Alaqaqai Littafi Na Ɗaya Complete Hausa Novel
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA NOVLS DOCUMNTSWASAPP080663 for more(20:26, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAƘAƘAI-01.(m) Nazir Adam Salih(c) Yarima Gangariya.DAYA 1Wata ranar lahadi aka tashi da gagarumin hadari wanda yakan firgita birrai. Kodayake a safiyar ranar ba’a tashi da alamun hadarin ba. Sararin samaniyar tarwai yake babu alamar gajimare ko kankani wannan shi ya baiwa rana lasisin ci gaba da dumama rufin gidaje da kayuwan bani adama tun daga karfe goma na safiyar har zuwa karfe daya na ranar. Abin bai zowa mutane a bazata ba musamman ma wadanda suka sha miya da yawa domin sun dade da yin amannar cewa duk sa’ar da zafi ya tsananta alokacin damuna to hadari ne ke son haduwa.Haka kuwa akayi babu zato ba tsammani sai hadarin ya fara haduwa sahu sahu sannu ahankali har ya dakushe hasken ranar ba’a dade ba sai iska gamida feshin tsattsafar ruwa nan da nan jama’a suka fara tserere akan tituna domin su sami gurin fakewa acikinsu harda Ni wanda rabona da ofishina tun karfe tara na safe da wani mutum yazo karbar bashinsa na gudu..Wannan bashine karo na farko ba dana fara tserewa masu bina bashi kusan watanni tara kenan da harkar fim ta juya min baya tun fitowar fim dina na DAREN MUTUWA shikenan sai mutane suka dau karan tsana suka dora min.Iskar hadarin ta fara tsananta dan haka sai nayi sallama da mai shagon dinkin da nake boye aciki tun safe nace dashi.ISYAKU zan koma ofishina. Isyaku tela ya dubeni cikin damuwa daman yasan irin matsanancin halin danake cikiGara ka tafi gida Hilal domin komawarka ofis ayanzu ganganci ne… Na dubeshi gamida murmushin yakekada ka damu isyaku leka waje ka gani hadari ne bakikirin ga iska.. Nasan dai mutum yanzu in ba maye bane dole ne ai yabar ofishin….. Kuma bugu da karawa ma dole ne na koma ofishin domin na sallami sakatariyata LAURIYYA dan nasan ko kudin mota bata dashi…… Abincin rana ma bansan yadda zatayi ba.. Isyaku ya dubeni cikin mamaki.Kana nufin haryanzu Lauriyya tana tare dakai? Na gyada masa kai kwarai kuwa ai tattaraba ce uwar alkawari ita kadai ta rage a yarana duk sun barni sai ita kadai… Isyaku ya dan yi murmushi yana dubana.Itama akwai dalili.. Na dube shi cikin mamakidalili… Kamar yaya ban fahimce ka ba isyaku yayi atishawa sannan yaceHaba Hilal har sau nawa kake so in maimaita ma cewa Lauriyya sonka take.Nayi saurin girgiza kaiA’a bari bari isyaku kada kayi min mummunan fahimta na yarda ni dan fim ne amma zakayi mamaki idan nace dakai tunda nake ban taba soyayya ba da wata yar fim..Kakkarfar iskar hadarin dake ta hankoron dauke rufin dakunan masu rangwamen gata ta bugo kofar shagon telan da karfin gaskeIsyaku yasa kafa ya tokareta.Baka fahimce ni ba Hilal ko kuma ince kasan gaskiya ka ke takewa ai ko makaho ya laluba yasan lauriyya tana mutuwar sonka..******* ********* ************.Lokacin dana baro shagon telolin saina tsallaka titi na nufi ofishina cikin sauri da kyar nake ganin gabana saboda kakkafar iskar ma’abociyar kara dake ta bulbule min idanu.Kura ta turnuke ko ina haka nan garin yayi jajur duhu ya lullube ko ina kai kace karfe shida da rabi na yamma tayi duk kuwa da cewa karfe daya ne na rana.Cikin sauri na nufi ofishin inata waige waige domin haryanzu jikina na bani cewa akwai sauran masu bina bashi cikin ofishin suna jirana.Tun kafin na karasa ofishin na fara hange hange da rabe rabe sannu ahankali har na isa kofar ofishin wacce ke rufe tana duban bakin titi.Nayi tsaye a kofar ofishin kusan minti guda nayi kasake kamar barawo ina saurare ko zan ji surutai ko hayaniya shiru banji komai ba na dan dada matsawa kadan na kara kunnuwana ajikin katuwar kofar nayi ajiyar zuciya sannan sainayi shahada na daga hannuna zan tura kofar kenan sai kawai naga an bude daga ciki.Sannu da zuwa hilal yi maka ka shigo daga ciki yanzu yanzun nan EMEKA yatafi tun sha daya yaketa jiranka nace dashi katafi kaduna… Amma yaki yaddaKirjina na dakan uku uku cikin sauri na shige ofishin.Lauriyya ta mayar da kofar ofishin cikin gaggawa ta rufe sannan saita jingina bayanta ajikin kofar ta kura min idanu bata ko kiftawa.Na nufi cikin ofishin ahankali hannayena cikin aljihunan wandona zuciyata na kuna nayi kokarin nazarin ofishin amma saboda duhun hadarin bana iya ganin komai cikin ofishin.Lauriyya ta fahimci haka cikin sauri ta nufi makunnar lantarki ta kunna nan da nan dakin ya gauraye da haske.Lauriyya tayi tsaye jikin makunnar lantarkin tana kallona ina kallonta.Akwai alamar tausayi karara a fuskarta banda wannan kuma naso na hangi kwalla acikin kwayar idanunta. Cikin sauri na dauke kaina gefe guda sannan nafara nazarin ofishin….. Da a da dan wani lokaci can daya shude babu wani ofishin darakta na fim daya kai koda rabinsa a tsaruwa amma koda na tsaya ayanzu ina nazarin ofishin sainaji kamar na fashe masa da kuka lallai ruwa ya daki babban zakara.Saidai hakuri Hilal haka duniya take rawar yan mata lauriyya ce ke magana abayana cikin wata rarraunar murya. Naji abinda ta fada to saidai kuma ban iya juyowa na kalleta ba ballantana ma na tanka mata.. Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan shudadden zamani sa’ar da…………(20:26, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAƘAƘAI-02.(m) Nazir Adam Salih.Zuciyata da tunanina suka koma baya kadan wani dan shudaddan zamani…. Sa’ar danake tauraron jarumai na wasan fina finan hausa.Na rufe fuskata da tafukan hannuna sannan nafara tunanin sa’ar dana shigo harkar fim da kafar dama cikin watanni ukun farko da shigata harkar na fito cikin fina finai sama da shirin wadanda duk nine jarumi acikinsu sannu ahankali sai sunana yayi tambari duk inda ka zagaya babu sunan wanda ake fade sai HILAL.Duk inda na zagaya yara da manya basa barina na huta sun yita bina kenan abaya kungiya-kungiya kamar uban garke idan naje sayayya kasuwa ba’a karbar kudina haka nan da zarar an kyalla ido na ganni saikaga anata rububin ganina kowa na gayyata dana zo nayi siyayya ta a rumfarsa duk kuwa da cewa ba kudina zasu karba ba.Na mallaki abubuwa da dama a shekarata ta farko da shiga harkar fim wanda adacan wani lokaci ban taba mafarkin mallakarsa ba akwana kusa motoci uku na hawa kayan sawa na kwalisa sama da kala dari uku da goma sha takwas agogunan sarka ashirin na fata goma takalma sittin safa kuwa da singileti duk wacce nasa sau uku bana kara amfani da ita sai wata sabuwar.Sannu ahankali samari suka fara kwaikwayon yadda nake direshin duk abinda nayi koda sakarci ne sai ya burgesu saikaga sun zamo masu kwaikwayona..Ashekarar ne na bude katon ofishina wanda aka kawata shi da kyale kyale gami da manya manyan kujeru masu numfashi da taushi kamar ada da sau da yawa idan muka sauki baki indai har zasu shafe mintuna goma suna zaune sai an sami wanda ya bingire da barci saboda dadi.Duniya ta dawo min sabuwa ina da yara dake aiki akarkashina sama da mutum ashirin suna kuma jin maganata fiye data iyayen da suka haifesu wasu suna bina sau da kafa ne wai don kawai suna so na sa su kokuma nayi musu hanya su shiga shirin fim yayinda wasu kuma suke yi min biyayya don kawai kaunata da sukeyi. Nazama kamar sarki acikin fadawa duk abinda nake so shi za’ayi batareda bata lokaci ba. Da ace yarana awannan lokacin suna da iko da fitsari da numfashi ma su zasuyi min.Muna nan ahaka har shekaru biyu suka shudeKwatsam ran nan sai duniyar data dagani sama ina shanawa tafara yin kasa kasa dani sannu ahankali ta damfara ni da kasa.Abin yafara ne a yammacin wata ranar lahadi sa’ar danake karbar kudaden sabon fim dina RAGAS daya fito.Shagon farko danaje sai akace dani wai fim din baya tafiya nayi mamaki domin tunda kamfanina yake fim ba’a taba samun wanda bai shiga ba.Me ya faru da fim din? Na tambayai wani dillalin kasa kasan fim din.Eh to kasan dai mutane yadda suke ba’a iya musu inajin dai gajiya sukayi dakai…. Kuma sunata korafi akan cewa wa fina finanka na kwanan babu labari mai kyau.Tun daga ranar ne al’amura suka dagule min abin kamar sa hannu komai na taba sai ya lalace gashi dai nagama kashewa fim din Ragas kudi… Na ranto kudin jama’a duk na lafta saboda a tunanina zaiyi bala’in karbuwa saigashi cikin ikon Ubangiji saidata kawo ko kashi daya bisa goma na kudin fim din basu komo ba.Rayuwata tsananta kaina ya dauki zafi rikici goma da ashirin ga tarin bashi fal akaina gashi kuma ya furodusoshin ma da suke daukana na fito musu a matsayin jarumi duk sun gujeni ba’a dade ba duk yarana suka watse suka barni daga ni sai yar amana LAURIYYA..Koda na daga fuskata sa’ar danake tunanin na dubeta saina tuno da kalamanta saa’ar da gari yayi mana zafi bazan taba mantawa da ranar ba. Ranar wata laraba da yamma bayan sama da mutane goma sun zo tambayata bashin su.Hilal.. Ina da shawara in zaka yarda. Lauriyya tace dani na dago kai na dubeta.Fadi shawararki lauriyya…indai mai amsuwace ai na dauka.. Tunda dai ko banza dai ke kadai kika rafe atare dani.. Wallahi lauriyya ayanzu kin wuce sakatariya agurina saidai ko in Yar Uwa.Lauriyya ta dan matso daf dani duk da yake duk ranmu abace yake to amma na lura da alamun jin dadin abinda nace karara a fuskarta na sani ba tun lokacin ba har zuwa yanzu Lauriyya sona takeyi to amma ta rasa yadda zata fito ta fada min.Hilal… Ni ina ganin a shawara da ace kullum mutane suyita binka suna tambayarka bashi… Suna muzanta ka kamar barawo gara in kana ganin babu damuwa ka daga dan kadarorin daka mallaka kasa su akasuwa in yaso saika biya mutane bashin su… Ko banza dai ina ganin ai tsira da mutunci yafi tsira da kudi. Hakan data fada saina fahimci tabbas ta fadi gaskiya ba’afi sati daya da bada shawarar ba na sayar da motocina guda uku gidana kai da duk wani abu danake ganin zai iya kawo min wasu dunkulallun kudi saida na sayar dasu.Acikin makonne na biya jama’a da dama basussukansu ni kuma nakoma gidan yayana inda daman tun farko acan nake kafin na samu abin duniyaUNGULU TA KOMA GIDANTA NA TSAMIYA.To saidai kuma abin bakin ciki duk da kadarorina dana sayar basu isa biyan bashin da ake bina ba.Gashi kuma haryanzu babu wani labari daga gurin masu shirya fina finai wadanda ada suke ta bina agindi agindi suna rokona danazo na fito musu a fim yanzu da sun hangoni sai su fara buya domin duk labari ya ishesu acikin kankanin lokaci kamar wutar daji cewa wai kasuwar fim ta daina yi dani……… Wannan duk wani Abune daya shude Abaya..LABARIN AKWAI DAMBARWA KU DAI KASANCE DANI(20:27, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI 03.(m) Nazir Adam Salih.Wannan duk wani abune daya shude abaya.Hilal aka kira sunana abaya na juya firgigit Lauriyya ce har yanzu tsaye ajikin makunnar lantarkin tana kallona idanunta sunyi rau-rau kamar zata fashe da kuka.Tunanin me kakeyi Hilal? Ta tambayeni bakinta na rawa na juyo ahankali hannayenta harde da juna makale abayanta.Kikace Emaka yazo nemana? Lauriyya ta gyada min kai bata yadda ta bude bakinta ba ina tsammanin da tayi magana alokacin fashewa zatayi da kuka.Sauran cikon kudin kwalin kaset din daya buga mana yazo karba nace da ita batareda na iya hada ido da ita ba.Ban da shima su shafi’i sunzo wai karbar kudin kayan kwastum… Haladu da sabo da ma duk sunzo maganar cikon kudinsu…Tsahon lokaci babu wanda ya sake cewa kala nida ita can bayan wasu yan dakiku sai lauriyya ta matso daf da inda nake tsaye inata faman karatun wasikar jakita dafa kafadata tace dani.Juyo ka dubeni hilal… Ina da shawarar da nake tsammanin me yiwuwa ta zama mafita agareka. Adaidai lokacin aka saki wata katuwar aradu data girgiza ofishin sannan wata walkiya mai tsananin haske ta harko cikin ofishin duk kuwa da kwan lantar dake ci..***** ******* ****** ****** ***.Na zurawa lauriyya idanu ina kallonta sannan kamar wani sahorami domin bansan me zance da ita ba ganin bance da ita komai ba sai ta dafa kafada na sannan ta sunkuyo da kanta tace dani.Ka gafarce ni hilal ba wani abu ne yasa nake tare dakai ba haryanzu sai don…… Ta kasa karasawa tausayinta yakamani haryanzu iska ake ta ketawa awaje saikuma sautin yan kananan kwayoyin ruwan da iska ke ta alakoro dasu akan rufin gidaje kafin isashshen ruwan ya karaso.Cigaba lauriyya…. Ke nake sauraro nace da ita a sanyaye lauriyya tayi dan jim na yan dakiku kana saitace cikin karyayyyiyar murya.Kau…..narka ce ta rike ni har zuwa wannan lokaci ina tare dakai…. Duk abinda ya same ka kamar ni ya shafa ne domin lokacin danazo garin nan kai ka karbeni ka mutuntani ka maida ni mutum.Banida cewa akan abinda tace dan haka sai nayi shiru ina sauraron abinda zataci gaba da cewa.Hilal…..abinda nake kokarin baka shawara akai shine me zai hana muje kamfanin fina finan su ALHAJIJI me yiwuwa…… Bata karasa ba sakamakon sauyin yanayin data gani karara a fuskarta.Haba lauriyya wace irin magana kikeyi ina ni ina wani Alhajiji kuma? Lauriyya ta dada matsowa gareni kamar zata kankameni.Hilal ka saurari abinda nake son fada ma dan Allah nsan dole bazakaji dadi ba domin zan saka yin abinda baka so ba. Ta dan saurara.Duk acikin yan shirin fim shi kadai ne nasan baya bakin ciki dakai…. Shiyasa tun jiya nake tunanin me zai hana muje mu gani ko zai samo ma wani fim din ajefaka aciki koda a mataimakin jarumi ne saikaga kadan samu wani abu ka rage bashin dake kanka. Tayi shiru tana dubana. Nayi dim na yan dakiku ina jujjuya kalamanta acikin zuciyata.Lauriyya abinda nake so ki lura dashi shine mutumin nan fa babu irin nacin da baiyi min ba sa’ar da nake kan ganiyar tashe na akan nazo nayi masa jarumi a finafinansa amma naki… Ke din nan da kanki sau nawa yana bugo waya ina cewa kice dashi bana nan….?Duk da haka dai hilal….. Haka nan zaka daure muje ai durkusawa wada ba gajiyawa bane ni nasan ba zai wulakanta ka ba tunda dai koda ada din ma ai ba fitowa kayi kiri kiri kace dashi bazakayi masa fim din ba. Na girgiza kai sa’ar danaji tayi shiru.Lauriyya ban ki shawarar ki ba amma abinda kamar wuya wai gurguwa da auren nesa ina ta faman nuna miki Annabi kina runtse idanu abinda nake so ki gane shine tuni labari ya watsu aduk fadin duniyar fina finan hausa cewa kamfaninmu ya fadi bama wani tasiri akasuwar fim shiyasa kikaga fa kowa ya gujeni an daina rububin sa ni a fim domin ana ganin nazama asara.To in dai kuwa hakane wacce irin hauka ce ta hau kan alhajiji da kike tsammanin zai sani cikin fim dinsa in janyo masa asara sa’ar danayi shiru saina lura tuni hawaye ya fara sartu akan kumatun lauriyya..Daina cewa zaka janyo masa asara Hilal….abin da nake so ka gane shine ba kaine ka daina tashe ba kamfaninmu ne ya karye ya daina tashe amma ni nasan ita duk duniyar nan basu yarda ba ni nayi imani da cewa kana nan akan HILAL dinka jarumin jarumai.Kukanta yafara bayyana a fili.Nayi sauri na rike hannayenta nace da ita a sanyaye.Daina kuka lauriyya shikenan na yarda zamuje to amma kuma wani hanzari ba gudu ba.Lauriyya ta dago kai tana share hawaye cikin rashin fahimta.Yanzu idan mukaje bamu dace ba kinsan fa labari zai watsu aduniyar fina finan hausa cewa tsohon jarumin jarumai yafara tallan kansa….. Wacce illa kike tsammanin hakan zata janyowa durkusashshen kamfaninmu? Lauriyya ta bata fuska tace.Hilal so dai kakeyi saika bata min rai ko? Da dai bana son na fada amma yanzu ka takura ni saina fada? Na dubeta cikin mamaki me zaki fada? Lauriyya ta harareni gamida murmushin yake tace.Alhajiji yana mutuwar kaunata nice dai ban bashi hadin kai ba. Ni nasan ko yana so ko baya so dolene idan nayi masa magana yasaka acikin sabon fim din zaiyi. Tana gama fadin haka ta kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro………..SOYAYYAR GASKIYA AKWAI DADI BA IRIN SOYAYYAR SU O’O BA(20:27, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-04.