littattafan hausa novel complete

Al’almarin Ubangiji Littafi Na Ɗaya From Page 1 To 120 HausaNovel

 Copied ByHAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) (ADMIN OF ADMINS)        (admin    Hayat hausa novelsHausa novels and fashionCool novel, makeup and kitchen1⃣Cool novel, makeup and kitchen2⃣                   AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣)       WHATSAPP NO:        09030159301(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀  *AL’AMARIN UBANGIJI.*                     🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W.**Mmn Abduljalal.*🥀🥀🥀🥀🥀🥀1-5.*Domin Nishad’inku masoya.*😍😍*بسم الله الرحمن الرحيم*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*”D*addy, gaskiya wnn qauye ya min, ya ban sha’awa ba kad’an ba, har naji kamar na dawo nan da zama.”D’an nema, tun yaushe nake binka mu zo tare da kai kana qi, an gaya maka ni d’in a banza nake son zuwa qauyennan ne.Duk lokacin da na ziyarci qauyennan nakan samu nitsuwa ,kwanciyar hankali da nishad’i.Snn yakan tuno min da abubuwa da dama wad’anda suka shud’e, shi yasa kaga bana jimawa ban leqo ba.””Gaskiya daddy, nima ai yanzu na gane, tare zamu riqa zuwa.”Kallon shi na d’an lokaci daddy yayi.”Kai Habibullah, wato babu maganar karatu a agender ka ko, har yanzu baka shiryawa tafiyar ba kenan kake ikrarin zamu rika zuwa nan tare.Shafa kanshi Habibullah yayi yana neman abunda zai cewa daddy.Isowar wata ‘yar yarinya da gudu ya ceceshi dan ya rasa excuse din da zai bawa daddy.Yarinyar tayi butu butu da ita, uniform dake jikinta duk yasha qura, gaba daya jikinta datti ne.Kafa gwiwowinta tayi a kasa dab da tabarmar da suke zaune a kai, tana washe kananan fararen  hakoranta, tana kuma haki, alamar taci gudu.Idonta kan Daddy tace “Lah, baba Alhaji, yaushe kazo.”Shima kallonnata yakeyi da murmushi d’auke a fiskarsa, kafin daga bisani ya kawar da fiskarshi alamar fushi yake da ita.”Nayi fushi ‘yar Baba, tun jiya nazo garinku amma ban saki a ido ba sai yanzu.”Karyar da kanta tayi tace “Ayya, yi haquru Baba alhajina, bansan kazo ba.”Sai kuma ta rike baki “Lallai Innata da mugun hali take, yanzu a ce kazo tun jiya bata fad’a min ba.”Kallonta yayi yace “Um, um Bintu kada ki sake fad’ar haka, uwa bata mugun hali watakil dai ta manta ne.”Turo d’an qaramin bakinta tayi tace “Ba wani mantuwa da tayi, yoo in ba mugun hali ba baba Alhaji mai zai sa ma ta manta da zuwanka.””To ko dai wani laifin kika mata ‘yar baba?”Gyara zama tayi nan kasa ta ce “tsaya babana in lissafa maka abunda nayi jiya ta rika make ni kamar na mata wani laifi.Kaga da na tashi da safe, fitsari naje na fara yi, snn nayi alwala nayi sallah, na na wanke bakina, na tafi karatun allo, da na dawo sai hararata takeyi wai ina wasa a hanya na dad’e zanyi lattin Makaranta Ka ji d’aya.Gyad’a kai yayi yace “Naji Bintun baba.”Ban kulata ba, naje nayi wanka naci d’umame na na wanke hanu da bakina na na shirya na tafi makaranta.Da na dawo ban san hawa ba ban san sauqa ba sai kawai naji dundu a bayana wai nayi datti da kayan makaranta na, ni qazama ce.Kaji biyu.Ta fad’a tana d’aga mishi yatsunta guda biyu.”Naji Bintuna.””Na uku kuma bayan naje islamiyarmu na dawo naci abinci nayi sallah, me ya rage?”Ta tambayeshi tana waro mishi madaidaitan fararen idanunta.Biye mata yayi da cewa “babu yar baba.””Yauwa baba alhajina kana ji?””Ina jinki.””Tunda babu abinda ya rage sai na fita na biya gidansu Indo muka tafi dandali muka warwasa .”Tana fad’an warwasan tana girgiza jikinta irin ansha rawa d’innan.””To meye laifina anan, kuma na manta ban fad’a maka ba dana dawo daga islamiyarmu ma saida ta rankwasheni da zata aikeni wai saura kuma naje na zauna.Kaji Uku.”Duk fa nayi haquri na kyale shine kuma dan naje dandali ta kama ni ta zane ta kuma fad’awa baffana ya min fad’a, dan Allah baba wnn ba mugun hali ba?”Ta tambayeshi tare da kureshi da ido ita a dole amsa takeso ya bata.”Bintu na kenan, ba mugun hali bane ,yar baba, tana yi miki hakane sbd ki zama ya ta gari, ki zama mutuniyar kirki kinji ko?”Gyada kanta tayi tace “naji baba alhaji.  “”Yauwa Bintun baba, daga yau idan an tura ki karatu ko aika ki rika dawowa da wuri ,ki daina tsayawa wasa a hanya, kuma ki daina zuwa dandalinma kinji ko?”Zaro ido tayi waje kamar an fada mata wani mummunan abu.”Babana to rawanfa?””Kiyi a gida .”Ya bata amsa a takaice.Watsa hannayenta tayi tace “Ai gidanmu ba kid’a.””To ki haqura da rawan ai ba dole bane, kuma ma karatu ya kamata kiyi ba rawa ba.”Ba tare da ta amsa ba ta maida kallonta kan Habibullah, da shi dinma ita yake kallo da mamakin yawan surutunta ba ko gajiyawa.”Lah baba, ina ka samo dan Hindiyawa?”Ta tambaya tana dubanshi sama da kasa.”Yayanki ne, yarona ne shima Bintu.””Tabd’ari amma aradun Allah, yayi bala’in kama da Hindiyawa.”Dariya yayi yace “A ina kikasan su.””A TBn gidan kansila nake ganinsu.”Zuba mishi ido tayi ba ko kiftawa kamar yanda shima bai daina kallonta ba.”Kai babana yaronnan akwai ruwan kyau.””Kema ai kina da kyau Bintuna.”Farfara ido tayi tace “Allah, Baba Alhajina, to dani dashi wa ya fi kyau.”Qasa2 tayi da murya “Allah yasa yace nafi shi kyau aga ruwan yanga a garinnan.”Dariya dukansu biyu suke mata dan sunji abinda tace.”Bintuna ai kinfi shi kyau, ya isa ma ya had’a kyanshi dana ‘yar Babanta.”Wani murmushi jin dad’i ta saki tana kara qarewa Habibullah kallo.Matsawa tayi kusa da shi tasa hanunta kan dimple d’inshi.”Kai baba alhajina yaronnan gasa yake so yayi dani, kaga tayani kyaunshi irin nawa.”Dariya Daddy ya kuma yi “Ai naki ya fi nashi kyau.”Cire hanunta tayi daga fiskarshi ta mayar  kan fiskarta tana shafawa “Ni kodai kama mukeyi da shine, ko da yake ma Baba yace nafi shi kyau, shi dogon fiska ne dashi ni kuma nawa bai kai nashi tsawo ba.”Suna kallonta tana ta zuba shirmenta sai kuma ta mike da sauri “Baba alhajina Barin je inyi fitsari.””To ‘yar baba, daga nan kici abinci duka.”Kafin ya karasa tayi nisa dan ba karamin gudu ta kwasa ba.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Cikin nitsuwa ta fito tamkar ba itace ta gama zuba rawan kai awanni da suka shud’e ba.Sake take da atamfa riga da zani sai d’an madaidaicin hijabi da ta saka light blue. Kafarta sanye da takalmin rubber.Hanunta rike da ‘yar ledar litattafan islamiyanta.Tsaf tsaf da ita kamar ba ita ce tayi butu butu d’azu ba.Nan inda ta bar su ta dawo ta samesu, kasan bishiyar mangoro, saidai ya ba suturar d’azu bane a jikinsu dukansu biyu.Kusa da Daddy tazo ta rusuna “Baba alhaji na d’azu na manta ban gaisheka ba , ina wuni ?””Lafiya lau ‘yar baba mun sameku lafiya.”Ba tare da ta amsa ba tace “Baba alhaji sai yanzu na samu na fito nan ma sbd zanje islamiya ne, ina fad’a maka innata ta b’aci da mugun hali kaqi ka yarda gashi ai ta fara nuna maka, daga barin je inyi fitsari in dawo ta rike ni ,saida naci abinci nayi wanka nayi sallah, ta kuma hana ni fita saida na kuma wani sallar kafin ta bar ni na fito.””Bintuna ki daina cewa innarki tana yi miki mugun hali so take ki nitsu, ki rika hutawa , yanzu baki ga yanda kika fito fess dake ba, kinga kyaun da kika qara kuwa?”Juya ido tayi “Allah babana?””Sosaima kuwa, yanzu dai tashi maza ki tafi islamiya idan kika dawo sai muci gaba da hirar mu ko?””To babana.”Ta fada tare da mikewa zata tafi.”Baba alhaji sai na dawo, yaron baba alhaji kaima sai na dawo.”Habibullah dake kishingid’e ya mike ya zauna “Tsaya in rakaki islamiyyar.”(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal.*🥀🥀🥀🥀🥀🥀    *5-10*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*G*aba tayi yana binta a baya har sukayi nisa.Can ta juyo ta kalleshi taga da rata tsakaninsu.D’aga muryarta tayi tace “Kai yaro, kayi sauri idan ba haka ba tafiyata zanyi in barka.”Sai kuma ta sauke murya tana cewa .”Hmmm, idan kayi wasa idan ban barka ka bata ba, babanka yayi ta nemanka babu abinda ya shalleni.Har ya iso kusa da ita mita take ta zubawa danjin haushin ya b’ata mata lokaci.”Kaga yaro, wlh yanzu kam idan bakayi sauri ba tafiyata zanyi, kasan abinda nakeso inyi ne kafin na isa islamiyyar, ko so kake yau ma a tareni latti.”Ta karishe maganarta tana zumburo baki tare da fara tafiya.Kamo hanunta yayi, “Wa kike cewa yaro?””Kai mana, to nasan sunanka ne, ba Babana yace kai yaron shi ne ba?””Idan ni yaronshine sai kema in zamo yaro a gunki, ganki yar mitsitsiya dake sai raini.”Kallonshi tayi fiska a daure, ganin shima nashi fiskar a daure tace ” to aini bansan sunanka bane.””Sunana Habibullah.””Tabb, Habibalah.”Tace tana rike baki.”Habibullah akace.”Ammafa sunan yaso yayi kama da na Abulahn gidan malam lawwalli.”D’aure fiska ya dad’a yi “Ke kika kuma b’ata min suna saina fasa bakinki.””Yi haquri, kiran sunan ba dole bane, kuma ma naga bani na tambayeka sunanka ba, kai ka fad’a ko?”Ta karishe da alamar tambaya.”Ko ba ke kika tambaya ba sai kin fad’a daidai, dan bazan zuba miki ido kina cemin yaro ko bata min suna ba.Suna ci gaba da tafiya tace “To kawai nace maka biba mana tunda sunan da tsawo, ni kuma ba iya wa zanyi ba.”Matse hanunta yayi da dan k’arfi har ta yi qara, “Kice Habi.””Habi.”Tace da sauri.Ya karasa da bullah.”Nanma ta maimaita.To had’a ki fad’a muji.”Saida ta d’an d’au lokaci kafin tace “Bibillah.””Ina kikabar harrufa biyu na farko, anya keko baffa ba asarar kud’in tara yakeyi ba?””Cabb, aka fad’a maka kud’in kirki yake ban ne balle yayi asara? Naira biyar ce fa, sai nayi sa’a ya bani goma wollah.””To lissafa min, a sati nawa yake kashewa.”Shiru tayi nad’an lokaci daga bisani tace idan lissafin biyar biyar za’ayi a sati ishirin da biyar ne, idan goma ne kuma ishirin da biyar sau biyu, kuma ai ba kullum yake bani goman ba nace maka.””Na wane ishirin da biyar sau biyu?””ishirin da biyar da ishirin da biyar.”Ta bashi amsa da full confidence dinta.”Idan an had’a goma da goma fa?””Goma sha goma.”Nanma ta bashi amsa.Nawa wnn?Ya tambaya yana nuna mata gudan ishirin.”shine ishirin din ai.””To idan an had’ashi da wani ishirin d’in fa?””Ishirin da ishirin mana.””Idan an had’a da goma fa?””Ishirin da goma.””Gyara dai.””To goma sha ishirin.””Ammafa ke d’innan wawiya ce ta gaske.”Fizge hanunta tayi daga rikon da yayi mata “Kai Bibilah ni kake cewa wawiya da girmana?”Duk da baiso yin dariya ba saida ya dara “Wai da girman ta.”Ya fad’a ranshi yana kuma murmushi.”Yi haquri babba, muje kada kiyi latti.”Gyara tsayuwa tayi tana fiskantarshi “Bibi, ai, Habi, ba nace maka akwai  in da zanje kafin na je islamiyyar ba?””Ina ne?””Can gurin bishiyoyin yazawan (cashew) nan ka gansu can a jere, sai na cira zan isa islamiya raka ni muje kaji.”Har wani langabe kai takeyi ita gata mai wayo.”Babu inda zaki sai kin iya kiran sunana.””Na shiganga.”Ta fada tare da d’ora hanu a kanta.””Yanzu duk kokarin da nayi baka gani ba? To qara fad’in sunan yanzu zan haddace.””Ha.bi.bu.llah.”Ya fada mata daddaya.”To me zai hana nace maka habu tunda yafi sauqi.”Zare mata ido yayi “Kinji nace miki Habu ne.”Kanta ta girgiza a tsorace tayi shiru kamar mai nazari, can tace “Habibi, dan Allah mu barshi haka ka rage min tsawon sunan.Maimaita Habibi yakeyi cikin ranshi can kuma ya kalleta “Sake fad’a muji.””Habibi nace.””Yauwa barshi haka ma yayi.”Da sauri tace “To zamu je? Sai ka hau ma ka cire min na huta hawa, ko mai shi yazo yau bazan gudu ba dan nasan kana da karfi, ka jibgar min shi sosai fa, dama haushinsa nakeji kullum mutum yaje ciran yazawa idan ya ganshi sai ya mishi masifa, hhhh, yau kam zaka jibgu Baba audu.”Ta fad’a har da d’an tsallenta.”Ta ina ne islamiyarku?”Ya jefo mata tambayar.Kaga wancan hanya? Da mun yanki kwanar can zakaga islamiyar an kewayeshi da karare.”Tana gama fad’i ya sunkuceta ba tare da yayi magana ba ya sab’a ta a kafad’arshi yabi hanyar da ta nuna.”Kai, Habibi saukeni kada ka cuce ni, yau idan ban sha yazawan nan ba bazan ci tuwo ba.”Ko kulata baiyiba, ya ci gaba da tafiya.Wuntsila kafafunta ta shigayi tana zamowa daga jikinshi.A haka yaci gaba da tafiya tana ta zille zille da surutai har ya gane islamiyar.Kofar islamiyar ya sauke ta ya had’e rai, “Maza shiga ciki kafin na kira malamanku su zane min ke.”Cuna bakin tayi ta shiga ji take kamar ta cijeshi ko zata huce takaicin da ya tura mata.Zama yayi a kan wani gungumen itace kusa da islamiyar yana ta kalle kalle, har suka tashi.mantawa tayi da cewa tare da wani take suka fito suna ta tsalle tsalle da qawayenta.”Indo Innarki tayi gullun suwa?””Eh tayi anjima zan kai dandali.””Muje ki ban rabona.””Ki bari mana bintu saimun fita dandali.””Allah yanzu zaki bani , ai kinsan ba ko yaushe nake zuwa dandaliba idan innata ta ganni hanani takeyi, jiya ma fa saida na sha duka da zagi da harara da rankwashi, ke innata muguwa ce fa.”Ta karasa tana rike hannun Hali dake gefen hanun hagunta.”Hali ke kuma me innarki tayi?””Hana baba tashi.”Hadiyar yawu tayi tace “Yauwa indo mu fara zuwa gidan su Hali muci hana baba tashi kafin mu wuce gidanku.Dadai sun karyi kwana zasu shiga lungun gidan su Hali taji an dawo da ita baya.A tsorace ta kalleshi  ta waro idanu “Dama baka tafi ba, me kake jira ?”Bai tankata ba yaja hanunta suka fara tafiya.” Mun shiga uku turawa sun shigo gari sun fara satar mutane, wayyo Allah.”Indo ta fad’a da k’arfi.Had’a baki sukayi dasu Hali suna kwala ihu “Jama’a ku zo ,ga bature ya saci Bintu.”Juyowa tayi tana dariya “Ku, kubari Habibi ne fa yaron Baba Alhaji, tare muka zo dashi yasin.”Jin ta fadi haka sukayi shiru suna kallonsu har sukayi nisa.”Nifa yau kana ta cutata, ka hanani shan yazawa, kace d’aya.”Biye mata yayi yace d’aya.””Ka hanani shan gullu suwa, kace biyu.””Biyu .”yace”Yauwa ka hana ni cin hana baba tashi, uku kenan ko? “Tun bata ji abinda zai ce ba tace “Dan Allah baka cuce ni ba Habibi.””Ban cuceki ba ke dai kika so ki cuci kanki, dan nasan idan kikayi dare duka zaki sha gurin innarki.”Dariya ta kwashe dashi “Kai yaro, ai Habu, wai,🙊 Habibi, ni fa bana cutar kaina da wayo na wlh, cin dad’i nakeyi son raina aradun Alla.””Meye ma sunanki.””Baka ji Babana yana ce min bintu ba.””Banda shi fa?””Na ainihin kakeso in fad’a maka?””Eh.””Na aininhin ainihin?”Ta kuma tambayarshi.””Eh, shi d’in.””Fad’imatu ko Fatsuma amma fa bintu ake kirana.””To ni Islam zan kiraki.”Wani wawan birki taci kamar wacce taji abunda ya tsoratata tace “Me? Islam, ban tab’a ji ba tunda innata ta haifeni, kuma itama tunda innarta ta haifeta bata tab’a ji ba nasan da ta fad’a min yasin.””Ba sai kin taba ji ba ni hakan zan kiraki wuce muje.”Cigaba tayi da tafiyar tana mita a hankali “A a ba Islam ba idan yaso islamiya, haka kawai ka qala min sunan da ban taba jiba, kamar ma ba sunan mutane ba.”Sai kuma tace “Amma dai sunan Hindiyawa ne ko?”” Ba a koya muku addini a makarantarku na boko?””Ana koya mana mana.””To ya kuke kiran subject din?””I R K.”Ta bashi amsa.””Menene full meaning na IRK.””Ni nasan maka wani pulmin, zaka ta min yaren hidiyawa ance maka ina ji ne?”Dariya yayi kadan yace “Turanci ni na miki ba indiyanci ba.””To mu ba’a koya mana ba.””Kina so na koya miki ?””Sosai ma , haba da anga ruwan yanga a garinnan wlh, yaro, au, Habibi sai wanda na ga dama zanwa magana aradu.”Dadai isowarsu kofar gidansu, ta fiskanceshi “Zaka koya min yanzu.””Shiga gida Islam maghriba ta gabato sai mun samu lokaci.”Ya fad’a yana duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hanunshi.”Turo baki tayi ta juya tayi hanyar shiga gida,” islo,” tace tana mai jin haushin sunan da ya qira ta dashi.Har ta shige gida yana tsaye yana kallonta yana murmushi.Gidansu da suka sauqa ya shiga ya tarar da Daddy yana shirin fita yayi alwala zaije masallaci.”Sannu daddy.””Yauwa Habibullah, kun dawo? ina yar tawa ?””Ta shiga gida Daddy, barin yi alwalar mu tafi tare daddy…..*Aunty Ruqayyat ce .*🥀*08161594233.*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Al’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal.*🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *10-15*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*L*abarin abinda Bintu tayi ya rika bawa daddy yana ta murmusawa, haka kawai yaji yarinyar ta shiga ranshi ,surutanta burgeshi sukeyi.Ita kuwa bintu da haushi biyu ta kwana, ga na Habibi da ya takurata ya hanata rawar gaban hantsi gana innarta da ta sa mata ido ta hana ta fita dandali, haka tana ji tana gani tayi bacci bata ci dad’i ba a cewarta.Washegari, bayan ta kammala shirin tafiya makaranta.Trayn silver mai ďauke da kwanon sha da kofuna sai kwanon sameera.Koko ne da kosai aciki.D’auka tayi tana tafiya a hankali gudun kada ya zube dan ya mata nauyi.Sallama ta rika kwaďawa da tsattsamar muryarta saida taga fitowar Habibullah ta daina kwaďa sallamar.Da sauri yasa hanu ya karb’i tray d’in yana cewa “Wnn bai fi qarfinki ba Islam?””To ba innatace ta bani na kawo muku ba…. Ina babana?”Jin bai amsa ba yasa ta kalleshi taga kokarin juyawa yakeyi.”Ina kwana Habibi.””Nayi tsammanin baki iya gaisuwa bane ai.”Kamar bata jishi ba ta sake ce mishi “Ina kwana.””Lafiya lau, ina jakar makarantarki?””Yanzu zanje in ďauko, ina babana nace?”Ta sake tambayarshi.”Yana ciki shigo ki gaisheshi.”Bata sake magana ba ta juya ta koma gida.Jakar makarantarta ta ďauko ta fito. Babannata ta gani a kofar gida ta gaisheshi, cikin fara a ya amsa yana sa mata albarka.”Yar baba za a tafi makaranta ko, Allah ya bada sa a , kiyi karatu sosai kinji?””To babana sai na dawo.”Habibullah taga ya fito yana kallonta, tun baiyi magana ba  ta fara nunashi da yatsarta tare da kankance ido, “aradu karkace zaka rakani, babu ruwana dakai, aradu tun jiya da dare fushi nakeyi da kai.”Dariya yayi yana mai ci gaba da kallon ďan karamin bakinta da take zumburowa.”Me ya haďaku yar baba?””Hanani cin dad’i yayi jiya baba kuma yace min wawiya, kuma ke ta cemin islam, babu ruwana dashi baba.””Yi haquri yar baba , bazai sake ba.””To baba shi ya bani haqurin mana, kuma yace bazai qara ba.”Kallonshi daddy yayi yana dariya “To kaji kanwarka tace ka bata haquri.””Yi haquri .”Yace a taqaice.”Kuma ba zaka qara ba?”Ta faďa cikin son ya jadadda mata hakan.Gyaďa mata kanshi yayi ba tare da ya sake magana ba.Dariyar jin daďi ta saki ta fara tafiya “Sai na dawo babana.””Yauwa, Allah ya tsare a dawo lafiya.””Ameen babana.”Saida tayi nisa kamar ance ta waiga bayanta taga Habibullah yana binta a baya hannayenshi soke cikin aljihun wandonsa.Bori ta fara mishi tana bubbuga kafafunta a qasa.”Bana so, bana so, bana so, ba nace kar ka sake kula niba?”Kusa da ita ya qaraso yace “Ba kince kina so na koya miki turanci ba?”Washe baki tayi tace “Eh, fa, na manta ne.””To in kinaso ki daina fushi dani.””Na daina .”Tace da sauri.””Ammafa nima zaki koyamin fulatanci.” Waro idanunta tayi “Kai da girmankannan baka iya fulatanci ba?””Ban iya ba Islam.”Haďa fiskarta tayi ta turo baki “Ba nace bana son sunan ba?””Bakya son turancin kenan.””Ina so mana.””Idan kina so dole ki amsa Islam.”Shiru tayi ta ci gaba da tafiya sai can tace “Allah da ba don inaso na iya turancin ba dabazan amsa ba.”A haka suka isa makarantar tana ta zuba mishi shirme.Naira ďari sabuwa qal ya zaro ya mika mata.”gashi kiyi break dashi.”Baya tayi tana ďaga hannayenta “Babu ruwana baffana ya hanani karban kuďin mutane.””Nine mutanen islam, niba yayanki bane, Habibinki nefa ni islam.””Ni dai ba ruwana sai na tambayi baffana.””Wato kinfi jin maganar baffanki akan ta innarki kenan.””Ai dan shi yana so na ne, baya duka na,  kuma ni ma ina son shi, nafi son shi kan innata. Kaga shi idan nayi laifi cewa yakeyi, Bintu me yasa bakya jin magana ne, me yasa kike haka ne, ki rika jin magana kinji, Allah ya shirya min ke, ita ko innata ….” kwafa tayi ta juya.”Sai na dawo Habibi.”Daga nan ta kwashi gudu ta shiga cikin yara ta fara picking.Ya jima yana tsaye yana hango ta daga nan har suka kare picking suka yi assembly, suka shiga classes ďinsu kafin ya wuce ya koma gida.Tab’o suke ta kwab’awa suna yin kananan tukwane duk sun yi kaca kaca da uniform ďinsu, suna gamawa suka hau yin đaki da jikakken yashi dake gurin da suke zazzaune.”Hure, Jiya ban ganki a dandali ba, na ajiye miki hana baba tashi har na gaji da jira na cinye kayana.”Cewar Hali dake lodawa kafarta yashi.”Ke, Hali baki san innata ba da munfurci, da ya musa ta haďani ya zauna a kofar gida da tsumagiya  ya hana ni fita, shima babban munafiki, watarana aradu sai na buďa mishi barkono a ido in wuce bai ganni ba ďan iskaro kai..”Kwashewa Bintu tayi da dariya ” ashe kema innarki ta iya muguntar, nima haka innata take min ta hana ni fita.”Cikin son qara tura musu haushi indo tace “Bakuji dafa tallen da Habi ta kai dandali jiya bane, shegen daďi gashi yaji manja da attaruhu, daďi sosai kamar ya tsinka kunne.”Kafin wata ta sake magana cikinsu suka an daka musu tsawa “Ku tashi ku wuce gida.”A tsorace duk suka tashi suna zare idanu, kowacce ta ďau jakarta ba bu wacce ta tsaya ganin mai korannasu ko wacce ta kama hanyar gidansu a guje.”Islam.”Cak ta tsaya tana kallonshi “Dama shi ya tsoratasu, ya akayi bata gane muryarshi ba.””Allah ya isanmu, tsorata mu da kayi , Allah ya isa nama ya gasu malam zo muci.”Buge bakin ta yayi yace “Wa kike yiwa Allah ya isa?””Allah ya isa ban yafe ba, tusan mariya babban wando.”Ta kuma cewa.Murďe bakin yayi ya sake kafin ya ce “Idan kika sake min Allah ya isa sai na fasa bakin, dama abunda kukeyi kenan idan an tashi makaranta shi yasa bakwa komawa gida da wuri?.”Rike bakinta tayi ta fara tafiya.”Me aka koya muku a makaranta?”Har zata yi mishi rashin kunya ta tuna har yanzu bakin bai bar yi mata zugi ba sai ta share tayi shiru.””Ba tambayarki nake ba.”Sake bakin tayi tana turoshi tace “To ba bakina yana min ciwo ba?””Yanzu da bakina kikayi maganar.”Dariya ta kwashe dashi kafin ta dab’ashe a kasa ta zauna ta kifa kanta kan cinyarta.”Meye haka kuma?”D’agowa tayi tace “Ďaya kukayi ku qara.”Tana kuma nuna mishi yatsarta ďaya.Da mamaki yake kallonta, itama kallonanashi takeyi tana dariya.”Habibi, kana ji, wani malaminmu ne kullum ya shigo ajin mu sai yayi bacci, idan ya samu karatu sai ya kifa kanshi kan benci, sai munyi har mun gaji sai ya ďago kai ya mana yanda kaga nayi nnan sai yace “Sau ďaya kukayi ku qara.”Ta faďa tare da kwaikwayon muryar malamin.Dariya ne ya ciyoshi yanayi tana tayashi.”Allah ya shiryeki Islam.”Bata amsa basa ta tsaya tana kallon yar karamar kaza tana tafiya tana tsiyau tsiyau.”Ayya iyarki ta tafi kogi.”Ta faďa da yanayi tausayi a fiskarta.Jin bata daina ba ta mata da fullanci “Mi vi ma iya ma dilli mayo.””Ke dawa kike magana?””Gata, iyarta take nema  na taimaketa na faďa mata ta tafi kogi kuma ko kula ni batayi ba.”Maida kallonta tayi kan yar tsakon ta sake cewa “Mi yetti, anani, miiyetti masin.””Me kenan kika ce?””Ce mata nayi na gode sosai.””godiyar me kike mata?””Na kin kula ni da tayi mana, gobe ma rana ce, aradu idan na ganta bazan sake kulata ba.””An ce miki taji abinda kike cewa ne?””Aradu suna jin magana, yasin haka innata tace min.”Dariya yayi kawai suka ci gaba da tafiya tana bashi labari har suka dawo gida.Shigarsu gida ba da jimawa ba ta fito da kwanon abinci a hanunta tana bin wata tinkiya  tana cewa “zo ki qarasa cegiya.”Tinkiya ko ganin tana mika mata ta dawo ta saka baki cikin kwanon ta ci gaba da ci.Ajiyye kwanon tayi cikin b’acin rai take cewa “A tappaka on, a tappaka mivi cegejo.” tana faďa tana huci.Itako tinkiya taci gaba da dabdala.Jibgegiyar sandarta ta samu ta kwaďa mata a baya cikin mugunta.”Assha.” taji baffan ta yace “Me ta yi miki haka yar baba.”Cewar daddy.Kallonsu tayi idanunta cike da hawaye sai kawai ta fashe da kuka “Abincina fa ta shiga madafi taci shine kuma da naji haushi na ce ta qarasa maimakon ta gudu ko taban haquri sai taci gaba da ci.””To ai dukan yayi yawa bintu baki ga tayi nauyi ba, haquri zakiyi mata ai dabbace bata da hankali?””Mayya ce babana idan ban mata haka ba in ta gama cinye abincin ni zata cinye, baku ga yanda cikinta yayi qato ba, cin maita takeyi.””To munji, je kice innarki ta baki wani abincin.”Ciki ta koma tana kunkuni da jan Allah ya isa, ita bata yafe ba.Dariya daddy yayi yana cewa “Bintu kenan, ga wayo ga wauta duk ta haďa .””Haka halinta yake alhaji wani lokaci haka zaka jita tayi ta magana da dabbobi kamar mai magana da mutum…..*Aunty Ruqayyat ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers.