Hot romantic hausa novel complete

Rayuwar Madina Hausa Novel Complete

Rayuwar Madina Hausa Novel Complete
 
 
 
 
 
 
 
 
RAYUWAR MADINA*
 
 
 
 
 
*CONTINUE… STORY OF MEEMA FARUKH*
 
 
 
 
 

*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._

______________ *EPISODE 1*
_____ *ZARIA CITY*
Ƙaramar ƙauye mae cike da albarkatu kala-kala, yanki ne da ake shuke-shuken kayan gona waɗanda ake samun iri masu ban sha’awa da burgewa, wanda hakan ne ya zamewa ƙauyen abun dogaro kuma sana’a a gare su, da noma suke ci suke sha kuma suke siyarwa a garuruwa mabambanta saboda Allah ya basu wadataccen fili mae kyau; ga kuma ƙorama da ke fitar da ruwa sosai, da lokacin damina da lokacin rani gaba ɗaya idan suka yi shuka suna ganin albarkan abun sosai. Sai dai kuma wannan ƙauye tana ɗaya daga cikin ƙauyukan da har yanzu basu waye ba a cikin al’umma, al’adun su sun sha bamban da sauran na mutane, har yanzu kansu a duhu yake wanda su sun ɗauki wasu al’adu tamkar addini a wajen su, karatun Boko ma har yanzu basu wani yarda dashi ba, iyakan su karatun Arabia da suke yi a zaure, da zaran kuma kayi sauka shikenan sai kuma ka ci gaba da sana’a ko kuma a aurar da kai, shiyasa su a tsarin su Mace tana kai wa shekaru 13 suke kaita ɗakin Mijin ta
 
A cikin ƙauyen akwai wani babban gida wanda a gaba ɗaya cikin ƙauyen shi ne Babba domin babu kamar shi, gida ne babba da sassa kusan goma sha biyar a ciki, kuma duk wannan gidan ahali ɗaya ne domin Mutum ɗaya ya haifi yaran gidan, waɗanda su kuma sun yi aure a cikin gidan sannan suka hayayyafa. Sai dai a yanzu Allah ya yi wa Malam Umaru rasuwa wanda ya kasance shi ne Kakanmu kuma mai Ahalin nan gaba ɗaya, tare da Matarsa guda ɗaya mai suna Faɗime da ta haifa mishi Yaransu goma sha uku cif, kuma gaba ɗaya babu wanda ya rasu face Mutum ɗaya, wanda shi ne ɗa na uku a cikin yaran gidan, Malam Sule. Ya rasu tun da ƙuruciyarsa, ya bar yara guda biyu dukka Mata, yayinda Matarsa ta fita tayi aure a cikin Zaria
 
Yanzu haka Babban ɗan Malam Umaru shi ke jagorantar gaba ɗaya Ahalin nan, Malam Abubakar. Muna kiran shi Baban Sasa; wanda shi ne Babba sannan kuma ya fi kowa iyalai a gidan. Matansa su huɗu ne ko wacce da nata zugan Yaran, wasu sun yi aure wasu kuma suna nan sun fantsama ƙauyaku suna sana’a
 
Sai kuma mai bin masa Malam Ali; da muke kiran shi da Baffa, shi kuma Matan shi biyu ne da nashi zugan Yaran shima, domin shima Allah ya albarkace shi da yara da yawa
 
Sai Malam Sule wanda ya rasu da jimawa, kamar yanda na faɗa muku Yaran sa biyu ne tal a duniya, kuma shi ne Mahaifina
 
Sai sauran waɗanda yawancin su Mata ne suna aure a sauran yankuna na ƙauyakun, wasu kuma sun samu ci gaba suna aure a cikin birnin Zarian. A taƙaice dai Iyayenmu Maza a gidan su takwas ne, sai Mata su biyar kuma kowanne Allah ya albarkace su da Yara da dama. Duk da akwai wayewa yanzu sosai a cikin rayuwarmu amma har yanzu muna da al’adun da muka kasa barin shi, duk wani ci gaba bamu yarda mu watsar da al’adun nan ba sabida muna ganin shi ne tushenmu tun iyaye da kakanni, idan za’a yi wa yarinya aure Iyayenmu da kansu suke zaɓa mana Mijin aure, sannan kuma dole ne ko wacce Mace sai an yi mata kaciya. Eh kaciya, su Iyayenmu sun mayar da al’adunmu ba namiji kaɗai ake yi wa kaciya ba har da Mata, kuma har yanzu suna nan a kan bakansu sun ƙi dena wannan al’adan sabida sun ɗauke shi da matuƙar muhimmanci. Suna ganin ta wannan hanyar ce zasu natsar da ƴaƴansu Mata wajen kamewa da riƙe budurcin su har sai sun yi aure, kuma suna ganin hakan na ƙara wa Mijin jin daɗin Matarsa wajen kwanciyar Aure; ko kuma taimakawa wajen samun ciki da sauƙi. Wannan al’ada an laƙanta shi da auren wuri kuma duk mutanen da ke cikin wannan ƙauyen zaka tarar Mace ba’a ɗauke ta a bakin komai ba kuma bata da daraja ko kaɗan, suna yin wannan kaciyar ne da zaran Mace takai shekara goma sha ɗaya sannan sai ayi mata, bayan shekaru biyu kuma sai a aurar da ita, duk da a yanzu ya sha bamban da rayuwar baya, ada can ana yi wa yarinya kaciya ne da zaran takai shekaru biyar a duniya, amma yanzu kai ya waye an samu ci gaba dole sai yarinya takai shekaru 11 sannan za’a yi mata
 
Duk yadda Mutum ya so ya dubi al’ada; ba ta wani ɓangare da ya cancanta sam. Cin zarafi ne na ɗan Adam da bai cancanta sam ya zama yana wakana koda a kan kowa ba, domin wannan ɗabi’a na sanya wa Mata da aka yi musu kaciya; zasu kamu da matsaloli da suka shafi lafiyar Mace (mental and physical health challenges) a gaskiya ba Macen da ya kamata ayi mata kaciya. Haka wannan al’umma suke alaƙanta kaciyar Mata da addini, musamman addinin musulunci. Haka ma a wasu ƙasashe da dama suna amfani da addini domin yi wa Mata kaciya; kuma suna kafa hujjarsu mara tushe a kan wannan aika-aikan, duk da cewa basu da hujja kuma basu da takamaiman inda zasu kama a cikin Al’ƙur’ani ko hadisan Manzon Allah. Wannan na faruwa ne saboda rashin cikakken ilimin addini da kuma mabiya da basu san alƙiblan su ba, wanda ya kasance abun da suke aikata wa Mace daban da abun da yakamata su cire mata, sam kaciya bata dace da Mace ba, hanyar da suka dauko ba shine wanda ya dace ba, a ganin su daidai ne. A dalilin haka wannan al’ada ta samu shiga sosai a wannan ƙauyen, kuma babu wanda ya isa ya tsallake wa hakan.
 
