Hot romantic hausa novel complete

Jini Daya Hausa Novel Complete

Jini Daya Hausa Novel Complete
 
 
 
 
 
 
 
JINI ƊAYA
 
_Story And Written
⬇️
*Mrs BBK*
 
 
 
 
 
 
 
wanna ƙir ƙirrarren labarine banyishi dan wataba ko wani idan yayi kamanceceniya da rayuwarki kuskure ne,

 
BISMILLAHI
ina farawa da sunan Allah mai yawan rahma da jink’ai. Alhamdulillahi na godewa Allah mahaliccina daya bani rai da lafiya da natsuwa, da konciyar hankali ya kuma ƙaramin ya buɗa min tunani na ya haskamin nazarina har na samu daman fara wannan sabon littafi nawa mai suna JINI ƊAYA ya Allah ina riƙonka da ka tsare min Al’ƙalami na daga rubuta sharri da abinda zai zamewa bayinka guba ko fitina, ya rabbil izzati ka tsarkake min tunani na ka kame min hannu na daga rubuta wani abinda zai zame min danasani duk ƙanƙantarshi, ya Allah ka bani rai da lafiyar gama littafin nan lfy-lfy, dani da masu karatun baki ɗaya.

Marubuciyar:
Adalilin so
Now
 
Jini Ɗaya
 
 
Kaoje kebbi state
 
 
 
*Episode 1*
 
 
 
