Zuri’a Ɗaya Littafi Na Ɗaya Complete Hausa Novel
🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com*PAGE* *1*~*2* *Warning**Nayi litafin nan domin fad’akarwa da nishad’antar da massoya na,ban yarda a canza min litafi ba yin hakan kuskure ne, Kuma duk Wanda ya canza min wani Abu a novels na ban yafe ba, da fatan zaku kiyaye* *Ina gargad’i da babban murya, ko wace ce ta b’ata min novel na RAYUWAR NAJWA,ban yafe ba kuma Ina gargad’in ki kada ki sake yin min haka domin bazan wahala in tsara labari na inyi typing kizo ki b’ata min ba,har kina cire suna na to wallahi zan d’auki mataki, ko wace ce ke Ina gargad’in ki, ki fita a harkan novels na**Kwance* take akan kujera tayi tagumi da hannun ta tayi nisa a tunani, abin duniya ya ishe ta, Jin an tab’a tane yasa tayi firgigit ta dawo hayacin ta, d’agowa tayi sai taga mijinta ne, murmushi ya sakar mata tare da zama kusa da ita,Ya rik’e hannun ta yace”kyakyawar fuskar ki ya kanyi Muni a duk lokacin da kike cikin damuwa, Wanda damuwar ki yake jefa Ni cikin matsala ko Zaki iya fad’a min yanzu meke damun ki my wife?”Wasu hawaye ne suka zubo mata Nan ta rushe da kuka,cikin rud’ewa yace”Subhanallah please kiyi shiru ki fad’a min mene ne?”Cikin kuka tace”kasan matsala na meyasa zaka damu da tambaya na, ka fad’a min meyasa bazan Damu ba?”Sauke ajiyar zuciya yayi yace”wifey bana son kina saka damuwa a ranki har ciwo ya Kama min ke,Dan Allah kiyi hak’uri ki kwantar da hankalin ki”Cikin damuwa tace” sweety kana ganin zan bar damuwa ne, shekaru goma Sha biyu da yin auren mu amma ko b’arin ciki ban tab’a yi ba, meyasa bazan Damu ba, wallahi Ina son haihuwa”ta k’ara fashewa da kuka,A hankali ya fara Mata nasiha cike da k’aunar ta, har jikinta yayi sanyi, sannan ya samu ta daina kukan, daga nan ta tashi ta had’a Mai dinner,Washegari da safeKasancewar weekend ne, yau tana ta aiki sai ta zauna a parlour Dan ta huta, t.v ta kunna ta fara kallon news can taga ana nuno wani jariri cikin kwali sabuwar haihuwa, mahaifiyar ta Yar da shi bayan ta haifa,haka mutane suka dinga magana akai yanda zamani ya lalace,sai mace tayi cikin shege ta yar da abin da ta haifa,Ji tayi an rungume ta, tace”yauwa sweety zo kaga meke faruwa” zama yayi kusa da ita Yana kallon news d’in,can ya tashi ya kashe t.v yace”irin wannan abin Sam bai dace kina kallo ba, Dan wannan rashin imani ne mutum ya haihu ya jefar da abin daya haifa”Tace”gaskiya Babu imani Kam Allah ya Kare mu da aikata zunubi,yanzu mene ne laifin yaran da za’a jefar dasu,wasu na nema wasu na zubarwa” Yace”Allah ya ganar dasu gaskiya dai”Tace”Ameen”Bayan kwana biyuDawowan shi daga gurin aiki kenan yayi salama har ya shigo amma shiru, sai da ya shiga bedroom sannan ya ganta ta k’udundune a blanket tana rusar kuka, da sauri ya k’arasa gurin ta Yana tambayar ta lafiya, kuka kawai takeyi,da k’yar tayi shiru,Cikin damuwa yace”mene ne ya faru?”Cikin damuwa tace” Dan Allah ka yarda mu d’auko yaro gidan marayu mu raine shi, wallahi Ina son in gani da baby please na rok’e ka da ka yarda Dan Allah?”ta fashe da kuka,Cikin tashin hankali sosai yace”mu d’auko yaro Kuma, meyasa ba Kya tunani ne haihi fa na Allah ne,sau nawa zan gaya miki hakan yanzu Kuma so kikeyi mu samo yaro daga gidan marayu mu raina, ai kamar mun cire rai da samun haihuwar ne”Cikin fushi tace”ai dama nasan baza ka yarda ba ka fad’a min sau nawa muna zuwa k’asashen waje amma maganar sai d’aya ne cewan baza mu samu haihuwa ba, Ni yanzu Ina son gani na da baby ne kawai Dan Allah ya d’aura min son yara wallahi Ina son su sosai”ta fashe da kuka,Yasan da cewan tayi nisa a yanzu baza taji Kira ba dan haka gara suje gurin iyyayen ta domin su San meke faruwa, Nan yace ta shirya zasu fita,batayi gardama ba ta shirya suka shiga mota,a tunanin ta ya yarda ne su d’auko yaro gidan marayu,Tayi mamakin ganin gidan su suka shiga, taji haushi ba kad’an ba,bayan sun gaida iyyayen ne, ya fad’a musu duk abin dake faruwa,Salati mahaifiyar ta tayi cikin b’acin rai tace” yanzu *AISHA* meyasa ba kya Jin magana ne sau nawa ana Miki nasiha akan ki yarda da k’adara akan rashin haihuwar nan, iye”Kuka ta fashe da shi tace” *HAJJA* na yarda da k’adara cewa nayi fa kawai muje mu d’auko yaro gidan marayu shine nayi laifi”Hajja tace”gidan ku waye sa’an ki anan ana magana kina”Mahaifin ta *ABBA* yace” haba my daughter meyasa kike hakan ne, ya Kamata kiyi hak’uri Allah zai baku haihuwa a Koda yaushe mutane nawa ne sukayi shekaru,amma daga baya Allah ya azurta su da haihuwa”Hajja tace” lokacin da Anabi Zakariyya Alaihi-salam(A.s) ya rok’i Allah Subhanahu wata’allah yace Allah ka bani ZURI’A D’AYABA, Kai ne maijin Addu’an bayin ka, Allah (S.W.A) Ya amsa Mai addu’an shi ya Azurta shi da samun haihuwa duk da matar shi ta wuce haihuwa Dan ta tsufa, ta haifa Yahya(A.S),Kinga Allah ya karb’a addu’an su, to Kinga matuk’ar bawa Yana aikata aikin ibada, tare da yawaita istighfari, Allah zai amsa addu’an shi matuk’ar ya daina sab’on Allah, Dan haka Ina Miki nasiha da ki yawaita yin addu’a tare da Istighfari, Allah Yana amsa addu’oin bayin shi,Kuma Allah shine Mai yafiya Mai Rahma Mai Jin k’ai”Gaba d’aya jikin Aisha yayi sanyi, Nan dai su Abba suka k’ara musu nasiha sosai sannan sukayi musu sallama suka nufa gida,*Asalin su*Mahaifiyar Aisha su biyu ne gurin iyyayen su,ita da k’anwar ta *AMINA* har sun girma *HADIZA* (Hajja) sunyi aure Allah yayi ma iyyayen su rasu sakamakon hatsari da sukayi suka rasu lokaci d’aya,sunji mutuwan iyyayen nasu sosai, lokacin Hajja na auren Abba Wanda dama shi maraya ne,ita Kuma Amina tana auren wani mutumin kirki malamin Islamiyan ne bashi da Hali sosai daga shi sai yayan shi iyyayen su suka haifa yayan Yana ji dashi Yana son shi, Nan ya aure Amina, sunan shi Malam Zakariyya,Suna zumunci sosai tsakanin Hajja da Amina, sai dai mijin Hajja wato Abba ya tsani Malam Zakariyya Dan shi baya son talaka balle yaga yanda Hajja ke shiri da Zakariyya sai duk ya tsane shi, a wannan lokacin ne Hajja ta haifa kyakyawar y’ar ta Mai suna AISHA, bayan shekaru biyu Amina ma ta haifa kyakyawar y’ar ta Mai suna *ZAINAB* inda jini ya b’alle ma Amina ta rasu gurin haihuwa, Hajja ta girgiza sosai da Jin mutuwar k’anwar ta, Nan ta rok’i alfarman Malam Zakariyya da ya bata ZAINAB ta raine ta Dan tana son ta sosai, dama ta shak’u da k’anwar ta Amina, duk da cewan Abba baya son Malam Zakariyya Amma ba yanda zaiyi dan Hajja ta kafe sai ta raina yarinyan k’anwar ta, hakanan ya hak’ura, Malam Zakariyya Kuma ya Kuma can wani k’auye dake cikin Abuja da zama gidan yayan shi, sai dai yak’i yin aure Dan baya Jin zai samu Mata da zata maye gurbin Amina, YAYAN nashi Yana da mata da yaro Mai sunna *ALIYU* Yana son yaron suna shiri sosai, lokaci zuwa lokaci Yana zuwa cikin garin Abuja domin ganin y’ar shi har tsaraba yake Mata sai dai ba kaita gurin shi, Dan basu San k’auyen ba,Hajja taci gaba da rainon ZAINAB tare da AISHA, sun taso tamkar ya da k’anwa wani lokacin idan Hajja ta kalle su sai ta tuna da yanda take da k’anwar ta, AISHA ta taso cikin gata Dan mahaifin ta na k’aunar ta sosai har Yana nuna banbanci tsakanin ta da ZAINAB, Dan baya k’aunar ta, ita ko Hajja