littattafan hausa novel complete

Tattalin So Littafi Na Ɗaya Hausa Novel

TATTALIN SO 1**1KANAL ALIYU Gwarzo jarumin sojakenan, Alh yahuza shine mahaifinsa,matansa biyu da ‘ya’ya biyar. Hajiyahabiba itace uwar gida, da ‘ya’yanta uku.Aliyu shine babba, sai sani da sadiya, sai hajiyatalatu me ‘ya’ya biyu, ni’ima dahamza.Dukkaninsu kansu a hade yake, da yakesun samu tarbiya sam babu irin ‘yanubancin nan bare nuna bambamci ajunansu. Alh safiyanu kanin alh yahuza ne,uwarsudaya ubansu daya, matarsa daya hajiyasaude, da ‘ya’yan su uku, maza biyu farukda sadiq, sai karamarsu mace mai sunazainab.Babban gida ne kowane da bangarensa, gabadayansu akwai kyakyawardangantaka da son juna a tsakaninsu.Mahaifiyarsu hajiya Babba, itama a gidantake bagarenta daban.Dattijuwar arziki ce mai addini da ibada,gata da kokarin zumunci, du inda taji dan uwantawanda ko kaka dangantaka tahada su, saita jawo shi jikinta yaciarzikinta dana ‘ya’yanta. Hajiya kyaftinkenan dattijuwar arziki, ko yaushejikokinta suna tare da ita tana hadakawunansu, tana yi musu nasihohi da tattausarmurya, ta rinka yi musu tarihinannabawa da abubuwan data san zasukaru dasu, su kara samun fahimta koda amakaranta ne.Idan lokacin sallah yayi takan hadasamarin gidan su tafi masallacin gidan, ita kumada ‘yan matan subi masallacindaga gida.ZAINAB itace karama a gidan, a lokacintana ‘yar shekara shidda. Zainab yarinyace mai wayo da basira, ga dabara,yarinya ce ma shiga rai, du wanda ya zauna daita sai yaji yarinyar ta shigemasa rai lokaci daya.Gaba daya ‘ya’yan gidan su takwas sunagida banda yaya Aliyu, dashi yanakaduna gidanshi, don ya gamakaratunshi tuni ya zama soja yana zaune agidanshi na kaduna.Bayan sallar ishsha, hajiya kyaftin dasadiya me shekara goma sha takwas, dani’ima mai shekara goma sha uku, saizainab ‘yar shekara bakwai, suna idar dasallar sukayi addu’a suka shafa. Zainab ta miketa duba fulas din abinci,tasa babban faranti ta zuba musushinkafa da miyar kaji. Ta bude firij tadebo musu lemukan kwalba guda hudu,da pure water guda hudu, da coca-colaguda hudu. Tace hajiya ga abinci idan mun cinyesaimu kara.”ni’ima tace ki kyalemu dai masu cin abinciidan mun cinye idan mun cinye ma karaamma banda ke me cakula ki daukehannu, da dai kayan zaki ne.Zainab ta tabe baki, kin ganta ko aunty sadiya?Sadiya tace, “ni’ima wai meyasa kike sontsokanar zainab ne, kinsan ita kadan takejira taki cin abincin ma.”sai anan hajiya tayi magana, tace, “habaita ta fara, aida na danneta nayi mata dura. Kuzomuci abinci kada ya huce.”gaba daya sukayi bisimillah suka fara ci.Yaya Aliyu ne ya tako cikin kasaita da isa,yayi sallama ya shigo dakin, gaba dayasuka mike da murnan cewa, “ga yaya, gayaya. Hajiya ta rinka tafa hannu cikin murnatana dariya, tace “babban mai gida yaukuma saukar dare akayi mana?Yace wallahi hajiya motarce ta banimatsala a hanya.” tace, ikon Allah, tohAllah ya kiyaye gaba.” daya bayan daya kannannasa suke gaishe shi.Tuni zainab ta hada mishi abinci agabanshi dasu lemo da ruwa, yace sannuautarmu.” zainab ta koma waje daya tazauna.Hajiya tace, a’a taho mana muci gaba da cinabincin? Zainab ta shafa cikin tace,”Allah yajiya na koshi.”ni’ima tace kin gani ko hajiya? Data faracin abincin nata wai ta koshi, shiyasakullum bata girma saboda bata son cinabinci.” sadiya tace zoki zauna na baki abaki.”zainab tace haba aunty dazu fa kina kallonasha youghot da biskit, nifa bana jinyunwa.”yaya Aliyu ya daka mata tsawa, tashi kijekuci, wato har yanzu kina nan dakin cin abincinnaki ko?Ta mike jikinta na rawa, tazo tana cusaabincin ba a son ranta ba, don tasanhalin yaya Aliyu, baya son wargi, yanzuintayi wasa yakai mata duka. Don gabadayansu suna shakkar yaya Aliyu, don shi damabai fiya yawan magana ba, kumabashida sakin fuska koda wasa, shiyayasa da ya shiga makarantan sojojimutane dayawa suka rinka ganin ya daceda soja.Suna gama cin abinci ta hada kwanukan takwashe, daga nan ta kyallabangarensu da gudu ta fada dakinmamanta, taje ta ta kwanta a bayantatana hakin gudu.Maman nata tace lafiya gudun me kikeyihaka? Tace “mama yau yaya ya kusa dukanaakan cin abinci.”maman tace, Allah shi kara, inama yadokekin.”tace mama saiki so ya daken da wannanhannunsa mai zafin? Tace “kwarai kuwa, ba dolenaso ya dake ki ba tunda bakyason cin abinci, kinfi so kullum kita zama ahaka ana tsokanarki dace mik ‘yar tsanarmama ko?Zainab ta zumbura baki ta juya matabaya, tace shikenan ma nayi fushi.” maman tacenima nayi fushi ba ruwanadake.”zainab tayi saurin juyowa, tace nadainamama, ki daina fushi dani kinji? Mamantace, toh na daina indai zaki rinka cinabinci kinji? Tace toh naji mama zan rika ci.**** *** *** *** ***sadiya da ni’ima suma duk suka mike kowacce tayi bangarensu, hajiya ta dubiAliyu tace yanzu anya Aliyu bazaka yiaure ba. Idanfa kayi aure zaka karawa kankadaraja a gurinmu da wajenkannenka. Kai ba abun farin ciki banekannenka su rinka faduwa suna tashi agidanka bane, don Allah ka daure kayiaure.TATTALIN SO 1**2Yace, kai hajiya, kin matsanta min damaganan auren nan, wai ke bakyakishina ne?Tace ni ai indai akan wannan ne banayi,ka samo min abokiyar zama, idan kuma kaibazaka iya ba ni na samo maka.”hajjaju kenan, za’a nemo in Allah yayarda. Tace dakai wani ne saika samo ahadaka da ‘yar uwarka sadiya, tundakaga ansa rana data yi candy za’ayi aureinsha Allahu.” yace kai hajiya, kedai kina sonhadasabgata da yaran nan so kike su rainanine?Tace, “ai kaji sha’anin naka, sai songirma kamar gyambo, yo meyesa bakanemo tuni kayi ba? To bari kaji na fada maka, koka nemo yarinyar da kake so ayiauren kafin bikin sadiya, ko kuma ayiauren lokaci daya da sadiya.”ya mike yana dariya, “hajaju kenan, kintaba ji anyiwa namiji auren dole? Taceza a fara shi kuwa daga kanka.” hajiya dai dagaske take lamarinta, donta matsu taga Aliyun yayi aure, tana soya kara samun daraja da mutunci a guniyayenshi, saboda Aliyu yaro ne nutsatsemai hankali da nutsuwa, yana da biyayya.Du abunda iyayensa suke so shi za yayi. Du dakarancin shekarunsa yanada halinya kamata, shiyasa ya zama abokinshawarar iyayensa.Karfe shidda na yamma direba ya kwaso’yan makaranta tun safe. Da yake zainaba firamare take, karfe daya ake tashinsu, to saitashiga lesson na awa daya, karfebiyu take fitowa sannan antashi susadiya da ni’ima da suke ‘yan sakandare.To sai suyi sallah direba ya kawo musuabinci suci, sai kuma shiga islamiya datake duk a cikin makarantar. Karfe hudu zasu fitosallar la’asar, suyi dan ciye-ciyensu su kuma komawa aji, sai karfeshidda za’a tashesu suyo gida.Yau direba yana tsayawa zainab ta budeta fito tayi bangarensu, kicin ta nufa dontasan mamanta tana kicin ita da ‘yan aikinsu dongudanar da girkin dare.Hajiya saude ta tari ‘yarta da murna tanacewa, “sannu da zuwa auta.” tarungumeta suna dariya ta cika uwar tatata nufi firiji tana cewa, wallahi mamayunwa nake ji.” ta bude firij tace kai mama inavanilla ice-cream dina?Mama tace a’a zeey bana son rigima, batun jiya kika gama shanye naki ba?Tace “to mama bana sa ragowar dayan afirij ba.” tace to ai kuwa dashi sadik yatafi makaranta da safe. Zainab tanajin haka tayarda jaka ta hautsalle da ihu tana kuka, “wallahi saiyabiyata ice-cream. Faruk da sadik sukashigo duk da goyon jakunan su, sumanasu direban ya dauko su, donmakarantar matan daban ta mazan daban akasakasau.Tace “wai ice-cream dinta tasa a firijwaye ya daukar mata a cikinku. Farukyace “mama ai sadik ne ya tafi dashimakaranta.”sadik yace ai banaki bane ragowa ne na dauka dazaki kama yiwa mutane kuka.”tace “to bani nasa shi a firij ba kaje kadauka min ba, wallahi sai biyani abuna.”taci gaba da kukanta tana tsalle. Aliyuyana dakinsa ya ringa jiyo ihunta, yashigo da sauri yana cewa lafiya? Me akayi matamama? Tace rigimar datasaba ne kawai, ice-cream ne du sunsharoba dai-dai, ragowar daya ne wai tadauka tasa a firij shikuma dan uwandayan abokin yin nata ya dauke ya tafimakaranta dashi ya shanye, shiya kawo wannanrikici nata.” ya daka mata tsawa,”tashi zaune.” ta mike a razane tayi dakida gudu. Dai-dai lokacin ni’ima takeshigowa take cewa “wallahi yaya koabinci bata ci a makaranta ba saiyoughot me sanyi ta rinka siya tana sha wuniguda, yaya sadiya tai ta mata fadata kwace youghot din ta siyo mata meatpie da yambos, saida taga zata daketasannan taci.Aliyu yace a’a ba akai muku abinci bane?Tace, “ankai mana mana, bata cin abinci saikayan zaki dana sanyi take sha.”ya kwada mata kira da karfi, “zainab kinaina? Ta fito daga falon da sauri ta rabe awaje daya. Yace maza ni’ima shiga kicinki zubo mata abinci ina zaune ta cinyeshi. Ni’ima ta zubo mata abinci ta dire agabanta, Aliyu ya daka mata tsawa daukiki cinyeshi. Taja filet din ta fara cinabincin, tsoronsa take ji sosai, don tasanbaya wasa.Yace ki cinye shi du idan kika rage ko kaka nidakene. Ya juya ya fita, ya samidireba a waje ya bashi dubu biyar, yaceyaje bakori ya siyo masa ice-cream dayoughot masu sanyi, da gashashiyarkaza guda biyu.” ya wuce dakinsa. Zainabkuwa tana zaune tana kuka tana tura abincin,saida ta cinye tas sannan tatashi tayi daki ta kuka, me aikinsu ta bitatana rarrashinta, ta hada ruwa a baho, tacuda ta sannan ta kyaleata ta karasawankan da kanta ta dauro alwalar sallarmagariba, tana cikin shiryawa taji sallamar direbada yake kaisu makaranta.Mama ta amsa masa, ya shigo yadurkusa yace, “gashi mama inji yayaAliyu, na zainab ne.Maman ta karba tana budawa, tace “Aliyukenan, ai shine ma ja gaban sangartar da zainab,don daman can shiya koya matairin wannan cimar bata damu da abinciba, gashi ta fara girma abu yana nema yazame mata jiki.ta kwala mata kira, ta fito da sauri tanacewa “mama me yayan ya kawomin. Ta tura makayan, gashinan ‘yar lelen yaya.ta fito ta kama dubawa, robar yght gudashida, ice-cream guda shida, gasassunkaji guda biyu, ta dauki robar ice-creamda nono dai-dai ta saka a firij, tace wlhmama kada ki bari sukuma daukar min.TATTALIN SO 1**3MAMAN