Zahra!!! Zahra!!! “Na’am Inna “wlh idan kika bari nashigo ɗakin,nan na sameki sae jikin ki yafaɗa miki, da gudu Zahra ta fito daga wani ɗaki dake chikin gida, ɗakine da kallo ɗaya zaka masa kasan wadda ke rayuwa a ɗakin bashi da gata fitowa tayi tsakar gida, subhanallah farache tas doguwa mai dogon hanchi ga kyawawan manya manya ido laɓabɓan’ta kuwa ɗan karami pink colour Mai zanen love, gata da yalwar gashin gera mai gazar gazar gashin idon ta zara Zara, ga wani kyakkyawar saje baki sai sheƙi yake kwanche a gefen kumatun’ta, gashin ta kuwa har tsakiyar bayan’ta ga shape, Sss ɗin tan’nan kamar zasu fashe kwata kwata bazata wuche 15 years ba amma akoi yalwar boobs kyakkyawar gaske che kamar ita tayi kanta, sanye take chiki wani tsunmar atamfa duk yasha ruwa ya koɗe daga gefen rigar ma ayay’yage, a nitse take takawa da kyakkyawar kafar tai ɗauke da kyawawan zara zaran yatsu farchen kafarta sai kyalli suke.
Gaban inna tazo ta ɗuka tana faɗin “inna ganinan wani gigitachen mari inna ta sakar mata a kumatu, wadda yasata kwala wani irin ihu tare da dafe kunchinta, hawaye wani na bin wani, chikin faɗa Inna ta fara magana “ke ni sa’an wasan kine dazaki ajiyeni tun ɗazun ina jiran’ki to wlh kitashi ki ɗauki nikar nan, ki kai min kuma minti 20 na baki idan kika kuskura kika wuche minti 20, wlh sai na lahira yafiki jin daɗi, mikewa Zahra tayi jikinta har ɓari yake tanufi kichin, jim kaɗan sai gata ta fito kanta ɗauke da wani roba da alama nikar ne a chiki, ajiye robar tayi a tsakar gida tanufi ɗakin data kira fito, wani tsunmar hijabi ta ɗauko wan da duk ya koɗe pink ne amma sai da yazama fari saboda koɗewa, saka hijabin tayi ta fito ta ɗauki robar nikan tanufi waje, a zaure ta samu bappa zaune yana jin radio har kasa ta ɗuka tace “bappa ina wuni ɗaure fuska bappa yayi yana kawar da kai gefe alamar bai san ganin ta yace “lfy, Mikewa tayi jiki ba kwari tanufi waje, tafiya take tana rera karatun Qur’ani suratul khafi, a dai dai zata shiga wani ɗan ma daidai chin gidane tajiyo daga bayanta ana kiran su nanta, ɗaure fuska tayi sosai kafin ta juyo, da gudu yar matashiyar yarinyar wadda bazata wuche tsarar Zahra ba ta kariso wajen sai haki take tana faɗin “ni ma niƙa na kawo shine naje wajen chan ina wasa, muje ki ajiye nikar taki kizo muje muyi wasar,kafin a niƙa kara ɗaure fuka Zahra tayi tace “ke asiya ki kama gaban’ki wai bana faɗamiki ki dai’na min magana ba “kai Zahra wai meyasa baki son kawanche da nine me namiki asiya tayi tambayat da alamun damuwa a face ɗinta, tsaki Zahra taja san nan da wuche chikin gidan, da Sallama ta shiga ta ajiye nikar’ta kusa da bakin injin san nan ta ɗuka ta gai da mutanen dake wajen, chikin sanyin murya take faɗin “maman Sadiq dan Allah ki nika’min da wuri Inna tace kar na wuche minti 20, mikewa maman sadiq tayi daga zaman datayi saman kujeran katako tana faɗin “bari na nika miki zahra wlh badan ke ba bazan kunna inji yanzu ba “to maman Sadiq ngd ta faɗa tana kokarin miƙewa, gefe takoma ta zauna tayi tagumi tayi shiru tana tunani, Allah kajikan mamana Allah kamata rahma, tayi nisa chikin tunanin taji an taɓata firgigit tayi ta ɗago kai maman Sadiq che tsaye rike da nikar ashe har tagama nikawa ban saniba, Zahra tafaɗa a chikin zuchiyar’ta mikewa tayi tasa hannu ta ansa nikar tana faɗin “ga kuɗin “Zahra’u tunanin me kike “murmushi Zahra tayi wadda har dimple nata sai daya lotsa “babu komai maman Sadiq Zahra tafaɗa tana kokarin wuchewa, dafa kafadar’ta maman sadiq tayi tana faɗin, “ki chigaba da hakuri kinji Zahra komai zai wuche “to kawai Zahra tace tare da wuche wa da sauri dan kar lokachi ya kure sauri take sosai Kamar zata tashi sama, bata ankaraba kawai sai wani yaro mai keke ya bugeta ta faɗi kasa nikar nata ya zube gaba ɗaya, Yaron kuwa ganin yamata ɓarin nikar ne yasa yaja kekensa ya gudu, da kyar ta mike ga hannunta duk ya kukuje sai jini yake ita batama damu da hannun nata ba ta nikar nata daya zube take,wayyo Allah nashiga ukku ni Zahra ya zanyi me zan cema inna idon naje gida ta ƙarasa maganar kuka mai tsuma zuciya, haka da tattara sauran gari da yarage tazuba cikin robo ta nufi gida, sai rakuɓe rakuɓe take, Muryar inna tajiyo nata cewa, ” don Banki kizo nan ina kallon ki tsayuwar mi kike a waje da bazaki shigoba, jikin zahra har rawa yake da sauri ta ƙaraso inda inna take zaune, jikin har rawa yake, ta durƙusa ƙasa riƙe da fasassar roba da sauri inna ta mike tsaye tana faɗin me ” zangani haka”? ƙoƙarin magana Zahra take taji saukar Mari mai mugun zafi, da sauri dafe kunce ta tana kuka mai tsuma zuciya, duka inna take kaimata ta ko’ina tana faɗin, ” shegiyar yarinƴa matsiyaciyar banza yau sai naga bayan ki, taƙarasa mganar tana huci, cikin kuka Zahra take magana, ” inna don Allah kiyi haƙuri Wlh ba