bata nuna banbanci, Aisha tayi karatun ta har University sannan ta had’u da wani kyakyawan saurayi Mai suna *NASIR* inda suka fara soyyaya har akayi musu aure, baban Nasir Yana Raye sai dai Maman shi ta rasu, Yana son Aisha sosai duk da wani lokacin bata da kunya haka yake hak’urin zama da ita, tsawon shekaru goma Sha biyu da auren su Amma Aisha Bata tab’a b’arin ciki ba, tun abin na damun Nasir har ya hak’ura domin yasan Allah zai basu wataran, ita ko Aisha tana son yara kamar me haka zatayi ta kuka har k’asashen waje sunje anyi musu bincike sosai, ance bashi da matsala ita ce Mai matsalar aiko tayi bak’in ciki, ga ta da kishin tsiya, dan shi fa bai damu da Mata ba, basa gaban shi shiyasa ta kwantar da hankalin ta a cewar ta bazai Mata kishiya ba, ZAINAB budurwa ce kyakyawa tana da hankali da natsuwa, ga ladabi da biyyaya, shiyasa Hajja ke son ta, yanzu ta gama karatun ta na secondary, dan bata fara makaranta da wuri ba kasancewar Abba ya hana a sata sai da Hajja tayi da gaske tukun tayi karatun,Amma tana da ilimin Addini Kuma Allah ya Bata kwakwalwa Dan tana da saurin gane Abu, tun bayan lokacin bikin yayar ta Aisha Allah ya d’aura Mata son mijin Aisha wato NASIR, tayi bak’in ciki da ta gano cewa tana son mijin Aisha haka zatayi ta kuka dan tasan yayi Mata nisa Kuma har abada baza ta iya auren shi ba, gashi suna shiri sosai da Aisha sai dai ZAINAB bata son zuwa gidan Aisha,*Wannan kenan*Cigababan labariBayan kwana biyu, Aisha kamar ta hak’ura sai Kuma taji baza ta hak’ura ba dan gaskiya tana son haihuwa, ranar ta yini cikin damuwa da tunanin samu mafita duk da zuciyar ta na Bata wani shawara sai dai tak’i amincewa sai daga baya ta yanke ma kanta hukunci tunda ta samo mafita,Bayan Nasir ya dawo aiki ta same shi da maganar cewa tana son yayi aure sai da yayi Mata dariya yace bazaiyi ba bashi da sha’awar tara Mata, Aiko ta fashe mai da kuka yak’i yarda sai da k’yar ya amince ama shi bai San inda zai samo ba, Aiko tace ta samo Mai Mata daya tambaye ta sai ta fad’a Mai cewar ai zainab take son ya aura yace Ina ai Sam baya so ta Nemo wata Amma banda Zainab Dan shi ya d’auke ta a matsayin k’anwar Aisha ne, sai tace Mai to ya aura Zainab d’in amma da sharad’in idan Zainab d’in ta haihu zai sake ta, yayi mamakin yanda ta shirya wannan abin Kuma fa duk akan haihuwa take yin hakan, kawai ya k’yale ta ya bar gurin, Bayan sati uku kullum cikin yin Mai magana takeyi amma yak’i yarda sai da k’yar ya amince duk da bayason yaudaran Zainab d’in tunda ai yaudara ne ya aure ta Kuma idan ta haihu ya sake ta tabar musu abin da ta haifa gaskiya bai so hakan ba amma yazaiyi tunda Yana son haihuwa Kuma Yana son farin cikin matar shi Dan haka ya amince,Lokacin da ya amince taji dad’i sosai dan burin ta ya cika plan d’in ta ya tafi dai-dai, saura Kuma Zainab d’in da iyyaye su yarda,Bayan kwana biyu taje ta samu Zainab a gida suka gaisa sukayi hira sannan ta fara Mata magana akan ta yanda take fama da rashin haihuwa tana cikin damuwa sosai, tana Jin haka ta fara Mata nasiha sai dai Aisha ta fara Mata magana akan ta amince ta aura Nasir domin su samu haihuwa, Cikin razana Zainab ta mik’e tsaye tace”Aunty Aisha kinsan ko me kike cewa in aura mijin ki fa, gaskiya hakan ba zai yuwu ba”Cikin lalashi tace” Eh haka nake nufi Dan Allah ki taimake Ni ki amince ki aure shi” ta fara hawaye,Zainab zaro Ido tayi tace”haba please ki bar cewa haka Dan bazan tab’a yarda in aura mijin ki ba”Cikin kuka tace”taimako na zakiyi Zainab idan ba Kya son shi ma to ki yarda ayi auren inyaso in kin haihu sai ya sake ki”Cikin rud’ewa da tashin hankali tace”wannan wani irin magana ne, kenan kuna son amfani da ni dan ku samu haihuwa, Ni Kuma kun cuce Ni kenan ku raba Ni da abin da na haifa to bazan yarda ba Dan wannan ko a Addini Babu kyau”Cikin dabara tace”Aa ba hakan nake nufi ba Kinga kina son cigaba da karatun ki kawai zan Baki wasu mak’udan kud’i kije Canada kiyi karatun ki acan Dan Allah ki yarda da Ni kinsan bazan cuce ki ba Kuma kiyi tunani da kyau ki yanke shawara” Nan ta fita ta barta da tunani iri-iri,Bayan sati biyu Gaskiya tayi tunani sosai Kuma tana son Nasir ko Dan son da take mai zata yarda ta aure shi Kuma ta dage da addu’a Allah ya sa kar ya rabu da ita Kuma tunda Aisha da kanta tace ta aure shi to tana ganin ba matsala,yanzu tunanin ta d’aya shine baya son ta, lokacin da Aisha ta kira ta Nan ta gaya Mata ta amince da auren, duk da Aisha taji zafi sosai a ranta haka ta hak’ura tunda tana son haihuwa, Nan ta fad’a ma Nasir cewa Zainab ta amince da auran,Bayan Nan Aisha tace ya samu iyyayen da kanshi suyi magana kar aga kamar ita ta had’a abin, Nan ya fad’a ma baban shi aka je Nemo Mai auren Zainab gurin Abba duk sunyi mamaki sosai inda Hajja ta kira Aisha take tambayar ta ita da Zainab ko sun amince,Sun tabatar mata da sun min amince Kuma taji dad’i sosai tunda da amincewar su za’ayi auren,Nan tayi musu nasiha sosai akan su rik’e junan su, Aisha Kam ko kad’an nasihar bai shigeta ba tunda tasan ba jimawa auren zaiyi ba, yayin da Zainab ta rik’e nasihar,Nan aka sa ranar auren wata uku kawai, inda Nasir ya gina wani gida Mai shegen kyau na bene, babban parlour ne a k’asa sai kitchen da d’akin bak’i upstairs Kuma bedrooms d’in su ne, har d’akin yara sai da akayi, ga wurin wasan yara da aka tanada a cikin gidan Dan gidan babba ne sosai, Dan mahaifin Nasir Mai Arzik’i ne gashi Kuma Nasir d’in aikin banki yakeyi, ita Kuma Aisha tana da wani company na kayan sawa, Wanda mahaifin ta ya bud’e Mata,Lokacin da taga gidan taji dad’i balle da taga d’akin yara, sai dai tayi kishin ganin ita da Zainab zasu zauna,Amma ai na lokaci kad’an ne injita,Ranar d’aurin aureAnyi duk wani Abu da ake ma amarya inda Hajja ta gyara y’ar ta sosai, da Aisha da Zainab sunyi kyau ranar Aisha sai farin ciki takeyi kamar ba wace za’ayi Mata kishiya ba,Dan tasan abin da ta had’a shiyasa bata damu ba,K’arfe 2:00pm aka d’aura auren NASIR da ZAINAB akan sadaki mafi daraja inda dubanin mutane sun shaida,*Muje zuwa masu karatu**Taku ce UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:21 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *3*~*4* *DEDICATED TO RAHMAT NALELE**Ina yin ki Ina Jin ki Ina tare da ke ako da yaushe, Ina rok’on Allah ya k’ara zumunci tsakanin mu, Allah ya k’ara Miki basira da hazak’a, heart u dear sister*♥*Thanks for your love and support* 😘😍*Bayan* ankai amarya gidan ta ne mutane suka watse inda ya rage ita kad’ai a bedroom, da missalin k’arfe 9:00pm ne Nasir ya shigo gidan direct bedroom d’in Aisha ya nufa,tana ganin shi ta mik’e da sauri tana cewa”Ango kasha k’amshi”Dariya yayi yace”Aisha ke ko kishi na ba Kya yi ne,har wani nasha k’amshi kike cewa”Dariya ita ma tayi tace yazo suje ta kaishi d’akin amarya, sai da yayi wanka ya shirya suka nufa d’akin,Zainab na kwance har ta fara gyangyad’i sai taji sallaman su, bayan sun shigo ne an gaisa yayi musu nasiha sannan Aisha ta bar bedroom d’in, Nan dai sukayi salla da K’yar Zainab taci Naman kajin Dan a tsorace take da shi duk da zuciyar ta na k’aunar shi,Aisha ko ta kasa yin barci a wannan daren domin wani irin kishi takeji sosai sai