ta bata kaza daya da youghot guda uku,ice-cream guda uku, gashi nan saii tafi gidanhajiya ki hadu keda ‘yan uwanki mata da mazantunda suna can kuci, wannan kuma in na nashigawajen su hajiya cin abinci maci acan.”zainab ta dauki ledar tayi bangaren wajen hajiya,ta shiga da sallamarta, ni’ima ta tarota tanadariya tare da cewa, “sai ‘yar gidan daddy, mekika samo mana.Tace, “ai bazaki ciba tunda kika sa aka sani cinyeabinci.” tace haba yi hakuri ‘yar kanwata, kinsantsakaninmu bata baci.”sadiya ta karbo kayan tace, bawanin kunyi fadada ita dani take shiri.” gaba daya suka hadu sunacin kazar da youghot din da ice-cream din. AhakaAliyu ya shigo ya sami kujera can nesa dasu yanaduba jarida. Zainab tasa jummai mai aikinsu tadauko mata jakarta ta islamiya tana son yinhadda, don gobe malaminsu yace su zo masa dahaddan Arrahaman izu bakwai.Ta bude Qur’ani ta bawa hajiya, tace hajiyarikemin nayi hadda, gobe malam yace muzo masada hadda, du wanda bai iya ba zai sha bulala.Hajiya ta rike mata Qur’ani ta fara karantoArrraman cikin kwararen larabci irin wanda akekoya musu a islamiyasu, da yake tana da zakinmurya, gashi ta iya fitar da kowane harafi, ta iyarera karatun da kome kake yi in kaji saika tsayaka saurareta.Aliyu ya lumshe ido yana mai jin dadin karatunnata, a ransa kuwa fassara suran yake yi yanafasalta mata ‘yan aljannan da Allah ya yiwarahama. Tana kaiwa karshen suran taceAlhamdulillah, na haddace a kaina.”hajiya tace “barakallahu fik, kin wuce dukanmalam.” hajiya tace shiyasa nake sara mikimutuniyatashagwabarki bata damuna tunda akwai ki dakwakwalwa mai kyau, du abunda aka gaya mikikya dauke shi a kanki.Sadik yace “iyayi dai da neman suna wai ita acemata mai ilimi.”zainab tace toh ilimi karyane? Ai ilimi shine kangaba a rayuwar dan Adam. Ilimi lallai ne mace yakasance tana kula dashi, ilimin addinin ta dakuma ilimin rayuwa.Misali, bari na baka misali da kowanne. Iliminaddini don tasan yadda hukunce-hukunce sallah,tsarki, jinin al’ada, jinin biki da dai sauransu.Ilimin rayuwa kuwa, don kanta ya waye yakasance tasan abunda yake faruwa a duniya,koda ta sauraron ko radiyo, kada ace mace batasan sunan gwamnan garinsu ba, ko shugabankasa. Kinga akwai karancin wayewa a wajenkikenan.Ilimi wani abune da yake karawa mutum daraja,Allah mai girma da daukaka yace “Allah ya shaidalallai babu abun bautawa da gaskiya sai shi.”kuma mala’iku ma’abota ilimi sun shaida yanatsayar da adalci mabuwayi mai hikima. Kagasaboda muhimmacin ilimi a wannan aya, sai Allahya ga hada shaidarsa data mala’iku da kuma tamasu ilimi.Ashe du wanda ba malami ba, ba kuma maineman ilimi ba, toh bai cika cikakken mutum ba.Haka kuma annabi ya fada acikin wani hadisi,”duk wanda Allah yaso shi da Alkhairi, saiyafahimtar dashi Addini.” haka kuma yana cewa,”neman ilimi farilla ne akan kowane musulminamiji ko mace.Kuma Darajar farko idan ance ilimi shine iliminaddinin musulunci,sai kuma ilimi na rayuwa,kamar su ilimin likita, injiniya, siyasa, mu’amalada dai sauransu.Daraja da kimar ‘ya mace tana karuwagwargwadon yadda ta kula da iliminta, kamarkuma yanda darajar da kimarta take lalacewa awulakance sakamakon yanda taki yin ilimi.”mace ta gar itace wadda kunya bata hanataneman ilimi, ilimi na addini kona rayuwa. Ka dubaka gani, nana Aisha matar manzon Allah (S.A.W)du da yarinya ce karama, domin har annabi yabar duniya shekarunta sha takwas ne, amma tayigwagwarmaya da maza wajen haddace hadisanAnnabi (S.A.W), domin itace ta hudu a cikinmutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisaiannabi acikin sahabbai.Kaga wannan yana nuna kulawar mata da ilimikenan.To kada kuma yi min zargin son gwaninta neyake sani yin karatu, a’a inason yin koyi da nanaAisha ne, don nima inaso na zama mace mawadatatcen ilimi.Hajiya tace Allahu akbar, Allah ya baki ikon yi.’yan’uwan suka sa mata dariya, tare da cewa saiauta.Aliyu yarinyar yaji ta burgeshi, ta kara shigaransa sosai, yanda take da kyakyawarkwakwalwa ya kamata abarta tayi ilimi mai zurfidon ta zama wani abu gaba. Iliminta ya amfanisauran al’umma.Washe gari yaya Aliyu sammako yayi ya komakaduna bakin aikinsa. Cikin hukuncin ubangiji saiga mama da ciki, don ita harta fitar da ran sakehaihuwa, to ta ga zainab shekara bakwai hardawata uku. Sannu a hankali hajiya tana matsawaaliyu da maganar aure, shifa ya gaya mata bashida lokacin da zai tsaya duba matar da zai aura,ita tace “to ta nemo masa, don ita tanada lokaci.Du da akwai gidan makocinsu Alh haruna, ‘yargidan mansura ita take mutuwar son Aliyu, dusanda yazo tai ta shige da fice kenan a gidan, ayimasa soye-soye na kayan dadi akawo masa,amma baya kulawa saidai kannensa su cinye,hajiya ta zuba tukuici.Duk yanda mansura taso taja ra’ayinsa don yasota, ya rinka sauraranta bata isa ba, ko kallontaba yayi saboda miskili ne.Ita kuwa hajiya taga tayi tayi dashi ya samomatar da zai aura ya kasa, suka nema masaauren mansura.TATTALIN SO 1**4SUKA nema masa auren mansura. Alhharuna mahaifinta yaji dadi, inda yace ahade sa ranar data yaya sadiya ayi bikigaba daya.”da mansura taji wannan labarin kamar ta zubaruwa a kasa tasha don zumudi damurna. Shikuwa yaya Aliyu ya hakura neya yarda don bashi da yanda zaiyi, tundaiyayensa da kakansa sunfi karfinsa.Yaya sadiya sunyi candy a ranar suka yifatin candy, kawayenta da ‘yan makarantar sunshayin hotuna hardabidiyo caset don dai tarihi. Sun kakkarbiadireshin junansu da lambobin waya,don dai su rinka tunawa da juna sunasada zumunci a junansu.Satinsu biyu da candy yaya sadiya ta fara rabonkatin bikinta. Inda itama mansurata ke raba nata katin bikin ga kawayentada ‘yan uwa.Haka yaya Aliyu anbawa sani ya kaimasa katunan can kaduna, yanatarabawa abokan aikinsa da abokan arziki. Ranaralhamis akayi kamun mansura,ranar jumma’a akayi kamun yaya sadiya.A ranar yaya Aliyu ya dira daga kaduna,da wasu tawagar abokanan nasa da yayimusu masauki a daya daga cikin gidajeniyayensu. Washe gari ranar asabar akayi daurinaure, gaba daya ankon galila shaddasuka matsa, da hadadden dinki yi matana aikin saa. Du ita suka sa, saida akajegidan su mansura aka dauro auren yayaAliyu, sannan aka daura auren yaya sadiya, daganan maroka suka shigabusa da kade-kade, su Alh suka shigarabon kudi ana watsawa maroka kudi.Haka abokanan yaya safiyanu mijinsadiya, sukai ta watsawa maroka kudi.Karfe hudu dai-dai aka shirya walima, kawayenyaya sadiya da kawayenmansura, abokanan yaya Aliyu daabokanan yaya safiyanu, du sun cikwalliya ta kece raini, hadaddun ‘yanmata gogaggu, wannan ta wace wannan,wannan tana wace waccan, sun sha ado dakwalliya.A harabar gidansu akayi da yakefarfajiyar katuwa ce, an kafa rumfunaaciki an zuzzuba kujeru farare acikinrumfar.An ware gunda Aliyu da mansura, safiyanu dasadiya zasu zauna.Anyiwa wajen ado da fulawoyi da robabalan-balan, an wadata wajen da amareda angwaye, sunyi kyau kamar fulawaaka dasa dan kyau.Ni’ima ‘yar shekara sha hudu ta fara zamabudurwa, domin makerin budurcihar ya fara kerata. Tayi kyau ta ratsocikin tsakiyar filin gurin da lasfika take, tadauki lasfikar tace, “ansuturillah.” ta fadasau uku, jama’ar sai kowa sukayi shirusuka zuba ido. Ni’ima ta kalli inda iyayenta suketagadaddyn zainab da Abbansu, shigarsu iridaya. Haka iyayen su mata duka su ukunshiga iri daya suka yi.Ta kalli jama’a taga kowa yayi shiru yanutsu ya zuba mata ido. Saita ce “muyi salati gaannabi.” gabadaya suka ce (s.a.w).” bayan an gamakarantawa tace, “ya shafi sha biyu, Allahya shafe du wata fitina da zata kunnowama’auratan nan.” gaba daya akaceameen.” bayan angama tace Ayatul kursiyu kafauku, Allah ka karemu ga mugun ji, mugungani, sharrin mutum dana Aljan, dasharrin duk wani abunki.Allah ya basu zaman lafiya, Allah ya basuzuri’a dayyiba saliha, Allah yasa anyi wannanaure a sa’a.Ta cika da fatiha, ta daga hannunta tanaaddu’a ana amsawa da Amin. “wamanyattikillah yaja’allahu makraja, wayarzurku min haisu lah ya tasiri, wamantawakal alallahi fa huwa hasbun, innallaha baligulamri kadija’Allahu li kullishai’in kadira. Amin.Yayinda kowa ya shafa.Tace to Alhmdllh, jama’a muna yi mukubarka da zuwa, mungode da hallartattaronmu da kuka yi don ku taya mu murnar auren’yan uwan mu.Bari na kira muku autarmu dan tazo tayimana ‘yar fadakarwa kadan kafinmalaman namu da zasu yi wa’azizzikansu gama karasowa, tace “zainab zeeydaddy bismillah.” zainab ‘yar shekara takwas tataso cikinnutsuwa tana murmushi daya karawafuskarta kyau, tana sanye da dan dandatsetsen yelow les da yake ta walwali,dambara-damran dutsuna ajiki kamarmadubi, tasa gwagwaro yelow, ta yafa dankwalinles din. Tasa fashion azurfamai yalayen dutsuna wuya da kunne, dazobensu, tasa warwaraye suma yaleye.Yarinyar tayi kyau sosai, tsarin kwaliyartakamar wata babba. Shiga iri daya sukayida ni’ima komai da komai. Ni’ima ta mika matalasfikar suna yiwajuna murmushi, yayinda masu hotunasuke basu flasha, masu filet din dvd dacd suke ta dauka, ni’ima ta koma wajenzamanta, zainab cikin zakin muryartatace “Aslm ‘yan uwa musulmi.” gaba daya kuwasuka amsa mata da “wslm.”hakika ina taya ‘yan uwana murna dawannan rana ta aurensu, Allah ya basuzaman lafiya dauwamamme, yaya sadiyada aunty mansura, yanzu Allah ya kaikuwani matsayi da rayuwarku zata canja ba kamarsanda kuna gida ba. 1- abu nafarko da ake so ‘ya mace ta gane tafahimceshi shine, hakkin mijinta akanta,ta gane cewar miji shine shugabanta, tarinka jin hakan a ranta.Saboda Allah ubangiji yace, maza masu tsayuwane da shugabanci a kan mata,kuma maza suna suke da fifiko wajengirma da daraja akan mata.”wadanan dalilai su zasu mace ta dingajin cewa, namij fa shugabane, kuma tadinga jin haka a jikinta, kuma tasan yana dahakki akanta, domin tasan bazata fitaba saida izninsa, kuma duk inda zata jesaita san ransa bazai baci ba.Manzon Allah (s.a.w) ya fada a cikinhadisi ingantacceTATTALIN SO 1**5YA fada acikin hadisi ingantacce, saboda girmanhakkin miji akan matarsa, “da za’a umurci waniyayi sujjada ga wani, dana umurci mace tayiwamijinta sujjda. Kodamiji zai bukaci amfani da matarsa, ita kuma tanakan sirdin rakumi, to kada tahanashi.A wata ruwayar ta bukhari, manzo Allah(s.a.w) yace, “idan mij ya kirawo matarsa zuwaga shimfidarsa ita kuma taki har ya kwana yanafushi da ita, to mala’iku zasuyi ta tsine mata harsai an wayi gari,bukhari ne ya ruwaito.Idan mace ta gane hakkin miji akanta,kuma tayi masa da’a akan abinda basabon Allah bane, to hakan zai taimakakwarai wajen gyara zuciyarta. 