this.”

  “Then explain mey contact na yarinyan nan keyi a cikin wayanka da kuma dalilin da zaisa tana kiranka Yayanta.”

   “Sunanta Amal and am willing to marry her.” Wani irin mumunan fad’i gabanta yayi aure de?

  “Aure?” Ta nanata cike da k’in yarda. “Aure Ya Rouhi? Aure kake shirin yi?”

  “Yes Nazeefah ina son in k’ara aure kuma Amal nike son in aura, kiyi hak’uri na rashin sanar dake da wuri da banyi ba but kar kiyi tunanin nayi hakan ne don inci zarafin ki. Not at all, I do have a reason for not informing you, nafi son se na gama had’a miki kayan fad’an kishiyanki ne, auran namu is in three weeks time in Allah ya yarda.”

  “No!” kai ta shiga kad’awa yayinda take k’aryata duk wani abinda ya fad’a, take wan irin sharp headache ya kamata. “This can’t be possible” ta shiga cewa “It can never be possible dan Allah kace wasa kake mun Ya Rouhi” ta rok’esa yayinda take hawaye sosai. 

   “Dan Allah kibar kukan haka Nazeefah.”

  “Aure fa kace Ya Rouhi? Mey nayi maka da zaka auro mun kishiya? Idan wani laifin na maka wanda ban sani ba dan Allah ka sanar dani a shirye nake da in baka hak’uri amma please let this be a joke.”

  “It is no joke Rabba’atul Bait and ni baki yi mun laifin komai ba, I love you, you know that right?”

  “No” ta katsesa “You don’t love me Ya Rouhi, you’ve never loved me, inda kana so na da baza ka ta6a tunanin yi mun kishiya ba, why? Why?” Tuni ta rushe da wani irin masifaffen kuka. Rungumota yayi niyyan yi amman sam ta hanasa da k’yar ya samu ya rufe ta gam ajikinsa yayinda kukan nata ya tsananta. Sun dad’e a hakan yana ta bata hak’uri amma ina ta kasa hak’uran se kuka take. Chan ya d’agota daga jikinsa ya shiga share mata hawayen nata “Come with me” ya buk’aceta. Batayi gardama ba ta bisa a baya yayinda ya rik’e hannunta cikin nasa ya jata izuwa parlour inda D’anladi ya jera akwatunan nata. 

   “Do you believe it’s not a joke now?” Ya tambayeta a nitse. 

  “Mey wannan d’in?” Ta tambayesa a hankali. 

  “Kayan fad’an kishiyanki Nazeefah.” Bata iya k’ara yin magana ba yayinda ta rushewa da wani fitinannen kuka mey tsuma zuciya. Shikenan ya tabbata aure Afzal zeyi amma ko be kyauta mata ba, na mey zeyi mata kishiya bayan duk wani abinda yake so tana mishi, bayan nan ace seda aure ya rage sati uku ze sanar da ita? Me tayi da za ta fuskanci hukunci me tsauri haka daga garesa? Bazata iya zama da kishiya ba, da ta zauna da kishiya gomma ta rasa ranta. 

  “Ya Afzal you’re such deceit, ka cuceni kaci amanata kuma ka sani I’ll never forgive you, I’ll never forgive you for tricking me that you did. For all these while you made me believed you loved me ashe ba haka bane wasa da hankalina kawai kake chan a waje kana da wacce kakeso kake kuma son ka aura ka kasance da ita, me na ta6a yi maka da zaka mun wasa da hankali haka? Ashe k’arya kake mun duk sanda ka ce ka yafemun.”

   “Ko da wasa Nazeefah, ki yarda da ni idan nace miki na yafe miki na kuma mance da duk wani abinda kikayi mun da a baya, I’m terribly sorry Nazeefah bazan gaji da baki hak’uri ba ki sani ina sonki, I really do love you.”

  “No you don’t love stop lying to me” Hannayenta biyu ya had’a acikin nasa  “I’m not lying to you Nazeefah, I really do love you wallahi I do.”