**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀   *15-20*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*B*ayan sallar azahar ta fito da yar littafinta 20 leaves da pen a hanu.Sallama tayi a kofarsu taji shiru, cikin gidan dake manne kusa dasu ta shiga da sallamarta.Kafin ta shiga ciki ta tsinkayo muryarshi yana hira da ďan gidan cikin ďakin bukkarshi.Bakin kofar ta tsaya ta doka sallama, suna fitowa ta ďaga littafin tana nuna mishi.”Habibi karatu zamuyi.””Ok.”Yace yayi hanyar waje ta bishi a baya.Tabarma ya shimfiďa musu qasan bishiyar da suke zama da daddynshi.Da alphabets suka fara yaga ta iya, sai suka koma two letter words, sun dau lokaci suna karatun kafin ya rufe  littafin yace su koma koyon fulatanci.”Dame za’a fara?”Ta tambayeshi.”Me ma kika cewa yar tsakon nan ďazu.””Miyetti?””Eh, shi “Mi yeti ko?””Miyetti zaka ce.””Miyeti.””Mi..ye..tti nace, kaga aradu idan kayi wasa zaneka zanyi kar kaga ka fini girma, malaminmu yace ba a girma wa karatu””To miyetti.”Yace yana dariyar maganar ta, dan har wani waige waige takeyi ita nan neman bulala takeyi.”Yauwa sake faďa.””Miyetti.””Again.”Ci gaba yayi da faďa ita ko ta kifa kanta kan cinyoyinta , sai can jimawa ta ďago tace “Sau ďaya kayi ka qara.””Ke na gaji.”Zaro mishi ido tayi “Haka ake karatun, mufa idan aka ce mu qara qarawa mukeyi.””To ni ba ku bane, mu ci gaba da wani kuma, yawwa me ma naji kike cewa tunkiyar can ďazu?.”Saida ta ďanyi jimm kafin tace “Oh, a tappaka?””Eh, me hakan yake nufi?””Ina nufin bata daku bane.””To kace a tappakan mu muji.”Haka yayi ta mata tambayoyi tana amsa mishi daga bisani ta buďe littafin tace yayi shiru zata yi kiran suna.Shirun yayi yana kallonta ta qarashi rubuce rubucenta can ta ďago tace “Fatima Barkinďo.”Da kanta tace “Present.”Sai tace “Habibi Barkinďo.”Jin yayi shiru tace “Aradu idan bakace present ba aspen zan sa maka.””Present.”Yace yana ci gaba kallon shirmen da take zanawa a book ďínta.Can tace “Halima Isuhu.””idan  ba tazo ba aspen zaka ce min.””Malamata tsaya in ďan miki gyara kaďan, ba aspen ake cewa ba absent ake cewa.””Absel?”Ta faďa cikin nitsuwa dan so take ta faďa kamar yanda taji ya faďa.Gyara mata ya rika yi har ta faďa dadai.Suna wajen har daddy da baffa suka dawo suka samesu, suka zauna a haka aka ci gaba da karatun har la’asar tayi.Innarta na shiga sallar isha i ta kwashi takalman ta a hanu ta sanďe ta fita.Saida ta ďan yi nisa da gida ta zuba takalmanta a kasa ta sanya, tana magana ita ďaya ” yasin yau sai na ci hana baba tashi, kuma dafa tallenma dani za a ci, haka kawai ayi ta cin daďi bana ci.Haka tayi ta surutanta har ta isa dandali.Ba a cika sosai ba amma mutane sun fara taruwa.Hankali kwance ta saki jiki suna ta zuba hira da kawayenta suna ta ciye ciye.Can ta hango baffanta yana zuwa wajen yana ta dube dube.Ta tabbatar da cewa ita yake nema.Wuff ta mike ta shige cikin mutane ta samu ta bar wajen ba tare da ya ganta ba.Gida ta nufa a guje tana suďe hanu sbd romon dafa tallen da bai gama fita daga hanun ba.A kofar gidan ta tsaya tana maida numfashi.A hankali ta leqa ta hango innarta zaune tsakar gida kan kujera yar tsuguno ta rabka tagumi, fiskar nan q murtuke.”Yau kuma muguntan sun motsa.”Ta faďa a hankali tare da kaucewa daga gurin.Jikin zanan gidan taje ta jinginu daga gefe, tana kallon duk masu wucewa.Ta jima tsaye a gun dan duk lokacin da ta leqa tana hango innarta bata bar gurin da take zaune ba.Baffanta ne yazo ya wuce cikin sauri hankalinshi tashe, tana jin yana faďawa innarta bai ganta ba kuma ance bata je dandali ba.Tana kallo innar ta fita ta shiga makotarsu, shi kuma baffa ya shiga gurinsu baba alhaji yana cewa bari ya duba ko ta shiga wajensu.Cikin sauri ta shige cikin gidan ta nufi ďakin da take kwana.Adakar da suke zuba kayan sawarsu “Irin akwatin karfe babba na mutanen da ďinnan.Ta buďe sauri sauri ta fitar da kayan ciki ta zuba ta bayan adakar, ta shige ciki taja kofar ta rufe ta bar ďan guri kaďan yanda iska zai rika shigo mata.Tana ciki ta jiyo muryar yayunta mata biyu da suke qure sun shigo tare da innar suna ta jajanta al’amarin.D’akinta suka shiga har da leka karkashin đan karamin gadon qarfen dake cikin ďakin.”Kai, na gaji da yawo aradun alla, yanzu dan Allah ina yarinyar nan ta shiga tun ďazu.”Babbar yayarta ta fada tana fifita da gyalen da ta yafa.”Allah dai ya bayyanar mana da ita cikin koshin lafiya.”Cewar ďayar tana kwance goyon ta.Motsi taji a bayanta yasa ta saurin waigawa, bata ga komai ba, hakan yasa ta haska tocin dake rike a hanunta.Babu abunda ta gani, yasa ta gyara zama suka ci gaba da jajantawa suna addua.Can kuma suka sake jin motsi, ďayar tayi saurin haska tocin.Ta gurin akwatin suka ji alamar motsin hakan yasa duk suka nufi wajen suna dubawa.Motsi sosai tayi cikin akwatin wanda yasa su kwalla qara dukansu biyu suna rige rigen fita daga ďakin.Ihunsu ya janyo hankalin su baffa da su baba alhaji da ke kofar gida suma suna maganar yanda zasu bullowa al’amarin.Dukansu suka ďuru cikin gidan a lokacin da inna ta taresu take tambayarsu abunda ya sasu ihu.Dakyar suka nitsu suka faďa mata motsi sukeji a ďakin Bintu.Da sauri baffa ya shiga ďakin  Habibullah na take mishi baya, dan ba karamin tashin hankali ya shiga ba da suka nemeta basu ganta ba.Gurin adakan suka isa baffa yana haska tocila, tsit suka ji daga baya kuma suka kuma jin motsin.Cikin dakewa baffa ya bud’e akwatin yayi saurin ja da baya.”Dan kwalinta ne ya fara bayyana, hakan yasa Habibullah, leka akwatin.Zuru zuru ya  ganta ciki tana ta raba idanu gata tayi sharkab da zufa.”Islam.”Ya faďa cike da mamaki .Kasancewar basu san sunan ba yasa baffa ya matso sosai yana tambayar “Menene aciki?”Abulle (zainabu) da Muna (Maimuna) yayunta  suka matso suma dan suga menene yake cewa islam ďin.Itako Inna tana daga bakin kofa.”Bintu.”Suka haďa baki wajen faďa.Dakyar ta mike ta fita ta fara murza idanu.”Me ya shigar dake cikin nan.”Baffa ya tambaya cike da mamakinta.”Bacci nayi Baffa.””Bacci?”Suka haďa baki wajen faďa.Fizgota innarta tayi cikin jin haushi tana cewa “Babu wani baccin da tayi fakon idonmu tayi ta shigo ni na tabbata wani gurin taje.”Ta karasa tana kai mata duka.Ihu mai qarfi ta qwala tana kiran innarta zata kasheta.Cikin azama Habibullah ya jawota ya maida ita bayanshi yana cewa “Inna kiyi haquri bazata sake ba.””Habibu da ka barta ta daku watakila ta yi hankali.””Baffa kuyi haquri.”Wuff ta fice da gudu ta tafi gurin baba alhajin da ke tsaye daga hanyar fita.Cikin muryar kuka tace ” Babana daga bacci ya kwasheni cikin adaka shine fa innata ta fara dukana.””To bintun baba me ya kaiki cikin adaka har kiyi bacci, duk kin ďagawa mutane hankali.””Baba kace kada ta dukeni bazan sake shiga ba.””Baza ta dukeki ba ai, ya wuce.”Ya faďa yana fita daga cikin gidan.Shi ma Habibullah fita yayi har lokacin baibar mamakin abunda islam ta yi ba.Suna fita yace “Daddy anya yarinyar nan lafiyarta lau kuwa, kaga inda ta shiga ta rufe kanta, ni fa ta bani tsoro.””Lafiyarta lau Habibullah ita kuma kalar tata yarintar kenan.”Jinjina kanshi yayi yace “Nata yarintar ya bambanta da ta sauran yara.”Dariya daddy yayi yace “Kar ka sha mamaki a samu wacce ta fita ma.”Tana ganin sun fita ta faki idon innarta ta shige ďakinta da gudu ta rufe kofar gararam.”Ke buďemu mu tafi gida fitinanniyar yarinya.”A tsorace ta kallesu “Me ya kawo da dare nnan nenne abulle.”Duka ta kai mata ta goce “da kika tasomu kika ďaga mana hankali dole kice me ya kawo mu ai.””Ku kuka so meye abin ďaga hankali, kunsan ni bintu bazan b’ata a cikin garinnan ba ai.””Sannu bintu min yetti.”Cewar Muna.Bata kulasu ba ta ďale gadon karfenta ta kwanta tana cewa “Idan kun fita ku rufe min kofa.”Innarsu taji ta shigo tana cewa “Kinyi sallah ne da kike kwanciya?”Wuff ta mike ta kama gefen zanin abulle, “Nenne abulle binki zanyi, aradu inna dukana zata yi kema kin san halinta.”Tana ganin innarta ta nufota ta fita a guje tayi kofar gida tana kiran “Nenne abulle kuzo mu tafi.”Nacewa tayi saida tabi abulle gidanta ta kwana.*Aunty Ruqayya ce.*🥀(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal.*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*25-30*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Z*aro idanu yayi yana kallonta shi duk a tunaninshi ko taji ciwo.Sai ganinta yayi ta mike tana kakkab’e jikinta, tana turo baki.”Kai ina ta ce maka ka tare ka tare saida ka barsu suka faďo baka tare ba, idan suka fashe aradu sai ka biyani.”Shi dai baice mata komai ba saima tunanin da ya fara yi kan maganar baffa da yace tana da aljanu.Bakar leda mai ďan girma ta fitar daga cikin zaninta ta warware ledar ta fara ďura mangoron a ciki.Kasan bishiya ya samu ya zauna yana bin bishiyoyin mangoro da ke gonar kallo.”Habibiii.”Yaji ta kira shi da qarfi.D’agowar da zaiyi sai ganinta yayi a bayan motar akori kura.”Islam!.”Ya faďa da karfi.”Na tafi wuro magaji sai na dawo.”Ta faďa tana waving ďinshi.Hannayenshi duka biyu ya ďora a kanshi yana faďin inna lillahi wa inna ilaihi ra ji uun.Yana kuma bin motar da kallo har ta b’acewa ganinshi.A kiďime ya dawo bakin hanya suka haďu da wani matashi yana tsaye yana b’abb’a ka dariya tare da kallon hanyar da motar su bintu ya bi, da alama wani abun dariyar tayi mishi.”Dan Allah ďan uwa ina yarinyar can ta nufa?”Ya tambayi matashin kamar zaiyi kuka.”Bintu, bintu, indai bintu ce anjima kaďan zaka ganta ta dawo.”Ajiya zuciya ya sauqe ya koma jikin wata bishiya ya zauna ya dafe kai.Addu a yakeyi Allah yasa ta dawo da wuri.Yana zauna anan la asar ta sameshi yaje yayi sallah yaci gaba da jiranta.Motar na isa garin magaji ta dira ta sauqa.A guje ta shiga gidan kanwar mamanta tana kiran “Inna Dija nazo.””Oyoyo Bintun Inna.”Innar ta faďa daga cikin madafi.Madafin ta nufa sukayi kicibis da inna tana fitowa daga madafi.”Inna jam b’andu.” “Jam bintu yaya innarki.””Lafiyarta qalau tace in gaisheki.””Inna ina Haulatu?””Tana bacci.”Da gudu ta shiga ďakin inna dije tana cewa “Ina ta tunaninta inna dije.”Jijjiga yarinyar ta farayi har saida taga ta buďe ido.Ďagata tayi ta jefa ta ta cab’e tana mata waqa (Haulatun Inna Dije na ta girma.”Tsakar gida ta fito da ita, yarinya sai binta takeyi da kallo.”Ina Altine Inna.””Tana gidan su Dijatu.”Da gudu ta fita rike da yarinyar inna tana ” Bintu kada ki kada min ita.”Tare suka dawo da altine.Suna shiga tace inna kin gama girki ne?””Bintu miya na gama saura tuwo.””Miyan meye kika dafa.””Karkashi.””Yauwa inna zubo min zan sha shi haka, innata tace kar na jima.”Zubo mata inna dije tayi ta zauna ta na sha tana lasawa Haulatu a baki.Tana gamawa ta tashi ta wanke hanunta.Daga haulatu takeyi tana dariya itama yarinyar tana babbaka dariya.Can tace.”Altine bari in jefo miki ita ki cafe.”Da gudu inna ta fito daga ďakinta, ko kafin ta iso har bintu ta jefa wa altine ita.Wani irin qara yarinyar ta tsanyara sbd zafin faďuwar da tayi ta dan altine bata samu ta cafe ta ba.Da sauri bintu ta je zata ďauketa inna ta rigata ta dauketa ta sa mata nono a baki.Dakyar ta samu tayi shiru.”Maza bintu koma gida kada dare yayi miki a hanya.”Ta faďa tana mika mata naira ďari.”Ki gaida innarki.”Hanun Haulatu ta rike, “Haulatu na kiyi hakuri, Altine wawiyace bata iya cafewa ba, baza mu sake wasan da ita ba kinji.””Jeki kedai Bintu ki gaisheda baffanki da innarki.””To.” tace ta fita tana tsalle tsalle.Wani shago ta shiga mai ďan girma, ta sayi babyn roba ÿar karama, da biscuit da sha ka hura.Cikin zaninta ta b’oye ta nufi gurin motocin da tasan zasu koma qauyensu.Daya ta tarar an loda buhuhuna, zata tashi, batayi wata wata ba ta ďale bayan motar ta kame ta b’are biscuit ďinta suna tafiya tana ci tana kalle kalle.Kasancewar sun iso bakin kogin motar ta rage gudu.Ganin bintu da yayi a bayan mota ya sashi mikewa tsaye da sauri.Dirowa tayi ta nufo inda yake.”Habibi ina mangoro na?”Ta fara ce mishi.”Ban sani ba dama kin bani ajiya ne?”Turo bakinta tayi ta nufi gurin da tabar ledar mangoronWayam ta gani babu komai.Wangale bakinta tayi zatayi kuka ta hango baba iliya da yaronshi suna zagaye gonar.Da gudu ta isa wajensu, tana haki tace “Sannu baba ina wuni.””Lafiya bintu yaya gidannaku?”Langab’e kanta tayi ta marairaice murya tace “Baba baka ga mangoron da na ajiye cikin bakar leda acan ba?””Dama mangoron naki ne?”Washe baki tayi tace “Eh nawane baba.””To wa ya baki izinin cirewa.””Um.am, baba baki mukayi shine nace bari in ciran musu mangwaronka masu zaki susha suyi santi su bada labari a garinsu.D’auko ledar yayi ya mika mata yace “Maza koma gida , kinga garin a haďe yake, kada ruwan sama ya sameki a hanya.””To nagode.”Tace tare da barin wajen da sauri.”Habibi mu tafi.”Tace mishi ta ci gaba da tafiya ledar mangwaronta rike a hanunta bata kuma damu da kallon expression da fiskarshi ta nuna ba.Har suka haye kogin babu wanda yacewa wani qala.Sunkuyawa yayi wa warware nad’in da yayiwa qafar wandonshi.Ya ďago da niyar ya ci gaba da tafiya sai ya ganta tsaye kusa dashi tana kallonshi.Warware babyn roba da sha ka huran da ta siya tayi daga bakin zaninta tana nuna mishi.”Habibi, kaga babyna da na siya zanyi wasa, karfa ka faďawa innata dan kwacewa zata yi ta hanani wasa da ita.Ga sha ka huranka da na kawo maka tsaraba, kar kuma kasa kwaďayinka akan biskin ďina dan na cinye duka ban rage maka ba aradu.”Kallonshi tayi jin bai amsa mata ba kuma bai karb’i sha ka huran da take bashi ba.”Me ye, yaya da kallon?””Ke zan tambaya meye kam ai.”Ya faďa yana banka mata harara.Haushi hararan ya bata.Ta takarkare ta gyara tsayuwarta harda rike qugu.”Mele da maleqata ya mele maka jan ido ka kasa ganin habbakar da rana da farin wata da tauraro guda bakwai.Kaji min Habibinnan fa ni ban ďurkite ka ba (Harara.) kai da ka bar min mangora a tsakiyar gona har mai shi ya gani ya ďauka kai zaka ďurkite ni, kaji min fa.”Ga abin dariya ga abin haushi ya rasa ma wanne zaiyi ďaya sai kawai ya kama kunnenta ya murďe “”Ke wani irin rashin ji ne yake damunki, yanzu da kika shiga motar mutane suka tafi dake da sun sace ki fa.””Wayyo Baffana.”Ta faďa tana rike hanunshi dake rike da kunnen.Sakin kunnen yayi ya fara tafiya ya jinta tana magana.”Motar kawujin ne zaka ce zasu saceni, mukam garinmu ba a satan mutane saidai in a garinku, kar ka mana fata umhum, kuma mun b’ata nayi fushi da kai kar ka sake yai min magana, kuma in ka sake ce min islam wuta bal bal, bullukutun bakar mutuwa.”Shi dai gaba yayi ya barta tana ta soki burutsunta, Alla alla yakeyi su koma gida lafiya kar ta b’allo mishi wata damuwar kuma.Ganin ya mata nisa ta ruga da gudu ta kamoshi amma ba magana bakinnan a ture, ita a dole tana fushi.Wake wakenta ta fara rerowa da fulatanci ta yi wannan ta sake ta kama wancan.Wasu gun gun shanukai ne suka tunkarosu, yana gani ya koma gefe can ya fara bin cikin ciyayi.Itako hijabinta ta cire ta saka ledar mangoronta a ciki ta ďaure  tagoya mangoron a baya.Cikin shanukan ta shiga tana wakewakenta tana tab’a duka wanda tabi kusa dashi.Saida suka gama wucewa kafin ya fito kan hanya.Dariya ta tuntsire dashi tana nuna shi “Habibi ase kai kulďo ne (Matsoraci ) ase haka kake da kulol (Tsoro.)Kallon yanda ta dage take dariya har da sunkuyawa yayi ya kalli sama yanda hadari yake kara haďuwa yace.”Ke, ki wuce mu tafi kada ruwa ya tare mu anan.”Haka kawai sai taji ba dadi da ya ce mata ke.”Ni ba sunana ke ba.””Ni bansan wani sunanki ba to kuma kince in na kira ki islam wuta bal bal…..Tun bai kare maganar ba tace “To kace islam ďin na yafe ka.””Ni kam mu tafi kada ki jaza min mura.”kafin su isa ko ruwa ya sako, gudu ya fara, ya juyo sai ya ganta ta ware hannayenta ta rufe ido tana tsaye ruwa na dukanta, sai dariya takeyi da alama nishaďi ruwan yake sakata.Dawowa yayi kusa da ita zai mata buďa mata wuta dan tayi sauri su tafi , sai kuma ya tsaya qare mata kallo.Dariyar da takeyi ya bayyanar da jerarrun fararen haqoranta, dogayen gashin idanunta suka jike da ruwa suka qarayin baki sidiq, sai cikakken bakin gashin girarta da ya kwanta lub.  ga lotsawar dimple ďinta wanda ya qara wa fiskarta kyau.Sai yau zai iya cewa ya tsaya ya kalleta da kyau, lallai ya yarda da maganar daddynshi da yake ce mata itama kyakkyawace.Ware idanunta tayi a kanshi sai kuma ta hau share fiskarta da ruwa yake zuba akai.Hanunshi tayi tsalle ta cafke tana lilo dashi, “Kai Habibi ya kaji daďin ruwannan.”Kawar da kanshi yayi daga kallonta “Sake min hanu ba kin ce mun b’ata ba kada in sake yi miki magana.”Sake shi tayi ta sauri ta ďaure fiska, “Ai nima dan na manta ne.”Waige waige ya farayi yana duba kasa.”Me kake nema?””Bulala.””Me zakayi?””Tsabgeki zanyi dan naga taurin kanki yayi yawa, KUNNEN K’ASHI gareki.””Banda duka kam Habibi kaji, mu tafi bazan sake maka taurin kai ba. Inji baffa na yace ni ‘yar albarka ne ko?”Shiru ya mata yana jan hanunta suna tafiya sauri sauri.”Kaga fa ban isa YUSA bafa gun inna kulu, a wuro magaji kawai na tsaya gurin inna dije.Kallonta yayi yace wani yusan kuma bayan wannan.”Yusan biyu ne fa, akwai yusa, A, Hab’e (“Arna ) su suka fi yawa a gurin, sai ka wuce wuro magaji zaka je wajen, idan kana zuwa daga jalingo kuma sai ka wuce wajen zaka isa garin magaji .nan kuma YUSA B. ne shi ake kira Yusan fulani.”Wonderfull.”Taji yace.”Hhhh Habibi ai ful da ful kam e ton wuro magaji. Nufinta ( wonderful yana garin magaji.)”Me kenan kika ce?”Fassara mishi tayi har da daddagewanta.”Wonderful nace ba ful da ful ba.”Ya fada yana dariya.”Oho, woldaful ai na iya ko?””Um, kawai yace mata suka ci gaba da tafiya, kafin su karasa ruwa ya gama jika su sharkab.Koda ta shiga gida inna tana mata faďa sai cewa tayi gurin inna dije taje kuma tace a gaisheta, tana faďa tana tub’e kayan jikinta ta saura da pant, har zata shiga sai ta dawo ta ďauki ledar mangoronta ta shiga dashi.*Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*30-35*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*D*a daddare, tare suka shiga da baffanta gurinsu baba alhaji tana rike da ledar mangoro da hanun hagu, hanun baffanta da hasnun dama.Suna isa ta gaida babanta ta ciro manyan mangoro nunannu guda uku ta ajiye mishi, tace “Baba alhaji ga tsaraba.””Ina kikaje.””Gona muka je ďazu da wannan.”Ta fađa tare da nuna Habibullah.Sauran biyu na cikin ledan ta mikawa daddyn tace “ka bashi idan na fita.”Dariya daddy yayi yace “Ba gashi kusa dake ba me yasa baza ki bashi ba?””Mun b’ata bamu magana baba, mangoron ma na bashi ne dan kar yace tare mukaje yana gani na cire ban bashi ba, Allah ya so shi ma ďaya ne kawai ya fashe da ko ďaya bazan bashi ba yasin.””Rike mangoron ki bana so, ai nima bance ki bani ba.”Matsowa tayi kusa da shi “Yi haquri habibi na yafe maka kasha kaji.””D’auki kayanki nace bazan sha ba.””To a andi Allah a waďa munyal mi metata.””Banjiki ba ai.””Nace in kasan Allah kayi haquri bazan sake ba.””Ba zaki sake me ba?””Taurin kai.””To kaji , tace baza ta sake ba.”Cewar daddy.”Yauwa kaji babana ma ya faďa maka, karb’a kasha kaji, da zaki aradu.Karb’an ledar mangoron yayi daga hanunta yana cewa “Sai ki kawo min ruwa na wanke kafin nasha.»»»»»»« »»»»»Sabo sukayi sosai har ya kasance yanzu cikin gidansu bintun suke karatu.Yau ta kama asabar kuma aranar zasu koma jalingo.Da safe sukayi karatu  kan tabarma, a cikin gidan su bintun.Innako tana ta kai kawo tana ayyukan gida.Saida suka kare karatu yace mata “Islam yau zamu koma gida.”Waro ido tayi tace  “Kace aradu.””Aradu.”Yace yana dariya.”Kace yasin.””Ke bana son shirmen ki nnan, meye wani aradu, da yasin kuma.””Rantsuwa ne mana.””Ana rantsuwa da wani abu bayan Allah ne banda shirmenki.””To meye aradu da yasin ďin.””Kin san tsawa da akeyi idan ana ruwan sama ko idan za ayi?””Na sani ba wnn giriri ďin ba?””Shi ďin dai, to shine aradu, idan kina yawan ambatar shi kuma hmm ni dai babu ruwana.””To me zai faru?”Ta tambaya tana watsa hannayenta.”Ni dai bazan faďa ba, ki daina fađa kawai.””Yasin fa.””Yasin sura ne cikin al -qura’ni mai girma.””Kace aradu yasin ba sunan Allah bane?”Zaro idanunshi yayi “Baza ki daina ba ko, ba ruwana fa.””Na daina to yasin bazan kuma ba.”Yar karamar tsaki yayi murmushi yana escaping lips ďinshi.”Islam zan yi missing ďinki, ke fa?””Na san maka shi?””Me ďin?””Misil ďin.””Missing nace miki.””To meye shi ďin ban sanshi ba.””Zakiyi kewata idan na tafi?””Kewa ? Meye shi?””Islam.””Na’am.””Ba zakiyi tunani na ba idan na tafi?””Tunani kai, Habibi har da mafarki ma.”Murmushi yayi yace “To shi nake nufi, idan na tafi zanyi ta tunaninki.””Yeah, Habibi, kayi ta tunani kar ka manta ni fa.”Ta faďa tana girgiza mishi yatsar ta manuniya.”Bazan manta ki ba islam, nima kada ki manta ni kinji.””Haha, Habibi, bazan manta ka ba ai, kaga kullum sai na tuna dogon hancinkannan, da wannan tayani kyaun irin nawa, zan rika tuna fiskarka, da dariyarka, da ďaure fiskar nan da kakeyi, da tafiyanka, da sa hanu cikin aljihunka, kai kai na manta har da tsoron shanunka hhhh.”Ta karishe da dariya.Dariyar shima yayi yace “Islam idan na  rokeki wani abu zaki yi min.””Zanyi.”Ta bashi amsa cikin saurin baki.”Dan Allah ki daina b’atawa inna rai, ki daina zuwa dandali, ko ba dan dali bama ki daina fita yawo idan ba aikanki tayi ba, ki daina wasa idan an tashi karatu, ki daina biye biyen gidan mutane, kuma ki rika karatu sosaifa.””Kai Habibi ka rage mana yayi yawa.”B’ata rai yayi “Babu wanda zan rage a ciki idan bakiyi niyyan bari bane ki faďa tun yanzu.”Marairaicewa tayi tana kallonshi “Ni dama dan kar kazo ace maka nayi wani abunne kace banji maganar ka ba shi yasa.””Bakiyi niyar gyarawa ba kenan.””Nayi zan gyara.””Yauwa my islam, I love U.””Taďari, aradu ba don yau zaku tafi ba da sai na rama zaginnan, haka kawai dan zaku tafi sai ka antaya min zagi, haka ranar ma naji ka ka faďa kyaleka kawai nayi aradu, ka jima kana zagina da turanci ina haquri, idan ba zagi ba me yasa da na tambayeka abunda ka fada kaki fassara min kamar sauran?.””Rama zaginki  islam.””Ni dai na yafe.””Ni kuma ban yafe ba sai kin rama.””A lob yu ma Habibi kai ma kaji inda daďi.””Yauwa kinga mun tashi one one kenan babu wanda ya kwari wani .””Habibi .””Na’am Islam.””Yaushe zaku sake zuwa?”Zamu zo ai, ko zaki bimu ne?Washe baki tayi sai kuma ta ďaure fiska.”Kana ji ba, Habibi, da ba don baffa na ba da binku zanyi ko dan na huta da dukan da innata takeyi min, kaga yayana mudassiru da ya koma gidan kawunmu a jalingo ya huta da duka ai.””To muje kema kiyi karatu a can mana.””Taďari, in tafi in bar Baffa na, aradu na fi sonshi a kan kowa ma, bazan biku ba yasin.”Kallo inda inna take yayi, ta kawar da kanta tana harkokinta tamkar bata jinsu.Kusa da ita yaje ya tsuguna ya mata sallama kafin suka fice tare da Islam.Gurin Baba alhaji suka je suka sameshi tare da mutane , daganan suka wuce gidajen relatives ďinshi ya musu  sallama suka dawo.Saida taga tafiyarsu kafin ta shiga gida tana sharar kwalla.Daga ranar kuma kayan da baba alhaji ya kawo mata tsaraba su suka zama kayan sawarta, sai innar tayi da gaske take sa wasu.Hirar Habibi kuma duk inda ta zauna sai ansan labarinshi.Kusan kullum sai yakira baffanta sun gaisa ya kuma ce a bata wayar su gaisa, tun tana tafka mishi qauyanci a wayar yayi ta dariya har ta saba, a hakan kuma yake kara mata karatu.A b’angaren Habibullah ma haka abun yake , kullum sai sun sha labarinta a gida, daddy ma har qara basu labarin wasu daga cikin shirmenta yakeyi suyi ta dariya.Yayarshi Nafeesat dake zaune da mijinta da ‘ya’yanta biyu a Owoniyi quarters duk da ba tare suke ba, amma tasan labarin Islam.Wani lokacin idan yaje gidanta har gaisawa sukeyi da ita ta waya.Saida suka kara watanni uku kafin suka kuma zuwa YUSA.Wnn karo Islam (Bintu) tasha tsaraba fiye da yanda ta saba samu daga guri baba alhaji, murna kuwa kamar ta goya Habibi takeyi, labari na kirki, shirme har da na wofi duk ya shasu.Wnn karo kwana uku sukayi suka koma.Daga baya ya zamanto ko daddy baice zai je ba Habibullah yana zuwa ya wuni ko ya kwana, wani lokacin tare da yar shi Nafeesat suke zuwa su zaga dangi.BAYAN SHEKARA BIYU.Cikin tashin hankali daddy ya fito yake kwalawa Habibullah kira.A tsorace ya fito yana amsawa, tare tambayar daddyn ko lafiya dan ya ganshi duk a hargitse.”Yi maza ka shirya yanzu zamu tafi Yusa, Baban yarinyar nan ya rasu.””Wace yarinya daddy.”Ya tambaya gaban shi na faďuwa.”Bintu, yanzu Malam Husaini ya kira ni ya sanar dani rasuwan.””Inna lillahi wa inna ilaihi rraa jiuun.”Ya furta yana juya kai cikin alhini.”Jeka Habibullah, kwana uku zamuyi sai anyi uku zamu dawo.”Da sassarfa ya shiga ďakin ya fara shiri.Haďa kayanshi yakeyi amma tunaninshi na ga islam, wani hali take ciki yanzu? Ko me take ji cikin zuciyarta, ya tayi da ya rasu.”Har ya kare shiri tunanin da yakeyi kenan.Lokacin da suka isa sun tarar an kaishi,sai jama a suka tarar cike a kofar gida, mata kuma sai ďuruwa cikin gidan suke, wasu daga kauyukan da suke makwabtaka dasu ma suke zuwa.Nan suke jin cewa lafiya aka rabu dashi jiya da dare ya shiga gida bayan sunyi sallar isha’ i dashi kafin asubah Allah ya amshi kayanshi.Hankalinshi ne ya gaza kwanciya dan baiyi tunanin zai iya jira zuwa  anjima su shiga ciki  kamar yadda daddy ya ce ba.Can dai ya tab’o Ila wanda suke kusan sa ‘o’ i dashi dama shine abokin hiran in yazo garin duk lokacin da islam taje makaranta.”Mu shiga ciki Ila ina so inga Islam.”