 
 
 
 
 
 
⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐⭐
 
_____Kamar yanda kowacce shekara ake samun waɗanda ake musu wannan kaciyar, hakan ta kasance a cikin wannan ƙauyen. Mata da yawa waɗanda aka shirya domin aiwatar musu da wannan al’adan a gobe juma’a
 
Inda a babban gida kamar yanda muke kiran sunan gidan mu, Mata shida su ne waɗanda za’a yi wa kaciyar suma, shiyasa kowacce Uwa take tausayin ɗiyarta sabida abun da zai faru gobe, suna ganin daga yau kuma ɗiyar su ta zama babbar Mace, ta tashi a ƙaramar yarinya, da zaran an yi kuma sai maganar aure da zai fara tashi, inda za’a zaɓawa kowacce Mace Mijin da zata aura, wannan dalilin ne yasa Idan ka shiga babban gida zaka ga kowa jigum haka suke zaune duk babu karsashi a jikin su, musamman ma Yaran da su za’a yi wa kaciyar kana kallon fuskokin su zaka ga rashin walwala a tattare da su, ko kaɗan ba sa ƙaunar gobe tayi sabida azaban da zasu sha.
ƴan uwanmu suna bamu labarin wahalar da ake sha, mu ma kanmu muna gani, amma kuma wacce ta tsallake shikenan, bamu da yadda zamu yi dole ne mu fuskanci wannan ranan kamar yanda ƴan uwan mu suka fuskanta a rayuwar su.
 
Da yammacin ranan ne Baban Sasa ya yiwa ƴan uwan shi kira suka zauna suna tattaunawa a kan gudanar da al’adar tasu a gobe, wanda a cikin jawabin Baban Sasan ne yake cewa, “tunda yanzu Madina ta kawo girma itama, babu wani sa’ar ta a cikin gidan nan sauran duk yara ne, to, sai a haɗa ta da sauran Yayyinta da za’a yi musu kaciya gobe itama ayi mata, ai ina ga babu matsala tunda da shekara ɗaya suka girme ta, kunga mun huta ma.”
 
Jin zancen Baban Sasa babu wanda ya musa, kowa ya ga dacewar hakan, sai kaɗa kai suke yi suna cewa, “ƙwarai kuwa hakan ya kamata, ai itama tana da girman jiki ta kamo su a girma, babu wanda zai ce sun girme ta, za’a haɗa su kawai ayi musu.”
 
Ana haka sai gani na shigo cikin falon riƙe da kwanon sha da aka aiko Ni in kawo musu farau-farau. A hankali na ajiye kwanon shan tare da durƙushewa na soma gaishe su cikin girmamawa irin nawa, sannan na isar da saƙon kamar yanda Matar Baban Sasa ta aiko Ni, Matarsa ta farko wacce muke kira da Inna Lami
 
“Yauwa Madina, ajiye.” Cewar Baffa da yayi maganar yana kallo na, domin a cikin su duk shi ne wanda yake da sakin fuska da wasa da Yara sosai
 
Har na miƙe Baban Sasa ya tsayar da Ni yana cewa, “zauna Madina akwai maganar da zamu yi da ke.”
 
Hakan yasa na samu wuri na zauna a saman ƙafafu na yayinda kaina ke ƙasa na kasa ɗagowa. Baban Sasa ya soma sanar min da hukuncin da suka yanke a kaina wanda lokaci ɗaya na ɗago kai ina kallon su ɗaya bayan ɗaya, duk da ba wani wayau ne da Ni ba domin a lokacin shekaruna goma ne cif; amma kuma ina sane da wannan Shegiyar al’adan tamu wacce ina ɗaya daga cikin waɗanda suke matuƙar tsoron zuwan wannan rana a gare mu, musamman yanda naga Yayata ta sha wahala a lokacin da aka yi mata, tayi ciwo sosai kuma ta sanar min akwai wahala sosai, daga ƙarshe dai Allah ya bata lafiya har aka yi auren ta, yanzu shekara ɗaya kenan kuma har da ƴarta guda ɗaya da ta haifa ko kwana hamsin ba’a yi ba. Jin cewa da Ni za’a yi kaciyar gobe zuciyata tuni ta cika da tsoro wanda ya kasa ɓoyuwa a kan kyakkyawar farar fuskata da take ɗan tsut da ita, kullum a rame kamar ba na cin abinci, to kusan haka ne tunda dama rayuwar gidan yana matuƙar min wahala kasancewata marainiya babu Mahaifina, sannan kuma mahaifiyata ta fita tayi aure a can cikin Zaria anguwan ƙaya, shiyasa muke matukar shan wahala Ni da Yayata Haula, sai dai kuma yanzu ita tayi aure ta huta ba kamar Ni ba, kullum kamar Ni ce jakar gida ko wacce Mace Ni take sakawa aiki, babu damar aga wulƙawa ta sai ɗaya daga cikin matan gidan sun kira Ni sun saka Ni aiki, da su saka yaran su sun gummaci su sanya Ni, shiyasa a kodayaushe bani da lokacin kaina kullum cikin bautar Matan gidan nake yi, kuma dole inyi tunda bani da ƙyuya ko kaɗan, idan ma ban yi ba abincin da ake bani sai dai in rasa domin babu wacce zata bani ban yi mata aiki ba, shiyasa na zama tamkar Almajira a gidan kamar ba ƴar gidan ba, idan aka yi min wani abu sabo sai dai idan Baffa ne, ko kuma Baban Sasa wanda yake haɗa kowa na gidan da sallah yayi musu sabon kaya, to idan ba sallah ba Ni ba na samun me min komai koda biki ake yi a gidan namu, babu me min anko ko ya siyan min sabbin kaya, sauran yaran kuwa iyayen su mata suke siyan musu duk abin da suke so tunda duk suna sana’a suna samu, kasancewar rayuwar gidan mu yawanci matan su suke yiwa kansu hidima na yau da kullum, iyayen mu maza basu saba ba kuma baza su taɓa yi ba sai idan sun ga dama, yana ɗaya daga cikin uƙuban rayuwar da Matan cikin ƙauyen namu suke sha, har yanzu kai ya ƙi wayewa. A gaskiya na shiga tashin hankali jin cewa har da Ni za’a yiwa kaciya, na ruɗe sosai sai dai na kasa yin magana sabida kasancewar Baban Sasa ne mai maganar, domin shi ba ya ɗaukar raini kuma ba ya so yana magana ana katse shi, yana da son girma sosai duk abin da ya gindaya to babu me iya tsallakewa. Hakan yasa ya bani umarnin, “in je gidan Yayata in kira ta.” Babu musu na miƙe na fita jikina na rawa kamar mazari, har ina jin tamkar ƙafafuwana baza su iya ɗauka ta ba, duk yanda na so na daure kar na fitar da halin da nake ciki amma hakan ya faskara, tuni hawaye sun soma sauka a kan dandamalin fuskata sai shatata suke yi kamar an kunna famfo, dole na miƙa hanya na fice daga gidan namu na doshi gidan Yayata da babu nisa sosai, tunda naga na fita cikin jama’a sai na soma kuka wi-wi kamar ana yankan naman jiki na, har ba na iya ganin gabana a yanda nake tafiya a haka nakai ƙofar gidan da Yayata take Aure. Gidan ba wani babban gida bane kuma su uku suke zaune, daga surukar su sai Wan Mijin Yayata; da Matarsa shima da yara biyu. Ina shiga babu kowa a tsakar gidan sai na nufi kaina tsaye ɗakin Yayata, ina shiga ɗakin kuka na ya janyo hankalin ta da har barci ya soma fizgar ta, tana rungume da jaririyar ƴarta me sunan Umman mu, Asiya, mu kuma muna kiranta da Ihsan
 