2- abu na biyushine amana, anaso maceta zamo mai amana bata cikin abunda yashafi dukiyarsa, kuma bata ha’ince shibaakan karan kanta.Ha’intar miji wajen dukiyarsa daukanwani abunsa batare da iznin sa ba. Ha’intarmiji aka karan kanta kuwa, shineta bada kanta ga wani namiji. Ko kumatayi kawance da mijin da banata ba. Dumatar kirki bazata yi haka ba.Toh macen kirki itace wadda bataha’intar mijinta daga dukiyarsa ko kumaakanta. Salihan mata masu da’a ne gamazajensu, masu tsare mutuncinsu neda dukiyoyin mazajensu, basa ha’intarmazajensu alokacin da basa nan.Manzon Allah (s.a.w) ya fada cewa babuyanda za ayi mace ta dauki wani abu adakin mijinta ba tare da izninsa ba, to baihalatta ba,sai sahabbai suka tambayi annabi cewa “koabinci ne? Sai annabi yace “wannan shine mafidaraja acikin dukiyoyin mu, ba a yarda mace tadauki abincin mijinta tayi kyauta dashi ba.TATTALIN SO 1**6BA AYARDA mace ta dauki abincin mijinta tayikyauta dashiba saidai in dafaffe ne in tayi, gudunkada ya lalace, to sai a sadaukar dan gudun kadaya zamo almubazaranci. Shima idan miji ya dawosaiki sanar masa, ko gidanku zaki aika da abincisaiki sanar masa, bare ki bawa wani can daban.Wannan yana cikin cin amanar miji.Manya mutane suka rinka mikewa suna yiwazainab kyautar kudi, saboda yanda yarinyakarama ta burgesu, Abba da daddy sai washebaki suke yi don jin kokarin ‘yar tasu dakwazonta.Mamanta kuwa tayi hamdala acikin ranta, tanamai jin dadin baiwar da Allah yayi wa ‘yarta tuntana karama, kowane tebir mutum hudu ne azagaye dashi, akayi umurni da masu sabis su fararabon abinci, shinkafa ce fara da taliya itamahaka, sai soyayyun kaji da gasashen nama, saimitfy, samosa, sopringros, haka kowa za a tsirakaton filet a dire a gabansa, mata masu wa’azisun zo, wajen yayi shiru an nutsu ana cin abinci,yayinda aketa kwararo wa’azi akan zaman aurega ma’aurata.Washe gari akayi yini, ranar litinin akayi fati, aranar kuma aka kai amare dakunansu. Burinmansura ya cika, yau ta auri gwarzon namijicikakke, wato Aliyu.Tasan sarai Aliyu miskili ne bai fiyawasa da dariya ba, shi hasalima magana wahalatake masa yi masa, don inzaka daka ta tashi saidai kuyi ta zaman kurame dashi.Aliyu mutum ne mai tsafta, dan gayu ne mai sonkamshi, baya damuwa du tsadan turare zai sayaindai kamshin shi yana da dadi. Aliyu yana ji dakansa, akwai iya jan aji, yana da tsananin iyayida gwalli kamar mace, ya fiya kasaita da songirma kamar wani basarake.Washe gari ranar talata gajiyar biki bata barni’ima da zainab zuwa makaranta ba. Tun asubada aka tashe su suka yi sallah, suka sakekomawa gado suka nade cikin bargo suna bacci.Karfe bakwai masu aikinsu sukayi ta tashinsu donsu shiry su tafi makaranta, amma du sunki tashi.Dole sai rabuwa suka yi dasu.Karfe goma dai-dai Aliyu ya shigo gidan dongaishe da iyayensa. A farfajiyar gidansu mai gadida direbobi suna ta risinnawa suna gaisheshi.Aliyu ya cewa malam idi direba, “ina ‘yanmakaranta , i ce kodai basu makara bako?Malam idi yace ai basu fito ba, yau ban kaisumakaranta ba.” a zuciye Aliyu ya shiga gidan,kafa kawai yasa ya daki kofar ta bude garam.Ni’ima da zainab suka tashi a firgice, sunamitsike ido. Suna dago kai suka ganshi. Kafarshidaya akan gadon, dayar tana kasa, fuskar nantayi kirtif da ita kamar bai taba dariya ba.Zumbur suka mike suka diro kasa daga gadon,suka durkusa can nesa dashi, suka kama cewa”yaya ina kwana? Bai amsa musu gaisuwar ba,sai tambaya daya jefo musu cewar “meya hanakuzuwa makaranta? Gaba daya jikinsu ya hau barisuna in’ina da kame-kame abunda zasu ce, yadaka musu tsawa “ku tashi ku saka uniformdinku, ina jiranku a falo.” suka mike da saurikowacce ta nufi kwaba. Shikuma yayo falonsuyana tsaye. Mintuna kadan suka fito sanye dakayan makaranta da jakunkunansu a rataye, yasasu a gaba har farfajiyar gidansu, ya kwalawamalam idi direba kira, ya taho jikinsa na rawa.Yace “daga yau du ranar daka kara kin kaisumakaranta abakacin aikinka.”malam idi ya rikice jikinsa yana bari, yace “kayihakuri yallabai, wallahi ba laifi na bane sune basufito ba.” yace “daga yau idan kaga basu fito bakayi min waya kawai ka gaya min. Yace “toyallbai.” suka shiga motar direban ya jasu.Shikuma Aliyu yayi cikin gida. Zainab tace,”inbanda abun yaya, daga yin aure saika fito dasassafe. “ni’ima tace, “ai gwandake bangarenkuma na ‘yan firamare ne, ni ‘yar sakandare nasanwallahi sai an dake ni, daya kyalemu gobe basamuzo ba.”gidan Aliyu yana nan daga bayan gidansu banisa. Amma tunda aka kai mansura basu je gidanba, saboda basu da wani lokaci sai dare, sukumaba fita suka yi da dare ba.Yau alhamis ana tashi daga boko gida suka yo,dan ba islamiya. Ni’ima da zainab tuni sun gamashiri, anko sukayi na wani dandatsesen materialbaki, ni’ima tana rike da hannun zainab suka tafi.Suna zuwa gidan suka shiga, ‘yan aikin gidan saisannu da zuwa suke yi musu. Suka karasababban falo inda matar gidan take, sukayisallama, saida akayi musu izni sannan sukashiga. Mansura ta taresu da murna, a’a sai yauzaku zo, nayi fushi.” suka rike hannunta sunacewa, “tuba muke aunty, kinsan kullum damakaranta.Tace, “to amma gaskiya yau anan zaku kwana.”suka ce wai kwana aunty? Ai baza a barmu ba agida.” tace haba don Allah, ya ya zasu hanakukwana a gidan babban yaya.” yayinda takekwalawa mai aikinta kira talatuwa, “na’am rankiya dade, ta amsa da saurinta, ta durkusa agabanta, mansura tace “bakya ga munyi bai nebaki kawo musu komai ba, nifa bana sonshashanci, kirinka kula da aikinki fa.”talatuwa tace kiyi hakuri aunty. Ta fita da saurita shiga kicin ta hado musu lemuka da snackstaje ta durkusa a gbansu ta ajiye. Zata mikezainab ta bude jakarta ta dauko dari biyar tamika mata. Talatuwa tasa hannu biyu ta karbatana godiya. Inna laraba tashigo ta durkusa agaban mansura tana tambayarta hajiya me za’agirka?TATTALIN SO 1**7TA YAMUTSA fuska tana tsara mataabunda zata girka. Harta mike tafara tafiya zainab tabita tasa matadari biyar a hannunta, tsohuwalaraba tace, “auta me za a sayo miki?Tace a’a ki rike baki nayi. Laraba tawashe baki tana murna tana godewazainab.Yaya Aliyu ya shigo, da sauri zainabda ni’ima suka yi masa sannu dazuwa tare da gaishe shi. Ya wucebangarensa. Mansura ta kwalawatalatuwa kira, tazo da saurinta.Mansura tace, “ki hadawa Aliyuabinci kikai bangarensa.”zainab kanta data ke yarinya tayimamakin abun, bare ni’ima data farazama budura. Sun san haka baikamata ba, don ba haka ake yi agidan su ba.Wata mata ce da goyon ‘yarta ta fitada hayyacinta kamar almajira, tadurkusa tana gaida mansura.Mansura ta hade rai tana ya musta,da kyar ta amsa gaisuwan matar.Ni’ima da zainab suka gaishe damatar, zainab tace kwanto yarinyar,bata da lafiya ne? Matar tace”wallahi zazzabi ne da amai da kashina hakori.” yayinda take kokarinsakkota. Zainab ta mika hannu zatakarbeta, mansura tayi karaf tace “kezeey auta yarinyar ba lafiya kokarindaukarta kike? Saita yo miki amaiajiki.” zeey tace to kije ki sai matamagani ta sha mana.Matar ta girgiza kai cikin yanayi natausayawa, tace, “aiba kudin ne,magani har dari tara da hamsin,banida kudin dazan sai mata, kudinyayi yawa, ko dari da hamsin banida’ita bare har dari tara da hamsin.”zainab ta bude jakarsu ta zaro gudandubu daya ta mikawa matar, “ungokije kisai mata maganin.” matar takarba bakinta yana rawa.Mansura tace, “ke zeey kudin wa kikasamu kiketa rabarwa haka? Zainabtace daddy ne ya bamu da zamu zoko zamu sai wani abun.Mansura tace to shine kike rabar dakudi baku sai komai ba.” zainab taceaunty ai muna da komai me zamusaya? Ba gwanda mu bayarba.”matar nan dai tanata sawa zeeyalbarka harta fice ta tafi.Ni’ima ta fuzge jakar daga hannunzainab, ta bude ta leke bakomaiaciki, ta harareta to kin rabar manada kudin, to yanzu dame zamu saiice-cream din? Ni shiyasa wallahibana so nabar kudin mu a hannunki,du saiki rabarwa da mutane mu kibarmu haka. Nidai kawai kirinkabayar da iya naki, kada ki kumabayarmin da nawa kudin.”zainab tayi murmushi, tace “habayaya ni’ima, abunki ai nawa ne, zaniya iko da komai naki, Allah ya bamurai da lafiya, muna da kudi a gida,ko an bamu ma tarawa muke yi idanbamuda abun siya. To ga masubukata saimu hanasu.” ni’ima tace,”to amma ai bakya bayar du ba, aikinsan zamu sai ice-cream.”zainab tace bakomai yaya ni’ima,zaki ga Allah ya bamu wasu, donranan malaminmu yace, “anasomutum ya rinka ya waita sadaka,saboda tana juyar da bala’i.A zamanin annabi sulaiman (a.s)akwai wani mutum a gidansa akwaiwata katuwar bishiya, tsutsuwa tayi’ya’ya akai. Sai wata rana matar tagaya wa mijinta cewar, ya hau kanbishiyar nan ya debo musu ‘ya’yanwannan tsutsunwar zasu ci suda’ya’yansu.Mutumin nan ya kwaso ‘ya’yan, sukagashe shi, shida matarsa da ‘ya’yansasuka cinye. Sai tsunsuwar nan takaikarar wannan mutumin gurin annabisulaiman (a.s), shikuma yasa akakirawo mutumin yayi musu tsakanida wannan tsuntsuwar, mutuminyayi alkawari bazai sake ba.Ana haka sai wata rana matar nan yakuma gayawa mijinta ya hau bishiyaya kuma debo musu ‘ya’yantsunsuwa, mutumin yaki, yace”annabi sulaiman ya hana shi ya sakedibar mata ‘ya’ya.” sai matar tacekana ganin annabi sulaiman zaiyimaka wani abu danka kwashe ‘ya’yantsunsuwa, alhalin shima meshagaltuwane da mulkinsa? Matardai tai ta rudarsa har ya hau yadebo.Sai tsuntsuwar nan tasake kai kararsawajen annabi sulaiman, annabisulaiman yayi fushi, ya kirawoshaidanu guda biyu, daya dagagabas daya daga