   “Wallahi k’arya kake you don’t love me you’ve never once loved me” ta k’aryatasa cikin tsananin kuka. Tausayi sosai ta basa barin ma ganin yadda hawayen ke tsiyaya daga idanunta, na matuk’a ta basa tausayi. 

  “Nazeefah please stop crying” yayi maganan yana k’ok’arin rungumarta sede tak’i barinsa. “Don’t you dare touch me!” Be saurareta ba haka na k’arfi yayi hugging nata ya shiga shafa bayanta a hankali yayinda yake showering kisses akanta. “Shhh! I’ve got you, I love you so much.”

  “Idan da har kana so na da baza ka fara tunanin k’aro aure ba” tayi maganan had’e da raba jikinta da nasa tana share hawayenta “Mey yayi zafi da zaka yi mun kishiya Ya Rouhi? Mey ka ta6a nema a gidan nan ka rasa, girki ne inayi maka, ina respecting naka ina tsaftace maka muhalli baka ta6a neman hak’k’inka a guna ka rasa ba, duk abinda kace kana so shi nakeyi wanda baka so kuwa koda hobby na ne ina k’ok’arin dainawa, mey yayi zafi da har seka k’ara aure?”

  “Nazeefah kin manta ni miji ga mata hud’u ne? Bayan nan bakisan mata sun fi maza yawa a al’umma ba yanzun? Idan kowani na miji yace mace d’aya kacal ze aura sauran kuma waze auresu? Bakiya son ‘yar uwarki ta raya sunna itama ta cika umarnin anmabin mu SAW?” Nasiha ya shiga yi mata sosai saidai ina kishi ya riga ya rufe mata ido bata jin kira. 

  “No Ya Afzal! Bazan bari ka auro wata muddin ina raye, bazan zauna da kishiya ba.”

  “Wayace kishiya zan auro miki Nazeefah? Abokiyar zama zan kawo miki.”

 “Bana sonta bana so.”

  “Nazeefah please calm down kiga baki ma santa ba fa amma kike cewan baki sonta, Amal is a very nice girl ina da tabbacin you two will get along.”

  “Bana son sanin ko ita wacece ina ji ina gani bazan bari wata ta sace mun kai ba Ya Afzal, I’ll do whatever it takes in tabbata wannan aure be auku ba you’ll see.”

   “Nazeefah-“

  “Kuma ka tattara kayakin fad’an kishiyanka or whatever you call it bana buk’ata” tana kaiwa nan ta nufi d’akinta ko amsa kiran da yakeyi mata batayi ba. Hijabinta ta sanya ta d’au makullin motarta yana ganinta yasan fita zatayi be hanata ba saboda yasan ba amfani ko da yayi maganan ma ba sauraronsa zatayi ba. Kad’an ya rage bata take k’afan D’anladi ba da ta zo fita daga gate d’in, gida ta wuce direct se d’akin Mummy.

  Khalifah ta tarar mik’e kan gado se faman latsa wayansa yake. 

  “Ya Nazeefah” ya kirata had’e da mik’ewa zaune. 

  “Ina Mummy?”

  “Tana wanka” ya amsa take. 

  “Jeka d’auko mun ruwa” tayi maganan tana cire hijabinta. 

  “Ni shikenan kinzo ki fara aikan mutum ba” ya watsa mata harara. 

  “Nace kaje ka d’auko mun ruwa wallahi kar ka bari in sauk’e haushin da nakeji akanka.”

  “Ki sauk’en mana a jinki zaki iya duka na ne?” yayi maganan had’e da mik’ewa, daga bakin k’ofa ya wulla mata gorar ruwan da ya d’auko matan sannan ya haura sama d’akinsa. Kad’an tasha ta rufe ta ajiye, bada dad’ewa ba sega Mummy ta fito. 

  “Ha’ah Nazeefah ce a gidan namu yau.”

  “Mummy” ta kirata tana turo baki tamkar wacce zatayi kuka. 

  “Meya faru?”

  “Mummy kina jin Ya Afzal wai aure ze k’ara.”

  “Dama bakida labari ne?” Mummy ta tambaya tana mey zama a gefenta. 

  “Aww kina sane dama?”

  “Eh though nima ban dad’e da sani ba be sanar dake bane ke?”