Yayata hankalin ta ya tashi ganin yanda na shigo mata ina kuka, shiyasa nan da nan ta ruɗe ta soma tambaya na, “Madina lafiya mene ne? Me aka yi miki? Faɗa min inji?” Dukka ta rungumo Ni jikinta tana kallon fuskata; yayinda ita nata fuskar cike da damuwa tsantsa
 
Ni kuma kukan nake yi na kasa denawa. Dole ta zauna bani haƙuri har nayi shiru sannan ta sake tambayata? A nan na bata labarin komai har da kiran da Baban Sasa yake mata
 
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un…” Salati kawai take rafkawa lokaci ɗaya ta sake rikicewa wanda har hawaye ne suka soma sintiri a kan fuskarta me kama da nawa sak, cikin tsantsan tashin hankali tace, “yanzu kina nufin da ke za’a yi wa kaciya a gobe?”
 
Shashsheƙa na soma yi ina gyaɗa mata kai a hankali, yayinda wani kukan ya sake taho min sai na faɗa jikinta ina cewa, “shikenan Yaya Haula nima zan fuskanci wannan uƙuban rayuwar da ku ka sha? Ni yanzu ya zan yi wlh bazan iya jurewa ba, idan aka yi min mutuwa zan yi, don Allah ki kai Ni wajen Ummana ba na so ayi min, ki ce musu ba na so.”
 
Haula ta kasa magana illa sake rungume Ni da tayi tana kukan itama sosai cike da tausayina, ta san kuma aikin gama ya rigada ya gama dama wannan ranan take gudun zuwan ta, tana tausayin ƙanwarta musamman kasancewar ta me rauni sosai, tana gudun zuwan wannan ranan ga ƙanwarta, amma babu yanda zasu yi dole ne itama sai an yi mata. Ta kasa rarrashina yayinda Ni kuma nake ta sambatu ina kuka ina faɗa mata, “Ni ba na so.” Riƙo kaina tayi tana ɗago Ni tare da kallon fuskata da nake ta shatatar ruwan hawaye, haka itama nata tuni idanuwanta sun yi jawur tace, “haka nan za ki yi hakuri Madina babu yacce zamu yi, wannan al’adan dole ne ayi, dama tunda kika kawo girma dole za ki fuskanci wannan rayuwar, ko ba’a yi miki yanzu ba a nan gaba za’a yi miki, domin baza a taɓa aurar da ke ba sai an cika wannan al’adan, kiyi haƙuri kinji babu yadda zamu yi. Tashi mu je kar su ji Ni shiru ya zame min laifi.” Ta ƙare maganar tana cire hannunta daga kaina, yayinda ta bi Ni da kallo ganin yanda na ci gaba da kukan ban fasa ba, “kiyi haƙuri Madina kiyi shiru, kukan nan be da amfani kar ki sakawa kan ki wani ciwon, ki share hawayen ki mu tafi, bari in goya Ihsan.” Sai ta tashi ta saɓa Ihsan ɗin da ke faman sharan barcin ta hankali kwance, sai da ta gama goya ta sannan ta yafa mayafi ta kalle Ni tace, “mu je, ki dena kukan nan nace kar mu je a ganki a haka.”
 
Kai kawai na gyaɗa mata ba don zan dena ba, domin kukan ma na kasa tsayar dashi sai shashsheƙa nake yi yayinda wasu sabbin hawayen suke ta kwaranya a kan fuskata, sai saka hannu nake yi ina sharewa amma hakan babu amfani. Hannuna ta riƙe muka fita a gidan tunda babu kowa bare tace musu, “zata je ta dawo.”
 