yamma. Yace sutafikan bishiyar nan su zauna, idanmutumin nan ya sake zuwa wajen’ya’yan tsunsuwar nan su rikekafafuwansa su watsoshi kasa.Shaidanu suka je kan bishiya sukazauna. Shikuma mutumin ganin yadebo wa’yancan ba ayi masa komaiba, don haka sa wannan karon ma yasake komawa domin ya debo ‘ya’yan.Har ya taka kafarsa zai hau, sai yajialmajiri yana bara a kofar gida, saiyaumurci matar nan data bawaalmajirin nan wani abu. Sai matarnan tace bakomai awajenta.Sai mutumin nan ya dawo ya samulomar abinci ya bawa almajirin nan,sannan ya koma bishiya ya debo’ya’yan tsuntsuwar nan, saita sakedwowa ta gayawa annabi sulaiman,sai yayi fushi mai tsanani, ya kirawoshadanun guda biyu daya tura kanbishiyar. Sai suka ce bamu saba makaba, muna kan bishiyar koda yaushe,lokacin da mutumin zai hau kanbishiyar sai wani almajiri yayi baraya koma ya bashi lomar abinci,sannan ya dawo ya hau. Zamu kamashi kenan sai ubangiji ya aiko damala’iku guda biyu, daya ya kamanita wuya ya jefar dani inda rana takebullowa, daya yakama abokina yajefar dashi inda rana take faduwa.To kinga dalilin sadakar da yayi yakubuta daga sharrin shaidanu. Aliyuyana daga dakinshi yana jinsu, yasake jinjina hankalin autarsu, yasanhakika akwai bawar da Allah yayiwaautarsu na musamman.Ya fito daga dakinshi.TATTALIN SO 1**8YA FITO daga dakinshi, yayigyaran murya, ya ciro dubu biyar a Aljihunsa yamikawa zainab, yace “zeey auta ga kudin ice-cream.” ta rissana ta karba tana godiya. YayaAliyu ya wuce ya sake fita. Zainab tace yayani’ima kinga abunda nake fadamiki ba, inka bayarda kadan sai Allah ya baka mai yawa.” ni’imatace nagani, amma bani su nan kada ki sakebayar mana.” ita kuwa mansura a zuciyarta cewatakeyi, “wannan yarinyar da shegen iyayi take.Wajen mangariba suka isa gida. Bangaren hajiyasuka nufa sukayi sallar mangariba, zainab tamike tayi bangarensu, saita tarar da mamantakwance tana juyi. Ta tafi da sauri ta rikota, tanacewa menene mamana, meya sameki? Mamantace banida lafiya zaina, marata da bayana ciwosuke yi. Nan da nan sai zainab tasa kuka tanacewa, “mama tashi muje asibiti kinji? Mama donAllah tashi mu tafi asibiti ko kya samu lafiya.Maman tace da kyar, saboda ta fara galabaita”zainab asibiti babu abunda zasu iya yi min, Allahne kadai zai bani lafiya. Ki kirawomin hajiya daumma da ummi, tayi cikin gida da sauri, du tagaya musu gaba daya suka taho, a lokacin Aliyuyana gidan. Maman ta galabaita sosai, kohannunta bata dagawa. Umma tana ta hadokayan haihuwar a dakin. Umma tana rike damaman, hajiya tana mata tofi a ruwa a kofi,zainab din taje ta rike maman tana jijjigata tanakuka, tana cewa mama! Mama!! Ki bude idonkikiga hajiyan fa na kirawo miki ita. Ki bude idonkikifa tofi take miki, don Allah mama ki bude idonkikiga umma da ummi., kefa kika ce nakira mikisu, don Allah ki tashi.” ta kama jijjigata tanagwale mata ido, tana cewa mama! Mama!!. Aliyuyace “umma ku kamata mu tafi asibiti.” a lokacinAliyu yaiwa abba da daddy waya, suka ce tosuma sun wuce asibitin.” a can suka tarar dasuAbban har sun riga zuwa, aka shigar da mamadakin haihuwa, zainab sai kuka take yi, ta tafi tarungume daddynta tana kuka tana cewa daddykana ganin mama bata da lafiya sun shigar da itacan, daddy kazo mu bita. Ya rungumota yanararrashinta, “kiyi hakuri zainab, ki kwantar dahankalinki, mamanki haihuwa zatayi. Ko bakya sotasamar miki kanwa? Tace ina somana daddy.”to kiy shiru ki daina kuka, mamanki haihuwazatayi kinji ko? Kita yi mata addu’a kinji? Tace”to daddy zanyi mata. Abba yace, hajiya su komada zainab gida a ar umma da ummi a gurinta.Abba ya taho da hajiya da zainab gida, zainab saikuka take yi, suna zuwa gida suna ni’ima dasadik su ni’ima suka tare su da cewa ta haihu?Hajiya tace musu a’a ta dai kusa. Du rarrashin dahajiya take yiwa zainab ta kasa yin shiru, saikuka take yi. Su kuwa can asibiti sun kasasamun nutsuwa, saboda jikin mama da yayitsanani. Wajen karfe uku na dare ta haifi ‘yartamace, su umma da ummi suka ta hamdala sunayiwa Allah godiya. Karfe bakwai na safe gabadaya ‘yan gidan sun hallara, ganin yanda jini yatsinkewa mama, hankalin kowa ya tashi. Daddymijinta yana rike da ita yana salati, yayindalikitoci suketa iya bakin kokarinsu. Sunyi mataallura jinin ya tsaya, du ‘yan uwa sun zagaye ta,harda sadiya amarya da mansura, su sadik dani’ima du suna wajen. Zainab kuwa hajiya tajanye ta suna falon dakin da aka kwantar damaman nata. Saboda kuka da zainab din take yi.Ita kuma mama jikin nata yayi tsanani, sai wasiyatake bayarwa, sai cewa take cikindakushashshiyar murya, “ina zainab autata, kikirawo min zainab dina. Sadik ya fita da guduyana kuka ya kira zainab, ta taho da gudu ta rikehannun maman nata ta jijjigawa, tana cewa “ganimama, tashi gaya min abunda zaki gaya min, kinjimamana? Ta kwantar da kanta akan ruwan cikinmaman nata tana kuka, maman data ke fitar danishi da kyar ta dora hannunta kan zainab dintana shafawa, a hankali ta rinka motsa bakintatana karanto kalmar shahada ‘yan uwa sunataamsa mata, tana ta shakewa. Su sadiya dani’ima kuwa gaba daya sun rikice da kuka. Canmama tayi shiru, hamza cikin firgita yace, “tamutu! Iyayen suka dauki salati ga daya dahawaye, yayinda yaran suka cika daki gaba dayada kururuwar kuka. Zainab kuwa tana yin bayaba’a ankara ba ta sulale ta fadi kasa banumfashi. Aliyu ya sunkuce ta aguje ya shigaoffice din likitan da ita. Likitan ya karbe ta dasauri ya dorata kan gado yana kokarin cetorayuwrta. Aka tafi da mama gida akayi matasutura aka binneta, kowa yaji ciwon mutuwarmama. Mama mutuniyar kirki me kawaici dahakuri, daddyn zainab karfin hali kawai yake yi,domin yasan yayi rashin da da wuya ya mayarda’ita. Don rashin hajiya saude ba karamin gibirayuwarsa tayi ba. Anata amsar gaisuwa shikuwasai yayi jigudin yana tunani, ga ‘ya’yanshi ‘yanmazan faruk da sadik suna manne da jikinsa,yaran sun kasa manta mutuwar, sai dai kawaikada suna sharar hawaye. Faruk shine sa’ani’ima mai shekara goma sha hudu, sadik kumashekararsa sha daya. Kwana daya da rasuwarmama aka sallamo zainab suka taho, da yakeummi ce a wajenta. Yarinyar tayi wata irin ramasai kace wacce ta dade da ciwoTATTALIN SO 1**9YARINYAR tayi wata irin rama sai kacewacce ta dade tana ciwo.Wajen umma ta wuce ta karbi babyn damamanta mutu ta bari, ta rungume ‘yartana wani irin kuka mai ban tausayi. Aliyu yashigo da abokanansa zasu yiwa suumma gaisuwa, yana ganin halin dazainab take ciki da jaririyar sai yajitausayinta ya dameshi, ya runtse idoyana taya ta kukan zuci, don ba hawaye.Yace “umma ya za kubar zainab da yarinya arungume a hannu alhalin jikintaba kwari, tama ci abinci kuwa? Ummatace “wallahi tun dazu nake fama da itata bayar da yarinyar taki, kaga abincintadana girka mata da kaina ma taki ci.Ya mikawa zainab hannu, yace “bani ‘yar. Zainabta mika masa babyn yarungumeta, yace mata dauki abincin kici.”ta jawo fulas din tana cin abinci tanayamutsa fuska, don ba dadinsa take ji ba,har wani daci yake yi mata a makogwaro.Idonta kuwa ya kasa tsayar da hawaye. Yamikawa umma yarinyar. Umma tasazani ta goyata. A hannun umma jaririyartake, ita taci gaba da kulawa da ita.Saidai yarinyar ma madara take sha,gado daya suke kwanciya da umma dajaririyar da zainab. Ko yaushe zainab tana mannedajaririyar, ita tasa mata babyn mama, hakaaka cigaba da zaman makoki. Ranarkwana shidda babyn mama taci sunanmaman, wato saude, itama a ranar tarasu, saboda wani zazzabi daya kamata. Zainabtayi ihun kuka da tumami,numfashinta ya rinka futa sama-sama,muryarta ta dashe saboda kuka, ranarsadakar bakwai hajiya iya mahaifiyarmama ta nuna tana son zata tafi dazainab wajenta, tunda itace karama kuma mace,zata ci gaba da rikonta.Daddy yace shi bashida magana saiabunda yayansa ya zartar.” hajiya iyatasa aka kirawo mata Abban Aliyu, tanemi alfarmar abata rikon zainab, Abbayace don Allah tayi hakuri, bazai so raba zainabda ‘yan uwantaba, saboda abunzaiyi mata yawa, kuma shi gaskiya bayason raba kan ‘ya’yansa, kada taje tanatasowa a ware.Du iya kokarin hajiya iya don ta samu yabata zainab, yace shidai hakuri yake bata, ba zaiiya rabuwa da zainab ba.Yana tausaya mata rashin uwa data yi.Dole ne yasa ido a rayuwarta. Dole hajiyaiya tayi hakuri tabar musu ‘yarsu.Bayan sati uku da rasuwar mama, duyara sun koma makaranta boko da islamiya.Zainab kwance kan cinyarumma, Aliyu ya shigo, yana ganin zainabdin ya daka mata tsawa, “ke meyasa bakitafi makaranta ba? Ta kama in’ina takasa cewa, “bakomai. Ya kama yi matafada, “me kike nufi? Haka zaki zauna baza kiyikaratu ba sai sangarta, kinaganin wannan shagwabar itace gata?Wallhi du ranar makaranta nazo nasameki baki je ba, sai jikinki ya gaya miki.Tashi ki sako kayanki ki fito na kaiki.” tamike da sauri ta shiga dakin umma. Aliyu ya kallimahaifiyarsa ya kwantar damurya yana cewa, “haba umma, habaumma, ya zaki daka ta tata ki kyaletabata je makarantaba? Umman tace”wallahi tashi tayi da ciwon kai, gazazzabi a jikinta, shiyasa bta jeba. Wallahi nikuma bana son takura ta,saboda tausayi take bani.Yace “to umma in ance haka za ai tadaka tajin tausayi nata ai sai a lalatamata rayuwa, yanda yarinyar nan ta tasoda kwazo da basira da anbar wani abun ya tauyiilimin nata, shikenan an cutar daita.Umma tace to shikenan ba za a kumaba.”zainab ta fito a shirye cikin uniform dinta,umma ta miko mata fulas din data zuba mataabinci, tace “um-um, umma ba zaniya ci ba.Umma tace anya zainab ayi haka, a cebazaki rinka cin abinci ba.” Aliyu yacekyaleta umma ta shige mu tafi.Suna tafe ya tsaya ya sai mata ice- cream, yasauketa a makaranta, saida yarakata har ajinsu sannan ya fita ya tafi.Kamfanin iyayensu ya wuce, yayi sallmaoffice din daddyn zainab, bayan yayimasa iznin shigowa ya shiga, ya rissinaya gaisheshi, ya jawo kujera ya zauna gabantebur din. Daddy ya hada shayi yafara sha.Yace “daddy don Allah ka bani zainab nariketa a wajena.”daddy yace, “aibakomai Aliyu, dani dakudaya, zainab