RANA DAYA COMPLETE HAUSA NOVELS PAGE 11 to 15
PAGE 11 to 15
Haka nan de rayuwa ta cigaba da kasance ma wannan ma’aurata ba tare da cigaban komai ba. Nazeefah bata tashi kalmasa kalamunta ga Afzal se idan buk’atan ta ya tashi wanda shi kuma yake biyan mata badon komi ba se don yana ganin nauyinta ya koma kansa yanzu kuma tunda yana da hali. Bayan nan ba abinda yake sake had’asu, girki ma idan ta tashi yi ba dashi takeyi ba kaman yadda ko ta kan kulolinta bayyayi shima. Ana nan watan bikin Nana ya tashi, wanda akayi events duka a nan garin Maiduguri banda dinner wanda dangin ango sukayi organizing a Abuja. A daren tafiyan (bayan d’aurin aure) Nazeefah ta shirya akwatinta tsaf amman ko sanar da Afzal zatayi tafiya batayi ba shide kawai ganinta yayi washegari tana jan akwati amman ko k’ala be ce da ita ba.
Kamar yadda ango da abokansa zasu bi jirgi haka itama amarya da k’awayenta suka bi, cikin d’an k’ank’anin lokaci suka isa Abuja, da yammacin ranan suka shiga shirin dinner sede tun abun be damun Nazeefah har ya soma yi a hankali. Kusan kowacce daga cikin k’awayenta seda samarinsu suka kirasu suka yi masu sun sauk’a lafiya amman banda ita da take da miji, ko text message bata gani ba balle kira har d’aya daga cikin k’awartan ke tambayarta ko lafiya taji Afzal shiru itako tayi mata k’arya cewa shima Afzal d’in yayi tafiya bai ma k’asar kwata-kwata.
Haka nan suka je dinner suka dawo still Afzal be kirata ba yo taya za ayi ya kirata daman bayan bata sanar dashi inda zata ba. Ta fannin Afzal kuwa koda da yamma yayi har dare ya shiga amman Nazeefah bata dawo ba, be damu ya kirata ba kamar yadda be damu ya kira gidansu ba don jin ko lafiya. K’ofansa yayi locking yayi kwanciyansa.
**Washegari da kowa ke juyowa gida ita Nazeefah tak’i akan ita se washegari, haka seda ta k’ara kwana sannan ta juyo. Lafiya k’alau Allah ya dawo da ita gida, koda ta iso ciki a kulle ta tarar da k’ofa, da ta gwada tambayan me gadi key kuwa yake cemata Afzal be ajiye masa ba da ze fita haka nan ta zauna bakin k’ofa tana jiran zuwansa. Ba da dad’ewa ba ya iso inda ya tarar da ita zaune kan kujera a varenda, k’arisawa yayi ya bud’e k’ofar ya shiga ba tare da yace da ita komai ba, itama ko k’ala bata ce masa ba iyaka bin bayansa da tayi ta nufi d’akinta.
Gaba dai gaba dai, har Allah ya kawo su Nazeefah k’arshen semester Alhamdulillah ta samu tayi clearing duka courses nata. Tunda akayi hutu mutumiyar ku ta samu saran fita yawo tun safe se yamma take dawowa gida ba wai kuma tana tambayan izini bane fitanta kawai take tamkar zaman kanta take a gidan, ta d’ayan 6angaren kuwa Afzal ya riga ya rantse kan cewa duk uban rashin hankalin da zata tafka a gidan ba zeyi mata magana ba tunda Allah yayi tana da hankali bawai bata da shi ba, sarai tasan what’s right and wrong.
Ana cikin tafiyan ne k’awar Nazeefah wato Nana wacce akayi auranta bada dad’ewa ba tayi mata waya take sanar da ita k’aruwan da suka samu ita da mijinta. Lis jikin Nazeefah ya mutu tuna yaushe ne akayi bikin nasu har gashi sun samu k’aruwa, ita da auranta ke neman wata shida ko bakwai amman shiru. Zama ita kad’ai tayi bayan wayan tana nazari, gashi de ta fad’i hali d’aya na Afzal da ke k’untata mata ta kasa har rana me kaman na yau bata ta6a jinsa yana waya da budurwa ba, kud’i idan ta tambaya yana bata, girki se ta ga dama takeyi kuma ko uffan bai ce mata, ta rasa dalilin daya sa basu jituwa. Samarukan nata ma da take ganin suna sonta tana da tabbas a kansu suma gashi yanzu da zama yayi zama suma sun soma watsewa suna ja da baya, shin me takeyi wa kanta? Tunani ta fara kode ta sauya halayenta ne ta bawa Afzal dama? Wala Allah zasu daidaita tsakaninsu suma su soma zaman lafiya kaman yadda kowani ma’aurata keyi saidai inaa jiji da kanta baze barta ba. Se ce mata wani ra’ayin yake ai ma idan neman sulhu ne na miji ne ya kamata ya fara ba mace ba don haka zata zuba wa Afzal ido taga iya gudun ruwansa bi izinillahi shi ze soma nemanta. Haka nan ta cigaba da tafka rashin hankalinta amman mey bata ga cigaban komi ba, sam ba canji ta fannin Afzal, tamkar bata gidan haka yake rayuwansa ko kallonta bayayi harkan gabansa kawai yake. Da kad’an-kad’an abun ya soma damun mutumiyarku har ya zammana ita kad’an ta seta had’a tagumi a d’aki tana tunani, ita bawai son sa take ba, ta rantse baza ta ta6a sonsa ba kawai de ita zama haka ba kulawa daga gun miji ne ya soma isanta, duk buro-uban da zata tada a gidan akan lallai-lallai se Afzal ya saketa shi ko be ta6a biye mata ba, hasali ma idan ta fara haukan nata d’akinsa yake shiga ya rufe k’ofa bai fitowa kuwa se ya tabbata tayi shiru kokuwa ya fita ya bar mata gidan ma gabad’aya.
Ganin ba mahalicci se Allah kawai ta d’au wayarta ta buga wa Aminiyarta Rumaysa kira don tuntu6arta shawara inda zancen nasu ya k’aye haka;
“Hmm Babe kenan ai ni da jimawa nasan Afzal nakin nan na son ku daidaita tsakaninku kece de baki gane ba” cewar Rumaysa.
“Kaman ya kenan K’awa?” Nazeefah ta tambaya take.
“Kiga mana bayi fa miki magana bale fad’a ko kin neme sa da magana ma baya biye miki gashi kud’i ko nawa kika tambaya ze baki, ai duk neman ki sauk’o ku shirya ne” tayi mata bayani.
“Toh meke hana sa sakewa dani? Kiji fa d’azu Nana ta kirani wai she’s pregnant.”
“Kai don Allah!” Tayi exclaiming “Allah inganta.”
“Ameen fah wallahi jikina ya mutu haka ranan ma Mummy ta kirani tana min wani irin magana, bata de fito fili tace gashi ba amman na fahimci inda ta dosa.”
“Ke yanzu kina son Afzal d’inne?”
“Allah wadai inso Afzal wallahi yayi kad’an.”
“Toh na me kike tada hankalinki akanshi?”
“Rayuwa hakan ne ni ya isheni tunda baze iya bani kulawar da ya kamata ba a matsayin matarsa ya sakeni in je in auri wanda zamuyi zaman aure mana.”
“Kema kinsan Afzal kam baze sake ki ba.”
“Toh ya kikeson inyi?”
“Ki sauya d’abi’un ki na banzan nan kawai, ku daidaita tsakaninku shikenan, shi Afzal bashi da matsala.”
“Babe wai nufi kike in soma yi masa ladabi da biyayya?”
“Sosai ma kuwa” ta amsa ta take.
“Shamawai! Wallahi bazata saku ba wai bindiga a ruwa think of a better solution kawai.”
“That’s the only option you have left Nazeefah ki duba kiga da auran ki beyi wata shida ko bakwai ba? Me kika tsinana wa kanki banda kondon-kondon zunubi?”
“Yanzu K’awa nice kike gayawa magana haka? Ba laifinki bane ni na kiraki har nike tambayar ki shawara ai se anjima.”
“Nazeef-” bata bata daman k’arisa abinda tayi niyya ba ta katse wayar abinta tare da wulla sa kan gado yayinda ta shiga tunani. Tafi sati tana nazari akan abinda Rumaysa ta fad’a mata daga k’arshe de taga fa idan ba wai ta sauya halayan nan nata bane al’amura bazasu ta6a dai-daita tsakaninta da Afzal ba don haka tayi fad’a wa kanta ta d’an rage yawon banzan da take, da safe zata tashi tayi wanka tsaf tasha kwalya ta fito parlour ta zauna tana kallo sede ko Afzal ya fito bata iya gaishesa, dukda cewan tana son ta gaishesan amman ina tak’ama da jiji da kai irin nata baze barta ba. Shi de Afzal ko da yaga canji kwana biyu beyi magana ba, da farko kan ma yayi tunani ko motarta ce ta 6aci amman jin bata yi masa magana a kai ba se shima ya basar kawai ya zuba mata ido don ganin iya gudun ruwarta. Abinsa ze fita office daga chan idan ya tashi ya wuce gidansu Amal atimes kuma in batada abinyi a gida tazo ta tayasa da abokinsa Sultan hira a office nasa. Shak’uwa na hak’ik’a ne ya shiga tsakaninsu wanda a rana idan basu ga juna ba ko kuwa basu ji muryan juna ba se suji kaman zasu shiga cikin matsala.
A haka ne har new session ya gabato wato watan d’iban sabon admission wanda Afzal ya tsaya akai sosai don ganin Amal ta samu wannan course da take da buri akai, admission na fitowa bim sunan Amal na cikin first batch wayyo dad’i tunda Afzal ya fad’a mata ta samu admission take ta tsalle-tsalle a gidan ta hana kowa sakat. Chan anjima ta d’au wayan Mami ta kira shi ita yaushe ne zasu fara lectures ita bata ma tunanin registration da sauransu damuwarta kawai lectures ne. Ana fara registration Afzal ya sata a gaba haka ze karb’i excuse a office sujesu Unimaid su bi wa Amal layi inda sanin ido yayi magana ayi mata nata da wuri su gama su koma gida har Allah ya kawo su k’arshen registration d’in, kuma da ikon Allah basu ta6a had’uwa da Nazeefah ba se aranar k’arshe ne layin final clearance wata classmate na Nazeefah back then a secondary school wanda bata samu admission ba se this year ta ga Afzal da Amal. Binsu ta rink’ayi har seda taga sun shige mota sannan ta kira Nazeefah ta labarta mata komai wato Nazeefah bata ta6a sanin tana kishin Afzal ba se a wannan lokaci wani irin wawan kishi ne ya tokareta wanda alokacin takeji inda zata ga wannan yarinya seta soketa har lahira. A farko kan ma taso k’aryata batun k’awar nata har take cemata ai office Afzal d’in ya fita yau don tun 7am ya fita kaman yadda ya saba not knowing daga office d’in ya zarce gidansu Amal ne. Hankalinta de ya kasa kwanciya yayinda ta shiga sintiri a parlourn tana jiran isowan Afzal tayi confronting na shi. Ba shi ya tashi dawowa gida ba se chan yamma. Bata ce masa komi ba dukda cewan a tak’ure take ta mai magana sede wani abun nata rik’eta shin ma me zata ce masa bayan rabonsu da suyi magana wa juna kusan sati kenan yau tun ran da ta tambayesa kud’in wasu handouts da textbooks. Kuma ma ai idan ta mai maganan yanzu ze ga kaman ta fara sonsa ne har take kishi akansa kode ta share maganar ne? Kash sede tana ganin idan har batayi confronting nashi ba tana iya mutuwa don haka bayan sallan Isha ta tabbata ya dawo gida ta fito tayi kansa a lokacin yana zaune a parlour yana ta faman aiki akan laptop nasa. Kujeran dake kusa da nasa taje ta zauna akai, shi a tunaninsa ma gabad’aya kud’i take buk’ata dan kuwa bata tashi zama cikin kamala haka se idan damuwanta ya tashi, duk maganan da zata yi masa tana tsaye a kansa takeyi. Bata kaiga mar magana ba ya katseta “Nawa kike buk’ata?” Ya tambayeta ba tare da ya kalleta ba.
Har ga Allah ranta ya 6aci wato irin gata karuwan nan ba ta inda tafi kauri seta fannin kud’i but even still she has no one to blame but herself itace se idan tana neman abu take mar magana ko gaisuwa bai had’asu. Danne zuciyarta tayi tace, “Ni ba kud’i nake buk’ata ba.” D’ago kai yayi yana kallonta da nufin idan ba shi ba toh me? Numfasa tayi sannan da k’yar ta furta kalaman “Ina kaje yau da ka fita?” Shi dariya ma ta basa, murmusawa ya shiga yi sosai ta gefe wanda hakan ya bawa one sided dimple nasa daman lotsewa ciki wanda hakan ya mugun fito da kyansa. Shi don dariyan data basa ma ko iya tanka ta ya kasa, don haka kawai ya miyar da kansa kan laptop nasa yana me cigaba da aikin gabansa. Nazeefah da ta ciko dam ji take kaman ta waske latptop d’in ta buga a k’asa wato ma mahaukaciya ya miyar da ita tana mishi magana sede ya kalleta yayi murmushi ya cigaba da harkan gabansa da kyau.
“Afzal magana nake maka” ta fad’a cikin tattausar murya.
“Sorry regarding?” Ya tambayeta had’e da kafa mata lumsassun idanunsa.
“Where did you branch to after work today?”
“I think that’s none of your business” ya mayar mata tare da kawar da kansa.
“Ban gane it’s none of my business ba, matarka ce ni and I demand to know your whereabouts.”
“Really?” Ya tambayeta yana me sauk’ar da laptop nasan zuwa kan center table had’e da kewayo da kallonsa gabad’aya a kanta. “Duk yawon da kikeyi a gidan nan did I ever questioned you ina kike zuwa? Tafiya kikayi gabad’aya kin sanar dani ne? And is like you seem to be forgetting wa ke zaman wani a gidan nan, remember that, kece kike k’ark’ashina and not the other way round.”
“Ai da sauk’i tunda ni yawo nakeyi ba’a ta6a buga maka waya ance an ganni ina yawo da wani k’ato akan layi ba kamar yadda kake yi da karuwanka-“
“Kul!” Yayi saurin katseta “Ko da wasa kar ki sake kwatanta baiwar Allahn chan da karuwa.”
“Idan na sake fa?” Ta tare shi. “Ai ba k’arya nayi ba idan ba karuwa ba tasan kanada aure amman take janka kuna yawo a titi kowa na kallonku, wannan abun kunya dame yayi kama sede a kirani ace min ga miji na akan layi da wata?”
“Tun yaushe kika fara regarding d’ina as mijinki? That aside koma wanene ya kawo miki wannan rahoto tell that person ba komai tsakani na da yarinyar nan da suka ganmu tare, ta samu admission ne na kuma taimaka mata ta kammala registration nata that’s all.”
“That’s all? Amman kana da mata a gida baka iya ka mata hakan ba? Kana ganin kayi adalci kenan?”
“Lmao, har kina da bakin furta kalman adalci?? See I’ve had a very busy day and as you can see I’m still working idan ke baki da abinda yafi k’wak’wulo suratai please allow me work I’m not ready for this.”
“Toh wallahi ka cigaba muddin ni zan mutuntaka in dena biyewa samarukan da nikeso suke kuma sona don kare maka mutunci I see no reason why da bazaka min haka ba kaima ka dena biyewa karuwanka, ko ka dena ko in d’au mataki da kaina trust me you won’t like the details nide na fad’a maka” tana kaiwa nan ta mik’e ta fice. Shi de Afzal bin ta kawai yayi da kallo sannan ya cigaba da harkan gabansa.