Muna shiga zauren gidan mu; ta sake share min fuska domin kar a gane nayi kuka, amma kuma duk da haka ana kallo na za’a san kuka nayi, yanda idanuwana nan da nan suka tashi suka yi girma sosai suka yi ja, dama ga su manya ne sai suka sake luhu-luhu, sai jan majina nake yi ina shashsheƙa. Kai tsaye falon Baban Sasa muka wuce ba tare da mun shiga cikin gidan ba, tunda sashin shi daban ne ba sai ka shiga ainihin sasukan gidan ba, sai dai idan ka haɗu da mutane a hanya amma babu me ganin ka, tunda gidan yawa ne baza ka rasa yara suna wasa ba. A bakin ƙofan Yaya Haula tayi sallama ta shiga riƙe da hannuna, hakan yasa na sauke kai ƙasa kar ma su gane a halin da nake ciki, har yanzu jan ajiyan zuciya nake yi na kasa denawa. Zama muka yi a wuri ɗaya inda ita Yaya Haulan ta soma gaishe su cikin girmamawa
 
Suka amsa ta cike da kulawa wanda har Baffa yake cewa, “Ina Ihsan ɗin; ba dai tayi barci ba?”
 
“Eh Baffa tayi barci.”
 
“Ayya uwar son jiki; ai na kula yarinyar irin Uwarta Madina ce, Allah ya raya ta.” Yafaɗa cikin murmushi da wasa a fuskarsa
 
Tsirarun mutanen wurin suka amsa da Amin har da Yaya Haula, kana ta ƙara da faɗin, “Baba gani an ce kuna kira na.”
 
“Eh Haulatu. Maganar ƴar uwanki ne da muka yanke hukunci a kanta, gobe da ita za’a yi wa Yaran gidan nan kaciya sabida a huta, to ke ƴar uwanta ne shiyasa muka kira ki mu sanar miki, sannan ki buga waya ki sanar da matafiyarku halin da ake ciki.”
 
Cike da sanyin murya Haula tace, “to Baba.” Batare da ta sake furta komai ba bare tayi gardama
 
Sai ya bata umarnin tafiya, shiyasa ta tashi zata fice. Nima hakan yasa na miƙe na bi bayan ta, yanda zuciyar Yaya Haula gaba ɗaya babu daɗi ta kasa rarrashina saboda tunda muka fito na fashe mata da kuka, dole ta ja hannuna muka wuce gidan ta, ta zaunar dani tana ta faman rarrashina, ita kanta karfin hali ne irin nata amma ba wai farin ciki take yi ba, bata san ma ta hanyar da zata sanar da mahaifiyarmu ba sabida a yanzu bata da waya ta lalace, shiyasa ta yanke shawaran goben nan zata nufi can anguwan ƙaya ta sanar mata, ko hakan zai taimaka ita Umman tamu ta zo ta basu haƙuri a ƙyale Ni zuwa nan gaba, tabbas da cutuwa ace kamata za’a yiwa kaciya, su kansu da aka yi musu da shekarun su ya fi nawa sun sha baƙar wahala bare Ni, shiyasa take matuƙar tausayi na. Ni kuma duk rarrashin da tayi min na ƙi yin shiru, Ni gani nake yi kamar idan aka yi min shikenan mutuwa zan yi, rayuwata ta gama yawo, bazan sake ganin Ummata ba, itama Yayata zan rabu da ita
 
Ana haka sai ga surukarta ta shigo gidan, jin kukana shi ne ta shigo ɗakin tana tambayar ba’asi?
 
A nan Yayata ta sanar mata komai abun da ke faruwa
 
Sai tace, “oh! ke kuma Madina mene ne na tayar da hankali bayan kin san kowacce Mace da haka ta saba? Haka nan za ki yi haƙuri idan an yi miki yanzu ai kin huta, Haula sai ki rarrashe ta tunda ita yarinya ce dole sai ana tausan ta, Allah yasa ayi a Sa’a.”
 
“Amin Mama.” A cewar Haulan
 
Inda ita kuma Maman ta fice tana sake tausa na
 
Ni kuwa ina jikin Yaya Haula ina ta ƙananun kukana na kasa yin shiru, ƙarshe har aka kira sallan magriba kafin na tafi gida, shima sai da ta bani abinci na ci daƙyar domin na kasa cin komai, haka ta lallaɓa Ni sannan ta tura Ni gida
 
A lokacin da na isa gida har maganar ta zagaya ko ina, cewa dani za’a yi kaciyar gobe, masu tausayi na nayi waɗanda kuma basu damu ba takan ƴaƴan su suke yi, babu ruwan su da Ni tunda su ma abun ya shafi ƴaƴan su. Haka na wuce ɗakin mu da muke kwana dukka ƴan matan gidan sa’anni na duk da ni ce ƙaramar su, babu mai walwala a cikin mu gaba ɗaya, dama Ni ce to yanzu an ce har da Ni za’a yi, shiyasa nima na bi ayarin su. Tunda nayi sallah na haɗa da magriba da isha’i na kwanta a tsumman katifana na kasa tashi bare in fita, ina jin hayaniyar ƴan gidan amma na kasa fita bare ayi dani, yawanci su ma sauran suna zaune a ɗakin, wasu kuma sun wuce ɗakin iyayen su suna can ana rarrashin su, Ni kuwa ba mai rarrashina, ina jin sanda samarin gidan suka dawo suma ake basu labarin ai har da Ni za’a yiwa kaciya, wasu sun tausaya min a ciki, wasu kuma suna cewa, “haba har dani memakon a bari sai wata shekaran? Ai nayi ƙanƙanta tunda su Fa’iza sun girme Ni.” Yawanci maganganun da suke tayi kenan, Ni kuma jin hakan ke ƙara raunata min zuciya, sai kawai hawaye suyi ta zuba min ina danne baki kar kukana ya fita; ya zame min wani bala’in. wayyo Allah! ya zan yi da rayuwata? Shikenan gobe zan fuskanci wata rayuwa? A haƙiƙanin gaskiya ba na ƙaunar wannan kaciyar, ina matuƙar tsoro amma babu yadda zan yi, bazan iya tsira ba. A haka na kwana a cikin zullumi, ko in ce muka kwana dukkan mu, barci na ragagge ne a wannan ranan da nayi; cike da tsoro da zullumin zuwan goben.
 