(m) Nazir Adam Salih.Tana gama fadin hakan saita kama hannuna ta fara jana kamar wani karamin yaro..Zo mu tafi dan Allah kada afara ruwa. Nabita abaya sumi sumi kamar tunkiya muka shiga cikin iskar damina.Jarumin jarumai Na kira kaina da kaina sannan sai na saki daddadan murmushi. Lauriyya ta luraMurmushin me kake? Na girgiza kaina nace babu komai…. Kece kawai kika burgeni,.****** ********* *************.Sa’ar da muka isa kamfanin fina finai na alhajiji sainaga toge abaya abjikin wani kantin kayan karau nace da lauriyyaJeki kuyi magana dashi ni bazan karasa ba… Lauriyya ta dubeni zatace wani abu saikuma ta fasa me yiwuwa itama ta lura da taron yan alabaku mu samun fim dake tare birjik akofar kamfanin duk kuwa da uwar iskar da ake ketawa. Lauriyya ta rike hannuna tace.Toh shikenan hilal jirani anan naje na dawo ta lura da fuskata haryanzu a murtuke take cikin damuwa.Kada ka damu hilal komai zai zama daidai in Allah ya yarda.Kaidai ka jirani. Tana gama fadin hakan saita matsa hannuna sannan ta jefeni da wani boyayyen murmushi mai kunshe da dubban manufofi ta juya tana rausaya ta nufi cikin kamfanin..Na duba agogona bayana na jingine da itacen wayar lantarki dake daf da kantin na cika da mamaki sa’ar danaga tuni har mintuna goma sha uku sun shude da shigar lauriyya cikin kamfanin. Adaidai lokacin da damuwata ta fara tsananta saina hangi lauriyya ta fito alhajiji kuma yana biye da ita cikin fara’a akwai alamun farin ciki karara a fuskarsa me ywuwa na murnar zanyiwa kamfaninsa fim ne. Sa’ar da kuma na tuna da cewa nifa ayanzu ta kare min sai nafara tunanin to me yiwuwa ganin lauriyya ta nemi alfarma agurinsa ne yasashi murna.Ina nan tsaye har suka iso gareni.Yallabai! Yallabai!! Alhajiji yace dani cikin wata murya mai sautin amon alburushi sannan ya cafki hannuna kamar zai tsaga minsu saboda riko. Alhajiji kato ne baki mai katon ciki da dogon gemu babu gashin baki fuskarsa cikakkiya ce a mulmule kamar kwallon kafa duk sa’ar da yayi dariya saikaga ya zama tamkar mutum mutumi wannan ce tasa dayawa daga cikin shakiyan jaruman fina finan hausa suke so suga yayi dariya dan kawai su sha dariya. Wata shekara an taba fitowa dashi cikin wani shirin fim na abin dariya amatsayin dan daudu..Saika rabe kuma daga nan Hilal aiSINAD PRODUCTION kamar gidan kace. Ya dubi lauriyya cikin murmushi itama kuma ta dubeni da murmushin yaudara ta kifta min idanu.Mu shiga daga ciki Hilal…. Wallahi nayi farin ciki da ganinka domin kaya ya tsinke agindin kaba daman yanzun nan nake kokarin buga ma waya saiga Lauriyya domin akwai wani babban fim dinmu na shekara da za’a fita gobe kai nake so ka fito a jarumi sunansa.MUTUWA DA FARINTA TAKE TAKE!Sa’ar da na dubeshi na dubi Lauriyya sainaji kamar na fashe da dariya domin ko shakka banayi nasan karya yakeyi dayace wai ni yayi niyyar sawa amatsayin jarumin tun farko kamata yayi a sanar dani tun satin daya gaba tabbas Lauriyya ce ta yaudaro shi..Loading………. KASHI NA BIYU 2(20:27, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI 05.(m) Nazir Adam Salih.BIYU. Daga inda nake zaune ina iya jiyo sautin zubar ruwan saman akan kwanukan gidajen jama’a.. Na muskuta ahankali sannan na mike tsaye na nufi tagar dakin na dan janye gilashin tagar feshin ruwan saman gami da sansanyar iskar ruwan suka bugi fuskata. Nayi sauri na rufe tagar sannan nakoma na zauna akan kujerar ina nazarin dakin. shin wai yaushe za’a dauke ruwan nan ne. iskar dake cikin dakin ta fara karanci, hakan shiyasa fankar dake juyawa ta kasa yin maganin zafin dake addabata, gashi kuma idan nabude tagar dakin ruwa yajikani.Nasake mikewa tsaye naci gaba da safa da marwa hakika indai har ba dauke ruwan nan akayiba to da kyar zan iya barci. Gashi kuma tuni karfe dayan dare ta gota. Dakin danake ciki matsakaicine kamar dai sauran gidajen gwamnatin dake gurin. kujeru ukune kacal adakin kamar aya gami da tsohon gadon katakon dake dakon katuwar sabuwar katifar dana saya kwanaki biyu da suka wuce. daga bangaren arewa na dakin akwaitalabijin mai kala da bidiyo asamanta. sannan kuma asaman bidiyon fulawace ta roba acikin kofin tangaran Amatsayina naTAURARON JARUMAN WASANNIN FINA-FINAN HAUSAdole ne naga nayi kokarin kawata dakin danake kwana koh don taren bakin dake tafaman sintirinkawomin ziyarce-ziyarce dare da rana. Yawan bakin da suke kawomin ziyara ne yasa kawuna ya waremin bangare guda agidan ya sanyakatanga tsakanina dashi domin nasamu damar ganawa da bakina, tunda dai haryanzu banyi aure ba.MAFARIN RIKICIN KENAN WANNAN RUWAN SAMAN.(20:28, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAƘAƘAI-06.(m) Nazir Adam Salih. Na koma bakin gadon na zauna sannan na cire rigata na kwanta, inajin zazzafar iskar da fankar dakin ke busawa akan fuskata sannan kuma lokaci guda ina mai adu’ar Allah yasa a dauke ruwan saman koh na bude kofar dakin nasha iska. Na rufe idanuna amma barci ya kasa daukata gashi kuma gobe tashin asuba zanyi domin awashegarin ne zamu fara sabon fim din kamfaninSINAD PRODUCTIONmai suna MUTUWA DA MAFARINTA TAKE TAFE, amatsayina najarumin fim din dole ne nasamu isashen bacci domin na sami nutsuwar yin abin da daraktana yace nayi, toh sai gashi kuma zafi na neman hanani barci. toh ashe abun daban saniba shine bayan zafin dake addabata akwai wani al’amari daban dazasu kawo wa shirin fim din nawa matsala.. Ban san sa’ar da barci ya daukeniba acikin barcin ne nayi mafarki wai ana ta bubbuga kofar dakin danake ciki nayi firgigit na farka ina mutsutstsuka idanuna sannan ne to naji ana buga kofar dakin danake kwance nayi shiru cikin mamaki ganin mafarkin nawa ya zama gaskiya sannan kuma nayi mamakin shin wanene ke buga min kofata cikin wannan talatainin dare.Nadubi agogon dake makale ajikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da muka shirya wasan fim dinDAREN MUTUWA dasu karfe biyu da rabi na dare Tsoro ya kamani domin kuwa banga wanda zai bugamin daki ba cikin wannan daren sai koh BARAWOAka sake bubbuga kofar dakin Das Das kamar ana bugun kwarya da sillan kara Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin kowane ne ke buga kofar dakin hakika yana tausayamata aka sake bugawa raf raf raf har sau uku. Gumi yafara kwararowa kan fuskatahakika acikin mafiya yawan finafinan danake fitowa ni jarumine mai zafi marar tsoro to amma fa azahiri tsoro ne dani kamar farar kura dan karamin yaro ma yana iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona..ABUN TSORO SAI MA GABA JARUMI HILAL(20:28, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-07.TA’AZIYYA GA IYALAN DAN UWA ABOKIN CHART WANDA DUK POSTING DINA SAI YA KARANTA YAKUMA YI COMMENTIBRAHIM ABUBAKAR.ALLAH KAYIWA IBRAHIM ABUBAKAR KADUNA GAFARA KASA ALJANNAH CE MAKOMARSA DAMU GABAKI DAYANMU AMIN .(m) Nazir Adam Salih. Me yuwuwa kawuna ne nace da kaina to amma kuma ban yadda da kalaman da zuciyata keyiba domin nasan tun da kawuna ya ware min bangarena daban bai taba koda lekowa ba idan kuwa shine to nasan tabbas ba lafiya ba toamma kuma idan shine ai kiran sunana zaiyi gami da kwankwasa dakin, jikina ya sake daukar bari na juya a hankali na dubi ‘yan kayan dake dakin indai dan wannan ne sai nabasu su tafi.Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na daddakesu wasu kuma kamasu nake in daure to amma wannan daban wasane, yanzu kuma shine zahiri tunda gasu akofar dakina, Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi abude,ko da yake daman kuma kullum ahaka take kwana saboda maziyarta da abokan arziki dasuke yawan zuwa gurina da daddare to amma ba karfe biyu da rabin dareirin wannan ba………..Raf Raf Raf aka ci gaba da kwankwasa kofar Na yunkura hantar cikina narawa na nufi kofar dakin, ina ta salati da salalallami.Wai…..wai wane ne? Nace muryata ashake ban iya shaida muryar amatsayin tawa ba. Maimakon abani amsar sai naji an sake kwankwasawa,Wa……Nene? Na sake kuma tambayar shiru ba abani amsa ba haushi ya kamani sannan sai na tuno da fim din DAREN MUTUWA Muntaba wani sin mai kamar wannan inda barayi suka zo suna kokarin balla kofata nikuma na bari sai da suka gama jingina ajikin kofar sannan na bude sukazubo cikin dakin kamar an hankadosu nikuma nabisu na daddakesu. To yau ma zan kwatanta.Nace cikin zuciyata Saidai kuma wannan karon inhar Allah yabani sa’a suka zubo cikin dakin to tsallakewa zanyi na gudu.. Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi. jin haka shiyasani tunanin komai bugun kofar kafadarsa ya jingina ajikin kofar yake kokarin balle kofar dakin. Nan da nan nayi wuf na zare sakatar dakin na janyo kofar da karfi.Sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abin da yabiyo baya.. Ashe dai ko agaske jarumi ne wata zazzakar murya tace dani Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki daya sani wangame baki fayau ina dubantaAtsaye abakin kofar sanye da bakar riga doguwa da jan lullubi jikinta na digar ruwan saman daya doke ta, wata mace ce ajin farko a jerin kyawawa.Shin ko na iya shigowa, sanyi nakeji gaskiya, gashi kuma duk kayana sun jikeNa sake kallon katuwar akwatin mai taya dake hannunta na dama NaceMalama Lafiya? Daga ina kike Meya kawo ki gidana cikin wannan daren?Ta dubeni sannan ta jefeni da wani lallausan murmushin Allahkashemu dan dadi, tace Lafiya kalau HILAL ,daga wata nisan duniya natawo domin kawai na ganka, na dade ina ganin finafinanka ina kaunarka raina na Begen ganinka. Shine naga bazan iya jurewa ba sai nazo naganka tun daga maiduguri Nake motar mu ce ta lalace ahanya shine mukayi dare yanzun ma direban motar ne yaga nayi dareshine na roke shi yakawoni nan , Tayi shiru tana dubana.Jarumi Hilal, Ina fatan yanzu dai ka gamsu Shin na iya shigowa, sanyi nakeji wallahi Hilal. Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane ta ajje akwatin atsakardakin sannan tajuyo ta dubeni.In bazaka damu ba dan Allah nunamin inda bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf. To ke kuma ki zauna dame Ina dubanta baki bude Tayi murmushi Sai na zauna aciki idan sunsha iska saina mai dasu jikina nafito, Sannan fa takura min idanu tana dubana ko kiftawa batayiOh Hilal yau dai Allah ya nunamin kai wallahi kada kaga irin son danake ma duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nacema acan maiduguriakwai kawayena da suke kirana da suna HILAL tayi shiru tana dubana me yuyuwa koh dan ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata ba Hilal yaya kake yimin irin wannan kallo ne, koh haryanzu baka amince dani ba? Bahaka bane malama amma abin dake bani mamaki shine zuwanki cikin wannan tala-tainin daren kuma…… Ta katseni.Nace dakai motar muce ta lalace, Haba Hilal nifa bakuwar kace. To naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana. Haba hilal Mutane nawane suke ziyartarka arana daga jihohi daban daban kawayena nawa ne suka zo gurinka ai kwatancen gidanku ba wuya tunda agidajen gwamnati kake ga kuma lamba daman kuma ance kai kadaine abangarenka daban amma kada ka zargeni agurin maziyartanka naji.Mukayi shuru muna duban juna sannan sai tasake cewaNunamin bandakin Hilal kada mura ta kamani da wannan jikakken kayan jikin nawa. zo muje nace da ita na shiga gaba tana bina abaya Bandakin gidan acan baya babban falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin tacikinfalon akwai kofar dazata kaika cikiGa kofar nan Nace da ita ina duban yala-yalan gashin kanta Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi tashige bandakin ta rufo kofar gararamm a daidai lokacin ne toh aka saki wata aradu Rugugugu……….INA MAI AMFANI DA WANNAN DAMAR A YAU GURIN MIKA TA’AZIYA TA GA MEMBERS DIN SOYAYYA RAYUWA GROUP FACEBOOK & WHATSAPP DAKUMA IYALAN IBRAHIM ABUBAKAR KD BISA RASUWAR SAINA ROKON ALLAH YA GAFARTA MASA YASA ALJANNAH CE MAKOMARSA YA BAIWA YAN UWA DA IYAYEN SA DA MATAR SA HAKURIN JURE WANNAN GAGARUMIN RASHI DA SUKA YI ALLAH YA YI RIKO DA TAIMAKON YARAN DAYA BARITABBAS IBRAHIM BAZAMU TABA MANCEWA DA KAI BA ADUK LOKACIN DA MUKA TASHI YIWA KAWUNAN MU ADDU’A.Hadiza SirajoINA TAYAKI ALHININ RASHIN ABOKI NAGARI(20:28, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-08.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.MASU KARATU KUYI HAKURI DA WASU YAN KURA KURAI DA ZAKU CI KARO DASU TUN DAGA NA DAYA ZUWA NA 10 TAYANDA WASU SHAFUKAN ZAKU GA NA MAIMAITA SU KUMA HAKAN YAFARU NE SABODA WASU DALILAI NA KUSKUREN RUBUTU DANAYI TUN A FARKON LABARIN KUMA ZAIYI WAHALAR WARWAREWA SAI AKASHI NA 10 ZAREN LABARIN ZAI DAWO DAIDAI NAGODE. AMMA INA NEMAN AFUWAR KU .Na sake mikewa tsaye akaro na biyu naci gaba da safa da marwa cikin dakin. In har ba dauke ruwan akayi na bude tagar dakin ba zaiyi wuya in zan iya barci.Banda wannan kuma al’amuran da suka faru ma a yammacin ranar sun isa su hanani barci na daga kaina na dubi agogo karfe daya na dare daidai..Sa’ar da muka baro kamfaninsu alhajiji (Sinad Production) sai Lauriyya tace saita rako ni har gida.Kiyi hakuri lauriyya kinsan yanzu ba kamar da bane sa’ar danake agidana yanzu kinga agidan yayana nake kare. Duk da yake dai bangarena daban ne to amma fa mutanen unguwa sun gama sa min ido dan sanin kanki ne duk yan fim yan isa aka daukesu ana son mune ana kuma kyamar mu. Lauriyya ta fahimci abinda nake nufi.Toh hilal sai gobe din kenan ma hadu. Kada ka manta fa da asussuba alhajiji yace zaku fita…. Na dubeta cikin murmushi ban taba sonta har cikin zuciyata ba kamar wannan ranar.Dan haka sa’ar dana fara zirga zirga acikin dakin inata lissafin dimbin basussukan da suke kaina sainayi mamakin irin tsabar son da lauriyya takeyimin.Kafin naci gaba da labarin nan danake baka bari in baka hoton lauriyya. Dakuma ranar da muka fara haduwa da ita domin lauriyya tana da matukar muhimmanci acikin labarin..LAURIYYA doguwa ce launin kofi mararta ashafe siraran yan yatsun kafarta da na hannu gami da dan madaidaicin bakinta ma’abocin tattausan murmushi tare da taimakon dara daran fararen idanunta gamida dogon hancinta mai kamar kan biro su suka fallasa kyawun da ta gado daga kakanninta fulani mazauna Gongola.Haduwar mu da ita tsautsayi ce domin adaren wata juma’a ne nafito daga ofishina mukayi kicibis da ita dauke da jaka kallo daya nayi mata ta burgeni.Sannan naga zatayi daidai da budurwar da muke bukata acikin fim dina na DAREN MUTUWA.Kaine Hilal?Kwarai kuwa nineWallahi daga gongola nake masauki nake nema. Hakanan a saukake don tsabar taren aradu da ka dakuma neman tsautsayi da rashin tunani sai kyawunta ya rufe min idanu na samar mata masauki batare da na binciki abinda ya rabo ta daga gida ba. Yan kwanaki kadan na fahimci ashe tanada ilmin boko mai dan tsayi domin har diploma ce da ita abangaren tsimi da tanadi. Haka nan tanada wayo da hikima hakan ce tasa na maida ita amatsayin sakatariya lokaci lokaci kuma nakan jefata a fina finai naso ace duk fim din da zan fito tare zamu fito to amma saboda acewarta.Bana son fuskata tayi yawa acikin fina finai sai kawai na kyaleta ban kuma tambayarta dalili ba.Har yanzun nan da nake safa da marwa cikin dakin bayan shekaru biyu cif cif da faruwar al’amarin ina tambayar kaina shin me ya raba lauriyya daga gaban iyayenta? Hakika lauriyya ta fara shiga raina sosai.Adacan sa’ar dana fara ganinta kyawunta ne kawai ke burgeni babu dadi ba ragi. To amma ayanzu abin ya wuce haka lauriyya ta zama jinin jikina abin tunaninaba dan komai ba kuwa sai don na fahimci ita kadai ke damuwa da fushina ita kadai ke farin ciki da karuwata ita kadaice komai ke sani dariya ta dauke min kewa aduk lokacin dana shiga damuwa.Gobe in Allah yaso saina tambayeta labarinta baki daya. Nayiwa kaina alkawarin hakan..Haryanzu ruwan saman ake tafkawa kamar da bakin kwarya na sake nazarin sabon dakin dana dawo cikin takaici domin baikai ko rabin bandakin da nake wanka ba atsohon gidana dana sayar na biya bashi.Dakin danake ciki dan kankani ne kamar dai sauran dakunan da ake yiwa boyi boyi agidajen gwamnati kujeru uku ne kacal dakin ya iya dauka. Koda yake dai in ma zaici fiye da hakan ba samu zaiyi ba domin duk na sayar da kujeruna sama da talatin na biya bashi ayanzu kam in kadauke tsohon gadon katakon dake dakin katifar daya dana tsira da ita gamida talabijin daya mai kala da bidiyo da rediyon jin labarai mai gidan kaset daya dakin babu komai sai shegen zafi gamida manya manyan saurayen dake fizgar rigata ta baya ina kwacewa dakyar.Dakin danake zaune ayanzu an tanadae shi ne dan yaron gida dayake kawuna ma’aikacin gwamnati ne ya kuma san irin yadda mutane ke ta kawo min ziyara sai ya shawarce ni dana dawo nan na tare tunda da dai karayar arziki tazo min..Nakoma bakin gadon na zauna sannan na cire rigar dake jikina na kwanta akan tsohon gadon inajin zazzafar iskar fankar dake busowa akan fuskata.Sannan kuma lokaci guda ina mai addu’ar allah sa adauke ruwan kona sami damar bude kofar nasha tsabtatacciyar iska.Ina nan kwance idanuna rufe zuciyata cike da zullumin basussukan da ake bina gamida tunanin Lauriyya ga kuma shegen zafi wannan shi ya hana barci ya daukeni. Nashiga cikin damuwa domin nasan gobe da asusussuba zan tashi domin tafiya sabon fim din da aka daukeni na Sinad production. Gashi kuma yanzu ba da ba. Domin banida ko jaki ballantana mota.Bansan sa’ar da barci ya daukeni ba adaren.Acikin barcin ne harna fara mafarki wai anata bubbuga min kofar dakin danake ciki kuma wai muryar lauriyyace ke kirana. Nayi firgigit na farka ina mitsitstsika idanuna sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa a gaske kofar dakin nawa ake ta bugawa…….