kanwarka ce, kai kuma dana ne, kajeka tafi da ita, Allah ya baka ikoniya rikonsu.Aliyu yace, “yauwa daddy nagode, barinaje office din Abba na sanar masa.”daddy yace, “to, saika fito.Aliyu yayi sallma office din Abbansu, akayi masaiznin ya shiga, ya samu wajeya zauna, sannan ya rissina ya gaishe daAbban nasu.Yace, “daman nazo na gaya maka ne,don Allah inaso kubani zainab na riketa awajena.” Abban yace, “haba Aliyu, baka tausayinzainab? Yarinya da ita tayi rashin uwa,sannan yanzu kazo ka rabata da cikin’yan uwanta ka kaita waje a ware, itakadai ai bazata ji dadin zama ba.Aliyu ya kara rissinawa yace “Abba ba gani ba,nima ai dan uwanta ne, kumasun saba da mansura.” Abba yace nankakarta hajiya iya, ba yanda batayi daniba don na bata zainab nace tayi hakuriba zan iya rabata da ‘yan uwanta ba. Tokuma sai suji nabawa nawa dan, alhalin matarkayarinyace ko haihuwar fari batayiba.Aliyu yace yi hakuri Abba ka bani zainabdin, insha Allahu zakuji dadin rikondazanyi mata, zamanta a gida yana tayarmata da hankalin rashin ganin ba mamanta. Idankuwa bata gidan zatasamu kwanciyar hankali.”TATTALIN SO 1**10ABBAN yace “toh shikenan Aliyu, Allah ya tayakariko.” Aliyu yace amin Abba, nagode, Abban yaceto ka gayawa daddyn naku? Yace “eh, saida nafara zuwa nayi shawara dashi tukunna.”yace, “to ai shikenan komai yayi dai-dai, Allah yatayaka riko.” ya amsa da Amin. Ya yiwamahaifinsa godiya ya tashi ya nufi gidansu, yagayawa kakarsu.Hajiya murna tayi takara karfafa masa gwiwadaya rike ‘yar uwarsa dakyau, ta hakane zumuncizai kara karfi a tsakaninsu.”don ita hajiya mace ce mai zumunci, tana so tagakan zuri’ar ta a hade, yayiwa hajiyar alheri, hajiyatanata godiya dasa masa albarka, ya fice ya nufibangarensu. Ya tarar da umma da ummi ababban falo suna hira.Yace musu, “ku hadamin kayan zainab dadaddare zan zo na tafi da ita.” gaba daya sukahada baki cikin razana suka ce, “zaka tafi da itaina?Gidana zata koma zan cigaba da rikonta.Umma ta mike ta kama yi masa fada, ” wato muka raina irin rikon da muke yi mata, shine zaka cezaka dauketa saboda kafi mu sanin darajarta, koiko zaka nuna mana akanta?Yayi murmushi yace “kuyi hakuri, umma ba hakabane.” iyakacin maganar kenan yayi musu shiru.Sun riga sun san bai fiya yawan magana ba, saidai yayi atakaice. Inkin ji shi yana hira mai tsawo,to da iyayensa ne maza.Ya mike yana ce musu, “umma bari na karasagida.” umma tace “saboda maganar tamu bata daamsa ko? Yayi murmushi ya dire musu kudi agabansu, yace ummi kwasai goro.” tace “to,mungode, Allah yayi albarka.”yana fita umma ta kama baki, tace, “ki gane minyaro, wai shi babba har ya fimu sanin abunda yadace. Ummi tayi dariya tace “Aliyu kenangadanga kusan yaki. Shifa zuwan da yayi yagadazu bata je makaranta ba, gani yake kamarzamu kara sangartar da ita mu rika biyewashagwabarta.”Aliyu yana isa gidansa yayi fakin ya shiga, a faloya zauna yana karkade kafa. Mansura ta fitodaga daki, tace “sannu da zuwa Aliyu, ga breakdinka can, koda yake rana ma tayi kaine kayi fitarsafe.”yace “nayi break a office din daddy bana tare dayunwa.” yace kisa a share wancan dakin, zandawo da zainab gidan nan zata zauna acikindakin can.Ta dafe kirji tace “haba Aliyu, ya zaka ce zakadawo da zainab? Ai zaka takurawa rayuwarta.Don Allah ka kyaleta a gidanku, wannanshagwababiyar yarinyar in zamu iya da ita anan?Ya doka mata harara yace ba shawararki nazonema ba, idan zainab tazo kada ki barta ta zaunaki koreta.”tace, “haba Aliyu kai ka fiya zafin zuciya, daga’yar wannan maganan saika hau tari, ba nufi nahaka ba, ita da gidan wanta “ai ban isa na koretaba.” yamata shiru bai sake ce mata komai badaman tasan ba zai sake magana ba, don ya fiyamiskilanci, baya son yawan magana.*** ****karfe shidda ‘yan makaranta sun dawo, suna cinabinci ba dadewa akayi mangariba, suna idar dasallah hajiya ta rungumo zainab jikinta tana shafakanta, tace “zainab yanzu fa yayanki zai zo zaitafi dake gidansa, zaki ci gaba da zama acan.”zainab tasa kuka tace, nidai hajiya bazan jebanace, yai tamin fada koma ya dokeni, hajiya tacebazai dokeki ba, kuma fada ma ya daina yi miki.Kije ki zauna kinji zainab? Ta make kafada, um-um, ni ba zanje ba.”suna haka taji yo sallamarsa, da sauri ta tashi dagudu tai cikin dakin hajiya. Aliyu ya shigo ya sakegaida hajiya, hajiya tace masa “zainab dai tacebaza taje ba, ka ganta can harda kuka.”ya kwala mata kira ta fito a tsorace, tazo tadurkusa a gabansayace “shine kika ce bazaki gidana ba? Ta girgizakai alamar cewa, a’a yace to meye nayin kukan?Yi min shiru. Tasa hannunta ta toshe bakinta tahadiye kukan.Yace ki goge hawayenki kije, kiyi wa Abba dadaddy sallama.” tace to, ta goge fuskarta. Tashiga bangaren su umma ta tarar da Abba daumma da ummi suna falo, Abba yace yaki ‘yatatazo ta zauna a jikinsa.” yace menene nagaidonki alamar kinyi kuka? Tace bakomai, Abbasallama nazo inyi muku zan koma gidan yaya.”Abban yace “zainab bana son abunda zaitakuraki, in bakya son zuwa ni zansa ya kyalekikiyi zamanki.” tace a’a Abba zanje.” yace toshikenan zainab, Allah yayi miki Albarka, kici gabada maida kai da kokari a makaranta, tanan nezaku fi shiri da yayan naki kinji ‘yata?Tace “to Abba nagode.” ta mike ta shiga wajendaddynta, ta daura kanta akan cinyarsa tanakuka. Yasa hannunsa yana shafa kanta yace “kiyihakuri zainab, nasan bakya son tafiya. Zainab koyaushe kina raina, dana ganki saikin tunamin damamanki. Zainab du ina tausaya mana ni dakena rashin mamanki.Kiyi hakuri zainab kiyi zamanki, nasan zai rikekida amana kamar ni. Kiyi masa biyayya shidamatarsa, banda rashin kunya kinji? Tace “todaddy zan kiyaye.” ya bude firij ya dauko rubutu aroba ya bata, ungo shanye rubutunki maganintsari da kariya daga shaidanu.” ta karba tayibisimilla ta shanye, ya karba yasa ruwa yadauraye mata, ta karba tasha, ragowar ya zuba ahannunsa ya shafa mata a kanta da fuskarta.Yaita mata nasiha mai shiga jiki, yace ta dainakuka ta tashi taje su tafi.” hajiya dasu ni’ima susadik har gindin mota suka rakota suna hawayetana hawaye.TATTALIN SO 1**11HAJIYA tana rungume da ita tanararrashinta suka bude mata gabanmota ta shiga, ta dunkufar da kantaakan gwiwoyinta tana ci gaba dakukanta kasa-kasa, Aliyu ya sallamesu du yaraba musu kudi, yace sukoma gida, suna tunanin ‘yar uwarsuwai anrabata da gidansu kenan.Ya kalleta au baki daina kukan ba?Tayi saurin hadiye kukan nata, tagoge idanuwanta. Tafiya kadan sukaisa gidansa, suka fito har daki yakaita, “nan shine dakinki, talatuwazata rinka taya ki kwana.” dakin yayikyau, a yau dinan ya sayo matagadon silba da madubi, sai kwaba tajikin bango, sai labuye da jan kafet,shikenan ba wani shirgi, sai toiletaciki dake gefe, tace “to yaya.” yafita ya nufi sashinsa, zainab itama tashiga dakin aunty mansura.Zainab ta kwantar da hankalintatana zaune a gidan yayanta,tsakaninta da abinci saita ga damarci, ko yaushe yayan nata yana cikinsiyo musu ice-cream, youghot subiskit da cakulet, da yake abinci baidami zainab ba, ita hakan saya fiyemata dadi.Ita kuwa mansura ta fiya lalaci dasangarta, bata wani iya girki ba,shikuwa Aliyu dan gaye ne mai aji,gashi da kyankyami, don haka bazaiiya cin abincin mai aiki ba.Don haka inya zo garin ma saidaiyaje gida yaci abinci, don a gidansainna laraba ita take yin girki. Babbarmace ce amma da kwarinta, donbata wuce yin aure ba, sai ‘yarbudurwa wato talatuwa, ita take yimata shara dasu goge-goge dagyaran gado, inta yi baki ta kuladasu. Don wata wauta ta mansuradai-dai da mijin ma inya nason waniabu sai dai ta kira talatuwa.Don haka ma ko meye yagwammace yayi da kansa, abincikuwa saiya je gidansu sannan yaci. Agidansu su umma har fada suke yimasa, don me zai rinka baro girkinmatarsa baya son ci.Sai dai yayi murmushi kawai yacemusu bakomai. Bama yanzu damansura take fama da laulayi. Dasafe yana zaune a falo da wando iyagwiwa da farar shirt, yana lumsheidanuwarsa kamar mai jin barci.Mansura tana zaune kusa dashi tanacin wainar kwai da dankalin turawa,ta zuba shayi a kofi yana ta turiri,gashi yayi kauri da hadin madara danaskofi da dai sauransu.Zainab ta fito sanye cikin shirinmakaranta, ta durkusa ta gaishe dayayan nata da mansura. Ta mike agurguje take, dan takusa makara. Tadauki shanyin gaban auntyn natatadan kurba, tace “wai aunty wannankaurin ai yayi yawa, bakya tsoron yakulle miki ciki?Mansura tayi dariya tace, laifinbabynku ne ba ruwana. Zainab tayidariya tace ai, “ai gwanda ki dinga cisosai don ki haifa mana katon babyin rinka daukarsa da kyar.” ta nufifirij ta dauko ice-cream da youghotda cake, tazo ta wuce su da saurisaboda yayan nata, tace aunty natafimakaranta.” kafin tayi magana Aliyuya kirata “zainab.”tayi saurin juyowa tare da amsawa, asanyaye tace na’am yaya.” zo nan. Tadawo ta durkusa a gabansa. Yacehaka zaki tafi makaranta baki karyaba? Tace yaya zanci cake da ice-cream da youghot a mota.” yacewato har yanzu kina nan dakin cinabincin ki ko sai kayan kwadayi? Kewace iri ce ne? Da safe ma sai kin shasanyi bazaki ci abinda zai dumamamiki ciki ba?Mansura tace wallahi haka nakefama da ita, bata son cin abinci,daga shan kayan zaki sai shan kayansanyi.” yace ina break din nata?Mansura ta kwalawa talatuwa kira,tace mata ina break din zainab?Talatuwa ta shiga dakin zainab dasauri ta dauko break din data kaimata, yanda ta ajiyeshi haka yake,ko budawa bata yiba. Ta ajiye agaban zainab din.Aliyu ya kalleta yace to maza kicinye shi yanzun nan.” idonta yayirau-rau alamar sonyin kuka. Shikuwasai ya jingina da kujera ma yalumshe shanyayyun idanuwansakamar zaiyi barci. Ba yanda zata yi,haka ta rinka tura dankalin nan dakwai tana shan ruwan shayin.Cikinta ya cika taji kokarin yin amaitake yi, tace a hankalin cikin sanyinmuryanta, “yaya ya dago kai yayimata wani kallo, bata iya fada masakomai ba, ta sake sunkuyar da kanta,ya sake lumshe idonsa.Haka taci gaba da ci tana hawaye,saida ta cinye du. Dakyar ta iya tashitsaye, tace yaya na