 
 
_Labarin zai zo muku a duk sati sau uku a rana ne, every Juma’a; Saturday and Sunday, please babu ƙorafin hakan don Allah. Waɗanda suke son magana dani kai tsaye a WhatsApp zasu same Ni a kan wannan numban 07065334256. Nagode Masoyana._
(10/06, 2:51 pm) +234 706 533 4256: 💎💎💎💎💎💎💎💎
*RAYUWAR MADINA* 💧
💎💎💎💎💎💎💎💎
 
_Writing Story:_
*NAFISAT ISMA’IL*
_(UMMUDAHIRA)_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
 
 
 
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* 🌞
 
“`( WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)“`
 
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
 
*P.W.A✍️*
 
 
 
 
 
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga ƴan uwana Mata waɗanda suka fuskanci uƙuban rayuwa a zamantakewar su na Aure, Allah yasa mu dace ya kawo mana ƙarshen wahalar rayuwa._
 
 
 
 
 
 
 
 
 
 
______________ *EPISODE 2*
_____Washe gari Yaya Haula ta sanar da Mijinta saƙon Baban Sasa, ta CE mishi, “zata je ta sanar da Umman su.” Shiyasa ya barta ta tafi kusan ƙarfe goma na safe, tafiyar awa ɗaya da rabi ne ya kaita cikin Zaria anguwan da Umman su take Aure
 
Dayake yau Asabar ne tana gida ita da yaranta, Mijinta ne kawai ya fita ƙwadugon sa da ya saba, ba wani me shi bane tunda kullum sai ya fita sannan zai samu wanda zasu ci a rana, shiyasa Umman namu take aikatau a wani gida da ke kusa da su, Matar tsohuwa ce sai jikokin ta da take zaune da su, shiyasa aka sama mata me aiki tana rage mata wasu abubuwa, to a nan ne su Umman mu suke samun na rufawa kansu asiri, ga Yaranta Hassana da Hussaina da ta haifa sun girma sosai, domin yanzu shekarun su kusan bakwai ne, tunda tun sanda Baban mu ya rasu ta koma ƙauyen su, sai tayi aure babu jimawa, to daga kan su Hassanan ne bata sake haihuwa ba duk da tayi ɓarin wasu ƴan biyun
 
Umman mu tayi mamakin ganin Yaya Haula da safen nan, shiyasa ko zama bata yi ba ta soma tambayar ta hankalin ta duk a tashe saboda gani take yi kamar babu lafiya, musamman yadda ta ga fuskar Yaya Haulan ta koma
 
Yaya Haula bata ce komai ba sai da ta zauna sannan ta gaishe ta, ƴan biyu ma suka gaishe ta; ta amsa su tana musu murmushi
 
Sai Umma ta cewa Hassana, “ta tashi ta ɗauko mata kofi ta zuba wa Yayar su koko.”
 
Hakan yasa Hassanan ta miƙe ta je ta ɗauko ta kawo
 
Umma ta amsa ta zuba mata, ta tura mata da raguwar ƙosan da ke gabanta tace, “ga shi ki ci, sauko min takwaran tawa.”
 
Babu musu ta kwanto goyon Ihsan ta miƙa mata, yarinyar sai Barci take yi tunda bata da aiki sai barci
 
Umma bayan ta amshe ta ta ɗaurata a jikinta tana kallon fuskarta, tare da kai hannu tana cire mata kwantsan da ke idanunta ɗaya; kana ta kalli Yaya Haula tana cewa, “kina mata amfani da maganin dana ba ki?”
 
“Eh Umma har ma ya ƙare, jikin nata da sauƙi yanzu ai.” Ta bata amsa tana tura ƙosan a bakinta tare da korawa da kokon; tunda dama ba kari mai kyau tayi ba, Mijinta shima be dashi sai ya fita yake nemo wa, kullum a cikin ɗame-ɗame suke ga shi ita tana shayarwa, shiyasa yanzu ɗin ta shanye kokan tass tana siɗe baki
 
Sannan Umma ta kalle ta tana cewa, “ina jinki meke faruwa ne? Hankalina ya kasa kwanciya duk yanda aka yi ba lafiya ba?”
 
Ajiyan zuciya Yaya Haulan ta saki, kana damuwarta ta dawo sabo, a nan ta sanar da Umman duk abun da ke faruwa
 
Shiru Umma tayi sabida yanda maganar ta bige ta ainun; yayinda idan hankalin ta yayi dubu to ya tashi a wannan lokacin
 
“Ni Umma ba wai yin kaciyar bane yake damu na, Madina yarinya ce duk su Binta sun girme ta, ita ce ƙarama memakon su barta sai wata shekaran amma sun CE da ita za’a yi, Umma ki duba yanda na sha wahala a lokacin da aka yi min; idan har aka yiwa Madina yanzu bamu san wani hali zata shiga ba, don Allah Umma ki je ki roƙe su a dakata ko zuwa nan gaba sai ayi mata, Madina yarinya ce.”
 
Umma tace, “to Haula ya zan yi wannan abun ya fi ƙarfi na, amma ban ji daɗi ba; ba ki ji yadda zuciyata take zafi ba hankalina duk ya tashi, wannan al’adan kwata-kwata be da tsari, da ace ina da fawan da zan ɗauko ɗiyata ta dawo hannu na da na jima da yi tunda na san dole zasu yi mata wannan kaciyar, sai dai na san baza su taɓa yarda ba, insha Allahu Allah bazai basu dama ba dole ne zan je in Yi musu magana tunda ina da haƙƙi a kanta.” Sai ta kalli su Hassana da ke zaune suna ta shan kokan su tace, “ku tashi idan kun gama ku je gidan Asabe ku zauna, idan lokacin Islamiyar ku tayi sai ku wuce; Ni zan tafi anguwa.”
 