(20:28, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-09.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Sannan ne to ga mamakina sainaji ashe kuwa da gaske kofar dakin nawa ake bubbugawa.Nayi fakare kamar zakara zuciyata na harbawa cikin mamakin ganin mafarkin nawa yazama Gaskiya.To saidai kuma buga kofar yasani cikin damuwa domin na lura haryanzu sheka uban ruwan ake kamar da bakin kwarya tabbas nasan ba lauriyya bace.Toh wanene ? Na tambayi kaina nadubi agogon dake jikin bangon dakin wanda ke dauke da hoton yan wasan da mukayi shirin flm din Daren mutuwa dasu.Karfe biyu da rabi na dare. Domin kuwa banga wanda zai buga min kofa ba cikin wannan uban daren sai ko barawo.Aka sake bugun kofar dakin Das Das Das kamar ana kugun kwarya da sullen kara. Nayi mamakin jin bugun kofar dakin babu karfi domin ko wanene ke bugun kofar to yana tausaya mata.Aka sake bugawa Raf Raf Raf har sau uku gumi yafara sartu a goshina hakika amafi yawan fina finan danake fitowa ni jarumi ne mai zafi marar tsoro to amma azahiri tsorone dani amar farar kura domin dan karamin yaro ma na iya tsoratani da bindigar wasan yara saboda tsorona.Me yiwuwa lauriyya ce…. Kai ba ita bace babu mamaki dai kawuna ne nace dakaina. To amma jikina baiyi amanna da kalaman zuciyata ba domin tun ranar dana tare agidan kawuna bai taba lekowa bangaren danake ba in son ganina yake saidai ya turo ayi kirana indai shine to tabbas ba lafiya ba. Can kuma sai wata zuciyar tace dani to ai kuwa idan shine kiran sunana zaiyi kai tsaye basai ya tsaya yanata kwankwashe kwankwashen kofar ba. Wannan shiyasa cikina ya dada durar ruwa jikina ya dauki bari nan da nan naji hakorana sun fada haduwa da juna kaf kaf kaf saboda tsoro.Najuya ahankali akan tsohon gadon na dubi yan tarkacen da suke dakin nace da kaina. In dan wannan ne sai na basu su tafi sun dauka jiya yau ce. Kawai wayannan barayi da rashin basira suke su basuda labarin na tsiyace ne ?Acikin fina finan danayi nasha arangama da barayi da yan fashi na doddoke su acikin sauki ina hura hanci wasu ma darakta yasa na kakkama su na daure.To amma duk wannan daban domin wasa ne yanzu kam shine azahiri domin gasu akofar dakina.Na lalubi aljihuna na dauko rubabbiyar naira goman da mai mashin yabani canji daman naira hamsin ce kadai ta rage a aljihuna sa’ar da zamu rabu da lauriyya na bata ashirin ta tafi gida nikuma na hawo acaba naira ashirin nakaraso gida da goma. Na zargi kaina saboda barin kofar gidan danayi a bude koda yake kusan ko yaushe ma ahaka take saboda abokai da maziyartan dake yawan zuwa gurina cikin dare wasu lokutan ma sai na dawo daga daukar fim cikin dare zan sami baki suna jirana. Amman ban taba samun bakin kusan karfe biyu na dare ba. Raf Raf akaci gaba da buga kofar na yunkura hantar cikina na rawa na nufi kofar dakin inata salati da sallallami.Wai wan….ne ? Nace muryata ashakre ban iya shaida ta ba amatsayin tawa, maimakon abani amsa sainaji an sake kwankwasawa.Wai wanene? Nasake kuga tambayar shiru ba amsa ba. Haushi yakamani saina tuna da fim din DAREN MUTUWA. Mun taba yin wani guri mai kamar wannan inda wasu barayi sukazo suna kokarin balla kofata nikuma nabari saida suka jingina da kofar suka gama bada karfinsu akanta sai na bude kofar da karfi suka zubo dakin kamar an handakosu nikuma na doddoke su. Yau ma zan maimaita nace cikin zuciyata saidai kuma sabanin wancan karon yanzu idan Allah yabani sa’a suka fado cikin dakin tsallake su zanyi na Gudu.Aka sake kwankwasa kofar awannan karon da karfi jin hakan shiyasani tunanin me yiwuwa mai bugun kofar jikinsa ya jingina akofar don haka cikin sauri saina zare sakata na janyo kofar da karfi sai naji sakayau kamar na janyo gadon kara babu abinda ya biyo baya.Ashe dai ko a gaske Jarumi ne. Wata zazzakar murya tace dani. Nayi sororo ina duban abin haushin dake tsaye akofar dakin cikin mamaki.Mace ce tsaye akofar dakin sanye da doguwar riga baka da jan lullubi akanta jikinta na digar ruwan saman daya daketa hakika ajin farko ce ajerin kyawawa..******** ********** **********.Mun shafe kusan rabin minti muna tsaye muna duban juna haushi da fargaba da mamaki sun hanani magana.Shin ko na iya shigowa sanyi nakeji gaskiya kuma duk kayana ajike suke. Idanuna suka kai ga katuwar akwatin mai taya dake hannunta sai hakan ya tuno min da farkon haduwarmu da LAURIYYA.Malama ina fatan dai lafiya?…. Ma’ana daga ina kike cikin wannan uban daren? Kuma da wacce kika zo? Yar budurwar ta dubeni sa’annan t jefeni da lallausan murmushin Allah kasheni don dadi.Lafiya kalau Hilal tun daga wata nisan duniya nataho gareka domin kawai na ganka na dade ina ganin fina finanka ina kaunar araina da begen ganinka shne naga bazan iya jurewa ba sainazo na ganka da idanuna. Ta danyi shiru tana kokarin share ruwan dake sartu daga cikin gashinta zuwa fuskarta. Gashi dai cikin duhu muke tsaye dakin babu wuta amma duk dahaka fuskarta har sheki takeyi idan akayi Walkiya. Ko makaho ya lalubeta yasan Allah yayi halitta agurin.Tsarki ya tabbata ga mahaliccin kyawawa.Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba….KUCI GABA DA HAKURI DAI SAURA KIRIS HARHARDEWAR DA LABARIN YAYI WAJEN TYPING DINA YA WARWARE(20:29, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-10.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Haryanzu dai baki gama amsa min tambayata ba nace da ita ina dubanta. Yar budurwa ta daga girar idanunta sama cikin rashin fahimta can kuma saita girgiza kai gamida wani alakaron murmushin.Oh kana nufin daga inda nake? Daga maiduguri nake motar mu ce ta baci ahanya shiyasa mukayi dare yanzun ma direban motar na roka Allah da Annabi shine yakawo ni har nan tayi shiru tana dubana.Jarumi Hilal ina fatan dai yanzu ka gamsu…..shin na iya shigowa?Sanyi nakeji Wallahi hilal akwai wani abu a tattare da ita dake damuna fiyeda yawan murmushinta gashi kuma ko ganina azahiri bata taba yi ba sai yanzu yanzu ma kuma acikin Duhu..Na matsa gefe guda ta shigo cikin dakin zuciyata cike da tunane tunane. Ta ajiye akwatin sannan ta juyo ta dubeni.In baka damu ba don Allah nuna min bandaki yake so nake na shanya kayana duk sun jike jagaf.Gabana yafadi ras na bude baki cikin kaduwa nace Ki shanya kayanki? Na tambayeta adolance. Ta gyada kai. To ke kuma ki zauna dame? Tayi murmushi lokaci guda tasa hannu ta yane jikakkken lullubin dake kanta nan da nan siraran gashin kanta baki sidik suka zubo kan kafadarta koda walkiya ta hasko cikin dakin sainaji zuciyata na harbawa da sauri na dade banga gashi da kyawun nata ba.Saina zauna aciki idan sun sha iska na maida kayana nafito. Na sunkuyar dakaina kasa a rude kai yau na gamu da gamona. Nace cikin zuciyata koda na daga kaina sainaga ta kura min idanu kamar zata hadiye ni.Oh hilal yau dai Allah ya nuna min kai. Wallahi kada kaga irin son danakeyi maka duk cikin yan wasan hausa babu wanda nake kauna kamar ka zakayi mamaki idan nace ma acan maiduguri akwai kawayena da yawa da suke kirana da suna HILAL.Tayi shiru tana dubana me yiwuwa ko don ganin duk surutun da takeyi ban tanka mata bane.Hilal yaya kakeyi min irin wannan kallon ne haryanzu baka amince dani ba. Akaro na farko sainaga ta dan hade fuska amma duk da hakan saida idanunta suka nuna alamun murmushi.Bahaka bane malama abin da haryanzu ke rudani shine zuwanki cikin wannan talatainin dare kuma….. Ta katseni.Nace dakai motar muce ta lalace haba hilal nifa bakuwarka ce in kuma korata kakeyi shikenan bari natafi nagode. Ta yi nan tsaye bata dai motsa ba akaro na farko saina sassauta murya nace da ita a tausashe.Toh naji na yarda amma kuma yaya akayi kika san gidana?Yar budurwar ta dubi akwatin dake kwance atsakar dakin sannan ta dawo da dara daran idanunta kan fuskata.Hilal kaga in bakaji dadin zuwana ba simple ce kawai na fita saina fice ma daga daki ko a tasha na kwana da safe na koma garinmu yaya zaka sani agaba da irn wadannan tambayoyi kamar wani tsohon dan sanda. Ta harareni gamida murguda min baki ta danyi shiru tana maida numfashi.In banda abinka hilal mutane nawa ne suke zuwa ziyartarka arana daga jihohi daban daban ? Kawayena ma nawa ne suka zo gurin ka? Ai kwatancen gidan fitacce kamar ka ba wahala bane musamman agidaje irin wadannan na gwamnati kasan fa kowane gida yanada lamba…kodayake dai zuwana ne kawai baka so. Ta juya min baya tana kallon kofar dakin.Allah baki hakuri nace da ita a tausashe juyo mu fuskanci juna basai kin juya min baya ba yar budurwar ta juyo da faffadan murmushi.Lah hilal menene kuma na bata rai nifa ba fushi nayi ba ai ko ina fushi da mutane hilal kai ka wuce nayi fushi dakai idanunta suka kai ga agogon dake makale abangon dakin. Na dubeta nima karfe biyu da rabi na dare 2:30am.Lah wannan ai hotonku ne na fim din Daren Mutuwa. Budurwar tace cikin karaji sannan cikin hanzari ta matsa kusa da agogon ta kura masa idanu.Nikuwa hilal daman inason na tambayeka na dubeta cikin mamaki.Me zaki tambayeni? Yar budurwar ta dora dan yatsanta na hagu akan hoton ta nuna fuskar Lauriyya tace. Amma wannan yarinyar ko agaske ba’a fim ba budurwar kace ko? Naji gabana yafadi ras na girgiza kai.Kokusa kada kiyi tunanin haka fim ne kawai kinsan ku yan kallo kusan ko yaushe kuna da wannan kuskuren fahimtar.Irin kallon datakeyi mane a fim din na lura ya wuce na wasa….. Na dubeta akaro na farko sainayi mata murmushin yake..bakya rabuwa da kame kame baiwar Allah bakisan yan dirama bane yanzun nan sai suyi miki abu kiga kama da gaske nan kuwa karya suke. Bata juyo ta kalleni ba haryanzu kallon hoton take amma na lura da murmushinta ba zato ba tsammani saita juyo ta fuskance tace.Ai kuwa kyakkyawa ce. Mukayi shiru na tsahon lokaci muna duban juna..Nuna min bandaki hilal kada mura ta kamani da wannan jikakkun kayan dake jikina.Zo muje nace da ita domin nagaji da jayayya.Nashiga gaba tana bina abaya kamar bawa da balarabe bandakin acan bayan falon yake saidai kuma zaka iya shiga bandakin ta cikin falon batareda k fita waje ba.Ga kofar nan nace da ita ina duban yala yalan gashin kanta. Hakika kyakkyawace ajin farko ta dubeni sannan ta sake jifana da murmushi ta shige bandakin gamida rufo kofar gararam da karfin gaske karar rufr kofar suka cakude da rugugin aradun nayi sauri na rufe kunnena.Akwai lokuta da dama da bana son sautin aradu domin ji nake kamar ni zata fadowa………(20:30, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-11.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Domin ji nake kamar ni zata fadowa…Na juya ahankali na nufi dakin ina shiga saina janyo kofar dakin amma ban rufe ta gaba daya ba. Na zauna abakin gado nafara jujjuya batun wannan kyakkyawar budurwa mai ziyarar tsakar dare cikin zuciyata.Akwai wani abu atattare da ita dake bani tsoro na lura da ita ko kusa ko alama batada tsoro haka nan batada kunya kuma babu alamar bakunta ajikinta bugu da kari kuma acikin amsoshin tambayoyin danayi mata akwai amsa daya na tabbata karya takeyi..Shin duka duka wata na nawa da tarewa awannan gidan da har maziryata na zasu kwatonta mata inda nake? Nidai a iya tunanina tun dana tare agidan bansamu wani maziyarci daga bakuwar jiha ba ina nan zaune ina jiran fitowarta na dubi agogo karfe uku saura kwata 2:45am nasan ni da sake samun wani isashshen barci kuma sai abinda hali yayi tunda dai nan sa sa’o’i biyu da motsi zamu fita sabon fim dinsu Alhajiji. Nayi murmushi sa’ar dana tuna yaudarar da Lauriyya tayiwa alhajiji kai wannan al’amari da daure kai yake nace da kaina saikayi mamakin yadda kudi da mata suke tsananin tasiri azuciyar Mazaje.Naji gabana yafadi sa’ar da wani tunani ya fado min nan da nan naji gumi ya fara sartu agoshina yanzu idan garin Allah ya waye wani kokuma kawuna yazo ya sameta adakin nan me zance dashi? Kirjina yafara dakan uku uku tuni nasan mutanen unguwa sun dade suna zuzzuga kawuna akan wai dole sai ya hanani harkar wasan kwaikwayo domin wai duk yan wasan kwaikwayo yan iska ne marasa mutunci da kyar nasamu na shawo kansa. To yanzu kuma bayan duk wannan idan yasami mace ta kwana adakina fa?Gumi yaci gaba da sartu akan goshina kaga dan samari wata zuciya tace dani abu mafi sauki shine data fito daga bandaki katafi da ita gidan kawunka ka kwankwasa masa kofa nasan in nayi masa dogon bayani yana iya fahimta sai su kwana tare da matarsa.Tunanina ya katse adaidai lokacin danaji wani abu kamar sautin mota wajen gidan na dubi agogo karfe uku harda kusan rabi 3:30am kai amma dai ta dade cikin bandakin nan kodana lissafa sainaga kusan sa’arta guda aciki na mike tsaye cikin sauri na nufi falon ina zuwa saina wuce kai tsaye zuwa kofar da zata kaini har bandakin ga mamakina sainaga kofar a bude. Gabana ya ya fadi na mtsa ahankali na kara kunnena ajikin kofar bandakin ko zanji motsi shiru sai sautin zubar ruwan sama akan kwanuka zuciyata na harbawa saina kwankwasa kofar bandakin. Malama haryanzu kina ciki? Shiru ta gaida kunnuwana.Malama ina kike ne? Na sake kiran sunanta to saidai kuma ni kaina nafara tunanin bazanji amsar komai ba.Na bude kofar bandakin ahankali sainaga WAYAM. Babu ita babu alamarta. Nan da nan na ruga aguje zuwa kofar gidan. Ina kike ne? Adaidai lokacin ne to naji sautin injin mota an tuka anbar gidan. Nakarasa aguje amma ni kaina nasan bazan taba samun motar ba na tsaya sororo ruwan saman na dukana ina hangen danjar motar tana daukar idona kamar gauta acikin rana.Sannu ahankali har na daina hangota..UKU 3.Nadawo cikin dakin jikina na rawa kamar tsohuwar data sami kwarto karkashin gado. Na zauna jagwaf atsakar dakin kamar tsohuwar saniya na kurawa akwatin data bari danu sama da tambayoyi dari suka fara turereniya cikin zuciyata.Shin wacece ita? Daga ina take? Menene dalilin zuwanta? Yanzu kam dana tabbata TA GUDU na tabbata duk abinda ta fada abaya karya takeyi. Sannan babu zato babu tsammani saina tuno da akwatin datazo da ita.Na mike zumbur kamar an sokeni da kibiya na nufi inda akwatin take jikina na tsuma na daukota na dora akan gado sannan na fara kokarin budeta. Atunanina acikin akwatin ina iya samunwata shaida da zata sanar dani ita wacece. Allah ma ya taimakeni data bar akwatin nace cikin zuciyata.Na danna mabudan akwatin ina mai wasi wasin budurwar ga mamakina sainaga ta bude fayau. Na dubi cikin akwatin ina mai mamakin ganin babu komai ciki sai wani dan kyallen yadi fari lullube da wani abu. Jikina ya dauki rawa kamar mazari. Nasa hannuna kan farin kyallen sannan na janye farin kyallen.Numfashina ya kauracewa kirjina yawun bakina ya kafe kana yar autar cikina ta manne jikin hanjin cikina. Akwance male male akasan akwatin.DAN JARIRI NE.Sabuwar haihuwa kyakkyawa dashi kamar dan larabawa akusa dashi kuma takarda ce ko liketa ba’ayi ba ajikinta sakone a rubuce kamar haka………HILAL.Na dade ina ganin fina finanka kuma kana matukar burgeni hakan nema yasa begenka yafara mamaye zuciyata. Hakika tun danake arayuwata ban taba ganin jarumin danake kauna ba kamar kai ka iya shiri kwararrene kai mai burge yan kallo to saidai kuma katsam sai gashi acikin fim dinka na DAREN MUTUWA ka bani haushi kasa na tsaneka. Lokacin da ka dauki jaririn nan acikin fim din zaka jefa shi cikin rami sainaji kamar da gaske zaka jefa ciki.Baka dade ba da gama fim din sai nima na sami nawa jaririn abin dai kamar acikin dinka na daren mutuwa CIKIN SHEGE NE don haka sai naga abinda ya dace shine na sako shi cikin akwati na kawo maka shi tunda dai ka saba jefa jarira acikin rami me yiwuwa kana iya rabani da nawa abin kunyar ka taimaka ka Jefar min da shi. In kuma kana so to gashi nan nabaka shi kyauta a matsayin ka na kwararren jarumin fim dinDAREN MUTUWA.Sai anjima kada ma ka nemeni domin bazaka taba samuna ba domin GARIN MU DA NISA…..!.NA ajiye takardar cikin akwatin jikina na rawa sannan na dubi jaririn dake kwance cikin akwatin sainaga kamar yanayi min dariyar kuda. Na dafe kirjinsa da tafin hannuna na girgiza kai cikin Kaduwa lallai kam kyauta ta musamman. Hakika kam nayi dace da kyautar kyakkyawan jariri in da ba don MATACCE BANE..