zagaye bedroom d’in takeyi, ji take kamar taje ta shak’e wuyan Zainab tace ta fasa had’a plan d’in ta,Ni ko nace kin makara Dan aikin gama ya gama,tuni Nasir ya kusanci Zainab,Washegari da safeAisha ta gama had’a breakfast,amma taji shiru basu sauko downstairs ba haushi duk ya ishe ta,wani irin kishi takeji,ganin su tayi cikin shiri sun sauko, sannan suka gaisa, Zainab ko kunyar had’a Ido takeyi da Aisha wani irin kunyar ta takeji, Nan sukayi breakfast, Nasir ya bar gidan su Kuma suka d’anyi hira,A kwana a tashi ba wuya gashi yanzu har anyi wata biyu da auren NASIR da ZAINAB, Aisha kan nuna ma Zainab cewa ita ce matar gida, Dan haka za suyi ta soyyayar su ko a gaban ta ne, sai dai ta kawar da Kai amma tana Jin kishi,ba daman tayi wani abu yanzu Aisha za tace bata yarda ba Dan miji da gidan nata ne, sosai Zainab ke hak’uri da duk abin da suke mata, shi ko Nasir tausayin ta yake ji,Kuma yasan tana da hak’uri da biyyaya shiyasa yake tausaya Mata,Cikin dare Zainab ta tashi da wani irin azababen ciwo, ga amai da take kwararawa kamar hanjin ta zai fito, duk ta galabai ta dayake kwanan Aisha ne,suna can tare, zuwa safiya duk ta wahala, dauriya kawai take yi, ranar ta fito parlour kenan taga Aisha na gyara ma Nasir necktie zai fita aiki, cikin sauri ta k’arasa tana gaishe shi gani tayi kawai ya fita ba tare da ya amsa mata ba, Aisha ce ta kalle ta ganin yanda lokaci d’aya ta canza Nan tace” Zainab meke damun ki ne?”Cikin dane damuwar ta tace”ba komai Aunty Aisha me Kika gani?”Tace”no kawai Naga you look somehow ne ko baki da lafiya ne please ki fad’a min?”Girgiza kai kawai tayi tace”lafiya na k’alau”Tace”ok amma in wani abu na damun ki let us know kinji”Tace”okay”Cikin kwana biyu ciwo takeyi sosai ga amai da take fama da shi ko abinci bata iya ci,tun Nasir bai lura ba har ya gane bata da lafiya idan ya tambaye ta sai tace malaria ce kawai, a haka har sukayi wata d’aya, a wannan lokacin ne Aisha ta lura tace ai Ina sai doctor ya duba ta, Nan ko Nasir ya kira doctor, yana zuwa ya duba ta yayi test d’in urine, Nan ya gano tana d’auke da ciki, mik’a ma Nasir hanu yayi yace”congratulations matar ka na d’auke da ciki”Tunda ya zo duniya bai tab’a tsintar kanshi cikin farin ciki irin wannan ba sujudud shukur yayi ya gode ma Allah, Aisha ko rasss taji gaban ta ya fad’i,sai Kuma taji farin ciki Nan tayi ma Allah godiya domin ji takeyi kamar ita ce da cikin, Zainab ko wani irin dad’i da sanyi taji a ranta lokaci d’aya taji k’aunar abin da ke cikin ta, Doctor ya tayasu da murna Dan yasan shekaru da dama suna neman haihuwa gashi yanzu Allah ya amsa addu’an su ya basu haihuwar, Nan yace suje hospital a k’ara duba ta da abin da ke cikin, ai Nan suka tafi, anyi mata bincike ba abin da ke damunta sai laulayi, anyi scanning cikin wata uku kenan, sunji dad’i sosai,Tunda suka gano tana d’auke da ciki suka fara ririta ta tare da nuna Mata gata, duk abin da take son ci sai an nemo mata, ga abubuwan da ake siyo mata har da na banza, duk wani abin kwad’ayi sai Aisha ta kawo mata, Nasir ma Yana ji da ita haka zasu tasa ta agaba da ci wannan Sha wannan, abu kad’an sun tafi hospital, wani lokaci sai Aisha ta tasa ta agaba da tambayoyi ko akwai abin da ke damunta, shima haka zaiyi ta tambayar ta ko akwai abin da ke damunta, murmushi kawai takeyi tace ba komai, Zainab ko haka zata zauna wani lokacin tayi ta kuka dan tana son cikin ta gashi za’a raba ta da abin da zata haifa, sai taji wani irin bak’in ciki, a wannan lokacin ne suka je gidan su Hajja tana ji da ita wani irin kulawa na musaman take Mata, Baban tane yazo shida ALIYU yaron yayan shi, Nan suka gaisa dayake su kad’ai ne nan tayi musu bayanin duk abin da ke faruwa, har sakin da Nasir zaiyi Mata , ai ko baba yayi Mata fad’a yace meyasa zata yarda da irin wannan auren kenan sunyi amfani da ita ne, Wanda ko a musulunci bai dace ba, nasiha sosai yayi Mata sannan suka yi sallama yana cikin tausaya Mata, Aliyu ko cewa zai kira ta a waya akwai taimakon da zaiyi mata,Cikin ta wata takwas kenan yayi girma sosai gashi yana samun kulawa, dan su Nasir su na nuna Mata gata, cikin dare ta tashi cikin matsanan damuwa ya zama dole ta bar gidan nan idan har ba so takeyi a raba ta da abin da zata haifa, dama ta yanke shawaran barin gidan ta tafi inda baza su ganta ba, dama sun shirya da Aliyu cewan zaizo su bar gidan, dama tana da wani kud’i Nan ta kwashe ta had’a kayan ta cikin akwati sai ta kira Aliyu cewan yazo da asuba su tafi, dan akwai wani k’auye da zasuje, d’aukan biro da wani papper tayi tayi rubutu tana kuka sannan ta ajiye, shafa cikin ta tayi cikin kuka tace”bazan Bari a raba ni da Kai ba zan tafi da kai in Raine ka da kaina in baka tarbiyya domin nice mahaifiyar ka bazan yarda a raba mu ba”ta fashe da kuka,K’arfe 4:00am Aliyu ya kira ta cewan gashi nan a k’ofar gidan ta fito, kasancewar su Nasir sunyi barci yasa ta fito da k’yar komai tanayi a hankali har ta bud’e gidan ta fita, lokacin da taje wurin gate ta cire duk wani key da sak’ata dayake d’akin maigadi a gefe yake, gashi dama sarkin barci ne,duk baiji ba har ta fita daga gidan,Aliyu ta gani yayi tashar mota Nan yasa akwatin ta a ciki, suka shiga Nan suka d’auki hanyar wani k’auye, Lokacin da Nasir yaje masalaci dama idan ya dawo Yana shiga gurin ta yaga ko tana lafiya, aiko shigan da zaiyi sai yaga bata nan har toilet ya duba bata nan hankalin shi ya tashi haka ya k’ara zagaye gidan amma bai gan ta ba da sauri ya samu Aisha a bedroom yana tambayar ta ko taga Zainab cikin rashin fahimta tace bata ganta ba aiko ya fad’a mata shima bai ganta ba, cikin rud’ewa suka cigaba da zagaye gidan amma Babu Zainab babu alaman ta ko da suka zo gate sai gani sukayi a bud’e da aka tambaya maigadi yace bai san lokacin da ta fita ba, Aisha tayi mai fad’a sosai tace ba amfanin gadin da yakeyi tunda har za’a fita gidan yace bai sani ba, cikin bedroom d’in Zainab suka shiga Nan suka ga alama babu wasu kayan ta Dan ta hargitsa Kaya, kan bed d’in suka ga wani paper Nasir ne ya d’auka ya fara karanta abin da yake a rubuce kamar haka, *Assalamu Alaikum**Ku yafemin domin gaskiya bazan iya yarda in haihu in bar muku abin da na haifa ba Ina son baby na bazan iya rabuwa da shi ba, Aunty Aisha ki gafarce ni domin bazan iya baki abin da na haifa ba, Nasir Ina son kasan da cewar Ina k’aunar ka soyyayar da nake maka ne yasa na tafi da gudan jinin ka, Ina rok’on gafarar ka, kada kuyi wahalan nema na domin nasan lokacin da kuke karanta wannan letter nawa na Jima da yin nesa da ku, nayi nisan da baza ku gani ba*, *Matar ka Zainab*Zama yayi kan bed yana fad’in sunayen Allah hannun shi ya rik’e kanshi da shi yana girgizawa, ganin hakan da Aisha tayi sai ta d’auki letter ta karanta, tana gama karantawa ta fad’i k’asa sumamiya, cikin tashin hankali ya d’ebo ruwa ya yayafa mata, d’ago ta yayi yana fad’in ta tashi kar ita ma ta tafi ta barshi,Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta rushe da kuka, Nasir ma dauriya kawai yakeyi Nan ya fara bata hak’uri, cikin kuka tace” wallahi Zainab bazan tab’a yafe Miki ba, kin cuce mu”ta fashe da kuka,Cikin lalashi da k’arfin hali yace” kukan nan bashi ne