laifi nane ba bata kaiga ƙarasa maganar ba taji saukar icce a bayan ta, wata irin ƙara Zahra buga nan take tayeke jiki ta faɗi ƙasa a sume, da sauri Inna lamishi ta ƙara so cikin gidan tana kiran ” jimmai mike faruwa haka”? ” meyaru da Zahra”? taƙarasa inda Zahra take kwance jijjigata inna lamishi take tana kiran,” Zahra !!! Zahra !!!, ” jimmai bani ruwa suma Zahra tayi kiyi sauri don Allah, inna jimmai ko tsaye tayi kaman bada ita ake magana ba, ina lamishi naganin haka tamiƙe da kanta tawuce bakin randa ta ɗebe ruwa sai faman zubawa Zahra ruwa take, can ta sauke Ajiyar zuciya, cikin sanyi murya inna lamishi take magana, “Zahra sannun kinji muke damunki”? cikin Muryar kuka take magana, ” inna “na’am Zahra, ” inna bayana ke ciwa bazan iya tashi ba, ” kiyi haƙuri Zahra kinji, zaunar da ita inna lamishi tayi, sai faman lallashin ta take, Zahra ko sai kuka take, muryar Inna jimmai suka tana faɗin,” ai tunda kin tashi sai kije ga dawa can baki turmi ki maidashi gari yanzun nan kuma, ” jimmai Wlh kiji tsoron Allah, kibi duniya a sannu ina jiyemiki tsoron randa Allah zai kamaki da hakkin ƴarin ƴarnan shiken don mahaifin yarta bata raye Ubanta ma kin mai dashi bawonki sai yadda kikayi dashi, da karfi jammai take magana har jijiyoyin wuyan ta natashi,”ina ruwan ki da rayuwata bana son sa ido lamishi wlh kifita a idona, ” lamishi ubanwa ma ya baki izinin shigomin gida batare da izinana ba, kala inna lamishi bata ce mataba, ” Zahra ke don Ubanki kitashi kiyi aikin da nasaki, ɓatawa kanki lokaci kike gara ki tashi, da dafa dafa Zahra ta miƙe tsaye, inna lamishi kam sai kallon ikon Allah take da reshin imani irin na jimmai, ” jimmai kiwa Allah kibar ƴarin ƴan nan ta huta don Allah, ” lamishi wai miye matsalar ki kam, naka alama kina son wace gona da iri don Allah ki fitar mi a gida ta ƙarasa maganar tana nuna mata ƙokar fita, ” jimmai basai kin ƙoreni ba zan fitar miki a gida ina mai faɗa kimi kiji tsoron Allah ki tausayawa Zahra wannan wane irin rashin imani ne, ” kin saka ƴarin ya a gaba sai A zabtar da ita kike, ” jimmai tun shigowar ki gidan nan kika tar watsa musu farin cikin su, kin raba Ƴarin ƴa da farin cikin ta kin maishe ta marar gata uban cikin ta kinsa duk duniya ba abinda ya tsana kaman Zahra, ” jimmai yakama ta kiɗau darasi ko akan reshi haihuwa da kike nema ido A rufe Allah bai ba baki ba, ” jammai so nawa kina ɓarin ciki a gidan nan, ko don wannan ya kama ki ɗau darasi Allah bazai taba baki abinda kike so har sai kin dane zanuntar mareni yar Allah, ” jimmai Wlh ki nemi yafiyar Zahra in ba haka ba duniya zata koya miki hankali,rai a ɓace inna jimmai tashiga maida martani,” lamishi kindai ji kunyar duniya wanna wane irin sa ido ne haka to wlh kifita a idona na rufe in ba haka zaki gani,cikin zafin rai inna lamishi ta maida mata martani ” jimmai bari nafaɗa miki ba abinda zan gani sai Alherin Allah, Indai zalunci ne ki ci gaba dayi zaki girbi abinda kika shuka, nan fa faɗa ya cakuɗe tsaka ninsu , Zahra kam sai kuka take, ga mutane sai shigowa suke,inda sabo sun saba da halin jimmai munɗin zaka faɗa mata gaskiya akan Zahra tofa kowa zai jiku, daƙar suka rabasu duk da sunsan inna jimmai bata da gaskiya, ƙawarta larai ɗai tagoyi bayanta, rai a ɓace inna lamishi tabar gidan, mutane na fara watsewa Zahra ta fara dakan gari, sai bayan isha’i ta gama, nan tafara shirin ɗora abinci,inna jimmai sai zaginta take, inda sabo ta saba da halin inna jimmai, sai kusan karfe tara tagama abinci, Saida ta kammala komi Sanna malam Buba tashigo gida, cikin ladabi Zahra ta duƙa har kasa tace,” Bappa Afo iyadu Bappa sannu da zuwa, ko kallon ida take malam Buba baiyi ba, Saida ya wuce Sanna Zahra tamiƙe tsaye abincin nai ta kaimai inda yake zaune tare da inna jimmai, ƙoƙarin zama take wata irin tsawa inna jimmai ba buga mata Saida ta zabura, ” shegiyar ƴarin ƴa mu warin kine da zaki zauna wajen mu munafukar banza, ɓacemin da gani jiki na rawa Zahra tabar waje tana hawaye, malam Buba sai kallonta yake har ga Allah baya jin daɗi yadda jimmai kema Zahra gashi baida bakin magana, duk lokacin da yaga jimmai na tsongwomar Zahra har ga Allah rai nai ɓaci yake sosai ya kayan tausayawa Zahra gashi itace ƴa ɗaya tilo da Allah ya bashi har Zahra ta shiga ɗaki idon malam Buba na kanta,”Buba har so ukku tana kiran shi bai juyo ba Saida ta dafa shi, da sauri ya maida kallonshi ga jimmai, ” Buba”na’am jimmai kallon me kakewa Zahra”? murmushi karfin hali malam Buba yayi sannan yace ,”bakomi jimmai,” hmmm ɗai inna jimmai tace, cikin dauriya malam Buba ya gama cin Abinci shi, shidai yasan irin damuwar da yake ciki, hira suke sama sama yake amsa mata, inna jimmai na lure da yanayin da yake ciki, sai murmushin mugunta take har suka wuce ɗaki jikin Malam Buba a mace,
 