*********** ************ ******************.ALAKAKAI-12 Loading……(20:33, 1/19/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-12.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Hakika kam da nayi dace da kyautar kyakkyawan JARIRI in da ba don MATACCE BANE..************ ********* *******.Idanuna suka fara zafi banyi mamaki domin gumin dake sartu akan fuskata kamar ruwa tuni yafara shigar min idanu.Nasake duban kyakkyawan jaririn dake kwance acikin akwatin na tsahon lokaci sannan sannu ahankali saina janyo farin kyallen na lullubeshi gami da rufe murfin akwatin ahankali kaikace tsoro nake kada na tashe shi daga barcin dayake. To saidaikuma nasan shi da farkawa sai ranar da aka busa kaho.Kafin na rufe akwatin saida na dauke wasikar da budurwar tasa aciki na tura ta cikin aljihuna sannan na mike tsaye ina muzurai ni kadai kamar tsararraren kwarto.Shin wace mata ce wannan? Shin danta ne? In kuma bana ta bane menene alakata da jaririn menene kuma dalilin dayasa ta rasa wanda zata kaiwa gawar jaririnin sai Ni? Kai wannan rashin imani na mutanen duniya da yawa yake.Haryanzu ba’adaina tsugu uban ruwan saman ba haka nan lokaci lokaci saikaji an ruguza aradu kamar ta tsaga dakin. Ama ni duk wannan ba ita bace agabana babban abinda yafi tayar min da hankali shine yaya zanyi da jaririn?Ka kirawo yan sanda wata zuciya ta shawarce ni. Acan kuma wani bangaren na zuciyata akace dani.Kai shashashan banza idan ka sake ka kirawo yan sanda ka kashe kanka daman tsammani zasuyi sato shi kayi ka rude shine ka kirasu.Basai kayi musu bayanin yadda budurwar ta kawo maka shi ba? Wata zuciyar ta sake kwabata in ka sake ka kira yan sanda ka karasa rusa kanka a harkar fim domin dole ne labari ya watsu abokan hamayyarka kuwa sun sami makamin da zasuyi ta yakarka har sai sun kai ka kasa.Can kuma sai wata zuciyar tace danikai dan samari rufawa kanka asiri tun wuri ka dauki jaririn nan yadda ta baka shi kaima kaje ka jefar dashi ka hutawa kanka tonon silili.Kokuwa na tashi yayana na sanar dashi? To sai dai kuma haryanzu zuciyat nan nata kururuwa cikin kwakwalwata kai fa baka rabuwa da sakarci Wallahi mutumin da tuni mutanen unguwa sun gama zuzzuge kawun naka ana cewa yan iska ne ku yan shirin fim bakajin cewa idan yaganka da jariri zai iya tunanin ko naka ne aka kawo maka shi har gida dan bariki?Ai kawai ka dauki jaririn nan bakinka alaikum ka jefar dashi.Abinda yakama nayi kenan nace da kaina. Nasan dai yanzu babu jami’an tsaro akan tituna ballantana kuma mutane na mike tsaye cikin sauri ina mai fargabar kada gari ya waye min akamani da jariri dumu dumu ahannu.Wani zazzafan gumi yayi zarya tun daga kan doro wuyana har zuwa bayana. Kagafa hakane. Nace da kaina. Lallai kam mafita ta daya ce kawai na hanzarta na dauki jaririn nan na jefar dashi na huta in yaso daga baya na nemi uwarsa. Amma tabbas in har maganar ta fito fili to ko kawuna bai zargeni da komai ba sai mutanen sunyi ta yawo da zancen me yiwuwa ma wata rana yazama abin gori ga ‘ya’yana.Akaro na farko tun bayan da akayi min kyautar jaririn sai naji sanyi sanyi araina. Kwakwalwata kuma tafara tunani sosai da sosai.Na nufi kofar dakin ahankali sannan na shiga falon. Na duba hanyar da zata kaika har bandaki saina girgiza kaina. Lallai budurwar tayi kyan dan maciji na wuce kai tsaye na nufi kofar da zata kaini har waje na budeta kadan. Sassanyar iskar dake ta faman watangarariya da kwayoyin ruwan dake zubowa adoron kasa daga sararin Subhanahu Wata’ala ta bugi fuskata yan sa’o’i kadan da suka wuce bazan iyayin maraba da iskar ba amma ayanzu saita zame min tamkar na’urar sanyaya daki alokacin zafi.Na juyo dakin cikin sauri na sunkuya abakin gadon sannan na tura hannuna na dauko katuwar rigar leda ta ruwa wacce azamanin danake tashe aharkar fim idan zamu tafi daukar shirin fim lokacin damina da ita nake fita.Koda na dauko rigar na karkadeta saina dorata akan rigar dake jikina sa’annan na fara balla maballin rigar bugun zuciyata yafara dawowa daidai ayanzu na sake sunkuya karkashin gadon akaro na biyu na dauko takalman ruwana nasa sannan na duba akwatin da mataccen jaririn ke ciki na tambayi kaina da cewa…To yanzu kuma ina zaka jefar da akwatin waje na farko daya fara zuwa zuciyata shine wani katon kango dake bayan gidan wani attajiri wanda ya saye ginin kwamnatin gidaje uku ya hadesu ya kera katon gida.Katon kango ne yadade ahaka an zagaye shi ba’a gina ko daki daya acikinsu ba. Lokacin damina kamar yanzu kangon cike yake da dogayen ciyayin tafasa da rai dore awani lokacin dan daya wuce zamanin muna yara acikin kangon muke bata lokaci muna wasan boyayyeniya idan mun taso daga makaranta. Bazan manta ba maciji ya taba cizon abokina Sani Ayuba acikin kangon. Nayi sauri na kawar da tunanin hakan daga zuciyata tabbas nan ya dace nakai akwatin.Na sunkiya ahankali na dauki akwatin mai tsaya wacce jaririn ke ciki na nufi kofar dakin cikin sauri.Koda na bude kofar dakin sainayi murmushin yake cikin duhun daren kamar awani fim din Daren mutuwa.Allah sarki jiya ba yau ba nace da kaina.Na dade akofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi. Daga karshe dai sai……(07:09, 1/20/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-13.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Na dade a kofar tsaye ina duban duhun daren ina tsammanin ko zanga wani dan motsi daga karshe dai sai na saduda naga tsoro da fargaba basu amfana ta awannan lokacin sai kawai na jefa kafata waje na shige cikin ruwan ina mai Addu’ar Allah yasa duk wanda muka hadu dashi yayi kuskurena a matsayin jami’in tsaro.Naci gaba da tafiya ruwan saman dake zuba kamar da bakin indararo sai dukan bayan rigata yake fas fas. Duk dayake dai nayi sa’a duk kusan bangaren gidajen an dauke wutar lantarki amma Hakan bai bani kwarin gwiwar fitowa nayi tafiya kai tsaye cikin takama ba Ina tafiya ina bin inuwar bango kamar Kadangare wata sa’ar ko Walkiya akayi sai na rabe kadan kafin naci gaba da tafiya.Ina nan tafe lokaci guda kuma duk Addu’ar da Tazo bakina sai in karanta… Kwatsam sai nafara hango gidan attijirin tsakanina da gidan akwai yar tazara kafin ka kai ga kangon dake jikin gidan saikayi tafiya cikin wata yar farfajiya wacce babu gine gine a cikin ta sai ciyayi haka nan kuma anan filin wasan kwallon kafa na samarin Unguwar yake.Gabana ya fadi sa’ar dana hango fitilun lantarki naci a kofar gidan dakuma kan katangar reras dasu kamar taurari tabbas injin wutar lantarki ya kunna.Ganin hasken ne ya sani sauya shawara na kauce nabi wata yar siririyar hanya wacce ta ratsa ta cikin filin wasan kwallon kafar takuma bi ta bayan gidan attijirin zuwa cikin kangon da nake hari.A daidai lokacin ne to najiyo sautin abin da ya kusa sa akwatin dake hannuna ta subuce….Ko shakka babu mutum ne abayana. Nayi mutuwar tsohuwa a tsaye tsoro da fargaba suka hanani juyawa. Wani abu ya dunguri dunduniyar takalmina na dauke numfashi cak ina kokarin zama gunki har yanzu wanda ke bayan nawa bai ce Dani uffan ba sannan ne to naji wani gurnani abayana marar dadin jiGashin jikina ya mimmike tsaye kamar gashin bushiya tuni wani zazzabi zazzabi yafara kokarin rufeni nayi ta yan maza na juya a hankali na dubi bayana sai mukayi ido hudu da bawan Allah mai bakaken idanu kamar ifritu yana gurnani wani dankareren kare ne mai jajayen idanu da zako zakon hakora kamar tarko babu alamar farin gashi a jikinsa.Wani katon kare ne ya kwada min uban haushi WAW-WAN Nayi tsallen gefe guda sai yakawo min sura santsi ya kwashe ni nafada cikin cabin ruwan nagama gigicewa maimakon na Jefar da jakar saima na sake mikewa tsaye da ita kankame a kirjina kai kace wasu makudan kudade ne aciki.Mukayi tsaye cirko cirko nida karen ya dube ni na dube shi saina juya da gudu karen kuwa yace da wa Allah ya hadashi bada ni ba.Tun kafin tafiya tayi nisa karen ya fara kawowa dunduniyata sura. Allah ya taimake ni da takalman ruwa a kafata akaro na biyu ne ya sami Nasarar farka rabin rigar ruwan dake jikina..Wayyo Allah.Na kwalla ihu na manta da abun da ke dauke a hannuna na sake juyowa a firgice na kaiwa karen duka da jakar dake hannuna Saidai kuma dukan na matsoraci ne domin bai iya kwantar da ko da yar budurwa ba ballantana mahaukacin kare alokacin ne toTAFARU TA KARE. Wani abu mai kamar guduma ya sulalo ta cikin duhun daren ya daki tsakiyar kaina kafin na gama warwarewa sai wani abu kuma mai kamar katakon duka ya daki bayana naji kamar an soke ni da mashi.Wayyo Allah na kwalla ihu.Zakayi ihu ma sai agaba shege BARAWO Meka sato acikin akwatin?Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren…………*************** ************* ***********.INASON CIGABA NEPA SUN HANA SAIKU JIRA SU .ALAKAKAI-14 loading…….(20:57, 1/21/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-14.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Zakayi ihu ma sai agaba shege barawo.Me ka sato acikin akwatin? Wata kakkausar murya tace dani daga cikin duhun daren…..********* *********** ********.Adaidai lokacin dana sulalewa zan fadi acikin cabalin ruwan ne sai wani busashshen hannu mai kamar iccen makera ya cafi kwalata ya dagoni sama da karfin tsiya ya girgizani.Me ka sato aciki Barawo? Aka sake tambayata akaro na biyu sannan sai busashshen hannun ya damki makwogorona.Idan baka fadi abinda ke cikin akwatin nan ba kasheka zanyi shege azzalumi kudin wa ka sato?Wallahi ba kudi bane.. Nace dashi cikin karaji.Uwarka ce to aciki? Shege Allah ya tona asirinka kananan barayin unguwa daman jira kakeyi afara ruwa saika biyo dare ka dauki wannan ka zari wancan kamar mayen karfe ko?Haryanzu ba’a daina tsuga uban ruwan saman ba na hadiye yawu da kyar ba karamin riko yayiwa makoshina ba dakyar nake numfashi gashi ya daga hancina sama ruwa sai shiga yakeyi kamar bututu.Busashshen hannun ya dada girgiza ni zuciyata sai harbawa takeyi Tam Tam kamar tamaula tsakanin hakarkarina akwatin kankame akirjina na san idan na sake ya bude akwatin kashina ya bude.Daureka zanyi yace dani yau Allah ya toni asirinka bazan buda akwatin daka sato ba amma da zarar gari ya karasa wayewa zan mika ka ga hukuma.Mutumin ya tura ni riki riki da akwatin ahannuna muka nufi katon gidan attajirin nan mai katanga dauke da fitilun lantarki burjuk kamar hasken rana.Mutumin yaci gaba da jana kamar mushe rabi ina tafiya rabi kuma kafata na jan kasa kamar kafar gawa.Wani lokacin idan aka kwantsama aradu mai karfin gaske sai mutumin ya dan dakata da jana yace.Shege dama ta fado maka azzalumi.Nayi mamakin ko wanene azzalumin tsakanina dashi.Bayan wasu yan tsirarrun mintuna muka kawo ga kofar gidan attajirin nan. Na dubi dankareren gidan kana na dubi yan mitsi mitsin kwayoyin ruwan dake ta zubowa bila adadin daga sararin Subhanahu Kamar hazo lokaci guda kuma na juyo akaro na farko nayiwa mutumin kyakkyawan kallo.Banyi kuskuren fasaltashi cikin zuciyata ba.Domin kamar dai yadda nayi tunaninsa haka nan yake saima abinda ya dadu kato, baki, jajayen idanu, fankaceciyar kafada, kamar kofar shagon kasuwa. Abin dayafi bani mamaki ga halittarsa shine duk da girman jikin nan nasa kansa dan kankanine haka kuma fuskarsa tsukakkiya ce fatar bakin siririya kama an tsaga wanda da tsinin wuka.Koda ya dada fizgata muka dada matsawa daf da kofar gidan sai tangamemiyar kofar ta bude wasu dogayen mutane suka fara fitowa daya bayan daya har suka zama su uku. Basu damu da ruwan da ake kwararawa ba.Mutanen uku duk Buzaye ne sirara masu dan rakeken wuya kamar kasan almakashi ka dauke.Kowannensu dauke da dakon katon rawani kamar mushen tunkiya rike da takobi tsirara.Wa Allah kuma ya hada ka dashi MAMUDA?Daya daga cikin masu gadin ya tambayi katon mutumin dake tike da wuyan rigata.Irin yan kananan barayin unguwannin nan ne dake damun unguwa da yan sace sace yanzu ma dubunsa ce ta cika na zagaya cikin ciyayin can sainaji DUNA yana haushi nakai masa agaji nakamo wannan karamin marar kunyar.Yana gama fadin haka saiya hankadani gaban buzayen da karfi na fadi ricaaa agabansu..Wannan akwatin fa dake rungume akirjinsa?Buzun maigadin ya tambayaban budata ba babu ruwana da abinda ya sato ku barshi kawai idan gari ya waye saimu mika shi ga jami’an tsaro domin irin kananan barayin nan annoba ce ga al’umma dan irin su ne idan suka rika sai su zama yan fashi da makai.Yasa kafa ya daki Duwawuna da karfin gaske na kwalla kara.Au dan dan wannan ma? Ai somin tabi ne kawai na baka ladan kamu ne saima gobe idan kaje hannun yan sanda kayi mai dalili Ya fashe da dariyar mugunta.Ku jefa min shi cikin dakin injin bada wuta yace da buzayen.To! Suka amsa baki daya sannan kowa daga cikinsu ya kama inda yafi rainawa ajikina sukayi sama dani kamar gadon kara suka nufi cikin gidan dani.Kada ma ku damu kanku da sai kun daure shi kudai ku kulle shi kawai aciki karamin barawo ne babu abinda zai iya yi.Suka karasa dani kofar wani dan daki dake manne ajikin bangon gabas na farfajiyar gidan dan dakin kusan duk akere yake da shuke shuken furannin alfarma haka nan duk farfajiyar gidan. Nayi bakin ciki domin duk da mummunan halin danake ciki basu barni na kashe kwarkwatan idanuna ba.Muna isa kofar dakin sai suka ajiyeni akasa biyu daga cikinsu suka rikeni yayinda dayan ya bude dakin jannaretan nan da nan karar injin dake cikin dakin gamida hayaki suka gauraye gurin.Anan zaka kwana in kuma kaso ma to kana iya sace injin gaba daya duk ribar kafa ce wai giwa ta taka kwado. Suka jefani cikin dakin kaina ya bugi jikin injin. Sannan na mirgina gefe guda ina murkususu.Masu gadin suka mako kofar garam!!! Sannan naji karar kwadon sun kulle dakin..Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda karajin inji sannan kuma idanuna kamar zasu fito waje saboda hayakin injin dake shigo min.To amma fa duk wannan bai sa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba(10:23, 1/22/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-15.