mafita ba yanzu ki tashi muje gidan dan su Hajja su san abin da ke faruwa”Gidansu suka nufa inda Nasir ya fad’a musu abin da ke faruwa, Aisha ko kuka kawai takeyi, Hajja ko bata yarda hakan Zainab ta gudu ba sai dai ko sunyi mata wani abu, Nasir bai b’oye mata komai ba tun daga abin da Aisha ta had’a har zuwa yanzu, sai dai yayi ta bada hak’uri Kuma yayi nadama da yace zai saki Zainab, gashi ta tafi ta barshi, habawa ran Hajja ya b’aci sosai tayi musu fad’a Kuma tace Aisha ta cutar da yar’uwan ta gashi yanzu Hajja Bata san inda zata nema Zainab ba dan bata san inda mahaifin Zainab d’in yake ba ko dan halin Rayuwa tsabar bak’in kishin Abba ya Hana ta sanin komai dan gane da baban Zainab, dan lokacin da akayi auren k’anwar ta Amina cikin birni suka zauna, bata san k’auyen da yake ba,Sun d’auki sati biyu suna neman Zainab amma Babu labarin ta abin duniya ya dame su, Nasir na ganin cewa yayi ganganci gashi har ya rasa matar shi da abin da zata haifa wanda yake bala’in son cikin gashi yanzu babu su, ita kuma Aisha tana ganin cewan Zainab ta cuce su ta gudu da ciki bayan tun samun cikin Nasir yace ya bata abin da za’a haifa, gashi tana k’aunar cikin ji takeyi kamar ita ke da cikin, ga son yara da yake damunta,Anyi kwanaki da barin Zainab gidan inda Aisha ke cikin matsananciyar damuwa dan bata hak’ura ba so takeyi ta ganta da baby, bale idan ta kalla d’akin wasan yara da bedroom d’in su sai tayi ta kuka, ana cikin haka ne kwatsam sai gashi tazo gidan da yarinya, Nasir ya dawo aiki sai da ya huta take fad’a mai cewa ta samu yarinya, tana cikin driving sai taga anyi accident ko da ta fito mota sai taga wata mata ce aka buge ga tsohon ciki, shine aka sa ta cikin motan sukaje hospital, bayan sunje aka shiga da ita theater room inda aka ciro yarinyan mahaifiyar Kuma ta rasu, to ganin babu Yan’uwan matar ne Babu Wanda yasan ta ga alamun matar kamar mahaukaciya shine tace ma doctor d’in zata rik’e yarinyan insun yarda, Kuma sun amince Dan har police sunzo Kuma sun yarda, Nan ta nuna ma Nasir takardun sa hannu na amincewa, ya Kuma gamsu da maganar ta Nan ta d’auko Mai baby’n ya rik’e, lokaci d’aya yaji wani irin k’aunar yarinyan tare da son ta, gata Kuma kyakyawa, Aisha tace yasa mata suna aiko Nan yayi mata hud’uba yasa mata suna *NUWAIRA* ,Washegari da safeSuka zagaya dangi da iyyaye suka gabatar da NUWAIRA Kuma an taya su murna inda akayi jimamin b’acewar Zainab, sunci gaba da kula da NUWAIRA cikin so da k’auna kamar su suka haife ta, lokacin da NUWAIRA ta cika shekaru goma da haihuwa akayi mata birthday dan ana nuna Mata gata, a ranar birthday d’in ne wata ta gaya ma NUWAIRA cewar ai su Aisha ba iyyayen ta bane, ai ko tayi ta kuka sosai inda Aisha tayi fad’a da matar, Nasir da Aisha duk sunyi mata bayanin komai suka lalashe ta ita ma ta cigaba da d’aukan su a matsayin iyyayen ta Dan tana k’aunar su, *Mene ne labarin Zainab bayan ta bar gida?* K’arfe 2:00pm suka isa wani k’auye dama Aliyu akwai mahaifiyar Maman shi a k’auyen, gidan ta suka nufa da yake tasan da zuwan su Nan ta karb’e su cikin mutunci, bayan Zainab ta huta taci abinci ta fara tunanin gida da halin da Nasir zai shiga, Cikin Zainab ya Kai wata tara inda ta haifa kyakyawar y’ar ta mace Mai Kama da mahaifin ta, Zainab ta sa Mata sunan mahaifiyar ta wato *AMINA* za’a dinga Kiran ta da *MEENAL* ,haka Zainab ta cigaba da kula da *MEENAL* har tayi shekara d’aya sannan suka koma k’auyen da mahaifin ta yake, Lokacin da Malam Zakariyya yaga y’ar shi yayi farin ciki Dan ciwo ne ya kwantar da shi dalilin da yasa bai je cikin Abuja ba kenan bare yasan abin da ke faruwa, Nan ta fad’a Mai komai dama tak’i zuwa Nan ne Dan kar mahaifin ta ya matsa Mata sai ta koma gidan Nasir, Nan Malam Zakariyya yayi Mata fad’a yace bai dace tayi haka ba, Nan tace ita bazata Koma ba, Nan ya k’yale ta Dole wataran ta koma da kanta Dan shi Yana fama da ciwo,*********** *************** *AFTER EIGHTEEN YEAR’S* *BAYAN SHEKARU GOMA SHA TAKWAS* Cikin tafiyar k’asaita take saukowa daga upstairs kamar ba zata take k’asa ba, kyakyawar budurwa ce chocolate colour ce tana sanye da armless d’in riga da three-quarter ko d’ankwali babu a kanta, *NUWAIRA* kenan,Zuwa tayi ta zauna kusa da Hajiya AISHA, cikin shagwab’a ta kwantar da kanta a cinyar ta, cikin murmushi Aisha ta shafa gashin kanta tace” Daughter na an kawo kayan da Zaki sa na Graduation d’in ki, sai ki duba idan yayi Miki” ta mik’a mata wasu gown masu shegen kyau colours daban-daban, Karb’an kayan tayi ta ya mutsa fuskar kamar za tayi kuka tace”mom I don’t like this design gaskiya a canza wani duk basuyi kyau ba” Da sauri tace”okay sorry daughter yanzu zan sa ayi miki irin Wanda kike so kinji don’t worry” Nan ta d’auki waya ta kira ma’aikatan company d’in ta nayin Kaya ta fara musu fad’a cewan wanna kayan baiyi ba su shirya wani,Nuwaira kwantar da kanta tayi a kafad’ar mom(Aisha),********** *********Wata kyakyawar budurwa ce tana sanye cikin uniform cikin natsuwa ta shigo cikin wani gidan k’asa, cikin zazak’ar muryan ta tayi sallama ta shiga tare da cewa”Ummie na dawo”Zainab ce ta fito daga d’aki da sauri budurwan Nan ta rungume ta tana cewa”miss you Ummie na”Janta tayi tace” wai *MEENAL* so kike ki k’arya Ni ko?”Shagwab’e fuska tayi ta k’ara langwab’ewa a jikin ta, Aliyu ne ya shigo Yana cewa” ai Ni bansan ranar da Meenal zata girma ba, sai shagwab’a”Turo Baki gaba Meenal tayi tace” Kawu Aliyu Ni ban girma ba a gurin Ummie na”Ummie (Zainab) tace” Ni d’aga Ni kije ki cire uniform, kin tsaya surutu”Mik’ewa tayi ta shiga wani d’aki,*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:21 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *5*~*6**Dedicated to Badiyerh (beauty queen) & Maimounath o.g* *Ina son ku irin totally d’in nan buri na mu zama ZURI’A D’AYA, domin ku d’in na daban ce Allah ya k’ara had’a kanku ya Kare ku daga sharin makiyya da mahassada Ameen* *Kawaliya kawar Arzik’i Ina yinki sosai Allah ya kaimu biki mu kwashi shoki*💃🏻*Sis Ina gaban ki kina baya na bazan barki ki wuce niba, muje k’asar waje mu kaiki amarya, Allah ya Kare min ke I love you wujiga wujiga*😍 *Hussaini 80k ban manta da alkhairin ka gare Ni ba Allah yasa ka gama exams lafiya Allah ya bada nasara*✍🏻An had’a ma Nuwaira party na Kamala secondary School da tayi, naira yayi kuka anyi b’arin kud’i sosai an raba abubuwa iri-iri, Nuwaira sai farin ciki takeyi ta gama school, Daddy (Nasir) ya sama mata gurbin karatu a Open University of Abuja inda zata karanci business,Wani mota ne guda biyu suka yi parking cikin wani gida mai shegen kyau, driver ne ya fito da sauri ya bud’e mata k’ofa, Nuwaira kenan tana sanye cikin Riga pink da wando black Wanda ya kama jikin ta, gashin Nan an zubo shi gyale ya rufe rabi, sauran gashin na waje tasha make up, rik’e take da waya, har ta isa cikin parlour’n gidan, K’arasawa tayi inda mom take tayi Mata kiss a goshi tare da cewa”hey Mom I’m back”Cike da kulawa tace”welcome back sweet daughter, kunyi waya da Daddy’n ki kuwa?”Cikin shagwab’a tace”yeah he said he’s not coming back this week, and bana son fara zuwa University baya nan”Tace”don’t worry daughter ai Ina