Washegari…
Gidan wata k’awar Ummi dake sayar da zannuwa, laces da ready made hijabs Afzal ya wuce inda ya d’iba wa Amal kaloli da dama, koda k’awar Ummi ke neman tsokanansa take tambayarsa duka wannan wa amaryar mu ne shiru yamata yana murmushi. Daga chan ya wuce 3G ya sai mata shoes and bags na dad’in fita lectures sannan ya biya gidansu. Kasancewar anyi musu kwalta yanzu har gaban gidansu mota na iya kaiwa, yayi parking dab gaban k’ofar nasun inda ya saba kullum sannan ya mata waya yace ta fito. Ba tare da 6ata lokaci ba ta fito sanye da hijabinta kamar kullum se fara’a takeyi ta k’arasa ta shige suka gaisa bayan nan take tambayarsa dalilin daya hanasa k’arisawa ciki yau.
“Haka kawai nace yau bazan shiga ba.”
“Kai Yaya kode wani laifin akayi maka ne inyi gaggawan bada hak’uri.”
“Ai Lily bata laifi.”
“Toh ya kake ya office?”
“Alhamdulillah yau ba islamiyya ne?”
“Akwai fa amman bazan samu daman zuwa ba Mami tace zan rakata suna.”
“Ohh! Ina fatan kin soma shirin school, kinsan in a week time zaku fara lectures.”
“Haka nagani a jikin time table d’in, Allah kai mu.”
“Ameen mu fita in sauk’e miki kayakin naki ina da meeting by 3” yayi maganan yana duban babban agogon dake d’aure a hannunsa.
“Wasu kayaki kuma Yaya?” Shiru yayi bece komi ba har seda ya bud’e booth d’in motan ya sauk’e kayakin tukuna. “Kinga jami’a zaki shiga yanzu dole kiyi sabin kayaki in bahaka ba wataran seki nemi na sawa ki fita lectures ma ki rasa.”
“Yaya kana nufin duka ledojin nan kayaki ne aciki?” Tayi maganan cike da k’in yarda yayin da take k’ok’arin lek’a cikin “Haba Yaya ina zan kai wannan kayaki haka? Gaskiya kayi hak’uri amman bazan iya amsa ba.”
“Kinde san bana wasa dake ko? Kai zo!” Ya kira wani almajirin dake wucewa, “Zo ka k’arisa da kayakin nan ciki” yana gama kaiwa ciki Afzal ya sallameshi. Ba yadda Amal batayi da Afzal ba yashiga ciki su Papi su mai godiya amman yak’i ya jirata ta shiga ciki ta musu magana ma yak’i haka nan ya tafi sannan ta shigo ciki tana kallon kayakin, ninke acikin d’aya daga cikin atamfofin ta tsinci kud’in d’inki. Ita kam sau dayawa takan zauna tayi tunanin mene tayi wa Allah daya shigo da Afzal cikin rayuwarta, damuwarta tun kan ta furta ze yaye mata shi, d’azun take tunanin yadda zata na fita lectures har ta fifftito da kayakinta tana ware sababbin wanda basu sha ruwa sosai ba. Koda ta kira sa anjima, chan bayan sallan Isha dan su Mami suyi masa godiya kashe wayan yayi wai shi baya so. Washegari ita da Mami suka kai mata d’inki.
A satin daya zagayo ta amshi d’inkunan nata da tailor tasamu ta gama don fara fita lectures dasu, tomorrow being her first day at school, tun Asuba da Mami ta tada ta sallah bata sake komawa bacci ba ta fad’a bayi tayi wanka, tana cikin shafa mai sega wayan Mami na ruri kasancewar wayan a gunta ya kwana jiya. Ba tare da 6ata lokaci ba ta d’aga suka gaisa yake sanar da ita by 6:30am zezo ya d’auketa he’ll be the one to drop her off today, duk yadda taso hanasa yak’i ya amince ita a ganinta d’awainiyan ze yi masa yawa. Shirin ta kammala nan da nan ta karya tashiga jiransa, ana cikin haka ne Papi ya fito ya tarar da ita, kud’in mota dana abinci ya bata inda take sanar dashi halin da ake ciki na cewa Afzal yace ze zo ya kaita. Fad’a sosai Papi yayi mata kan meyasa zata amince masa da hakan maza ta kirasa tace masa zata tafi da kanta.
Yana cikin karyawa wayan nasa na dake gefensa akan table ya shiga ruri dai-dai lokacin Nazeefah ke k’arisowa dining d’in zata d’au condensed milk daga cikin fridge da alama itama makarantar zata wuce kaman an aiketa ta lek’a screen na wayansa inda taga ‘Lily’ na flashing akai. Tunani ta soma don a iya saninta Afzal bai da k’anwa kowacece wannan d’in? Fridge d’in ta bud’e ta shiga neme-neme don ta samu daman sauraron wayan nasa. Goge bakinsa yayi da wata mini towel sannan yayi picking call d’in freely, “Halo Lily?”
“Na’am Yaya nace ka bari kawai zan tafi da kai na.”
“Meyasa?” Ya tambayeta take.
“Kamar yadda na fad’a maka haka ma Papi yace babu amfani kawai zaka sa kanka wahala ne.”
“Ai ni nace zan kaiki ki jirani ina zuwa.” Baki wangalau Nazeefah ta bud’e tana kallonsa daga baya kode wannan d’in itace wacce k’awarta Aisha ke fad’a mata ranan? Amman lallai Afzal ya cika wato ita be ta6a cewa ko hanya ze rage mata ba amman idan karuwarsa ce har nema-nema yake tana hanasa da kyau. Duk yadda taso sauraron abinda Amal ke fad’a ta wayan ta kasa. Daga k’arshe de taji Afzal ya kammala wayan da yana fitowa yanzu. Yana juyawa ya bud’e wallet ya ajiye wa Nazeefah kud’in makarantarta bekai da taka k’afa ba ta kira sunansa wanda hakan ya sanya sa tsayawa chak. “Yes?” Ya juya yana kallonta.
“Nace mota na ya lalace jiya shi kad’ansa yake hayak’i kuma gashi ina da lectures 7:30 you’ll have to be the one to drop me off to school” ta shirya k’aryar nan take. Iska ya fisga yana me sosa kansa cike da rashin sanin abun yi “Why didn’t you inform me tun jiya mey gyara yazo ya duba miki?”
“Na mance se yanzu na tuna.”
“Inada muhimmin gun zuwa yanzu let me talk to Ummi’s driver yazo ya kaiki” be bata daman magana ba ya fice. Tun kan ya fita ya kira driver’n Ummi ya sanar dashi buk’atan shi. Haushi ne ya cika Nazeefah dam daba don ta makara ba data bi sahunsa taga gidan wannan ‘yar dake raba masa hankali.
Isan Afzal gidansu Amal keda wuya yayi parking ya shiga ciki, tana ganinsa ta mik’e tare da yi masa sannu da zuwa sannan ta shiga ta ma Papi magana. Bayan gaisuwa Papi ke masa fad’a kan mey nan da makaranta da baze bar Amal taje da kanta ba, se yake ce masa ai dan yau ranar zuwanta na farko ne shiyasa dukda kuwa shi bek’i kullum shi zena kaita ba muddin yana da hali. Da haka Papi ya musu Allah ya kare suka fito.
“Lily?” Ya kirata chak ta tsaya tare da juyawa tana kallonsa, camera kawai ya haskata dashi. “Bade hoto kamin ba Yaya?” Ta tambaya tana kare fuskarta. “Yaya dan Allah ka goge ai ba a yiwa mutum hoton bazata haka.”
“Village girl waya fad’a miki? Ke bakisan unexpected pictures sunfi kyau ba?”
“Toh ai yau banyi kyau ba fuska na du yabi ya kumbura.”
“Inji waye? Ai dan kyan da kikayi yasa na d’aukeki hoton and today is your first day at school too.”
“Wai nayi kyau kaide kasan kan zagin mutum Yaya.”
“On a serious note kinyi kyau Lily, kyau sosai tabarakallahu feek.”
“Thank you Yaya” ta amsa cike da kunya, haka take duk lokacin da Afzal yace tayi kyau setaji kunya ya ziyarceta, ta kuma rasa dalili. K’arisawa cikin motan sukayi ya jasu, har gaban lecture room nasu ya sauk’eta sannan ya sallameta nan ma seda suka kusan fad’a sannan ta amince ta amshi kud’in, Allah bada sa’a ya mata ta fice seda yaga shigewanta ciki ya ja motansa ya wuce office.
Ta fannin Nazeefah kuwa koda driver’n Ummi yazo d’aukanta ko ta kansa batayi ba, motarta taja don bak’in ciki ta wuce school. Throughout the lectures kuwa hankalinta bai jikinta se tunani take haka har suka fita cin abinci ma daga k’arshe seda Rumaysa taja ta gefe take tambayarta ko lafiya, abinku da shagwa6a66iya ba seta 6arke da kuka ba kawai da k’yar Rumaysa tasamu ta sata tayi shiru, ta fad’i meke damunta kuma tak’i, k’arshe gida kawai ta dawo ta watsa ruwa ta kwanta ta hau tunani.
Bata son ta tabbatar da abinda zuciyar ta ke raya mata, taya ma zata fara son Afzal?? Is it even possible?? Taya zuciyarta zatayi mata haka bayan ta d’au alwashin bazata ta6a sonsa ba, a farko taso yaudarar kanta da cewa kishinsa kawai take ba sonsa ba amman kuma ai se idan kanason abu ne har zakayi kishi akansa yanzu shikenan ta fad’a kogin son Afzal kenan? Sai dai sam bata bawa kanta laifi ba dalili kuwa shine ta tabbata ko wace macece aka kawota gidan tabbas itama seta fad’a tarkon son Afzal batare da tasani ba, da irin abubuwan da yake yi komin taurin zuciyan mutum dole ne zuciyar tayi laushi ta soma sonsa. Na farko bai ta6a k’untata mata ba a gidan se har idan ita ta tsokolosa, na biyu se abinda takeso takeyi ko k’ala baya ce mata, ga kud’i ko nawa ta tambaya bata yake, wannan a gefe babban tashin hankalinta shine ta gansa zaune ba kaya gashi yadda kukasan al’ada haka ya camfa zama shirtless a gida. Muddin yana gida toh befi yasanya d’an three quarter wando ba idan yayi mutunci shine ya sanya singlet dake bayyana well defined chest nasa, taya idanunta bazasu kwad’aita wa zuciyarta wannan kyakkyawan halitta ba? Ita yanzu damuwanta d’aya ne yadda za’ayi ta cire soyayyan Afzal daga zuciyarta tun wuri kafin tayi mata illa, sede ya zatayi hakan? A tunaninta idan auran nasu ya mutu soyayyar ma zata mutu don haka yau tayi making up mind nata, Afzal na dawowa gida zata tisa sa a gaba yadda ko ya so ko ya k’i seya rubuta mata takardan sakinta tun wuri tasan inda gari ya waye mata.
PAGE 1⃣2⃣
Tun dawowan Afzal gida ta soma yi masa k’orafi ita ya saketa zaman ya isheta, be kaiga sa key a k’ofan d’akinsa ba ta hankad’e k’ofan tana masa ihu haka yadda ya dawo a gajiye da ciwon kai ya sake ficewa abun tausayi yabar mata gidan gabad’aya ko tanka ta beyi ba. Gida kawai ya nufa ya wuce site nasa inda ya watsa ruwa ya mik’e kan gado se bacci chan kaman a mafarki yaji ana yi masa knocking tamkar wanda baze tashi ba ya lalla6a ya bud’e segani Ummi yayi tsaye bakin k’ofan.
“Ashe de dagaske ne ka shigo” ta soma da fad’i tana binsa da kallo na sosai, jin be amsa ba ta k’arisa ciki “Prince?”
“Uhmm” ya amsa yana kakkafe lumsassun idanunsa wane wanda ya sha abu ya bugu.
“Lafiya dai ko? Mey haka sekace wanda yasha wani abu?”
“Ummi please we’ll talk later, a gaje nake yanzu, kaina ciwo allow me to rest.”
“A gidanka ba wajen hutu ne da seka zo nan zaka kwanta? Ba za ayi wannan rashin hankalin dani ba. Meye dalilin ka? Chan d’in meya samesa?”
“Ummi please kiyi hak’uri kaina ciwo yake I’ll explain everything to you later.”
“Fad’a min meke faruwa tukun ko sena kira Abbanka?”
“Gidana ba lafiya and I need to rest right now please kiyi hak’uri” ganin yadda idanunsa ke kakkafewa kawai yasa ta fice ta ja mar k’ofar. Komawa yayi ya kwanta bashi ya tashi ba se bayan Maghrib, ya na idar da sallah ya nufi site na Ummi inda ya zauna a gefenta suka gaisa take tambayarsa meke faruwa.
“Babu kawai mun samu misunerstanding ne da Nazeefah” yayi mata k’arya, har ga Allah beyi niyyan fasawa Nazeefah tyre ba saboda there’s no point ma, k’arshenta kawai ze had’a kanta da iyayenta ne ya kuma zubar mata da mutunci da girma a idon Ummi.
“Prince kalleni” ta buk’acesa. “K’arya kakeyi.”
“Kamar ya kuma k’arya Ummi? Wallahi matsala muka samu amman na tabbata yanzu ta sauk’o zan koma gida muyi negotiating komi idan Abba ya dawo ki gaishe shi.”
“Toh shikenan ka gaishe da Nazeefan kuma ka k’ara hak’uri kaji? Ko zaka tsaya kaci abinci? An kusa sauk’ewa.”
“A’a bana jin yunwa tea kawai zansha idan na isa gida.”
“Toh Babana bari in raka ka se hak’uri zama da mace kaji?” har gun motansa ta rakasa tana yi masa nasiha sannan ta dawo ciki. Da ikon Allah har ya isa gida ya shige d’akinsa Nazeefah dake bayi tana wanka bataji dawowansa ba se chan kusan k’arfe goma da ya fito d’aukan soda daga fridge suka had’u, ba wanda yace ga d’an uwansa ko k’ala kowa harkan gabansa ya cigaba dayi.
Kusan sati Afzal ya jera yana kai Amal makaranta sannan ya samu wani me napep suka daidaita wanda ze na kai Amal makaranta yana d’aukota a k’arshen wata se a biya sa. Sosai Amal ta miyar da hankalinta ga karatu, daga bokon har islamiyyan bata bar ko d’aya ba.
Ta fannin Afzal kuwa ababen sun soma canzawa suna ca6e masa wanda kuma ya rasa dalilin hakan, haka kawai yake tsintar kansa cikin wani irin nishad’i duk lokacinda yake kallon hotunan Amal kokuwa yake sauraron muryarta baya manta sati d’ayan daya jera yana kaita makaranta, a kullum tana sanye da three quarter hijabanta da side bag nata a gefe kokuwa ta rataya backpack nata a baya. Komin bak’in cikin da Nazeefah ta cusa masa muddin ya shiga kallon hotunan Amal toh seya nemi wannan bak’in ciki ya rasa. Yau ma kaman kullum yana zaune a office nasa gabad’aya ya zurfafa yana kallon wani hoton Amal da take sanye da wani navy blue hijab me hannu, yatsunta ta k’ayatasu da jan lalle wanda ta rik’e fuskarta dasu ta gefe yayinda hankalinta ya duk’ufa kan wani abu, da alama bata ma san an d’auketa hoton ba. Har Sultan ya bud’e k’ofa ya k’ariso cikin office d’in ya zauna Afzal besan ya shigo ba se ji kawai yayi an fisge wayan daga hannunsa kafin yace ze amshe har Sultan ya k’are wa hoton kallo.