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Na tashi zaune ahankali dodon kunnena kamar zai fice saboda Karar injin sannan kuma idanuna kamar su fito waje saboda hayaƙi injin dake shigo min.Toh amma fa duk da irin wannan wahala baisa na jefar da akwatin dake rungume a kirjina ba na yunkura Dakyar sannan na nufi kofar kofar dan karamin dakin injin bada wutar lantarkin adaf da kofar dakin akwai wasu yan kananan tagogi ajere reras guda shida don haka ina Karasawa ga tagogin Saia tura hannuna ta cikin kofar daya daga cikin yan kananan tagogin hakan danayi shi ya bani damar shakar tsaftatacciyar iska sannan kuma sassanyar iskar ruwa ya bugi fuskata nan da nan naji na dan fara dawowa hayyacina akusa da kofar dakin daga hannun hagu akwai wai katon duro na mai.Na matsa kusa da durom din na ajiye akwatin akai na jingina dashi sannan kuma wani lokaci guda fuskata na cikin yar Jafar tagar ina shakar iskar tsaftatacciyar iskar ruwan Saman ahaka ko barcin gajiya ya dauke ni.Bansan iya sa’o’in dana share ina barci ba Nidai kwatsam ba zato ba tsammani sai ji na nayi nadaku da kasa. Sannan naji wani abu ya Fado min awannan sa’ar na tashi firgigit cikin tsoro sannan ne to na fuskanci ashe barci ne ya daukeni a tsaye harna ture durom jakar dana ajiye da kuma akwati.Na tashi tsaye da kyar jikina na rawa ga mamakina sai Naji gidan yayi tsit wannan shi ya tabbatar min da cewa an Dade da dauke ruwan saman acan wani bangare kuma na Unguwar nasu wani ladan mai zakin muryar gaske yana kwada kiran sallah asuba tayi nace a zuciyata kashina kuma ya bushe kenan. Na sake cewa a zuciyata Daman nasan da gari ya waye marasa imanin masu gadin nan zasu Mika ni hannun yan sanda shin anya kuwa haka zata yiwu? Yafa kamata ka motsa ko zaka samu hanyar tsira wata zuciya tace dani.Na nufi kofar dakin ahankali kafata kamar zata balle saboda ciwo nasa hannuna a jikin kofar na dan jijjigata sannan ne to naga kofar dakin……… Karshen abubuwan…….. Ne..Karfe da gilashi kuma gilashin dake daf da inda nake masakalin dan makullin yake a daya sakon. Nan da nan zuciyata tafara harbawa inama ace zan iya murde dan makullin na ce da kaina. Namika hannu naji hannun ya taba kwadon dakin kamar wasa sai kawai naji kwadon ga mamakina ya bude gumi yafara sarara agadon bayana sannan ne to wata zuciyar tace dani shashasha mai gadin bai balle kwadon ya shiga daidai ba. Nan da nan na murde kwadon na tura shi sama sai ya fadi can kasa Tim. Jikina kamar mazari na rawa na dauki akwatina sannan na tura kofar ahankali sai ta dan bude nayi shiru ina saurare ko zanji motsi shiru babu motsin komai sainaga hanya yakin bishiyoyin gidan da iska ke kadawa banyi mamakin jin shirun ba domin nasan hankalin masu gadin a kwance yake tunda dai a tunanin su ina nan a kulle abu na farko da ya fara zuwa zuciyata shine hanyar da zan bi na tsere to Saidai kuma tuni na tabbatarwa da kaina cewa bashi yiwuwa na tsere ta kofar da suka shigo dani idan nayi gangancin bi ta kofar to kamar na tura kaina ga halaka ne da gangan..Tsakanina da inda dakin yake dakuma tangamemiyar kofar gidan yake akwai tazara don haka sai wata zuciya tace dani tunda dai kofar bata biyuwa me zai hana ka lallaba ta cikin duhun shuke shuken da suka kare dakin ka zagaya ta baya? Nan da nan sai na koma ina mai amincewa da shawarar zuciyata tunanin daya fara zuwa min shine na zagaya bayan gidan saina haura katangar indira cikin tsohon kangon dake makwabtaka da gidan wanda Daman tun farko anan nayi niyyar jefar da akwatin mai JARIRIN.Na tura kofar dakin ahankali sannan na fito waje.Sannan ahankali ina bin lungu lungu sako sako dake cikin shuke shuken har na kawo ga ginin gidan adaidai lokacin to naga yar siririyar hanyar data bi ta bayan ginin dakunan gidan har zuwa katangar arewa wacce itace ke makwabtaka da gidan.Fasalin ginin dakunan gidan irin Fasalin nan ne da zaka iya ginin dakunan su kadai ne a tsakiyar gidan batareda an jingina koda gini daya da katanga ba wannan shi ya baiwa rufanin damar yin yado ajikin katangar hakan nan kuma yan dukur dukur fitilun alfarmar suma suka kai kusurwar katangar kudu ta gidan abin gwanin ban sha’awa me yiwuwa hakan ce tasa akayi ginin tsakiyar gidan batareda an jingina shi da koda katanga daya ba..Na lallaba ahankali kirjina na Dakan shida shida na bi yar siririyar katangar ta tsakanin shuke shuken na nufi katangar.A daidai lokacin ne to sainaga tagar daki ta bude nayi sauri na sunkuya acikin shuke shuken dake daf da tagar kadan ya rage tagar dakin ta buge min kai domin jikin ginin dakin nake bi bantaba zaton za’a bude tagar din ba haka nan shiyasa ni tunanin ko na koma da baya na sake hanya domin a baya na akwai jerin wasu tangagogin har guda biyar kafin nakai ga katangar danake hari. Bangama shawara ba sai na sake jin abin da yasa zuciyata harbawa da karfin gaske. Wata shakakkiyar muryar magidancin mutum tace…..Ke FADILA tashi munafuka INA KIKA JE DA DADDARE naji shiru na dan lokaci sai Naji an sake cewaKe ba ke Nake yiwa magana ba? Shiru ba’a amsa ba can sai Naji an amsaBABA NI WALLAHI BABU INDA NAJE……..Jin muryar shi yasani mikewa zumbur kamar wanda aka sokawa kibiya na sake saurarawa dakyauTo don iyayen ki ni zakiyiwa karya ina kallon ki fa jiya ana wannan ruwan kika fice dauke da akwati a hannun ki Ina Kika kai akwatin ina kuma kika ajiye motar da kika dauka? Wani abu mai Kamar gizo gizo ya biyo tun daga babban dan yatsana har zuwa bayana.Bab…… Don Allah tafara kuka na Mike tsaye ahankali na leka tagar dakin sannan ne to naji numfashina ya dauke ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI NE(13:00, 1/24/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-16.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Ko shakka babu yarinyar data bani kyautar JARIRI ne..Tana zaune abakin gado ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta gashin kanta awarware wani katon mutum ne dattijo tsaye akanta sanye da babbar riga bana raba daya biyu mahifinta ne. Naci gaba da saurarensu jikina na rawa.Ina kika kai jaririn munafuka? Mutumin yace sannan ya matsa kusa da ita ya gaura mata mari tasina kuka kai jaririn iye? Wato jefar dashi kukayi ko? To zakici gidanku…. Yau daga ke har shegiyar uwarki data bataki sai kun fice min daga gidana ke kuwa ahannun yanda zan mika ki.Kai Allah wadaran haihuwar irinku haihuwar bakin ciki. Adaidai lokacin ne to naji budewar kofar acan cikin dakin.Kada ka zageni. Wata sassanyar muryar mace tace duk abinda yafaru akan FADILA kai ka janyo ai sai da nace dakai kada ka riga sakarwa fadila kudi tun tana karama nayi nayi dakai ka kikasai mata mota har guda uku don shagwaba har kasashen turai kake tafiya da ita tokuma shin ayanzu don…..idonta ya bude da iskanci har ta sami nasarar ba wa… DAN GWARZO shine kuma zaka zargeni ? Matar tayi shiru tana maida numfashi ai saida nace dakai a zubar da cikin ka ki yo kuma yanzu don ta haifi dan ta jefar shine zaka zo kahauta da duka ka dagata don Allah Alhaji kada ka kashe min ‘ya ba fa taka bace kai kadai.Mutumin ya dubi matar a fusace yace.Allah wadaranki Wallahi nima kaddara ce tasa na aure ki rabon dai in sami wannan tsinanniyar yarinyar da zata janyo min abin kunya agari kema kafin na aure ki ciki nawa kikayi aka zubar?To kace ma fadilar ba ‘yar ka bace mana.Matar tace a fusace nan da nan sai maigidan ya sake shake yarinyar yahauta da duka.Wayyo Allah baba na shiga uku fadila ta fada cikin kuka.Baki shiga uku ba ma tukunna sai ma na dora wuka a mokogoronki don ubanki. Ina kika jefar da jaririn..Batare da na sake jiran komai ba sai kawai na dauki akwatin na koma… Da gudu ban damu da ko masu gadin zasu ganni su sake kamani ba. Ina zuwa saina nemi kofar shiga babban falon na tura kofa na shiga bayan nayi yan dube dube saina jiyo hayaniya awani daki. Hakan shi ya bani damar gane cewa shine dakin da nake nema.A ina kika jefar da jaririn? Ya sake tambayarta banyi wata-wata ba saina tura kofar na fada cikin dakin babu sallama. Gaba daya mutanen uku miji da mata dakuma ‘ya suka juyo a firgice suka dubeni kamar wani Aljani.Kayi hakuri alhaji da shigowata babu sallama.Nace dashi. Zuwa nayi na ceci ran ‘yarka domin ba sai ka dora wukar a makogoronta ba. Ga Jaririn nan bai yi nisa ba dazun nan tayi min kyauta dashi amatsayin kyakkyawan jaruminta na shekara.Nayi musu murmushin yake su kuma suka dubeni saroro kamar wadanda suke tunanin na tabu. Na ajiye akwatin agabansu sannan nace.Jaririnta yana cikin nan yana barci ni zan koma Alhaji saidai kuma don Allah kayiwa masu gadin nan magana domin su Barawo suka kamani jiya da daddare adakin injin dake baku wuta na kwana. Allah ne ma yasa zan raba wannan rikici shiyasa na fito..Karya yake Wallahi baba shine ya sace jaririn wallahi shi ya sace min fadila tace.Yi min shiru munafuka mutumin ya buga mata tsawa na dubeta nayi murmushi sannan na lalubi aljihuna na dauko wasikar datayi min na mikawa mutumin nace.Duba min nan Alhaji shin wannan rubutuna ne ko nata? Ni sauri nakeyi domin muna da fim din da zamu fara idan an jima. Idan kuma kana bukatar karin bayani to saurareni da kyau.Mutumin ya amshi wasikar daga hannuna nikuma saina dubi Fadila itama ta dubeni nayi mata murmushi nace.Kadan ya rage ki kai labari yan mata to saidai kuma kyautar da kikayi min tayi girma dayawa. In banda abinci ina ke ina yi min kyautar Jariri? Ai tayi min yawa ina laifin ma ki bani KyautarKWALBAR TURARE KO FULAWAAdaidai nan naji sautin sawun masu gadin suna ta guje guje atsakar gidan.Lafiya meye haka? Mutumin yace yana dubana nayi masa murmushi nace dashikada ka damu masu gadinka ne suke nemana.Fadila ta daga kai idanunta cike da kwalla tace.HILAL nace Na’am FADILATace don Allah ka yafe ni. Na dubeta na tsawon dakiku sainaji tausayinta ya kamani saina dubeta da tattausan murmushi nace.Na yafe miki Fadila saiki nemi kuma gafara agurin Ubangijinki dakuma mahaifinki.Fadila ta fashe da kuka.Adaidai lokacin ne masu gadin suka kwankwasa kofa.Ku shigo nace dasu.Waya saka? Mutumin yace dani na dubeshi nayi masa murmushin ko in kula..HUDU 4.Kusan minti guda muka share tsaye muna duban kofar kodayake fadila bata kallon kowa sai ni.Kofar dakin ta fara budewa ahankali kamar iskace ke turota sannan sai kakkausar muryar kartin nan tace.Salamu Alaikum….Alhaji mu shigo ne?Mahaifiyar fadila wacce ke tsaye rike da tsantsa tana huci kamar kububuwa.Mamuda ne? Shigo kai kadai. Maigadin yace bakinsa na rawaGarsakeken katon ya shigo dakin cikin sanda yana zuwa saiya dubeni ya rusuna agaban maigidansa yace.Kayi hakuri don Allah Alhaji Wallahi adakin injin bada wuta muka sashi ya gudo.Bari inyi waje dashi na hada shi da yan sanda. Yana gama fadi saiya yunkuro DAMKE NI………… .17Yana Tafe Anjima Insha Allahu Zan Biya Bashin jiya I banyi ba saboda balaguron da mukayi(13:00, 1/24/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-17.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Yana gama fada ya yunkro zai Damkeni….Uhm Uhm mamuda kada ka taba shi.Maigidan yace cikin karaji. Mamuda yayi cak kamar ruwa ya cinye shi.Alhaji barawo ne…Kada ka damu mamuda jeka waje kaci gaba da aikinka kawai.Toh yallabai katon yace cikin girmamawa lokaci guda kuma ya nufi kofa.Af mamuda… Maigidan ya kira sunansa katon ya juyo cikin sauri na lura duk a rude yake me yiwuwa tunda yake gadi agidan bai taba shiga wannan dakin ba.Wannan maganar daga kai sai mu ka.Kafadawa abokan aikina ma bana so ta wuce tsakaninku. Kakuma kawo min akwatin daya bari adakin injin wutar. Katon ya gyada kai cikin fahimta sannan saiya dubeni. Kallon dayayi min na iya nufin komai.Nayi masa murmushi cikin sanda ya juya kamar yadda ya shigo ya sulale daga dakin..Muka sake yin shiru na tsahon mintuna akaro na biyu mahaifin fadila na kallon tattausan kilishin dake dakin yayinda fadila ke kallon. Nikuwa idanuna na kallon mahaifiyar fadila wacce ta kurawa fadila idanu bata ko kiftawa. Azuciya na yarda da maganar mahaifin fadila dayace da mahaifiyarta tun farko itace ta bata fadila domin na lura da alamun damuwa karara a fuskarta dakuma kauna ga fadila yarta.Ku shiga daga ciki RASHIDA. Maigidan ya kira sunan matarsa akaro na farko. Nayi zaton zata hau masifa amma maimakon hakan saita dubi Fadila tace. Taho mu tafi. Fadila tayi min kallon gefe idanu tabi mahaifiyarta suka bi ta wata yar tsukakkiyar kofa suka shige ciki. Maigidan ya dubeni gamida sassauta yanayin dake fuskarsa yace.Zauna bawan Allah ya nuna min kujera araina sainaji na kaunace. Hakan shi yasa nayi biyayya na zauna batareda nayi jayayya ba. Ya danyi shiru gamida sakin wani tattausan tari kana sai ya dago kansa…Tun tana karama muke fama da ita kadarar yarinya ce ka ganta nan gashi da babu abinda ta rasa agidan nan na daga kayan alatu amma bata iya zama sai shegen yawo. Mahaifiyarta ce ta bata tun tana karama…. Yayi shiru akwai alamar takaici karara a fuskarsa. Na tausaya masa.Babu daman nayiwa yar cikina fada sai mahaifiyarta ta hauni da masifa. Haka kullum nake fama kwatsam ran nan sai muka fahimci yar banzar yarinyar tayi ciki mahaifiyarta tayita uzura min sai a zubar da cikin. Nikuma ina tuna mata yin hakan barna ce domin kisan kaine saimu bata goma biyar bata gyaru ba. Haka mukayi ta fama har zuwa ranar data haifu shine yanzu don tsabar rashin imani suka hada baki ita da mahaifiyarta suka kashe dan jaririn wata daya kawai da haihuwa….hawaye ya fara kwarara akan fuskarsa.Na yunkura akan kujerar cikin damuwa ni duk maganganun sun fara gundurata duk da dai basu shafeni ba ni abinda kawai nake so shine yabar ni na tafi dan na lura tuni har gari yafara haske. Duk da yake banga agogo ba ina kyautata tsammanin biyar na safe ta wuce. Fita fim dinsu Alhajiji ne araina.Alhaji…. Allah ya sawwake.. Nace dashi ina ganin in babu wani sauran abu to ni zan tafi alhaji domin kaga duk wannan abubuwan da kake fada bai kamata na sani ba domin sirrinku ne ku kadai bai shafe ni ba. Mutumin ya dago kai yana girgiza shi.Ya shafe ka bawan Allah. Awannan karon ni na dube shi cikin mamaki.Tayaya ya shafeni? Mutumin ya sunkuyar da kai na tsawon lokaci yana girgiza kai. Can saiya dago alamar damuwa a fuskarsa a fili. Ga mamakina sainaga ya mike tsaye ya nufo inda nake ya sunkuya akaina ya dafa kafadata yace.Bantaba neman alfarma agurin kowa ba tun da nake…. Amma yau zan fara. Abinda yace sai ya daga rudani.Ban fahimce ka ba. Ya daga girarsa sama kamar biri na lura karfin ikonsa da kwarjininsa na attajiri sun fara dawowa gare shi.Abinda nake nufi shine ina neman kayi min alfarma guda biyu bawan Allah.Ni kuwa zan saka ma da abinda baka taba zato ba. Numfashina ya dauke abinda ban taba zato ba? Indai ba kuskuren fahimtarsa nayi ba nasan abinda kalmar ke nufi muddin ta fito daga bakin ATTAJIRI.Wa…. Wacce alfarma kake so? Ya dubeni na tsawon lokaci kana yace.So nake ka rufa min asiri maganar jaririn nan ta zama daga kai samu don Allah na rokeka ka rufa min asiri domin idan ta fito fili nagama yawo… Kaga shekara mai zuwa nake son tsayawa takarar GWAMNA zuciyata ta harba tsakanin hakarkarina. Bakina na rawa nace dashi.Indai don wannan ne Alhaji kada ka damu in Allah yaso babu wanda zai kara jin ta abakina. Nayi tsammanin zai saki fuska cikin jin dadi amma sainaga haryanzu dai tana nan yadda take babu yabo babu fallasa.Sai kuma alfarma ta biyu bawan Allah yace. Lokaci guda kuma naga akwai alamar razana a fuskarsa.Fadi muji ranka ya dade. Nace dashi ina dada kwantar da murya domin kalaman dayayi ne zaiyi min abinda ban taba tsammani ba yasa zuciyata lissafe-lissafe,,,, na tuna da dimbin bashin da ake bina..Bawan Allaj me ye sunan?Sunana Hilal.Yawwa hilal.Alfarmar danake nema tanada nauyi amma kamar yanda nace dakai abaya zan saka ma. Ya danyi shiru sannan saiyace,Zaka iya hilal? Na dubeshi cikin mamaki nace to ai bansan me zanyi ba Alhaji.Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya daga kansa ya dubeni ido da ido yace.SO NAKE KA AURI ‘YA TA FADILA..