“To Umma.” Suka amsa mata suna miƙewa tunda sun gama abun da suke yi
 
Ita kuma sai ta miƙa wa Haula Ihsan ɗin ta miƙe tana cewa, “bari ta ƙarisa aikin ta.” Da haka ta fice daga ɗakin
 
Itama Haulan miƙewa tayi ta shimfiɗa Ihsan ɗin sannan ta fita ta taya ta aikin, dama shara ne kawai da wanke-wanke, suna gamawa Umman ta saka kaya da hijabi suka fito gidan, sai a waya ta sanar da Mijin nata, kuma bae hana ta ba sai fatan alkhairi da yayi mata. Kai tsaye gidan da take aiki suka nufa sabida tana son ta faɗa musu, “baza ta samu shigowa yau ba.” kar Matar ta ji ta shiru
 
Suna shiga kuwa suka cid da tsohuwar Matar a katafaren falon ta, duk da ta manyanta sosai amma kana kallon ta zaka san ƴar kwalliya ce, domin har yanzu gayu take yi babu ruwanta da tsufan da tayi, hannayen ta dukka sun sha jan lalli da aka yi mata hannu da ƙafa ya ɗauki farar fatanta sosai, sai sarƙa da awarwaro da ta zuba su na gwal sai walwali suke yi, duk da fuskarta babu kwalliya amma ta sha kwalli da Powder tayi kyau ainun, tana zaune a kan sofa tana kallon labarai a t.v, ta amsa musu sallaman cikin fara’an ta tana cewa, “yanzu nake tunanin lafiya ban ji ki ba? Shiyasa nake tunanin in aika a duba min ke.”
 
Murmushi Umma tayi tana zama a ƙasa tare da cewa, “wlh kuwa Hajiya, baƙuwa nayi ƴata ta zo daga ƙauye, shi ne zamu je can saboda wata matsala, abun da yasa ban zo ba kenan kuma kar in tafi ban sanar miki ba shi ne na shigo. Ina kwana Hajiyam?” Ta ƙare maganar tana gaishe ta
 
“Lafiya lau, wlh babu komai, nima fita zan yi ai.”
 
Haula wacce ta zuƙuna itama a ƙasa ta gaishe ta cikin girmamawa
 
Hajiya Ummee ta amsa mata cike da fara’a tana cewa, “yanzu Asiya wannan yarinyar ƴarki ce?”
 
“Eh wlh Hajiya, ita ce babban ƴata sai ƙanwarta.”
 
“Masha Allah sannun ki, ya sunan ki?” Hajiya Ummee ta tambaya cikin fara’a tana kallon Haulan
 
Itama Murmushi tayi cikin girmamawa tace, “suna na Haula.”
 
“Masha Allah! suna mai daɗi.” Sai kuma ta kalli Umman tana cewa, “yanzu ki je kichen ki haɗo muku Breakfast sai ku ci kafin ku tafi.”
 
“Wlh a’a Hajiya sauri muke yi, kuma mun ci abinci yanzu kafin mu fito.”
 
A lokacin ne Ihsan ta tashi ta soma kuka
 
Hakan yasa cike da mamaki Hajiyan tace, “wai da goyo ne a bayan ta dama?”
 
“Eh, ɗiyarta ce.” Umma ta bata amsa
 
“Ikon Allah! Ɗiyarta?” Inji Hajiyan tana sake cika da mamaki yayinda take kallon Haulan, “yanzu Asiya kina nufin yarinyar nan tana da aure ne?”
 
Murmushi Umma tayi tace, “eh Hajiya, ga ta nan har da ƴarta takwarata.”
 
Hajiya Ummee ta cika da al’ajabin da ya kasa ɓoyuwa a kan kyakykyawar fauskarta, sai ta cewa Haulan, “ta sauko yarinyar ta bata.” Hakan yasa ta sauko ta ta miƙa mata, sosai yarinyar ta bata sha’awa tana faɗin, “Masha Allah yarinya tubarakalla. Amma taya ya zaku yiwa yarinya kamar wannan aure Asiya? Wannan ai ganganci ne; kamar wannan fa?” Ta sake maganar tana nuna Haula da a yanzu ta koma ta zauna tana kallon Hajiyan cike da burgewa
 
Ita dai Umma murmushi kawai take yi bata ce komai ba
 
A lokacin ne wani kyakykyawar farin saurayi yayi sallama ya shigo cikin falon; yana riƙe da farar riga lab coat a hannun sa, yayinda idanuwansa suke sanye a cikin farin medical glass da ya haskaka mishi idanun suka ƙara yin kyau ainun, jikinsa sanye da ƙananan kaya riga da wando sun mishi kyau, kansa kuma babu hula sai kwantaccen gashin kansa me haɗe da yalwataccen sajen sa tare da ɗan guntun gemun sa, kana kallon sa zaka ga kamalan sa da kwarjinin sa a fuska
 
Duk amsa mishi sallaman suka yi, inda Hajiya Ummee take cewa, “Ah ah! Mashkur ka dawo ne kuma?”
 
Sai da ya samu wuri ya zauna kafin ya bata amsa yana cewa, “eh. Already na gama abun da na je yi.” Daga nan sai ya mayar da hankalinsa a kan Umma yana gaishe ta
 
Ta amsa a cikin sakin fuska tana tambayar shi aikin nashi?
 
Yace, “alhmadulillah.”
 
Itama Haula gaishe shi tayi
 
Sai ya ɗago yana kallonta, kana ya amsa ta a hankali yana ɗauke kai a kanta; ya mayar a kan yarinyar da ke hannun Hajiya Ummee, “yarinyar wace ce?” Ya tambaya yana ci gaba da tsira mata idanu
 
“Yarinyar Haula ce ɗiyar Asiya, ga ta nan zaune ai.”
 
Hakan ne yasa ya sake ɗaga kai yana kallon Haulan; yayinda mamaki kwance a kan kamilalliyar fuskarsa na jin cewa wannan figaggiyar yarinyar; tsamurarriya; ita ce Maman jaririyar nan, ikon Allah! domin abin mamaki ya ba shi, saboda gani yake yi ai baza ta wuce shekaru 14 ba amma har da ɗiya? sai dai bai ce komai ba saboda shi ba mai yawan magana bane
 
Inda ita Hajiyan tace, “Mashkur akwai kuɗi a hannun ka; ka bani zan ba wa Asiya ne?”
 
“Eh akwai.” Ya furta yana saka hannu cikin aljihun wandon sa tare da zaro kuɗin, bai ma san ko nawa bane ya miƙa mata
 
Itama sai ta amsa ta miƙawa Umma gaba ɗaya tana cewa, “to ga shi sai ku rage kuɗin mota, sauran sai ki ba wa Haula, Allah ya kiyaye hanya, nima fita zan yi kuma zamu kai yamma kafin mu dawo, sai Allah ya kaimu gobe sai ki zo; yau dai ki huta da aikin nan.”
 