zaune take a ɗaki tasa kwanan Abinci A gaba takasaci sai faman kallon hoto take tana hawaye Masu mugun zafi da raɗaɗi, cikin rawar murya ta soma magana, ” Allah yajikan ki da rahama Ummi na Allah ya gafar tamiki tana magana tana kuka mai tsuma zuciya, nan take zazzaɓi mai ƙarfi ya rufe ta sai rawan ɗari take, haka ta kwanta nata makarkatan sanyi, daga sama taji murya inna jimmai tana cewa.
 
 
 
 
 
WANNAN PAGE SADAUKARWA NE GARE KU MRS BMB, ZAHRA ALLAH YA QARA MANA ZUMUNCI DA QAUNAR JUNA, AMEEN.
 
 
 
 
 
 
More comment and share
 
 
 
 
*MRS* *BBK* *ce*
BEAUTY LADY
 
 
 
*JINI ƊAYA*
 
Story And Written
 
*Mrs BBK*
 
 
*Episode 2*
 
 
https://chat.whatsapp.com/JkrY3yDMLmv6vEJjX54Ung
 
 
💖الحَمْدُ ِلله سبحان الله الله أكبر💖
 
 
” don ubanki Ni kike jira na kwashe miki kwandan da kika bari a waje, cikin rawar murya Zahra ta soma magana da ƙyar maganar nata ke fita, ” inna don Allah kiyi haƙuri wlh bana jin daɗin jikina, ” ko mutuwa zakuyi sai kin fito kin kwashe kwandan nan, sai kuka Zahra take da ƙyar ta miƙe tsaye tana talgal talgal, ta fito waje ta kwashi kayan ta kai kichin, inna jimmai na tsaye tana kallon ta har tagama Sannan ta koma ɗaki, Saida Zahra taga wucewar ta ɗaki sannan itama ta wuce ɗaki ta kwanta sai kuka take tana juyi, sai kusan Assuba baccin wahala ya ɗauke ta,
 
 
can cikin bacci taji Muryar inna jimmai ta kwala mata kira, da sauri Zahra ta miƙe tsaye tana dafe bango har tafito waje, tsaye inna jimmai take riƙe da ƙugu kaman mai shirin dambe har ƙasa Zahra ta ɗuƙu cikin sanyi murya tace,” ina kwana inna,Kamar daga sama Zahra taji saukar Mari mai mugun zafi a fuskarta, a’razane ta dafe kunchin ta tana hawaye Masu mugun zafi, ” me hanki fitowa da wuri, ” don Allah kiyi haƙuri wlh zazzaɓi ke damuna, ” ko mutuwa zakiyi yau saikin yi aikin gidan nan, ” zanyi inna kiyi haƙuri don Allah, nata batun tashi malam Buba tashigo gida da wowarshi kenan daga masallaci, cikin sanyi murya Zahra tace” Awalijam bappa ina kwana bappa,
 
Ganin irin kallon dayake matane Wanda koyaushe yake nuna gazawarsa amatsayi na uba
Ita Kuma Bata taba yimasa kallon ya Gaza din saboda tasan hakan qaddararsu ce su duka tun daga kan mahaifiyarta da Bata Raye har inna jimmai wadda take ganin itace tafi cutatuwa ato kowanne bangare na rayuwarsu.
 