“Iyye! Ka fad’a kace” ya fad’a mishi cike da meman tsokana. “Kace ta sace maka zuciya.”
“Mtsw! bani waya na” Afzal daya had’e rai kaman hadari ya fad’a cike da tsiwa. Ba gardama Sultan ya mik’a masa wayan amsa yayi ya rufe had’e da cusawa cikin aljihunsa.
“Hope I’m not interrupting something?” Sultan ya sake tambayansa mockingly.
“Kaga bana son suratan banza, if you’ve nothing better to say just shut up.”
“Yau kuma? So tell me ka sanar da ita kokuwa kana jira muje ne tare?”
“What’re you even saying?” Ya tambayesa tamkar be fahimci inda ya doso ba.
“Don’t pretend you don’t know, maganan Amal nake.”
“What about her?”
“C’mon maza yau kuma ni zaka 6oye ma abu? Kana son Amal ko ba haka ba?”
“So fa kace? How is that even possible?”
“I’ve been observing you lately, duk abinda ya shafi Amal baka wasa da lamarinsa, the way you smile anytime ta shigo office d’innan shima is not normal ba haka kake ba da gashi typical example yanzu har na bud’e k’ofan ka na shigo na zauna baka san da shigowa na ba gabad’aya hankalinka ya duk’ufa akan kallon hotonta.”
“Shikenan kuma se akace don ka k’irga wannan ababe ya zame ina sonta? Kokuma haramun ne in kalli hotunan dake cikin waya na?”
“Ai ba kallon tsakani da Allah kake ba.”
“Lmao, da tsakani da tsuntsu ne?” ya tambayeshi sarcastically.
“Kallon soyayya kakeyi mata do you deny that?”
“Shima son yana da kallo ashe ban sani ba.”
“Maza jokes apart daman ni nasan za’ayi haka jiran ranan kawai nake, so ka sanar da ita ne kokuwa kana jiran muje tare?”
“Nifa suratan banza ne banaso shikenan ban isa in kalli hoto a waya na ba se kace ina son mutumin?”
“Baka amsani ba zamu je tare ne kokuwa ni in je a madadin ka?”
“Wallahi da kuwa me hanani yanka ka se Allah.”
“Lol ka yarda kana sonta kenan.”
“Dan Allah drop this topic ni ban ce maka ina son Amal ba, taya ma zan fara sonta bayan kasan yadda take mutuntani ta kuma d’aukeni a matsayin yayanta data amince da shi, that aside ko ka manta ma ni ina da mace a gida.”
“Toh kuna jituwa da matar naka ne kokuwa ance kai mijin mace d’aya ne?”
“Ba a ce ba amman ni banida ra’ayin rik’e mata biyu.”
“Kana nufin da ba don igiyan auren Nazeefah dake a kanka ba kenan da zaka auri Amal?”
“Eh I mean no! Subhanallah I mean please shut the fvck up!” Ya k’arisa a fusace.
“Woahhh! Lallai kayi nisa maza Amal ta gama da kai.”
“Tashi ka bar min office tashi ka fita.”
“Hab-“
“Sultan am serious ka tashi ka fita min daga office idan har kasan suratan banza zaka cigaba dayi get out.”
“Lalle bature beyi k’arya ba daya ce love can make you do weird things yau amininka kake kora kaman kashi daga office akan mace?” Mik’ewa Afzal yayi a fusace “Tashi ka fita I’m damn serious.” Ganin yadda Afzal ya fusata sosai Sultan yayi shiru ya shiga basa hak’uri yana mai da maganan wasa, “Yi hak’uri ni wasa nake da Allah.”
“Ka fita nace ko sena sa securities sunyi waje da kai?”
“Idiot kai shikenan baka san wasa ba? I said I’m sorry.”
“Iskanci kawai mtsww” komawa yayi ya zauna “Ya office yau?”
“Lafiya bazaka ci abinci bane yau?”
“I’m not hungry yanzun nasha coffee I’m good.”
“Toh nikam bari in k’arisa I’m starving” fad’in Sultan sarai yasan inda Afzal ze nufa so yake ya biya ya d’auki Amal suje suci abincin su biyu. Yana ficewa ba da jimawa ba kuwa Afzal ya d’aga waya ya kira Amal ta wayan Mami da kusan kullum tana zuwa school da shi saboda security reasons. “Halo Lily?”
“Na’am Yaya ina yini?”
“Lafiya ya lectures?”
“Alhamdulillah yanzu ma ya k’are sauran na 3 kuma.”
“Inzo muje muci abinci?”
“Beyi maka nisa ba Yaya?”
“Not at all inzo?”
“Yaya har seka tambayeni izini ne? Se kazo ina jiranka” da haka sukayi sallama in less than 30 minutes Afzal ya iso ya d’auketa. A farko yaso su ci abincin ma a makaranta a cikin unimaid garden amman tuna achan Nazeefah ke cin abinci yasa suka fito suka nemi wani gun daban. Kaman kullum haka yata d’aukanta unexpected pictures tun tana hanasa har tagaji ta miyar da hankalinta ga abincinta kawai. Suna gama ci ya mai da ita school ya koma office.
A haka har su Amal suka samu wata d’aya a makaranta, sosai lectures yayi zafi har ya zammana bata samun time na karatun mahadiyya sosai amman dukda hakan ranan da bata gaji lis ba tana tashi cikin dare tayita bita ko hadda. Yau Asabar bayan sallan Azahar Amal ta shirya ta wuce cafe don yin assignment nata kasancewar bata da smartphone irin na zamani na Mami kuwa baida internet. Ana cikin mata assignment d’inne Afzal ya kirata dake ta fita da wayan Mami ta samu ta d’aga “Halo Yaya ina yini?”
“Lafiya Lily ya kike?”
“Lafiya k’alau ya weekends?”
“Alhamdulillah ya lectures ko yau baki fita ba?”
“Wallahi.”
“Why?” Yayi saurin tambaya a tunaninsa gabad’aya bata da lafiya ne. “Lafiya dai ko?”
“Assignments aka bamu senazo cafe kuma zan samu inyi.”
“Geez Lily I’m sorry.”
“What for Yaya?”
“Gabad’aya na manta bamu sai miki waya ba.”
“Kai Yaya kai kam kashe kud’i baya baka wuya, gashi Allah ya kawo sauk’i akwai cafe kota ina a unguwa mey amfanin wayan?”
“Amman ai still stress ne, har yaushe zaki na fita cafe kullum kina yin assignments?”
“It is worth the stress ai Yaya karka damu please.”
“Toh shikenan dama baki kira ba yau nace lemmi call up inji ko lafiya”
“Wallahi lafiya kuma kana raina nima.”
“Alright toh a gama assignment lafiya I’m hanging up.”
“Alright take care” da haka sukayi sallama. Washegari da yamma ya shirya tsaf cikin wasu k’ananun kaya da suka mugun amsansa ya feffeshe da turare sannan ya fito parlour inda Nazeefah ke zaune tana yin assignment nata, a two seater ya ajiye wata ledar dake hannunsa sannan ya k’arisa dining space d’auko ruwa. Cikin wannan lokaci Nazeefah ta tashi ta bud’e ledar inda taga sabuwar iphone 6s dal cikin ledar. Mumunar fad’i gabanta yayi, take gun ta yanke hukuncin kaiwa budurwarsa zeyi, wani irin wawan kishi ne taji ya tokareta bata kaiga motsawa gun ba Afzal ya k’ariso ya k’wace ledan daga hannunta.
“Ina kuma zakaje?” ta tambayesa lokacinda yake duba cikin ledan don tabbatar da cewa bata ta6a abu aciki ba. Shiru ya mata ya kama hanyan tafiya yayinda tasha gabansa “Yanzu kana ganin abinda kakeyi ka kyauta kenan? Kana ganin kana min adalci kenan a gidan nan? Wallahi ka cigaba Allah na kallonka.”
“Kaman yadda yake kallonki ba, tell me mey kika ta6a nema a gidan nan kika rasa dukda rashin hankalin da kike min ban ta6a tauye miki hak’k’inki ba duk abinda kikeso shi kikeyi a gidan nan without getting questioned what else do you need?”
“What else do I need?” Ta nanata da mmaki tana kallonsa “Your attention and for you stop flirting around taya da aurenka zaka tsaya kana bin ‘yan mata a waje? Do you deny wannan wayar ba wa budurwarka zaka kaiwa ba?”
“I don’t have time for this, na sha fad’a miki ni banida budurwa a waje idan ma ina dashi ba abinda ya shafeki bane I’m a husband to four wives so learn to stay in your lane.”
“Abinda zaka fad’a min kenan Afzal? Dududu auren namu watanni nawa ne har zaka soma kula ‘yan matan waje?”
“Ko nayi ina da laifi ne? Never once did you ever regard me as your husband inba wai buk’atunki sun tashi ba, a tsammaninki kina da right na min magana ne?”
“In girki ne kakeso naji na yarda zan fara yi maka girki.”
“Ni bance ina son girkin ki ba, keep it to your self abu d’aya nakeso da ke learn to mind your business kaman yadda kike duk abinda ranki yaga dama a gidan nan ba wanda ke miki magana nima haka nake da ‘yanci ko fiye da hakan ma because this is my house and I do only what pleases me.”
“Wallahi Allah ze sak’a min.”
“Tare ze mana sakyyan kuma kidena had’ani da Allah” yana kaiwa nan ya wuceta ya fice. Kuka kawai tasa a wajen da k’yar tayi shiru taja mayafinta se gida. Mummy na ganinta ta gaskata zancen akwai matsala a k’asa don haka ta jata d’aki ta shiga jero mata tambayoyi hajiyarku kam ba se kuka ba mutum na iya cewa wani gaggarumin laifi ne Afzal ya mata har Mummy ta soma tunanin ma ko dukanta Afzal d’in yayi. Da k’yar de ta samu Nazeefar tayi shiru sannan ta fad’a mata halin da ake ciki na cewa Afzal na shirin yi mata kishiya ne. Da Mummy ta tambayeta hujja kuwa bata da ko d’aya banda iphone 6 data ga cikin leda se kuma ce mata da yayi wai shi miji ga mata hud’u ne.
“Ke shikenan don kinga ya sai sabon waya seki ce wa budurwa ze kaiwa?”
“Wallahi Mummy wa budurwa ne” ta fad’a tan share hawayenta sau dayawa ina jinsa yana waya da ita kuma ranan ma k’awata tace ta gansa da wata a school.”
“Toh ai koma meye Afzal d’in yayi banga laifinsa ba se naki inda kin bashi girmanshi kin rik’e shi da mutunci da amana kina kula dashi a matsayinsa na mijinki wallahi nasan Afzal baze fara gaggawan k’aro aure ba ko baki fad’a ba Nazeefah nasan baki kula da Afzal a gidan can da k’yar ma idan kina basa girmansa as mijinki wanda kike k’rk’ashinsa, kin musanta?” Shiru Nazeefah tayi tabbas ba k’arya cikin kalamun Mummy ko d’aya. “Dake fa nake? Nayi k’arya?” Shiru tayi chan ta kad’a kai.
“Tell me meyasa bazeyi tunanin sake yin aure ba tunda baki kula dashi baki basa muhimmanci?”
“Toh Mummy shi yana nunawa ya damu dani ne? Tafiya nayi gabad’aya don ban sanar dashi ba ko kira na yayi min na isa lafiya beyi ba.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un Nazeefah!” Mummy ta dafe k’irji “Yanzu har kiyi tafiya bazaki sanar da yaron nan ba? Yau kin fallasheni ni Fatsuma shin tarbiyyan dana baki kenan? Yanzu har kiyi tafiya bazaki sanar da mijinki ba? A tunaninki zaman kanki kike ne a gidan, Iyyeh? Kodan kinga bayi magana ne?” Shirun da Nazeefah tayi ya bata daman cigaba da magana “Da ke fa nike!”
“Toh ai na tuba bazan sake ba ni kawai ki kirashi kice mishi ya dena neman wannan yarinyar da yake.”
“Saboda gani uwar banza ko? Lallai ya tabbata bakida hankali to ki bud’e wannan kunnuwan k’ashin naki wallahi ki saurareni, in ke bakida hankali ni ina da shi kuma muddin baki zubda wannan banzayen halayen nan naki ba haka kinaji kina gani Afzal ze k’aro aure matar ta k’wace miki shi kina ji kina gani kuma ba abinda zaki iya k’arshe yaga dama ma ya sakoki.”
“Dan Allah Mummy ki kirashi ki bashi hak’uri wallahi zan dena rashin hankalin da nakeyi zan shiryu.”
“Kar ma kiyi mana karma is coming for you.”
“Mummy dan Allah kiyi hak’uri.”
“Sani fa ya rage wa me shiga rijiya ko ki canza ko ki sha mamaki.”
“Toh Mummy ya zanyi in karkato da hankalinsa a gareni? Wallahi bazan iya rayuwa da kishiya ba.”
“Kidena rashin ji, bari na bari- yi na yi, kina tsaftace kanki da muhallinki, girki kar ya ta6a wuceki, shin ina kika kai hud’uban dana miki kap kafin in kaiki gidanshi Nazeefah? A ina kika zubar dasu?”
“I’m sorry” ta furta tana turo baki.
“Amman har me kike masa yasa sa wannan gaggawa? Dududu auren naku wata nawa ne?”
“Ni ba abinda nake masa.”
“Oh bazaki bud’e baki kimin magana ba sena kira Daddy’nkunna k’irga mai komi tukun?”
“Mummy dan Allah na tuba, wallahi komi ma na mishi Mummy ko girki ban ta6a mishi ba amman daga yau zan fara ni banason ya sake yin aure.”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un ai kuwa aure ki k’addara a ranki an riga an d’aura believe me idan da nine Afzal d’in wallahi tun auren naku na sati biyu zan kawo amaryata, wannan rashin hankalin da me yayi kama? Kina nufin for morethan five months yaron nan kullum siyan abinci yakeyi a waje? Where is my phone wallahi sena k’irga wa Daddy’nku.”
“Dan Allah Mummy kiyi hak’uri” ta fad’a da sauri tare da janye wayan kafin Mummy ta d’aga.
“Bani wayata sakariya kawai bani!”
“Mummy kiyi min rai wallahi Daddy yaji kasheni zeyi I’m sorry please don’t call him.” Fad’a sosai Mummy tayi mata Nazeefah se kuka, bayan nan tayi mata nasiha sannan ta tura ta gida.
Ta d’ayan 6angaren kuwa, Afzal tun fitansa ya zarce gidansu Amal acikin mota ta k’ariso ta samesa suka gaisa bayan d’an hiran da suka ta6a kad’an ya mik’a mata ledar.
“Toh kuma mey aciki Yaya?”