*Aunty Ruqayya ce*🥀(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*35-40*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*S*higa sukayi sukabi duk inda matan suke tare suka gaishesu.Har cikin đakin inna suka shiga suka sameta suka gaisheta.Ilan ne ya tambayi inda Bintu take.Kwance suka sameta cikin ďakin baffanta, yayarta Abulle zaune kusa da ita.Rungume take da rigar baffan a jikin ta ta kudundune jikinta gu ďaya.Gaisuwar da yayi wa abulle ce ya sa ta tashi da sauri tana kallonshi, shima ďin kallonta yakeyi cikin tausayawa , fiskarnan tayi jazir, idanun duk sun kumbura, da ka ganta kasan ba qaramin kuka ta sha ba.Tausayinta ne ya daďa kama shi, tunawa yakeyi da lokacin da take ce mishi tafi son baffanta kan kowa, ganin baffan yakeyi yanda yake tasata gaba yayi ta kallonta cikin nuna tsantsar soyayyar da yake mata, irin kulawar da yake bata, da yanda idan tayi laifi ko ya mata fada sai ya koma lallashi, gashi yau mai rabawa ta raba, mutuwa ta ratsa tsakanin bintu da baffanta,Lallai Allah ba ya bari wani dan wani yaji daďi.Allah yaji kan baffa yasa ya huta.Baisan sanda kwalla suka fara kwaranyo mishi a fiska ba.Fashewa ta yi da kuka ta rarrafo ta zo ta ďora kanta jikinshi “Habibi baffa ya tafi ya barni, sun ďaukeshi sun tafi dashi sun binne shi cikin qasa,   jiya da daddare fa yace min zai je Yusa A ya nema min makarantar gaba da primary, amma yau ya tashi ya mutu ya tafi ya barni.”Sai ta kuma fashewa da kuka har kamar zata shiďe.Ba shi kadai ba Abulle da Ila ma duk tayata kukan sukeyi , dan dukansu shaida ne a kan irin shaquwar dake tsakanin bintu da baffan.Babbuga bayanta yakeyi kaďan kaďan yana share hawaye.Dakyar murya a shaqe ya iya ce “Hakuri zamuyi Bintu, Allah da ya ďauke shi ya fi mu sonshi, kowa kuma lokacin shi yake jira, baffa kam saidai mu bi shi da addu’a, Allah yaji qanshi ya sa aljanna ce makomarshi, Allah ya kyautata makwancinshi.””Amin.”Duka suka amsa banda bintu dake ta shessheka.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Har akayi uku jinyar Bintu da lallashinta ake dan duk lokacin da abun ya faďo mata sai ta birkice musu.Sosai baba Alhaji ma yake kokarin ganin ya kwantar mata da hankali.A lokacin da zasu koma Habibullah ya shiga cikin gidan domin sallamarsu.Lokacin jama a sun watse sai yan uwan inna da na baffa, mata uku, yayarshi ďaya da kannenshi mata biyu.Dukansu suna cikin ďaki sai Bintu dake takure jikin zana tana ta sharb’an kuka, Abulle tana gindin murhu tayi jugum, sai Muna da ke wajen wanke wanke, dukansu kallo ďaya zaka musu kasan suna cikin tashin hankali.Kusa da bintu ya matsa ya sunkuya, “Mene ne kuma Islam?”Cikin kuka tace “Ba goggo Rabi ce tace zata tafi dani ba, kuma zata bawa yaronta yunusa ni ya aura, kuma tace bazan sake karatu ba.Shiru yayi zcyrshi na bugawa, can kamar an mintsine shi ya mike ya fita cikin sauri.Cikin tashin hankali yake faďa mishi abunda Islam ta faďa mishi ya qare da “Yanzu daddy haka zamu barta ta tafi da ita watakila taje tayi ta bata wahala, tunda ta tab’a ce min matar bata son innarta bata sonsu, duk lokacin da tazo sai tasa innarta kuka.Shiru daddy yayi yana nazarin maganar Habibullah.”To ya zamuyi Habibullah, watakila haka Allah ya tsara mata rayuwarta.”Kamar zaiyi kuka yace “Daddy dan Allah kayi wani abu akai, ka roki baffanayentannan su bamu ita mu tafi da ita tayi karatu a can.””Habibullah su fa basu barin yaransu suyi karatu sosai, kaga itama zaiyi wuya su barta ,gashi ma kaji har sun fara maganar yi mata aure daga yanzu.””Daddy yarinyar nan baza ta wuce 12 yrs bafa, idan akayi mata aure zata cutu.””Hakane Habibullah, amma ai kaga su haka sukeyi, baka ga yayunta ma ba,ba wani girma ne dasu ba, amma kaga har da yaransu.”Guri ďaya ya kafawa ido Kamar mai tunani yayi, cikin sauri ya ďago ya kalli daddyn.”Daddy to a ďaura auren dani, kaga sai mu tafi da ita kawai tayi karatunta a can.”Shiru daddy yayi a ranshi yana cewa “Tarihi zai maimaita kansa kenan.”A fili kuma sai yace “To idan akayi airen yaya zaka yi da ita, dan nasan tausaya mata kakeyi.”Daddy har da sonta ma inayi, ka nema min auren kawai.”Ya faďa cikin rawar baki.Ajiyar zuciya daddy ya sauqe yana tunanin ya samu wata dama da zai tankwara Habibullah ya tafi karatu, ga kuma ladan taimako.”Habibullah, zan nema maka auren Bintu, amma da sharaďi .”Da sauri yace “Faďi sharaďin daddy komai wahalarshi zan bi.””Ba wani mai wahala bane, sharaďin shine zaka  tafi makaranta kamar yanda na buqata tun farko.””Daddy! Yafaďa yana zaro ido.”A a ba dole bana Habibullah, idan baka so shi kenan sai a haqura kawai a aurar da ita ga wani.”Da sauri yace na yarda Daddy zan tafi makarantar.”Ma sha Allah, Allah ya tabbatar da alkhairi.”Yace kafin ya bar wajen ya tafi gurin iyayen bintu maza.Bai wani sha wahala sosai ba suka amince mishi dan dama sun sanshi suna sane da mutunci da alkhairin da yake yiwa ďan uwansu, shi yasa suke mutunta shi.Cikin gidan suka shiga dan sanar da mahaifiyar yarinya da sauran yanuwa.Dukansu sun ji daďin maganar banda goggo Rabi da goggo Rahi.Shi yasa da suka fita suka hau zagin inna kan cewa ta nuna tafi son bare akan su dan taga yana da kuďi, shi yasa ta mallake musu ďan uwansu ta hanashi qara aure  dan idan ya mutu ta gaji shanukanshi, gata ba haihuwar kirki takeyi ba, shekaru goma sha tara da aure ‘ya ‘ya huďu kacal.”Zagi dai kala kala, su kam sai kuka sukeyi, suna tuna baffansu.Ďaga tafiyar sukayi.Washe gari aka ďaura auren *Habibullah Muhammad Bello*Tare da.*Faďimatu Barkinďo*Akan sadaki dubu Ishirin.Habibullah kam ya rasa wani yanayi yake ciki, dan farin ciki yanayi saidai ya rasa gane abunda yake faďar mishi da gaba, daga baya ya alakanta hakan da zuwan auren a bazata ne ya sa yake jin hakan.Makwabta da suka ji labari sai shigowa yima inna barka sukeyi.Shirye shiryen tafiya akeyi ,inda aka sa goggo Rabi da inna Dije zasu bisu a cikin mata, su ko maza baffanta wan babanta ne zai je.Neman bintu akeyi ta fito tayi wanka su tafi abin mamaki aka neme ta aka rasa.Nemanta aka shigayi gida gida sbd tunanin ko bata so ta rabu da innarta ne yasa ta gudu ta b’uya.Gidajen qawayenta duka saida akaje amma suka ce bata shigo ba.Yayunta gidajensu suka koma suka duba, Abulle har da leka kasan qado dan ta san ba abin mamaki bane Bintu ta makale a wajen,nan ma shiru.Habibullah har gonar mangoro da suka je da ita ranannan saida ya je yayi ta duba saman bishiyoyi, amma babu ko alamunta.Lokaci guda labari ya karaďe kauyen cewa Bintun Marigayi Mal. Barkiñďo ta b’ata, abunka da kauye tuni aka hau shigowa gidan dan tabbatarwa.Wasa wasa har yamma ana abu ďaya babu labarin bintu.ŤIRQASHI.Wai ina Bintu ta shiga ne?”*Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*40-45*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*M*utuwa kam ya dawo musu sabo dan tuni aka fara koke cikin gidan.Shima kanshi daddy ji yake kamar yayi kukan, idan ya tuna yau kwana uku da rasuwar bawan Allah, ‘yar shi kuma ta b’ata, inna ke bashi tausayi dan yasan babu wanda zai kaita shiga damuwa.Gefe đaya kuma ga Habibullah da ya zamo tamkar marar lafiya yayi yawon neman Bintu har ya gaji.Tafiyar da ba’a yishi ba kenan a ranar.Washe gari, ďaukan mudassiru yayan Bintu yayi yace suje garin magaji gidan inna Dije ko can ta tafi.Daga gurin sukayi ta bin gidajen ‘yan uwan Bintu da suka san zata iya zuwa.Daga baya suka fara shiga qauyukan da ke kewaye da Yusa, inda suka san zata iya shiga.Har Jambutu, kauyen da goggon Bintu take aure saida suka je, duka dai shiru ba labari.Har akayi bakwai Bintu bata dawo ba, ba kuma labarinta, inna tun  tana haquri tana nuna kawaici har ta gaza , duk lokacin da ta kalli ďakin bintu ko wani a bu na bintu sai tayi kuka.Haka kuma duk shigowan da Habibullah zaiyi cikin gidan sai ta fashe da kuka.Faďin irin damuwa da Habibullah ya shiga b’ata lokacine dan har gizo Bintu take mishi.Ko da yaushe fiskarta yake gani ko tana dariya, ko ta cuno baki yanda ta saba yi mishi.Wani lokaci kuma har jin muryarta yakeyi cikin kunnuwanshi tana yi mishi magana.Babu abunda yake ďaga mishi hankali idan ya tuna ranar da take ce mishi zata bi baffanta, tana so ta je ta ganshi.Tsoro ne yake shiganshi idan ya tuna da hakan.Lokacin da tunanin ya fara faďo mishi saida ya nemi Ilu suka tafi makabartar da aka binne baffa, a tunaninshi ko zai ganta a wajen.Duk wani gurin da ya tab’a bi da bintu idan yaje sai ya tsaya yayi ta tuna shirmen da ta tab’a tafka mishi a wajen.Yakan tuna yanda take kama hanunshi ta ďangale tana lilo.Duk lokacin da tunani ya faďo mishi sai ya bi hanunshi da kallo , wani lokacin har yayi ta rike hanun, yana jin kewarta na ratsa shi.Bayan bakwai sauran mutane suka watse, sosai sukayi ta kukan rashin baffa da na bintu, a ranar goggonayenta da pendonayenta duk suka koma gidajensu.Mudassiru kawai aka bari da inna dan ya rika ďebe mata kewa.Dakyar  Habibullah yarda ya bi daddy ya suka koma da zummar zasu dawo ba da jimawa ba.Lokacin da suka sanar da mummyn Habibullah ba karamin mamaki tasha ba na auren bazata da akayi mishi, saidai b’atar da akace yarinyar tayi ne yasa bata nuna hakan ba, sai addu’ar da tayi na Allah ya bayyanata.Masallatai da makarantun Allo daddy yake zuwa ya nemi taimako addu’a Allah ya baiyan bintu , ya kareta a duk inda take.Saukar Qur’ani yasa ake tayi mata da sadaqa.Kayan abinci kuwa sosai daddy ya haďa ya bawa driver aka kaiwa Inna.Suma can qauyen basu cire tsammani ba, kullum cikin nemanta suke, kowa mamakin b’acewarta yakeyi lokaci guda babu labari, kuma babu wanda ma yace ya ga lokacin da ta fita.Sati biyu suka qara suka koma, wnn karo har da Mummy da Nafeesa, suka je sukayi ta’aziya tare da jajen b’atan Bintu.Wuni guda sukayi suka koma.*1 month later.*Zuwa wnn lkc Habibullah yaje Yusa yafi a kirga, ya shiga qauyukan da bai tab’a tsammanin zai shiga ba akan Bintu.Duk da har yanzu bai cire rai da ganinta ba wata rana amma fa ya karaya.Addu’a kuwa yi yake ba dare ba rana.Ya zama wani sukuku dashi.Tun Mummy na mishi faďa har ta gashi ta zuba mishi ido sbd damuwar da ya sa kanshi.Ko fita yayi idan yaga yarinya kamar bintu sai ya tsaya ya kalli fiskarta, gani yake babu mamaki ya ganta a cikin jalingo ,tunda tace a kwai gidan kawunta a nan.Computer business center da ya kallafawa rai, yake hana shi karatu, ko yaushe yana wajen ma yanzu ya daina zuwa, ya bar wasu suna kula da wajen.A da bashi da burin da ya wuce kullunlm ya ganshi yana sarrafa computer, dalilin haka daddyn shi ya buďe mishi wnn gurin, amma daga baya shi kanshi daddyn saida buďewan ya dameshi, sbd yanda ya makalewa gurin ko yaushe yana gurin, baya yarda ko da wasa wani abu ya nisanta shi da gurin, hakan ya sa yaki tsayawa yayi karatu mai zurfi dan a cewarshi abarshi da ilimin computer da yake dashi ma ya isheshi.Dan bayan ya kammala sec. Sch, certificate yayi a computer, daga nan kuma daddynshi ya buďe mishi business center, har training na wasu sukeyi a gurin.Saidai a yanzu baya sha’awar ko zuwa wajen computer centern har mamaki daddynshi yakeyi, ashe akwai abinda zai iya ďauke hankalin Habibullah daga computer.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Kwance yake kan cushion hanunshi rike da wayarshi yana kallon hotunan da yayi wa bintu a qauye, wasu hotunan ma idan ka gansu sai kayi dariya sbd styles ďin da tayi wajen ďaukansu.Wasu kuma kwalliyar da ta cab’awa fiskarta ne zai baka dariya.Sosai hotunan suka fito kamar a kirata ta amsa.Kare kallonsu yayi ya koma kan videos.Muryarta tar tar yake fitowa gata ta fito rass kamar ya janyo daga cikin wayar ya ganta a zahiri.Kan wani videon da ya mata ya tsaya yana kallo, shine first vedion da ya fara ďaukanta.Sanye take da zani da riga na atamfa, ta ďaura ďankwali irin ďaurin asetta ďinnan, hijabinta kuma ta cire tayi ďamara dashi.Waka take rerawa da fulatanci tana rawa, a dole ita tana koya mishi rawa.D’aukanta yakeyi yana dariya ba tare da ta fahimci abunda yakeyi ba.Saida ta qare tazo kusa dashi tana maida numfashi take ce mishi ya tashi ya gwada rawan taga ko ya iya.”Zo ki gani.”Yace mata yana nuna mata wayar.Zaro idanunta tayi lokacin da ta ganta cikin wayarshi tana tikar rawa, ga kuma muryar ta dake fitowa rass daga cikin wayar.Baya ta koma da sauri.”Habibi wani irin madubi ne wnn?”Ta tambaya tana nuna wayar.Jin baiyi magana ba ta matso kusa dashi tana leka wayar, still ita ďin ta gani cikin wayar.”Amma Habibi mayu ne suka ďauki kamannina suka shiga cikin wnn abin ko?”A ina ka sameshi, wa ya baka?”Ta tambaya da ganinta a tsorace take.””Waya ce fa islam ba madubi bane.”Matsawa baya tayi tana hararar shi tace “Mannawa kanka hauka, an ce maka ban san waya bane, baffa nama yana da waya fa, wnn qaton abun maitan ne zaka ce min waya?””Zo ki gani mana, da gaske waya ce.”Ta bayan shi ta dawo ta tsaya ya sake kunna mata tana gani.tsalle tayi ta dire.”Aradun alla, Habibi wnn maitane, yasin nafi qarfinku namana da ďaci baza ku iya ci ba.Ta karishe tana cije harshenta .Dariyar shirmenta yakeyi bai ankara ba ta wafce wayar sai jinta yayi tace “Bismillahi, wa makarun makaran kubbara.”Wai ita a dole tayi addu’ar mayu.”Jefawa zan yi a kogi su tafi can suje suci kansu Bintun baffa tafi qarfinsu.”Tana faďin haka ta ruga a guje ta nufi hanyar kogi.Ganin da gaske takeyi ya rufa mata baya yana kiranta, haka suka rika gudu.Sai ya kai hanu zai kamota ta zille , haka sukayi ta zagaye tana ce mishi ya barta ta jefa mayu cikin ruwa.Dakyar ya samu ya cafkota suka zube a wurin dukansu suna maida numfashi.Karb’an wayan zai yi ta maidata ďaya hanu ta b’oye a bayanta, ya sake ta sake maidawa ďaya hanun.””Islam ina tausaya miki ne fa, idan karfi zan gwada miki kinsan wayarnan baza tayi second goma a hanunki bako?””Kafin ka gwada min karfin bari kaga, da karfinta tayi tsalle…..*Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*45-50*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*J*ifa zatayi da wayar ya yi saurin cafkewa “Ke Islam kina da hankali kuwa?””Garau aradu, zan koya musu hankaline, kaima ďin yanzu ban yarda da kai ba tunda kakeson zama dasu.”Su wa kenan?””Mayun mana.””kina nufin nima mayenne kenan?””Eh, mana kasan ni bana tsoron mayu . Idan nace wa makarun makaran kubbara babu abinda suka isa su min.””ashe ke zan fara cinyewa kenan.””Ni, Bintu, yasin nafi qarfin maitanka.”Tana gama faďa ta sake cije harshenta, ta shiga kwance hijabinta daga ďamaran da tayi dashi.Dariya abunnata yake bashi, wai ita a dole ta cije harshenta kada mayu su kamata.Har ta juya zata tafi, ta fasa ta dawo da baya tana cewa “Aradu bazan cuci Baba alhaji ba, sai na nuna mishi wnn abun mayun yasan abunda kake aikatawa.”D’aga hanunshi mai wayar yayi sama yace “Zo ki karb’a ki kai mishi.”Tsalle takeyi da iya karfinta ita sai ta kwace wayar shi kuma yana mata dariya. Cire wayar yaji anyi daga hanunshi da gaske, hakan ya dawo dashi daga tunanin da ya lula.Tashi yayi zaune ya maida kallonshi kanta.”Sister yaushe kika shigo?”Shafo hawayen da ya gangara daga idonshi zuwa kunnenshi tayi, bayan ta kalli abunda yake kallo a cikin wayar.”Habib ashe haka kake? Kana namiji kana yin abu kamar mace, baza kayi haquri ka fawwalawa ubangiji al’amarinshi ba.Kada ka manta da saninshi komai ke faruwa, shine masanin gaibu, abunda kakeyi bashi zai bayyanata ba, kasawa zcyrka hakuri da dangana, In Allah ya yarda zai bayyanata , mu dai fatanmu Allah yasa tana hanu mai kyau.””sister baza ki gane bane, ce min tayi fa zata bi baffanta, tsoro nakeji wani lokaci zcyta na raya min watakila bata raye.  Idan kuma tana rayen akwai abun da nake tsoro ne.”Saida ya ďan ja fasali yaci gaba da magana.”Sister, islam tana da wani habit wanda yake bani tsoro, yarinyar nan da kike gani kina tare da ita baza ki ankara ba sai ki hangeta kan machine ko cikin mota, bata da tsoro sam, a hakan sai ta bisu taje wani qauye ta dawo, ina gudun ta faďa motar mugaye su cutar da ita, yanzu Allah ne kaďai ya sani ko tana raye ko bata raye.”Ya qarasa maganar cikin karaya.”Hakuri zakayi Habib muna nan muna addu’a Allah ya bayyanata, dan Allah ka rika cin abinci ko zaka yi kyan gani, rayuwa baza ta tafi a haka ba.””Na gode sister, ina yaran?””Suna wajen mummy, dama na shigo in duba ka ne na tarar da kai kwance kana kuka kana murmushi.”Ta karishw maganar tana murmushin yake, dan sosai damuwar ďan uwanta yake damunta.Tare suka shiga wajen mummy suka haďu da yaran akayi ta chapter, sai bayan isha’i ta koma gida.Sosai suke kokarin ganin ya kwantar da hankalinshi, daga daddy Mummy har Nafeesa, shi kanshi addu a yakeyi Allah ya kawo mishi sauqi a cikin lamarinshi.Dan shi kanshi bazai iya cewa ga takamammen abunda yakeji game da ita ba, kawai dai yasan yana azabtuwa da rashinta.Akai akai suke zuwa yusa, kuma har yanzu basu bar nema ba kamar yanda dangin  Bintu ta gefen uwa da uba basu daina nemanta ba.Kayan abinci kuma ko wani zuwansu sai sun loda ma inna har itama tana bawa makwabtanta.Duk da yana kokarin hana kanshi damuwa tunaninta nanan cikin ranshi, ranaku ďaďďaya ne kuma zai kwanta baiyi mafarkinta ba.A kwana a tashi ba wuya, b’atan bintu ya kai wata biyar yanzu.Yanzu haka sunje qauyenne kamar yanda suka saba, saidai da drivernsu suka je sbd shiga kauyukan da sukeyi idan sunzo yasa daddy ya bada shawarar su dinga zuwa da driver.Gurin bishiyoyin yazawan da take maitan hawa a ko da yaushe yaje ya tsaya, hanunshi soke cikin aljihunshi.Kallon bishiyoyin yakeyi ďaya bayan ďaya.Gani yake kamar zai hangota saman ďaya daga cikin bishiyoyin.Ya jima yana tsaye a gurin har ya gaji dan kanshi ya kamo hanya ya dawo gida Kasan bishiyan mangoro da suke zama nanma ya tsaya yana tunanin abubuwan da suka wuce, wnn karon tunanin ba nata ita kaďai ba har da na Baffanta.”Indo da Hure ne suka fito daga gidan inna suna sharar kwalla ya bisu da ido. Dan suma duk lokacin da suka shiga wajen inna sai sun fito da kuka.Binsu yayi da kallo har sun ďanyi nisa sai ya bi bayansu da sauri, sunayensu ne bai rike ba sbd haka sai ya ďaga murya yace “Sannunku.”Tare suka juya suka kalleshi, indo ce tayi karfin halin ce mishi “Sannu Habibi.”Wani iri yaji dan ya jima ba a kirashi da sunan ba sai yau.Murya a shaqe ta gaisheshi itama Hure ta gaisheshiRasa abunda zai ce musu yayi kawai sai yace musu ya gode su gaisheda mutanen gida.Yana tsaye yana kallonsu har suka b’acewa ganinshi,Sabuwar damuwa ne da tunani suka shige shi hakan yasa shi kasa barin gurinYana nan tsaye har Ila ya zo ya tadda shi.”Habibu yaya ka tsaya anan kai kaďai.”Cikin sanyin jiki ya kalleshi na ďan lokaci kafin yace “Ila, anya Islam tana raye kuwa?””Haka muke fata Habibu, zo mu shiga   ciki.”Ya faďa da niyar basar da zancen.D’akinsu na cikin gidansu da daddy ya shiga shi kuma Ila ya shiga gidansu da niyar yin wanka.”Islam, ina kika shiga?me yasa kika tafi?Ina kike yanzu?Yaushe zaki dawo garemu?Dani da inna muna muna buqatarki Islam ki tausaya mana ki fito.Bana fatar ya zamo kin bi baffanki da gaske kamar yadda kike faďa.Allah yasa kina raye islam.Allah ya bayyana mana ke cikin koshin lafiya.”Surutan da yake tayi kenan shi kaďai wanda sha a tunaninshi zancan zuci yakeyi, saida yaji drivernsu ya amsa da amin kafin yasan cewa a bayyane yayi maganar.A sanyaye ya tashi ya shiga wanka.Yana fitowa yayi arba da Ila dake zaune yana jiranshi.Kafin yayi magana Ila yace .”Habibu nazo da wata shawara.”Kusa dashi ya isa ya zauna yana kallonshi “Wace irin shawara Ila?””Akwai wani qauye dake ta cikin kunini yana gaba kaďan da kuni gurin da muka je kwanaki, duk da dai zaiyi wuya ace ta shiga wajen dan qauyen yana ciki sosai ne, ko za mu gwada dubata a wajen.”Cikin zafin nama ya mike, tashi muje Ila, daga can ma zamu tambaya idan akwai wani ta ciki duk zamu shiga.”Amma da ka bari sai gobe muyi sammako Habibu dan qauyen yayi ciki sosai, nima kaina ba sosai nasan qauyen ba, sau ďaya na tab’a raka wani abokina yakai aika.”Muje kawai idan ya kama kwana ma zamuyi a wajen. Ko a cikin mota sai mu kwanta idan yaso goben muci gaba da nemanta.Hakan ko akayi suka kama hanya, Driver da Ila a gaba dan ya nuna mishi hanya , shi kuwa Habibullah yana baya, sai kallen kallen hanya yakeyi ko Allah zaisa ya hango ta.Quarter pass four suka shiga cikin qauyen, basu b’ata lokaci ba wajen fara cigiya tun daga farkon qauyen.Har suka shiga ciki, saidai duk tambayar da sukayi sai a ce musu ba a san wata mai suna bintu ba.Daga baya gidaje biyu aka kaisu aka nuna musu wasu masu suna bintun amma sai suka ga ba ita bace.Sun kare duk kwatancensu sai a ce musu ba a ganeta ba.Tambaya sukayi aka nuna musu wani qauye kusa dasu, nanma suka shiga kusan magriba.*Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*50-55*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*D*rivernsu ne ya tsaya ya fita yaje yin fitsari. Ila zaune a gaban mota yana jiran dawowarshi.Shi kuwa Habibullah fitowa yayi ya jinginu da jikin motar ya harďe hannayenshi yana bin ko ina da kallo.Kamar a cikin mafarki ya hango mai kama da Bintu ďauke da kirare a kanta.Sanye take da wasu koďaďďun kaya ta ďaure itacen da hijabinta.Saidai wnn baqa ce, kuma tayi rama da yawa.Tafe take tare da wata yarinya kusan kansu ďaya, itama kiraren ne a kanta, saidai da alama masifa mai kama da Bintun take suburbuďawa ďayar.Goge idanunshi da yaji kamar suna mishi dishi dishi yayi , ya runtse ya kuma buďe su.Suna daďa matsowa kamannin bintu yana bayyana a jikin yarinyar.Runtse idanunshi ya kuma yi ya buďe, ya sake goge su a karo na uku.Tabbas wnn muryar bintu  yakeji take zuba surutu da tsattsamar fulatancinta.Kamar ance ta đago kai, tana ďagawa taga wanda bata zata a yanzu ba yana tsaye ya kafe ta da ido, ko a bacci aka tashe ta ko cikin magagi babu abinda zai hana in ta ganshi ta ganeshi.Cakk ta tsaya tana kallonshi kamar yadda shima yake kallonta. Ko maganar da abokiyar tafiyarta take mata bata jinshi.Gizo take min ko mafarkin da na saba ne.Ya faďa cikin ranshi.Jifa tayi da kiraren da ke kanta ta nufe shi da gudu.”Habibiii.”Ta faďa daidai lokacin da ta rukunkumeshi.Marin fiskarshi yayi da kyau yana jin kamar ba a gaske bane. Fiskarta ya ďago ya kalleta da kyau kafin ya rungumeta sosai kamar zai maida ta ciki.Bai ankaraba sai jin hawaye yayi suna sintiri kan fiskarshi.”Habibi, wa ya faďa muku ina nan?”Ta fada cikin kuka.Share fiskarshi yayi kafin ya ďago fiskarta yana share mata hawaye.Cikin wani irin murya yace “Islam, ashe zan ganki?”Ila da tun da ta iso gun ya fito daga motar yake kallon ikon Allah yayi saurin cewa “Alhamdulillahi, Habibu ku shiga muje kawai.””Ma sha Allah, driver ma ya faďa cikin farin ciki dan tunda ya iso ya gansu rungume da juna ya gane itace suke nema.”Bintu to njata?”(Bintu ina zaki je?”)Suka tsinkayo muryar abokiyar tafiyarta tana fada lokacin da taga zata shige cikin mota.”Yauwa tsaya Habibi ku jirani ina zuwa.”Tace tana fasa shiga.”Jira a ina? Common get into d car.”Cewar Habibullah ya na maida ita.”Yauwa ka tunamin zamu ci gaba da karatunmu ko Habibi.”Ta fada tana shigewa fikin motar.Shiga tayi ta zauna kafin tayi kwafa “Da ka barni na je na sameta ai ta faďi yaren garinsu.”Sai ta qara da cewa.”Yaya Ila ko waďi on yeccai  yam on warai  heb’a mi tappa Fa’i ďo ba mo wujji mota.”(Yaya Ila ya baku faďa min zaku zo ba samun in daddaki Fa’innan kamar  wacce saci mota.”Dariya Ila yayi yana tambayar ta me tayi mata, lokacin har sun fara tafiya  sun bar yarinya sake da baki , saida taga sunyi nisa ta ruga da gudu tayi cikin gida tana ihun an sace bintu.”Hmm, O Nafikijo.”