cinye, na tafi? Yabude ido daya yayi mata alama dahannu wai ta tafi. Ta fice inda direbayake jiranta ta shiga ta tafi.Mansura tace gaskiya Aliyu kanamatsawa yarinyar nan, da nice saikabata min rai kace ina takurawakanwarka.” ya bude ido daya yacekarki manta shekaranta goma shadaya, yanzu ta shiga sakandari ajidaya, har yanzu ita yarinya ce, idanbana matsamata taci abinci saiyunwa ta kamata.”ta tabe baki tana gunguni, “in rashincin abinci ne ai a wurinka ta gado,tunda kaima baka cin na gidanka.”ya kwanto akan cinyarta yace, kiyimin da kanki mana, du rashindadinsa ai zanci. Amma zaki rinka satsohuwar mutane wahalar girki,sannan kisa wata yarinya daban itacemai bani abinci, kallon yarinyar nankadai tayar min da zuciya yake.”ta zumburi baki bata ce komai ba, yashafa cikinta yana cewa, “i luv ubaby, yaushe zaka iso kagadaddynka? Tace ai kuwa zai jimabaiga daddyn ba, sai nan da watabiyar.” ya gyada kanshi, Allah kawominshi lafiya.”tadan rankwafo kanshi tace, “Aliyudan Allah zaka danyi min tausa?TATTALIN SO 1**12ALIYU dan Allah zaka danyimin tausa? Yace nikuma me zakiyi min? Tacebakomai.” yace to kyaleni bacci nake ji.” ta turemasa kansa akan kujera, tace to dagani naje nakwanta.” yau alhamis karfe biyu direba ya daukozainab daga makaranta, saboda yau basudaislamiya, shiyasa basu kai shidda ba. Ta shigotana jan jakartata, ta zube a falo tace “wash!Aunty sannu da gida, ya bybynmu? Mansura tacegashi nan dai yana ta min zillo. Aunty ki bashiabinci yaci yunwa yake ji, inya ci zai daina yimiki zillo.” ai naci abinci zeey, kin zata ni irinkice sai anyi min dura ina kuka? Zainab tayi saurinmikewa, bari na tashi kada ya shigo ya gannianan ya kuma sani cinye abincin daya fi karfincikina.” tayi dakinta suna dariya. Da mangaribani’ima tazo gidan, sukayi tsalle suka rungumejuna suna masu jin dadin ganin juna, kamar badazu suka rabu a makaranta ba. Suka zauna afalo suna dariya. Ni’ima tace auntyn mu ina wuni,ya babyn namu? Lafiyarsa kalau gashi nan yanajinki.” ni’ima tace zainab kinsan gobe ne fatinzara’u yusuf shidda na yamma, ya zamuyi wajentafiya, don yanda muke da zara’u dole ne mufasa fatin nan? Zainab tace, wallah yaya ni’imaina so in rakaki, to amma ya zamuyi da yaya,dama ya tafine da sauki, to shi sai ranar littininda safe zaiyi sammakon tafiya kaduna kan bakinaikinsa.” ni’ima tace, “ai dolene ma kije zainab,tare fa nayi mana ankon fatin, har gwagwaron,har takalimin da not din iri daya ne. Kuma yandazara’u take sonki, ke wallahi kin fiya tsoro, ba saikice masa zaki zo gida ba sai muyi tafiyar mu tagida.” mansura tace amma ni’ima anyi saurinyiwa zara’u kawarki aure da wuri, shekararki shabakwai fa? Koda yake daga ganini zara’un nan tagirmeki, Allah ne dai ya hada kaunarku.” ni’imatace shekara biyu fa ta bani, yanzu da ita fazamuyi candy, wai mijin zai barta ta karasa agidansa.” to saurin na meye? Inji mansura, saurawata shidda fa kuyi candyn, da ya kyaleta takarasa ba shikenan ba.” ni’ima tayi dariya tacetsoro yake yi kada ayi masa kwace, tafiya samaridaya wa.” talatuwa ta shigo tana jera musuabinci, ni’ima ta bude jalof din taliya ce dafarfesun kifi. Ni’ima tace zubamin jalof din kadanda farfesun.” talatuwa ta zuba mata. Zainabkuwa farfesun kawai ta diba, ta debo musufantar gwangwani a firij. Ni’ima tace, zainab waike wace iri ce? Ban taba ganin makiyin abinci basama dake, yanzu kuma inkinci wannan shikenansaida safe ko? Tace “a haba yaya zai taho manada cake da icream. Ni’ima tayi tsaki tace,shikenan abincin naki.” tace don Allah aunty kirinka yi mata fada, shiyasa kullum gata nankamar a busheta ta fadi. Mansura tace ai tasankaronsu da yayanku, saina shiga gaya masatukunna.” talatuwa ta dawo da tangaram a rufe,da gasasshiyar kaaza aciki da mansura tasaagasa mata. Ni’ima tace kai aunty ni aida nasanda wannan ai bazan ci farfesun ba, ba ruwankiaunty, abinda kike so kici shi zaki ci. Muma daiAllah ya aurar damu, ina daga kwance aita yiminkomai.” mansura tayi dariya tace, ke kumaabunda yake baki sha’awa kenan. Suka fara cinkazar suna hirarsu, zainab ta fara cire hannuntawaita koshi, ni’ima da mansura kuwa har kashisaida suka taune. Ni’ima ta kwalawa talatuwakira tazo, “gani. Kije ki gayawa direban gidan nangani nan fitowa zai kaini gida.” talatuwa ta fitada sauri. Ni’ima ta mike tana yafa mayafinta dajaka, zainab ta rike hannunta tace, “don Allahyaya ni’ima ki bari sai anjima kya tafi kinji? Tacea’a zainab gwanda na tafi, kinsan yanzu yayayana kan hanyar dawowa gida, kada ya gane ninazo najaki ya hanaki zuwa goben.” tace toshikenan saina zo goben. Ta rakata har mota tatafi. Sannan ta dawo ciki ta wuce dakinta, alwalatayi ta tayar da sallar ishsha. Aliyu ya shigo yawuce dakinsa, sai da ya watsa ruwa ya danshafa lotion a jikinsa, yasa kananan kaya, ya fitofalo yana kallon tashar zee-aflam, suna wanitsohon film mai kyau. Mansura tana gefensa tanacin tufa, zainab ta fito daga daki ta durkusa agabans, tace, yaya sannu da zuwa.” ya amsa ahankali. Taci gaba da tsugunnawa tana so tatambayeshi zuwa gida gobe ta rasa ta ina zatafara. Ya kula da ita yasan akwai abunda take sota tambaye shi, don haka sai yaci gaba dakallonsa ya dauke kansa daga bangaren tanazaune tana zaune tana wasa da yatsun hannunta,tace “yaya. Yace “uhm! Ba tare da ya kallo taba.Saita yi shiru ta kasa cewa komai. Shikuwa yanajingine da kujera ya lumshe ido yana kallo kamarma baisan da zamanta a wurin ba, ta sake cewa,yaya don Allah gobe zanje gida. Yace me ake yia gidan? Tace bakomai. Yace to bazaki jeba.” tasunkuyar da kanta sai hawaye kawai itada batada wahalar yin kuka. Mansura tace don Allah kakyaleta taje.” yayi mata shiru kamar baiji abindatace ba. Mansura tace, ni tsiyata dakai kenan, saiayi ta ma magana kayi shiru kana jin mutanekamar wani kurma. Ko motsi bayyi ba balle yasandashi take. Zainab ta mike a hankali zata wucedaki, ya kirata “zainab.” ta juyo da sauri tare daamsawa na’am yace “don nace bazaki jeba shinekike kuka?TATTALIN SO 1**13 TA juyo da sauri tare daamsawa na’am. Yace “don nace ba zaki gidan bakike kuka? Tayi saurin girgiza kai. Yace bakidabaki? Tace a’a ta koma ta durkusa a gabansatace, “yaya dama bikin kawar yaya ni’ima za’ayi,shine zan rakata.” yace “to me ya hanaki ki gayamin gaskiya? Tace, “don Allah yaya kayi hakuriba zan sake ba.” ya jinjina kai. Tace yaya najegoben? Ya daga kai. Amma kada kiyi dare.” tayimurmushi, “yaya nagode, Allah ya saka daAlheri.” tamike ta shige dakinta tana murna. Dasafe a makaranta zainab take gaya wa ni’imayaya ya barta zata zo. Ni’ima tayi murna, tace”to ki taho da wuri dai. Bayan sun tashi dagamakaranta, karfe biyar na yamma ni’ima ta bugowayar mansura tana neman zainab. Zainab dintana karba ni’ima tace, “haba zeey, ki sauri kizoman biyar fa tayi. Zainab tace, “nayi wanka nagama kwalliya, yaya nake jira ya fita nasa kayanana taho. Tace baya barki ba ki fito ki taho kawaimu tafi. Tace mata, cewa fa yayi kada na dade,to kinga gwanda yasan ban taho da wuri ba.Tace eh to gaskiya hakane. Yauwa kingan shican ma ya fitarsa, yanzu direba zai kawoni.Wajen fatin ya hadu, ango da amarya sunyi kyaukamar fure, sai walwali suke suna sheki. Ni’imasai kaiwa da komowa take a matsayinta nababbar kawa, du inda tayi kuwa zaki ga idanuwansamari a kanta, saboda ni’ima ta zama budurwakyanta ya kara fitowa, ga gwalli ga iyayi. Sumasu sabis da aka dauka sunata kaiwa mutaneabinci dasu swan, lemon kwali dana gwangwani.Jama’a suna cin abinci Ali jita ya saki kida, tunizakin kidansa yasa jama’a suka fara kada kai.Amarya da ango suka shiga filin rawa, nan fakawaye da abokan ango ‘yan uwan amarya da’yan uwan ango, aka shiga filin rawa aka rinkawatsi da naira kamar ba a san zafin nema ba.Hankalin zainab ya tashi ganin har takwas nadare tayi, ta rinka damun ni’ima ta taho su tafigida. Ni’ima tayi tsaki, waike meye hakane? Kibari agama basa mu tafi ba. Zainab tace um-umyaya ni’ima, kinsan halin yaya, kizo mu tafi,ni’ima tace ke wallahi kin fiya matsala, saika cewata matar aure, kita faman jin wannan tsoron,bafa abunda zaiyi miki. Tace um- um, nidai kizomu tafi bana son bacin ran yaya, wallahi du sainaji na damu.” dai- dai lokacin da Ali jita ya sakicashiyar karshe ni’ima ta riko hannun zainabsuka fice suka shiga motarsu, direba ya kawo sugida. Saida aka sauke zainab sannan ya wuce dani’ima gida. Yana zaune a falo yayi zaman nasana kasaita kamar wani basarake, ya lumshe idodaga gani tunani yake yi, mansura tana kwanceda littafi tana karatu, zainab tayi sallama tashigo, mansura ta amsa sallamar tare da cewar”kun dawo? Tace mun dawo aunty.” tace yayasannu da gida.” ya bude ido daya yace sai yanzukuka ga damar dawowa? Bance ku dawo da wuriba? Ta marairaice, “don Allah yaya kayi hakuribazan sake ba.” ya daga kai “shikenan tashi kije.Ta mike tana hamdala a ranta da abin yazo dasauki. Ranar littini da asuba Aliyu ya nufi kadunabakin aikinsa, sai kuma ranar jumma’a da yammazai dawo. Kwanci tashi asarar mai rai, cikinmansura ya shiga wata tara harda kwanaki, tanazama dakyar tashi da bisimillah. Ranar jumma’ada mangariba Aliyu ya iso, bai samu wata tarbaba, sai dai mansura ta langwabe masa bata dalafiya, sai kuka take yi masa. Shikoma du yawani rikice, don shi kukan yaro ma baya so barena babba. Ya kwasheta suka nufi asibiti, rakitake yi da ihu tana murkususu acikin motar.Zainab kuwa sai hawaye take yi, tana cewaaunty kidaina ihu salati zakiyi. Tun a motar Aliyuyayi waya gidan su mansura da gidansu. Sunaisa asibiti aka shigar da mansura dakin haihuwa,Aliyu yayi tagumi yana sauraron ikon Allah,yayinda zainab ta dukufar da kanta acikingwiwarta tana kuka kasa-kasa. Tana tunalokacinda suka kawo mamanta acikin irin wannan halin,wanda haihuwarce sanadiyar mutuwarta, ‘yangidan su mansura sun zo. Yart da kishiyarbabarta. Can saiga ummi tazo, zainab ta tafi takankame ummi tana kuka, ummi ta rinka shafakanta tana rarrashinta. Wani ihu