  “Wallahi se yau yake fad’amun.”

  “Ai na d’au kina da labari auran sauran sati biyu ne ko uku nema.”

  “Wallahi Mummy bazan yarda ba adalilin mey ze auro mun wata? Wai harda akwatin fad’an kishiyansa.”

  “Guda nawa?”

  “Ni nama irga ne amma yafi shida de naga kaman.”

  “Toh ai ki godewa Allah.”

  “In godewa Allah fa kika ce Mummy? Uwar mey zanyi da kayan fad’an kishiyan nasa? Tsirara nake yawo ne?”

  “Kiga Nazeefah kowa yasan kishiya da zafi amma idan Allah ya k’addaro maka toh fa dole ne ka hak’ura banda ke da abin ki an riga an sa rana, rana ya gabato ajinki akwai borin da zakiyi ne da ze hanasa yin auren?”

  “Wallahi auren nan bazata saku ba komin yaya ne se nasan yadda zanyi in hana aukuwan hakan.”

  “Uhn uhn fa Nazeefah kar ki bari kishi ya kaiki ga halaka ki kwantar da hankalinki don za ayi maka kishiya bawai hakan na nufin mijinka baya sonka bane, kefa da bakinki kikace yayi miki kayan fad’an kishiya ai yaci ace kin hak’ura Afzal na sonki ke kanki kin sani, a zamanin nan ba kowani na miji bane ze yiwa uwar gidansa akwati dan wai ze k’ara aure. Ga akwati ba d’ayaba ba biyu ba keda kanki kikace zasu fi shida.”

   “Son banza so a baki, wallahi baya sona da yana sona da baze ma fara tunanin yin wani auren ba mene bani yi masa da zece seya sake aure. Ke yau shekara nawa kuke tare da Daddy meyasa bece ze sake yin wani auren ba? Idan ba fitina ba mata nawa yaga Abbansa ke da daze kama yace shi se yayi mata biyu.”

  “Kowa da ra’ayinsa Nazeefah. Kisani Afzal daban yake da Abbansa ko ni dake nan ba d’aya muke dake ba. Shi kishiya kuma tana kan kowa wallahi ko ni nan ban isa in bugi k’irji ince Daddy’nku baze k’ara aure ba, a yau d’innan yaga dama ze k’ara auransa, hak’uri ya zama dole.”

  “Ni wallahi bazan yarda ba auren namu dududu shekara nawa ne befa kai uku ba, ya bari ma idan na gama haihuwa na mana amma ko k’wark’wata ban ajiye ba har ya fara tunanin yin wani auren, Allah bazata saku ba.” 

   “Ta ma riga ta saku ne fah Nazeefah don banga abinda ze hana aukuwan auran nan ba idan ba mutuwa ba. Dan Allah ki rufa min da Daddy’inku asiri ki d’au hakan a matsayin k’addarar ki, ni kaina zan saki a addu’a Allah ya sa hakan shi yafi alkhairi.”

  “Amma Mummy kin ban dariya har akwai alkhairi ne acikin kishiya?”

  “Toh kije Nazeefah kiyi duk abinda kika ga ya dace amma idan kika zo kika rasa auren naki daga k’arshe kar kiyi blaming d’ina nide na fad’a miki” bata sake cewa komai ba ta ja hijabinta ta fice. Gidan k’awarta Suwaiba ta nufa da ikon Allah kuma mijinta baya gida. Zama tayi ta irga mata halin da ake ciki, sosai Suwaiba ta ji mata takaici amma ta nuna mata lokaci ya riga ya k’ure ba yadda za’ayi a hana aukuwan auren. 

  “Taya zakice haka Suwy? Nida nake cewa zaki share mun hawaye idan nazo.”

  “Wallahi ba yadda za’ayi saidai idan malamai zaki fara bi.”

   “Malamai? Wasu irin malamai kenan?”

  “Malaman tsibu nake nufi.”

  “Subhanallahi Suwy! Kin san ko yin hakan shirka ne?”