************ ************** ************* *********.KU HUTA TUKUNNA SAI MUCI GABA.NA SADAUKAR DA WANNAN KASHI NA 17 GA DUK WAYANDA SUKA JE KADUNA TA’AZIYAR ABOKIN HULDA AWANNAN DANDALIN IBRAHIM TAREDA DUK WAYANDA SUKAYI TA BUGO WAYA SUNA MIKA TA’AZIYAR SU TA HANNUN MU DAKUMA MASU COMMENT A CIKIN POSTING DINA NA RASUWAR DA TAFIYA TA’AZIYAR ALLAH YAYI MANA RAHAMA DA RAHAMARSA BADON AIKIN MU BA(13:22, 1/27/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-18.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya..Ya dada saurarawa lokaci guda kuma saiya dago kansa ya dubeni ido da ido yace.SO NAKE KA AURI ‘YA TA FADILA..********* ******** ***********.Ba karamar girgiza nayi da kalamansa ba. Kaduwar danayi ita ta sani zaune nayi mutuwar tsohuwa na kasa cewa dashi komai domin bansan me zance dashi ba. Na auri fadila? Chab babbar magana.Yaya kayi shiru Hilal ko baka sonta ne? Na girgiza kaina cikin kaduwa.Bahaka bane Alhaji… Kaga dai yan sa’o’in da suka wuce na santa kuma…. Ya daga min hannu.Hilal basai ka fada ba nasan abinda kake tunani. Auren yarinyar banza kamar fadila ko?Yarinyar data yi cikin shege ko? Ya danyi shiru sannan yaci gaba.Abinda yasa na baka duk tarihinta abaya shine so nake ka aure ta da halinta. Kuma ko da yake baka dade da saninta ba kai kasan fadila kyakkyawa ce bata da wani aibu in ya wuce na dabi’unta na banza.Hilal inason ka sani cewa in dai kana sonta zaka aureta da halinta to zan saka maka da babban alheri domin tuntuni na gaji da zamanta agidan nan. Ganin sharrin dataso ta dora ma shi yasani tunanin babu wanda yadace ya aureta sai Kai.Na gama rudewa zuciyata sai dum dum dum takeyi duk abubuwan dake faruwa ji nake kamar amafarki.Mecece sana’ar ka hilal? Mutumin ya tambayeni hakan dayace shi ya sani dada gyara zama.Harkar shirin fim nakeyi… Nace dashi cikin gaggawa mutumin ya shafi kansa da tafin hannunsa na dama yace.Saurareni da kyau hilal zan baka lokaci kayi shawara zan kuma sami Fadila nayi mata maganar.Ya danyi shiru sannan yaci gaba. In dai zaka yarda zaka aureta da halinta nayi maka alkawarin zan sayo maka duk abubuwan da kake bukata na harkar shirin fim idan nafita kasashen ketare. Ko gobe ka amince kazo ka sameni ka fada min zan aika cikin sati guda a sayo maka duk abinda kake bukata inason kuma ka nemi gida mai girman gaske a ko ina ne zansa arugujeshi agina maka kamfanin fina finanka zan kuma zuba maka jarin naira Milliyan biyar kyauta. Na shiga uku nace cikin zuciyata. Milliyan biyar?.Alhaji zanyi shawara…. Abubuwan sunyi yawa akaro na farko sai ya saki wata tattausar dariya yace.Ai kadan ma ka gani ya mike tsaye sosai zo muje in rakaka. Jikina na rawa na bishi abaya.Ruwan saman ya tsaya cak. Tuni gari har yafara haske naji sa’ar da agogo ya buga karfe shida na safe. Muka bi ta wata yar kofar sai na ga mun bulla a filin ajiye motoci.Motovi bakwai ne ejere kusan duk sababbi ne akwai jeep guda biyu Lexux daya marsandi biyu da honda shudiya da ja. Ga mamakina sai naga ya tsaya ajikin motocin.Alokacin ne fa nayi masa kyakkyawan kallo dogo ne siriri fari mai gashi irin na buzaye yalo yako me yiwuwa bafilatani ne kokuma mutumin Mali. Allah masani. Sa’ar daya dubeni yayi dariya sainaga hakorinsa na sama guda daya a bantare..Zan baka sati guda kayi shawara hilal abinda ka yanke saika zo ka fada min ni da kaina zan sami iyayenka.A ina kake ne? Ya tambayeni hannunsa na dama akan rufin motar lexux.Anan unguwar nake can ciki nake (No 106)Af ashe ma makwabvina ne. Ya fadada murmushinsa ya laluba aljihun doguwar jallabiyar shudiya dake jikinsa ya dauko dan makullin mota sannan ya nufi shudiyar motar honda.Alha….. Alhaji bama sai…. Ka bari kawai saina karasa ma akasa. Murmushinsa ya fadada.Uhm hilal kenan kaifa nace dakai yanzu ka dan ma ka gani. Ungo rike wannan. Ya miko min dan makullin mota ya nuna shudiyar motar da baki yace.Gata nan nabaka kyauta. Wannan kyautar bata cikin wancan yarjejeniyar tamu koda baka amince ba wannan motar dai taka ce… Na bude baki cikin kaduwa da mamaki chab. Dan saurayi hilal anya kuwa ba mafarki kake ba?Bansan irin godiyar da zanyi maka ba alhaji na gode Allah… Ya katse ni ta hanyar daga min hannunsa a fuska..Kada ka gode min Domin asirin dakayi alkawarin zaka rufa min yafi dahaka. Da’ace ciniki zamuyi.Ya dan saurara yana dan dukan saman motar da yan yatsunsa.Shikenan hilal sainaji daga gareka kana iya shiga motarka Allah yabamu alheri nakuma gode domin nine da godiya. Yana gama fadi saiya juya yayi ciki da sauri. Yakoma cikin gidan ta inda muka fito..Na dade anan saroro a rude domin abin kamar a mafarki awani bangare kuma na zuciyata sai cewa akayi dani wannan yaudarar ce irin na aljanu.Amma sa’ar dana bude hondar na lume acikin kujerar direba sai na gaskata faruwar dukkan al’amarin.Ada na dauka dana shiga motar zan ga ta bace saina tsinci kaina kwance akan tsohon gadona. Amma tabbas ko shakka babu duk abinda nagani tun daga dare har zuwa wayewar gari gaskiyane babu zancen aikin aljanu KAMAR A FIM..Nayiwa motar key na tashi sannan na fara tukata ahankali na nufi kofar gidan azuciyata nace Allah mai yadda yaso yan sa’o’i kadan nine ke yawo da mataccen jariri ina neman inda zan jefar dashi sannan lokaci guda kuma na tsinci kaina amatsayin barawo sai gashi akarshe cikin ikon Rabbana motovina da bashi ya cinye daya ta dawo daga cikinsu.Koda na fara tuka motar sai na juyo da nufin na yiwa ginin gidan kallon karshe gabana yayi RAS. Sa’ar dana hangi……AKWAI CIGABAN ANJIMA IDAN KUNA SO(13:24, 1/27/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-19.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Gabana ya fadi ras sa’ar dana hangi FADILA tsaye agindin taga tana daga min hannu ba ganin nata ne yasa zuciyata ninkaya ba sai tunanin cewa ayanzu abinda ke tsakanina da zama miloniya shine kawai na yarda zan aureta. LAURIYYA ta fado min arai.Ga koshi ga kwanan yunwa nace araina.Koda masu gadin suka hangoni tafe sai sukayi sauri suka bude min kofa atunaninsu ubangidansu ne koda suka fahimci nine sai suka bi ni da kallo bakunansu a bude cikin kaduwa. Dankareren katon daya kamoni amatsayin barawo idanunsa suka firfito cikin kaduwa kamar idanun kwado. Na daga masa hannu harda murmushi na take sabuwar motata abina na nufi gida..********** ********* *********.Tun daga nesa na hangesu tsaye akofar gidana motoci biyu da mutane biyar kowannensu nata waige waige suna ta duban hanya akwai alamar damuwa a fuskokinsu.Nayi fakin da dalleliyar hondar adaf dasu ina ganin alhajiji ta cikin gilashin motar yana duban agogo baiko damu daya kalli motar data tsaya afad dasu ba domin nasan babu wanda acikinsu yake tsammanin nine na bude kofar motar ahankali.Sannunku da zuwa furodusa. Nace dasu da faffadan murmushi. Duk su biyar din suka juyo acikin mamaki ganin nine sai fuskokinsu suka washe.Dan Banza daga ina a ina ka kwana? Tun dazu karfe biyar da rabi muke nan muna jiranka duk sauran yan wasan sunyi gaba kai kawai ake jira na dubeshi bayana jingine da motar ina karkada dan makulli.Kun aika gidan kawuna ne nemana? Na tambayesu gabana na faduwa.A’a bamu aika ba daman USMAN ne ma yace mu aika nikuwa nasan da wahala in kana ciki. Nayi ajiyar zuciya da sun aika gidan kawuna nemana da sun janyo min jaf’i.Bari in shiga gida in dan wasa ruwa sai mu tafi ko? Usman dake ta kallona tun zuwana yasaka magana saboda kullewa sai kawai safa da marwa yake.Kaga malam tun dazu da muke jiranka fa anan sai zamuyi ta jira har rana tayi mana dubi fa karfe shida da rabi. Na fashe da dariya.Dubi rigata fa usman ka gani gaba dayansu suka zubo min idanu sabodar tsabar kaguwa da sukayi basu ko kula da yanayin da rigar ruwan dake jikina take ba.Me ya sami rigarka haka naga duk a yayyage… A’a kaima ai duk a jike kake da chabi. Duk jikinka tun kafin suyi tambayar nagama tsara amsar da zan basu cikin zuciyata.Ai jiya muna rabuwa dakai lokacin daka bar mu da Lauriyya sai wasu suka daukeni muka tafi daukar wani fim. Da Allah da Annabi suka janyeni domin wai jarumin da sukayi niyyar fim din dashi baya gari kuma daukar da zasuyi suna bukatar ruwan sama. Shiyasa suka takura sai mun tafi acan na kwana. Kai jiya munyi fim da wuya. Don nasha dukan ruwa….To indararo…. Don Allah alhajiji barshi yaje ya shirya yafito mu tafi inka biye tashi sai yayita zuba kenan daga nan har azahar. Kasan ba gajiya yake da magana ba…. Usman yace cikin fada. Na dube shi nayi masa gwalo… Sannan da gudu gudu na shige cikin gidan..Bayan mintuna ashirin nafito nayi wanka na sanya kayana tsaf dani inka dauke zunzurutun tunanin dake raina. In banda na amsa musu tun jiya da ba zanje fim din ba milliyan biyar..Mu tafi nace dashi cikin sauri na nufi sabuwar motata.Hilal mota ka sake ne? Alhajiji ya tambaya na san gatse yake son yi min ya dauka arota nayi domin duk fadin duniyar fim babu inda labari bai watsu ba cewa taurarona ya daina haske.Daman ai chanji zanyi shine yasa na saida wadancan nan da sati guda ma za’a kawo min marsandi daga kwatona.Alhajiji ya dubeni cikin kaduwa akwai alamun hassada karara a fuskarsa. Hakanan kuma na lura da cewa kamar dai na barshi cikin wasi wasin gaskiyar abinda nafada. Ganin ya kasa magana saina ce dash.Ina lauriyya? Fuskarsa ta washe nan da nan. Ai ka fini kusa da ita..BIYAR 5.Ina ganinta tsaye sa’ar dana nufo ofishin ta raba hannuwanta ajikin kofar tana ta hange hange ko shakka banayi ni lauriyya take hange taga ta inda zan bullo to amma har sa’ar danayi fakin da sabuwar honda akofar foshin Allah bai nuna mata ni ba domin atsammaninta akasa zata ganni na bullo.Nayiwa kaina murmushi sa’ar dana fara rufe gilashin tagogin motar duk yadda akayi masu karbar bashine cike suke jirana. Don na lura da yanayin fuskar lauriyya hankalinta atashe yake. Babu mamaki ma duk hange hange da take kokari take taga ta inda zan bullo tayi min inkiya na gudu batareda masu karbat bashin dake ciki sun sani ba.Na dubi bakar jakar dake ajiye akan kujerar motar. Kudin da kamfanin Sinad produtions ne suka biyani na fim din danayi musu aranar. Naira dubu talatin da biye ne cif cif.Fim din da muka dauka aranar ya burge duk ma’aikatan amfanin musamman ma alhajiji. Domin ya yaba da kwazona. Da wannan ne ma tasa sa’ar da aka kammala saiya kirani yace.Hilal akwai sauran kusan gurare hudu da zakayi mana sati mai zuwa amma zan biyaka kudinka yanzun nan baki daya.Godiya nake furodusa. Nace dashi.A’a ai ni nake da godiya domin Wallahi Hilal na dauka ka gama mutuwa domin tuni ake yawo da labarin wai tauraronka ya daina haske sai yanzu ne na lura da cewa ashe duk hassada ce.Ya danyi shiru….TAKUN FARKO NA RIKICIN KENANKU BIYO NAZIR(13:27, 1/27/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-20.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Tuni ake yawo da labarin wai tauraron ka ya daina haske sai yanzu ne na lura cewa ashe duk hassada ce.Ya danyi shiru na yan dakiku sannan ya ci gaba.Dubu ashirin da takwas mukayi da kai ko?Na gyara kai sai yaceToh ga dubu talatin da biyar nan saura kyauta ce ta musamman daga kamfanin sinad production domin baka taba yi mana fim ba sai yau ina kuma dada tabbatar maka in Allah ya yarda wannan fim din sai ya dada haskaka ka domin mu muna da labarai masu kyau sauran kuwa duk shirme ne dahaka ai suke so su kashe ka.Har na baro gurin alhajiji bai daina Yabona ba da zan baro gurin ma har kyautar shadda mai tsada yadi goma yayi min Don haka sa’ar dana gama rufe gilasan motar sai na dauki kudin da jakar yadin shaddar na nufi kofar ofishina.Lauriyya bata tashi ganina ba sai dana zo daf da ita sai tace cikin rada.Lahh ta Ina ka biyo? Na kalli motar ina murmushi acikin wannan motar nazo lauriyya ta waiga bayanta a tsorace bayan ta tabbata babu mai ganina daga cikin ofishin saita kifta min idanu akan na guduWanene aciki? Na tambaye ta a tausashe.Emeka ne tun safe yake nan har yafara fada yana cewa yau ko zai kwana nan sai ya same ka in kuwa bai ganka ba toh gobe da yan sanda zai zo lauriyya ta dada waigawa tana dubana.Mu shiga daga ciki kada ki damu ai yau a shirye nake da zuwansa hakan dana ce shiyasa lauriyya ta kalli jakar ledar dake hannuna nan da nan sainaga fuskarta ta washe cikin mutanen murmushi ta matso inda jakar take ta karbi jakankunan guda biyu daya ta kudi daya kuma ta shadda.Har naji dan dadi Wallahi Hilal.Tun dazu gabana ke ta faduwa Wallahi bana son naga kana ta guje guje akan bashi. Allah sarki lauriyya nace cikin zuciyata irin wannan kulawa tata ita take dada rura wutar begen ta cikin zuciyata. A da can ban dauketa a komai ba amma a Yan kwanakin nan dana shiga masifa lauriyya ba karamin tallafi bace agare ni.Tana gaba ina binta Abaya har muka shiga cikin ofishin.Hello Emeka barka da zuwa ya juyo firgigit kamar an tsikare shi da kibiya.Kada ka karya min kujera a banza da wacce kazo naji ance kusan kullum sai kazo nemana ko? Emeka ya Harareni.Ai kafi kowa sanin abunda yakawo ni tun yaushe ne alkawarin cikon kudin kaset din mu ya cika? Kasa sai kashe kudin mota Nakeyi a banza duk ribar ta tafi ga masu mashin da mota.Huta da nunfashin ka kada hauhawar jini ta hau ka a banza. Nace dashi ina murmushi Lauriyya ta ajiye kullin jakankunan daga can bayan teburina sannan ta fice cikin sauri ta koma can dakin karbar baki.Nawa ne cikon kudin naka? Emeka yabata rai dubu ashirin da biyar.Na bude baki cikin mamaki kai kace da man can bansan yawan kudin ba.Dubu ashirin da biyar? Ashe dai kudin naka Emeka da yawa. Ya Harare ni.Kaga Hilal ni kada ka bata min lokaci in banda lalacewar ka nawa ne dubu ashirin da biyar agurin ka. Na dube shi gamida girgiza kai.Sanin da kayi min yanzu abubuwa ne sai a hankali. Ina gama fadin haka saina sunkuya kasan teburina na zaro naira dubu goma sha biyar na Riga nasan teburin yakare Emeka bazai ga daga inda nake zaro kudin baNawa ne nan? Emeka ya Kalleni fuska a yatsine sa’ar daya ga kudin basu cika ba.Nawa ka gani?Dubu goma sha biyar.To ka godewa Allah daka sami wannan kayi min hakurin dubu goma sai bayan sati guda.Tsawon lokaci Emeka na nan zaune yayi jim kamar ruwa ya cinye shi can saiya nisa yace ba jiran sati guda ne aiki ba cika alkawarin kaKada ka damu zama sami cikon kudin ka.A haka na lallaba shi muka rabu a zuciyata nace shashasha baisan ba a yanzu tsakanina da miloniya kalma daya ce tak kawai..Bayan na raka Emeka saina dawo kan kujerata na zauna sannan sannu ahankali kamar a hoton majigi sai abubuwan da suka faru adaren jiya har zuwa asuba suka fara dawowa garai garai a faifan zuciyata.Fadila ta zame min ALAKAKAI.hakika ga dama ta sameni nace cikin zuciyata na farko dai idan na amince zan auri Fadila saina rabu da duk bashi da ake Bina saina zama gagara gasa acikin duk kamfanonin shirya Fina finan hausa. Na dubi hannun rigata sainaga har yafara kodewa sainayi tsaki fitaccen jarumi kamata yana bukatar kayan sawa akalla kala dari biyu a talauce..Zan saya maka duk abin da kake bukata na harkar fim. Kalamansa suka Fado min a zuciya.To amma duk wannan da zarar na tuna da halayarta sai inji duk al’amarin Yafita daga raina hakika ina matukar son kudi a halin danake ciki a yanzu domin basussukan da ake Bina sun kusan miliyan guda to amma acan cikin zuciyata ni nasan auren fadila ba daidai bane na farko dai ba dole bane tace tana sona in kuma ma ta amince Dani ba itace irin uwar daya kyautatu na samarwa ‘ya’ yana ba domin ayanda ubanta ya bani labarin halin ta ko na aure ta zaiyi wuya in zata daina bin maza.A dacan kuma wani bangare na zuciyata nasan duk kwane kwanen da nake na abu daya ne hakika na kamu da son lauriyya tabbas in har zan auri wata mace a duniya toh lauriyya ya kamata na aura nace da kaina……..NIMA YARIMA NACE KA HAKURA DA FADILA KA AURO LAURIYYA TALAUCI YACI GABA DA SUBURBUDAR KA..NI KAM INA JAM’IYYAR FADILA DA BABANTA(13:28, 1/27/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-21.