Sosai Umma tayi godiya, daga ita har Haula, sannan Hajiyan ta miƙa mata Ihsan ɗin ta goya ta, daga nan suka yi musu sallama suka fice.
 
 
 
 
Kai tsaye keke napep suka yi drop ya nufi da su ƙauyen. Bayan sun kai suka wuce babban gidan su, koda suka shiga Yara suna hangen Umma suka soma mata Oyoyo suna cewa, “ga Umman su Madina, ga Umman su Madina.”
 
A lokacin ina cikin ɗakin mu naji abun da suke faɗa, ai da gudu na fito domin gasgata abun da suke faɗa, ilai kuwa Ummata ne tare da Yaya Haula da suka shigo sasan a yanzu, da gudu na nufe ta ina kiran sunan ta, na rungume ta cikin tsantsan murna da farin cikin ganin ta; domin ba ƙaramin murna ne ya kama Ni ba sabida rabo na da ita tun bikin Yaya Haula
 
Murmushi ita kuma take yi tana shafa min kai tare da cewa, “kar ki ka dani mana Madina.”
 
Ni kuwa sai dariya nake yi murna ta kasa ɓoyuwa a kan fuskata, nace, “Umma sannu da zuwa.”
 
“Yauwa Madina.” Umman ta amsa tana kuma mayar da hankalinta a kan Yaran da suke mata sannu, su ma tana amsa musu
 
A lokacin ne Inna Lami ta fito daga ɗaki tana ɗaura ɗankwali a kanta; tare da cewa, “wa nake ji kamar Asiya a gidan namu?”
 
“Ni ce wlh Yaya. Ina wuni?” Umma tafaɗa cikin yalwata fuskarta da fara’a sosai
 
“Lafiya lau, maraba da zuwa, ke Madina ɗauko mata tabarma mana kin barta a tsaye.”
 
Da gudu na shiga ɗakin Inna Lamin na ɗauko tabarma, ta amsa ta shimfiɗa mata sannan Umma ta zauna itama ta zauna, a lokacin sauran Matan Baban Sasa suka fito su ma suna cewa, “Ah ah Asiya ce a gidann namu?”
 
“Wlh Ni ce.”
 
Daga haka aka soma gaisawa cikin mutunta juna tunda an yi zaman lafiya tare, aka kawo wa Umma ruwa ta sha. Sun ɗan taɓa hira kaɗan ana ta raha daga nan ne ta miƙe ta wuce sauran sasan suma aka gaisa, sai ta wuce ita kaɗai sashin Baban Sasa, ta same shi yana kwance a falon shi, ya kishingiɗa yana fifita kasancewar babu wuta, ta shiga da sallama ya amsa mata yana miƙewa zaune tare da kallon ta
 
“Asiya ce?”
 
“Eh Yaya.” Ta furta tana zama a ƙasan tare da gaishe shi cikin girmamawa
 
Ya amsa ta shima cikin kulawa yana tambayar ta iyalan nata?
 
“Alhamdulillah suna nan lafiya.”
 
“To Haulatu har ta sanar miki da saƙon namu kenan?”
 
“Eh yau ta je gidana ta sanar min, shiyasa na taho sabida in roƙi alfarma.”
 
Gyara zamansa yayi yana mayar da idanunsa a kanta tare da cewa, “to fa! Wanne alfarma kenan Asiya?”
 
Shiru ta ɗan yi ita kuma, kana kuma ta buɗe baki tare da cewa, “a kan maganar Madina ce da za’a yiwa kaciyar nan Yaya, Madina yarinya ce bata kai shekarun da ake yiwa sauran ba, shiyasa nace idan da hali a barta zuwa wata shekaran kamar yanda lokacin ne ta cika shekarun da za’a yi mata, don Allah a duba maganata Yaya.”
 
Ɗan jimm. Baban Sasa yayi kana kuma yace, “mu ma mun yi wannan tunanin Asiya tun kafin kiyi, amma abun lura a nan dole ne fa za’a yiwa yarinyar nan al’adan nan tunda babu wanda zai tsallake ta, mu kuma muna ganin sauƙin hakan ne shiyasa muka yanke wannan shawaran, ba ki fi mu sanin me muke yi ba babu abun da zai samu Madina don wai bata kai shekarun sauran ba, ko a baya da muke gudanar da al’adar nan daga shekaru 5 ne zuwa 6, amma yanzu ita takai shekaru goma a lissafina, kinga kuwa tayi girman da itama za’a iya mata, duk a gidan nan babu kuma wani sa’anta da za’a haɗa su wata shekaran ayi musu, sauran duk Yara ne, to, a ganin mu da mu sake jira wata shekaran ayi mata da wasu tsirarun ƴan ƙauyen gwara a haɗa su gaba ɗaya ayi musu yanzu; tunda mun duba duk basu da yawa, Ni abun da yasa nace a sanar miki sabida ki sani ne kar a shiga haƙƙin ki a matsayin ki na Uwarta, amma ba shawaran ki muke so ba.”
 
Umma da ke faman share hawaye tun soma maganar sa, kasa ɗagowa tayi da kanta sai da yace mata, “zata iya tafiya tunda shi ya gama magana.” Sai ta ɗago tana roƙon shi cikin magiya tana sake jaddada mishi, “Madina yarinya ce a barta ta sake girma, tana gudun abun da zai biyo baya kar su kashe mata yarinya.”
 
Ran Baban Sasa ya soma ɓaci, shiyasa ya buɗe baki a zafafe yace, “ke Asiya ba ma son maganar banza da hofi a nan, ita kanta farau ne da za ki ce wani abun zai same ta? Tun yaushe ake wannan al’adar babu wani abu da ya taɓa samun jama’a sai a kanta? Idan ba’a yi mata ba taya zata cika Mace a martaba ta a duniya? Ba na son zancen banza tun kafin raina ya ɓaci muyi rabuwar ɓatacciya ki ɓace min a gaba na.” Sai ya ja dogon tsaki yana mayar da jiki ya sake kishingiɗa tare da kuma mitan cewa, “idan ba shirme ba; Ni ne za ki zo gabana kina gaya min abun da yakamata? ita ƴar uwanta da aka yi mata uban me ya same ta? Al’adan mu ne babu wanda ya isa ya hana ta.”
 