  “Tabbas na sani amma kuma idan bada su ba mutum baze ta6a iya mallake mijinsa ba kinga Ibrahim (mijinta) idan nace masa zauna ya zauna se abinda nakeso yakeyi I can’t bear the risk of sharing my husband da kowata shegiya idan a shirye kike gobe goben nan ina iya kaiki gidan malami na ya share miki hawaye.”

  “A’a kam gaskiya zan zauna inyi tunani am sure akwai wata hanyan da zanbi in hana aukuwan auren nan ba tare da na fita daga musulinci ba.”

  “Toh sani de ya rage wa me shiga rijiya kije kiyi shawaran anytime your mind is made up, gidan malam kullum a bud’e yake yana maraba wa bak’i.”

  “Toh ni zan wuce.”

  “Bari in raka ki.”

  “A’a yi zamanki keda kikayi nauyi, Allah de raba lafiya.”

  “Ameen toh se anjima.” Maimakon ta zarce gida ta wuce gidan wata k’awarta Maimuna har bayan maghrib tak’i dawowa gida. Tun Afzal na trying numbanta har ya gaji ya dena don kashe wayan tayi gabad’aya don kar ya tak’ura mata. Se wajajen k’arfe tara ta dawo gida. Tana shiga sega Afzal zaune kan kujera kallonsa tayi sannan ta kawar da kai ji take kaman ta nad’a masa duka don takaici. Daga bisani ta shiga takawa bata kai ga shiga corridorn da ze kaita d’akinta ba ya kira sunanta. Banza da shi tayi se akaro na biyu sannan ta tsaya had’e da kewayowa. 

  “Ina kikaje?” Ya tambayeta. Shiru tamai ko ta kallesa ma bale wai tasan yanayi. 

  “Magana nake miki Nazeefah ina kikaje? I’ve been trying to reach you but am sure da gan-gan kika kashe wayan naki don kar in sameki, yeah?”

  “Gida naje, wayana kuma ya mutu ne ba charji” ta amsa sama-sama. 

  “Don’t think of lying to me, na kira Mummy tace tun La’asr kika bar gida so where did you go?”

  “Gidan k’awata excuse me” bata kai ga juyawa ba ya dakatar da ita mik’ewa yayi ya tako zuwa inda take tsaye. “Da izinin wa kika fita sannan ya dace a matsayin ki na matar aure ki fita se cikin daren nan ki dawo?”

  “Kayi wa kanka fad’a kafin kayi mun Malam, ya dace a matsayin ka na magidanci amma kana neme neman mata? Bayan nan se three weeks to d’aurin aurenka zaka sanar da ni a matsayina na matarka?” Sosai ransa ke 6aci duk lokacinda ta kwatantasa da mey neme nemen mata sanin ba halinsa bane amma ya ya iya? Dan dole ya danne zuciyansa, yasani duk acikin zafin kishin ne don haka yayi mata uzuri. 

  “Look Nazeefah” yayi maganan had’e da aza hannunsa a kafad’unta “I know this’s not going to be easy on you, I know how it must hurt, ina sane da komai shiyasa nake rok’anki da kiyi hak’uri dan zan k’ara aure bawai hakan na nufin mabud’in wahala maki bane kokuwa wai zan mance dake ko in walak’anta ki. Nazeefah I love you, I’m proud to have as my Rabba’atul bait, Amal might be my bride but kece uwar gida na, which applies being my soul. Please karki bari kishi ya rufe miki ido yayi destroying relationship namu, I love you Nazeefah and I don’t wanna lose you.”

   “Duk k’arya ne” ta fad’a had’e da sauk’e hannayensa daga jikinta “wallahi duk k’aryar banza ce inda kana so na da bazaka ta6a tunanin k’ara aure ba.”

  “Nazeefah dan zan k’ara aure ba wai hakan na nufin na daina sonki bane, zan k’ara aure saboda sunna ne, ki d’au Amal a matsayin ‘yar uwarki ba kishiya ba.”