“Amsa ki duba” ba gardama ta bud’e thunderstrucked taga sabuwar waya pil aciki wayan da ko a mafarki bata ta6a kawowa kusa da tunanin ta zata rik’e irinshi a kwanakin kusa ba. Dan mamaki da murna ta ma kasa magana se chan baya ta shiga tambayansa dagaske wayan nata ne kode wasa yake mata. Godiya sosai tayi masa, sam ta kasa 6oye farin cikinta a rayuwa batasan ya zatayi ba idan ba Afzal yanzu shikenan zata nayin assignments nata cikin sauk’i ba seta je cafe ba ‘yan iskan samari nan suna bin mutum da kallo da kalamun soyayya. Sabon sim daya sai mata yasa mata a ciki ya nuna mata yadda zatayi charging wayar idan ta shiga ciki sannan ya mik’a mata ya kuma ce mata duk abinda bata gane ba she shoud feel free to call and ask him. Godiya mara adadi Amal ta tayi masa har zuwa lokacinda ya tafi. A hankali ya bud’e mata account a WhatsApp, Instagram da Snapchat dukda cewa ita bata wani damu da su bama, dama-dama WhatsApp d’inne take d’anyi dake anyi adding nata a group na ‘yan class nasu ta na kuma samun informative messages ta wajen.
A hankali a hankali kan Amal ke wayewa har ta soma amfani dasu snapchat tazo ta bud’e Twitter account da kanta, yarinya tana wayewa tana k’ara kyau da k’warjini. Tuni samari suka fara yi mata chaa sede dake tasan daraja da k’imarta kota kansu batayi duk wanda ya tsareta ce masa take akwai tambayan wani a kanta. A haka har suka shak’u da wata coursemate nata Maamah, yarinyar nada hankali sosai kuma ba k’aramin son Amal take ba. Suna da kud’i amman hakan besa ta rasa tarbiyya ba yawancin kullum suna tare da Amal. Bayan lectures ya k’are yau Amal ta shiga sauri don kar ta rasa keke napep kasancewar mai napep nata bai ji dad’i ba ta sanar da Afzal yazo ya d’auketa kuma tana ganin duk sasa aiki ne gara kawai ta tafi da kanta.
“Ya naga kaman kina hanzari yau lafiya?” Maamah data karanchi saurin da Amal keyi ta tambaya.
“Wallahi me napep d’ina ba lafiya gashi kinga yamma yayi banason in rasa abu hawa.”
“Toh ki bari mana idan Yaya na yazo d’aukana se muyi dropping naki ba a Jiddari kike ba? Kinga mu muna Polo layin duk d’aya ne.”
“How kind of you, but na gode karki damu I can manage.”
“No please Amal I insist dan Allah kibari mu sauk’eki yau.”
“Maamah da kin bari kawai I don’t want to he a burden.”
“C’mon karki damu kode tsoron Yayan nawa kike tun kafin ki gansa?”
“Kusan hakan” ta amsata tana jin kunya.
“Karki damu Yaya baida matsala muje mu zauna akan slabs d’incan yanzu ze zo” ba gardama suka k’arisa suka zauna bada dad’ewa ba sega 406 na yayan Maamah ya iso, k’arisawa tayi ta mishi bayanin situation d’in gladly yace ta kira Amal d’in suyi dropping nata. Gidan baya Amal ta shiga ta zauna had’e da gaishesa kanta a sauk’e, shiko tun da ta taso yake kallonta haka kawai ta mishi kyau dukda cewar bawai wani makeup take sanye dashi ba. Throughout the drive yake satan kallon Amal ta mirror har Maamah ta gane, ba yadda Amal batayi dashi ba ya sauk’eta a bakin junction zata k’arisa ciki da kanta amman yak’i sam wai se ya kaita har k’ofar gidansu hakan kuwa akayi, godiya tayi musu sosai da suka sauk’eta. Bata kaiga shiga gida ba se ga call na Afzal, bayan ta d’aga yake tambayarta ko tana school ne har yanzu shi sam baida labarin rashin lafiyan driver’n nata se yanzu da ya kira mutumin don jin koya sauk’e Amal.
“A’a yanzun na iso gida ko shiga ciki ma banyi ba.”
“Mesa baki kirani nazo na d’auke kiba?”
“Yaya I’m sorry amman naga kaman duk saka wahala ne tunda zan iya tahowa da kaina.”
“Ba fata ba amman idan aka sace min kefah?”
Dariya kad’an ta saki “Haba Yaya sekace yarinya, bale ma brother’n friend d’ina ne ya kawo ni sun rage min hanya.” Alokaci guda kawai yaji ransa ya 6aci yayinda wani irin zazzafan kishi ya mamaye masa zuciya. “Motan wani kika shiga?” Ya tambaya cike da 6acin rai da tsiwan daya mugun firgitar da Amal, sosai ta razana game da tsawan da ya daka mata.
“Yaya wan k’awata nefah” ta furta a hankali cike da tsoro.
“Meaning? Don wan k’awarki ne se akace ki shiga motanshi? Inda kuma bakinsu a had’e da k’awar naki suka yi miki wani abu fah? Ke bakisan ba a yarda da mutum so easily bane yanzu?” Ya k’ura ta.
“Yaya I’m sorr-” katse wayan ma yayi gabad’aya a kanta. Da mamaki ta sauk’e wayan daga kunnenta tana mamakin yadda ransa ya 6aci lokaci guda haka, tana iya rantsewa bata ta6- jin 6acin ransa ba se yau. Yau ta shiga uku ta 6ata wa Yayanta rai ita da tasan ransa ze 6aci haka dama bata sanar dashi gaskiyan lamarin ba kokuwa da bata amince ta shiga motan wan k’awar nata ba. Yanzu ta ina zata fara bashi hak’uri????
PAGE 1⃣3⃣
Da mamaki ta k’arasa ciki ta watsa ruwa taci abinci, dab bayan sallan Maghrib ta gwada kiran Afzal sede kamar yadda ta k’udurta a ranta haka mutuminku yak’i d’aukan wayan, sau biyu take kiransa ta regular line nasa amman yak’i d’agawa, private line nasa ta kira next. nan ma yak’i d’agawa dagangan dan kuwa wayan na a gefensa yana mik’e kan gado sede ya kalla ya cigaba da zura wa ceiling ido. Sak’o ta tura masa ta text message tana basa hak’uri nan ma yak’i reply bayan ya karanta. Duk da haka bata kariya ba, ta bisa whatsapp ta tura masa messages bil adad tana basa hak’uri tana kuka duk seya karanta ya kuma k’i reply abinda yafi ci mata rai kenan. Taya har ze karanta amman baze bata reply ba? Yau ina zata sa kanta? Assignments nata data d’ibo zatayi ma taji baza ta iya ba tsan-tsan tashin hankali.
Dab tazo kwanciya wajajen k’arfe goma na dare ta sake kiran lamban nasa sai da still Afzal yak’i d’agawa, ganin ba mahalicci se Allah kawai ta tofe addu’o’inta ta kwanta abinta duk da cewan ba baccin take ji ba, gabad’aya hankalinta yana kan halin da Afzal ke ciki. Ita da tasan hakan ze biyo baya wallahi da bata shiga motan Ya Abdul d’in bama tun farko.
Washegari lectures nata na safe na k’arewa tama driver’nta waya ya dawo da ita gida. Aldeb da zo6o me dad’in gaske ta d’au lokacinta ta had’a ta zuba masa a silver flasks nasa sannan ta tanadar wa Papi da Mami nasu a gefe. Wanka ta sakeyi ta canza kaya tasa matching color hijab ta feffeshe da turare sannan driver ya sauk’eta a office nasu Afzal. Tun da ta ga motansa a fake hankalinta ya d’an kwanta. Tana isa bakin office nasan a sama tayi knocking inda ya amsa da “Come in” a hankali ta bud’e ta shiga. Sosai mutuminku yayi murna da kuma mamakin ganinta amman ya dake a gun yana wani mozewa, kansa ya kawar tamkar ba mutum neba ya shigo office d’in had’e da cigaba da aikin dake gabansa. Ajiyar zuciya ta sauk’e ta k’arisa ciki ta zauna kan kujerar da ta saba zama a kai kullum tare da yin shiru.
Ganin be da niyyan yi mata magana na kusan tsawon minti biyu kawai se ta gaishesa “Yaya good afternoon” Yadda kuka san da kurma take magana haka yayi mata, ko kai be d’aga ba balle ya kalleta se rubuce-rubucen sa kawai yake.
“Yaya gaisuwan nawa ma bazaka amsa ba?” Ta tambayesa cikin kamala a hankali tamkar wacce take shirin yin kuka. “Yaya so kake ne ciwon zuciya ya kamani in mutu? Dan Allah kayi hak’uri” har anan be ce mata komi ba.
“Yaya I’m sorry, I’m so sorry” ta fad’a had’e da rik’e kunnuwanta yayinda idanunta suka soma cikowa da hawaye.
“Yaya yanzu se nayi kukan zaka mun magana?” Yanzu kam har hawayen sun soma d’iga sede har anan Afzal yak’i koda d’aga kai ne ya kalleta.
“Toh shikenan” tayi maganan tana share hawayenta “Bari in koma inda na fito tunda ko d’aga kai bazaka iyayi ba ka kalleni” ta ja hanci “Ga Aldeb da zo6o nan na kawo maka, I’m still saying sorry” tana kaiwa nan ta mik’e, bata kai ga taka k’afarta ba Afzal ya mik’a hannu ya rik’e hijabinta, chak ta tsaya gun ba tare da tace komi ba se faman kukanta take a hankali.
“Don’t go” yace da ita a hankali dad’i sosai taji amman ta fake itama “Ni ka sake mun hijabi.”
“Nace ki tsaya” ya nanata cikin tattausar murya. Juyowa tayi tana kallonsa yayinda hawaye ke d’igowa sama-sama daga idanunta. “Bayan tun jiya ina baka hak’uri kak’i kulani bale ka hak’ura ni ka sakeni inyi tafiya ta dama tun ba yau ba na gano ba ka sona.”
“I’m sorry toh zauna kin ji?” Ya ce da ita a hankali.
“Nifa tafiya ta zanyi ka sakeni kurum.”
“Lily nace ki zauna.”
“Toh haka akeyi ne?” Ta tambayesa had’e da turo d’an bakinta. “Ko baccin kirki na kasa yi jiya, I called and texted you severally sarai kana gani kak’i responding d’ina, Wallahi if only ka san yadda hankali na ya…” ba se kawai ta rushe mishi da kuka ba. Yana tayi shiru tayi shiru kar ta tara masa jama’a amman inaa tak’i jinsa, se kukarta take harda me sauti. A haka ne har PA’n Afzal ta lek’o take tambayan ko lafiya. “Lafiya Blessing don’t mind her kukan banza take” yace da PA’n sannan ya samu ta ja musu k’ofan ta fice.
“Yanzu Lily ni ke miki magana amman bakiya ji? In ce miki kiyi shiru kik’i yi? Se kin tara mun duka mutanen office d’in tukuna zaki ji dad’i?” Itama yadda kuka san bada ita yake ba, se aikin kukanta take harma tana k’ara sautin, gaban hijabinta ko lis ta jik’asa da hawaye. “Toh kiyi hak’uri, yi hak’uri kibar kukan haka” ya soma pampering nata yana bata hak’uri.
“O’o ba tun jiya nake baka hak’uri ba kak’i ji na.”
“Toh ba ya wuce ba?”
“Ni seka cemin ka hak’ura tukuna” ta fad’a tana zum6uro baki yayinda ta 6oye kusan rabin fuskarta k’ark’ashin hijabinta.
“I’ll think about it keep quiet first.”
“O’o ni seka ce ka hak’ura” ta sake sa wani kukan sanin sarai ya tsani hayaniya.
“My Goodness!” Ya furta cike da tashin hankali yana susa temple nasa. “Da gan-gan kike ko?”
“Ni se kace ka hak’ura” ta kuma sa wani kukan.
“Fine! Naji na hak’ura shikenan kiyi shiru.”
“Ka hak’ura dagaske? Bazaka sake ignoring calls d’ina ba?” Se anan ta ciro fuskan nata gabad’ai tana kallonsa. Ba k’aramin dariya ba reaction na fuskarta yasanya sa da k’yar ya had’iye dariyan ya gyad’a mata kai “Bazan sake ba” ya sanar da ita.
Se anan taji sanyi a ranta ta shiga share hawayenta, hannu ya cusa a aljihunsa ya ciro hanky ya mik’a mata. Ba gardama ta amsa ta share hawayen nata dashi bayan da ta gama ta mayar mishi ya amsa ya mayar cikin aljihunsa.
“Wato taurin kan nan namu na nan har yanzu ko?”
“Wani taurin kai kuma Yaya?” Ta tambayesa tamkar bata fahimci abinda yake nufi ba.
“Baki na nawa ina ce miki kiyi shiru amman ki k’i yi?”
“Toh ba kaine ba, inata baka hak’uri amman kaki hak’ura.”
“Toh ai kece kika janyo.”
“Kawai don na shiga motan wan k’awata? Believe me da nasan hakan ze 6ata maka rai wallahi bazan soma ba.”
“Na ji and I’m sorry for making you worried and restless jiya but on a serious note bana son in sake jin kin shiga motan wani Lily, komin ya situation d’in yake kuwa, duk randa driver’n ki bashida lafiya call me up and let me know if I’m too busy to come pick you up zan tura driver’n office kona gida yaje ya d’auko ki banason in sake jin kin shiga motan wani, kinji?”
“Na’am Yaya, in shaa Allah anyi na farko anyi na k’arshe.”
“Masha Allah that’s my Lily.”
“Amma Yaya, Maamah is my very good friend bana tsammanin har zata iya cutar dani. I trust her.”
“Ni bance miki Maaman ne ban yarda da ita ba wan nata ne ban yarda dashi ba.”
“Toh amma-“
“Lily enough, nide na fad’a miki in ba wai fad’a kikeso muyi ba toh karki sake shiga motanshi ko na wani banda nawa kinji?”
“Naji Yaya” ta amsa tana mamakin iko irin na Afzal lallai wannan da ace yana da k’anne da sun taso da discipline don ba k’arya yayi kalan yayun dake jibgan k’annensu idan suka tafka rashin hankali.
“Ya lectures toh?” Yayi maganan yana janyo cup a saman fridge nasa don tsiyaye Aldeb d’in. “Kawo in tsiyaya maka” tayi maganan tana k’ok’arin amsan cup d’in “Lectures Alhamdulillah amma ba dad’i mutun kullum 7 ya fita sekace d’an secondary school.”
“Lol toh me maraban ki da ‘yan secondary school d’in?”
“Yaya wallahi akwai difference.”
“Toh big girl naji” yayi maganan yana amsan cup d’in “Thank you” yace da ita.
“You’re welcome” chan tace, “Ba kace yayi dad’i ba” tare da had’e gira.
“Ina santi ze bar ni in fad’a? Rabonki da ki kawo mun Aldeb har na manta.”
“Forgive me Yaya daga yanzu kam zanyi k’ok’ari koda once in a week ne ina kawo maka.”
“Keda kike school yanzu? Don’t bother.”
“When it comes to my Yaya komin yaya ne se an mishi abinda yakeso so kar ka damu.”
“Hakane?” Ya tambaya yana me jin dad’in amsan data basa.
“Sosai ma kuwa.”
“Toh shikenan thank you.”
“You’re welcome, I guess I can go now, kaima ka samu ka kammala aikin dake gabanka, zani gida inje inci abinci yunwa nakeji.”
“Let’s eat out it’s almost lunch time” yayi maganan yana duban agogonsa. Ba musu ta jirasa ya d’an k’imtsa kan table nasan sannan suka wuce restor suka ci abinci, bayan sun gama ci ya sauk’eta a gida sannan ya komo office.