(Munafukace.)Ta bawa Ila amsa. Kafin ta ci gaba da cewa “Yaya Ila ina su inna ta  su yakumbo, (Mamanshi)Su Nenne Abulle adda Muna.”Sai jera mishi sunayen mutane take tayi.Shi ki yana ta amsa mata sunanan cikin tsan tsan farin cikin sa’ar samunta da sukayi.Tallabe hab’a yayi yana kallonta , a ranshi yana tuna babu a bunda ya ragu a halinta na surutu.Kallonshi tayi taga yanda ya kafe ta da ido ta rufe fiska tana dariya.Hannayen duka biyu ya rike yana kallonta .”Islam me ya kawo ki nan ? Ya kika yi kika zo?.”Juya idanunta tayi tace “Ance maka ni na kawo kaina  ne, nima kawo ni akayi.”Wa ya kawoki?””Ba goggo na bane tasa yaronta ya kawoni.”Cikin mamaki yace “Wace goggon ?””Goggo Rabi mana.””Ila, ba da matar nan akayi ta neman islam ba, kusan ma tafi kowa nuna damuwa a wajen, kana ji kuma wai ita ta ďauketa.””Nima kam abun ya bani mamaki Habibu.””Hmm, lallai sanin zcyr  mutum sai Allah, to nan ďin gurin wa ta kawoki?””Ba fa ita ta kawoni ba , yaya yunusa tasa ya kawoni gidan wata mata Innawuro, wai kawartace, tunda nazo gidan tace ni zan rika dafa musu abinci , da nace mata ban iya ba, tace haka zan koya wai idan nayi aure wa zai dafa min, har da shara da wanke wanke ďiban ruwa, da ďebo itace duka inayi, kuma kasan waye mijin?””Um, um.””Ka sani mana Habibi, ba ranar na fađa maka ba, yaya yunusa ne fa, shima yana zuwa wai gurina yake zuwa, yana kawo min kayan kwalliya da man shafawa har da turare, ka san me kuma?  Innawuro bata barina nayi kwalliyan sai yaya Yunusa yazo wajena sai inyi wanka inyi kwalliya ta fesa min turare mai kamshi .”Haushi ne da takaici suka haďu suka mamayeshi, idan ba jahilci ba tana sane da aurenshi a kanta take turo ďanta zuwa zance wajenta.”Wai ma idan yazo wajenkin me yake ce miki.””Kaga idan yazo, gaisheni yakeyi, sai yace goggona tana gaisheni, kuma sai yace min, innata ma tana gaisheni. Wai tace inyi haquri wasu mutanene suke so su sace ni shi yasa aka kawoni nan aka b’oyeni, idan sun gaji da nema na sun daina zuwa za a maida ni sai muyi aurenmu, na haifa mishi kyawawan yara kamar ni.””Shut up.”Yace a tsawace saida ta razana.Hakan kuma bai hanata cewa “Kaima shatap.”Qasa2 ba.”Wai haka idan yazo kike zuba mishi surutu.”Ya tambaya yana tsattsareta da ido.Kawar da kanta tayi tace “Amma dai kaima Habibinnan, an ce maka bani da kunya ne, ance maka idan ana zance ana kallon juna ne? Haka nakeyi , kalla ka gani.”Juya baya tayi ta bashi Qeya taja ďankwalinta tana rufe fiska, tace “Haka akeyi, idan mutum yace yana sonka sai kayi ta b’oye fiska, idan banyi haka ba ai sai a ce bani da kunya, kuma ma wa yake yiwa mijin da zai aura rash.. .””Ke ya isheni haka.”Ya dakatar da ita cikin b’acin rai.Ila da driver sai dariyarsu sukeyi, shi yake tambaya idan ta bashi amsa kuma yaji haushi.Zumb’ura bakinta tayi ta maida kallonta waje, tana ta kunkuni.Shiko banda tafasa babu abinda zcyarshi keyi, faďi yake a cikin ranshi lallai matar nan bata da hankali, a tsammaninta zai gaji da neman Islam ne ya haqura kenan ta aurawa ďanta .’yar qaramar tsaki yaja ya kuma cewa “To waima tayaya kika fita daga gidan har kika tafi babu wanda ya ganki?”Banza ta mishi tamkar ba da ita yake ba.”Islam ba ki ji ne?”Nanma ko kallonshi bata yi ba.Matsowa yayi kusa da ita ya kama fiskarta ya juyo da ita ta fiskanceshi “Ina magana kin min shiru baki ji na ne?”Kwace fiskarta tayi ta sake juyawa.Kamo fiskar ya sakeyi yana kallonta , yanda ta haďe ran sai yaso ya bashi dariya ya dake.”Kina so ki sha mari ko?”Shafa fiskarta tayi, kamar ya riga ya mareta ďin ta kalli fiskarshi  taga yanda ya haďe rai, cikin rawar murya tace “To me nayi?””Baki ji tambayar da nayi miki ba?””To, to, ba itane ina bacci da daddare a ďakin baffana taje tasheni tace in zo zata aikeni, shine nace mata zan faďawa innata sai tace min, innata tayi bacci idan na tasheta kanta zaiyi ciwo, shine ta kaini waje wajen yaya yunusa tace na hau machine ďinshi in bishi zan karb’o mata saqo ne, shine da na hau kuma sai ya kawoni nan.””Ila kaji ko, tsabar munafurci dare dare ta sa aka tafi da ita kuma tafi kowa nuna damuwarta.” Ya faďa cikin tsantsar jin haushin matar kamar ya ganta alokacin ya gaggaura mata mari.”Habibu ni ina tunanin ma da ba don ya kamata innarta tasan an ganta ba, da wucewa zakuyi kawai kada kowa yasan an ganeta.””Yanzunma za mu iya yin hakan Ila nasan idan mun roki inna bazata bayyana maganar ba.””Hakan za a yi.”..*Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJ*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*55-60*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*C*ikin kunini sukayi sallar magriba da Isha’i.Daga nan suka sayo balangu da minerals.Kin ci Bintu tayi ita a dole tana fushi da Habibinta.Saida ya haďa da rarrashi, nanma saida Ila yasa baki snn ta yarda ta fara ci.”Amma Habibi wnn ba naman akuya bane ko?Nifa bana cin naman akuya idan naci tayar min da saďaure yakeyi.””Ba shi bane Islam.””Kace aradu.””zan miki karyane.””Na yarda to, amma fa naman nan kamar yaso yafi na wuro magaji daďi kaďan.””Kina cin balangun wuro magaji ne?”Ila ya jefo mata tambaya.”Sosai yaya Ila, sai kaji daďi kai mutuminnan ya iya gasa nama, da wuta fa yake gasawa.””Dariya suka sa mata dukansu.”Habibillah yace “Dama akwai inda ake gashi da ruwa ne?””Oho, na sani? Yaya Ila inajin harda Kafi zabuwa aka daka yajinnan.”Ta fađa tare da jefa tsokar nama bakinta.Ta bayanta Habibullah yakai hanunshi ya tareta yana dariya, “Ila ba sai ka bata amsa ba na sa mata waigi.””Habibu kasan abinda ya ban dariya ?””Sai ka faďa Habibullah yace.””Wai fa tace bata cin naman akuya, kuma naga naman akuyar suke sayarwa a garin magajin.”Da sauri tace ” Hunu a viya   aradu yaya ila.”(Rantse Kace aradu)”Hakkunde am be Allah.”(Tsakanina da Allah.)Ya bata amsa.”Kai ammafa Dauda ya cuceni, amma na yafe mishi.””Duk dai ke kaďai.”Habibullah yace.Tsula gudu suke tayi yayin da Bintu ta fara Hamma alamar bacci zatayi.Can ta fara gyangyaďi.Haskata Habibullah yayi da wayarshi yace “Islam Bacci.””A’a nikam ba bacci nake ba inajin duk abinda kuke cewa.””To me akace yanzu.””Nidai na sani ba sai na faďa ba.”Ta faďa tana qara zuba Hamma.Sai qarfe 9:47 suka isa qofar gidansu Islam, lokacin tayi nisa da bacci.Dakyar ya tasheta ta tashi suka fita daga cikin motar, tana tambayarshi wai sun iso ne? kofar gidan suka nufa tana ta murza idanunta. Su Ila ko gidansu suka nufa suka barsu anan dan basu so hankalin mutane ya dawo garesu.”Sallama ya kwaďa, daga ciki Inna ta tambaya waye.”Habibullah ne inna.”Cikin sauri ta taso tana cewa “Allah yasa dai lafiya.”Inna buďe Bintuce.”Bintu ta fada cikin zumuđin jin muryar innarta.Ai inna har tuntub’e takeyi wurin zuwa buďe kofar tana fatar Allah yasa abunda taji da gaske ne.Tana buďewa Bintu ta fad’o jikinta ta kankameta.”Bintu ase zan ganki?Ashe kina raye.”Inna ta faďa cikin kuka.”Inna mu shiga daga ciki.”Cewar Habibullah.Ciki suka shiga bintu na maqale jikin innarta.Har cikin ďakin inna suka shiga suka zauna “Habibu ina ka samota?””Can wani qauye inna ni banma sunan qauyen ba.”A tuni Bintu ta amshe zancen ta fara zubawa inna bayani, nan ta sanarwa inna cewa goggontace ta sa aka kaita qauyen, da zuwan yunusa da duk karairayin da yake shera mata.Daga baya kuma ta shiga tambayarta labarin ‘yan uwanta da qawayenta.Sosai Inna tayi mamakin goggo Rabi, “in ba rashin hankaliba yarinya da aurenta ki ďauke ta ki b’oyeta?””Inna waye me auren?”Bintu ta tambaya.Basar da zancen tayi da cewa “Sannu Habibu Allah ya maka albarka, Allah ya biya maka buqatun ka sannu da kokari.””Amin, inna nagode.””Inna dama nace ko gobe zamu wuce da islam ďinne, kuma in so samu ne kada kowa yaji har sai goggon tazo a ji abunda zata ce game da rashin ganin bintun.”Ya faďa yana sosa tsakiyar kanshi.”Babu komai Habibu, duk yanda kayi daidai ne, amma sammako zakuyi ko?””In sha Allah.””Habibi Ina zaka kaini kai kuma?””Gidanmu zan kaiki gurin Baba alhaji.”Cikin murna tace “Harda Baffana ma zan gani.”tausayinta ne ya rufesu dukansu kafin inna tayi magana Habibullah yace “Islam, wanda ya riga ya mutu baya dawowa, addu’a zamu bishi da ita, dan itace gatanshi a yanzu kinji.”A sanyaye ta gyaďa kai ta tashi ta fita daga ďakin inna, duk sun ďauka wani abin zatayi sai ji sukayi ta tura kofar ďakin Baffanta ta shiga .Kallon inna yayi itama shi ďin ta kalla.A sanyaye ya mike ya shiga ďakin ya sameta ta haďa kai da gwiwa tana kuka.”Yanzu bazan sake ganin baffana ba?”Ta tambaya lokacin da yaďago kanta yana share mata hawaye.”Kiyi haquri Islam, ki kwanta kiyi bacci kinsan gobe sammako zamuyi.””Da innata zamu je?””A,a zamu fara zuwa dake in yaso daga baya inna ma taje, kuma har makaranta za a saki a can kiyi karatunki yanda kikeso.”Zaro ido rayi tana murmushi “Kace aradu Habibi.””Allah da gaske nake, kiyi karatunki, gaki ga Habibi ga kuma Baba alhajinki, kuma harda wasu sabbin qawaye ma zaki samu.”Saida yaga ta saki ranta har tana dariya snn ÿa fita daga ďakin yana mata saida safe tare da jaddada mata ta kwanta ta huta.Inna ko har ranta tana jin daďi tare da godewa Allah da hukunta Habibullah ya zamo miji ga Bintu, dan ta lura shi zai iya da shiriritarta, sosai take jin daďin kulawar da yake bata.Haďa kayanta inna tayi itako har ce mata tayi ta haďa mata da litatafanta, na koyon haďa bakin hausa da na english wanda Habibi ya saya mata, tana kuma jaddada mata a saka mata kayayyakin da baffanta ya ďinka mata.Da asubah inna ta tasheta tayi sallah, tana idarwa ta kai mata ruwan wanka da ta surka da ruwan zafi.Kokon da ta dama kawai suka sha suka kama hanya tun gari bai gama wayewaba.Daddy Habibullah ya kira yace mishi yana zuwa da wani surprise kada ya fita.Tun bai faďa ba jikin daddy ya bashi anga Islam, sbd haka farin ciki ne ya mamayeshi ya zauna zaman jiran isowarsu.Tun daga bakin gate Islam ta saki baki da Hanci tana kallo har aka wangale musu gate suka shiga.Fitowa daga cikin motar ma aiki ne, a take taji tsoro ya shige ta, saida yayi da gaske ta yarda ta fito.Rike hanunta yayi suka nufi cikin gida, itako babu abinda takeyi sai bin harabar gidan da kallo baki sake.A tsorace take gaba ďaya ko magana ta gagara yi har suka isa kofar palourn mummy.Sallama yayi mummy ta amsa.Da gudu ya idasa shiga palourn ya rungume mummy yana cewa “Ku tayani murna mummy na ganota.”Wani dumm mummy taji, sbd haka ta fara sassauta rikon da tayi mishi, tana kakalo murmushi yake.”Congrats son, ina take?””Kuttuse, aradu da wayona ba za a cuceni, yusa daret no gargada zan koma.”Bintu ta faďa daidai lokacin da ta leko da kanta cikin  falon.Shi kuma alokacin ya juya dan nunawa mummynshi ita dan shi duk a tunaninshi tana biye dashi a baya.Da gudu ta kwasa iya qarfinta tana mai burin ganin ta bar gidan.Da sassarfa ya biyo bayanta yana kiran sunanta, ganin da gaske takeyi ya sashi fara gudun shima yana cewa Bala mai gadi ya rufe kofa dakyau kada ya barta ta fita.Daddy da ya fito ya hangota a guje, kafin yayi magana yaga Habibullah ya take mata baya shima agujen.Dariya yayi yana cewa “Aiki ya sameka Habibullah.”Saman gate ďin ya sameta ta haye sbd samun shi da tayi a kulle,  kara hawa gate ďin takeyi kamar ‘yar biri dan niyyar dira ta baya takeyi, taji ya cafkota.Wani irin gigitaccen qara ta saki wanda ya tilasta Bala toshe kunnuwansa.”Ka sakeni, ka sakeni take cewa  tana ta mutsu da harba kafafu.” Ki nitsu mana Islam.”Ya faďa a tsawace.Fashewa tayi da kuka tana cewa “Aradu na gano wayonka. Yasin komawa yusa zanyi bazan shiga wnn guri ba, dama shi yasa goggona ta b’oye ni dan ta gano ka na so ka sace nine ka kawo ni gidan yankan kai, Wamakaru makaran kubbara, Wallahu gaalibun alaa amrihi.”addu’oi ta shiga jerawa duk wanda yazo bakinta yinshi takeyi tun bata qarasa ba sai ta cafko wani…. *Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*60-65*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*W*a ya tab’a min Bintun Baba, Habibullah kaine ko?”Ta tsinkayo muryar Baba Alhajinta.Cakk ta tsaya da kukan kamar anyi ruwa an đauke.Ta kuma bar buge bugen da takeyi.Ganin haka yasa Habibullah sauqeta tako dira da sauri tana kallon Baba alhajin.Share fiskarta ta shiga yi tana smiling.”Baba alhaji dama nan gidanka ne?””Gidanane Bintu yanzu kuma ya zama gidansu Bintun baba ko?”Dariya tayi ta riko hanunshi tace “Ni na zata gidan yankan kai ya kawo ni aradu, kuma da da qafa zan koma yusa, nasan zan gane hanya , kuma idan na fara gudu daga nan bazan tsaya ba sai na ganni cikin gidanmu, kasan mufa ance mana ana satar mutane a cikin gari irin wnn.”Tana maganarne suna ci gaba da tafiya har suka iso kofar falon.Ganin tiles shimfiďe sai walkiya sukeyi ya sata fara ďangale kafa tana tafiya cikin sanďa.”Yaya Bintu muje mana.”Zamewa zanyi babana, muje a hankali.”Dariya yayi yace “Baza ki zame ba muje.”Duk wnn abunda sukeyi Habibullah na biye dasu a baya.Suna isa tsakiyar falon ta taka center carpet taji uban laushi, cikin sauri ta dab’ashe a gurin.”Yaya haka Bintu, karasa ki zauna kan kujera mana.””Nanma yayi babana.”Ta faďa tana danna lallausar carpet ďin da yatsunta.Kamota yayi yace “zodai ki karasa.”Ya faďa yana kamo hanunta tare da mikar da ita.Mikewan tayi ta bishi har gurin kujeru, ta tsaya tana binsu da kallo.Kusa da Habibullah taje ta ďosana tana kallonshi tace a hankali “Idan kaga zan zunduma ciki ka riko ni Habibiii.”Bai tankata ba saida yaga ta zauna shima a hankalin yace “Ki zunduma mana ina ruwana.”Kwafa tayi ta maida kallonta gurin baba alhaji tace “Ina kwana babana.””Lfy lau bintun baba ya kika baro  innarki?””Habibii ba tace maka ka gaisheshi ba kayi shiru kana ji yana tambaya.””To kuma ni ya tambaya ne?”Bata tanka shi ba sai maida hankalinta da tayi kan mummy “Sannu Hajjajo ina kwana?”Mummy da ta saki baki tana kallon ikon Allah tace “Sannu ‘yanmata.””Innata tace Habibi ya gaisheku shi kuma yayi shiru bai faďa ba.””Muna amsawa.”Suka ce Daddy ya qara da “Mungode.””Habibu ina aka ganota ne, ashe da rabon zamu sake ganinta.””Wai dama b’arayin haka suka ce muku baza ku sake ganina bane?”Ta tambaya tana binsu da kallo.”Daddy da bai fahimci zancen ba yace “B’arayine suka saceta habibullah?.””Baba alhaji nifa ba b’arayi ne suka sace ni ba, goggona ce ta b’oyeni dan kar b’arayi su saceni. Kasan abinda yasa nayi tambaya?”Um um, daddy yace yana kallonta.”Kaga lokacin da Habibi ya ganni can qauyen da goggo ta b’oyeni, sai naji yace “Ashe zan ganki islam.”Ta faďa tana kwaikwayon muryarshi.”Snn Innata ma da ta ganni tace ashe zan ganki Bintu.”Itama ta kwaikwayi muryarta.Da ci gaba da cewa “gashi kaima kace ashe da rabon zaku ganni, shine nayi tsammanin ko dama b’arayin sunce muku baza ku ganni bane.”Kwaikwayon muryoyinsu da tayi ne ya basu dariya, shi kuwa habibullah kokarin gimtse dariyar yakeyi dan Ya nuna mata fushi yakeyi da ita sbd haka sai ya wayance da cije leb’enshi na qasa .”Bintun Baba yau kin dawo gidan babanki da zama ina fatar kinyi farin ciki.”Gyaďa kai tayi tana washe haqora.”To kuje mummynku ta nuna miki ďakin da zaki zauna sai kiyi wanka kizo ku karya ki huta , kafin su Miemie da Iman su dawo ko?”Kallon juna suka shiga yi ita  da mummyn, sam ita hankalinta bai kama mummynnan ba, ga dukkan alamu haka abun yake a gurin mummyn ma.Ita ta fara kawar da kanta ta maida kallonta ga Habibullah dake danna wayarshi tamkar baisan wainar da ake toyawa ba.Wai magana zata yi mishi bata kuma son aji, maimakon ta kai bakinta kunnenshi sai ta haďa kunnenta da nashi tace a hankali “Ni bazan bi hajjajonnan ba ka faďa wa Babana.”Abunda tayinne ya bashi dariya, ita a dole wai tayi sirri.Yana murmushi yace “Ke ki faďa mana baki da bakine?” “Habibullah tashi ka nuna mata ďaskinsu Iman ka nuna mata komai idan tayi wanka kuzo ku karya.”Mikewa yayi itama tayi saurin mikewa tana kallonshi.Hanyar upstairs taga ya nufa hakan yasa ta zaro ido.”Yau akwai rikitowa a gidannan.”Ta faďa kasa2.Yi yayi kamar bai jita ba yaci gaba da tafiya.A tsorace take binshi har ya fara hawa stairs ďin.Ganin bai kulata ba yasa tayi saurin binshi.Ta taka step ďaya ta kara na biyu na uku sai kawai sunkuya ta fara rarrafe tana magana  ita kaďai “Yasin bazan yi sake jiri yq kwasheni ya zubar a wnn waje ba, inji ciwo innata batanan, baffana kuma ba dawowa zaiyi ba balle ya ce min sannu bintuna Allah ya baki lafiya.”Jin kananan mita yaqi qarewa yasashi waigowa yaga me take yiwa mita, aiko ya ganta ta daddage sai rarrafe takeyi.Kallo su daddy yayi yaga hankalin  su baya wajen taďinsu sukeyi.Dawowa yayi daga baya yana cusa wayarshi cikin aljihun jeans ďinshi, ba tare da yayi magana ba yasa hanu ya ďauketa cakk ya kama haurawa da ita.Itako sai zare idanu takeyi har saida suka shiga ďakin ya dire ta tare da dangware mata goshi.”Gaki da baki sai shegen tsoro.””To ba jiri ne zai kama ni ba, ta faďa tana rike kanta.Sai kuma ta saki murmushi .”yasin Habibi akwai ka da qarfi, ji yanda ka ďauke ni kamar wata bebin roba, kama rainani aradu.””Ni na raina ki ko, gud, ci gaba da qara wa kanki laifi.”Waro idanunta tayi tace “Dama akwai wanine?””Me ďin?””Laifin.””Ina zaki sani Islam, ba dai ni kika cewa ďan yankan kai ba, wato baki yarda da ni ba kenan.”langab’e wuyanta tayi tace “Kayi haquri ka yafe nima na yafe aradu.””Akwai aukin yafiya da bada haquri kam, ni ki shiga kiyi wanka ina da abin yi.”” A ina zanyi wankan?”Ta tambaya tana ninke ďankwalinta da ta cire.Kofar toilet ya tura ya buďu ya nuna mata da hanu.Wani irin yatsina fiska tayi “Idan ba kazanta ba bayangida a cikin ďaki.””Idan baza kiyi wankan ba zan tafi fa.”Nufan bayin tayi ba tare da ta amsa ba.Tana shiga ta fito da sauri tana yarfe hanu.”Mene ne kuma?”Ya tambaya yana kure ta da ido.”Ni kam dai na shiga uku Habibi har cikin gurinma da wnn abun sa zamewan.”Ya fahimci tiles take nufi, sbd haka yaje ya riko hanunta ya shigar da ita ciki, ya fara nuna mata yanda zata yi amfani da shower, ga kuma bath tube , yanuna mata soso da sabulu duk tana tsaye tana kallonshi saida yazo fita ta riko rigarshi ta marairaice fiska “Nikam Habibi ka kaini bayangidan waje mai yashi.””Mu kam bamu dashi.””To na fasa wankan.””Haba daii.”Ya tambayeta cikin salon rainin hankali.”Aradu.”Tace cikin dakewa dan ta tabbatar mishi da gaske takeyi.Bai kara mata maganaba sai jawota da yayi ya kunna shower daidai kanta ,bata ankaraba taji sauqar ruwa a kanta.Wani irin zabura tayi har numfashinta yana faman ďaukewa.Ganin haka yasashi saurin kashewa.Dogon numfashi taja kafin tace “kasheni zakayi Habibi.””Sorry yi wankan to.””Mi sorata .”Tace tana murguďa baki.Dariya yayi ya fita ya barta a gurin.Mota ya koma ya ďauko mata kayanta ya shigo dashi ya samu bakin gadonsu Iman ya zauna yana jiran fitowarta kunnenshi makale da earpiece.Fitowa tayi tana Zumbura baki ďaurin kirji tayi da towel ďin da ya nuna mata “Ina kayana?”Hanunshi ya mika mata ta matso kusa dashi, jin baice komai ba ta ďaga muryarta tace da qarfi “Ina kayana Habibi, sai kuma tayi qasa da murya “Kai in kasa wannan cegen abin a kunnenka kurmancewa kakeyi.Jawota yayi ya ajiyeta kusa dashi yasa hanunshi ya zare earpiece ďin kunnenshi ďaya ya saka mata a kunnenta. Tab’e baki ta shigayi  jin american music da yake tashi ta cikin earpiece ďin.Mikewa tayi tana zare earpiece ďin daga kunnenta ta zare na kunnenshi tana kallonshi, a masifance tace “Dama shirmen da kakeji a wnn abun kullum kenan? Shirme zalla, wani Tori ma torii, Kanshika kanshika ,kanshika.”Wai ita a dole wakar da taji takeyi..*Aunty Ruqayya ce 🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers.**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*65-70*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*K*arb’e earpiece d’in yayi daga hanunta yana gimtse dariyarshi.”Nikam ina kayana nace.”Ta fad’a fiska a had’e ita a dole ya bata haushi.Da hanu ya nuna mata inda ya ajiye jakar kayan yana maida earpiece ďin kunnenshi.Kayan shafanta ta fara fitowa dasu, ta fara da shafa mai tana satar kallonshi.Kamar baya cikin ďakin dan ko alama bai nuna yana kallonta ba.Tana gama shafa man ta shafa powder ta ďauko kajal ta zizara tana kallon fiskarta cikin ‘yar karamar madubin da ta rike.D’igeďigenta tayi a fiskarta snn ta shafa jan janbaki.Kayan sawanta ta fito dasu ta ajiye a gefenta kamin ta juya ta kalleshi.Duk da taga ba kallonta yakeyi ba sai da tace “Ka fita zan sa kaya.”Bai kulata ba saida ta qara maimaitawa ya juyo gaba ďaya yana kallonta.”Rike ki nayi da zaki ce sai na fita zaki sa kaya?”Cuno bakinta tayi wanda yasha jan janbaki tace “Ni dai ka fita kawai ehen.”Tana ganin ya mike tace “Amma dai kar kayi nisa ka barni ni kaďai in rikito fa daga saman nan.”Bai tankata ba sai nufota da yayi yana kađa kanshi irin kiďa yayi daďinnan.D’ankwalinta ya ďauka ya goge ďige ďigen da tayiwa fiskarta da janbakin, ita kuwa sai kawar da fiskarta takeyi tana harararshi.Janta yayi gaban dressing mirror dake ďakin ya fara gyara mata fiskar.Sakin baki tayi tana kallon kanta a madubi.Saida ya gama tace “To ina jan baki na?”Ba tare da yace komai ba ya ďauko wetlips ya shafa  mata a leb’enta, snn ya ďauko body spray ya fesa mata.”Wash Sanyi Habibi.”Tace tana kankame jikinta.Sai kuma ta lumshe idonta tana jan numfashi tace “Kamshiii.””Wuce kisa kayanki mu fita yunwa nakeji.”Kallon shi tayi tana b’ata fiska, ganin ko kallonta baiyi ba yasa ta wuce tana sanďa ta je ta saka kayanta.Tana juyowa suka haďa ido.Kwab’a fiskarta tayi tamkar zata fashe da kuka tace ” saida ka kalleni ko?”Kawar da fiskarshi yayi yace “meye zan kalla a wajen ,na duba ne naga ko kin gama, idan zaki b’ata mun lokaci ne kuma in tafi in barki ki ta rikitowa.””Oho, Allah ya so ka.”Murmushin gefen baki yayi yace ” da me zakiyi?””Zan haďa ka da baba alhaji.”Turare ya ďauko yana fesa mata yace “Me zaki ce mishi?””Kaii, Habibii wannan turare kamshinshi ya fi na wanda yaya yunusa yake sayamin.”A take ya ďaure fiska “Uban yunusa ba yunusa ba.”Rike bakinta tayi tana zare ido “Kai Habibii ,kasan waye baban shi kuwa? shine fa jauron Jambutu , aradu idan aka jika ba za a barka ba ni dai ba ruwana.”Iza keyarta yayi yace “Wuce muje.”Da sauri ta juya ta rike hanunshi tace “Ka wuce dai.”Bai kulata ba tana rike dashin suka fito daga ďakin.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Suna barin wajen mummy ta dawo ta zauna kusa da daddy.”Alhaji, wai wnn yarinyar itace matar Habibullah.”Fiskarshi ďauke da fara a yace “Itace Sa’adatu.”Dan jimmm tayi kafin ta kuma cewa “amma ai tayi kankanta da aure alhaji, dubi shirmen da take ta zubawa.””Abinda zaki duba, shi ďinma ba wani girmane da shi ba, nawa Habibullah ya ke ,yaron da bai wuci shekaru ishirin da ďaya zuwa da biyu ba.”Jinjina kanta tayi kafin ta kuma cewa “Amma alhaji baka ganin a yanzu dukansu biyu basu san zafin kansu ba, ta iya yiyuwa gaba suce basa son juna ko ďaya daga cikinsu ya bijire, kuma ma fa ni alhaji dama akwai yarinyar da nayiwa Habib tanadi, sai kuma lokaci guda …  “Sai kuma tayi shiru ta sadda kanta kasa alamar dai abin bai mata daďiba.Gyaran murya daddy yayi kafin yace “Abinda nakeso ki fahimta anan Hajiyata, Wannan *al’amarin ubangiji ne* kuma ba a ja da al’amarin ubangiji a duk yadda ta kasance.Ki sani cewa Allah da ya hukunta wannan al’amari shi ya barwa kansa sanin dalilin yin hakan, kuma ko menene, ya faru daga baya, Allah yana sane, shi kuma yasan yanda zai tafiyar da al’amarinshi saboda, haka shawarar da zan baki shine, kar ki ja da *al’amarin ubangiji*Ki rike yarinyar nan tamkar ‘yar cikinki, ki kula da tarbiyarta, ki bata farin cikin da ya kamata ace ta samu a gaban iyayenta, ki sani cewa ďa na kowa ne, dan shi kanshi Habibullah makaranta zai tafi ba wai zasu zauna tare daga yanzu bane, yanzu duk wani hakki na kulawa da ita yana hanunki.Bayan haka kuma ,maganar akwai wacce kika tanadar mishi da ita duk bai b’aci ba.Habibullah namijine kuma mijin mace huďu, sbd haka banga abin damuwa a ciki ba.”Ajiyar zuciya ta sauqe, sai yanzu taji hankalinta ya ďan kwanta, har taje tayi umarni da ahaďa musu break fast.