Umma miƙewa tayi itama ranta a ɓace, sai dai ta kasa tsayar da hawayen nata sai kwaranya suke yi, sai da ta fita sannan ta share hawayen gudun kar a gani, amma ana kallonta za’a gane tayi kuka, baza ta iya tsayawa tana kallo a yiwa ɗiyarta kaciya ba, kamar Madina, wannan ai zalunci ne, ko a sanda aka yiwa Haula bata da yanda zata yi ne, bata ma san an yi ba sai daga baya, sannan bata manta wahalar da Haula ta sha ba a kan wannan kaciyar, Allah ne ya taƙaita wahala sai da tayi ta zuwar mata da magani tana bata daƙyar ta samu sauƙi, domin su sun ƙi kaita asibiti a duba ta sai jiƙe-jiƙe da ake bata, kuma sun hana ta ta ɗauke ta ta kaita tunda basu yarda da asibiti ba sai magungunan gargajiya, dole ta riƙa zuwa da maganin a ɓoye na asibiti tana bata har aka samu ta samu sauƙi, sai ga shi yanzu za’a kuma a kan Madina wacce bata kai shekarun su ba ma, wannan mugunta har ina? Baza ta iya tsayawa ta gani ba. Shiyasa tana shiga sashin su Inna Lami tace musu, “ita zata tafi.”
 
“Ah ah baza ki bari ayi musu a gaban ki bane? Naji an ce Mutumin ne bai zo ba har yanzu.” Cewar Inna Asabe da ta fito tsulum daga ɗaki jin abun da Umma take cewa
 
“A’a bazan zauna ba, tunda nayi abun da ya kawo Ni dole zan tafi, su kuma Allah ya basu lafiya Allah yasa ayi a Sa’a.”
 
Tuni hawaye sun soma wanke min fuska saboda jin abun da Umma take faɗa, da sauri na miƙe daga kusa da Yaya Haula ina dire mata ɗiyarta, sai na nufi wajen da Umma ke tsaye na rungume ta ina me fashewa da kuka, cikin kukan nake cewa, “Umma kar ki tafi ki bar Ni don Allah, ba na so ayi min don Allah ki tafi dani.”
 
Wasu sabbin hawayen ne suka soma sintiri a kan fuskar Umma sabida tsantsan tausayi na, da sauri ta sa hannu ta share tana me kamo fuskata tare da cewa, “kiyi haƙuri Madina Allah shi ne zai kare ki, babu abin da zai faru da ke sai alkhairi, Ni zan tafi gida kinji?”
 
Kuka sosai nake yi a yanzu, ina cewa, “kar ta tafi.” Na ƙanƙame ta sosai a jikina ina kuka har da su majinu, kuma na hana ta tafiya
 
Dole Yaya Haula ce ta taso itama tana kukan ta kama Ni, amma duk yadda ta so ta ɓanɓare Ni ta kasa
 
Su Inna Lami kuwa sun samu abun yi sai faɗa suke yi amma ko jin su ba na yi, Ni kuka na da tashin hankali na ya ishe Ni, ƙarshe Yayan mu Shamsu aka kira tunda shi ne a sasan, shi ya zo ya ɓanɓare Ni ya shiga dani ɗaki, ita kuma Umma tayi musu sallama ta fice ba tare da ta jira cewar su ba, haka Yaya Haula ta bi bayan ta domin suyi sallama sai share hawaye take yi
 
Mutanen gida kowa taɓe baki yayi ya ci gaba da aikin gaban shi domin su a wurin su ba tausayi na basu ba, su ma idan da hali baza su so a yiwa Yaran su ba amma an fi ƙarfin su basu da yanda zasu yi, duk yaran su na gidan aure sai da aka yi musu ba yau suka saba shiga baƙin ciki irin wannan ba, dole su danne kayan su tunda ko sun nuna a fili ƙarshe a kansu zai ƙare
 
Ni kuwa daƙyar Yaya Shamsu ya natsar da Ni sai da ya saka min hannu, tare da daka min tsawa yace, “idan ya sake jin kuka na zan ga abun da zai yi min.”
 
 
Dole na gimtse baki har da riƙewa da hannu ina ta shashsheƙa, yayinda hawaye ke gudun tsere a idanu na amma babu halin fitar da kukana waje, idan ma na fitar abun da ya same Ni ni naso domin duk gidan nan babu mugu kamar Yaya Shamsu, shi a wurin shi ya kama yarinya yayi mata shegen duka na fitan hankali abu ne mae sauƙi, yawancin ƴan gidan namu haka suke sam-sam ba sa wasa Mazan. Ina nan a zaune aka soma kiran mu wai Mutumin da zai mana kaciyar ya iso, nan fa kuka na ya dawo sabo, ƙin fita nayi sai da aka zo aka ɗauke Ni, haka nake kuka ina bori baza ayi min ba, a lokacin da aka kai Ni zauren gidanmu har an yiwa Fatimah da Fa’iza sai tsandara ihu suke yi, saura su Luba da su ma kukan kawai suke yi, gaba ɗaya iyalan gidan mu Maza suna wajen, su Baffa da su Yaya Shamsu duk su ne masu kama mu
 
Nima fa sai na ruɗe kuka na ya ƙaru, amma sai aka ce a ɗaure min ƙafafu da hannaye tunda bazan tsaya ba sai bori nake yi. Hannayena suka soma ɗaurewa ta baya sai su ma ƙafafuna kamar wata akuya, aka rufe min idanu ya zamana ba na ganin komai sai kukana da na kasa denawa, dole shima aka ƙulle min baki saboda yanda nake yanka kuka kamar raina zai fita, a lokacin ne aka fito da bakin al’aurata da aka cire min skirt ɗin jiki na. Bayan wasu mintoci, sai na ji raɗaɗi, na yi kururuwa amma ba mai ji na, na yi ƙoƙarin fincike ƙafata amma sai na ji wani ƙarfe ya rirriƙe ƙafafuna, babu wani abun rage raɗaɗi sai wani ganye, ina jin sanda aka manna min shi a jiki na, daga nan ban sake sanin inda kaina yake ba sabida azaban da yayi min yawa, a tunani na raina ya gama ficewa a cikin jikina.
 

Leave a Reply

Back to top button