 
A hankali Zahra ta sauke Ajiyar zuciya
batare da ta ɗagoba ba, ta ɗan sake numfashi mai sanyi da rashin sauti kafin ta waiwayo da kyakkyawar fuskantar, idanun ta suka sauka kan inna jimmai dake hararta, da sauri Zahra ta kike tsaye tawuce ban daki a gurguje ayi Arwalla ta fito Saida ta gama sallah, Sanna ta fito tsakiyar gida,
 
nan take tafara aiki gidan kama daga shara wanke wanke ta had’a musu abunda zasu yi kumallo da shi kuma idan akwai wanki sai tayi shi babu islamiya babu boko dama dama wani lokaci ana Barinta ta tafi islamiya, koshi ko Saida malam Manu yayi tsaye Sanna inna jimmai ta yadda gashi yanzu duk ƴan mate ɗinta sun wace ta, Saida ta kammala komi Sanna takaimu nasu, bata wani ci Abin kirkiba don har yanzu zazzaɓi na munta, malam Buba na gama ƙaryawa ya fita waje, fitar keda wuya larai ƙawar inna jimmai tashigo har ƙasa Zahra ta duƙa tana faɗin,” ina kwana inna larai kala larai bata cemata ba sai harar ta take, da sauri Inna jimmai ta ƙara so wajen ta tana fadi,” kinji ƴar halak yanzu nake maganarki a raina, murmushi larai tayi tana faɗin, ” tasamu kenan,”Kinga muje daga ciki kar dengi Mayu su canye canye mu,
Inna jimmai ta ƙarasa maganar tana dariya, sannan suka wuce ɗaki,
 
 
Zahra da ido tabisu tana hawaye saboda tasan zuwan inna larai a gidan bana Alheri bane,
 
“Kinga nifa yunwa nakeji cewar inna larai, dariya sosai inna jimmai tayi Sannan tace, ” ina malam Tanimu ko bai kawo kayan kariba, nan take larai ta turmuƙe fuska tana faɗin, sai kace baki san halinshi ba nifa ban taɓa ganin lusarin miji irin Tanimu ba, ” larai to ai kece calir komi cewar inna jimmai ta ƙarasa maganar tana dariya sosai,
 
” jimmai zaki bani abin kari kodai maganar lusarin can zaki tsaya kina min, ” Kinga Allah ya huci zuciyar ki, kwanon Abin ta miƙa mata, nan take ta kawar da shi, inna jimmai kam sai kallonta take, Saida tagama Sanna tace yauwa, ” neman me kike min, saida ta sauke Ajiyar zuciya Sanna tace, “Larai”na’am jimmai, ” mike faruwa halam, ” Akwai matsala fa”? cewar inna jimmai,” wacce irin matsala kenan, ” Larai hankali Buba yafara karkatowa kan shegiyar ɗiyar nan tashi, da sauri Larai tamiƙe tsaye tana faɗin,” wanna ai duk saka cinki ne kinan s mudɗin hankalin shi ya dawo kan shegiyar yarinƴa nan kinsan kin samu matsala kuma burin ki bazai taba cika ba yazama dole ki tashi tsaye jimmai ina ba haka ba kina ji kina gani Zahra tafi ƙarfin ki, ” Larai kaman ya Zahra tafi ƙarfi na, ” oh mamaki ma kike ko, to wlh gara kisan tayi inba haka ba damar ki zata kuɓuce miki, ” yanzu to miye shawara cewar inna jimmai,” shawara ɗaya ce mukoma wajen boko shi kadai zaiyi miki maganin matsalarki, haka suka cigaba da tattaunawa, kamin nan suka wuce gidan boko,
 
 
Zahra Saida ta kammala aikin ta gabaki ɗaya Sannan ta shirya zuwa islamiyya Allah Allah take tabar gidan kafin inna Jimmai ta dawo karta hanata zuwa don ba ƙaramin aikin ta bane,Saida ta rufe ko ina sanan tabar gidan, gani da sauran lokacin yasa tabiya gidan kawu Manu, koda tashigo zaune suke a tsakiyar gida suna hira, har ƙasa ta duƙa ta gaishe su,” Baba ina wuni, ” Zahra’u kina lafiya”? ” Lafiya lau baba, cikin sanyi Muryar inna lamishi tace, “Zahra’u ina zakije haka, ” inna islamiyya zantafi shine nace bari nabiyo na gaishe, ta karasa maganar tana murmushi, ” ina innar taki, “su fita,
 