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Gurin saukowa daga stairs ďinne kuma aka shiga drammer dan gaba ďaya jikinta rawa ya keyi ,shi kuma yace da kafarta zata sauqa.Gamgam ta rikeshi suna sauka a hankali har suka ida saukowa.Wani wawan ajiyar zuciya ta sauke tace “Habibi Allah zai saka min wahalar da ka bani.”Wata ‘yar yarinya ce ta shigo wacce bazata wuci sa’ ar bintun ba ďauke da  tray a hanunta.Saida ta ajiye kan dinning snn ta duka har kasa da gaisheshi kafin ta kuma fita ta shigo da sauran abin bukata.Bin yarinyar  bintu tayi da kallo har ta fita snn ta maida kallonta kanshi.”Wacece wnn Habibi.””Larai sunanta.”Ya faďa a takaice.”Kanwarkace?”Ba tare da ya kalleta ba yace “Zo ki ci abinci sarkin surutu.””A ina? A saman?”Ta jero tambayoyin tana wurwurga idanu.”Ba zan ci a sama ba fa nikam.”Ta kuma faďa jin bai amsa mata ba.Nan tsakiyar falon ya tattaro ya kawo, ta ko zauna ta tankwashe kafafu tana kallonshi.Soyayyar irish ya fara zuba mata a plate ya tura mata.Kafin ya zuba nashi.”Meye wnn Habibi, aradu bazan ci ba. “Ta faďa bayan ta furzar da irish din da ta sa a bakinta, tana yamutsa fiska.”Me yayi.””Ba daďi, wani iri, nikam bazanci.”Tashi yayi ya koma dining đin ya ďauko ďayan warmern ya kawo ya buďe , luckily pepper soup na naman kaza ne a ciki.”Wnn fa?”Ya faďa yana nuna mata warmern.Leka cikin coolern tayi ta haďiyi yawu kafin tace “To ga abunda mutum ya sani kazo kana bani abunda ban sani ba.?Tana faďa tana karb’an warmer daga hanunshi.Cikin damuwa yace “Ai wannan bazai kosar dake ba Islam.””Yo shi wannan ďin kosar dani zaiyi da ka bani.”Ta faďa tana nuna irish ďin.Juye irish ďin yayi cikin warmer, ya zuba mata pepper soup ďin ya sa mata spoon snn ya je ya ďauko bread ya kawo.Ko kafin ya dawo tayi nisa abinta.”Gashi kici da wnn amma haka kawai baza ki koshi ba.””Habibi wa ya dafa miyannan, ko dai larai?””Mamarta ce.”Ya bata amsa a takaice.””Amma fa ta iya girki, zan je ta koyamin.””To ci ki koshi sai in kai ki wajenta ki koya.”Ya faďa yana haďa mata tea.Saida taci tasha tayi nakk, tayi hamdala kafin tace “Ya baka ci ba Habibi.”Hararar wasa ya zuba mata yace “sai yanzi kika san banci ba, da cikinki ya ďauka ko.”Dariya tayi tana shafa cikinta tace “Aradu na koshi kam.”Cin abinci ya shiga yi tana ta zuba surutanta yana shiru har ya kare.”Tashi muje na kaiki gurin su larai.”Shiru tayi saida ya sake maimaitawa.”Nima bazan amsa ba tun ďazu nake ta maka magana kayi kamar baka jina.””To baki ga cin abinci nakeyi ba, idan ana cin abinci ba a magana.””Na sani ai, haka innata ma take cemin, kullum sai ta make ni wajen cin abinci wai na cika surutu, to mutum kuma zai ga abun magana bazaiyi ba dan kawai yana cin abinci.”Ta karishe ta b’ata fiska tamkar a lokacin innar ta maketa.”Zo muje in kaiki wajen su larai, idan kuma can sama zaki koma kiyi bacci muje na raka ki.”” Wa, ni jikar Buba Yusa, (kamar yadda taji innarta ke faďa, wani lokacin kuma sai tace ni shashishatu, dan jin innarta takance ni Aishatu ) sai dai dai muje gurin su larai ďin dai.”Gaba yayi tana binshi a baya suka nufi hanyar kitchen.Tun kafin su iso larai ta hango su, sbd haka sai ta kama hanyar zuwa falon domin tattara kwanuka.”Larai, larai, larai kin shiga raina larai.”Bintu tace mata mata tana dariya lokacin da ta zo kusa da su zata wuce.Kaďan larai ta kalleta ta kawar da kanta ta wuce.Bakinta ya ďan ja yace “wannan bakin tsokana.”Tun bai kare magana ba ta rike hanun ta cuno bakin tace “wnn hanun cin zali.”Hmm, kawai yace suka karasa kitchen ďin.Gaisawa yayi da maman larai a mutunce tana tambayar shi ya hanya snn ta maida kallonta kan bintu tace “Bakuwa mukayi ne alhaji karami?”Kafin ya bada amsa bintu ta duka har kasa tace “Eh, ina kwana goggo Marka?”Kutttt😳*Aunty Ruqayya ce🥀*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*70-75*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*D*a sauri Habibullah ya bar wajen yana jinjina rainin wayo irin na Islam.Tana ji dai yacewa matar Mmn larai, amma tsabar rainin hankali irinnata sai ta ce mata goggo Marka.Ci gaba bintu tayi da gaisuwarta harda ce mata innarta tace ta gaishesu.Ita ko Mmn larai duk tayi tsammanin ko ta yiwa bintu kama da wata mai sunan ne shi yasa ta kira ta da hakan.Kujera yar tsuguno bintu taja ta zauna ta fara zubawa mmn larai surutu kamar dama can sun saba, har larai ta dawo ta samesu.Tana kallo larai ta wanke kwanukan da sukayi amfani dasu.”Ku nan a tsaye kuke wanke wanke,?”Tambayar da tayi wa larai kenan.Ita ko larai gyaďa mata kai kawai tayi.Cabbage da carrot Mmn larai ta fitar ta ajiyewa larai.Zumbur bintu ta mike ta isa wajen.”Meye wnn?”Ta tambaya tana tab’a cabbage.Tun kan su bata amsa ta kuma cewa “D’obo ďume jun ba leggal bindigaru ďo?”(Wnn kuma menene kamar sandar bindiga.”Ta tambaya tana nuna carrot.Dariya Mmn larai tayi ta fara mata bayani ďaya bayan ďaya.Haka ta zauna cikin kitchen ďin sai uban tambayoyi take ta zuba musu,duk abinda ta gani bata sani ba sai ta tambaya har suka kare girkin.Ko da suka gama binsu BQ tayi nanma sai zuba musu surutu takeyi.Habibullah da ya leko yaga suna tare ya fita ya tafi harkokinshi dan yasan Mmn larai bata da matsala sai dai asamu akasi ta wajen Islam.A can wajensu taci abinci, tayi sallar azahar da la’asar.Sai da yamma Habibullah ya shigo, lokacin su Mmn larai suna kitchen itako bintu ta samu ruwa ta buďe zai zuba yakeyi a jikinta tana ta tsalle.Can yaje ya sameta tana ta tsalletsallenta bata ma san da mutum a wajenba.”Islam, me kikeyi anan?””Gashi kana gani wanka nakeyi.”Ta faďa tana share fiskarta, snn ta kara da “Yaushe kazo nan Habibi?”Karasawa yayi ya kashe famfon tun kafin yayi magana tace “Yauwa Habibi ďauko min kayana.””Da ban dawo ba fa?””Sai larai ta ďauko min tunda kasan nidai ba hawa sololon samnnan zanyi ba.”Gyaďa kai yayi aranshi yana ayyana za a sha daga da ita kafin ta saba da yanayin gidan nasu.”A ina zaki canza kayan to?””D’akin su larai, anan naci abinci na yi sallah ma.”Waro ido yayi yace “Kina nufin tun ďazu baki koma ciki ba?  Watakil kinsa mummy tana ta nemanki.””Wace mummy, oh Wannan Hajjajon?Ta karishe da sigar tambaya.”Baza ta nemeni bama na sani.”Juyawa kawai yayi yaje ya kawo mata wasu kayan.Anan ďakin su larai ta saka kayan, ya shanya mata jikakkun kafin ya jata suka koma part ďin mummy tana tambayarshi baba alhaji.Suna shiga su Iman da Miemie ma sukayi sallama suka shigo. Sun dawo daga makaranta sanye da uniform.Da murna suka tareshi suna mishi oyoyo dan basu san ya dawo ba sai lokacin, itako tana tsaye tana kallonsu cike da sha’awa dan sun burge ta cikin uniform ďin.Da gudu suka haura stairs suna kiran mummy ita kuwa tana tsaye sai kallonsu take tana mamakin rashin tsoro irinnasu da suke iya hawa da gudu, a ranta take cewa nima cire tsoronnan in fara hawa har na iya hawa da gudu, duk tunaninnan da takeyi fiskarta ďauke yake da murmushi.”Islam magriba ta kusa dan Allah ki zauna ki nitsu guri ďaya kinga baba alhaji ma ya kusa dawowa.”D’aure fiskarta tayi tamkar ba ita ke smiling yanzu ba.Ganin yadda ta gimtse fiskarta ya gane gardama zata yi mishi, hakan yasa shi cewa .”Muje in raka ki gun mummy.””Sai dai gurin Goggo Marka.”Ta amsa mishi da sauri ganin nufin shi su haura stairs ne, dan ta gwammaci tayi ta zama gunsu larai da ta je gun mummy ko ta haura stairs.”Wai me yasa kike cewa matar nan goggo marka ne, bakiji maman larai muke ce mata ba?”Juya idanunta tayi kafin tace “Kaima dai Habibinnan meye na tambaya, bakaji muryarta tana kama da ta goggo marka, mai wakar, ehhh, goggo mar, goggo mar, goggo marka ba?”Kaďan ya hana dariya ta sub’uce mishi ganin yadda ta dage tana wakar a nufinta ya gane wakar da take nufi.Dakewa yayi yace “ni ban san wakar ba ai balle nasan yanda muryarta yake.””To tsaya kaji ďayar.”:Ehh, soyayya, “Gidan mutuwa ake kuka mata gidan biki sai guďa.”Eh, soyayya.”Wannan karo harda rawarta.”Wnn fa, kasanshi.””Ban sani ba Islam, wanka zanyi kike ta b’ata min lokaci.”Ya faďa yana barin wajen da sauri dan yasan muddin ya biye mata saidai yaji ana kiran sallah.Tab’e bakinta tayi qasa qasa tace “Sannu kifi ko kwaďo, karewar son wanka.”Yana fita ta fice kitchen, ta samu maman larai tana kwashe tuwo.”Sannu da aiki goggo marka.””Yauwa sannu ‘yar albarka.””Ina larai?”Ta tambaya tana bin kitchen ďin da kallo.”Tana sashinmu.”Buďan bakinta sai cewa tayi “Cegiya kurma, wai ita haka take ne bata magana? Ana mata magana sai ta kalli mutun ta juya kai, nifa bana son irin haka.”Murmushi mai sauti Mmn larai tayi tace “Dan baku saba bane, in kun saba zata sake ku rika taďi.”Nan ta shiga tayata suka kammala tare ta bita kofarsu.Yanzuma a can tayi sallah taci abinci.Sai bayan sallar isha,i ta shiga part ďin su mummy, nan ta samesu cikin main palour.Shigowarta ba da jimawa ba, Daddy da Habibullah suka shigo.Duk yadda sukayi tazo suci abinci cewa tayi taci a gun su larai, a koshe take, dan ita sam hankalinta bai kama mummy da yaranta ba shi yasa ma bata so ta rika shiga cikinsu, baranma yanzu da ta shigo tana musu magana babu wanda ya amsa mata daga cikinsu, ita kuma uwarsu tana gani bata tambayesu dalili ba, hakan ba kqramin kular da Bintu yayi ba.Zamanta tayi cikin palour tana kallon T.V har suka gama suka dawo cikin palourn.Daddy ne ya fara tashi yana mata sai da safe snn mummy tabi bayanshi, daga nan su mie mie ma suka yi ďakinsu suka barta da Habibullah.”Islam, wato bakyajin magana ko, nace ki zauna kada ki fita saida kika koma gunsu Mmn larai, har da cin abinci wajensu.”Ta tsinkayo muryar Habibullah daga gefenta.A kaikaice ta kalleshi ta maida hankalinta ga T.V kadin ta tab’e baki tace.”Ni aradu gun innata zan koma dan dukanku haushi kuke bani banda baba alhajina.”Waro idanunshi yayi yace “Haushi?”Ni da wa.”Tamkar tana jiran tambayar tace “Kaida wannan hajjajon da yarannan da suka tashi, su Mamu ko Mume kuke ce musu oho, aradu dukanku haushinku nakeji.”Kusa da ita ya dawo ya zauna a kasa kamar yadda take zaune dan sam bata son zaman kujeran ganin ko ta zauna ma kafanta ďangalewa sukeyi basa saukowa qasa.Juyo da fiskarta yayi zuwa b’angaren  da yake ya tambayeta “Me muka miki daga zuwanki Islam?”Kwace fiskarta tayi ya sake juyo da ita “Ni dai ka mayar dani gun innata bazan iya zama a gidannan ba, mutane daga babba har yaro sai mugun hali, ayi ta ďaure maka fiska, kayi wa yara ‘yan uwanka magana suki amsawa, snn kai kuma kace in zauna cikinsu kar inje gun su goggo marka, idan naje kace bana jin magana?”Ta karashe maganan idanunta cike tab da kwalla.Tausayinta yaji ya kamashi jikinshi kuma yayi sanyi, tabbasa yaso ya fahimci yanayin mummyn tashi game da Islam saidai baiso gaskata hakan ba, duba da yanda take sonshi da nuna mishi kulawa a tunaninshi koda dabba ya kawo yanuna yana so zata bashi kulawa ta musamman balle kuma mutum, mutum ďimma mace mai rauni, marainiya, wacce kuma take a matsayin matarshi.Katse mishi tunani tayi da cewa “Zaka mayar dani gobe Habibi?”A sanyaye yace “Yi hakuri Islam bazan iya ba.”Waro idanunta tayi tana kallonshi “Baza ka iya me ba, Habibi?””Maida ke gurin innan.”Ya faďa ya kawar da fiskarshi daga kallon fiskarta sbd yadda expression ďinta ya nuna bai mishi daďi, bai tab’a tunani dawowarta gidansu zai sata cikin damuwa ba kuma sam baya fatar hakan ta kasance.Shesshekar kukanta yasashi juyowa da sauri yana yana kallonta “Ya salam, Islam da gaske kikeyi ne wai?”Bata tanka shi ba saima ci gaba da kukanta da tayi.Jawo ta yayi a sanyaye ya kwantar da ita kan cinyarshi snn ya ďora hanunshi akanta yana cewa “Yi haquri Kanwata, ki bar kukan gobe ma ba a gidan zaki wuni ba, basai sunga idonki ne ba zasu yi miki mugun hali, kuma bazan sake hana ki zuwa wajen su larai ba, snn ke da zaki shiga makaranta ma me zai dameki?”Da sauri ta ďago “Kace aradu, yaushe zan shiga makarantar? “tana tambaya ne tana hango kanta cikin uniform irinnasu Miemie goye da schl bag a bayanta.Take kuma ta fara sakin murmushi tamkar ba ita ke kuka ba.Share mata hawayen fiskarta ya shiga yi snn ya mayar da kanta ya kwantar kafin yace mata “Wannan term yana karewa zaa shigar dake makaranta kinji.””To ina zamuje goben kuma?”Ta sake jefo mishi tambaya.”Yawo zamuje, zan kaiki gidan Aunty Nafi ma ki ganta, tana sonki sosai fa.””Wacece aunty Nasin.?””Aunty Nafi nace ba Nasi ba.”Dariya ta kwashe dashi tace “Na sani ai, Nasin yafi daďi ne, haka Baba jauro yake kiran wata jikarshi mai irin wnn suna Nasii, ai yafi daďi ko?”Ni dai banji daďi a Nasi ba, ke dai na lura ďabi ar kice canzawa mutane suna..Ya kara da tambayarta “Wa ya miki kitson nan.””Babba ‘yar Inna wuro muka je gidanta tayi min, dan Yaya Yunusa zai zo ahi yasa kaga tayi min mai kyau, ayya yaune fa zai je kuma bazi sameni ba.””Islam.””Habibi.””Islam, idan na sake jin sunan yaronnan a bakinki.””Me zakayi .”Ta tambaya da sauri.Kwafa yayi yace baza ki sani ba sai kin sake.”Turo baki tayi tace “Kuma mutum da ďan uwanshi sai a ace kar ya kira sunanshi , ni ka daina tab’a min kitso da zafi, kuma dan baka san kukan da nayi tayi ba lokacin da ake min kitson.””Wai kukan kitso kike yi?”Kamar jira takeyi tace “Sosai ma har da majina.”*Gaisuwa da godiya gareku masoya, na gode kwarai da kulawarku gareni, Allah ya bar zumunci.**Kamar yadda kuka sani ba isasshiyar lafiyace dani ba, duk da dai naso na karasa littafin kafin azumi, amma banyi tsammanin hakan zai kasance sbd a yanzu ba ko da yaushw zaku rika ganin posting kamar da ba, sai duk randa Allah ya bani iko zaku gani, Na gode kwarai.*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*75-80*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Congratulations dear sister, KHAIRAT UP for the successful completion of ur novel TAKAICIN D’A NAMIJI**Littafin yayi ba qarya, jinjina gareki my khairy,Allah ya qara basira, hazaqa da kuma fasaha. Muna jiran sabon novel Allah ya bada iko.**More ink to ur pen sister khairy.*😍😘😍*D*ungure mata kan yayi kaďan yace “Kinji kunya me kukan kitso har da majina.””wash, zafi aradu kuma yasin ban yafe ba.”Ta faďa tana shafa gurin da ya dunguren.”Ni kika cewa baki yafe ba Islam?”Ko a jikinta tace “To yau na fara?””Ba yau kika fara ba, amma daga yau baza ki sake ba dan zanyi maganin rashin kunyan.”Wani dariyar tsoro ta saki tana cewa “Na yafe aradu kuma bazan qara ba, kayi haquri kaima ka yafe.””Wannan kam kin iya , tashi kije kiyi wanka ki kwanta.”Wani irin wawan zabura tayi ta tashi ta zauna, ta kankance ido ta Wan..?”Wanka.”Ya bata amsa.”Aradu, kaji nace aradu, to bazanyi ba yasin, to ma ba ďazu nayi wanka ba,  aradu ko gidan innata sau biyu nake wanka, gidan inna wuro kuma sau ďaya cikin kwanciyar hankali, shine anan kuma zaka ce inyi sau uku?””Wa.can ba wanka kikayi ba ai, kindaiyi wasa da ruwa kin jika jikinki ne kawai.””amma ai kasan jikin ba datti ko tun da ba wasan qasa nayi ba.”Duk naci shi haka ya gaji ya kyaleta, ta shiga ta kwanta nanma tace bata san wnn ba dan ita gwara mata ta kwana a palour da ta kwana a sama.Cikin son tsoratar da ita yace yana zaro ido “Ke kaďai zaki kwana a nanan ďin.”Ba tare da damuwa ba tace “To meye, gidanmu ba ni kaďai nake kwana ba.”Gyaďa kanshi yayi aranshi yana cewa zan yi maganinki.Kashe TV yayi yana kallonta da gefen ido dan yaga reaction ďinta.Kwancyarta tayi kan center carpet tana cewa dama ce maka akayi na san abunda sukeyi.”Zan kashe wutan fa”Yace duk dan ta tsorata.”Kashe Habibi idan ka fita ka rufo min kofar.”Ta faďa babu alamun tsoro a tare da ita.Kashe wutan yayi ya fita ya ja kofar ya rufe , ya tsaya yana jiran yaji me zatayi.Shiru ya biyo baya tamkar ma bata cikin palourn.Dan kanshi ya gaji da tsayuwa ya buďe kofar ya shigo yana haska palourn da hasken wayarshi.Nan ya sameta kwance har ta fara bacci.Ba tare da yayi magana ba ya nemi waje ya zauna ya jira na tsawon lokaci, saida baccinta yayi nisa snn ya shigar da ita ďakinsu Miemie._Washegari_Zaune take bakin gado ta zuba musu na mujiya tana kallon yanda suke shirin tafiya makaranta, dukansu biyu babu wacce ta nuna alamar tasan tana ďakin, harkokin gabansu kawai sukeyi.”Ina kwananku.”Tace dasu lokacin da suke fitar da uniform ďinsu zasu saka.Kallon juna sukayi s uka ci gaba da abinda suke ba tare da sun  tankata  haushi da takaici suka haďu suka tirniketa, ta tsani tayiwa mutum magana ya mata banza.Yar karamar tsaki taja ta dauke idanunta daga kallonsu, can taji iman nace mata “Ke miko min wancan book na bayanki.”Ai bata san sanda ta juyo ta wurga mata harara ba.”Ke ya da harara ? “Iman ta tambaya fiskarta dauke da mamaki.Cikin sanyin murya tamkar a tsorace take tace “Babu harara.”Snn ta miko mata book din.”Ashe tasan book.” miemie tace.Nan suka kwashe da dariyar da ya dada kular da Bintu.A hankali ta tashi ta shige toilet tana jin zuciyarta ba dadi, snn kuma kasan ranta shawara take bawa kanta da ta yi wanka itama tun yanzu ta shirya su sauka kasa tare dasu iman kar su barta ita kadai a dakin.Tana fitowa daga wanka ta ga dakin wayam ba kowa, nan take tsoro ya shigeta ta fara tunanin ko tayi saurin binsu.Daga baya dai ta karfafawa kanta gwiwa ta zauna ta fara shafa mai, tana tunanin yanda zata sauqa.Kamar yadda jiya Habibullah ya nuna mata haka tayi snn ta zabi daya da ga cikin sabbin kayanta ta saka ta fito tsaf da ita, dan bata manta fitar da yace zasuyi ba, kuma ta kudura in ta sauka baza ta kuma haurawa ba.Zama tayi tana tuna yanda zata sauqa.Tana nan zaune, taji sallamar Habibullah.Wani dadi taji cikin zumudi ta amsa sallamar tare da mikewa tsaye.”Ina kwana yaya.”Ta fada tana washe baki.Ba tare da ya amsa ba ya karaso kusa da ita ya murde kunnenta, “Yau kuma waye yayan ? “”Kai mana ba haka naji wadannan suke kiranka ba.””To bana so, ki kirani yanda kika saba. Me ya hana ki fitowa tun dazu ko sai yanzu kika tashi daga barci.”Kamar tana jira tace “Haba, haba tun tashin asuba ban koma ba aradu.” Takalmanta flat sabbi wanda basu wuci saku biyu ta musu ba ta dauka ta rike a hanunta snn ta fiddo hijabinta ta saka tana cewa “Muje.”Yauma dakyar ta sauqo sai kyarma jikinta yakeyi dan tsoro shi kuma ya dage lallai sai ta cire tsoron.Gurin breakfast kunun gyada kawai tasha ta tafi gun mmn larai tana tamhayarta ko akwai d’umamen tuwo, tayi sa a kuwa ta samu wanda suka d’uma zasu ci.Daddy dad’i ya ke ji ganin yanda ta saki jiki take walwala.Gidan aunty Nafi suka fara zuwa around 9 oclock. yaranta biyu Sudeis da shureim suka hau ihun murnar ganin uncle d’insu, sai daga su yake yana direwa suna ta dariya.Da murna aunty Nafi ta taresu , sosai taji dad’in surprise d’in da suka yi mata, haka kuma ba karamin farin cikin ganin Bintu tayi ba, duk da bata tab’a ganinta ba sai tau d’in, lokaci guda taji yarinyar ta shiga ranta, sai nan nan takeyi da ita.Ita kuwa Bintu ranta qal sai dad’i takeji yanda taga aunty Nafi takeyi da ita.Kad’an kad’an take d’iban ice cream tana sawa a baki tare da tsotsewa yanda taga yaran aunty Nafi keyi.Dad’inshi da sanyinshi ke ratsa ta har wani lumshe idanu takeyi.Su kuwa hiransu suke ta zubawa cikin d’okin ganin juna yana kuma bata labarin abunda ya faru game da b’atan Bintu.Can yace “yauwa sister d’azu naga jama’a a kofar gidan can me ya faru ne ? “Cikin alhini tace “Ka gane yaronnan Shabbas da suke shigowa cikin gidannan ? “”Na ganeshi.””Shine ya rasu shekaran jiya abun tausayi wlh, Allah sarki Mmn Shabbas.”Ta karashe maganar kamar zatayi kuka.Shima cikin nuna tausayawa yace “Allahu akbar, Allah yaji kansa, yabawa iyayen shi haquri da juriyan rashin sa.””Allaah sarkiii.”Suka jiyo muryarta.A tare suka juyo suna kallonta.Hada tayi dashi yana kallonta da alamar tambaya.”Sannnyiii.”Tace tana marairaice murya tare da nuni da ice cream d’in hanunta .Kallon juna sukayi ,take kuma dariya ta sub’ucewa aunty Nafi.Shima murmusawa yayi yace “Kadan kenan daga aikin Islam.”Cikin dariya tace “Wlh ni nayi tsammanin rasuwanne ya bata tausayi.””Idan tasan muna maganar rasuwa kenan.”Ko kulasu bata sake yi ba taci gaba da abunda takeyi har ta qare.”Shureit, shureit, Sureit .”Ta fara kwalawa yaran kira.”Ke da waye ? “Habibullah ya tambayeta.Ni da yarannan masu suna iri d’aya “Shureit da Sureit.”Aunty Nafi kam kallon ikon Allah kawai takeyi.”Me zasu miki ? “” Yauwa, kace babban yazo da abun hanunshin nan.”Kiranshi yayi ya juya ga aunty Nafi yana fad’ama aunty zata rakasu suyiwa Islam siyayya inji Daddy.A hankali take tambayarshi meye sunan abun hanunshi.”Remote control.”Yace mata .”Me akeyi dashi ? “”Nan ya kwanta jikinta ya shiga nuna mata yanda ake amfani dashi.Karb’a tayi ta fara sarrafa shi.Can ta mike ta isa kusa da TVn ta d’an kara volume na wakokin hausa dake  playing.Kad’an kad’a ta fara kad’a kai can kuma ta fara jefa kafa tamkar mai marching , da kid”a yayi kid’a sai ga Bintuna tana tikar rawa kamar ita kad’ai ke cikin falon.Tab’a aunty Nafi yayi ya nuna mata Bintu.Kallonta suke yi suna dariya itako bata ma san sunayi ba, cacewarta kawai takeyi har da jifa da hijabi.Saida ta gaji dan kanta ta dawo ta zauna tana maida numfashi.”Ashe haka kika iya rawa ? “Aunty Nafi ta zolayeta.”Hhh, ai haka mukeyi a garinmu , nan ma na fara mantawa ne dan na dad’e banyi ba.”Dariya aunty Nafi tayi tace “Kice kad’an ma na gani kenan.””Aradu kuwa.”Ta bata amsa .”Yauwa Habibi, nace  ‘yan biyun gidankun nan suna fitar da maciji ne ? “”Su waye kuma ‘yan biyu .””Mamu da Mume.”Ta bashi amsa.”Su suka ce miki su ‘yan biyu ne ? “Cikin jin dad’i tace “Kace aradu ba ‘yan biyu bane.””Su waye Mumen ? “Aunty Nafi ta tambaya.”Su Miemie fa take fad’a.””Ba ‘yan biyu bane Islam.”Ta bata amsa.Wani shu’umin murmushi tayi tana kad’a kai a ranta take cewa ,zaku ci ubanku tunda ku ba ‘an biyu bane, dama tunanin hakan yasa nake jin tsoronku .”Menene ? “Suka tambayeta tare.”Ba komai.”Tace musu, amma ita tasan abunda take ayyanawa a ranta.Sunanan har aunty Nafi ta gama girki suka ci, Mijinta suka shigo tare da abokinshi, wanda aka kira da Honouroble, shi kuma maigidan Engineer.Kusa da shi ta koma murya kasa kasa tace “Waye Babansu a cikinsu, Kolorogol (Honouroble) ko Injimiyan ? (Engineer).*Gaisuwa da fatan alkhairi gareku masoya**I heart u all*💝💝💝(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*80-85*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*B*akinki ne kolorogol d’in ai.Ya amsa mata.Cuno bakin tayi, “Idan baza ka fad’a ba ka bari kawai ba sai ka zageni ba, sunaye duk ba dad’in ji.Zuwan aunty Nafi ne ya katsesu ,take ce musu bari ta tambayi Daddyn su Shureim sai su tafi.Sayayya sosai suka mata kama daga English wears, atamfofi, english gowns da arabian gowns, takalma, hijabai gele, night wears, cosmetics da duk wani abin buqata.Aunty Nafi ta tafi da atamfofin zata kai mata dinki.Wurin computernshi ya wuce da ita, suna shiga ciki friends suka fara sowa suna washi “Na fati baban fati.”Shiko sai washe baki yakeyi yana mika musu hanu suna shaking.A can sukayi sallar la’asar.Sun d’an jima a gurin dan saida yad’an tab’a aiki, sai tab’e tab’e takeyi tana suburbud’o  mishi  tambayoyi.A hanyarsu ta komawa gida suka bi ta bakin kasuwa, sai kalle kalle takeyi.Ganin yawan jama’ar dake kai kawo ya sa ta jefo mishi tambayar da ta bashi mamaki.”Habibi wad’annan duk mutanene ? “Saida ya mata kallon mamaki snn ya kawar da fiskarshi tare da ce mata “aljanune Islam.”A tsorace tace “Dukansu ? “”Eh, to a had’e suke, da mutane da aljanun amma ba lallai bane ki iya bambancesu.””Innahu min sulaimana wa innahu bismillahi rrahmanirrahim.”Shi ta shiga maimaitawa a bayyane bayan ta rufe fiskarta da tafukanta.Sosai abin ya bashi dariya har yana buga steering mota.Wai ita in an barta da gaske taga aljanu kenan.Ya ayyana a ranshi.Itako bata ma san yanayi ba, saima kamo ayatul kursiyu da tayi tana karantawa duk da akwai errors a ciki bata gam a iyawa ba.Har suka isa gida addu’a takeyi, ba kakkautawa.A sanyaye ta shiga palourn ta tadda mummy da yaranta.”Sannu Hajjajo ina wuni ? “Tace a sanyaye.Kallon yanayinta mummy tayi ta tab’e baki snn tace “lafiya.”Ko kallon su Miemie batayi ba ta nemi guri a qasa ta zaune.Niki niki ya shigo da kaya, su miemie suka tashi suka karb’e shi, hakan yasashi komawa ya d’ebo sauran.”Wannan kayan fa ? “Mummy ta tambaya.”Na Islam ne Daddy ya ba da kud’i a sayo mata.”Ya bata amsa.”Madalla, Allah ya saka da alkhairi.””Amin.”Suka amsa dukansu.”Yauwa kuzo muje saman.”Tare suka haura dukansu , yaudai su Bintu anyi jarumta dan babu wanda ta rike saidai a d’ar d’ar ta haura.D’akin aunty nafi mummy ta nuna musu a matsayin ya zama na Bintu, an gyara shi tsaf.Murna kamar tsyi yaya har ta manta da damuwar da ta shigo da ita.Fita mummy tayi ,shima yabi bayanta dan tattaro kayan da suka shigo dasu. kamar tana jira ta zarowa su miemie ido “Ku kuma me kuke min a d’aki, ko dan jiya na kwana a d’akinku zaku rama yau, to aradun Allah baku isaba, babu wacce zata kwanar min ad’aki, ku fita ma tun d’akin bai saba da ganinku ba.”Ta karishe tana mai murgud’a baki.Mamaki kamar ta kashesu itako ko a jikinta, saima d’ale gadon da tayi ta zauna tana karkad’a kafa tare da bin komai na d’akin da kallo.A masifance Iman ta nufo ta zata zazzaga mata Habibullah ya shigo, hakan ya taka mata birki, Miemie kwafa tayi ta fita daga d’akin Iman ta mara mata baya.”Tashi mu shirya kayan malama kin wani hard’e sai kace kin samu kujerar sarauta.”Ya fad’a yana ajiye kayan hanunshi.Wuf ta mike “To tsaya Habibi barin yi fitsari.””In kin shiga ki had’a harda kashi ma.”Wani juyi tayi ta rufe fiskarta “Wayyo Allah, ashe haka kake baka da kunya kake kiran wnn abun.”Cikin dariya yace “To bakya yin ne.”Idon a rufe still tace “Kai daina fad’a dan Allah, ka tab’a jin nace zanyi ne, abunda b’oyewa akeyi kai kuma kake bayyanawa, na fasa fitsarinma.”Ta fad’a tare da fad’awa kan gado tayi ruff da ciki taki bud’e idon a dole ya bata kunya.”Kusa da ita ya dawo yana dariya, ya d’agota.Kam kam ta kankame jikinta sam taki yarda su had’a ido.”Wasa fa nake miki , je kiyi fitsarinki daga nan kiyi wanka.A d’ari ta fincike ta shiga bayangidan tana mita , wanka dai wanka dai kullum kullum.Daga murya yayi yace idan bakiyi  ba fa shigowa zanyi in miki da kaina.Itama d’aga muryar tayi tace “Kayi sa’a ba a magana a bayan gida aradu da na antaya maka zagi, kamin wanka babba dani sai kace wata ‘yar iska, ko an ce maka bani da lafiyane, ko innata ma ai ta dad’e da daina yi min wanka.Dariyar da yakeyi ya hanashi amsa mata, ko me tayi yanzu oho da take cewa ba’a magana a bayan gida.Dressing mirror ya fara shiryawa snn ya koma wardrobe, yashiga jera mata kayan daki daki.Rai a b’ace ta fito ita an sata wankan dole, dressing mirror tabi da kallo, yanda ya tsara gurin ya burgeta ba kad’an ba.Mai ta shafa snn ta d’auko turaruka tana juyasu tana kallo.Can tace “Wannene na fesawa a jiki wannene na kaya ? “Jin bai kulata yasa tace “Baban fati da kai fa nakeyi.”