****
A kwana a tashi be ragar da komi ba se gashi yau su Amal suna rubuta first semester exams nasu. A gida kuwa ta fannin Nazeefah da Afzal suna nan kaman kayan wanki ba cigaban komi, don koda tace wa Mummy kan zata fara yiwa Afzal girki koda wasa bata ta6ayi ba, ko tace zatayi se wata ra’ayin ta hanata ta hura mata kai kan cewa ai yanzu da zaran ta fara yi masa girki ze ga kaman sonsa take tana son su shirya kar tayi, itako seta biye wa ra’ayin. Amma se de bataji Afzal na waya da Amal ba, se zuciyarta tayi mata k’ona, zama take ta gabzi kukanta ta godewa Allah a hakan kuma ta tsaya tana cewa ita ba son Afzal take ba.
****
Amal da Maamah ne ke zaune akan slabs suna karatun paper’nsu na gobe Maamah ta fara janta da hira.
“Friendy?” Ta kirata.
“Na’am” Amal ta amsa cike da fara’a.
“Har yanzu fa baki bani amsa ba wallahi Ya Abdul ya tak’ura min.”
“Nikam kibar zancen can Maamah muyi karatu” Janye handout d’in Maamah tayi. “Ha’a! Ya da haka?” Amal ta tambaya tana k’ura mata ido.
“Wallahi yau kam sekin bani amsa haba mana friendy yanzu kodan k’awancan dake tsakaninmu ma baza ki bawa Ya Abdul dama ba? Wallahi he’s a very cool and gentleman if you get to know him, baida matsala sam.”
“Na sani Maamah bazaki gane bane.”
“Mey ne bazan gane d’inba? Kede kawai kice kin k’i min Ya Abdul kuma shikenan na gode ni kika k’i ba shi ba wallahi.”
“Wallahi ba haka bane don Allah karkiyi magana haka.”
“Ya kikeson inyi toh? Yaya na fa kikayi rejecting tun yaushe nake k’ok’arin shawo kanki amman ko lambarki kin hana in basa wallahi ko baccin arziki Ya Abdul bai samu kwana biyun nan as kullum tunanin ki yake tun kan ranan daya rage miki hanya har izuwa shekaran jiya da ya kaimu Unimaid garden.”
“Ji k’arya wai ko bacci baya iyayi a d’akinsa kike kwana ne da zaki san hakan?”
“Eh yimin wayo ki canza topic d’in” Maamah ta fad’a tana juya mata ido.
“Lol yi hak’uri toh.”
“Nide ba hak’urin da zanyi sekin amince in bawa Ya Abdul numbanki.”
“Ke dad’i na dake naci wallahi kibari mana mu gama karatun tukuna gobe ne fa exams d’in.”
“Friendy seconds nawa ne ze d’auke ki kice ‘ki bashi’ kawai? Wallahi rashin mutunci ba kyau.”
“Nikam kode biyanki Ya Abdul yayi ne? Dagewan naki fa yayi yawa.”
“Wallahi sam ba haka bane, you’re just the perfect girl for him wallahi tun da nasan Ya Abdul ‘yan mata biyu ya ta6a yi ta farkon har sun fara zancen aure Allah yayi mata rasuwa se kuma ta biyun sunyi nisa itama yazo ya gane tana son abokinsa se suka rabu daga baya tayi-tayi ta dawo mishi amman ina he’s already heartbroken.”
“Allah sarki Allah ya jik’an ran musulmi.”
“Ameen” ta amsa, “Kuma kinga kusan wata shida kenan da faruwan hakan ban sake jin yana neman wata ba se daya kafa idanunsa akanki Wallahi he’s intentions to you are clear.”
“Na ji kuma na gamsu Maamah kawai ina ganin this’s not the right time for me to be in a relationship ne kiga part one fa kawai nake I have almost 5 years to go Ya Abdul baze iya jira na ba.”
“Wallahi ze iya, he is willing to wait till forever for you.”
“Hmm” ta numfasa.
“Kode kam Yayan nawa be miki bane? Yayi muni dayawa ko?”
“Haba ai kema kinsan yana da kyau wallahi gashi chocolate skinned, ga saje ga ido kaman naki a nan.”
“Yana da kyau kenan?”
“Eh mana” ta amsa without knowing when “I mean ni ba ruwana ki rufa min asiri kiban handout d’ina” ta shiga canza zancen.
“Amal pleasee ki amince pleasee wallahi ko na basa lamban naki baze kiraki ba se mun gama exams shi da bakinsa ya cemun haka.”
“Toh naji ba se kin cinye ni ba ki bashi shikenan?”
“Yeyyyyy!!” tasa ihu had’e da hugging d’in Amal wane wacce ke neman suffocating nata.
“Toh nikam sakeni haka mu k’arisa karatun nan kinga har Azahar ya doso.” Handout natan ta mayar mata suka cigaba da karatu suna iddawa sukaje sukayi sallah sannan kowacce tayi hanyan gida. Kamar yadda Ya Abdul ya d’au alk’awari, seda su Amal suka kammala exams bayan kwana biyu ya buga mata waya, lokacin tana zaune tsakar gida tana bita wayan ya shigo. Ganin new number yasa bata d’aga da wuri ba seda ya kusan tsinkewa. Shiru tayi da ta d’agan chan daga d’ayan 6angaren taji bak’on murya nayi mata sallama. Cikin sark’ak’k’iyar muryarta me sanyi ta amsa da “Wa’alaikumus salam wa rahmatullah.”
“Amal ya kike?” Sama-sama suka gaisa dake har yanzu bata fahimci wake magana ba. “Baki gane muryan bako har yanzu?”
“Eh wallahi I’m sorry.”
“Abdul Rahman ne” ya sanar da ita.
“Abdul Rahman daga ina kenan?”
Murmusawa yayi kad’an sannan yace, “Ya Abdul toh” se yanzu ta fahimta ashe de Abdul Rahman ne complete name nasa, wow. “Laa! Ya Abdul ina yini?”
“Bayan wuyan da kika bani har kin manta dani ko?”
“Haba Ya Abdul ina na isa.”
“Gashi kuwa.”
“A’a wallahi kullum da Ya Abdul Maamah ke addressing naka bata ta6a ambaton full name naka ba kaga ko bazeyi in gane wanene ba at first thought” ta mar bayani a hankali.
“You’re right so ya hutu?”
“Hutu Alhamdulillah ya aiki?”
“Lafiya k’alau kun gama exams ko?”
“Eh wallahi.”
“Toh Allah ya bada sa’a.”
“Ameen thank you.”
“I thought I should call and check up on you.”
“Ayyah to nagode sosai a gaishe da gida.”
“Zasuji take care” a haka sukayi sallama. “Phew!” Ta numfasa had’e da ajiye wayan a gefe sannan ta cigaba da karatunta. Tun daga ranan Ya Abdul ke kiran Amal suna gaisawa, kar kuma kuyi tsammanin irin kira barkatai ba fasali d’innan ne, no a sati befi suyi waya sau biyu ba idan yayi yawa shine sau uku ko hud’u. A hankali shak’uwa ya fara shiga tsakaninsu ba abinda ke burge Amal a gun Ya Abdul kaman yadda yake yawan sanyata dariya, sede basuyi waya ba koda ranta a 6ace ne seya faranta mata da kalamun sanya dariyansa, he’s so jovial Maamah batayi k’arya ba da tace bashida matsala. A satin da zasu koma makaranta ne yayi insisting se ya zo sun had’u mutumiyarku da shegen tsoro kam ba se ta shiga yi masa corner-corner ba. Yau tace zata islamiyya, gobe tace zata raka Mami gidan suna ko makamancin haka daga k’arshe de ya gane tsoro take ta ke6e dashi shi kad’ai kuma bega laifinta ba hasali ma yaba mata yayi sosai hakan na nufin tasan abinda takeyi ne. Don haka ya tambayeta idan ze taho da Maamah zata amince ta fito? Tuni ta amince. Hakan ko suka shirya ranar Laraba da yamma se gashi da Maamah sun k’ariso gidansu, har ciki Maamah ta shiga suka gaisa dasu Mami sannan suka fito da Amal inda Amal ta zauna a gidan gaba ita kuma ta koma baya. Bayan gaisuwa suka sha hira sosai dukansu ukun cikin motan, se dariya Ya Abdul yake sanya su barin ma Amal dake dariya harda k’walla, kusan k’arfe shida Ya Abdul yace ya kamata su tafi, don dad’in hira Amal ji take kaman kada su tafi. Dab tazo sauk’a daga motan kenan ya mik’a mata wata leda, ta kar6a ita kuwa tak’i ba yadda beyi ba amman tak’i, daga k’arshe seda ya baiwa Maamah ta shigar mata dashi ciki har cikin d’akinta.
**** Bayan ta dawo ciki ta wuce d’akinta ta fito da ledar, zazzagewan da zatayi ta tarar da chocolates turum, ba wanda babu aciki da wanda Afzal ya koya mata ci da wanda se yau ma ta ta6a ganinsu, abu de yayi kyau. Haka nan ta 6oye abinta cikin akwati tana ci a hankali a hankali. Bayan sallan Isha ta kira Ya Abdul tayi masa godiya inda suka sake ta6a hira kad’an sannan sukayi sallama. Ganin goma be cika ba ta yi tunanin kiran Afzal da alama aiki yayi zafi ne ko nemanta bayya yi kwana biyu, daman yayi tafiya zuwa Lagos for a meeting, yau k’imanin kwana biyu zuwa uku kenan. Tana kiransa on the first ring ya d’aga, “Yaya kayi wuyan gani” ta soma cewa.
“Wallahi Lily, I’ve been so busy ko time na wayan ma bani dashi.”
“Allah sarki ya kake ya aikin?”
“Alhamdulillah ya gida dasu Mami?”
“Lafiyansu k’alau d’azu take cewa kwana biyu bata ji motsinka ba nace ai kayi tafiya, she’s sending her warm greetings so as Papi.”
“Toh ayya ina amsawa.”
“Yaya I miss you yaushe zaka dawo?”
“Saturday in shaa Allah.”
“Toh Allah kaimu barin barka haka nasan a gaje kake.”
“Alright Lily thank you have a peaceful night rest.”
“You too, seda safe” da haka sukayi sallama.
****
Nazeefah ce zaune gaban Tv ta sa channel na Zee world tana kallon wata indian series se faman buga tsaki take, ga takaicin rainin wayon da ake tayi a series d’in ga na rashin Afzal kwana biyun da tayi bata sanyasa a ido ba bata kuma ji muryansa ba, ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba, se a yanzun take sake jaddada cewa lallai-lallai ta fad’a kogin sonsa. Seta d’au wayarta zata kirasa seta kashe ta fasa, tayi hakan sau fiye da a k’irga. Daga k’arshe de ta dage ta kira har ya shiga yana ringing, se cewa kanta take ai don ya sanar dani zeyi tafiya ne yasa zan kirasa, da ace tafiyansa kawai ya kama yayi wallahi ko ta kansa bazan yi ba bale har in kirasa.
Ya kusan tsinkewa ya d’aga kasancewar har ya fara bacci. Shiru tayi bayan da ya d’agan kaman yadda shima yayi shiru yana jiran ta soma magana dukda cewan yayi mamakin ganin kirarta amman dake yasan halin matar nasa, tunaninsa gabad’aya yayi kan ko so take ta sanar dashi kud’inta ya k’are ne ya hankad’o mata wasu.
Ganin ba mahalicci se Allah mutumiyarku tayi gyaran murya had’e da cewa “Halo?”
“Yes?” Ya amsa cikin sleepy husky like voice nasa. Rasa na cewa ma tayi, tace ya isa lafiya ne? Toh ai tun shekaran jiya yayi tafiyar chan de ta gaishe sa kawai “Ina yini?”
“Lafiya” ya amsa casually, “Ya kike?”
“Lafiya k’alau ya aiki?”
“Alhamdulillah.”
“Dama nace in ji ko kana lafiya.”
“Toh thank you I’m good ba wata matsala dai ko?”
“Babu.”
“Toh yayi kyau.”
“Nace gobe zan fita gidan k’awata, ina neman uzuri.”
“Kikace?” Afzal da mamaki ya rufesa ya tambaya tun yana a mik’e akan gadon nasa har ya tashi ya zauna besani ba, kode gizo kunnensa ke masa ne? Har Nazeefah ce zata kira waya ta gaishesa musamman don ta tambayesa izini? Lallai yau za ayi ruwan mutane.
“Nace zani gidan k’awata gobe, am I permitted?”
“Sure you’re, kikaje ki gaisheta.”
“Toh seda safe.”
“Yauwa Allah tashe mu” da haka sukayi sallama. “Phewww!” Ta sauk’e ajiyar zuciya yayinda shima yayi haka ta d’ayan 6angaren. Afzal yana mey mamakin anya kuwa wannan Nazeefah ce yayin da ita kanta take tambayar kanta anya kuwa itace??
Ranan da Afzal ze dawo ne Nazeefah ta fad’a cikin kan zata mai girki sede da zaran ta motsa d’auko tukunya se wata ra’ayin ta hanata kan cewa har na me zata masa girki? Ai seya d’au sonsa take, yayinda wata ra’ayin ke ce mata mey aciki don tayiwa mijijta girki, besides ma ai ya sanar da ita ranan da ze dawo. Haka dey tayi nan tayi chan daga k’arshe girkin da ba azo anyi ba kenan. Haka nan ya dawo gidan dry ta nad’e k’afa a kan kujera tana kallo. Sannu da zuwa kad’ai ta masa ya amsa ya wuce d’akinsa. Yana watsa ruwa ya canza kaya ya fito se buga k’amshi yake, ko bata tambaya ba tasan gidansu Amal ze wuce. Wani irin zazzafan kishi ne ya tokareta ji take kaman ta rik’o k’afarsa ta hanasa fitan.
Da ta zauna tayi nazari kuma se taga ai duk laifinta ne da ace ta dafa masa abinci da sede tace yaje dining yaci hakan baze ma samu daman fita ba. Holy sh*t.
Kaman Nazeefah ta sani gidansu Amal direct Afzal ya wuce inda aka shirya masa abinci kala-kala ga smoothies d’innan ba wanda Amal bata had’a ba su Ginger ne, zo6o da kuma Aldeb nasa. Sosai ya ji dad’i, dalilin da ya hanasa cin abinci kenan through out yau saboda yasan Amal bazata taresa da dry hannu ba. Zama yayi ya gabza abincin sosai har ya buk’aci a sa masa ragowar a kula ya tafi dashi gida. Amal se dariya take tana neman tsokanansa tana kiransa glutton. Da yazo tafiya ne ya ciro masu tsarabar laces daya musu ita da Mami.
****
Haka nan tafiya ta cigaba har hutun su Amal ya k’are suka shiga second semester. Ita da Ya Abdul fa se abinda yayi gaba shi de har yanzu be furta mata kalamun so ba, but with the way he’s being so extra ita kanta Amal tasan relationship nasu ya tashi daga friendship ya koma wani abun daban. A rana se suyi waya sau biyu zuwa uku, har Mami ta fara sa mata ido tana zata k’wace wayan idan batayi hankali ba. Ana nan ana nan kwatsam rana d’aya Ya Abdul ya fad’awa Amal abinda ya juma yake son sanar da ita kan yana sonta, so kuma na aure. A wannan lokaci itama Amal ba k’arya ta fad’a kogin sonsa, saboda ko be kirata a waya ba, ita zata d’au wayarta ta kirasa. Tunda ya furta mata wannan kalamu ta daina d’aga wayansa ko message ya mata bata responding, ba k’aramin tashin hankali ta sanya sa ciki ba gabad’aya ya rasa meke masa dad’i. Gun k’anwarsa Maamah ya nufa yayi mata bayanin abinda ke faruwa kan dan Allah ta taimaka masa. Kwantar mai da hankali tayi ta kuma tabbatar masa da cewa in shaa Allah Amal ta sa ce saboda ita ta riga ta gane Amal na sonsa. Washegari ko school Amal tak’i fita sanin the moment ta fita zasu had’u da Maamah itako zata kira Ya Abdul ta had’asu don haka ta fake a gida da cewan cikinta na ciwo.