 
Zahra’u, ” na’am baba kinci Abin, ” ehh baba naci kafin nafo, baki buƙatar komi, ” a’a baba, ” Allah yayi miki Albarka Zahra’u kici gaba da haƙuri kinji komi zai wace wata rana sai labari, kuma ciki gaba da yin Addu’a Allah yayi miki zaɓi na Alherin kinji, mahaifinki ma kirinƙa yimai a Addu’a sosai, nan suka cigaba da yimata nasiha, ” Zahra’u tashi kitafi tun baki makara ba kinji, ” inna nata batu tashi baba Manu yabata 200 amshi wannan koda zaki sayi wani Abu, girgiza kai Zahra tayi tana faɗin, ” baba kabarshi kawai Nagode kuma bana buƙatar komi, muryar Inna lamishi taji tana faɗin ” haba “Zahra’u ki karɓa mana zaiyi miki amfani kinji da ƙar Zahra ta ƙarɓi kudɗin, tana faɗin ” Nagode baba Allah yasaka da Alheri,kala Baice mata ba, ” Zahra’u tashi kitafi karki makara kinji cewar inna lamishi,mikewa Zahra tayi tana musu godiya tana shirin fita Asiya tashigo, “Zahra don Allah ki jirani mutafi tare, Muryar inna suka jiyo tana faɗin, Zahra tafiyar ki karki tsaya jiran ta taɓata miki lokacin, kinsan jakije islamiyya shine zaki tsaya shiririta, wucewa Zahra tayi Abinda,
 
 
“Lamishi” na’am Malam, ” wlh Zahra tana bani tausayi, Ajiyar zuciya inna Lamishi tayi Sanna tace, ” Zahra dole duk wani mai imani ya tausayawa rayuwar ta dukda ƴarinƴa ce mai haƙuri da kawaici amman tana da ban tausai, duba kaga irin rashin mutunci da jimmai tayi min ranar da naje gidan su,
 
cikin sanyi murya malam Manu ya kira, ” Lamishi” na’am Malam ni ba Zahra’u dai ke bani tausai ba hadda ɗan uwan nawa kiduba ki gani yadda Jimmai ta maida Buba yanzu ya dawo marar Amfani duk wani Abu da akewa Zahra’u yana gani saidai baida bakin magana abin baƙin cikima shine duk lokacin da naje mai da maganar Jimmai kan irin a zabar da takewa Zahra saidai yace min ai tarbiyya ce a ke koya mata, in Banda reshin tunani irin na Buba yaushe ake koyon tarbiyya da duka, haka lokacin ba yadda banyi da shiba kan Zahra’u ta dawo gidana kodon ta rabuda Azaba Jimmai Amman ina, ya karasa maganar rai Abace, nasan da iyayen mu na raye haka duk bazai faruba, A kullum Addu’a ta Allah yaba Zahra’u miji nagari , cikin sanyi murya inna lamishi tace,” Amin malam, kaduba ka ganifa Asiya mada a ƴar uwatar Jimmai tahana su ƙawance, Ajiyar zuciya malam Manu ya sauke yana faɗin “Allah ya kyauta, Allah kuma yabamu hakuri, ” Amin malam,
 
haka suka cigaba da tattaunawa har Asiya tagama shirinta tawuce islamiyya,ta barsu nan suna hira,
 
 
Har Zahra ta dawo daga islamiyya inna Jimmai bata dawo gida ba, bata yi mamakin reshin da wowarta inda sabo da saba da hakan, har kayi maggariba da Isha’i inna Jimmai bata dawo, zaune take bakin ƙofa tana Addu’a, sai ga inna Jimmai tafe a fujajan kaman wata sabon kamu, sai kwalama Zahra kira take, ” ina kike shegiyar yarinƴa, da sauri Zahra ta miƙe tsaye tana faɗin ,” inna sannu da zuwa, ” Ashe kina ciki nazata kintafi yawan iskancin ki dakika saba , ina Buba yake ko har yanzu bai dawoba yana can wajen ragaitarshi, Zahra tabatun tayi magana suka jiyo muryar Malam Buba yana faɗin, ” Jimmai Kingan ninan yanzu nashigo, ” Buba yanzu kana nufin tun fitarka da safe baka dawo ba sai yanzu, cikin sanyi murya yace, ” ai nadawo ban tararda kowa a gidan shine nasake fita, wata irin tsawa inna Jimmai ta sakawa Zahra Saida ta zabura, ” don Ubanki ina kikaje yanzu don tsabar iskanci har kinyi muƙamin da zaki fita batare da izinina bako, ina kikaje, Muryar na rawa Zahra tace, ” inna islamiyya naje, ” waya baki izinin fita, ” Inna don Allah kuyi haƙari bazan sakeba , nan take Inna jimmai ta rufe Zahra da duka, malam Buba na tsaye yana kallo, Zahra banda kuka ba abinda take, malam Buba jiyake kaman ya fasa ihu ga wani irin zafi da zuciyar shi take, dakatar da Jimmai yake son yin Amman yakasa, dole tazuba mata idon badon yaso ba, Inna jimmai Saida tayiwa Zahra ligip Sanna ta kyaleta, sai maida nuntashi take, tashi tsaye Zahra tayi jikin ta har rawa yake haka tawuce ɗaki tana kuka mai tsuma zuciya, da ido malam Buba sai kallon ƴarshi yake tareda tausaya mata, jiki a mace ya ƙara da waje tabarma inada Zahra ta ajeye musu Abin ciki, zama yayi tareda zabga uban tagumi har jimmai ta fita da ɗaki ta zauna duk bai sani ba,
 