(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*80-85*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*B*akinki ne kolorogol d’in ai.Ya amsa mata.Cuno bakin tayi, “Idan baza ka fad’a ba ka bari kawai ba sai ka zageni ba, sunaye duk ba dad’in ji.Zuwan aunty Nafi ne ya katsesu ,take ce musu bari ta tambayi Daddyn su Shureim sai su tafi.Sayayya sosai suka mata kama daga English wears, atamfofi, english gowns da arabian gowns, takalma, hijabai gele, night wears, cosmetics da duk wani abin buqata.Aunty Nafi ta tafi da atamfofin zata kai mata dinki.Wurin computernshi ya wuce da ita, suna shiga ciki friends suka fara sowa suna washi “Na fati baban fati.”Shiko sai washe baki yakeyi yana mika musu hanu suna shaking.A can sukayi sallar la’asar.Sun d’an jima a gurin dan saida yad’an tab’a aiki, sai tab’e tab’e takeyi tana suburbud’o  mishi  tambayoyi.A hanyarsu ta komawa gida suka bi ta bakin kasuwa, sai kalle kalle takeyi.Ganin yawan jama’ar dake kai kawo ya sa ta jefo mishi tambayar da ta bashi mamaki.”Habibi wad’annan duk mutanene ? “Saida ya mata kallon mamaki snn ya kawar da fiskarshi tare da ce mata “aljanune Islam.”A tsorace tace “Dukansu ? “”Eh, to a had’e suke, da mutane da aljanun amma ba lallai bane ki iya bambancesu.””Innahu min sulaimana wa innahu bismillahi rrahmanirrahim.”Shi ta shiga maimaitawa a bayyane bayan ta rufe fiskarta da tafukanta.Sosai abin ya bashi dariya har yana buga steering mota.Wai ita in an barta da gaske taga aljanu kenan.Ya ayyana a ranshi.Itako bata ma san yanayi ba, saima kamo ayatul kursiyu da tayi tana karantawa duk da akwai errors a ciki bata gam a iyawa ba.Har suka isa gida addu’a takeyi, ba kakkautawa.A sanyaye ta shiga palourn ta tadda mummy da yaranta.”Sannu Hajjajo ina wuni ? “Tace a sanyaye.Kallon yanayinta mummy tayi ta tab’e baki snn tace “lafiya.”Ko kallon su Miemie batayi ba ta nemi guri a qasa ta zaune.Niki niki ya shigo da kaya, su miemie suka tashi suka karb’e shi, hakan yasashi komawa ya d’ebo sauran.”Wannan kayan fa ? “Mummy ta tambaya.”Na Islam ne Daddy ya ba da kud’i a sayo mata.”Ya bata amsa.”Madalla, Allah ya saka da alkhairi.””Amin.”Suka amsa dukansu.”Yauwa kuzo muje saman.”Tare suka haura dukansu , yaudai su Bintu anyi jarumta dan babu wanda ta rike saidai a d’ar d’ar ta haura.D’akin aunty nafi na da mummy ta nuna musu a matsayin ya zama na Bintu, an gyara shi tsaf.Murna kamar tsyi yaya har ta manta da damuwar da ta shigo da ita.Fita mummy tayi ,shima yabi bayanta dan tattaro kayan da suka shigo dasu. kamar tana jira ta zarowa su miemie ido “Ku kuma me kuke min a d’aki, ko dan jiya na kwana a d’akinku zaku rama yau, to aradun Allah baku isaba, babu wacce zata kwanar min ad’aki, ku fita ma tun d’akin bai saba da ganinku ba.”Ta karishe tana mai murgud’a baki.Mamaki kamar ta kashesu itako ko a jikinta, saima d’ale gadon da tayi ta zauna tana karkad’a kafa tare da bin komai na d’akin da kallo.A masifance Iman ta nufo ta zata zazzaga mata Habibullah ya shigo, hakan ya taka mata birki, Miemie kwafa tayi ta fita daga d’akin Iman ta mara mata baya.”Tashi mu shirya kayan malama kin wani hard’e sai kace kin samu kujerar sarauta.”Ya fad’a yana ajiye kayan hanunshi.Wuf ta mike “To tsaya Habibi barin yi fitsari.””In kin shiga ki had’a harda kashi ma.”Wani juyi tayi ta rufe fiskarta “Wayyo Allah, ashe haka kake baka da kunya kake kiran wnn abun.”Cikin dariya yace “To bakya yin ne.”Idon a rufe still tace “Kai daina fad’a dan Allah, ka tab’a jin nace zanyi ne, abunda b’oyewa akeyi kai kuma kake bayyanawa, na fasa fitsarinma.”Ta fad’a tare da fad’awa kan gado tayi ruff da ciki taki bud’e idon a dole ya bata kunya.”Kusa da ita ya dawo yana dariya, ya d’agota.Kam kam ta kankame jikinta sam taki yarda su had’a ido.”Wasa fa nake miki , je kiyi fitsarinki daga nan kiyi wanka.A d’ari ta fincike ta shiga bayangidan tana mita , wanka dai wanka dai kullum kullum.Daga murya yayi yace idan bakiyi  ba fa shigowa zanyi in miki da kaina.Itama d’aga muryar tayi tace “Kayi sa’a ba a magana a bayan gida aradu da na antaya maka zagi, kamin wanka babba dani sai kace wata ‘yar iska, ko an ce maka bani da lafiyane, ko innata ma ai ta dad’e da daina yi min wanka.Dariyar da yakeyi ya hanashi amsa mata, ko me tayi yanzu oho da take cewa ba’a magana a bayan gida.Dressing mirror ya fara shiryawa snn ya koma wardrobe, yashiga jera mata kayan daki daki.Rai a b’ace ta fito ita an sata wankan dole, dressing mirror tabi da kallo, yanda ya tsara gurin ya burgeta ba kad’an ba.Mai ta shafa snn ta d’auko turaruka tana juyasu tana kallo.Can tace “Wannene na fesawa a jiki wannene na kaya ? “Jin bai kulata yasa tace ” Na fati baban fati da kai fa nakeyi.”Barin abunda yakeyi ya yi ya juya ya kallota.Tun kafin yayi magana tace “Oho, nima ba ji nayi an fad’a ba, suwaye fatinayenkanne ma nikam ? “”Zo kiga d’aya.”Yace mata.Ta jikin mirror ya nuna ta yace “Kin ganta ? “”Ban ganta ba Bintu na gani.””Shi kenan lokacin ganin nata ne baiyi ba sai kiyi hakuri.”Ya fad’a tare da karb’ar turarukan hanunta snn ya shiga banbance mata..Doguwar baqar riga mai had,e da hularta ya mika mata, tare da skin tight iya gwiwa ta saka, tana sakawa cikin jin dad’i da annashuwa take cewa, “Aradu kyauta zanyi da tsofaffin kayana dama ai idan aka samu sabo sai a kyautar da tsoho, larai kin samu kaya yasin, ita zan bawa aradu.”Har ta qaraci surutanta bai tankata ba, isa gurin wardrobe d’in tayi ta leqa, La, ilaha illallah, Muhammadu b’ii Abdullahi.(Muhammadu d’an Abdullahi.)Allah am miyattima. (Allah na na gode maka.”Ta fad’a tana komawa baya baya.”Habibi wann tulin kayan duk nawa ni kad’ai ? “Sake juyawa tayi tabi d’akin da kallo, sai ko ta daka tsalle ta d’ale bayanshi, kad’an ya hana su tuntsura.”Meye haka, zaki ka dani ne ? “”Aradu duk cikin murna ne, wnn duka nawa ? Duka d’akin fa, d’akin ‘yan gayu, nima fa na zama ‘yar gayu.”Dirowa tayi daga bayanshi. “Tsaya kaga irin tafiyar da zan rikayi yanzu tunda na zama ‘yar gayu.”Wani taku takeyi tana d’angale hanu tare da mele baki sai wani yauki da yatsina takeyi ita a dole ta zama ‘yar gayu.”Idan kin gama tafiyan  gayun kizo in nuna miki.”Tsalle tayi ta haye gadon tana birgima, tana tsaya in more laushin gadonnan tukuna.”To na tafi, in kon gama morewa sai ki fito.”Ai da gudu ta sauko ta rikeshi “Tare zamu fita yasin, nuna min toh.”Wardrobe d’in ya bud’e yana nuna mata yanda ya rarrabe kayan, har aka kai kan kayan bacci.Ido waje tace “Hande en woni.(Yau mun banu)Bacci ma harda kayanshi, wani abu sai ‘yan gayu. “Shidai zuwa yanzu ya saba da shirmenta shi yasa ko tayi ma baya damunshi saidai idan ta bashi dariya ya dara.🥀🥀🥀🥀🥀🥀 *Garin sarki*Qauyen da aka b’oye bintu.Sun kasance cikin tashin hankali mara misaltuwa, tun daga lokacin da labari ya riskesu wasu sun d’auke Bintu a mota.Kauye ne da babu service balle ayi maganar waya, babu ta yanda zasu sanar da goggon Bintu abunda ya faru.Inna wuro tayi kuka ta tsinewa wanda ya d’auke Bintu yafi cikin kwando.Haka suka kasance cikin alhini da tashin hankali har zuwa lokacin da Yunusa tazo domin ganawa da sahibarsa Bintu.Nan yayi *Gamda katar* da mummunan labari.Cikin tashin hankali mara misaltuwa ya koma ya sanar da mahaifiyarshi abun da ya faru.Ba tare da b’ata lokaci ba ta nemi izini wajen jauro suka kama hanyar Yusa, sai kwantarwa yunusa hankali takeyi da cewa watakila ma ‘yan yusan ta gani ta biyosu ta dawo gurin innarta.Basu kara shiga tashin hankali ba saida suka iso inna ta nuna musu bata san da zancen ba, dama dai can ta riga tasan cewa bintu b’atacciya ce, kuma har yanzu babu wanda yace ya ganta ko ya ji labarinta.”To ko alhajinnan ne suka je suka d’auke ta”Cewar yunusa cikin karin tashin hankali.Girgiza kai inna tayi tace “Banyi tsammani ba, dan d’azu d’azunnan suka kirani suke tambayar ko anji labarin ta.Nanfa Goggo Rabi ta tsure ta fita mayafi a hanu zani na faman fad’uwa.Gidan babban wansu taje ta sa mishi kuka tana ta shiga uku  ta b’atar da ‘yar d’an uwanta, kuka sosai takeyi wanda ya d’agawa musu hankali gashi babu wanda ya fahimci inda zancenta ya dosa.Shiko yunusa yana can ya tasa inna a gaba sai rusa mata kuka yakeyi tana aikin rarrashi.Kaff ya had’a sauran ‘yanuwansu banda goggo Rahi dake aure can wani kauye dan ya fahimci lamarin nata babbane.Dakyar ta daure ta zayyane musu abun dake faruwa wanda ya jawowa sauran shiga wani sabon  tashin hankali sai salati da salallami suke ta zabgawa.Cikin matsanancin b’acin rai Babban yayansu yace “To yanzu da kika zo kika tasa mu a gaba kina kuka me kike so mu miki ? “Wato ki kara samu cikin tashin hankali naki hankalin ya kwanta ko ? Mu dama a hakan muka d’auka ta b’ata, me yasa yanzu zaki kawo mana wnn labarin ? Idan ba rashin hankaliba kina sane aka d’aura mata aure amma a haka kika dauketa kika boye sbd son zuciya , wa ya gaya miki ana ja da *Al’amarin ubangiji*To Wlh kiyi gaggawar nemo mana Bintu idan ba haka kotu ce zata raba mu.Sauran ma kowa fad’an albarkacin bakin shi yakeyi cikin nuna mata tsantsan b’acin ransu, babu wanda ya sassauta mata a cikinsu.Gidan innar Bintu suka tattaru suka koma, nan suka had’u sukayi ta jajanta al’amarin , tare da bawa innar bintu hakuri snn kuma suka ce kada goggo ta kuma zuwa gidan d’aya daga cikinsu har sai ta kawo musu Bintu idan ba haka ba basu ba ita.A cewar wansu babba tunda ta iya aikata haka ga ‘yar Barkind’o suma sun tabbata haka zata yi musu ko fiye ma idan taga bayan idansu.Itadai goggo Rabi sai kuka takeyi tana share majina da hab’ar zaninta.*Inna da Habibi ku taimaka ku bayyana Bintu ko goggo Rabi zata samu kwanciyar hankali🙏🙏*(01/05 11:26) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers.**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*85-90*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Congratulations  Zeezeen Fasaha, for the successful completion of ur nvl GAMDA KATAR**Littafin ya fad’akar kuma ya nishad’antar, Allah ya shiryi masu hali irin Nayna, Allah ya karemu da zuri’ar mu daga fad’awa irin wnn halaka.**More greese to ur elbow, sister Zainab Bugaje.**Sai mun jiki a sabon nvl in Allah ya kaimu bayan Ramadan.*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*K*amar yadda ya d’aukarwa kanshi shi yakeyi mata lesson duk bayan sallar la’asar, hakan yasa ya ke dawowa gida da wuri.Sosai take fahimtar karatun wanda yake arabic da boko ne .”Na gaji da karatunnan haka sai gobe kuma.”Tace tana miqa alamun dai da gaske ta gajinne.”Saura mana topic d’aya.”Baki a ture tace wanne kenan ? “” Qabli da Ba’adi.””A wani gari suke, a yusa ko anan jalingo ? “Tun da yaji tayi wnn tambayar yasan tayi niyyar baxatayi karatun bane, dan bazai manta ba haka ta tab’a mishi da zasu yi karatu akan tsarki.Sai ce mishi tayi “In ba jaye jayeba, sarki da girmanshi za a ma wanka, ita tasan har abada ba abunda zai sata tayiwa sarki wanka sbd haka baza ta b’ata lokacinta wajen karanta wankan sarki ba, duk yanda yaso ya fahimtar da ita tsarki yake nufi taki ta saurareshi da yake batayi niyya ba.Sbd haka yanzunma kyaleta yayi ya jawo ear piece d’inshi ya maqala a kunne ya kwanta rigingine.Kusa dashi tazo ta kwanta tana tambayarshi yaushe zai kaita gidan aunty Nafi.Jin bai amsa ba yasa ta zare earpiece d’in ta rike.Harara ya zabga mata yace “Dalla bani abu, ke kinki kiyi karatu nima hanani zakiyi ? “”Wnn ne karatun ? “Ta tambaya tana d’aga earpiece tare da yatsina fiska.Sa mata yayi a kunne yana cewa “Hadda nakeyi saurara kiji.””Laa ashe da gaske ne.”Ta fada Qira’a na tashi a ciki.””Ayya to yaushe zaka kaini ? “Ta sake tambaya tana marairaicewa.”C’mon get lost, damuwarki daban.”Yace yana karb’ewa gaba daya daga hanunta.Daddagewa tayi cikin fushi tace “Sharap, waddan harr, bugudul bul, bladi foket, nima ai na iya turancin ba kai kad’ai ka iya ba.”Ta karishe tana murgud’a baki da juya ido.Sakin baki yayi yana kallonta, can kuma tace “Kasan noi noises, to ni inada noinoinses.”Qarar wayarshice tasa ya maida hankalinshi ga wayar .”Sorry, wrong number.”Abinda yace kenan.Yana kashe wayar aka kuma kira.”Ikon Allah nace musu ba nambar bane kuma ya sake kira.”Bani wayar tace tare da fisgewa tun bai bata ba.”Alo.”Tace a masifance.Saida hanjin cikinta ya kad’a jin katon muryar da ya amsa mata.Dakewa tayi tace “Gwatigwal, gwati ta tattara kunduna. Becce yaama , cegejo.”Kitt taji an kashe wayar, hakan yasa ta kwashe da mugun dariya tace “Ya gudu, qaton banza.””Me kika ce mishi kenan? “”Kai, nima fa ban sani ba, becce yaman ne kawai nasani.Na ce mishi hakarkarin uwarshi.””Lallai na yarda ke d’in no nonsense ce.”Yace yana mata dariya dan ya fahimci hakan takeso tace d’azu take ta cewa noinoises.””Meye ne ma noinoises d’in ? “Ta tambaya tamkar ba ita ta fara kawo zancen ba.D’aga kafad’arshi yayi yace ban sani ba nima, ke baki san abuba sai kiyi ta fad’a.”Da haka zaman ya watse wai ita tayi fushi, ta tashi ta tafi wajen Mmn Larai.🥀🥀🥀🥀🥀🥀A kwana a tashi babu wuya a wajen Allah, yau ga Bintu sanye da uniform kamar yanda take mafarki gani a ko da yaushe.Washe bakinnan takeyi kamar gonar auduga.Duk wanda ya kalleta sai ya ga bayannanen farin ciki a tare da ita.Sbda yanda ta kwallafa rai a akaratun yasa bata wasa dashi, tana sa hankalinta sosai, in har bata gane ba kuma ba b’ata lokaci zatayi tambaya , saidai kam inta samu sarari akwai son wasa, ga kuma yanda ta maida kanta comedian a gurin mates dinta har da malamai, hakan yasa lokaci guda ta zamo very popular.Cikin kwanakinnan Habibullah yana cikin zafin kai sbd shirye shiryen tafiya makarantar da yakeyi, abubuwan ne suka cakud’u suka yi mishi yawa.Sam baya so yayi nesa da gida, ga kuma computer center da ya zame mishi tamkar jaraba wanda daddy yayi barazanar rufe shi muddin ya mishi gardama akan tafiya karatun , babban matsalar rayuwarshi kuma shine tafiyar da zaiyi ya bar BintuBaisan yayi mummunan shaquwa da Bintu haka ba saida aka tada maganar tafiya karatun, duk da dai yayi sa’a ba qasar gaba daya zai bari ba, Zuwa Bauchi ne, (ATBU) wanda yasan idan ya bushi iska zai iya zuwa yayi koda kwanaki biyu ne ya koma, amma hakan bai hana shi shiga damuwa ba.Wani irin matsanancin kewarta yakeyi tun kafin ya tafi, to inaga in ya tafi kuma.Gashi kuma abunda ya lura dashi sam bata sakewa da mummy da kannenshi, idan kaga walwalarta , tana tare dashi ne ko daddu ko kuma su Mmn larai.In dan ta itane ma bata qi ta koma gidan aunty Nafi da zama ba dan tafi jin dad’in can.Sosai yayi zurfi a tunanin shi har baisan kwalla sun gangaro daga idanunshi ba.saida yaji d’uminsu ta kunnenshi dake a rigingine yake.Sallamar da ta doka ne yasa shi saurin goge fiskarshi ya amsa da disasshiyar murya.Shigowa tayi ta zauna kusa dashi tana qarewa fuskarshi kallo kafin ta shafo hawayen da suka rage kusa da kunnenshi.”Habibi kai da kunne kake hawaye ? “Kad’an ya bud’e idonshi ya kalleta.”Me ya sameka kake kuka ? “Ta sake jefo mishi tambayar ganin yanda idanunshi suka rine.Tashi yayi ya zauna ya riko hannayenta duka biyu yana kallonta.A ranshi yake raya sun kusa rabuwa kenan, sai sun d’auki lokaci kafin su kuma ganin juna.”Na fati Baban fati.”Ta fad’a tana girgiza hannayensu da qarfi.Murmusawa yayi sbd duk lokacin da ta kirashi da hakan sai ya murmusa.”Menene ? “Ta kuma tambayarshi.”Zaki sha Ice cream ? “Ya tambayeta kamar baya so yayi magana.Saida ta lashe lips d’inta kafin ta gyad’a mishi kai dan gaba d’aya ya sanyayar mata da jiki da yanayinshi.”Tashi muje to.”Ya fada yana mikewa.”Harda gidan aunty Nafi ? “”Eh.”Kawai yace mata a takaice.Sallamar mummy suka kan zasu je gidan aunty nafi, nan su Iman ma suka ce zasu.Tafe suke cikin motar babu mai magana sai qira’ar Sheikh Ahmad Sulaiman dake tashi cikin motar.”Habibi, Ayya ka kaini gidan kawuna inga Hammana.””Kin san anguwar ? “Sai da ta d’anyi jimm kafin tace “Na sani a Tudun wada suke.”Hanyar tudun wada ya d’auka sai jin dad’i takeyi zata ga Hammanta yau.”Mun isa ta ina zamu bi ? “Ya tambaya yana kallonta.”Shiga lungun can.”Tace tana nuna mishi lungun.”Tsaya.”Tace mishi.Neman guri yayi yayi parking ,hakan yasa ta leko kanta ta windown mota.”Kai.”Ta cewa wani yaro da yazo wucewa.”Kasan gidan kawuna, gidan akwai Hammana sunanshi Mudassiru ? “Shiru yaron yayi yana kallonta.”Kai sunan kawun nawa kawu Ahijo, wani baki dogo yana da farin gemu.””Ban sanshi ba yaron ya bata amsa tare da barin wajen.Kwashewa da dariya su Miemie dake bayan mota sukayi, shi kuma Habibullah kallonta kawai yakeyi yanda taci serious ita a dole tayi abin kirki.”Wai dama baki san gidanba kikace muje .””Tambaya dama zanyi, dan bazan iya gane gidan ba.”Juya motar yayi yana cewa “Kin dai b’ata mana lokaci dai.”Cuno bakinta tayi tana cewa “da munci gaba da tambaya nasan zamu gane gidan.”🥀🥀🥀🥀🥀🥀Tun jiya da taji ma ganar tafiyar ta shiga tashin hankali  tun tana jin abin kamar wasa, taga shirin na gaske ne dan mummy da da Mmn larai sun dage sai soye soye sukeyi, ga kuma friends dinshi ta suke ta shige da fice dan zuwa mishi sallama.Lokacin da yake mata nasiha kan ta maida hankali ga karatunta banda wasa kuma banda kawayen banza kamar yanda ya saba yi mata a cikin ‘yan kwanakinnan .Kawai sai ta rushe da kuka, wasa wasa kuka yaki tsayawa, yayi rarrashi har ya gaji ya had’a da daddy.Shima kanshi da ya kauce saida yayi kukan dan shi kadai yasan abinda yakeji .Washe gari kuwa ranar tafiyar haka duk suka tashi a sanyaye.Basu shiga tashin hankali ba saida aka gama loda kayanshi a mota zai shigasu tafi gida yarud’e.Bintu kuka, Miemie kuka Iman kuka, suma kansu Mummy da daddy daurya kawai sukeyi.Da gudu Bintu ta koma palour ta kwanta tana risgar kuka dan bata son ganin tashinshi.i.Shi kuwa tana barin wajen ya bude kofa zai fito Daddy ya ya hana shi.Wani irin abu mai nauyi da daci ne yji ya maqale mishi a maqoshi yakan yasashi kifa kanshi kan cinyarshi har suka fita bai kuma d’agowa ba.Binyu kuwa jin tashin motarsu ya sa ta tsananta kukanta lokaci guda kuma zazzab’i mai zafi ya rufeta……(02/05 20:41) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*90-95*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Congatulations**Foulani Cerdia, (marubuciyar Mahaifina)* Our newly wedded Amarya.Ina tayaki murnar shiga sabuwar rayuwa da samun karuwa na aure da kikayi.Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa, Allah ya azurtaku da zuri’a dayyaba.*Happy Married life Deeyan papa*🥀🥀🥀🥀🥀🥀Wasa wasa sai da ta kai sati guda ana jinyarta duk ta zama abar tausayi.Sosai daddy ke nuna mata kulawa da tausayawarshi gareta, hakama aunty Nafi.Suma larai da Mmnta sosai ciwonta ya damesu, haka kuma tana samun kulawa daidai gwargwado daga garesu.Mummy kam dai ba yabo ba fallasa, a gaban daddy ne take bata tata gudunmawar kulawar, saidai yana bada baya itama zata shiga harkokinta ta manta da wata Bintu, balle kuma su Mie mie da ta zame musu abokiyar fada dan sam basa shiri, hakan yasa a yanzun ma babu wacce ta nuna tausayawarsu gareta.Ita da kanta take matsawa a kira mata shi, amma duk lokacin da aka bata wayar tana jin muryarshi zata fashe da kuka , shi kuma hakan ba karamin kara mishi damuwar yakeyi ba dan dama acikinta yake, gaba daya ya yi sanyi ya zama wani iri ba dadin jikinnashi yakeji ba, ko daga muryarshi ma kaji zaka gane hakan.Dakyar ta ware ta ci gaba da zuwa makaranta duk da dai abin ba gama sakinta yayi.Da suka samu hutun makaranta kuma da kanshi daddy ya dauketa ya kaita yusa.Sati guda sukayi suka juyo bayan ta zaga danginta sai murnar ganinta sukeyi dan dama inna ta sanar dasu komai ganin yanda goggo ta tayar musu da hankali, saidai ita goggo Rabince har yanzu bata sani ba dan wansu babba ya hana a fada mata yace su barta sai taji a jikinta sbd gaba.A gidan aunty Nafi ta qarasa hutun, cikin kwanciyar hankali kuma kullum sai sun gaisa da Habibullah.Tun daga lokacin idan akayi hutun makaranta daddy yake kaita da kanshi su dawo tare.Yawanci kuma a gidan agidan aunty Nafi take qare hutunta, acan kuma take koyon girke girke kala kala, idan ta dawo gida kum a ta d’ora a gun goggo marka inji ta.Can kuma Bauchi saidai Daddy yaje gurin Habibullah, dan sam ya hana shi zuwa duba da halin da suka shiga lokacin tafiyarshi, yace sai sun saba sosai da rashin ganin juna, hakan yasa saidai suji juna ta waya, da yake kuma a gidan abokin daddyn ya ke zaune, yaji labarin duk wani hali da Habib din ya shiga farkon zuwanshi.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Yau ta kama ishirin da bakwai ga watan Ramadan mai albarka.Diran bazata yayi musu ko daddy bai sani ba sbd yasan hanashi zaiyi.Kusan magriba ya iso, saidai mummy ta ganshi kawai kamar daga sama.Da murna ta tareshi tana tana ta cewa “My son zuwan bazata haka, ba sanarwa.”Shafa kanshi yayi yace “To ya zanyi mummy daddy ya hanani zuwa ni kuma kewarku ta dameni.”Ya fad’a yana rarraba idanu.”Mummy ina kannena ban ji motsinsu ba.””Suna gidan Nafeesa yau a can suka wuni.”Shiru ya d’anyi kafin yace “Barin je inyi wanka.” Saida ya biya ta kitchen wajen Mmn larai suka gaisa ta mishi barka da zuwa kafin ya wuce.Gun mummy ya sake dawowa yace ta bashi key zaije ya dauko su.Hanashi tayi tace ya huta sun kusa dawowa beside ma magriba tayi.Ba don yaso ba ya wuce masallaci.Ko da ya idar da sallar magriba dabino da ruwa kawai yasha ya tashi zai fita, saida tayu magana ya qara da fruits kafin ya koma bakin gate ya zauna, har akayi kiran sallar isha’i ya wuce ya tafi masallaci.Suna idarwa ya fito ba tare da ya tsaya dogon addua ba, ya nufi gun mummy yana tambayar ko sun dawo.A gajiye suka nufo palourn tana gaba suna biye da ita a baya.”Assala….”Sallamar ne ta katse sakamakon ganin wanda bata zata ba zaune yana facing kofar shigowa palourn.Wani tsalle ta doka tare da ihun kiran sunanshi ta nufeshi a guje.Cikin zafin nama ya cab’e ta ya daga ta sama yana juyi da ita cikin shauqi da ishiqi tare da tarin farin ciki marar misaltuwa.Ihunta yasa mummy fitowa daga dakinta cikin sassarfa, haka ma su miemie suka qaraso da sauri har suna hadawa da gudu dan ganin abunda takewa wnn ihun.Suma da mamakin ganinshi suke ta kallonsu, saida ya gaji dan kanshi ya direta kan kujera ya bata peck a forehead, kafin ya kamo hannayensu Miemie da Iman yana” i miss u my sisters.”Sannu da dawowa suka mishi cikin farin cikin ganishi snn ya maida hankalinshi ga Bintun dake kallonshi cike da madaukakin farin ciki tamkar yau ta fara ganinshi.”Habibi yaushe ka iso ?  Me yasa baka fad’a ba ?  