da suka jimansura tayi shine dai-dai da dan ya fado. Nursedin ta garzayo da gudu tazo ta kwantsama musulabarin haihuwa, tuni kowa ya washe baki yadaga hannu sama yana yiwa Allah godiya. Sunshiga dakin anata yiwa juna barka da yaba kyanyaron. Aliyu ya rungumeshi a jikinsa yana maiyimasa addu’a da fatan Allah ya raya shi. Washegari da safe ka sallamesu kasancewar mai jegokalau da ita da babyn. Gidan ya cika da ‘yanbarka ‘yan uwan Aliyu dana mansura.khamis IdrisTATTALIN SO 1**14GIDAN ya cika da ‘yan barka ‘yan uwanAliyu da ‘yan uwan mansura. Sadiya tataho tinkis-tinkis dana ta tsohon cikin,ni’ima da zainab suka rungumota sunamurnar ganinta. Dakin mai jego sai kamshi yake.Kowa yazo barka zainab cezata karbeshi da farin cikinta, ta dakkomasa jaririn. Ko yaushe yaro yanarungume ajikinta, kamar kada ta bawakowa.” ranar kwana hudu aka kawokayan barka a katuwar akwati, kayan jariri netsala tsala masu kyau, da danjeans da shet na yara, takalma, safofi,fidoji, saitin shawul da tawul, bargunamasu laushi.Kaya ne masu kyau da tsari duk ‘yanwaje. Sai karamin akwati kayan mai jego ne,turmin super holllan biyu, leshi biyu,shadda galila mai tsadar guda daya,kowanne da mayafinsa, sai takalma dajaka kala bibbiyu.Ya bawa ni’ima da zainab da sadiyasuper holland biyu su uku, ya karawa zainab dagalila anyi mata haddadendinki aikin sama mai tsalelen kyau.Da mangariba Aliyu yana dakinsa,mansura ta shiga da jaririn, Aliyu yakarbeshi yana murmushi, sai shafashiyake yana murmushi. A zuciyarsa kuwa godiyayakewa ubangiji daya bashikyautar da duk duniya babu wanda ya isaya baka kyautar da sai Allah.Mansura tace Aliyu nazone akanmaganan shirye-shiryen suna. Yace uhm!Me da me zaku yiyyi? “inaso da yamma ayiwalima, da daddaremu fita fati a daula hotel, sai bokitai damanyan robobi da kalanda, du za’ararraba a wajen.Yace za’ayi komai amma banda fati.” tawani harzuko, haba don Allah don Annabi, wallahika fiya yawa, ya zaka ceba za’ayi fati ba, alhali ni inaso na burgesaboda kawayena zamu kakko makadidon kawata fatin, kuma zaka kawo minmatsala.Yace albarka nake nemarwa ‘ya’yan, bana so sutaso akan harkar shaidanci.Ta mike ta kama masifa, kai dai kawaikana so ka wulakantani a gaban kawayena, haka wai haihuwar fari dan kwayadaya amma bazaka saki kudi ayibushasha ba, don kasan bakai kasha wahalarhaihuwan ba.Ya daga mata hannu yace, ya ishenihaka fita ki bani waje.” ta fito tanakunkuni tare da bakaken maganganu. Yadafe kai don jin kansa yana sarawa,mansura zata haddasa masa ciwon kai, shi bayason hayaniya.Ta dawo daki tana kunkuni da fadarmaganganunta. Saratu yayarta tace,meye kuma?Mansura tace kinji wai baza ayi fati dakida ba. Saratu tace, ai wannan wulakanci ne, yamayar damu kananan mutane bayan nihar na buga kati na fara rabawa?Lawisa kawar mansura tace, kawai inbazai bari mu tafi ta nan ba, ba saiki cemasa zaki je kiyi sunan a can ba, inyaso dadaddare muyi tafiyarmu fatin, ai munriga munyi dai ai shikenan.” saratu taceita wallahi jeki ce masa zaki tafi gidazamuyi sunan acan.Mansura tace wallahi yace na fice nabashi waje, idan na koma nasan halin zuciyarsa,sai ya iya marina.Saratu tace tabdi ya mareki? Ai kuwawallahi daya mari aurensa.Lawisa tace, tunda kuwa kika nuna kinajin tsoronsa kinsha wulakanci iri iri.Nan suka hadu sukaita aibata shi, suna fadarmaganganu son ransu. Zainabkuwa ranta ya baci, kawai saita sa kuka.Saratu da lawisa suka hau yi matamasifa. Kinji yarinya da munafunci, danuwanki yayi ba dai-dai ba zaki hanamufadane munafuka? Kiyi kukan jini bana hawayeba.” zainab ta mike tayi dakintatana kuka. Lawisa ta rike baki, tace ahakakike zaune da wannan yarinya maimiskilancin tsiya, har wani kuka take donanfadi laifinsa.Mansura tace kuma wallahi baki ga yanda yaketakura mata ba, ni hartausayi ma take ban, don inyana garibata da sakewa” saratu tace “ai wani irinmutum ne, shiko fuska baya saki donkada akawo masa raini.” ranar suna dolemansura ta hakura da maganar fati, akayi taronsuna da yamma akayi walima taburgewa da bajinta, mai jego sai shigatake tana fita tasa wannan ta cire tasawancan ta cire.Yaro yaci suna Ahmad, sadiya da ni’imada zainab, les din da Alh ya dinka musu sukasaka, da yamma a wajen walimasuka sa super ta wajen Aliyu. Canjimawa zainab ta canjo da shaddar daAliyun ya dinka ma, sadiya tayi matadaurin gwagwaro akanta, tayi kyau,kamar ka saceta ka gudu. Sadiya da ni’ima suncancanja shiga,suma dai shadda ce amma kalar ta kowadaban. Sadiya ta rinka raba kalanda maihoton zainab tana dariya rungume dajariri, kaandar tayi kyaukowa ya karbi kalandar ya kalla saiya yaba daita.Haka su saratu da lawisa su kaita rabarobobi da ‘yan kananan bokitai. Da hakataro ya tashi lfy, kowa yana san barka.Kayan barka da atamfofi data samu, darigunan jarirai kamar wadda zata bude shago.Ba ruwanta kibarta kawai take yi, taci maikyau tasha mai kyau, ta hau gado tamimmike ba ruwanta da harkar Ahmed,yana wajen masu rainonshi su zasu hadamasa madara su bashi yasha, su bashi ruwa,idan ya koshi su goya shi.Shan nononsa sai lokaci lokaci, saidaiidan ta jiyo kukansa ta kirawo ‘yan aikinnata ta balbalesu da masifa, mai suke yimasa yake kuka? Suyi ta faman rantserantse cewar, wallahi basu yi masa komaiba,sannan zata karbeshi ta bashinono, tasa su goya shi suyi ta famanjijjiga har sai yayi barci.TATTALIN SO 1**15TASA su goya shi suyi ta faman jijjiga shihar sai yayi barci.Sai dai fa du sanda zainab ta dawo dagamakaranta, tana yin sallah zata karboahmad daga wajen masu rainonsa, taita yi masawasa tana tarairayarsa, taitayiwa mansura naci da magiya dolesaita karbe shi ta bashi nono ya sha yakoshi.Ahmad yayi wayo sosai, yayi mugun saboda zainab, don har yafi ganeta akan mamanshidon zainab har ta iya yi masawanka, ta shirya shi cikin kaya masukyau, tasa mishi turare yaita kamshi. Harmansura taita sha’awarshi, abinda italalacinta da son jikinta bazai barta ta iyaba. Du da zainab din ba wani lokacine da itaba, inta fita tun takwas na safe sai shiddana yamma take dawowa, idan sun tasodata dawo gida inta ci abinci tayi sallah,tayi wanka tasa kayanta, saita dakkoyaronta ahmad taita yi masa wasa tanalallabashi, har lokacin bacci ta kaiwamansura shi ta bashi nono yasha yakoshi ta taho dashi dakinta ta kwantardashi a gado, ta canja kayan barci tayimusu addu’a taja bargo ta rufe su, tarungume ahmad a jikinta suyi barcinsu. Talatuwadata ke tayaa kwana idan yafarka cikin dare, ita zata dakko shi tabashi madara da ruwa, tasa shi shiakafada ta jijjiga shi yayi gyatsa ya komabaccin shi, saita shimfida shi a gabanzainab ta rufe su. Itama ta koma baccinta dusanda Aliyu yazo weekend, yana kulada abinda yake faruwa da yaronshi dayake kokarin zama marayan karfi da yaji.Sun sha fada da mansura akan sakarwamasu aikin dansa data keyi. Yasha korotaintaje kwana dakinshi, yace saita dakko mishidansa. Saita rabu dashi ta tafidakinta tayi kwanciyarta.A hankali ya fuskanci tsananin son dazainab take yiwa ahmad, ya gano zainabce take kwana da ahmad ba yan aiki ba,sai ya samu nutsuwa a ransa, yayi wa Allahgodiya, don yasan zainab tafimansura tarbiya da sanin ya kamata,yasan danshi zai taso da tarbiya matukaryana tare da zeey autarsu.Yau asabar, Aliyu yana gida, zainab babumakarantar boko, wajen tara na safe tayi waahmad wanka a bahon shi, Aliyu yanakallonta yana yaba baiwar da Allah yayiwa yarinyar, ‘yar da har yanzu bata cikashekara goma sha uku ba, amma tana danisan hankali da tunani wanda ‘yarshekara ashirin da biyar bata dashi, watomansura.Ta gama yi masa wanka, ta nade shi atawul tana yimi shi wakar data ke yi masainyana rigima. Wayar falonce tayi kara,zainab ta daga tace “hello yaya ni’ima.”daga can ni’ima tace yau ne fa yinin kawatamurja sule, kizo da wuri muje.”zainab tace don Allah yaya ni’ima kiyihakuri, ba zan samu damar zuwaba.”ni’iman tace saboda me?Zainab tace, yaya ni’ima wallahi bantambayi yaya ba, kuma kinga yau nadan samuhutu ba boko, ina so na wuni daahmadina, ba zan iya fita waje na barshiba.Ni’ima tace kinfiya shirme zainab, inauwarsa ko zaki zama mai rainonta ne? Itaba unguwa take ficewa ta barshi ba, sai ke zakizauna ki rinka yi mata wahaladashi? Tace “haba yaya ni’ima kada kimanta ahmad dana ne gudan jinina ne,don wallahi basu da maraba da abundazan haifa, tunda dan yaya nane. Inaruwana da halin uwarsa, tsarina daban natadaban. Kiyi hakuri wata rana narakaki, kinji yaya ni’ima?Tace to shikenan auta, ba komai kishafamin kan ahmad ki sumbace shi, kicemasa inji momynshi.”zainab tayi dariya tace, “to bar kiji ma nayi masakafin ki kashe wayar.” tasuabcin kumatun ahmad tace yaronamomynka tace nayi maka, tana kumagaisheka, inta dawo daga gidan biki zatazo ganinka.” ta ajiye wayar tana dariya.Ta zauna ta gama gogewa Ahmad danshinjikinsa, ta shafa masa manshi, tashafa mashi farar hoda, sannan ta dagawuyarsa da hammatarsa ta zazzagamasa, ta shafa masa kasan wuyansa dahammatarsa, tasa masa kwalli, tasa maipampas, tasa masa farar ves, tasa masa safa dadan takalminsa, ta shafa masaturarensa. Shirin yaron yayi kyau, gashiyana ta kamshi.Ta dama mishi madararsa a fida daidaicikinsa, tasa masa abaki ya kama zuka,ya shanye tas, ta bashi dayan fidar mai ruwa aciki ya sha, ta dora shi a kafadartatana shafa bayanshi, yaron har yayigaytsa.Ta dago shi tana yi masa wasa yanadariya, daga bayanta taji ance ” baniyaron naki na taya ki raino.” ta juyo da sauri tace”lah! Yaya yanzu ka shigo?Don ita kwakwata dazu bata ganshi ba,don ita inta na tar da Ahmad batatunanin komai sai yanda zata kula dayaronta. Ta durkusa ta mikawa Aliyu shi,ta gaisar da Aliyun ta mike tayi dakinta itama tashiga wanka. Tana fitowa tagoge jikinta da tawul, ta zauna gabanmadubi tana kalkale jiki.Zainab tun tana karamarta ‘yar iyayi ceda son kwalliya, gata da son kamshi, dakudinta ma sayan turaruka take yi bare yayaAliyu yana sai mata, hakamaAbbansu ko daddynsu suna bata.Ta tsara kwalliyarta cikin wani