Da misalin k’arfe goma Afzal ya kirata bayan sun gaisa yake tambayarta lectures take ce mai bata ji dad’i ba yau tana gida amman da sauk’i yanzu haka. “Se yau za’a same ki kenan Lily” yace da ita afterwards.
“Kamar ya Yaya?” Ta tambayesa cike da rashin fahimta.
“Throughout last week koda na kiraki kullum line busy nakeji wa muka samu haka?”
“Kai Yaya ba kowa fa idan ka kira kaji line busy to da da Maamah nake waya.”
“Anya kuwa Lily?”
“Dagaske Yaya.”
“Toh shikenan Allah k’ara sauk’i.”
“Ameen thank you.” Da haka sukayi sallama bata kaiga ajiye wayan ba se ga call na Ya Abdul kaman wacce bazata d’aga ba seda call d’in ya kusa tsinkewa ta d’aga had’e da yin shiru.
“Alhamdulillah” ta ji ya furta “Amal?” Shiru tayi “Amal kuma bazaki amsa ba?”
“Ina kwana?” Ta gaishesa a hankali.
LAmal mey nayi da zan fuskanci wannan hukunci daga gareki? Don’t you think hukuncin nan naki yamin tsauri dayawa?”
“I’m sorry.”
“Amal in sona ne bazaki iya yi ba you could have simply told me, I was worried sick about you gashi yau ko school kin k’i fita duk don gudun karki had’u da ni ne?”
“Nifa ba haka bane, cikina ne yake ciwo.”
“Why do I feel like you’re lying?”
“I’m sorry” haka kawai ta tsinci kanta tana basa hak’uri ba gaira ba dalili ko de don ita kanta tasan abinda tayi masa bata kyauta masa bane?
“Look I take back what I said to you kinji? Na gane you can’t love me back but please karki 6ata friendship dake tsakanin mu I cherish our friendship alot Amal.”
“Ya Abdul ka dena magana haka.”
“Toh ya kikeson inyi Amal? Haka kawai kika dena recieving calls d’ina kina ignoring d’ina anyhow.”
“I’m sorry.”
“It’s okay abu d’aya nakeson tambayanki Amal please give me a sincere answer.”
“What is it?”
“Who’s the lucky guy da ya rigani sace zuciyarki? I’m sure this’s all about him.”
“Wallahi ba kowa Ya Abdul I just need some space.”
“You mean I still have hope?”
“In zaka iya jira” ta amsa bayan tsawon lokacin da ta d’auka.
“Amal I’m ready to wait for eternity for you, Amal ba zaki gane irin soyayyan da nake miki ba, it’s been long since I felt this. Amal out of the blue kika sace min zuciya, I love and adore everything about you and I’m willing to wait for you for as how long it takes until you’re ready. Amal I love you.”
“Ya Abdul…” se kuma tayi shiru.
Yes Amal I love you and am not ashamed of it ko a gaban waye zan fad’a, I love you Amal.”
“Thank you Ya Abdul.”
“Gobe ki fita school kinji?”
“Ni banida lafiya” ta fad’a stubbornly.
“Haba beautiful? Duk don gudun kar inzo d’aukan Maamah mu had’u ne? Ki kwantar da hankalinki ni gobe ma zanyi tafiya.”
“Tafiya kuma Ya Abdul?” Alokaci d’aya se taji kuma tana missing nasa.
“Ba abinda kikeso ba kenan.”
“A’a fa ni bance ba.”
“Toh zaki fita school gobe inzo in kun tashi?”
“Eh kazo.”
Does this means you missed me too?”
“Ya Abdul yes, I missed you” ta amsa cuke da kunya ita kad’ai ce a d’akin amman tana kare fuskarta da pillow.
“Wow!” Yayi exclaiming cike da murna da farin ciki “That’s my girl, I miss you even more, so se na zo ko?”
“Toh Allah kaimu”
“Ameen, you take care okay? I love you.”
You take care too” da haka ta karse wayar tare da rungume ta. Haka kawai ta tsinci kanta tana murmushi ita kad’anta there’s no denying itama tana son Ya Abdul halan fiye da yadda yake jin yana sonta ma kawai de as a lady her ego comes before her feelings.
*****
Mu kwana mu tashi be ragar da komi ba, haka tun Amal tana 6oyewa Ya Abdul soyayyarta ta shiga nunawa, haka zata la6e a d’aki kaman tana bacci amman waya take. A school kuwa yawancin in sun fita break shima Ya Abdul seya kar6i excuse a office ya fito su had’u su sha firarsu. Afzal kuwa kasancewar ya samu cigaba a office, daga Assistant manager ya koma manager sam baya samun zama kullum cikin aiki yake da tafiye-tafiye hakan ya bawa Amal da Ya Abdul daman sake shak’uwa sosai.
Yau bayan juma’a Amal na karanta suratu Kahf wayarta ya shiga ruri dubawan da zatayi taga Afzal ke kira, wai wata sabon gani. D’agawa tayi take had’e da cewa, “Yau Yaya ya tuna dani kenan.”
“In ban tuna dake ba ai ke bakida niyyan kira na.”
“Inji wa Yaya? Wallahi kullum kana raina banason tak’ura maka da kira ne saboda naga kaman aiki na maka yawa yanzu.”
“Toh ya kike?”
“I’m fine just that am missing you.”
“I miss you too Lily ya school?”
“School lafiya k’alau.”
“Ki fito ina bakin k’ofa.” Dum taji zuciyarta ta buga a tunaninta gabad’aya Afzal baya gari ne, dan kuwa yanzun sukayi waya da Ya Abdul yace mata yana tahowa ya zatayi idan yazo ya iskesu da Afzal? Yau nata ya k’are me hana afzal kurara ta se Allah motan wani kawai ta shiga seda ya kusan cinyeta bale ace har ta kawo saurayi gida?
“Halo Lily? Fitowan ne baza kiyi ba sena k’ariso ciki da kaina?”
“A’a Yaya gani nan fitowa” daga nan ta ajiye wayan. Zagin kanta ta shiga yi, meyasa bata ce masa bata gida ba? Sede sarai tasan halinsa yana iya cewa bari ya k’ariso su gaisa da Mami, daga nan kuma Mami ta fallasheta. Numban Ya Abdul ta kira take don sanar dashi kar yazo yanzu ya bari se anjima zata fita sede kash two missed calls ta masa amman bai kusa. Yau akeyinta! Ta furta a ranta.
Qur’anin ta mayar mazauninsa ta d’an shafa powder da jan baki taja hijabinta ta sanya ta d’an feffeshe da turare sannan ta fice. Tun da ta fito Afzal dake zaune cikin motansa yake binta da kallo yayinda ya tsinci kansa cikin wani irin walwala da farin ciki maras misaltuwa. Se gani yake kaman yau ya fara sanya ta a idanunsa, tana k’arisawa cikin motan k’amshin turarenta ya mamaye ciki. “Kyau kenan Lily?” Ya ce da ita yana murmushi sosai.
“Kai Yaya” ta amsa tana kare fuskanta da hijabin nata “Dan Allah ka dena sani jin kunyanka.”
“Ai kuwa sede ki dunga cin kunyan nawa don bazan fasa fad’a miki kinyi kyau ba Lily.”
“Toh ai kaima kayi kyau in fact kullum ma cikin baza kyau kake.”
“Hakane?”
“Sosai ma Yaya.”
“Toh tsaya in d’aukeki hoto.”
“Yaya wai kai se mutum yayi muni zaka ce zaka mai hoto?”
“Kika sake cewa kinyi muni zamuyi fad’a.”
“Toh na dena amman d-” flash na cameran daya haskata ne y rufa mata baki. “Haba mana Yaya!”
“Tsaya mana kiga kinyi kyau” tsayawan tayi ya nuna mata se kuma taga batayi muni ba “See? I told you tsaya mu k’ara miki d’aya.” Daidaita zamanta tayi daram tayi posing yayin da ya haska mata flash ras ta fito ta kuma yi bala’in kyau.
“Toh saura kai, kaima ka tsaya a d’aukeka.”
“Ce miki akayi maza suna hoto?”
“Yimin yanga de Yaya” ta kai ga d’aukan wayanta a inda ta ajiye kenan sega Ya Abdul na kira kafin tace zata janye inaa har idon Afzal sun karance mishi sunan wanda ke kira as
“LOML❤🔐” meaning ‘Love Of My Life’ danqaree! Ba zuciyan Amal kad’ai bane ya buga harta na Afzal, infact nasa ma yafi nata tsinkewa take wajen yaji jikinsa yayi sanyi lissss. A hankali ta janye wayan, yadda ta kasa d’agawa haka ta kasa katsewa ta bari se ringing yake, yana tsinkewa Ya Abdul ya shiga kira again se a karo na biyu ne ta katse.
“Mey na katsewa kuma?” Afzal ya tambayeta yana me k’ok’arin 6oye kishi, k’unci da bak’in cikin da ya fad’a aciki.
“Ba important call bane” ta fad’a a hankali, gabad’aya kunya yabi ya mamayeta ba haka taso sanar da Afzal batun Ya Abdul ba.
“Love of our live yana kira kice ba important call ba Lily?”
“Yaya please-” tana cikin maganan ne Ya Abdul ya shiga kira again bata kaiga katsewa ba Afzal yace, “You’re excused, jeki amsa ina jiranki.”
“Yaya I can call him back later.”
“Ni nace ai kije Lily kar ki damu” kallonsa tayi one last time sannan ta sauk’a daga motan ta ke6e gefe guda. Afzal da yake ji tamkar na lahira ma yafisa jin dad’i besan lokacinda ya tada motan ba ya fice a guje ji kawai Amal tayi iska ya wuceta, juyawan da zatayi taga motan Afzal ne bata san lokacinda ta bawa Ya Abdul hak’uri akan anjima zasuyi magana ba ta katse wayar.
Yau kashinta ya bushe!
PAGE 1⃣4⃣
Tuk’in ganganci Afzal ke wane wanda ke shirin afka hatsari da gan-gan, ikon Allah ne kawai ya kaisa gida nan ma da yayi parking ya fito ko ta kan motan beyi ba bale ya zara key har ya rufe k’ofar, a wangale ya barota ya k’ariso ciki. Yana bankad’e k’ofan ciki se ga Nazeefah a shirye tsaf da alama ma fita take shirin yi.
“Yauwa Afzal zani suna ina buk’atan 5k” ta tambayesa ba tare da ta karanci halin da yake ciki ba, don 6acin rai Afzal ko kallonta beyi ba bale ma ya amsata, yazo wuceta kenan ta kira sunansa “Afzal magana fa nake.”
“Nace bani da shi!” ya sanar da ita a tsawa ce. Ranta ne ya mugun 6aci dan rainin hankali banzan 5k ne ze tsaya yana mata walak’anci akai? Ai ba wai ta rasa 5k d’in bane itama kawai de don tana neman k’ari ne, ma ba laifinsa bane ita ta tambaya. “Wallahi kama kanka izinin ma na fasa tambaya” tace dashi yana cikin tafiyar.
“Karki tambayan kuma dan Allah in kin fitan karki sake tako k’afarki gidan nan aikin banza kawai” yana kaiwa nan ya wuce d’akinsa bang! Taji yayi banging k’ofar kad’an ya rage bata ci tuntu6e ba don yadda ta firgita.
Anya kuwa lafiya? ta tambayi kanta. K’arisawa waje tayi garin fito da motarta daga parking lot taga k’ofan motan Afzal a bud’e, lek’awan da zatayi taga motar ma a kunne ya barta nan ne ta tabbatar da cewa lallai-lallai something went wrong somewhere. Key’n ta zara ta kashe motan ta dawo ciki ta ajiye mai sannan tayi ficewarta.
Tun shigansa ciki ya fad’a kan gado ya kwanta can anjima ya mik’e ya shiga zagaya d’akin yayi nan yayi chan ba tunanin da be yi ba akan Amal da wannan mutumin da yaga tayi saving lambansa as ‘LOMLgabad’aya ya rasa meke masa dad’i. Hannunsa da ya d’aga kawai yakai jikin bango, blow ya rink’a kai wa bangon yadda kuka san baya jin zafin a jikinsa, kafin ace me hannun nasa duk ya faffashe yana yoyon jini, ana cikin haka ne wayansa dake aljihunsa ya soma ruri, be damu ya cie bale ma ya duba wa ke kira ba se a karo na biyu. Ganin Amal ke kira kawai yaji zuciyansa ya sake 6aci yayin da ya shiga tafasa yana masa wani irin k’ona wurgi yayi da wayar seda ta rugurguje a k’asa (Allah sarki iphone 7) sauk’a har k’asa yayi yana wani irin kakkarwa. Mutum na iya rantsewa aljanu ne suke aiki a kansa. Idonsa ya rufe gam bud’ewan da zeyi sega hawaye na tsiyaya. Yau ran maza ya 6aci! Yafi minti goma durk’ushe a wajen, jini se tsiyaya yake daga hannun nasa, a takaice de yayi staining kan tiles d’in gabad’aya. Daga bisani ya mik’e ya shiga bayi ya bud’e tap tare da sa hannunsa k’ark’ashin running water d’in. Kun de san yadda sabon ciwo ke rad’ad’i idan ruwa ya ta6a toh k’una da rad’ad’in da zuciyan Afzal keyi masa kwatankwacin hakan ne. Bayan da ya wanke ciwon ne ya rage kayan jikinsa ya watsa ruwa sannan ya fito yayi dressing hannun nasa ya mik’e a kan gado.
Ta fannin Amal kuwa hauka ne kawai batayi ba layin nasa ta cigaba da kira ammana inaa se switched off yake ta cemata, private number’nsa da take kira shima switched off ke cewa dake layin a kashe ne. Gabad’aya ta rasa me ke mata dad’i, ashe da tun farko ta sanar da Afzal d’in batun Ya Abdul, a ganinta da abubuwa bazasu cha6e haka ba dan kuwa ita ko da wasa bata kawo a ranta wai kishinta Afzal yake ba, a nata tunanin ta d’au kawai he’s being over protective of her ne as her big bro. Ta d’au wai haushi Afzal yaji saboda bata sanar dashi kan cewa wani ya nemeta ba har sun daidaita, little did she know shi kansa Afzal d’in sonta yake. Har dare yayi har washegari bata fasa kiran layin nasa amman inaa se switched off yake ce mata, bayan data tashi daga school yau ta biya ta office nasa sede da mamaki securities suka ce mata ai be fito aiki ba yau kwata-kwata akan bey ji dad’in jikinsa ba. Wani sabon tashin hankalin ta fad’a, mey ke damun sa? Shin jikin yayi tsanani ne kokuwa? An rik’eshi a asibiti ne kokuwa yana jinya a gida? She needs to find out. Sede kamar yadda bata san gidansa ba haka kuma bata san gidansu ba balantana taje gun Ummi taji meke faruwa. Office nasu Sultan ta wuce chan ma ta tarar baya nan wai sun wuce meeting, zama tayi kusan na awa tana jiran dawowansa amman shiru dan haka kawai ta hak’ura ta komo gida. Tana isa gida ta watsa ruwa tad’an huta chan ta d’ago wayarta ta sake gwada numban Afzal luckily private line nasan ya shiga sede har ya tsinke be d’aga ba, a karo na biyu data gwada kuwa se yake ce mata number cannot be reached ko meye dalili? Ashe blocking contact natan Afzal yayi yasa a call divert yadda baza ta ta6a iya samunsa ba.