Me yasa baka kira aunty Nafi ka fada mata ba ? “”Wanne zan amsa a ciki Islam ? “Yace lokacin da yake zama kusa da ita , suma su aiman nan kusa dashi suka zauna dukansu cikin tsantsan farin ciki.”Habib kar ka biyewa shirmensu ka tashi kaje kaci abinci,kaje ka huta gajiyar hanya. “Cewar mummy.Sai a snn yasan da tana wajen.Yana tashi Bintu ma ta mike ta bishi tana cewa “da  ka fada mana zaka dawo ai da zama zanyi na had’a maka wani juice mai dankaren dad’i wanda aunty Nafi ta koya min.””Woow, ashe harda Juice kika iya ? “Ya fada lokacin da suka isa wajen dining din.”Kai harda girki mafa na iya.”Serving dinshi ta farayi tana tambayarshi me da me zaici.”Duk abinda kika sa zanci.”Ya ce mata.Labari take ta bashi yana cin abinci sai kallonta yake tayi yana mamakin girman da sukayi dukansu cikin shekaru biyu.Sai washe gari ya fito musu da tsarabarsu da ya kawo musu, Mummy sai korafi takeyi shi da yaje karatu me ya hada shi da tsaraba.Tare suka je yusa bayan anyi sallah da kwana biyu, sai a  snn goggo Rabi tasan da cewa an gane Bintu, dan sun hadu a can, shi kuwa Yunusa har yayi aurenshi, kawayen Bintu ma su indo duk sunyi aure. sosai sukayi ziyara dukansu har da su Miemie, satinshi biyu ya koma.Wann karo abin da sauki, cikin kwanaki uku ta ware.Daga nan kuma idan ya dan samu chance yake kawo musu ziyara.*BAYAN SHEKARU UKU*Zuwa wnn lokaci su Bintu an zama cikakkun ‘yan mata, SSCE suke rubutawa tare da su Miemie dan Habibullah ya bada shawarar haka tunda tana kokari a karatun , sbd da yanda ya tsara da ya qare service dinshi babu bata lokaci Bintu zata tare kuma daddy ma ya yi na’am da hakan.Saidai suma daddy da mummy suna nasu shirin game da maganar auren da zasu mishi wanda mummynce ta buqaci hakan, dan ta yanke tare za ayi bikin da kuma tarewar Islam din duk da dai shi uban gayyan bai da labari, saidai suna da yakinin bazai watsa musu qasa a ido ba.Zuwa wnn lokacin kuma Bintu ta kware wajen sarrafa girke girke kala daga wajen aunty Nafi da Mmn larai, dan sosai aunty Nafi ta ke koya mata su da kuma gyaran jiki da kuma dabarun zaman aure dan yanzu kam tasan cewa ita matar aurece kuma tasan mijin.Wani irin shaquwa sukayi duk da basa tare amma kusan kullum suna makale ta waya, a hankali da dabara ya cusa mata soyayyarshi wanda tun tana daukan abun wasa har ya zama so serious.Zaman su dasu Mie mie kuwa dai gashinan dai babu yanda suka iya da ita, dan ta zane musu kadangaren bakin tulu, babu abinda yafi damunsu game da ita illa ganin irin extra kulawa da take samu daga daddy da aunty Nafi da kuma uban gayya Habibullah.Mmn larai kam tana ganin fi’ili kala daga wajen Bintu a cikin kitchen yanda take sarrafa abubuwa take sha, har ita ma Mmn larai ta saba.Takan yi blending aya da dabino  da kwakwa tasa cikin fridge idan yayi sanyi tasha, wani lokacin har  ta kara da milk.Takanyi hadin Abarba, da kwakwa, tasha.Ko kuma ta hada fruit salad, ta yayyanka fruits daban daban ta sa fridge tasha.Takan hada kankana da ayaba ta yayyanka ta zuba milk tasha.Ko kuma milk din zalla ta hada da zuma ta gauraya tasha.Dabino kuma tare da aya ta rika hada su haka tana ci, wnn kuma cimar tace ko a makaranta.Indomie kuma ta dafa ta yanka dafaffen kwai akai tare da danyar tomatoes, taci, wani lokacin har jelouf sin shinkafa ko taliya haka take musu.Rice and stew hade da plantain ko kuma ta yayyanka ayaba akai tana ci tana lumshe idanu.Wnn duk training din aunty Nafi ne.Kuma sun zame mata jiki, babu wayewan gari da baza tayi daya ko biyu daga cikin wadannan ba, duk da dai bata san amfaninsu ba ita dai tana daukan hakan a jin dadinta ta kawai takeyi.🥀🥀🥀🥀🥀🥀Yau suka gama last papern su , a gajiye suka dawo gida sbd bata lokaci da sukayi da friends dinsu suna ban kwana harda pictures sukayi ta snapping , last pics with uniform.Saida ta fara biyawa ta wajen Mmn larai tana ce mata ta tayata murna yau ta rubuta last paper, tayi bye bye da secondry sch.Ta dan jima a wajenta kafin ta shiga part dinsu .Su Miemie ta tarar suna ta zuba surutu, daga sallamar da tayi sai sannu da gida da ta yiwa Mummy tayi wuce dakinta ta watsa ruwa ta canza riga da skirt na English wears marasa nauyi kafin ta sauko dan bawa ciki hakki.Tana sauqowa idonta ya sauka gurin da su miemie suke zaune kan three sitter sunsa wani handsome guy a tsakiya sai bashi labari sukeyi.Hada ido sukayi da gayen tayi saurin kawar da kanta. saida ta isa kusa da su ta sake dagowa.Ganin yanda ya kafeta da ido ya sata gaisheshi ta wuce.D’ebo abinci tayi taje ta bude fridge ta dauko kunun ayanta da tasa tun da safe kafin ta tafi sch. ta zo ta zauna nan tsakiyar falon ta basu baya ta shiga cin abincinta.Tana gamawa ta tattara gurin snn ta koma dakinta dan bude phone dinta da ta kulle kafin ta tafin.Mssgs din Mutuminnata ne sukayi ta shigowa na taya murna qare exams dnta sai kuma sauran na kalamai ne masu sanyaya zcy.Tana karantasu tana smiling cikin shauqi har ta gama kafin ta sake saukowa ta tafi wajen abokiyar hiranta goggo marka ,dan larai kam anyi aurenta.Sai dare ta shigo part din nasu ta zauna a palour tana kallo.Miemie kawai ta tarar dukansu babu wacce ta kula yar uwarta.Suna nan zaune ya shigo da sallama, direct kan two sittern da Bintu take zaune yaje ya zauna fiskarshi dauke da fara’a yace Gimbiya kallo akeyi ne? “Da mamaki ta kalleshi tana tunanin abinda ya sake dawo dashi yanzu kuma snn kuma ma shi wanene, meye matsayinshi a gidan da yake shigowa kai tsaye haka, dan ita in ba yau ba bata taba ganinshi a gidanba.karamin gyalen data yafa a kanta ya dan rike tare da cewa “Ba maganane queen.”Tsam ta mike tabar musau falon ma gaba day ta haura dakinta tana jin wani irin tsoro na shiganta.Washe gari abun mamaki saiga kiran Habibullah tun basu gaisa ba ya fara ce mata “I had a terrible dream yester night Habibty .””Me ya faru Habibi, wani irin mafarki” ta tambaya a kagauce.”Ganinki nayi da wani kuna zance, wlh mafarkn ya daga min hankali sosai ba kadan ba.”Zaro ido tayi kamar yana kallonta kirjinta na bugawa tace “Habibi sharrin mafarki ne, kaima kasan saidai a mafarkin hakan bazai faru da gaske ba.”Saida ya sauke ajiyar zcy kafin yace  “I hope so.”Sauran hiran dai anyi shi ne kawai amma gaba daya a tsarge take gani take kamar yasan wani ya mata magana jiya da dare……🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*95-100*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*T*un daga ranar saurayin da ta ji an kira da Hafiz ya maida gidan gidan zuwanshi.Ita kuwa ko da wasa bata yarda su hadu, duk abinda tasan zai iya hadasu kaucewa takeyi.Tana jinshi zata shige d’akinta ko kuma taje gurin Mmn larai ko gurin daddy.><()Yau gidan gidan gaba daya ya kacame da shirin tarban babban bako, wato  Habibullah, wanda ya qare service dinshi zai dawo.Mmn larai, Bintu har su miemie yau ba a barsu a baya ba duk suna kitchen, mummy kuwa aikinta bada umarni.Juice kala uku da sobo, Bintu ta hada sai sauran snacks da girke girke da sukayi.Duk wanda aka gama sai Bintu ta dandana tace bari taji ya taste dinsa yake.A haka suka qare aikin cikin zumud’i, dukansu cikin farin ciki suke.Suna gamawa ta kirashi ya sake tabbatar mata yana hanya.Wanka ta fad’a,ta dau lokaci kafin ta fito.Wajen zab’en kayan da zata saka ma saida ta b’ata lokaci, ta fidda wnn ta mayar, k’arshe ta zab’o wata pink material da akayiwa dinkin gown, wanda yasha adon stones, sai d’an madaidaicin gyalenshi wanda aka qawata bakin gyalen da adon golden coloured stones.Light make up tayiwa fiskarta, ta shafa pink din janbaki a lips dinta, lokaci guda fiskarta ya fara glowing, dan ba karamin kula da fatar  jikinta takeyi ba, sbd duk lokacin da zata shiga wanka sai ta shafa zuma yakai 15 minutes a jikinta kafin ta shiga wanka, wani lokacin kuma zuma da lalle take hadawa ta shafa.Turaren wankan da aunty Nafi take saya mata kuwa yanzu har ya riga ya bi jikinta.Tana cikin fesa turare taji Mummy tana kwad’a mata kira.A hanzarce ta gama ta fito tana mummy gani, duk a tunaninta Habibinta ya iso ne.Turus ta tsaya ganin  Hafiz kan dining table yana cin abinci tare da kurb’a sob’on da ta had’a.Wani kululun bakin cikine ya tokare mata maqoshi, ta fara tunani kiran me mummy ta mata, kodai ta kirata ne ta zo taga abin takaici.Bata qare tunaninta taji mummy na ce mata, “Yauwa Bintu, dama zaki raka Hafiz ne gidan Nafeesa, ya dade bai jeba, yace yas manta wajen, kin san baya garin, bai dade da dawowa ba.”Cikin kad’uwa da mamaki ta kalli mummy, snn ba tare da ta shirya ba tace “Mummy ina su Miemie, bazasu rakashiba.””Na aikesu ne, Bintu idan ba haka ba kema kinsan bazance ke ki rakashi ba.”Shiru tayi cikin kunar zuciya, to me mummyn take nufi da ta raka Hafiz da aurenta.”To mummy shi baxai haqura gobe ko wata rana su kaishi ba, sai yau.”Ta fada idonta kyar akan mummy.Had’e rai mummy tayi tace “Kina daiso ki nuna min ban isa dake bane Bintu, bankai in aikeki ba, ko da yake na jima da sanin baki d’aukeni a matsayin uwa ba.””Kamar yanda kema baki daukeni a ‘ya ba.”Bintun ta fad’a a ranta.A zahiri kuma sai ta juya tana cewa “Barin d’auko hijabina.”Nufinta idan ta shiga taki fitowa har sai taji Habibullah ya iso.Idan bazaki je bane ki fada min bawai ki tsaya ja in ja dani ba, meye a wnn gyalen na jikinki, ba mota zaku shiga ba?”Mummyn ta fad’a cikin b’acin rai.Maida kallonta tayi ga Hafiz, taga hankalinshi naga wayarshi tamkar baima san abinda ke faruwa ba.Cikin kunan zuciya ta fita daga palourn shima ya tashi ya bita, yana cewa mummy sai ya dawo.Suna fita bakin gate ta juyo ta galla mishi harara, shi ko tamkar baisan abinda tayi ba ya haske ta da murmushi.”Lallai wnn ya cika cikakken dan rainin sense.”Ta ayyana a ranta.Wuceta yayi ya isa gurin da yayi parking na motarshi kafin ya juyo ya kalleta.”Ya kika tsaya, let’s go pls.”Hararan ta kuma maka mishi kafin ta karaso kusa dashi.”Kai Hafizu kake ko Fa’izu, ka kiyayeni, ka fita daga idona in rufe.Wai meye damuwarka da nine, in ba rainin hankali ba ka rasa wanda zai maka rakiya sai ni, to bari kaji in fad’a maka babu inda zanje, Idan kaga dama kaje ka b’ata karewar rashin gane hanya.”Tun da ta fara masifarta ya kura mata ido yana kallonta fiskarsa dauke da murmushi,  shi a ganinshi ma masifan kyau ya qara mata baran ma yanda take motsa dan k’aramin bakinta da yasha pink lipstick.Saida yaga ta dasa aya ya d’aga hannayenshi irin surrender d’innan.”Bafa ni nace ki rakani ba mummy ce, kuma nasan baza kiki jin maganarta ba, ko ya?”Ya qarishe maganarshi yana d’age gira.””Da alama ta mance ni d’in matar aurece, shi yasa kaga ni kuma ban mance ba sbd nasan darajarshi.”Nuna ta ya shigayi da yatsarshi yana dariya “Ke d’ince matar auren, matar wa kenan? Kai da wasa ma kikeyi dan ni ban ga alama ba.”A masifance tace “Eh, da yake rubuce yake a goshi ba.””Ban ce ba muje kawai dear.”Tsaki taja tace “Babu inda zanje kayi tafiyarka kawai.” Tana fadin haka ta juya zata tafi.”Mummyn fa me zaki ce mata?”Taji ya jefo mata tambayar.Juyowa tayi a fusace.”Ina ruwanka da abin…..”Katsewa maganarta tayi sakamakon ganin motar da tayi parkin dan nesa dasu, tabbas motar ta gidansu ne.”Wani irin tsinkewa zuciyarta tayi, ganin Habibullah ya fito daga cikin motar har yana buge goshinsa.Kafanta ne ya fara rawa, jikinta taji duk ya saki.”Na shiga uku.”Tace a ranta.Kamar yadda ta kafeshi da ido haka shima ya kafe ta, duk suna tsaye tamkar an dasa su.Ganin yanda ta yanke maganarta ta kafa idanunta gu d’aya yasashi waigawa.Murmushi yayi ya qarasa kusa dashi ya mika mishi hanu.Sai a snn ya kawar da idanunshi daga kanta ya ja kafarshi da yayi mishi nauyi yabar wajen ba tare da ya kalli Hafiz ba.A hankali tabi bayanshi kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.Babu abinda ya d’aurewa Bintu irin ganin su Miemie sun fito suna mishi oyoyo, Mummy ma da fara’arta ta tareshi.Sakin baki tayi tana kallonsu har suka shiga ciki, tana nan tsaye har driver yazo ya wuce da kayan da ya dawo dasu, tana ta jin hayaniyarsu a palour.Qarasawa ciki tayi tana kallon mummy taji ko zata ce wani abu, amma ga mamakinta sai mummy tace “Ke kuma da ga ina?”Kwalalo ido tayi wadanda suka cika taf da qwalla, sai kuma ta maida kallonta ga Habibullah, taga shi d’inma ita yake kallo, sai ta sake kallon mummy da mamaki tace “Mummy ba..”D’aga mata hanu mummy tayi “Bance lallai ki fad’a min ba dan na lura yau kuma halin sun motsa.”Kallon mummy takeyi ko kiftawa batayi, tabbas yau mummy taci albarkacin ‘yayanta Habib da aunty Nafi, badan haka ba Allah ne yasan kalar tijarar da zatayi mata.”Yaya in zuba maka abinci ?”cewar Miemie.Maganar ya dawo da ita kenan daga tunanin da ta fad’a.Murya a shaqe yace.”No, basshi kawai sai anjima.”Ya bata amsa tare da mikewa yana barin palourn.Da kallo ta bishi har ya fice snn ta share hawayen da suka zubo mata, ta sake maida dubanta zuwa inda tasan mummy take, saidai itama mummyn ta riga ta bar wajen.A sanyaye ta dafa kujera ta zauna, ta shiga tunani.Tabbas akwai abunda mummy take nufi da ita, idan ba haka ba ai tace mata su Miemie basa nan kuma ta gansu cikin gidan, snn idan ba da wata a qasa ba wace uwa  mai kishin d’anta ne zata had’a matarshi da wani  wanda ba muharraminta ba  tace su fita tare.Tunawa tayi da irin zumudin da suka rikayi na son ganin juna, irin yanda yake gaya mata missing dinta da yayi da kuma yanda yake marmarin ya dawo ya ganta, yanda ta shirya yi mishi tarba na musamman, amma yanzu komai ya wargaje a dalilin mummy, komai ya koma musu b’acin rai.Goge fiskarta tayi ta tashi, a ranta tana fad’in dole taje ta kare kanta koda baxai saurareta ba.A hankali ta d’aga labulen d’akin tare da sallama a dakile.Kallo d’aya ya mata ya kawar da kai, a ranshi yana tuna wani munafurcin ne yasata kuka.Kusa dashi ta durkusa kanta a qasa, “Habibi dan Allah ka d’an bani Lokacin ka, zanyi explaining.”Ta fad’a muryarta na rawa.”Explain what,” ya katse ta cikin karaji saida ta rintse idanunta.”Me zaki iya fad’a min bayan abinda idanuna suka ganemin ba fad’a min akayi ba, Islam kin bani mamaki ,am really disappointed in you, da iliminki da hankalinki? to me amfanin karatun? Kwanaki da nace miki na ga hakan a mafarki me kika ce min? Ashe duk yaudarace?”Girgiza kanta ta shiga cikin sautin kuka tace “Wlh, ban sanshi ba, mummy ce…””Shut da hell up, baki sanshi zan ganku tare, fice min a d’aki before i lose my temper, getout i said.”Ya karasa a tsawace har jijiyoyin kanshi suna tashi.Fashewa tayi sosai da kuka har jikinta na rawa, “Pls ka saurareni kafin ka yanke min hukunci.””Ok fine, tunda ke baza ki fita ba ni bari in fita in bar miki d’akin “Ya fad’a tare da mikewa.Da sauri ta tashi ta tsaya tana kallonshi, “Ba sai ka fita ba, ni zan fita, Allah ya huci zuciyarka.”Tana fad’in haka ta fita da sauri tana mai ci gaba da kukanta.Binta da kallo yayi har ta fita, kukanta ba qaramin tab’ashi yakeyi ba, saidai shima a yanzu baiki ya samu yayi kukan ba ko zai samu relief a zcyrshi.Kwanciya yayi yana dafe zcyrshi da yakeji kamar zata faso kirjinshi ta fito tsabar bugawar da takeyi.Bada jimawa ba saiga miemie ta shigo da abinci ta jera mishi.”Sannu yaya, gajiyarne?”Ta tambaya tana kallon yanayinshi.Dafe kanshi yayi dan sam bayason magana, baiki su barshi ba dan kad’aicewa yake buqata.”Kayi haquri yaya, naga kamar ranka a b’ace yake.”Ta sake fad’a still tana kallonshi.Tashi yayi ya zauna yana fiskantarta.”Tun yaushe Hafiz yake zuwa gidannan Miemie?.”Ya tambaya tamkar zaiyi kuka.”Ya dad’e yana zuwa kuma kullum sai yazo, wani lokacin ma sau biyu yake zuwa a rana guda.””Me yake kawo shi kullum?.”Saida ta d’anyi shiru na d’an lokaci kanta a duke snn tace “Eh, to da farko dai zumunci yake zuwa , saidai daga baya naga idan yazo ma kamar gun Bintu yake zuwa wani lokacinma idan yazo kofar gida yake tsayawa baya shigowa.””Mummy ta sani?””Ban sani ba kam, amma inaga bata sani ba dan kamar basu so ta sani.””Tashi kije.”Kawai abinda ya ce mata kenan.Har ta mike zata tafi ta dawo tace “Yaya abincin fa?””Jeki kawai zan ci.” Har dare tana d’akinta bata fito ba, ko da daddy ya dawo bai ganta ba tambaya suka ce mishi yau ta shiga da wuri ne.Cin abincin yakeyi tamkar mai cin magani dan dai mummy ta tsare shine, hankalinshi duk yana gurinta dan yana da tabbacin bata fito taci abinci ba.Washegari ma haka har akayi breakfast bata fito ba, ko da daddy ya aiki Iman ta kirata ta dawo tace tana bacci.Har aka gama aka watse shiru, hakan yasashi zuwa ya leka ta da kanshi.Tana jin alamun motsin mutum tayi sauri ta kudundune kamar tana bacci, dan a halin yanzu bata son ganin kowa a gidan, baranma mummy.Ya dad’e a tsaye yana kallonta ba tare da yayi magana ba, daga bisani ya fita.Tana jin ya fita ta tashi a gurguje ta shiga tayi wanka,ta shirya ta d’auki karamar travelling bag dinta ta zuba kaya kala uku ta dauki duk wani abin buqata ta hada a ciki snn ta saka katuwar hijabinta har qasa ta fito ta rufe d’akinta ta sauko.Bata tarar da kowa ba cikin falon hakan ya qara mata qwarin gwiwan fita cikin azama ta nufi bakin gate.Sauri sauri takeyi har ta fita daga gidan ta nufi hanyar da tasan zata samu napep…….(10/05 22:11) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers.**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*105-110*🥀🥀🥀🥀🥀🥀D’akin Bintun ya sake komawa wnn karon da gudu ya haura steps d’in, wanda yasa Miemie da Iman sakin baki suna kallonshi, dan ko kallonsu baiyiba balle yayi musu magana.Wayam ya samu bata nan, har toilet ya leqa nan ma shiru, hakan ya dad’a tayar mishi da hankali, ya fara tunanin dama can tana ce mishi dan shi da daddy kawai ta zauna a gidan sai kuma goggo Marka dake d’ebe mata kewa, badon su ba da tuni ta bar gidan.A ranshi ya ce, hakan yana nufin mummy da yaranta suna kuntata mata kenan.Wnn tabbas haka yake,dan yaga Alamu da dama saidai rashin tabbatarwa.Me kuma mummy take nufi da had’a shi aure da Miemie, tunda bai tab’a ce mata yana sonta ba, shi asali ma kallon yar uwa ta jini ya ke mata.Ko hakan yana da alaka da barin bintu gidanne, ta yiwu watakil an gaya mata.Ganin tunani bazai amfana mishi komai ba yasa shi fitowa daga dakin da hanzari yana kuma tunanin inda ya jefar da wayarshi,  dan tunda ya dawo bai bi takan wayar ba.D’akinshi ya koma, ya lalub’o wayar ya shiga dialing nambarta, amma ko sau d’aya bai shiga ba, dan switch off ake ta ce mishi.Iska mai zafi ya furzar kafin ya zauna ya dafe kanshi.”Allah yasa ba yusa ta tafi ba baiwar Allah.”Ya fad’a a bayyane, cikin nuna tausayawa.Can aunty Nafi ta fad’o mishi, duk duniya itace abokiyar shawarar shi, dan baya b’oye mata komai game dashi, kamar yadda itama yake abokin shawararta.Yasan zai samu mafita a gurinta.Da sauri ya mike ya koma part ďin mummy.Iman ya aika da taje wajen mummy ta karb’o mishi keyn mota.Tare suka fito da Iman, tana mika mishi keyn tana tambayarshi inda zaije.”Zan ďan fita ne.”Ya bata amsa.Har ya fara tafiya ya dawo da baya.”Mummy ina Islam, yauma ban ganta ba.”Tab’e baki tayi tace “Tana ďakinta, ďazu ta fito taci abinci ta koma.””Amma na duba ďakin ban ganta ba.”Ya sake tambaya yana kallonta.”Ta yiwu ta fita ne, kasan idan zata fita ba faďa min takeyi ba, saidai inga dawowarta.Shiru yayi yana mamaki al’amarin mummy, wato dai lallai lallai sai ta b’ata Islam a wajenshi takeso.So take taga sun samu sab’ani.Ko meye dalilin hakan?”Ya tambayi kanshi .D’ayar zuciyarshi ta bashi amsa da sonkai, dan tana son ka auri ‘yarta, shi yasa tun farko bata ďauki Islam da mihimmanci ba.”Da kyau.”Yace a fili, wanda a tunaninta ta daďa kufular dashi kan bintu ne, batasan da ita yake ba, yasa kai ya fita.Gidan aunty nafi ya nufa kai tsaye, yana mai fatar Allah yasa tana can.Fruits take wankewa cikin kitchen taji muryarshi suna gaisawa da aunty Nafi.Take taji wani irin fad’uwar gaba ya ziyarceta, ta tsame hanu daga wankin fruits ďin da takeyi taja kujera ta zauna ta zabga tagumi.Kiran da aunty nafi ta mata ne yasata fitowa a sanyaye.”Gani aunty.”Tace tana zama can  karshen kujerun falon.”Habib ne yake kiranki.”Ta faďa tana binta da kallon nazari.Kallo ďaya tai mishi ta ďauke kanta, tace “Sannu da zuwa.”Kasa kasa, kamar bata son faďa.Bata jira amsawarshi ta tashi taje ta kawo ruwa da kunun gyaďan da suka dama a flask, ta jera su da kananan cups a kan tray taje ta ajiye mishi ta juya tayi cikin ďakinta ta kwanta.Duk abinda takeyi da kallo yake binta, ya ma rasa ta ina zai fara, gashi kuma ya ga a bintunta take dan ko kallonshi bata sake yi ba.Saida yaga ta shiga ďakin harda rufo kofa ya sauke ajiyar zcy tare da cewa “Akwai matsala.”Aunty dake kallon sabon salo, a ranta tana cewa dama nasan da wata a qasa.”Me yake faruwa ne Habib, ban gane muku bafa.”Murya a sanyaye yace “Babu abinda tace miki akayi mata ne aunty?””Ni bata ce min an mata komai ba, saidai tazo min a halin rashin lafiya, snn akwai damuwa sosai tattare da ita, saidai taki faďa min komai.””Hmm, mummy ta bani mammaki aunty.”Nan ya kwashe duk yadda akayi ya sanar da ita harda maganar auren miemie da Daddy yayi mishi.Cikin mamaki da tausayawa Bintu aunty tace “Lallai ka haďu da kaidin mata habib, amma mummy ra ban mamaki , sonkai a fili? Ba banza ba Islam tafi son zaman nan gidan da can, ba mamaki bata jin daďin zaman gidanne.””Hakannema sister, dan tasha nuna min hakan nine dai ban maida hankali ba.””To yanzu ya zakayi da mgnr auren miemien kuma?”Saida ya ja tsaki, ya daďa ďaure fiska tamkar miemien tana kusa yace “Daddy ne ai, ba don shi ba ko sama da qasa zasu haďu banga abinda zai sa in amince ba, kuma kinga yanzu duk abinda zanyi zaiga kamar bijire mishi nakeson yi, dan lokacin da ya faďa na nuna mishi bana, so, sai yace wai ko dan albarkaci riko da kulawar  da mummy ta bamu bai kamata naki tayinta ba, tunda ma zumunci take so a qarfafa, ni yanxu damuwata islam ya zanyi?””Je ka sameta ku sasanta kanku amma kada kayi gigin sanar da ita maganar auren.”Kamar mai tsoron shiga haka ya tsaya a kofar ďakin.Ita dai aunty nafi tana kallonshi da tausayawa dan dukansu biyu tausayi suka bata, har ya shiga ciki.Jinginuwa yayi da jikin kofar yana kare mata kallo, ita kuwa daďa lafewa tayi kama tayi bacci.Jin kamar ana doso ta yasa ta ďaga hanunta tana cewa a hankali “Aunty ki koma nayi bacci kar ki tashe ni sai na tashi da kaina.”Ta maida hanunta ta sake lafewa tayi shiru.Kaďan ya hana dariya ta sub’uce mishi duk da yana cikin damuwa, wato dai har yau tana nan da halinta na yarinta, in baka ba ina mai bacci zai yi magana.A hankali ha haura kan gadon ya kwanta ya rungumota ta baya tare da sakin kwakkwarar ajiyar zuciya.Da saurinta tayi yunkurin tashi ya maida ta.A kunnenta ya raďa mata “Dama mai bacci yana magana?”Turo baki tayi kamar yana kallon fiskarta tace “Ina ruwanka dani.””Haba my Islam kiyi hakuri ki yafe nima na yafe.””Nidai ban yafe ba.”Ta faďa cikin shagwab’a.Narke murya yayi yace “Ba haka bafa nake miki, idan kince in yafe yafewa nakeyi ko kin manta?””Aini bana maka tsawa kuma bana saka kuka.”Sake narke murya yayi yace “Nima ai kuskure ne da rashin sani bazan sake ba, kinji?”Shiru tamishi, sbd haka cikin kasalalliyar murya yace “Kin yafe?”Maqe kafađarta tayi tace um um.”Kuka kike son in miki.””Nidai bance ba.” ta amsa da sauri.”To tsallen kwaďo.”Girgiza kai tayi alamar a’a.”To me kikeso?”Ya faďa yana daďa shigar da ita jikinshi.”Ka kyaleni kawai.””Bazai yiwu ba.Ya faďa yana juyo da ita suyi facing na juna.”Islam pls mana.”Ya faďa tamkar zaisa mata kuka.”Na yafe to.”Ta faďa tana b’oye fiskarta a jikinshi.”Thank u my Habibty.”Ya faďa tare da pecking kumatunta.Bata amsa ba sai ce mishi da tayi.”Ya Babana?””Yana can yana fushi dake.”Da sauri ta ďago kanta tace “Da gaske? Baka fađa mishi abinda kuka yi min bane.”Ta faďa idanunta Suna tara qwalla.Girgiza mata kai yayi yace.”Wasa fa nake miki.””Ni dai kam Allah ya isa tsakanina da Fa’izunnan.”Ya fahimci Hafiz take nufi sbd haka yace “Kada kiga laifinshi, shima baisan kina da aure ba, shi ne kuma ya warware min komai, so munyi laifi kuma mun roki gafara a yafe mana.”Shiru ya biyo baya na ďan lokaci kamar baza tayi magana ba, daga bisani sai tace.”Habibi, dan Allah mummy ce ta haife ka?.”Anxo wajen.yace a ranshi.Jin yayi shiru tace “Kayi hakuri idan tambayar ta b’ata maka rai.””Baki b’ata min rai, tunanin nake ko wani irin musgunawa take miki a bayan idonmu, Islam, mummy ba ita ta haifeni ba, mahaifiyata ta rasu tun ina ďan shekara bakwai, mummy dai ita  ta rike mu bayan rasuwar kakarmu mahaifiyar daddynmu dan ita tayi rikonmu bayan rasuwar mahaifiyar mu.”Allah yaji kansu.”Ta faďa a sanyaye.”Amin.”Shiru duka sukayi na ďan lokaci kafin daga baya yace su koma gida.Nan kuma tace fafur baza