  “‘Yar uwa fa kace? Kar ka sake kwatantata da ‘yar uwata dan duk mutumin dake shirin sace maka miji ba d’an uwanka bane, Amal mak’iyata ce bana k’aunarta, bazan ta6a sonta ba kuma muddin ka auro ta a gidan nan toh wallahi kaida kwanciyan hankali kunyi sallama sena tabbata na tada maka hankali fiye da yadda ka tadamun nawa yanzu mu zuba da kai a gidan nan muga” tana kaiwa nan ta wucesa ta shige d’akinta had’e da sa key. Ruwa ta watsa ta sauk’e sallan Isha sannan ta fito in search of what to eat. Afzal ta tarar zaune kan dining yana shan corn flakes ko ta kansa batayi ba ta zarce kitchen ta shiga dafa indomie. Bayan da ya gama sha ya shiga yayi joining nata a kitchen d’in. 

  “Ni baza a dafa dani ba?” Ko juyawa ta kallesa batayi ba wai gani yake kaman wasa take ko? Ze gani. 

  “But I’m hungry.”

  “Kula da yunwan ka ya tashi daga kaina ya koma kan na amaryar ka. Idan har bazaka iya jure yunwan ba your bride is just a call away kana iya fita kaje ka sameta daman ka saba” ta basa amsa ba tare da ta koda juya ta kallesa ba. Be sake cewa komai ba ya jira ta, bayan data gama girkin yabita har cikin d’akinta. Duk yadda takeson ce masa ya fita haka ta hak’ura, tasan da gan-gan yake hakan don ya sata yin surutu. Bayan da ta gama ci ta sinche bathrobe dake jikintan ta sanya kayan baccinta ta feffeshe jikinta da turare sannan ta kewayo garesa “Malam kana iya bar min d’akin zan kwanta.”

  “Yau kuma nine Malam? Ba Ya Rouhi?” Shin wai ya d’au wasa take? Ze sha mamaki na lahira seya fisa jin dad’i. 

  “Ka de jini ka fice mun a d’aki.”

  “Naji anan zamu kwana yau?”

  “Malam am damn serious ka fice mun daga d’aki zan kwanta.”

  “In kinga nabar d’akin nan to dake ne in fact hak’k’i na ma nakeso, I need my wife.”

  “Idan a garinku ana kusantar matar da take haila toh bismillah” ta sanar dashi cike da rashin kunya. Duk yadda yaso 6oye dariyansa ya kasa “Baby kin manta yanzu kika idar da sallah ne?” Yayi maganan yana nuni da sallayar da tayi sallan akai. K’aramar tsuka taja “seka cinye d’akin idan ya zama abinci” sannan ta janye pillonta ta fice. Bayanta yabi izuwa d’ayan d’akin data shiga, haka suka tayi k’arshe tazo ta kwanta a parlour akan d’aya daga cikin couches d’in. Sarai yasan kujeran ba iya d’aukansu zeyi duka ba amman ya bita har kai dan neman magana, kusan rabin jikinsa akan nata yake. 

  “Wai don Allah meye haka?” Bata kaiga mik’ewa ba ya jata nan ya samu ya baje akan kujerar had’e da aza ta akan k’irjinsa. Gagam ya matseta yadda ko k’wak’k’war motsi bazata iya ba. 

  “Malam ka sakeni!”

  “Shhh let’s sleep baby.”

  “Ka sakeni ko sena shak’e tukun?” Adjusting nata yayi yadda zata na iya nishi da kyau amman bawai ya saketa ba. Duk kalan suratan da tayi-tayi hakan besa ya saketa ba, dan kanta ta daina surutun sabida yadda ta galabaita. Acikin awa d’aya bacci mey nauyi yayi awon gaba da ita, seda Afzal ya tabbata baccin nata yayi nauyi sannan a hankali ya sauk’eta daga jikinsa. D’agata yayi cike da dabara ya kaita d’akinsa ya shinfid’a ta akan gadon had’e da gyara mata kwanciya. Bayi ya fad’a ya watsa ruwa sharp-sharp sannan ya fito ya kwanta a gefenta had’e da kashe musu wuta. Pillonsa ya kawo kusa da nata sannan ya zagaye hannunsa a jikinta wane wanda wani ke shirin k’wace masa ita, a hankali bacci ya d’aukesa. 

Leave a Reply

Back to top button