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Idan har zan auri mace a duniyar nan toh lauriyya ce nace da kaina..To sai dai fa ga fadila ga miliyan biyar. Wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina acan wani bangare na ofishin agogon bango ya fara buga kararrawa karfe biyar da rabi na yamma.Zuciyata tagama shiga rudani abubuwa uku agabana.LauriyyaMiliyan biyar da fadilaBiyu nafi son na mallaka daga ciki to Saidai kuma daya daga cikinsu yashiga tsakanina da guda daya tabbas in har Inason lauriyya to sai dai in hakura da miliyan biyar.In kuwa kudin nake so dole ne saina hada da Fadila. Allah kiyaye nace cikin zuciyata. A can wani bangare kuma wata zuciya sai cewa takeyi dani kai shashashan banza saikace ba wayayye ba ka manta kawai da lauriyya ka auri fadila ko ka rabu da talauci da wulakancin Abokan harkar ka na shirin fim yanzu in banda shirmen ka har akwai wani abun kunya da aibu da miliyan biyar bazata iya lullubewa ba?Hilal….. Naji muryar lauriyya ta daki dodon kunnena na dago kaina firgigit ina shafar fuskata da hannu.Tunanin me kake yi? Ta tambaya lokaci guda kuma ta matsa kusa dani ta zauna akan teburin dake gaban kujerar danake zaune kadan ya rage gwiwarta ta gogi tawa.Akwai alamun damuwa karara a fuskar ta.Uhm.. Bawani tunani nake ba gajiya kawai nayi lauriyya ta zuba min idanu na tsawon lokaci na lura karyar dana shirya bata samu matsugunni ba.Mintunan ka ashirin fa kenan kana zaune cikin ofishin nan kai kadai kuma kace ba tunani kake ba? Sai fa dana kira sunan ka har sau hudu kafin kaji ni… Ban amsa mata ba dan banida abin cewa Gaskiyar ta tabbas tunani nake.Lauriyya ta ci gaba da wasa da Biron dake hannun ta tana kida dashi a tausashe akan teburin.Da wata shawara nazo da ita Hilal… Kokuma ince neman alfarma. Nan da nan na juya na kalle ta cikin mamaki sai a lokacin ne na lura ashe akwai jaka rataye a kafadarta.Ina zaki tafi ne naga kin dauko jaka? Lauriyya ta girgiza kai.Babu inda zani muka sake yin shiru.Ni Nafara magana. Wacce shawara ce…. Kokuma ince wacce alfarma kike nema? Na tambaye ta zuciyata na harbawa abin na da rudarwa. Yan sa’o’i kadan fa kenan da attajirin ya nemi alfarmar na Auri ‘yarsa to ko itama alfarmar na aure ta zata nema?. Hilal nasan ana binka basusuka dayawa wadanda na tabbata bazaka iya biya ba a kwana kusa.Lauriyya ta dago kanta ta dube ni sainaga kwalla ta taru cikin idanun ta.SHI Yasa nazo neman alfarma. Alfarmar itace zanyi Maka kyauta ta musamman da wani abu wanda zai taimaka maka ka rage mafi yawan bashi da ake binka.Idan na baka so nake ka karɓa kada ka juya hannun kyauta baya shine kawai alfarmar….. Wani abu mai kamar gare gare yafara zaryar cikin kwakwalwata.Me kike son ki bani? Na tambaye ta a iya tunanina lauriyya bata da wani abu da zai iya biyan koda rabin bashin da ake Bina.Jikinta na rawa ta sauke yar madaidaiciyar jakar dake makale a kafadarta ta dorata akan bencin dake gabana sannan saita daga jakar sama ta zazzage abubuwan dake ciki akan teburin. Alokacin sa al’amarin ke faruwa duhu ya gauraye dakin domin tuni har an fara kiran Sallar magariba kuma bamu kunna kwan lantarkin dake cikin ofishin ba. Amma duk da hakanan sai kyalkyalin abubuwan ya haskake dakin sarkokine yan kunnaye da sauran tarkacen kayan karau na kwalliyar mata duk dayake bansan darajar su ba amma nasan sunada tsadar gaske bakina na rawa na girgiza kai.Lauriyya…. Baza ta yiwu ba bazan iya raba ki da kayanki ba… Kuma ina kika same su ban taba ganinsu ajikin ki ba dan abin da kike samu kuwa a kamfanin nan bai isa ko iya tarawa kike balle har ya sayi wannan ba. Lauriyya ta matso gareni ta dafa kafadata tace.Kayiwa Allah Hilal kayiwa Annabi ka karɓa tunda nake ban taba neman alfarma agurinka ba sai wannan idan kaki karɓa ka gama bata min rai ka konan zuciya.Toh amma dai lauriyya bai kyautu ba ace in har ni ban yi miki ba ke ki….. Ta katse ni ta hanyar daga hannayen ta.Kada ma kafara wannan zancen Hilal tunda nazo garin nan wake wahala dani in ba kai ba Kaine uwata Kaine ubana Kaine abin kaunata ka kadai ne ka iya sani dariya har cikin zuciyata. Ta danyi shiru tana kokarin share hawaye.Farin cikin ka shine farin ciki na tunda nazo garin nan baka taba sanin tarihina ba baka kuma takura min saina fada maka sirrina ba amma kake taimaka min iya karfin ka yau juyi nane na taimake ka don Allah kwashe su Hilal ko a kasuwar barayi ka sayar dasu akalla zasu kai dubu dari shida. Ta dafa hannuna ta kankame.Kaji Hilal don Allah kwashe su Narasa abin da zance da ita. Wata zuciyar nacewa dani kada ka yarda ta rudeka dubu dari shida basu kai miliyan biyar ba.Karkari dai su biya ma bashin amma zata kare babu komai a hannun kaNayi fatali da kururuwar zuciyar. Hakika abunda lauriyya tayi min bazan taba mantawa da ita ba har iya rayuwata nasan cewa a yadda take da Matsalar ta sa komai tabani kadarar ta cancak ta makudan kudi zata iya bani naira miliyan dari inda ita tana da shi.Hilal… Hilal kayi magana mana ka zura min idanu in kuma banida matsayin da zan nemi alfarma kayi min saika fada na kwashe kayana na tafi.Kada kice haka lauriyya ki kuma daina cewa alfarma kike nema ai nine kika yiwa alfarmar bakisan wani abu ba lauriyya nace da ita ina duban ta ido da ido.DUK duniya a yanzu banida wadda tafiki in babu ke lauriyya bansan inda zan sa kaina ba kece garkuwa ta mai tallafa min na yarda zan karɓa amma ki ajiye min su agurin ki daga nan zuwa sati guda kawai.Lauriyya ta dada kankame hannuna saita fashe da wani tattausan KUKA.Ban taba farin ciki irin na yau ba Hilal kuma…..Kwankwasa kofar da aka yi shine ya katseta nan da nan ta Mike tsaye cikin sauri ta share hawayen dake idanun ta muka dubi kofar lokaci guda aka dada Kwankwasawa.Bari in je in gano tace dani a tausashe. Na gyada mata kai sannan nayi sauri na boye sauran kudin dubu ashirin da suka rage me yiwuwa wani mai karbar bashin ne nace cikin Raina.Bata dade da fita ba sai ga lauriyya ta dawo ta tsaya gabana ta rike tsantsa akwai alamun damuwa a fuskarta.Wata ce wai take son ganin Ka nayi ajiyar zuciya nasan aduk masu Bina bashi babu mace ko daya.Kice da ita ta shigo nace da ita… Ina Nan zaune sai Naji motsi ina daga kaina sainagan ta tsaye agabana. Nan da nan dakin ya hade da kamshi doguwa ce sanye da doguwar riga ruwan Hoda kanta lullube dan kyalle irin launin rigar. Baba iya ganin fuskar ta Sosai domin haryanzu ban kunna kwan lantarkin dad ofishin ba.Sannun ki da zuwa malama ga mamakina sainaga ta matso ta zauna a bakin teburina daidai da inda Lauriyya ta zauna.A’a MALAMA ga kujera nan koma can ki zauna mana ta fashe da dariya cikin wata zazzakar murya.Hilal Wallahi kabani mamaki daka kasa gane ni.Ko na kara kyau ne? Naji gabana ya fadi rasss nan da nan sai ta girgiza kanta lullubin dake kanta yafado kan kafadarta siraran gashin ta suka bayyana suna sheki.Me yiwuwa kafi gane ni ahaka ko haryanzu baka Gane ni ba JARUMIN JARUMAI.Ta sake fashewa da dariya.NICE FA FADILA…….SHIDA 6 Loading……… .ALAKAKAI-22 Loading……. .KAI ANYA KUWA NIMA BA JAM’IYAR LAURIYYA ZAN KOMA BA(13:30, 1/27/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-22.(m)Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Me yiwuwa kafi ganeni ahaka ko haryanzu baka ganeni ba JARUNIN JARUMAI.Ta sake fashewa da dariya.NICE FA FADILA…..SHIDA 6.Fadila nakira sunan ta a sanyaye ko shakka babu ta sani bala’in kaduwa domin ban taba tsammanin zan sake ganin ta kwana kusa ba Hilal kenan manyan gari ta tashi daga kan teburin ta nufi kujerar dake fuskantar teburina ta zauna.Babu wuta a ofishin ne ko kafi son zama acikin duhu ne? Na muskuta akan kujerar na fara farfadowa daga cikin kaduwar danayi.Akwai….. Wuta ban kunna bane ga makunnar nan a bayan ki Fadila ta Mike tsaye ta lalubi makunnar lantarkin ta kunna dakin ya gauraye da haske numfashina ya dauke yawun bakina ya kafe. Nashiga uku nace cikin Zuciyata ashe kyakkyawace ta gaske kamar ta karanta abin da ke zuciyata saita kashe min idanu tace.BAKA dauka na kai haka ba ko? Kallon tsoro kayi min jiya ta matso kusa da bakin teburin tana tafiya tana girgiza jikinta da gangan kusan ko ina a jikinta rawa yake ta dafa kan teburin da hamnayen ta na dubi yan yatsunta sirara ne farare sol babu wani alamar tabo ko kwarzane atare dasu kamar jikin maciji.Tsawon lokaci tana tsaye akaina ta lullube ni da kamshin turare da man dake jikinta bansan sa’ar data dauke hannaye ta daga kan teburin ta Mike tsaye ba.Hilal yaya naga kayi shiru ko bakaji dadin zuwana bane? Nayi kokarin na tattare hankalina guri guda nace.Da wacce yau kika zo kuma? Wata sabuwar kyautar kika kawo Min?Fadila ta bata raiKA cika rikon magana wannan zancen ya fita daga bakin ka Hilal.Abinda ya wuce ya riga ya wuce jariri dai tuni an gama binne shi an riga an binne shi tun da safe. Tayi shiru tana tsuke baki muka sake yin shiru.Amma…. Dai kinsan ai abunda kikayi baki kyauta ba ko? Ko kina ganin daidai ne Abinda kikayi? Fadila ta dauke kai gefe guda.Da zamu bar zancen nan dai da zaifi.Don me yasa kika ce haka?Saboda tone tone bashida dadi. Na Mike tsaye daga kan kujerar na jingina da bang.Fadila Gaskiya al’amarin ki sun dame ni kin…. Ta katse ni.Hilal Inason ka sani cewa duk abin da nayi adaren jiya nayi ne saboda mahaifina in baka sani ba kasani duk da cewa kuwa mahaifiyata tafi kaunata da shagwaba ni duk duniya babu wanda nake kauna kamar sa.A zuciyata nace duk yadda akayi yarinyar nan tanada tabin hankali babu mamaki Hakan ne yasa ake kokarin bani auren ta.Nasan Abinda kake tunani banida hankali ko? Ta dubeni. Na girgiza kai.Kada ka boye min jarumi Hilal naga alamu a idanunka amma yana da kyau ka yi tambaya kafin ka yanke hukunci.Toh….. Amma saiki kashe jariri kice wai saboda kaunar mahaifin ki kikayi? Ta kada min idanu tace…….. Nan da wata bakwai mahaifina zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna babu abin da nake buri irin ace yau mahaifina ne Gwamnan garin nan. Tayi shiru tana rangaji agabana kamar bishiya.Ina Fatan yanzu ka fara fahimtar hoton da nake kokarin zana ma? Kaga Hilal ciki dai nariga nayi Munso mu zubar da cikin nida mahaifiyata tun yana ƙarami mahaifina ya hana lokacin Dana haihu sainaga in har na bari dan ya girma nagama kunyata mahaifina kuma idan zancen yafito Abokan hamayyar siyasar sa na iya yin amfani da damar su bata mahaifina.Amma kuma bakya ganin yanzun ma bata sauya sani ba tunda dai ai jama’a da dama sun sani kinada cikin shege?Jama’a kamar su wa? Ta tambaye ni gamida daga girar idanunta sama.In banda kai dakuma likitan mu da ya auna ni ya tabbatar ina da cikin duk duniya babu wanda yasan inada cikin kai ko wanda yayi min cikin baisan inada shi ba domin tin yana dan wata daya aka hanani fita ko ina aka sa masu gadina har sai dana haife dan.Kawaye na da Abokan Arziki idan sun zo ne mana sai ace dasu bana Kasar..Nayi shiru ina sauraron shashashan zancen ga mamakina sianaji duk da kyawunta nafara tsanarta ko kadan bata da kunya.Ina ganin idan babu sauran wani abu da zaki fada ni zan fita nayi sallah kinga har an idar sa sallah a masallaci nafara yar tafiya a cikin ofishin.Au harma korata kake yi? Ta bata fuska.Babu zancen kora kora in kina iyawa jirani nayi sallah sai muci gaba da hirar daga nan zuwa asuba.Muga abunda Allah zaiyi nasaki Murmushi nafara Jin dadin badakalar.Wai dan Allah da gaske kike yi baki kawo min kyautar komai ba? Ta kawo min duka cikin wasa na kauce.Ya ishe ka haka kaga bana so.Ta juya ta fara tafiya akwai alamun farin ciki a fuskar ta.Muje to ka rakani.Muka ratsa ta cikin dakin karbar baki.Ban iya yarda na kalli inda lauriyya ke zaune ba.Toh amma na lura zaune take ta kifa kanta akan teburin dake gabanta.Nayi tsammanin zata biyo bayan mu da man Ga al’ada duk bakon da ya zo tare da ita muke raka shi amma Sam Sam bata biyo mu ba tun kafin mu Gama fita na hangi katuwar marsandin tana kyalkyali acikin hasken farin kwan lantarkin daya haskaka kofar ofishin…….KAI NIFA NA RIKICE NA RASA WACCE ZAN GOYA WA BAYALAURIYYA KO FADILA ????(21:03, 1/30/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-23.(m) Nazir Adam SalihBaban Ahmad Da Adam.(c) Yarima Gangariya.Tana kyalkyali acikin hasken farin kwan lantarkin daya haskake kofar ofishina..Muka karasa gindin motar babu magana muna tafe kafada da kafada da muka isa gindin motar ta fuskanceniyaushe zaka zo? Tambayar tayi matukar girgizani.Ina kike nufi? Fadila ta dafe kirji cikin razana ta harareni a fusace.Au baka san zancen ba?Wane zance? Fadila ta girgiza kai tace shikenan tunda baka sani ba daman babane yace nazo na sameka amma tunda kace baka san komai ba shikenan. Tana gama fadi saita juya cikin fushi ta shige motar.Shashashan banza sakarai. Wata zuciya tafara yi min kururuwa idan ka bari ta tafi baka lallasheta ba kamar kayi sallama ne da miliyan biyar. Mafarkinka duk ya zama shirme.Fadila Fadila na kira sunanta cikin gaggawa ta sauke gilashin tagar motar na sunkuya nace.Kiyi hakuri dan Allah Fadila… Idan kin kula duk ba’a ahankalina nake ba a rude nake… Fadila ta dubeni ta tabe baki sannan tayi tsaki tace.Yi sauri ka koma gurinta tana can tana kukan kishi kada ta mutu… Gabana yayi das das. Wa kenane kike nufi? Na tambaya baki bude.Kafini saninta… Wancan baiwar taka dake jiranka a ofis. Tasawa motarta giya ta firzgeta aguje tabarni anan tsaye ina hangen kurarta.SAI WATA RANA MILIYAN BIYAR.Nace da kaina kamar na fashe da kuka koda na nufi ofishina sainaji wani zazzafan zazzabi yana neman rufeni..*********** ****** **********.Har sa’ar dana dawo dakin karbar bakin lauriyya tana nan kamar yadda nabarta kanta kife akan teburina na tsaya akanta.Lauriyya na kira sunanta akwai alamar rawa a muryata. Ta dago kai ta kalleni da wani fatalwan murmushi. Ba sai an fada ba duk wanda ya kalli idanunta yasan taci uban kuka duk kuwa da matukar kokarin datayi wajen share hawaye.Har ta tafi? Ta tambayeni hannunta rungume a kirjinta.Ta…. Tafi na fadi muryata na sarkewa.Mukayi shiru babu wanda ya sake cewa kala har aka kira sallar isha. Sai lauriyya ta mike ta sakala jakarta akafada.Hilal zan tafi gida… Na danyi shiru na farko saikuma nace Gida? Haka da wurwuri… Ta danyi tsaki sai gabana yafadi tunda nake da ita bata tabayin tsaki a gabana ba.Banajin dadi ne… Shiyasa nake son tafiya yau da wuri muka dan sake shiru na tsawon lokaci.Dan dakata to ina da sauran magana dake.. Ta hade fuska.Maganar me kuma zakayi min na dauka mun gama komai tun dazu? Ga kayan ai acikin jakata. Ta nuna jakar da hannunta.Duk lokacin daka shirya saika karba in kuma kana so ma yanzu sainaba ajiye ce agurina.Akwai sauran magana lauriyya… A ina kika samosu? Naji ta rike numfashi cikin kaduwa.Hilal me kake nufi da a ina na samo su kana nufin kace ni barauniya ce?Dan girman Allah kada ki bata zancen nan lauriyya ni bahaka nake nufi ba. Ki tuna fa kyauta zakiyimin da kararki ta makudan kudi a iya sanina kuma ban taba ganinki dasu ba kinga kuwa ashe banida laifi danna tambaya.Ta sunkuyar dakai cikin takaici. Tambayar ta kona mata rai ta daga kai.Tunda ka dage saika san inda na samesu bari yo na fada ma MIJINA NE ya saya min su.Mijinki? Ta gyada kai.Kwarai kuwa baka san na taba aure ba kafin nazo nan garin ba? Nayi ajiyar zuciya.Ina fatan yanzu ka gamsu. Lauriyya tace sannan ta matso daf dani kusa dani har takai ina iya jinhucinta akan fuskata.ITACE TA BATA MAKA RAI ?Na kalleta a rude.Wa..wa kenan kike nufi? Lauriyya ta dafa kafadata tace.Nasan daman kafi karfina Hilal na dade ina kwana ina tashi da fargabar cewa watarana sai anzo har ofishin nan an kwace min kai!Gabana yafadi nayi sauri na dauke hannunta daga kan kafadata.Lauriyya nataba fada miki kuwa wata kalma kwaya daya?Wacce kalma ce wannan? Ga mamakina sai naji ina mai kunyar hada idanu da ita.Adacan Lauriyya ban dauki amatsayin komai ba fiyeda kawai sakatariya na. Nayi sa’a danaga ta kura min idanu kamar zata hadiyeni.Yau lauriyya na wayi gari duk fadin duniya babu wata ‘ya mace datafiki agurina. Lauriyya ta dada matsowa daf dani.Na Gode Allah Hilal tun ranar dana dora idanuna akanka nake kaunarka.Zan baki wani labari lauriyya ki saurareni da kunnen basira lauriyya ta dubeni dakyau. Labarin me kuma? Nakama hannunta muka wuce cikin ofishina. Wannan shine karo na farko dana taaba yi mata haka. Na zaunar da lauriyya akusa dani.Lauriyya jiya da daddare wasu al’amura masu kama da shirin fim sun faru akaina. Abubuwan na da matukar rikirtarwa to ahaka dai ni gama yanke shawara azcuiayata cewa ni dai KE NA ZABA LAURIYYA.Dan Amina Muhammadu.Lauriyya tace tana tafa hannu. Ban fahimce ka ba hilal….. Me kake fadi ne kace ni ka zaba ban gane ba.Me yiwuwa idan nabaki labarin ki fahimce ni ke dai saurara da kyau..Nafara zubo mata labarin al’amarun kyautar jaririn da akayi min tun daga farko har zuwa kan zuwan fadila ofis.Karfe tara saura kwata nagama bata labarin.Lauriyya tayi shiru bata ko motsi kamar ruwa ya cinyeta ga mamakina akaro na farko sainaji da gama fada mata labarin damuwa zuciyata ta ragu.Lauriyya ta mike tsaye tabar kusa dani sannan tafara safa da marwa….