ta koma ba ita dai ya barta anan.Saida ya haďa da aunty Nafi, nanma saida ya mata alqawarin zasuje Yusa snn ta yarda ta bishi suka koma gida.Mamakin ganinsu tare su mummy sukayi har mummy ta gaza haqura ta tambayeshi ko sun haďu da Hafiz.”Bamu haďu ba.”Amsar da ya bata kenan.Harkokinta taci gaba dayi kamar da, bata shiga harkar su mummy sosai, su ďinma dama bata gabansu, burin mummy dai taga miemie sun daidaita kansu da Habib, wanda shi kuma ko da wasa bai nuna yasan da wata magana akan hakan ba.Wani lokaci idan mie mie ta je inda yake da gangan yake aikanta ta kira mishi Bintu, kuma tana ji tana gani yayi ta janta da wasannin da zasu sosawa miemie rai, a tunaninshi ko zata zuciya tace bata son auren.Wani lokacin har goyon Bintu yakeyi a gabanta, ko kuma yace Bintu ta kama shi ya tashi sai tasa hanu ta rike hanunshi da zummar mikar dashi sai ya jawota ta faďo kanshi yayi ta mata cakulkuli suna kyalkyata dariya.Hakan kuwa ba karamin konawa Miemie rai yakeyi ba, saidai mummy na daďa karfafar mata gwiwa da ta kwantar da hankalinta zai dawo gareta.A haka maganarshi da Miemie tayi qarfi, ba tare da sanin Bintu ba, saidai tana ganin tsana sosai daga garesu, ita yanzu duk wani halin da zasu nuna mata baya damunta tunda tasan mummy ba ita ta haifi Habibinta ba. gurin Daddy, Habibi, da Mmn larai take samu tayi walwala.Dagewa Mummy tayi lallai saidai a hada bukin da tariyar Bintu, duk da daddy baiso hakan ba, yafi so Bintun ta fara tarewa kafin ayi maganar biki, amma mummy ta kasa ta tsare, lallai yadda takeso hakan za’ayi.Aunty Nafi ce ta bada shawarar suje su sanar da innar Bintu maganar Miemie in yaso ita ta sanar da ita, dan shi Habib yace bazai iya faďa ba.Itama aunty Nafi tace ba za aji mutuwar sarki a bakinta ba, kuma basu so taji a wani waje ko daga bakin su mummy.Sbd haka Habib da aunty Nafi tafi suka tafi Yusa ba tare da sanin Bintu ba.Sosai Inna ta fahimcesu kuma ta nuna musu dama ta sani dan daddy yazo da kanshi ya sanar da ita.In dan Bintu ne kuma su kwantar da hankalinsu Habib ya kawo mata bintun zata yi mata bayani da kanta.Kwanansu biyu da dawowa ya sake ďaukar hanyar Yusa tare da Bintu, sai murna takeyi zata je taga Innarta da sauran ‘yan uwanta. Shi kam har cikin zuciyarshi tausayinta yakeji, dan shi yasan irin zafin da yaji a ranshi lokacin da ya ganta da Hafiz, a ranshi yake tunanin ko yaya zataji idan taji labarin wani auren za a mishi…*Hmm, ko yaya Bintu zatayi idan taji wannan labari🤔🤔*(13/05 22:48) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*110-115*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*S*un isa lafiya, Inna sai nan nan takeyi da su.Shi kuwa Habibullah  faďuwar gaba kawai ya isheshi, wani irin fargaba yakeji, duk a binda yakeyi yake kawai yakeyi.Bata wani zauna sosai, ba gidan kawayenta da sisters ďinta tayi ta zagayawa a ranar.Duk gidan da ta shiga sai sunyi mata tsiyar ta tsaya gayu har yanzu bata haihu ba, ta biyewa boko.Ita abinma dariya yake bata.Basu samu keb’ewa da inna ba sai dare lokacin da suka zo kwanciya.Tana kwance kan cinyar inna tana shafa mata kai suna hira kaďan kaďan.Can inna ta kira sunanta ina serious tune.Amsawa tayi tare dajin faďuwar gaban dabata san dalilinshiba.Cikin hikima da dabara  ta fara tunatar mata da irin hallacin daddy garesu tun kafin ma Baffa ya rasu da kuma bayan rasuwarshi.A haka har ta gangaro kan irin soyayya da kulawar da Habib ya bata tun tana ‘yar karamarta, tana cikin dattinta na yarinta, ko kirgen dangi bata fara ba, wanda hakan zai tabbatar da cewa soyayyace ta gaskiya tsakani da Allah, ya ke mata bawai dan wani abu nata ba.Ita dai shiru tayi ta bada hankalinta tana sauraren inna, dan yau har wasu abubuwan da bata sani ba takeji daga bakin inna.A hakan inna ta sanar da ita maganar auren da kuma yanda abun yake, dan bata boye mata ba ta sanar da ita mummy ce ta haďa kamar yanda su aunty da Habib suka sanar da ita ,kuma shi ďinma ba da son shi bane.Diff tayi ta ďauke wuta, tana jin kamar duk wani abu mai amfani a jikinta ya daina aiki, gaba ďaya jikin ta ya saki, itama inna saida taji alamar hakan.Kiranta ta shiga yi tare da girgiza ta.Har wajen sau uku kafin hankalinta ya dawo jikinta ta amsa.”Menene?”Inna ta tambayeta.”Ba komai.Ta faďa a sanyaye.Itama kanta innar tausayin ‘yar tata takeji, sai kuma taji shirunta ya dameta, taso tayi magana taji ta bakinta, amma ina Bintu kam tayi gum da bakinta, dan a ganinta yau taji abinda yafi qarfinta, dan taji abinda bata zata ba.Nasiha inna ta shiga yi mata tana haďawa da rarrashi  karshe ta umarce da ta je ta kwanta.A hankali ta tashi taje tayi alwala, ta dawo tayi adduoi, ta kwanta.Tana kwanciyar wayarta ta fara neman agaji.Ganin Habib ne ya ke kiranta yasa ta gagar ďaukar wayar dan ita kaďai tasan abunda yake damunta, shi kuwa rashin ďaga wayar ba karamin tayar masa da hankali yayi ba, gashi dare yayi, hakan ya daure ya mata gudnight mssg ya tura mata.Kwance take amma sam bacci ya qauracewa idanunta sai tunani tak, kan irin zaman da zasuyi da miemie amatsayin mata Habib.Sai yanzu ta gane dalilin halin ko in kula da mummy take mata tun farkon zuwanta gidan.Ranar dai a sace bacci ya saceta wanda ba na daďi bane dan sai shirmen mafarkai take tayi.Tun da tayi sallar asubah ta bingire akan sallayar sbd rashin  samun isasshen bacci, amma duk da haka ba wani baccin kirki  tayi ba, tana ji ya suka shigo tare da Ila suka gaisheda Inna har tana ce musu Bintu tana bacci.Juye juye tayi tayi qarshe ta gaji da kwanciyar ta fito tayi wanka, ta zauna zata karya inna tace mata ta ďauki abin kari ta kaiwa Habibu.Saida taji zcyrta ya tsinke.Gyalenta ta ďauka ta yafa ta ďauki abincin ta fita a sanyaye Inna tana binta da kallo, daga ganin yanayinta bata samu baccin kirki ba.Da sallama ta shiga ďakin, shiko dama zaman jiran shigowarta yakeyi.Da sauri ya tashi ya karb’eta yana mai kallon fiskarta.Kasa tayi da kanta tamkar kunyarshi takeji,duk yanda yaso su haďa ido taki har suka shiga ciki .”Ina kwana Islam.”Abinda ya fara ce mata kenan yan qare mata kallo.Bata amsa ba sai hawaye da suka zubo mata sharr, tunda taji wnn labari sai yanzu ta samu tayi kuka, dan zcyrta bushewa tayi tun jiyan.”subhanallah, Islam kuka?”Ya tambaya tare da dawowa kusa da ita.”Me aka miki?”Ya kuma tambayarta.Bata san sanda ta galla mishi harara ba, sai ta kuma kawar da kanta.”To fah.”Yace a ranshi, ko ba a faďa mishi ba yasan ta samu labari.A hankali ya karaso ya ya dafa kafaďarta, “Islam, nasan bazai wuci maganar Miemie kikewa kuka ba.Ki daure ki bani hankalinki dan ki fahimci abinda zan fađa miki.Wlh, kinji rantsuwar musulmi, ban tab’a yiwa miemie wani so ba bayan na musulunci da ‘yan uwantaka.Habibullah, Islam kaďai yakeso, kuma ita kaďai yake fatar ta zamo abokiyar rayuwarshi.Ni na tabbata mummy karambani tayi wajen son haďani aure da miemie dan itama kanta tasan bazan iya yin adalci tsakaninku ba, dan ban tab’ajin son ta a raina ba kuma bana tsammanin zanji ko nan gaba.Islam, ina sonki, so mai tsanani wanda bazan iya kwatanta irin son da nake miki ba.Ni nasani miemie wahala zata bawa zcyrta in har ta amince da zama damu.Abinda nakeso dake kawai shine ki kwantar da hankalin ki Habibullah na Islam ne, ki yi kokari ki nuna ma su mummy abun bai dameki ba, kada ki basu fiskar da zasu nemi ďura miki b’acin rai da bakin ciki, kada ki bawa miemie fiskar da zata raina miki wayo.”Zumb’uro bakinta tayi tace “Basai na koma ba ma.”Zaro idanunshi yayi “Kamar yaya basai kin koma ba.””Nidai anan zaka barni.””Haba My Islam kada muyi haka dake mana, ai zasu ce kinji tsoro.””Su faďa mana.”Ta faďa tana share hawayenta.”To me kike so in cewa daddy.”Ya faďa yana tayata share hawayen.Shiru tayi mishi tare da kawar da fiskarta.Juyo da fiskar yayi yana cewa “Saki fiskar man Habibty, wnn irin shan mur.”Kafaďa ta make kamar karamar yarinya tana kwab’a fiska.”Faďa min to, me kike so, me zan miki?””Rawa.”Ta bashi amsa a shagwab’e.”Rawa kawai abu mai sauki, yi min wakar sai in yi miki rawan, ko kuma ki yi min afuwa zuwa lokacin bikin mu sai inyi rawan dampe , ko kin manta zamuyi rawan dampe.””A ina?”Ta tambaya tana waro ido.”Anan mana ko kin manta nan zamuzo muyi bikin,.Nan ya fara tuno mata da abinda tace lokacin da ya faďa mata da aurenshi akanta, a lokacin kin yarda tayi saida ya kira mata innarta ta tambayeta, nanma da taji da gaskene tuburewa tayi ita bata yarda ba, wani irin aurene wnn, ba kawo goro ba kawo lefe, ba rufi, bata ga an ďaura aure ba, ba  piknil (Picnic), ba tiggiti, ba ďaukan amarya balle ayi mata wakar ta rabu da jeki maza kizo maza, da sauran wakokin dai tayi ta jero mishi, duk saida yayi ta tuna mata shirmen da tayi ta zuba mishi a  lokacin har ta saki fiskarta ta fara dariya kafin hankalinshi ya kwanta.Kwanansu biyu da dawowa aka sa rana, kayan lefe kuma komai iri ďaya daddy ya bayar aka yi musu ba banbanci.Daddy ne ya kira Bintu yana daďa  kwantar mata da hankali, nasiha sosai ya mata inda har  ya ja mata ayar nan ta Fankihu maa ďaaba lakum minal nisaa,i mathnaa wa thulaatha wa ruba’a, wa in khiftum an laa ta’adiluu fawahidatan, harda misalai kala kala yanda dai wa’azin nashi zai shigeta yanda ya dace.Bata wani nuna damuwarta ba, baranma da taga mummy ta shigo tayi musu zaune, sai ta shiga sunne kai tana murmushi, karshe ma bayan tayi wa daddy godiya har ce mishi tayi, Allah yasa itama babanta ya zamo cikin adilan maza masu auran mathanaa ko thulaatha ko ruba’a,.Amin, ya amsa mata yana dariya, dan ita har yanzu bata ďaukarshi a suruki, a matsayin uba take ďaukanshi.Sosai abun ya bawa mummy haushi da mamaki, dan rashin nuna damuwar da takeyi ba karamin kular da Mummy yakeyi ba.Ita kuwa Bintu maganar innarta take amfani dashi inda take ce mata kada ta kuskura taja da al’amarin ubangiji, dan ohdan Allah ya hukunta al’amarinshi babu wanda ya isa ya canza.Shiko Habib abin ba a cewa komai dan yanzu ko a gaban waye zai nuna cewa Bintu tashi ce, kuma dole ka fahimci itace kaďai a gabanshi.Hakan ke daďa kular da mummy har ta ci alwashin zasu gane kurensu dukansu biyu.Sosai mummy ke gyara ďiyarta, bintu ko kallo basu isheta ba, goggo markan ta ce abokiyar hirarta, kullum cikin bata shawarwari masu ma’ana take.Aunty Nafi ma ba,a barta a baya ba.Saida biki ya kusanto aunty Nafi tazo ta ďauki bintu inda ta cewa mummy zata rage mata ďaya kada đawainiya ya mata yawa.Duk abunda aka sawa rana cikin hukuncin ubangiji zaizo, yau gashi Bintu da miemie dukansu suna matsayin mallakin Habubullah.Nasiha daddy ya mishi mai shiga jiki da yaji tsoron Allah ya rike matanshi bisa gaskiya da amana, dukansu biyu marayu ne, basu da uba shine mazamin ubansu, yanzu kuma sun dawo karskashinsa, sbd haka yayi qoqarin kamanta adalci tsakaninsu.A ranar da aka kai amare gidansu dangin su Bintu suka koma, aunty aka bari tare dasu.Bayan sallar isha,i suka haďu tare suka ci abinci miemie ta tashi tabarsu a gurin, hakanyasa aunty ta tisa bintu a gaba taje tayi wanka, kafin ta fito ta fitar mata da kayan da zata saka.Tana zaune tana jiranta ta qare shirinta suna ta hira, ta fesheta da turaruka snn ta lullub’eta da gyalen da ya dace da kayan tare da jawoshi har ya rufe mata fiska..Maida gyalen baya bintu tayita ďago tana kallon auntyn, “Meye haka?”Auntyn tace tana mata hararar wasa.”Ki rufe fiskarki kada ya shigo ya sameki haka.””Kai aunty Habibi nefa, shi ďin zan rufewa fiska.”Ta faďa a shagwab’e.”Ok, Habibi ko? Zaki gane Habibin da da na yanzu ba ďaya bane. Kuma ki adana shagwab’arki zai kiki amfani nan ba daďewa ba.”Ta faďa tana ďaukar jakarta .”To aunty kuma tafiya zakiyi?””Me zan tsaya in miki ke da kike zumuďin ganin angonki.”Ta fada da sigar zolaya.”Kai aunty dan Allah.””Nidai kinga tafiyata Engineer na yana jirana.”Tana faďin haka ta fita daga ďakin.Zata shiga ďakin miemie Habib ya shigo.Zolayarshi ta shiga yi dan ta ganshi shi kaďai tana cewa tsabar zumuďi bazai jira abokanshi suyi mishi rakiya ba.Washe baki kawai yakeyi da ka ganshi kasan yana cikin farin ciki.Jan shi tayi suka nufi ďakin miemie tare tana cewa tasan idan yashiga can kuma sai gobe.Suna fitowa ya takata bakin kofa ya kulle kafin ya nufo ďakin Bintu.Sallamarshi kawai taji wani irin faďuwar gaba ta fara tare da wani tsoron da batayi tsammaniba ya fara shigarta.Take taji wani irin sanyi yana ratsa ta wanda ta kasa gabne abinda take ji.Dafe kirjinta tayi tana addua har ya karasa shigowa, ya ajiye ledar hanunshi tare da qarasowa ya durkusa a gabanta ya dafa gwiwowinta.Kiran sunanta yayi a tsanake wanda tya tilasa mata ďagowa ta kalleshi.Suna haďa ido taga idanunsa sun juye mata wani iri, saida taji zcyrta ya tsinke.Kafin tayi wani tunani sai taga fiskarshi ya fara juyawa hakan yasa ta fara jin kamar jiri takeji, cikn kankanin lokaci fiskarshi ta juye nata na wani irin bakin mummunan dabba da bata taba gani ko jin labarin irinshi ba.Da qarfi ta mike ta fara ja da baya tare da kwalla wata irin ihun da ya razana shi.Binta ya shiga yi yana kiranta hakan yasa ta rintse idanunta dan sam bata fatar ta sake ganin kamannin wnn dabba.Mannuwa taji tayi ta jikin gini hakan yasa ta kankame jikinta idanunta a rintse, banda karkarwa babu abinda kjikinta keyiCikin kullewar kai ya tallabota yana yacewa” Islam buďe idanunki ,nine, menene?”Kaďan ta buďe ido ta kalleshi, a tsorace, still wnn dabban ta kuma gani, take ta sulale ta zube sumammiya……*Kuyi haquri fans, naso na qare littafinnan kafin azumui, amma matsalolin are beyond my control, idan na samu dama zan qara ko da page ďaya ne, idan abun ya gagara kuma sai ayi haqri da wnn sai bayan sallah, I heart u all.*(15/05 22:13) ‪+234 816 159 4233‬: 🥀🥀🥀🥀🥀🥀*AL’AMARIN UBANGIJI*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*Fasaha Online Writers**F.O.W**Na Mmn Abduljalal*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*115-120*🥀🥀🥀🥀🥀🥀*C*ikin ruďewa da tashin hankali ya shiga jijjigata yana kiran sunanta.Karshe kwantar da ita yayi ya samu ruwan sanyi ya yayyafa mata.Shiru bata motsa ba hakan ya jawo mishi rikicewar da ya rasa abinda ya kamata yayi, sai kawai ya durkushe a gurin yana tattab’a, bugun heart da pulse na hanunta .Ji yayi tamkar babu alamun numfashi a tare da ita.Aunty ya fara kira cikin muryar kuka yake shaida mata abinda yake faruwa.Kuka sosai yakeyi yana maganganu “Islam, ki rufa min asiri kada k min haka, dan Allah kiyi hakuri ki tashi da dss.”Cikin wnn hali aunty ta shigo ta samesu dan ko gida basu isa ba, ya kirata suka juyo.Itama ganin halin da take ciki hankalinta ya tashi, ta rasa ma dame zata fara.Daddy ta kira ta sanar dashi lkacin suna tare da mummy.Ba tare da b’ata lokaci ba ya tashi ya kamo hanyar gidan.Cikin wnn yanayi ya taddasu, habib sai kuka yakeyi aunty tana tayashi.Asibiti yace su kaita, nan suka kwasheta suka kaita asibiti, shi kuma mijin aunty ya wuce gida sbd yara.An ďauki lokaci sosai kafin aka samu ta farfaďo, har rige rigen shiga sukeyi.Habib gaba jin jikinshi yakeyi kamar paper, ba karfi sam.Hakan yasa aunty ta rigashi shiga ciki, sji kuwa daddy saida ya riko Habib ganin halin da yake ciki.Kwance take hawaye na zuba ta gefen idanunta tana tunani da kuma mamakin abunda ta gani fikin ďakinta ďazu.To ina Habibin kuma? Tambayar da tayiwa kanta kenan.”sannu my sister, me kikeji yanzu?”Aunty ta faďa lokacin da ta riko hanunta.Share hawayen da suka gangaro mata tayi tace “Aunty ina Habibi?”Daidai shigowarsu su tare da daddy ,aunty tayi pointing mata shi, tana cewa “Gashi yana shigowa.”D’agowarnan da zatayi, sai kawai tayi saurin kankame aunty tana pointing ďinshi da yatsarta bakinta na karkarwa ta gagara magana.”Menene?”Aunty ta tambayeta hankali a tashe.Zaro idanunta tayi sosai kan shi kafin dakyar ta iya cewa “Baba…Bata qarasa ba ta zube a wajen ta sake suma.Inna lillahi.. Me zan gani haka Islam?”Cewar aunty.””Daddy ka gani ko?”Habib ya faďa yana kuka mai tsuma zcy.”Ba kuka zakayi ba Habibullah, addu’a zamuyi mata, zauna ina zuwa.”Daddy ya faďa yana zaunar dashi kan ďaya daga kujerun ďakin.Kiran doctor daddy yayi suka shiga duba ta.Ko da ta kuma farkawa bata sake buďe idanunta ba, sai cewa aunty takeyi tayi mata addua.Addua sukayi ta karanto mata suna tofa mata har bacci ya kwasheta.Daddy yana fita daga gidan bayan ya sanar da ita abinda yaji mummy ta tashi tana ta zagaye palourn.Can ta kuma kiranshi ya sanar da ita halin da ake ciki na sake sumar da tayi da kuma abunda takeyi.Adduar samun lafiya ta mata  ta tambayeshi Miemie, sai a snn ya tuno da Miemie yace ta tura a ďauko ta ta koma gida dan bai kamata a barta ita kaďai ba.Turawa tayi a ďauko tan kafin tayi dialing wata namba ta yi shiru na ďan lokaci.”Me kika sa akayiwa ‘yar mutane?”Abinda ta fara faďa kenan.Daga ďaya b’angaren aka ce mata “Me kuwa zan sa a yi mata bayan abinda ya dace da ita.””Gaskiya ni bance ki haukata musu ‘ya ba, nace ya manta da ita kawai ta fita ranshi, ya komawa Miemie kawai ko ba haka mukayi dake ba?””Share kawai, sun cancanci susha wahalan dukansu harda uban shi yasa na musu haka, kuma kada ki matsa dan babu abinda zai canza, a hakan ma zasu manta da juna ke dai zuba ido kisha kallo kawai.”Kashe wayar tayi ta zauna tana tunanin ,anya wnn aikin yayi kuwa, gaskiya ba haka taso ba.A haka suka kwana suna mata addua, Washegari da ta tashi kamar abun da sauqi, dan Habibullah daga window yake lekota dan yana tsoron ta sake ganinshi ta sume.Da kanta ta sake nemanshi, yana shigowa kuwa ta qwalla qara tare da zubewa.Ganin abun sosai ne yasa daddy ya sanar da Baffanta wan babanta, shi kuma yaje ya sanar da Inna.Tare suka zo da innar tata, suka tarar da mummy da miemie da Iman duk suna nan, aunty kuma taje gida, sai Habib dake rakub’e, yaki tafiya gida kuma tsoron shiga yakeyi.Sosai daddy yayi musu bayanin yanda abun yake hakan yasa wan babanta ya ce a nemi sallama, wnn cuta ba na asibiti bane.Hakan kuwa akayi, sai dai suna fitowa ta hango Habibullah ta fara neman hanyar guduwa.Da kyar suka rirriketa, a haka suka tafi gida gaba ďaya bata cikin hayyacinta.Alfarma baffanta ya nema da abar musu ita suje su nema mata magani.Firr mummy taki amincewa, ita lallai a bar mata bintu zatayi jinyarta ai itama uwace.Da mamaki Habibullah ya kalleta, snn ya cewa daddy, shi kam yanaga zaifi a barsu su tafi da itan su jarraba aga abinda Allah zaiyi.Daddy yayi na’am da tafiyar nasu wanda sam ba haka mummy taso.Daddy ne ya kaisu da kanshi, saidai habib baije dan gudun kada ta kuma ganinshi jikin ya tashi.Kafin su tafi saida suka fara biyawa ta wani shahararren islamic chemist, daddy yayi wa malamin bayanin matsalar Bintun.Magunguna ya haďa musu da adduoi, snn ya bada shawarar Habib ya nisance ta na wani lokaci har sai maganin ya qare.Bayan komawan daddy baffanta ya haďa duka sauran ‘yan uwanshi har da goggo rabi da goggo habi da basu cikin garin sunzo.Bayani ya musu kan abinda yake faruwa ya qare da cewa yana fata ba hanun goggo Rabi cikin wnn al’amari, dan yasan halinta na rashin yarda da kaddara.Wnn maganar ba qaramin qona mata zcy yayi ba, har ta gagara haqura ta fashe da kuka ta hau rantse rantse kan bata da masaniya kan abinda ya faru da Bintu.Tabbas ayau tayi nadamar abinda ta aikata, abu ya faru wajen shekaru shida amma har yanzu yana bibiyanta.A zcyrta taci alwashin muddin in har yi ma bintu  akayi itama bazata bari ba har sai asirin wanda ya aikata hakan ya tonu.Kulawa sosai take samu daga wajen innarta  da’yan uwanta, saidai wajen shan magani ne sai anyi daga da ita, sbd sam bata son maganin, sai inna tayi da gaske take yarda tasha.Tun da aka tafi da bintu mummy ta kudura cewa yanzu ya kamata ta shigar da miemie gun habibullah, sbd haka duk wani kulawar da ta dace a mishi take sanar da miemie yanda zatayi.Kullum kuma cikin kwalliya da kamshi take.Shi kam Habib mamaki ma take bashi dan shi sam bai tab’a mata kallo da wata manufa ba da ya wuci ta kanwarshi tamkar yadda take a da, snn bai nuna alamar yana da niyyar komawa gidanshi bama balle ace su koma da miemie. Shi a yanzu cutar Bintunshi yafi ďaga mishi hankali, tunda ta tafi yake ciwon zcy dana gangar jiki, ga kewarta duk ta dameshi kuma an hanashi  zuwa ya ganta, shima kuma in ba warkewa tayi ba bazai so yaje ta shiga halin da take shiga ba idan ta ganshi.Shima kuma daddy bai barshi haka ba dan maganin tsari yake nema mishi, ga addu’oi da yakeyi ba dare ba rana.Duk da bata ganin wnn halittar yanzu amma bata mance da halittar ba, duk lkacin da abin ya faďo mata takan tsinci kanta cikin matsanancin tsoro da faďuwar gaba.Hakan yasa duk tabi ta rame dan yawanci sai tazo bacci kamannin abin yake dawo mata, sai ta gagara yin baccin ,sai inna tayi ta tofeta da adduoi, haka kuma tayi wani irin sanyi tamkar ba bintu ba, yawacin lokuta zaka ganta zaune jigum har idan anyi mata magana takan zabura.Suma dangin maman habib ba a batsu a baya ba wajen kawo gudunmawar taimakonsu.Abinda yake bawa inna mamaki shine yanda kwata kwata bintu ta manta da wani Habib.Yawancin lokuta idan ana maganar Habib bata nuna ko alamun tasan da wanda akeyi.Haka kuma idan daddy yazo yace mata Habib yana gaisheta sai tayi shiru tana kallonshi kamar tana so ta tuno wanene Habib ďin.Aunty Nafi ma tana kokarin zuwa dubata, haka idan tazo bintu zata nuna farin cikin ganinta amma tana kawo mata maganar Habib zata shiririce wajen kokarin tuno mai wnn suna.Da wayarta dake snapping ďinta ta tura mishi, wanda sam baijin daďin ganin ramarta.Inna bata fasa kawo mata zancenshi ba haka kuma idan ya kira wayarta tana bata su gaisa, saidai duk lokacin da taji muryarshi takan tsinci kanta cikin faďuwar gaba, amma sam bata iya amsa shi, har ya karaci maganar da zaiyi bata tankawa duk a kokarinta nason gano ko shi ďin wanene.Bata kuma tab’a tambayarsu waye shi ba saidai idan anyi maganarshi tayi ta binsu da kallo.Cikin ikon Allah satinta uku ta fara samun sauqi, dan ta daina ganin wnn halittar dake bata tsoro, yanzu tana baccinta peacefully, tana sakewa suyi hira da mutane ta fara dawowa asalin bintunta.Ganin haka inna ta fara sata shiga gidansu Habib dake kusa dasu ta gyara duk a tunaninta hakan zaisa ta tuno da Habib, amma ko da wasa bata tab’a kawowa inna maganarshi ba.Cikin sati biyu da warkewarta ta maida kibarta tayi kyau tamkar bata taba rama ba.Shima kanshi yaji daďin ganin hotonta wnn karon da aunty tazo, zuwa wnn lokaci kuma mummy tayi maganar su koma gidansu ya kai sau uku, daddy ne dai bai bada karfi kan maganar ba dan baya so ya takurawa Habib.Goggo Rabi kuwa bayan addua da taimako da take nemawa Bintu harda kaikayi koma kan masheqiya ta dage take nema.Zaune take a harabar gidan ta kurawa kasa ido guri ďaya take kallo, ba komai a ranta sai son tuno wani abu da take ji cikin kwana biyunnan game da gidan da inna take yawan sata ta gyara.Tabbas akwai wani abu mai muhimmanci dake tattare da gidan, amma baza ta iya cewa menene shi ba.Da sallama ya turo kofar gidan  shigo yana mai cike dason ganin wanene a cikin gidan nasu tunda yasan daddy bai zo ba.Cakk ya tsaya yana kallonta zcyrshi na bugawa, wata zuciyar tana bashi shawarar ya isa gareta ďayar tana hanashi, tunda bayi da tabbas ďin samun lafiyarta, sbd yanzunma malamin dake musu jinyanne yace yazo a gani ko an dace.So yake yabar wajen tunkan ta ganshi, tunda yaga kamar tayi nisa cikin tunani da alama bata san da shigowarshi ba ma.Idon shi ya gagara janyewa daga kanta ,kafafuwanshi kuma sun gagara yin motsin kirki da zasu bashi damar barin waje, shi bai shiga ba kuma bai koma ba.A hankali ta ďago idanunta ta sauqesu kanshi, wanda hakan yayi sanadiyyar qara qarfin bugun zuciyarshi.Sun jima suna kallon juna kafin ta mike ta fara takowa zuwa inda yake, fiskarta na nuna alamun tsoro da mamaki…..*Alhamdulillah, ‘yan uwa anan zan dakata, in sha Allahu sai nan da bayan sallah idan Allah yasa muna cikin rayayyu.**Allah ya yanuna mana farkon wann wata mai alfarma lafiya da kuma qarshensa, Allah ya bamu ikon yin ibada cikin koshin lafiya da tsaftaťacciyar zuciya, Allah kuma ya karb’i ibadunmu, ya biya mana buqatun na alkhairi.**Yan uwa idan akwai wanda na taba batawa rai yayiwa Allah ya yafemin, nima na yafewa kowa, Allah ya sadamu da alkhairi**RAMADAN MUKARRAM.*Copied ByHAYATU BABA ZUBAIRU(YAYA HAYAT) (ADMIN OF ADMINS)        (admin    Hayat hausa novelsHausa novels and fashionCool novel, makeup and kitchen1⃣Download Al’almarin Ubangiji Littafi Na Ɗaya HausaNovel

Leave a Reply

Back to top button