fine lesmai fulawoyi, bashida nauyi, riga da siketne filet, ta kafa daurin dan kwalinta dayakara fitowa da kyanta, ta fesa turaruka saikamshi take zubawa.Ta fito falo har yanzu Aliyu yana zauneyana lallaba Ahmad da yayi barci, taceyaya yayi barci kawo shi naje nashimfede shi. Ta dan marairaice masacikin shagwabarta tace.TATTALIN SO 1**16TA DAN marairaice masa cikinshagwabarta, tace don Allah yayakabarni naje gida.Yace meyasa kike so ki koyi karya ne, bainaji ni’ima tayo miki waya zakuje gidan bikibane?Tayi kasa da murya cikin shagwaba tace,wallahi yaya ba gidan biki zanje ba, ainagaya mata bazan jeba, tunda ban gayamaka ba. Daman su hajiya zan kaiwaAmadina su ganshi.” ya gyada kanshi, “kujedireba yana waje sai ya kai ku.” tayimurmushi, yauwa yaya nagode.” yagyada kanshi ya jingina da kujera yanata kallonta, tana ta hada fidar Ahmad taruwa data madara, da dan fulas dinshi naruwan zafi, ta debo masa kaya kala biyu dapampas guda biyu ta zuba acikin jakargoyonshi.Wannan page ya dan samu matsala yayibakikwanci tashi ba wuya, zainab ta zamabudurwa, tana da shekara goma sha bakwai,yanzu tana aji shidda asakandare. Zainab kyanta ya kara fitowa,tana da iyayi da kwainane, akwaita datsabta dason gayu, don du wata saita jesalon, bata gajiya da kunshin tafinkafanta ko zanen fulawa ta lalle. Ta fiya sanyimagana da marairaita; saikizata sangarta ce da shagwaba tayi matayawa. Idan tana magana mace maburgeta take yi bare namiji, akwaita daiyayi da yauki da yanga.Abinda yafi fisgar maza da hura wutan sonta aransu, inhar zata shiga wajesaita samu maza masu sonta. Ammabata iya tsayawa ta sauraresu, domintana tsoron yayanta, tana gudun abundazai bata masa rai, bata so tayi masa laifi.Don waya ma ya hanata rikewa, sai wata ranadata je gida Abba ya bata wata maikyau, amma ta rinka dari-dari da tsorongaya masa. Sai Ahmad ne ya dauka dagudu ya kai masa yana gaya masaAbbanshi ya bawa aunty maminshi waya.Saida ya mata gargadi sosai akan in ta sake yajita bawa wani saurayi numbarwayarta sai ranta yayi mummunan baci,don haka take kiyaye wa. Ni’ima anzamababbar budurwa sosai, tana karatundiploma har ansa mata ranar aure har maankusa bikin. Aunty sadiya tanada ‘ya’ya biyu,hafiz dasajida. Mansura kuwa tun daga Ahmadbata sake haihuwa ba, tace dama saiyashekara biyar, toh gashi yanzu yashekara biyar din. Zainab yarinya maihakuri, ga hankali da nutsuwa, tana da kwazo,don tayi saukar qur’ani yanzu tajuya hadda. Yau asabar tana tasowa adaga islamiya ta ware kitson kanta tanason zuwa salon, harta fara tunanin tayanda zata tambayi yayan nata fita, batason yayi mata fada. Zainab tayi murmushi tacedon Allahaunty gayawa yaya zanje salon. Tace”bazan je inda yake ba munyi fada.” tacehaba aunty, don Allah kije ki lallabashi kibashi hakuri, ki tambayo min nidai na tafi.Ta tabe baki tace hakuri? Hakuri fa kika ce? Donya kara wulakantani.” zainab takalleta cikin mamaki, Ahmad ya fito dagudunshi da hijabin nata a hannunshiyana cewa “aunty mami gashi mu tafikinji. Tace jeka gayawa Abbanka cewarzanje salon. Dai-dai lokacin Aliyu ya shigo,Ahmad yaje ya rike hannunshiyana gaya mishi “Abba inji aunty mamiwai zamuje salon. Ya dago kai ya kalleta,”saida kika dauki mayafin tafiya sannanzakice a gayamin.”ta durkusa cikin marairaice warta, tace don Allahyaya kayi hakuri, tun dazu nakejiran fitowarka, ba mayafin tafiyanadauka ba.”ya gyada kanshi kuje Allah kiyaye.Tace yaya na gode. Ya bawa Ahmadkudin salon din, suka tafi direba yakaisu. Sunayin fakin a gaban shagon salon din,suna fitowa daga kanta da zata yi karafidanuwanta suka hade dana wani dankyakyawan saurayi daya zuba mata ido,tayi saurin kawar da kanta, taja hannunAhmad suka shiga ciki, a gurin suka wanke matakai suka gyara mata shi,suka yanke mata farce, suka goge matakafa, du da karfa tata sumul take kamarta jarirai. Ta fito da youghot da biski tabawa Ahmad don kada yaji yunwa.akayi mata kunshi kunshi sarka a hannu da kafa,nan da nan ta canja ta kara yinkyau kamar tauraruwa. Tana fitowa dagawajen idanunsu suka sake haduwa, yayimata murmushi ta dauke kanta da sauri,ya taso ya tari gabanta. Yace “don Allahki taimakamin ki saurareni ki gaya min indagidanku yake nazo na sameki agida.”ta mika masa katin yayanta, tayi saurinshigewa motar direba yaja suka tafi.Saurayin nan ya sumbaci katin databashi yana mai jin dadi da farin ciki haduwarsada wannan bebdin.Suna tafe tana tunanin saurayin datagani, gaskiya ya hadu, itace da tsayawayau harda bawa saurayi katin yayanta,wyarta ce tes ya shigo, tayi mamakin waya turomata tes. To kodai ni’ima ce?Ta bude tes din, bakuwar lambace batasan mai lambar ba, ta fara karanta sakonkamar haka.”i ‘ve been lucking 4 a chance to tell u mymessage, i luv u.” mamaki ya kamata bataankara ba takuma jin shigowar wani sakon, ta bude tafara karantawa.This secret has been in my heart enoughnow i want to make it.Ta bude dayar da suka shigo tare, i told you thati want u to be my wife” a’awannan wane irin kalamomi ne masurikitar da zuciya, waye wannan? Ta sakedubawa ta maimaita karantasu gabadaya. Ba suna to waye wannan? Ita daitasan ba wanda suka hadu dazu bane, donshibata bashi lambar wayarta ba.Kuma tasan ba wani namiji data bawalambar wayarta, to ko waye?TATTALIN SO 1**17Har suka karaso gida zuciyarta tana cikeda tunane-tunane, waye wannan?Meyasa ya boye mata kanshi bai fadisunanshi ba?Ahmad yayi barci, ta saboshi akafada ta kwantardashi kan kujera. Mansura takalleta tace ammafa kinyi kyau, saide kindade.” ta zauna tace “hum! Kedai ki bariaunty, saurayi fa nayi a wajen, kumaharna bashi katin gidan nan, ina tsorokuma kada yazo yaya yayi min fada. Mansuratace a haba wane irin fadakuma? Ai yanzu kin wuce wannan ajin.Don ma keba wayayyi bace kanki a duhuyake, amma yanda kike kyakyawar nangaki danyar budurwa shine dai-dai farawankar samari, toke sai rashin waye wa, kullumkina like a gida, idan zaki fita kizurma hijabi saika ce gyatuma. Don Allahki waye.Tace, to aunty wai ya kike so nayi ne,wace iri ne ce wayewar?Haka dai ta ringa ce mata tanasa matsatsundinki ita kuma zainab tace bahaka Allah yace ba, ka waye akanaddininka shine wayewa, aunty sadiya ceta shigo da sallama da kanwar mijintayasira, a’a auntyn mu barka da zuwa.Zainab taje ta rungumeta, tace yasira rabon goronharda aunty kuke yi ne?Tayi dariya tace to ya zanyi tace da itaza’a kawowa zeey autarsu na fati.Zainab tace fati yasira, anya zan dai zomiki yini, yaya bazai barni naje miki fatiba. Sadiya tace haba don Allah, ke bari zakiyiyasan zakije? Kice masa gidanazaki zo, ni’ima ma nan zata zo saimu tafitare, nayi muku ankon fati dagwagwaronsa, harda takalmi set dinkayan.”zainab tasa ihu, “sai auntyn mu, kedai kina sonfito da ‘yan kannenki.A to inbanyi muku ba wa zanyi wa, kukenan fa kannen nawa mata, ai dole nagyaraku.Mansura tace, “ai wannan autar takusaikin dage mata don taki wayewa, kullum kantaa duhu yake.Sadiya tana dariya tace ai laifin mijinkine, bakina kallo yke takura mana auta ba,ki rinka hanashi kin barin ta da yake tasake.Mansura ta kama baki tace rufamin asiri dayayanku, idan nayi magana tawa cetake yin zafi, ranar jumma’a wato ranarfatin, mansura ta shigo dakin zainabtace, “bazaki je ki fada masa maganarfatin ba saiya fito? Tace don Allah auntygaya masa.” tace kinsan in ni na gaya masa cewazaiyi inason koya miki yawo.Ta mike bari naje, aunty kiyi min addu’aAllah yasa ya barni.” tace “to Amin.”yana shirin fita mansura ta kawo masajakarsa, zainab ta fito ta durkusa tace”yayana. Bai kulata ba yace “uhm! Ya akayi?Yaya dan Allah zanje gidan auntysadiya? Me akeyi a gidan?Bikin kanwar mijinta ake yasira, shinenake neman alfarma dan Allah yayakabarni naje. Ya daga kai kada ki dade. Tace toyayanagode.” yana fita ta tafi gidan sadiya,direba ya kaita. A can ta tarar da ni’imasuka rugume juna suna murna. Kinyi sa’a’yar uwa ya barki.”kinganni dai, yayan namu ne sai a hankali. Ammayau ba laifi fuskar tasa asake take. Hu! Aunty wannan material dinfa? Tana daga su tana yaba kyansu.Tace Abban yasir ne ya kawomin sutsaraba, amma naga sun zo akaya zansai muku. Yauwa auntyn mu kina burgemu fa.Sukagama tsra shirinsu na zuwa fati, wanihadadden material ne da aka sake fito dakyansa da wani dinki mai kyau.Gaba daya su ukun sunyi kyau amma bakamar zeey da kamar don ita aka yoshi. Sunabayan motar sadiya da mijinta sunagaba. A gidan fatin suka bi bayan amaryada ango suka rakata har mazauninta.Yaron sa’adu bori yanata kida da waka’yan mata sunata rawa daga baya akatsaya da kidan, babban kawar amarya tazo ta yiaddu’a tareda yiwa bakin dasuka zo barka da zuwa. Daga nan angoda marya suka tashi suka ja zugarkawaye da abokai suna biye da bayansuhar wajen masu sabis. Kowa shiyakesabis din kansa. Zainab duk inda tyi idon mutanene akanta, ita kallon ya isheta,don bata saba da irin wannan shiga ba,ta saba kullum tana hijabi, to ita abundayafi damunta ma sha daya har tayi, tanajin soron yaya fa.Amma yaya sadiya da mijinta sunce har dakintazasu rakata su bawa yayahakuri.. Wata kawarta tazo tajahannunta, dole saita yi rawa. A hankalitake juyawa, kusan maza hudu ne sukarufa kanta suna mata liki.Kamar daga sama yaya Aliyu ya diro wajen, saijitayi an damki hannunta. Tajuyo a tsorace dan ta razana, ganinyayanta ya hade rai kamar wanda baitaba dariya, saita firgice ta tsorata. Yafunciki hannunta yayi waje da ita, yabude mota ya turata ciki shima ya shiga. Tatakure a tsorace take, saboda tasanhalin yayanta sarai, akwai zafin zuciya.Aliyu ransa ya baci sosai ganin mazasuna yiwa zainab liki, ba dai sonta suke yiba? Wani abu ya soki kirjinsa, ya rinkaganin bibbiyu a idonsa, yayin da motar ta faratangal-tangal kamar zata kifa.Zainab ta fara salati ta baro kujerarta tarungume Aliyu tana ihu tana salati.Tirkashi! Mu hadu a littafi na biyu,waishin menene ya soki zuciyar Aliyu?Download Tattalin So Littafi Na Ɗaya HausaNovel

Leave a Reply

Back to top button