The following day still Afzal be fita office ba. Nazeefah kuwa ta rasa dalilin da ke sanya sa ababen da yakeyi kwana biyu, ko abincin da ya saba fita yana saya ma bata ga yayi ba yau, bayan nan ga bandejin data gani nannad’e a hannunsa. Ta duba dustbins na gidan kap bata ga fasassun glass ba bale ache ko yanka ya samu shin meke faruwa ne? Tun da ya kulle kansa a d’aki bey sake fita ba se zuwa masallaci kad’ai ke fitar dashi. Gwada tambayansa meya faru tayi inda sukayi baram-baram. Akan me don ta damu dashi tana tambayansa meke damunsa ze tsaya yana mata masifa? Aikin banza. Bayan kwana biyu da faruwan abun ne Afzal ya soma fita office, hannun nasa da sauk’i kam amman still be since d’aurin ba saboda ba k’aramin ciwo ya jima kansa ba.
“Triple A ina ka 6oye ne wai kam kwana biyu?” Kafin Afzal ya amsa idon Sultan ya kai ga bandejin dake d’aure a hannun Afzal “Tsaya bandejin mey haka?” ya tambaya nan take.
“Babu banji dad’i bane kwana biyu.”
“Afzal I’ve known you for morethan 20 years kar kayi tsammanin zaka iya 6oye min abu. Amininka ne ni idan baka fad’a mun damuwanka ba mawa zaka fad’awa?”
“Maza ba wani abu serious bane ciwon ciki ne ya rik’eni two days se kuma jiya na yanke da glass that’s all.”
“Toh Allah sawwak’e ya cikin naka?”
“Da sauk’i ya office?”
“Alhamdulillah dama nace barin dubaka kwana biyu lines naka duka basu shiga.”
“An sace wayan ai sena sai sabo tukun.”
“Subhanallah private line naka fa? Har shima switched off yake cemun idan na kira.”
“Kasan ban cika kunnasa ba shi” Sarai Sultan yasan k’arya Afzal ke masa kawai baya son yayi pushing nasa ne saboda yasan halin abokin nasa abu kad’an kan 6ata masa rai kafin su hankara se suyi kaca-kaca anan. “Toh lemmi go back to work.”
“Alright take care” da haka sukayi sallama Sultan ya fice. Da yamma Sultan na zaune a office nasa PA’nsa tayi knocking ta shigo take ce mai yayi bak’uwa.
Bak’uwa de ya tambaya inda take jaddada masa eh. “Toh ki shigo da ita” yace mata. Ko da yaga Amal ce beyi mamaki ba saboda yasani dama komin rinsti da Amal Afzal ya samu matsala, yana da tabbacin ita kad’ai ce zata iya d’agawa Afzal hankali haka saboda tun ba yau ba ya karanci Afzal nason Amal.
“Amal?” Ya kirata.
“Na’am Ya Sultan” ta amsa tare da k’arisawa ciki ta tsaya. “Ina yini?” Ta gaishesa “K’ariso ki zauna kinji?” Ba gardama ta k’arisa ta zauna inda suka gaisa. “Yau kuma kin tuna dani kenan” yace da ita tamkar besan meke tafe da ita ba.
“Ai Ya Sultan kullum sede bamu had’u da Yaya ba se nace ya gaishe ka.”
“Toh nide sak’on ki be ta6a iske ni ba.”
“Afuwan toh.”
“Ba komai, meke tafe dake ko de gaisuwa ce kawai?”
“Eh toh duka biyu” ta fad’a tana nazari.
“Toh ina sauraronki.”
“Ya Sultan taimakonka nake nema don Allah.”
“Game da mey kenan?”
“Yaya, Ya Afzal.”
“Meya faru?”
“Yau kwana hud’u kenan ko biyar bana iya samunsa ta waya, koda naje office nasa kuma se acemun baya nan ya fita meeting dan Allah ka taimakeni.”
“Wait hold on, mey ya had’aku? Fad’a kukayi ne?”
“Wallahi sam” se kuma tayi shiru bata san ta ina zata fara masa bayani ba tace mishi saurayinta ya kirata a gaban Afzal ne shikenan shi kuma ya hau zuciya yayi fushi da ita ko mey? Yau tana cikin wani yanayi.
“Feel free to talk to me kinji?”
“Ya Sultan wallahi da nasan ransa ze 6aci da tun farko da Ya Abdul ya tinkareni da kalman so da bazan amince ba kokuwa da zan sanar da shi Yayan wallahi bansan ransa ze 6aci haka ba.”
“Hold on, waye kuma Ya Abdul?”
“Wan k’awata ne…” nan de ta mar bayanin komi ba abinda ta ragar masa.
“Toh Amal naji bayanunki amman ke a tunaninki me zay sa Afzal miki fushi haka?”
“Wallahi ban sani ba Ya Sultan na zauna nayi tunanin nayi tunanin amman ina na rasa k’wak’k’warar dalili sede tun lokacin da ya hanani shiga motan wani bayan nasa nasan ya damu da lafiyata ce sosai kuma baya son inayin abu ban sanar dashi ba” ta sanar da shi.
“Haka ne kam k’warai, so ke a ganinki yanzu da ace keda bakinki kika sanar dashi cewa gashi wani yace yana sonki shi Afzal d’in baze ji haushi ba?”
“Eh Ya Sultan a gani na rashin sanar dashi da banyin bane ya haifar da komi, kuma wallahi ina da niyyan hakan kuma koda ace Yaya ya bud’i baki yace mun kar in amince da k’udurin shi Ya Abdul d’in in bari se karatu na yayi nisa tukun wallahi zan ji maganansa saboda tamkar wana na jini haka na d’auki Yaya nake kuma jinsa a jikina, duk abinda yace inyi muddin be sa6awa addini ba zan yisa, I respect him alot saboda son da yake nuna min bayan iyayena ban tsammanin akwai wanda ze nuna mun irinsa.”
“Toh Amal yanzu ya kenan? Bazan 6oye miki ba Afzal yana fushi dake sosai.”
“Wallahi nasani shiyasa nake neman taimakonka ka tayani basa hak’uri don Allah wallahi idan cewa yayi na dena kula Ya Abdul zan dena, zan iya yafe soyayyan kowa saboda farin cikin Yaya I care about him alot.”
“Toh shikenan Amal I’ll do all I can in shaa Allah Afzal ze sauk’o zanyi masa magana.”
“Toh Ya Sultan thank you so much dan Allah duk abinda akwai ka taimaka ka kirani ka sanar dani.”
“Here write down your number for me” yayi maganan yana mik’a mata wata jotter nan da nan ta rubuta mai tana masa godiya. Ya rakata tace sam kar ya damu zata k’arasa da kanta. Bayan ta fice ya zaro wayansa daya 6oye k’ark’shin wani littafi had’e da stopping recorder d’in. Wow ashe tun d’azun recording hirarsu da Amal yakeyi. A tunaninsa idan har Afzal ya saurari hirar nasu, ya kuma gaskata kalamun nan daga bakin Amal hakan ze iya sanya sa sanar da ita Amal d’in abinda ke zuciyarsa don haka washegari ya kira Afzal akan suje suci abinci tare. Suna tsakan ci ne Sultan ya d’auko topic na Amal.
“Jiya Amal ta shigo min ai” dum Afzal yaji gabansa ya fad’i, sosai fuskansa ya bayyana mamakin da ya sha amman ya basar pretending like everything is cool.
“Oh haba? Ya take?”
“Ba lafiya ba” ya amsa shi ba corner-corner.
“Why? Meya sameta?”
“Haba Triple A drop the act already.”
“Sorry but I don’t get you” yayi maganan had’e da d’age gira d’aya yana sipping drink nasa.
“Dan Allah ka dena wannan zurfin cikin wallahi ina gudun maka ranar da ciwon zuciya zata kama ka.”
“Why? Meya kawo wannan magana kuma?”
“Mesa kake bawa ‘yar yarinyan nan wahala haka? Shin baka tausaya mata ne? Wallahi ba haka so yake ba.”
“Excuse me?” Yayi maganan cike da rashin fahimta.
“Sarai kasan me nake nufi until when do you plan to stop torturing her life like this? Har yaushe Triple A? Kai fa na miji ne, idan kai a matsayinka na miji ka kasa tunkararta ka sanar da ita abinda ke zuciyarka taya ita a matsayinta na mace yarinya ma at that kake tunanin zata iya gano hakan da kanta, iyye?”
“Ni ban fahimce ka ba.”
“Wow!” Sosai Sultan ya sha mamakin abokin nasa, be ta6a sanin zurfin cikin Afzal ya kai ga haka ba se yau. “You can deny me for as long as you want amman bazaka iya k’aryata cewa kana son Amal ba, bazaka iya k’aryata cewa akanta ne ka samu wannan munafikin ciwon dake hannunkan ba kuma akanta ne ka fasa wayanka har seda ka sake siyan sabo ba.”
“Look I’m not ready for this, idan kasan don haka ka kirani nan toh save it bana son sauraron ko kalma d’aya am leaving” wallet nasa ya ciro ya k’irga bill na abincin nasu ya ajiye akan table sannan ya mi’ke ya shiga tattara abubuwansa be kai ga takawa ba Sultan yayi playing audio’n da yayi recording jiya na hirarsa da Amal. Jin muryar Amal chak Afzal ya tsaya be sake motsi a wajen ba seda audio’n ta k’are.
Haushin kansa ya shiga ji na kasa sanar da Amal abinda ke cikin zuciyansa, na bawa zuciyarta daman son wani d’a na miji ba shi ba and k’arshe na sanya ta cikin damuwa haka. Ji yayi kaman ya wuce gidansu yanzun ya sanar da ita gaskiyan al’amarin ya tabbata kamar yadda ta fad’a idan da har ze bud’e baki yace yana sonta zata yafe soyayyar Abdul Rahman masa amman inaa baze iya ba, baze ta6a iyawa ba. Mutuncin da Amal ke basa baze ta6a basa daman ya furta mata kalamun so ba, baya son hakan ya zama sanadin da zesa Amal ta guje sa gara suta turawa a hakan.
“Ina had’a ka da Allah ka d’au mataki Triple A yarinyar nan bata ma san kana sonta ba nayi imani da Allah da ta sani wallahi bazata bawa shi Abdul d’in dama ba bale har su yi nisa haka.”
“Ni Afzal ban ta6a bud’e baki na ce maka ina son Amal ba kuma idan har baka son muyi kaca-kaca da kai bazaka je ka samu yarinyan nan ka fad’a mata cewan ina sonta ba tunda baka ji daga bakina ba. Idan kuwa har kayi hakan toh Allah ya isa ni ban yafe ba-“
“Haba Afzal!” Sultan ya katse sa “Mey haka kakeyi? Mey yayi zafi haka har kake neman had’ani da Allah? Wallahi ko makaho ne yasan kana son Amal kuma muddin ka cigaba da wannan banzar d’abi’ar taka ba abin mamaki bane idan ciwon zuciya tazo ta kama ka, kamar kuma yadda kana ji kana gani Abdul d’innan ze auri ‘yar nan a idonka ba yadda ka i-“
“Enough Sultan!” Afzal da zuciyarsa ta fara tafarfasa ya katse sa cike da tsiwa “Ya isa haka don kana matsayin amini na doesn’t mean you have the right to speak to me like this. Ban damu da wanda Amal take so ba, ban damu da wanda zata aura ba kamar yadda ta fad’a maka nima haka zan sake jaddada maka I’m just hurt saboda bata sanar dani wani yace yana sonta ba a matsayi na na wanda take kira yayanta, wanda ke d’aukan nauyin karatunta da sauran ababe. Bata yimin adalci ba ace har sun daidaita da wani bata sanar dani ba bayan nan I have nothing more against her so please bana son in sake jin kana cewa ina son yarinyar nan, nide na fad’a maka” Yana kaiwa nan ya fice ya nufi motansa, tunda ya soma tuk’i kalamun Amal suke masa raha a kunne duk yadda yaso kawar da hankalinsa daga hakan ya gagara k’arshe seda ya afka hatsari ya bige wani me sai da mangaro kafin ya ce ze taka burki inaa har ya buge mutumin sede Allah ya takaita abun mutumin fad’i kawai yayi be ji ciwo ba wheel barrown nashi ne ya fad’i komi na kai yayi k’asa. Da wuri ya sauk’a yayi kan mutumin kaman yadda mutanen kusa suka yi kansu suma, nan de ya basa hak’uri ya biyasa asaran da ya janyo masa. Office ya k’arasa ya kammala aikin da ya rage sannan yayi gida ya watsa ruwa ya kwanta. Sede abin ya gagara ya kasa daina tunanin Amal, kalamanta se yawo suke masa a kai lokaci d’aya tausayinta ya kama sa.
Wayansa ya janyo yayi searching contact nata tare da unblocking sannan ya kirata a karo na farko ta d’aga “Yaya?” Ta kirasa da mamaki ba tare da ta basa daman yin sallama ba.
“Na’am Lily” ya amsa pretending as if everything is cool.
“Yaya you called!” Tayi exclaiming cike da farin ciki da k’in yarda.
“Yes Lily ya kike?”
“Yaya I’m sorry, I’m so sorry dan Allah kayi hak’uri.”
“Ya wuce kinji?”
“No Yaya nasan abinda nayi maka ba dai-dai bane amman kayi hak’uri it shall never happen again please forgive me.”
“It’s okay, stop apologizing already ya wuce.”
“I missed you so much Yaya dan Allah karka sake hukuntani haka wallahi hukuncin yamin tsauri, Yaya duk abinda nayi ba dai-dai ba kana da ikon min fad’a har zana idan ta kama zakayi mun amman ignoring d’ina haka is not a solution please.”
“I’m sorry too Lily, I just didn’t know how to react, my Lily is in love and I didn’t know sede kawai ingani da ido na.”
“Wallahi ina da niyyan fad’a maka Yaya Allah ne kawai be bani iko ba amman kayi hak’uri.”
“So do you love him?” Ya tambayeta shiru tayi ta kasa amsawa “Lily?”
“Na’am Yaya?”
“Answer me.”
“Yaya…” se kuma tayi shiru “Yaya in ganin mu tare ne baka so ina iya sanar da shi in bashi hak’uri.”
“Not at all Lily ai farin cikink shine nawa besides ban ma san shi ba bale ince bana son shi so tell me about him.”
“Sunan shi Abdul Rahman he’s 28 years old yana aiki a INEC office.”
“Masha Allah so do you love him?”
“Yes Yaya I do” ta amsa chan k’asa-k’asa wani irin k’una zuciyan Afzal yayi da jin hakan daga bakinta danne zuciyansa kawai yayi yace, “Masha Allah ki ja mishi kunne fa kice mishi Yayanki yace kar ya kuskura yayi toying da feelings naki dan ko idan yayi na lahira ma seya fisa jin dad’i.”
Dariya tasa sosai “Kai Yaya nasan ai bazaka bari wani abun ya sameni ba besides Ya Abdul ma baze aikata abinda zesa a hukunta sa haka ba.”
“I like that spirit, so abu d’aya nakeso dake Lily ki mayar da hankalinki da karatunki kinji? Karki bari Abdul ya d’auke miki hankali kin ji?”
“Na ji Yaya in shaa Allahu thank you.”