tare da ke ok”D’aga Kai tayi tace” I’m hungry now” ta turo baki,Da sauri mom ta k’wala ma Mai aiki Kira,sai gata da sauri ta iso, Nan ta shirya ma Nuwaira abinci da sauri Dan yanzu sai ta hau ta da massifa, *********************Yau ranar farin ciki ne a gare ta domin taci jarabawar ta na fita secondary School, gashi ta samu schooler ship an d’auki nauyin karatun su ita da wasu guda biyu a makarantar su, Nan ta fad’a ma Ummie sai dai sam Ummie tak’i yarda dan a Abuja ne, ita ko bata son duk wani abu da zai kaisu Abuja bare kuma Meenal, dan tunda Meenal tayi wayau ta fad’a Mata cewa mahaifin ta ya rasu tun kafin a haife ta,Zama tayi a tsakar gida tayi shiru tana tunanin wani hanya zata bi dan Ummie’n ta ta amince ta tafi karatu a University na Abuja, can dabara ya fad’o Mata Nan ta shiga wani d’aki inda Malam Zakariyya yake zaune,Fuskar tausayi tayi tace”Kaka dan Allah kayi ma Ummie na magana ta amince in tafi karatu please”Gyara zama yayi yace” AMINA me sunan manya yanzu ke sai kin tafi karatu, kiyi hak’uri kawai kiyi auren ki, in Kuma kin tsufa a gida ayi auren da ni” ya k’are da dariya,Kamar zatayi kuka tace” Allah ka cire maganar wasa wallahi Ina son yin karatu a Rayuwa ta Kuma an d’auki d’auyin karatu na yanzu ne nake da dama, kaga yanzu bamu da halin da za’a samar min wani karatun, please kayi mata ko zata yarda”Ya tausaya Mata sosai ganin yarinya da gatan ta amma ji yanda rayuwar ta ya koma yace” karki damu me sunan manya, zanyi mata magana inshallah”Murmushin farin ciki tayi tare da yin mai godiya, nan ta fito waje, Ummie ta gani tana dakan gero da yake tana d’an yin sana’a ana kawo mata dakan su gero da yaji,sai a biya ta,Cikin tausayin Ummie’n nata take ta karb’a tana cewa” Ummie na ki zauna ki huta ni zanyi”Ummie tace” Allah yayi miki albarka”Ameen tace sannan ta cigaba da daka, bayan ta gama ne sai ga Aliyu ya shigo, da sauri ta same shi cikin murya k’asa-k’asa tace”Kawu please ku tayani rok’on Ummie na ta barni inje University’n Abuja please kaji Kawu”Sai da yayi dariya yace”Abu Mai sauk’i, Ni kaina Ina son ganin kinyi karatu,dan haka ni zan shawo kanta ta amince idan Kuma bata amince ba zan shirya Miki komai ki tafi daga baya Dole ta hak’ura”Cikin murna tace” Kawu gaskiya ka kawo shawara Mai kyau, kace infara shiri”Dariya yayi yace”to sarkin sauri ai saiki bari kiji ya zamuyi”Tace” toh Kawu na”A haka kuwa akayi sun same ta sunyi mata magana tace ita Sam bata yarda ba ai su sunsan meyasa bata son Meenal taje can garin, sunyi-sunyi ta fahimce su tak’i,ganin idan suka bi ta nata Meenal baza ta samu karatu ba kawai sai suka yanke shawaran shirya ma Meenal Komai da student zata b’ukata har suka gama komai, amma Ummie bata san komai ba,A ranar da zata tafi Kaka(Malam Zakariyya)yace da Ummie ta bar Meenal ta ziyarci wata k’awar ta da take can wani k’auye dayake suna shiri tace ai ba damuwa taje, aiko Aliyu ne zai Rakata, haka suka samu mota a Tasha sai garin Abuja,inda Aliyu ya kaita har makarantar, Nan aka nuna Mata hostel d’in da zata zauna, inda ta rabu da Aliyu cikin kewa, bayan ya bata waya Dan su dinga Jin ta, Nan ta shirya kayanta dayake har da kayan abinci duk su Kawu sun siyan mata,*K’auye*Lokacin da Aliyu ya koma gida ya fad’a ma Kaka cewan ya Kai Meenal lafiya, sai ya kira Ummie suka fad’a Mata gaskiya,habawa hankalin ta ya tashi ji takeyi kamar an raba ta da y’ar ta ne,ko kad’an bata so hakan ba, sai dai da Kaka ya fad’a Mata babban dalilin da yasa gara Meenal tayi karatu sai ta hak’ura tunda ba yanda zatayi,*OPEN UNIVERSITY ABUJA* Sauri-sauri ta shirya cikin Riga da skirt na atamfa lemon green da d’igon light blue, wani k’aramin hijab ta d’auko light blue tasa sannan ta saka flat shoe Wanda shi kad’ai take da shi Kuma ya kusa tsinkewa,haka Nan tayi managing tasa, wayan ta ta d’auka tare da Kiran Ummie’n ta,Tana Jin ta d’auka tace” Ummie na ki gafarce ni domin ban kyauta Miki ba,Dan Allah Ummie na kiyi hak’uri Sam bana son b’acin ran ki”Ummie tace”Sam banji dad’in hakan ba sai dai ya zanyi bayan kun taru a kaina har da min dubara, yanzu ai shikenan, Allah ya sa ki fara karatu cikin nasara,Kuma zanja kunnen ki akan kici gaba da tsoron Allah, banda samari da k’awayen banza dan yanzu Babu na gari,kinji ko”Tace”eh Ummie na inshallah zan kiyaye baza ki same Ni mai karya nasihar ki ba”Nan tayi ta mata nasiha sosai tasa mata albarka sannan suka yi sallama, Meenal ce sai sauri takeyi wannan shine first time da zata fara shiga lecture bata son yin late, sauri kawai take Dan ta isa,Kyakkyawan saurayi ne na k’arshe Yana sanye da Riga black Mai kwalliyan Stones da wando white irin na Indian Nan, waya ne a kunnen shi yana magana sai sauri yakeyi, dai-dai ya taho bai lura ba ita ma ta taho kawai sai sukayi karo yayin da suka fad’i k’asa, wayan shi ya fad’i ya k’asa ita Kuma litafan ta suka zube,Mik’ewa tsaye yayi cikin b’acin rai ya kalle ta, yayin da ita ma ta mik’e tsaye, cikin b’acin rai yace”are you blind ko sama Zaki hau ne da baki kallon hanya”Takalmin ta ta kalla ganin ya tsinke ga litafan ta sun zube ga Kuma maganar da yake gaya Mata, cikin haushi tace” Kai hankalin ka na Ina ne da baka kallon hanyar,Kuma bazan yarda ba sai ka biya ni takalmi na ehe”ta murgud’a baki,Tsaki yaja tare da d’aukan wayan shi yace” idiot kawai baki da manners” ya fara tafiya,Binshi ta fara yi tana cewa sai ya biya ta takalmin ta amma ko kula ta baiyi ba ga mutane sai kallon su sukeyi, ganin bai kula ta ba Kuma ga litafan ta a k’asa ga time d’in shiga lecture zai wuce kawai sai ta hak’ura ta dawo ta kwashe su, ta tafi tana tunanin irin abin da zatayi mai in sun sake had’uwa Dan babu abin da ta tsana irin aci mutuncin ta ko na wani,After two daysWata shegiyar mota ce mai kyawun gaske yayi parking cikin makarantar Open University, tsayawa nayi Inga ko su wane a cikin motar, hmm Reader’s ko kunsan suwaye ne? Wani kyakyawan saurayi ne ya fito ta k’ofar zaman driver da alama shi ke driving d’in, wani saurayi ne shima d’in kyakyawan ne ya fito daga seat d’in baya sannan yayi nuni da hannu irin na ciki ta fito kamar yanda turawa keyi,Nuwaira ce na gani ta fito tana sanye cikin Riga da skirt na English wear tasa takalmi hill, tayi rolling d’in gyale a kanta fuskar Nan tasha make up ga wani sunglasses da tasa, cikin k’asaita ta fito, Wanda yayi mata alaman ta fito da hannu ya kalle ta yace” my queen sai yaushe kenan?”Cire sunglass d’in tayi tace”My prince charming you know bana jure zaman class I think Nan da two hours ka dawo ka d’auke ni mu tafi”Murmushi yayi yace” duk yanda Kika ce haka za’ayi”Tace”okay bye”Shima ya d’aga mata hannu alamar bye, kallon na kusa da shi tayi Wanda tunda suka fito motar baice komai ba tace mai”Bye *FAWAS* “Wanda aka kira da FAWAS d’aga Kai kawai yayi, na kusa da shi d’in ne ya buga bayan shi cikin Wasa yace” Kai banza ne wallahi kana ji my queen na maka sallama kak’i magana”Cizan lips d’in shi yayi na k’asa irin wai shi yaji zafin nan yace” banson haka fa *KAMAL* sai bayan kun gama soyyayar ku ne zaku tuna da ni ba”Wanda aka kira KAMAL yace” you know something idan Ina tare da queen d’ina mantawa nake da kowa”ya k’are da dariyan mugunta Dan yasan aminin nashi ya shak’a baya son maganar soyyaya dan yace soyyaya is just a wasting of time,Tsaki FAWAS yayi ya shiga kusa da seat d’in driver yayin da KAMAL ya shiga gurin driver yayi driving suka bar school d’in,*Shin su wane ne FAWAS da KAMAL?