 
 
” Buba, har so ukku tana kiran shi baijiba Saida ta dafa shi, tana faɗin, ” lafiya mike damunka”? Kodon na daki tsinarniyar yarinƴar nan ce kake wani zuba tagumi, ” a’a wlh badon haka bane kaina ne keciwo, ” kadai ake ji, nan suka zauna cin Abinci malam baiwani ci Abin kirkiba,
 
 
” Zahra” na’am inna da sauri ta ƙara sa wajen duk da jikinta da ke mata ciwo haka ta ƙara so waje har ƙasa ta duƙa, ” inna gani, ” Buba bani dari biyar ina Kanada,” jimma wlh ko sisi banda, ” matsiyacin banza, wani irin zafi Zahra taji a zuciyar ta, ” Ungo karbi nan kike kasuwa kisiyo min kosai da biredi, kuma wlh karbi bata min lokaci ke nake jira, hannu na rawa Zahra ta karbi kudin Sanna ta wuce tana hawaye Masu gun zafi,
 
 
tafiya take a natse har ta iso kasuwar kobo, taɗan jima wajen mai kosai sanan layi yazo kanta gabanta sai faduwa yake dare yafara gashi inna Jimmai tace kar jima jiki a mace ta kama hanya zuwa gida ba kowa sanan hanya sai ita tafiya take a tsorace, daga sama taji Muryar wasu samari suna fadin, ” yaufa munfito a Sa’a daga daga cikinsu ya kwashe da dariya, Zahra tun lokacin da taji maganar su jikin ta yafara rawa tafiya take da sauri sauri tana waigon bayanta,
juyowar da zatayi taci garo da mutum a gaban ta nan take ta yarda ledan ƙosai a ƙasa murya na rawa ta soma magana, ” don Allah kuyi haƙuri ku bari na tafi jirana ake a gida, ƙoƙarin rungumeta saurayin yake Zahra naja da baya tana bashi haƙuri tana kuka mai tsuma zuciya, labɓanta har rawa suke, tana batun yin ihu ɗayan saurayi ya rufe mata baki ɗaukar sukayi kaman wata yar bby suka wuce da ita cikin haki Zahra sai wulle wulle take tana ji tana gani suka kwantar da ita kasa kokarin cire mata kaya suke cikin ɗayan saurayin har ya cire wondo yana batun hawa cikinta Allah yabata ikon tafasa ihu da ƙarfi,
tafiya yake, mashin ɗinshi ya tsaya dai dai indasu Zahra suke, kaman daga sama yaji ihu dube dube ya farayi yana neman inda yajiwo ƙarar bai gani ba, har yatada mashin ɗinshi sake jini irin ihun da yaji ɗazu da sauri yaki mashin ɗinshi ya nufi inda yake jin ƙarar nasan shi sai faduwa yake, har yaƙara inda yake juyo ihun, ” Innalillahi wa inna ileyhiraju’un, da sauri samarin suka miƙa tsaye….✍️✍️✍️✍️
 
 
 
Masu karatu muhadu a next episode Insha Allahu nagode sosai Allah yabar zumunci,
 
 
 
 
masu buƙatar karatun littafin Jini ɗaya tunda ga farko har ƙarshe kiyimin magana ta wannan number 08149979652 don Allah banda kira,
 
 
More comments and share
 

Leave a Reply

Back to top button