“Toh barin yi shirin sallah ko?”
“Toh Yaya Allah ya kare goodnight.” Sauk’e wayan yayi daga kunnensa a hankali yayin da zuciyar sa keyi masa wani irin rad’ad’i. Ta riga ta fad’a tana son Abdul in har Abdul ne farin cikinta toh shi kuma aikinsa ne a matsayinsa na yayanta yayi farin ciki da hakan. Meyasa yake jin haushi toh? Meyasa zuciyarsa take yi masa k’una haka? Yana son Amal, ya juma yana sonta, yana d’aya daga cikin burinsa na kullum ya mallaketa ya mai da ita nasa. Jira kawai idan lokacin yazo ya sanar da ita abinda ke cikin zuciyansa.
Da da jimawa yayi hakan amman baya son abinda ze raba mata hankali daga karatu se gashi nan wani daga chan yazo ya hargitsa masa plans nasa gabad’aya ya karya mishi zuciya, ya tarwatsar masa da mafarkin maida Amal amaryarsa, k’arshe kuma ya d’auke masa farin cikin rayuwarsa. Sosai idanunsa suka kad’a suka yi jaa zur idan ya tuna da dukka wannan ababe, k’iris ya rage beyi kuka ba. Masallacin daya kasa zuwa kenan k’arshe a d’aki ya idar da sallan ya mik’e kan gado har bacci yayi awon gaba dashi.
***
Haka tafiya ta cigaba, gabad’aya Afzal ya rasa walwalar rayuwarsa kullum cikin k’unci da bak’in ciki yake. Amal ce me kirarsa kullum idan bata kira ba sede su zauna ahakan. Sau dayawa takan zuwa office nasa seya ce wa PA’nsa tace baya nan. Ita de Amal ta rasa dalilin duk wannan d’abi’u se Afzal ya d’au sati biyu be kawo mata ziyara kuma koda yazo d’inma baya iya sakewa da ita suyi hira kamar yadda suka saba, sau dayawa takan zauna tayi tunanin ko wani abun tayi masa amman ina ta duba ta duba ta rasa dalili. Ita da Ya Abdul nata kuwa se abinda ya k’au, tun bata barin ya d’auketa ita kad’ai a mota ta soma yarda da amincewa da shi. Zezo ya d’auketa su wuce gun shak’atawa idan ya tashi maido da ita gida kuwa ya cika mata leda da chocolates da ice creams.
Ta fannin Nazeefah ma sede abinda ya k’aru a kullum k’ara son Afzal take tun tana k’ok’arin 6oye masa abin ya gagara har ya kaiga shi Afzal d’in ya gane yanzu. Yau ma kaman jiya da ta tashi yin girki da shi tayi yana dawowa daga office tayi masa sannu da zuwa ya amsa sannan take ce masa food is ready. Banza yayi da ita seda ta bisa har d’aki “Afzal nace nayi girkin da kai fah.”
“Thank you a k’oshe nake.”
“Haka jiya ma kace, shikenan ni na rink’a girki kenan kullum kana cemin a k’oshe kake? Until when ne zaka dawo gidan nan da yunwa kaci abincin?”
“Please! Save whatever this is kin dega daga office nake ko? I need to rest.”
“Toh wallahi ni kuma bazan yarda ba akan me zanna maka girki kak’i ciki?”
“Ni na rok’eki kimin girki ne? Weren’t you the one that said da kiyi min girki gara kinyi hauka?”
“Toh kuma shikenan seka d’auka ka zauna akai? Ko kai zaman nan haka na maka dad’i I’m willing to change and start over this again why can’t you?”
“Because I don’t love you Nazeefah kin gane ko? Ko mey kikayi you’ll never impress me kin riga kin fita min a rai just let me be karki bari in sauk’e haushin da be shafe kiba akanki” yana kaiwa nan ya wuce bayi ya barta tsaye a gun. Hawaye kawai taji yana bin k’uncinta da k’yar ta iya tattara kanta tayi d’akinta ta shiga zuba kuka. Tun Mummy da Rumaysa suna ce mata tayi hankali tayi hankali kafin lokaci ya k’ureta tak’i ji gashi nan yau gar da gar Afzal ya bud’a baki ya ce mata ta fita masa a rai kuma ta tabbata ba komai bane ya janyo hakan illa rashin hankalin da tayita tafkawa, ina ma ace zata iya jan lokaci baya ta daidaita komi ba k’arya acikin zancen nan again tana son Afzal tana son shi kuma zatayi duk abinda ya kama don karkato da hankalinsa ya dawo a gareta.
Washegari da safe bim wajajen k’arfe sha d’aya ta shirya tsaf ta kira Afzal ta tambayesa izini sannan ta wuce gidansu Ummi dukda cewan bata sanar dashi inda zata. Maraba Ummi tayi mata suka zauna a parlour suka gaisa tasa su Esther suka kawo mata cookies da drinks.
“Kwana biyu kin k’i mu Nazeefah shima mijin naki ya kwan biyu be lek’o ba.”
“Allah sarki Ummi wallahi kinsan harkan makaranta yanzu ma dan mun samu hutu ne.”
“Wai bade har kun k’are part two din ba?”
“Eh wallahi Ummi se three kuma yanzu.”
“Masha Allahu karatun naku na tafiya gaskiya Allah sanya albarka aciki.”
“Ameen ameen Ummi nagode dama alfarma nazo nema ne.”
“Toh ‘yata ina jinki.”
“Game da Afzal ne.”
“Toh kuma bade wani abun bane ya faru ko? Ina sauraronki.”
“Ummi hak’uri nakeson ki basa.”
“Meya faru kunyi fad’a ne?”
“Ki basa hak’uri ya soma cin girki na don Allah, Ummi bazan 6oye miki ba tun auran mu ba wata jituwa a tsakaninmu as dukan mu bawai muna so auran bane mun yisq ne don ladabi da biyayya ga iyayenmu.”
“Wannan haka take ‘yata.”
“Toh Ummi bazan 6oye miki ba wallahi ko girki ban ta6a yiwa Afzal ba, rayuwansa yake daban a gidan nima haka, kullum daga office se parlour se d’akinsa yake zama nima daga school se parlour se d’akina amman abun ya isheni yanzu na zauna nayi wa kaina fad’a I want to give us a chance nace zan fara yi masa girki kuma na faran sede ko nayi baya ci Ummi wallahi ina son Afzal amman ko na second d’aya baya ma kallo na balle yasan ina cikin damuwa, be damu dani ba jiya har cemin yayi baze ta6a sona ba na riga na fita masa a rai and I don’t blame him saboda ni ne na janyo komi da kaina amman na tuba yanzu Ummi I promise to be a good wife to him but ya k’i bani dama, bansan ya zanyi ba wallahi ina son sa.”
Iya mamaki Ummi ta sha bata tsamman gaban dake tsakaninsun ya kai har ga haka ba ita da take jiran jika amman ace haka ai wannan da alama ko had’a kwanciya basu ta6a yi ba, lallai kam akwai k’ura sede kuma ta gamsu da tuban Nazeefah. Idan ba so na hak’ik’a takeyi wa Afzal ba ba yadda za’ayi tana mace ace bata ji kunyan idon surkarta ba har tayi admitting kurakuren ta haka.
“Ummi dan Allah ki basa hak’uri ko ze soma cin abinci na ya dena had’a min rai haka kullum.”
“Naji matsalar ki Nazeefah sede abu d’aya nikeson tambaya.”
“Ina jinki Ummi.”
“Ina fatan a iya zamanku baki ta6a goranta mai da wani abun ba?” Shiru tayi tana nazari chan tace “Wallahi nayi na masa akan girki.”
“Ai kin 6ata komi kenan gorin da kikayi masan ne yasa har yau ya kasa cin girkin ki.”
“Ummi amman ai idan kika basa hak’uri zai sauk’o.”
“Zanyi iya k’ok’arina but I can’t guarantee you hakan. Afzal halin mahaifin shi ya biyo se kuma har kaman nasa ma na son fin na mahaifin nasa. Kinga koni nan idan mukayi fad’a dashi se idan nazo na basa hak’uri yake sake amincewa yaci girkina kiyi imagining ke matarsa da har kikayi masa gori. Ina son ki sani cewa komin yaya fad’a ta 6arke muku da Afzal koda wasa karki kuskura ki goranta masa da wani abun dan shi idan yayi fushi da abu yayi ne har abada se wani ikon Allahn.”
“Innalillahi Ummi kina nufin yanzu Afzal baze ta6a cin girki na ba kenan?”
“Bana fatan hakan, in shaa Allah zan kirasa muhi magana duk abinda akwai zan kiraki in sanar dake.”
“Amman Ummi nagode sosai please don’t let Mummy know of this pleaase.”
“Karki damu ‘yata in shaa Allah maganan nan a tsakanin mu ne.”
“Thank you so much I shall get going.”
“Bazaki bari kiyi Azahar ba tukun?” Tayi maganan tana duban lokaci.
“Zanje inyi girki kinsan yau juma’ah 2 Afzal ke dawowa gida.”
“Toh Mama na Allah miki albarka bari in raka ki.” Tana raka Nazeefah ta dawo ta d’au wayarta ta kira Afzal a karo na farko ya d’auka.
“Halo Ummi?”
“Na’am Prince d’ina.”
“My Ummi ya kike? Ya Abba?”
“Lafiya k’alau ya aiki?”
“Alhamdulillah nace zaka iya biyowa nan idan ka tashi daga office yau?”
“Sure wani abu ne?”
“Kai de seka zo kawai.”
“Toh shikenan ina idar da sallan Juma’ah zan zo.”
“Yauwa Baby na Allah kawo ka lafiya yayi maka albarka.”
“Ameen Ummi take care bye” da haka sukayi sallama. Kaman yadda ya fad’a mata hakan yayi yana tasowa daga Juma’ah ya d’au hanyan gida, a hanya Amal ta kirasa, connecting yayi da car Bluetooth nasa sannan ya amsa suka gaisa take yi masa barka da Juma’ah. Yana isa gida ya fara wucewa site na Abba suka gaisa sannan ya k’arisa na Ummi.
Bayan gaisuwa Ummi tayi gyaran murya, “Dama ba komai bane yasa nace kazo illa batun matarka Nazeefah.”
“Toh kuma meya faru Ummi?”
“D’azu ai tana nan.” Se anan ya gane ashe nan tazo da ta kira take tambayansa izini.
“Lafia dai ko?”
“Ai ka fini sani, kai de bazaka ta6a barin wannan zurfin cikin naka ba ko?”
“Mey tazo tace miki?”
“Komi ma ta fad’a ba abinda ba ta sanar dani ba ai dama sau dayawa nayi suspecting zaman auren nan naku ashe haka kuka ta turawa har na tsawon shekara d’aya Prince? Wallahi I’m very disappointed in you idan ita Nazeefar yarinya ce bata da hankali ai kai seka nuna mata kana dashi amman ba wai ka tsaya kana biye mata ba kuna tafka wawanci ba, yanzu meye ribar ka? Yaci ace ka ajiye d’a a zaman ka yanzu haka wallahi.”
“Ummi don’t just jump into conclusions wallahi Allah ma sheda ne nayi hak’uri da Nazeefah iyakan hak’uri, ba me iyayin hak’urin da nayi da ita ni kawai bana son 6ata ta a idonki ne kikaga ko kin tambayeni ya gida nake miki k’aryan cewa lafiya k’alau.”
“Kalleni Prince” ta buk’acesa, ba gardama ya dawo da kallonsa a gareta “Zanyi maka wata tambaya kuma I want only a sincere answer.”
“Ina jinki” ya amsa bayan tsawon lokacin daya d’auka.
“Yadda kasan zaka mutu tsakaninka da Allah ka ta6a bawa yarinyar nan hak’k’inta na aure a matsayinta na matar ka?” Shiru yayi yana mamakin bade abubuwan da Nazeefah tazo ta irga wa Ummi ba kenan cewa ko hak’k’inta be ta6a bata ba, lallai kuwa!
“A dalilin mey zan had’a kwanciya da ita Ummi? Kinsan mey tace ne? Da kunne na najita tana cewa k’awarta da ta bani kanta gara ‘yan iska akan layi sunyi mata fyad’e kina ganin ya dace in raya sunnan manzo da ita?”
“Innalillahi! Nazeefar de?”
“Ummi k’arya zan miki ne? Wallahi da kunne na naji kefa baki san rashin hakalin da yarinyan nan take ba kuma wallahi albarkacin Abba take ci dan yanzu da zaran na saketa ko nayi mata wani abun kaman wa Abba nayiwa hakan ze iya 6ata tsakaninsa da amininsa ko ba haka ba?”
“Hakane Prince kuma na yabawa hak’urin ka amman seka duba kuma yanzu da ta gano kuranta take son ku fara sabon rayuwa, kamata yayi kayi hak’uri ka bata dama. Wallahi da bakinta anan take cemin tana sonka dan Allah in baka hak’uri.”
“Ni to bana sonta” ya fad’a mata gar.
“Wani irin magana ne haka Prince? Matarka ce fa! Haka kakeson ka cigaba da rayuwanka? Shin kai baka kwad’ayin ganin jininka ne?”
“Inaso mana amman bada Nazeefah ba.”
“Prince dan Allah kar kayi magana haka kamar yadda ka tsani yarinyan nan fa itama haka ta tsaneka da fari amman mey? Data bud’e zuciyarta maka ba gashi soyayyarka ta shiga ba kaima fa zaka iya dan Allah kar kace a’a.”
“Ummi kin de sanni, kin fi kowa sani na idan abu yafita min a rai ya fita kenan har abada, a da kafin in auri Nazeefah ban tsane ta ba kaman yadda na tsaneta yanzu. Zaman da mukayi da ita ya sake sa na tsaneta yarinyan can bata da hankali, bata da tunani, ba ta da fasalin komi, ba yadda za’ayi ta zame uwa ga ‘ya’yana no way!” Ya jaddada mata.
“Prince dan Allah ka dena magana haka, ka cigaba toh wallahi baza ka san lokacinda ze iske mahaifinka ba. Ka yayyafa wa zuciyanka ruwan sanyi kayi hak’uri ka bata dama ta sauk’e nauyinta a kanka a matsayinta na matarka.”
“Ni ta bari kawai na yafe mata haka zamu cigaba da zama har zuwa lokacin da Allah ze raba mu.”
“Wato kafi k’arfin in gaya maka magana kuma kaji ko Prince?”
“Ummi please kar kiyi magana haka sanin kanki ne banida kaman ki ans I always heed to you.”
“Then listen to me ka bawa Nazeefah dama.”
“Ummi zuciyana na mace d’aya ne kuma wata chan ta riga ta sace ta tafi dashi ba komai anan” yayi nuni da inda zuciyarsa ke. “Kinga ko ba yadda za’ayi in fara son Nazeefah.”
“Babban magana! Bade shirin aure kake yi ba?”
“Ko kad’an nide kawai na fad’a miki ne.”
“Akwai wacce kake so a waje kake nufi?”
“Yes.”
“Wacece ita?”
“I’m sorry Ummi but I can’t tell.”
“Hmm yaron nan ina tausaya maka, ina rabaka da ciwon zuciya, ba shakka kana bin soyayyar yarinyar nan ne a zuciya har ka rame kayi bak’i haka kwana biyu. Afzal ka tausayawa kanka ka dena rik’e abu a zuciya haka uhn uhn fa!” Ta ja masa kunne. Shi de shiru yayi zaune a gun yana sauraronta dan kuwa bashida abin fad’a mata, soyayyar Amal ne de baze ta6a furtawa ba.