**Ku biyo ni domin Jin Asalin su**TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:21 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *7*~*8* *DEDICATED TO MY LOVELY SISTER’S*Hafsat Musa indon K’auyeMummy’n SultanMSBRafee’atFaty AxlandSadnaf4realSadiya Adam SADNAFMEERAHSadnasLababat isma’ilSalmahZee yabourMaryam Y zango*Love you all*🌹*NUWAIRA* ce ta nufi class, duk da cewan tayi late amma haka ta shiga ba tare da ance mata komai ba, mamaki ne ya Kamata da taga wata a seat d’in ta,MEENAL ce zaune a seat d’in ta, zama tayi kusa da wannan seat d’in bata ce komai ba,Bayan an fito ne NUWAIRA ta kalle ta tace” Amma dai ke sabuwar zuwa ce ko?”Kallon ta MEENAL tayi da kyau lokaci d’aya taji k’aunar ta Nan tace” Eh ni sabuwar zuwa ce”NUWAIRA barin gurin tayi ba tare da ta sake magana ba, MEENAL tayi mamaki kawai sai ta share ta wuce, Haka Rayuwa yaci gaba da tafiya, MEENAL ta dage da karatu gashi Allah ya bata k’wak’walwa kowa na makarantar suna son ta saboda k’okarin ta kuma tana aiki a wani Restaurant sai a biya ta dan gaskiya bata da kayan abinci ga kud’in hannun ta ya k’are kuma sunyi waya da Kawu zai kawo mata wani abin amma har yanzu shiru, Yayin da sai NUWAIRA taga dama take zuwa makarantar, idan tazo ma ba abin dake had’a ta da MEENAL kasancewar ita ko k’awaye bata da su, Bayan sun fito daga class ne MEENAL ta samu guri ta zauna ta rik’e cikin ta dake faman Mata ciwo, NUWAIRA ce tazo wucewa sai ta lura da MEENAL cikin halin b’ukatar taimako, dan sai cije lips take da alama cikin na murd’a mata sosai,K’arasawa tayi gaban ta tana tambayar ta meke damun ta, amma MEENAL ta kasa magana, ganin yanda ta rik’e cikin ta yasa NUWAIRA gane cewan cikin ta ne ke ciwo, nan ta rik’e hannun ta tana cewa” kina b’ukatar a duba ki muje hospital, Girgiza kai tayi cikin azaba tace”Aa kar ki damu zai bari”Tace” No please ki daure mu tafi ko medicine a baki “Da k’yar ta mik’e tsaye NUWAIRA ta rik’e ta suka Isa gurin parking lot inda nan driver’n NUWAIRA ke jiran ta har a tashi dan ita bata son jira, shiga da ita motar tayi sannan ita ma ta zauna, Nan driver ya kaisu wani hospital,Doctor ya duba ta tare da bata magunguna dan dama idan period d’in ta zai zo haka take faman Shan wahala, tana Shan maganin taji ya fara sauk’i, suna hanyar komawa School ne NUWAIRA tace driver ya kaisu Restaurant suyi lunch tukun,Bayan sun gama ne suka koma cikin School har hostel NUWAIRA ta raka MEENAL, Kallon ta MEENAL tayi tace” A gaskiya bani da bakin gode miki sai dai ince Allah ya saka Miki da alkhairi, nagode sosai da kulawar ki gare ni”Murmushi NUWAIRA tayi tace” don’t mention, but I will like if you become my FRIEND” Cikin farin ciki tace” why not” ta mik’a mata hannun ta tace”by the way I’m *AMINA MUHAMMAD* amma ana Kira na da MEENAL”Mik’a mata hannun ta tayi ita ma tace” wow nice to meet you MEENAL”Tace” you’re welcome, ya sunnan friend d’in tawa”Tace” My name is *NUWAIRA NASIR MUHAMMAD*”Murmushi tayi tace” what a lovely name, nice to meet you too”Nan NUWAIRA tayi mata sallama ta tafi,The following dayKafin a fara lecture sai ga NUWAIRA ta shigo class, mutane sai mamaki sukeyi ganin bata tab’a zuwa irin wannan lokacin ba, direct kusa da seat d’in MEENAL ta zauna, cikin farin cikin ganin NUWAIRA tace” Ya kike?”Tace” lafiya lau ya jikin ki hope da sauk’i?”Murmushi tayi tace”naji sauk’i”Sun d’anyi hira sannan wani Malami ya shigo, Bayan sati biyuCikin satin Nan sun Saba da juna suna shiri, sai dai MEENAL ta lura NUWAIRA bata son karatu Nan ta fara cusa Mata ra’ayin karatu,Saukowa tayi daga upstairs, ta nufa dinning table inda su Daddy ke breakfast, “morning Mom and Dad” shine abin da ta fad’a tana had’a tea,Shafa kanta mom tayi tace”morning daughter”Daddy girgiza kai kawai yayi dan sam baya son halin turawan da y’ar shi ta d’auko, mik’ewa tsaye tayi tace”Na tafi ban son inyi late” ta k’arasa waje,Daddy yace”yanzu AISHA abin da kikeyi kin kyauta kenan kinsa ma NUWAIRA Ido wato tayi abin da taga dama, ki kala irin shigan da tayi kamar ba na yaran musulmai ba wannan wace irin Rayuwa ce, ki gyara gaskiya”Tab’e baki tayi tace”Ni banga wani abin tsiraici da NUWAIRA ke sawa Kuma idan atamfa kake son tasa ai bata iya sa irin wannan kayan ba kasan tafi son English wears to me zanyi Mata tunda ba ta so”Girgiza kai kawai yayi ance Wanda yayi nisa baya Jin Kira, shi dai Yana son NUWAIRA amma sam baya son irin tarbiyyan da Aisha ke bata kuma kullum cikin yin mata gyara yake akan ta daina hakan,ya tabbatar abin da yasa Zainab tafiya kenan dan Aisha Kam baza ta iya bada tarbiyya mai kyau ba,Rik’e yake da waya a hannun shi yayin da ya shiga mota Yana cewa”I’m on my way please don’t be angry queen”FAWAS dake cikin mota ya cika fam ya kalla KAMAL yace” Kai wani irin mutum ne wai tun d’azu Ina jiran ka sai yanzu zaka fito?” Kashe Ido d’aya yayi yace” na tsaya shiryawa ne da kyau domin queen d’ina”Cikin takaici yaja motan Yana cewa” Kai ka sani”Dariya KAMAL yayi tayin mai daga k’arshe da FAWAS yaga abin nashi iskanci ne sai ya sa earpiece a kunnen,Inda driver ta yayi parking Nan motan su FAWAS yayi parking, fitowa tayi ta shiga nasu FAWAS bayan ta ba driver kud’i dayawa,Yana driving har suka shiga cikin School d’in,su Kuma su KAMAL sai hiran soyyaya sukeyi,Fitowa tayi tace” Ina son muku introducing d’in new friend na”Cikin nuna farin ciki KAMAL yace”Congrats my queen tayi friend”Murmushi kawai FAWAS yayi, Nan NUWAIRA ta nufa hostel tare da Kiran MEENAL tazo ta nuna Mata boyfriend d’in ta da friend d’in shi, dama a shirye take tasa doguwar Riga black colour tayi rolling d’in gyalen akan ta, yayin da NUWAIRA na sanye cikin Riga da skirt ta d’an yafa gyale,Sun jera suna tafiya mai d’aukar hankali duk da cewan haka tafiyan su yake, tun daga nesa suka hango su, zuciyar su ne ya buga lokaci d’aya, su FAWAS kenan,Cike da natsuwa ta k’arasa ba tare da ta d’ago kanta ba, NUWAIRA ce tace musu ga MEENAL, KAMAL yace”hey MEENAL”D’ago da kanta tayi ta amsa yayin da fuskar ta ya sauka akan mutumin da sukaci karo ranar farkon ta a School d’in,Kallon ta FAWAS yayi tare da kawar da kan shi, cikin haushi ta nuna FAWAS tace” NUWAIRA wannan?”Murmushi tayi tace” sunan shi FAWAS best friend d’in KAMAL nane kuma d’a ne ga best friend d’in mom na”D’aga Kai tayi alamar gamsuwa, NUWAIRA tace” do you know him ne ko a wani guri?”Sai da ta harare shi tace” No kawai”Tsaki shima yaja yace” kinyi talkative friend ni Ina mota in kun gama KAMAL” shigewa mota yayi,Cikin jin haushin shi MEENAL tayi musu sallama, nan NUWAIRA ita ma tayi musu sallaman suka wuce,Cikin tsokana KAMAL yace” A Ina ka santa course na gane kun tab’a had’uwa”Banza da shi yayi har sai da ya k’ara magana sannan ya fad’a mai had’uwan su da MEENAL, habawa mai KAMAL zaiyi in ba dariya ba, shi dai FAWAS komai bai ce ba,*Shin su waye ne FAWAS da KAMAL?