(06:34, 1/31/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-24.(m)Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Lauriyya ta Mike tsaye tabar kusa dani sannan saita fara safa da marwa acikin ofishin akwai wani yanayi dake fuskanta daya hanani na katse mata hanzari don haka sainayi zamana ina jiran naji ta inda zata bullo inada kwarin gwiwar cewa indai har akwai mafita to lauriyya ce zata kawota na yarda da kwakwalwarta akan hakan..Hilal! Nayi firgigit sa’ar danaji ta kira sunana.Mecece shawarar Ki akai. Lauriyya ta dawo kusa dani ta zauna sannan taceZancen gaskiya Hilal indai kabar miliyan biyar ta wuce ka kayi shashanci. Na zabura cikin kaduwa.Me kike nufi? Lauriyya tayi dariya miliyan biyar tafi karfin wasa Hilal Amatsayina na mai kaunarka bazan so ka rasa naira miliyan biyar saboda ni ba.Tunanina ya kure na rasa abin da zance da ita.Ni shawara ta ta Hilal kaje ka aure ta.Lauriyya meke damunki ne ta girgiza kai.Lafiya ta Kalau babu abin da ke damuna ni har kullum babu abin da ke faranta min rai irin cigaban kaDa miliyan biyar kana iya wa duk Abokan hamayyar nisa.Lauriyya kibar zancen nan tuni nagama fada miki in har akwai wacce zan aura yanzu a duniya to kece. Idan kuwa na Auri fadila bansan da idon zan Kalle ki ba ta daga kai muka hada idanu tace.Ko?Kwarai kuwa na Mike tsaye.Ko sallah banyi ba yakamata naje nayi sallah lauriyya ta biyo ni Abaya.Kayi tunani Hilal tunda dai sati daya suka baka amma ni ina ganin gara ka aure ta Hilal.Ban juyo na kalleta ba sa’ar da take maganar domin na lura ita kanta akwai wani sirri datake kokarin boyewa daga gareni. Wata zuciyar ta ci gaba da yi min kururuwa. Duk kabi ka zama wawa Hilal haka kawai kabari matan zamani suna neman su zauta ka.Daya kasan yadda take dayar kuwa baka ma san koda tarihin taba.Zan tafi gida Hilal sai goben lauriyya tace.Mamakin abin da yasa ta firgicewa haka take sauri sauri ta tafi gida.Toh shikenan sai goben kenan. Ahaka muka rabu da lauriyya ta tsallake bakin titi tana sauri sauri na bita da kallo cikin mamaki meke faruwa ne? Yanzun nan fa take nuna tsananin kishin ta a gareni take nuna cewa duk duniya ni take kauna lokaci guda kuma tana cewa naje na Auri fadila… Tabbas akwai wani abu murdadde acikin al’amarin.. Bi a hankali dan samari kada ka bari matan zamani su haukata ka a banza nace da kaina…..*********** *********** *************.Karfe tara da rabi agogon mota ta ya nuna nayi kokari tun sa’ar dana baro ofis na fitar da komai daga cikin zuciyata abunda nafi kauna yanzu a duniya shine isashshen barci domin rabona da barci sa’o’i kusan ashirin da hudu kenan.Nayi fakin da motar a kofar gidana na rufe gilasan sannan na fito zan kulle kofar kenan sai Naji kamar motsi abayana na juya cikin sauri sainaga wata sura ta fito daga cikin duhu ta nufo inda nake.Tun dazun nake jiran zuwan ka JARUMIN JARUMAI..BAKWAI 7.Da wacce kuma kika zo? Na tambayi fadila lokaci guda kuma na jingina ajikin motar barcin dake idanuna ya zama tarihi a halin yanzu domin tuni nagama fahimtar fadila ta zama kamar tauraruwa mai wutsiya ganin ki ba.Nazo maka ne da wani babban labari domin dazun na fahimci wani gani gani kake yi min ka daukeni kamar wata yar iska fadila tace tana tabe baki.Fadila abin har Yakai da bakaken maganganu.Yama wuce da haka Hilal duk abin da nake yi ni ba mahaukaciya bace nasan abunda Nakeyi tayi shiru tana maida numfashiBabana yayi min bayanin duk abubuwan da kuka tattauna dashi jiya banyi mamaki ba sa’ar da nazo ofishin ka naga kana neman ka wulakanta ni ashe tallata maka ni akayi.Cool down fadila nace da ita rabi da turanci rabi hausa. Anki ayi cool down din da asama nake ta ci gaba da huci agabana. Ka dubi da kyau Hilal tun daga sama har kasa kaga makusa ajikina? Maganganun ta sun fara bani haushi dan haka sainace. Azahiri dai kam ko shakka babu baki da makusa amma a badini kuma fa…Ta yamutse fuska.Abar kaza cikin gashinta Hilal a kare wanne ne ba bare ba ku yanzu yan fim har kuna da bakin da zaku bude kuce wa wani dan iska? Kai yanzun nan Hilal kana tsammanin kai waliyi ne? Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim(06:34, 1/31/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-25.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Yan mata nawa kuka bata a harkar shirin fim?Kada kice haka fadila ba duka aka taru aka zama daya ba.Fadila ta zabura cikin fushi kamar zata hau ni da dukaKasani Hilal na kasance daga cikin dubban yan matan da Allah ya jaraba da son karance karance da kallon Fina finan hausa wannan ne ma tasa duk inda akayi wani gangami na yan shirin fim sainaje gurin ba don komai ba sai kawai don na ganku Abin da baka sani ba shine ba dade da sanin ka abin da yasa ban taba tunkarar ka nayi ma magana ba shine girman kanka musamman ma a lokacin da kake kan ganiyar tashen ka….. Na katse ta.Fadila duk naji kiyi hakuri don Allah kibar zancen nan mu rabu lafiya Wallahi barci ne a idanuna kamar na fadi nakeji. Tsaho lokaci tana nan tsaye tana ta kokarin dannan bakar zuciyar ta dake ingizota akan dokan danasani.Dole ne na fada maka tarihina Hilal dole ne na fada maka.Domin ka daukeni wata tambadaddiyar yar iska bayan kuma dan uwan ku ne dan shirin fim ya batani…… Bazan taba yafe masa ba har abada tafara kuka.Aure Kam ko zan rasa miji a duniya bazan aure ka ba domin nasan har abada bazaka taba yarda dani ba.Natafi Hilal ka huta lafiya…. Ta juya aguje ta nufi bayan gidan.Na bita da gudu gudu adaidai lokacin da take kokarin shigewa mota.Fadila….. Dan Allah tsaya ki saurare ni ta tsaya cak kafarta daya acikin motar daya kuma awaje.Babu wani abu kuma da zakace dani Hilal…. Me kake son fada? Zancen naira miliyan biyar?BAZAKA SAMI KO KWABO BA. tunda ka nuna min cewa kudin kafi so dani tayi tsaki agabana ta tsartar da yawu.Dubi idanun ka kiri kiri babu tsoro babu kunya.Kai yanzu har kana da bakin magana?Aure ne bazan aure ka ba tuni nafadawa mahaifina dazun bayan nabaro ofishin ka….. Jeka ka tsira da mota matsiyaci.Na yi taku biyu da niyyar kifa mata mari sai wata zuciyar tace dani..Uhm. Uhm dan samari yi hankali da tangaran.Fadila ta lura da niyya ta.Au dukana zakayi? To Bismillah zo doki nayi tsaye kamar gunki duk kwakwalwata a yamutse..Fadila ta shige motarta ta rufe kofar gararam sannan ta fizgi motar ta fice da gudu.Jikina na rawa na nufi kofar dakina na lalubi dan makullin dakin dake aljihuna sannan nafara kokarin bude kofar sannan ne to wata takarda ta Fado daga jikin kwadon.Na dubi takardar data Fado akan takalmina da farko na dauka shirme ce amma daga karshe sai zuciyata tace dani Kai duba dai…INA shiga dakin saina lalubo makunnar lantarkin na kunna lokaci guda kuma na bude takardar dan Sako ne kamar haka……HILAL.Me yiwuwa zaka so kasan wanda yayi min ciki zan fada Ma sunan sa domin abin yazama wa’azi a gareka ka kuma yi hankali kada abin da ya faru tsakanina dashi ya faru tsakanin ka da sakatariyar ka na lura ita tafi dacewa ka aura. Sannan wanda yayi min ciki sunan sa (ALHAJIJI)FADILA..************ ********** *************.Ban isa ofishina ba sai kusan karfe goma sha biyu na rana wannan ya samo asali ne sakamakon nannuyan barcin daya daukeni.Ahanya sa’ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suka faru a gareni tun daren jiya. A lokacin ne toh……….ME KUMA YAKE SHIRIN FARUWA DA KAI HILAL ?KA RASA MILIYAN BIYARKA RASA TSALELIYAR BUDURWA KAMAR FADILA.YANZU KUMA ME KAKE SHIRIN SAKE RASAWA?(06:35, 1/31/2018) +234 806 858 0203: ALAKAKAI-26.(m) Nazir Adam Salih.(c) Yarima Gangariya.Ahanya sa’ar dana nufi ofishina zuciyata cike take da tunane tunanen abubuwan da suke ta faruwa a gareni tun a daren jiya. Alokacin ne na yanke shawarar zuwa a ranar nasami mahaifin fadila mu gama kashe magana yanzu kam nagama saduda dacewa nayi sallama da zama miloniya tun da dai na tabbata fadila bazata aure ni ba.Haka ma yafi kwanciyar hankali akalla ka tsira da mota dan samari.Toh amma sa’ar da tunanin lauriyya ya Fado min duk sai Naji hankalina ya tashi bansan inane alkiblata ba. Abu daya dai dana dada tabbatarwa da zuciyata tun adaren jiya shine na share su baki daya daga cikin zuciyata domin ita kanta lauriyya na lura akwai wani abu na rashin gaskiya dake tattare da ita.Ina kokarin fahimtar ko wanne abu ne har har na isa ofishin.Nayi mamakin da ban ga lauriyya a kofar tana hange hangen ta inda zan bullo ba.Nasan ga al’ada ko goma na safe nakai banzo ofis ba zan Harare ta tana ta leke leke to ballantana kuma karfe goma sha biyu cikin gaggawa nayi fakin da motar na nufi ofishin cikin sauri gabana ya fadi sa’ar dana shiga gurin karbar bakin banga lauriyya ba nayi tsaye cak a tsakiyar dakin jikina Yabani cewa lallai ba lafiya ba.LAURIYYA. Nakira sunanta murya a sarkake shiru ta gaida kunnuwana to amma naji kamar motsin mutane acikin ofishina. Nayi taku biyu gaba da niyyar nashiga sai Naji motsin tafiya an nufo dakin saukar bakin.Sannu ahankali naji takun sawu taf taf taf har ta bayyana idonta sharkaf da hawaye tana ganina saita taho gareni ta fashe da kuka.Dan Allah Hilal ka yafe ni…. Ka yafe ni Hilal.Ta sake fashewa da kuka.Yi Shiru lauriyya menene kum? Kuma meke faruwa? Banyi mamakin jin muryata ko rawa batayi domin Daman tuni jikina Yabani cewa ba lafiya ba lauriyya taci gaba da kuka.KA yafe ni Hilal yau zamu rabu dakai……Bazan taba mantawa da abun dakayi min…. Ta sake fashewa da kuka iko sai Allah nace cikin zuciyata.Wai me ke faruwa ne lauriyya kin ki ki fada min komai sai…….. Maganar ta makale a fatar bakina sakamakon wani kwakkwauran motsi danaji acan cikin ofishina.Na juyo na dubi lauriyya nace.SU wanene aciki? Ta dubeni a tsorace ta kasa cewa komai adaidai lokacin ne to sauran mutanen dake ofishin suka fito nayi tsaye ina duban su cikin kaduwa.Mutanen su biyu ne daya namiji ne Kato mai doguwar kasumba yana sanye da shakwara da jamfa da wando na shudiyar shadda kai da ka ganshi kasan akwai kudi zai kai kimanin shekaru hamsin da biyu a duniya dayar kuma mace ce dattijuwa zatayi kimanin shekaru kusan hamsin. Kallo daya nayi nata na gane ta na fahimci ko wacece ita da lauriyya kamar an tsaga kara.Sannunka da kokari bawan Allah.Munji duk taimakon dakayi mata. Nayi saroro ina kallon su banida bakin magana matar taci gaba da cewa.Yau shekara uku kenan muna neman yar banzar yarinyar nan…. Kwana uku ka da daura mata aure ta gudo.Naji zuciyata ta harba akaro na farko saina kalli lauriyya nace…. KINA NUFIN KICE KINA DA AURE?Lauriyya ta fashe da kuka sannan ta nuna katon mutumin da dan yatsa tace cikin kuka… Ka ga mijina nan……. Wai wannan katon za’a aura min katon mutumin ya kamo kafadarta ya hankadata waje tsohuwar da nake tsammani mahaifiyata ce tabi su Abaya..Jikina na rawa na rufa musu baya tun kafin na karasa waje na hango wata mota daga can baya Kirar Toyota Coralla mutumin ya tura lauriyya aciki tana ta kuka tuni har yara sun fara taruwa suna kallon fim din. Cikin sauri na karasa gindin motar nace.Lauriyya….. Allah ya kiyaye kinji Allah taimake ki katon mutumin ya Harare ni alamun tsana karara suka bayyana a fuskar sa ban zarge shi ba ban kuma ga laifinsa ba shekara ta uku tare da matar sa nasan duk duniya babu wanda ya isa ya fitar dani daga zargin sa.Kaga malam ya isa Jeka kawai abin da kayi da ma ya isa.. Lauriyya ta yunkura acikin motar ta leko da kanta tace.Watarana zamu sake haduwa Hilal…. Nayi maka alkawari. Nagode Allah ya saka maka.Mutumin ya tashi motar sannan ya dubi Mahaifiyar lauriyya yace.GATA DAI YANZU AI MUN GANTA KIN YARDA DAI YANZU BA SAYAR DA ITA NAYI BA KO?Yana gama fadin haka sai ya sawa motar giya suka harba aguje.Koda suka tafi sai cincirindon yaran dake kallon diramar suka rufa musu baya aguje suna shewa me yiwuwa da yake sun saba ganin jaruman shirin fim na taruwa agurin sun dauko ko wani sabon fim din aka shirya musu..Kusan mintuna biyar ina nan tsaye sannan sai na juya na nufo cikin ofishina koda na shiga sai Naji shiru kamar makabarta zuciyata tayi kuna bakin ciki da takaici suka lullube Ni hakika rashin lauriyya kusa dani ba karamin rashi bane.Ba’a dade ba sai Naji kafafuna duk sunyi rauni kamar bazasu iya daukata ba dan haka sai na nufi kujerar da lauriyya take zama a tunani wai ko zata dauke min kewa na zauna a kai ina zama sai Naji duk kasala ta lullube ni dan haka saina dauki kafafuna na dora su akan teburin sannan na lumshe idanuna na fara tunanin matsayina a yanzu.TA LEKO TA KOMA. Nace da kaina babu Fadila na rasa lauriyya ga shi kuma nayi sallama da zama Miloniya.Ina Nan zauna sai nafara kiyashin kudaden da ake Bina bashi. Cikin zuciyata a iya sanina ana Bina kudi kusan dubu dari shida da hamsin wani zazzafan gumi yafara sartu akan goshina.Dole ne nasan duk yanda zanyi na biya su kudin su tun da dai wacce ke tarairayata da kwantar min da hankalin ma an dauke ta..Daga inda nake zaune ina iya hangen sabuwar motar da mahaifin fadila Yabani tana sheki acikin rana nasan banida wani zabi daya wuce na sayar da motar na biya mutane basussukan su zuciyata tayi kuna tuni labari ya ya fara yada duniyar fim cewa na sake shigowa gari domin duk cikin JARUMAI maza babu mai shiga motar da takai tawa a yanzu dan haka sayar da ita ba karamar faduwa bace.To amma banida zabi. Na lumshe idanuna sannan nace da kaina dan samari Hilal sayar da motar ka biya mutane bashin su ai zama lafiya yafi zama dan sarki ina yanke shawarar sai Naji nafara samun saukin rayuwa cikin zuciyata.Naji wani dadi ya lullube ni sa’ar dana tuna da cewa motar zatayi tsada idan na sayar da ita dole ne na samu rarar kudin da zanci gaba da juyawa acikin harkar fim.. Can kuma sai wani tunani ya Fado min nan da nan na zabura ai kuwa da zan maida duk abubuwan da suka faru akaina tun daga daren shekaran jiya zuwa yau fim. Ba karamar karbuwa zanyi ba murna ta cika ni sai nafara tunanin sunan da ya kamata na sa masa. Sai kuma tunanin wahalar dana sha kafin na jefar da JARIRIN nan tafado min tabbas ALAKAKAI zan Sawa fim din.Kwarai kuwa cikin zumudi saina tuma kafata da karfi akan teburin sannan ne to naji wani abu ya Fado daga karkashin teburin. Cikin sauri saina sunkuya na dauka.JAKA ne ya Fado.Yawun bakina ya kafe zuciyata tafara harbawa cikin sauri a kwance a tsakar dakin jakar lauriyya ce data kawo min adaren jiya dauke da sarkokin nan masu tsada jikina na rawa na bude jakar.Suna nan kamar yadda suke suna daukar idanu.. Lauriyya!! Nakira sunan ta cikin murna da farin ciki yanzu kam nasan bana bukatar saina sayar da motata dan biyan bashi..Jikina na rawa na Mike tsaye ni kadai kamar mahaukaci nafara juya jakar dake kyalkyali a hannuna kawai sai Naji na fashe da dariya sannan Nace da kaina…HILAL DAN DUNIYA ALLAH KE SON KA BA MUTANEN DUNIYAR FIM BA…KARSHE……Nazir Adam Salih (NAS)Download Alaqaqai Littafi Na Ɗaya Complete HausaNovel