*FAWAS SAIFULLAH shine cikaken sunnan shi, mahaifin shi SAIFULLAH asalin d’an garin Gombe ne, yayi karatun shi ya gama ya fara business a wannan lokacin ne Allah ya had’a shi da Mahaifiyar FAWAS wato ITRAN mahaifin ta d’an Nigeria ne Maman ta Kuma balarabiya ce na k’asar DUBAI,aiki ne ya Kai mahaifin ta can har suka had’u sukayi aure acan suka fara zama sai daga baya suka dawo gida Nigeria a Gombe ITRAN tana da yayan ta Abdulrahma, su biyu iyyayen su suka haifa, tun tana 16yrs ta had’u da mahaifin FAWAS lokacin da suka fara soyyaya kawai mahaifin ta yace gara ayi auren ta k’arasa karatun ta a gidan ta,haka ko akayi, taci gaba da karatu, sai kwatsam ta samu ciki,gashi tana wahala haka taci gaba da zuwa makaranta, bayan wata tara ta haifa kyakyawan yaron ta inda yaci sunnan FAWAS, tun daga Nan sai ta samu ciki ya zube baya zama, haka ta hak’ura da haihuwar suka cigaba da kula da FAWAS,FAWAS saurayi ne kyakyawan gaske fari mai d’auke da dara-daran Ido lips d’in shi dai-dai da fuskar shi, yana da fafad’an k’irji Kuma yana da tsawo dai-dai kuma Bai da rama Kai intakaice muku dai kyakyawan saurayi ne na k’arshe, shekarun shi 25, yayi karatun shi inda ya karanci business kamar mahaifin shi, yanzu haka ya fara aiki a Company d’in baban shi tare suke zuwa Kuma su dawo, KAMAL best friend d’in shi ne Dan tun a primary school suke tare har suka kammala, suna son junan su sosai,Rayuwar gidan su FAWAS Rayuwa ce Mai cike da dad’i da k’aunar junan su, Mom d’in FAWAS tana son shi tana ji da shi sai dai ta tsani a rayuwa ya kira ta da Mommy tace sai dai yace mata Aunty dan bata son tsufa Dan yanzu ji takeyi kamar y’ar shekara 20 dan ba k’aramar y’ar gayu bace idan kun ganta baza kuce ita ta haifa FAWAS ba y’ar kwalisa ce ga kyau jikinta mai kyau ne kuma tana da tsafta tayi karatun ta inda ta zama cikakiyar doctor na yara, Kai sai sun baku sha’awa rayuwar su,KAMAL KABIR shine sunnan shi, su biyu iyyayen shi suka haifa shi da k’anin shi AFAN d’an shekara 10, KAMAL kyakyawan saurayi ne bak’i ne sai dai ba bak’i sosai ba, Yana da saje da siririn hanci, shekarun shi 25, tare sukayi karatu da FAWAS aminin shi kenan, mahaifiyar KAMAL mace ce mai kirki da son mutane ga ladabi da biyyaya, mahaifin KAMAL wato Kabir bashi da hali me kyau, bai damu da abin da iyyalan shi zasu ci ba,gashi basu da hali, Dan wani lokacin har sana’a maman KAMAL takeyi domin ganin abin da yaranta zasu ci da taimakon Dad d’in FAWAS ya gama makaranta dan tun suna yara shi ke d’aukan nauyin karatun shi har ya girma Kuma shi yayi mai hanyar samun aiki a wani company, KAMAL Yana da fara’a da son mutane, da yayi y’an mata ayi ta hiran soyyaya sai dai FAWAS ba ruwan shi har fad’a sukeyi idan FAWAS yace mai ya rage yaudaran Mata da soyyayar k’arya tunda ba auren su zaiyi ba,Had’uwan NUWAIRA da KAMAL ya samo asali ne lokacin da taje yin shopping,shi Kuma kasancewar duk inda za suje suna tare da FAWAS dan aminan juna ne sosai,Har zata wuce sai taga FAWAS Nan ta tsaya suka gaisa kasancewar Mommy’n FAWAS da mom d’in ta k’awayen juna ne,Kuma suna zuwa gidan juna, bayan sun gaisa ta tafi ne KAMAL duk ya rud’e dan lokaci d’aya yaji wani irin k’aunar ta ya shiga zuciyar shi, Nan ya dinga ma FAWAS magana akan ya taya shi neman hanya dan NUWAIRA ta so shi,Ashe ita ma NUWAIRA ta tafi da son shi a zuciyar ta, har taje gida tunanin shi takeyi, bayan kwana biyu,KAMAL ya damu FAWAS sai ya kaishi gidan su NUWAIRA, shi ko bai cika son zuwa gidan ba dan bai cika magana ba,gashi baya shiri da mom a cewar shi mai zaije yayi a gidan,Da KAMAL ya matsa mai dolle sukaje gidan, NUWAIRA ko taji dad’in ganin su duk ta rud’e sai farin ciki takeyi, anan dai ya furta mata kalmar so Kuma ta amince da shi,Soyyaya ce mai k’arfin gaske yake tsakanin su, lokacin da Mom ta gano cewa soyyaya sukeyi Nan tasa akayi mata bincike ko waye KAMAL, bayan anyi mata bincike aka sanar da ita ai talakawa ne,ranta ko ya b’aci ko da ta gaya ma Dad cewa yayi to shine mai su talakan ba mutane bane, ita fa Sam bata amince y’ar ta tayi soyyaya da talaka ba Dan haka ta gaya ma Abba Nan shima yace Kar ta yarda Kuma shi da kanshi yace ta raba su,Mom ta hana NUWAIRA driving sai da driver dan ya dinga kula da ita kar ta had’u da KAMAL, ita ko sai ta ba driver kud’i tace kar ya fad’a,shine take Kiran KAMAL Dan su had’u, to da yake shi Kuma bai da mota sai yana Kiran aminin shi FAWAS Dan dama duk inda zasu tare suke, *WANNAN KENAN*👌🏻*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:21 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *9*~*10* *Sun* shak’u da juna NUWAIRA da MEENAL duk inda zasu cikin makarantar suna tare, haka kuma su KAMAL suna zuwa makarantar, tsakanin MEENAL da FAWAS sai harara dan ko kad’an basa shiri, KAMAL yana yawan yin ma MEENAL harka sun Saba da juna,A yau ne sukayi dasu NUWAIRA cewan zasu zo su kaisu shopping,haka ko akayi sun had’u a cikin makaranta,NUWAIRA ce sanye cikin matsatsun riga da wando sai gyale da ta rufe rabin gashin ta ga Sunglass da tasa, yayin da MEENAL ke sanye cikin riga da skirt na wani material sai dai tasa hijab iya gwiwa,Gaisawa sukayi sannan suka shiga mota,suka nufa SAHAD STORE, duk abin da suke so suke zab’a ita dai MEENAL tafi d’aukan abubuwan ciye-ciye, sai NUWAIRA ke bata wasu abubuwan, bayan sun gama ne,suka biya Restaurant suka d’an yi lunch dayake rana tayi,Ko da suka dawo makaranta har hostel NUWAIRA ta raka MEENAL, sannan suka wuce,Bayan wani lokaciSuna ta Shiri zasu fara exams, ga NUWAIRA ba wani Mai da hankali take a karatu ba,Nan ta rok’i alfarman MEENAL da ta dinga kwana a gidansu tana koya mata karatu, nan ta amince,ta shirya suka nufa gidansu NUWAIRA,Gida ne babba Mai shegen kyau, ga wasu flowers da suka k’awata cikin gidan,a parking lot driver yayi parking inda su MEENAL suka fito, cikin farin ciki taja hannun MEENAL tace” you’re highly welcome to our house”Murmushi tayi kawai tana mamakin kyawun gidan tun bata shiga ba, straight parlour’n gidan suka shiga,Mom na zaune tana ta faman aiki a laptop, Jin wata murya da ba zata tab’a mancewa bane yasa ta mik’e tsaye ba shiri, wata kyakyawar budurwa ta gani tare da NUWAIRA, K’arasawa ciki sukayi yayin da NUWAIRA ke cewa”mom ga friend d’ina”MEENAL ta gaishe ta cikin sanyin muryan ta,ba k’aramin rikicewa mom tayi ba dan maganar su iri d’aya da ZAINAB, da k’yar ta dai-dai ta kanta ta amsa cikin k’arfin hali,Zama sukayi yayin da Mai aiki ta kawo musu drinks, da k’yar mom tace” ke y’ar nan garin ce?”Da sauri NUWAIRA tace”No mom a wani k’auye take karatu ne ya kawo ta nan”Ba haka mom taso ba gaba d’aya bata son y’ar ta na hurd’a da talakawa, sai dai ba yanda zatayi tunda karatu zata dinga koya mata zuwa su fara exams,NUWAIRA ce tace su nufi bedroom dan su huta, nan suka shiga bedroom,Masha Allah shine abin da MEENAL tace a ranta,dan kamar Kuna k’asar waje ne tsabar had’uwan bedroom d’in,babba ne sosai, akwai wani corridor ta ciki akwai wani toilet da wani bedroom Kuma Wanda Kaya ne dasu takalma da handbags ne, Kai gaskiya an kashe ma bedroom d’in NUWAIRA dukiya, Wanka tayi sannan tace ita ma taje tayi, ai da ta ga toilet d’in ba k’aramin kyau yayi mata ba gashi komai orange and white colour ne, haka tayi wanka ta fito, can hannun ta NUWAIRA tayi ta shigar da ita d’akin kayan nan tace ta zab’a duk abin da take so ta d’auka tayi amfani da shi,Da k’yar ta d’auka wasu dogayen riguna na English wears tare da veils d’in su, Da missalin k’arfe 8:00pmDuk sun halara a dinning table don yin dinner, sai dai Babu MEENAL dan cikin ta na ciwo shine aka Kai mata nata bedroom,Da sauri NUWAIRA ta nufa upstairs dan bata son barin MEENAL ita kad’ai tunda ba ta jin dad’i, cikin mamaki Daddy yake tambayar mom ko lafiya NUWAIRA ke sauri haka, Nan ta fad’a Mai komai, yaji dad’in yanda yanzu NUWAIRA ta maida hankali tana son karatu, Two days laterSosai takejin dad’in yanda MEENAL ke koya mata karatu gashi tana ganewa, sannan tana jin dad’in zama da MEENAL ita ma haka take jin dad’in zama da NUWAIRA, Kuma har yanzu basu had’u da Daddy ba,Ranar suna zaune a parlour sai ga Daddy ya dawo, kallon MEENAL yayi nan take yaji k’aunar yarinyan bai san meyasa ba, cike da ladabi da biyyaya ta gaishe shi,ya amsa cikin farin ciki, gaskiya zai so NUWAIRA tayi k’awance da wannan yarinyan mai ladabi Dan iyyayen ta da gani sun bata tarbiyya nagari, wucewa yayi yana murmushi,Sun fara Exams, sun dage sosai ba wasa sun maida hankali, har suka gama lafiya sai jiran results, MEENAL ta shirya kayanta dan tafiya k’auye, NUWAIRA Kuma tace sai ta Kai ta har gida duk da Mom ta hana ta amma tak’i,K’arfe 2:00pm suka Isa k’auyen, a k’ofar wani gidan k’asa driver yayi parking, NUWAIRA tayi mamaki sosai dama nan friend d’in ta ke Rayuwa wannan ai ko gidan Mai aikin su sai yafi wannan,haka ta suka shiga daga ciki,Ummie na zaune a tsakar gida tana tankad’en garin tuwo, sai ganin y’ar ta tayi MEENAL, cikin farin ciki ta k’arasa tace”Ummie na I really miss you” cike da k’aunar y’ar ta take mata barka da dawowa,D’aga kan da zatayi sai taga wata kyakyawar budurwa lokaci d’aya taji k’aunar ta Nan tace”Bissmillah shigo” ta mik’e tare da gyara tabarma, zama NUWAIRA tayi ta gaishe ta cikin farin ciki ta amsa nan tace” ke haka akeyi MEENAL sai ki shigo ki bar ta?”Cikin dariya tace” No ba haka bane Ummie na farin cikin ganin ki ne, sorry NUWAIRA”Murmushi kawai tayi, Nan MEENAL ta kawo ma NUWAIRA ruwa duk da tasan da wuya tasha tunda bottle water taga take Sha, ga mamakin ta sai taga ta sha, Bayan sallar la’asar ne, NUWAIRA tayi musu sallama zata tafi, cike da kulawa Ummie tace”tafiyan dare zakuyi gashi yamma yayi da kin hak’ura kin kwana zuwa gobe Kar kuyi dare”Murmushi tayi tace”ba komai,”Haka sukayi sallama NUWAIRA ta shiga mota suka d’auki hanya,yayin da take jin k’aunar mahaifiyar MEENAL a ranta bata san meyasa ba,ko don ta nuna kulawar ta gare ta ne, Sai bayan isha’i ne Kaka ya shigo gidan, ganin MEENAL ta dawo yayi farin ciki sosai, can sai ga Aliyu da yake gidansu na kusa da nasu MEENAL ne, cikin farin ciki suka gaisa Nan akayi ta hira cikin nishad’i,****************** Kwance yake kan bed,yayi zurfi cikin tunani a gaskiya yayi missing d’in ta ko dan fad’an da sukeyi, gashi sai yanzu ya gano cewa yana k’aunar ta, Dan ko rufe ido yayi sai ya ganta, d’aukan wayan shi yayi da sauri ya kira NUWAIRA yace please ta bashi address d’in inda MEENAL take, tayi mamaki amma sai ta share nan ta fad’a Mai sunan k’auyen da gidan su, godiya yayi mata ya kashe wayar,Shiryawa yayi cikin riga navy blue da black jeans,wow looking handsome, fitowa yayi, Nan ya tarar da Mommy’n shi a parlour sai faman aiki take a system,Tana ganin shi tace”FAWAS sai Ina haka naga kamar you’re in hurry?”B’ata fuska yayi yace” Mommy zanje wani guri ne”Mik’ewa tayi tace” What how many times have I told you not to call me Mommy, meyasa kake son tsufar da nine haka da wuri?”Rik’e Kan shi yayi dan ya Saba da halin Mommy’n nashi, Dad d’in shine ya shigo yana dariya yace” my son meyasa kake tsufar min da mata ne wai?”Murmushi yayi yace”Dad she’s already old”D’auko pillow tayi ta jefa mai, tunda ya fad’i abin da ta tsana, Dad ne yayi saurin tarewa yace FAWAS ya tafi abin shi, fita yayi ya shiga mota yana ma Mommy’n shi dariya,Cikin lalashi Dad yace” ai Mata ta bata tsufa, ko ya Kika ce my one”Hararan shi tayi da wasa tace”bayan sai da ka gama goyon bayan shi”Da sauri ya k’arasa yana lalashin ta,Lokacin da ya Isa k’auyen bai wani Sha wahala ba ya gane gidan, parking yayi ya fito, wani yaro ya samu ya aika ciki ya kira MEENAL,Ummie ce zaune a tsakar gida, yaron ya fad’in aiken da akayi mai, tambayar shi tayi ko wane ne Nan yace ai wani Mai mota ne Mai kyau,Jin haka sai Ummie taji tsoro Kar dai yarinyan Nan ta fara soyyaya da maza ne, d’aukan hijab tayi ta fita Dan ta ci mai mutunci,Yana zaune kan mota sai ga Ummie ta fito, kallon shi tayi tace”Kai lafiya dai,meye ne kake neman MEENAL?”Saukowa yayi ya gaishe ta cikin ladabi, amma ya rasa wani amsa zai bata,Ummie tace”to Bari in gaya maka, ni y’a ta ba irin marasa kamun Kai bane,tukuna ma wai tsaya, mai kazo yi a k’auyen nan?”MEENAL ce ta dawo daga aiken da akayi mata,da mamaki ta k’arasa gurin ganin FAWAS, Ummie na ganin MEENAL tace”wuce kema ki shiga ciki gani nan zuwa kanki”Cikin rashin fahimta tace”meya faru ne Ummie na?”Tace”rufe min baki a Ina Kika san wannan da yake neman ki?”Dariya tayi tace”oh ai d’an’uwan NUWAIRA ne shi”Jikin Ummie ne yayi sanyi tace”shine bakayi min bayani ba ka barni Ina ta massifa, to ai sai ki wuce ki kawo tabarma da ruwa”Shigewa ciki tayi yayin da Ummie tace”kayi hak’uri kaji rashin sani ne,ai NUWAIRA yarinyan kirki ce”Murmushi yayi yace ba komai, ta yaba da halin shi a lokacin Nan take tambayar shi ko Yana zuwa makarantar su MEENAL ne dan tasan idan MEENAL bata yin samari ko k’awayen banza, shine yace Yana zuwa ba sosai ba Kuma MEENAL bata da k’awaye bare samari, ta yarda da shi Nan ta bashi amanar MEENAL ta Kuma rok’e shi da ya dinga kula da ita, ya Kuma amince,Shiga ciki Ummie tayi ya rage daga ita sai shi, Tace”Ya akayi kasan gidan mu ne?”Kawar da Kai yayi yace”ban sani ba”Tab’e baki tayi tace”to ai ya rage naka,yanzu dai yasu KAMAL dafatan suna lafiya?”Yace”lafiya suke”An d’auki 15minute bai k’ara magana ba can ya mik’e tsaye yayi mata sallama, godiya tayi Mai na ziyaran da ya kawo mata, Nan ta shiga gida yayin da shi ya d’auki hanyar cikin Abuja,Da daddare suna zaune ana Hira ana cin tuwo miyar kuka da yaji dadawa, Ummie ce ta fad’a ma Kaka Wanda yazo,inda yace”to ke in Banda abin ki ai ya Kamata ki bar yarinyan Nan ta tsayar da mijin aure amma inkin Hana ta soyyaya kenan baza tayi aure ba ko sai karatu?”Tace”ba haka nake nufi ba,Ina son dai ta natsu ne guri d’aya Kar ta had’a soyyaya da karatu”Yace”Eh na fahimce ki,in ma ta tsufa a gida ai sai muyi auren mu ko Mata ta?”ya k’are da dariyan Wasa,Turo Baki tayi tace”Allah ya kyauta, gara ka samu wata tshohuwa dai-dai da kai,ka aura,tunda kak’i aure”ta wanke hannun ta ta shiga d’aki, dariya yayi yace ai gara ta dage ko ya bada ta sadaka tunda tace ya tsufa,*Nima nace da gaskiyar ka Kaka*😂 *Ban ganin Comment d’in ku Fan’s kunsan shi ke k’arfafa min gwiwa*👌🏻*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *11*~*12* *A yau* ne hutun su ya k’are sai shiri MEENAL takeyi,ga wani irin kewa da take ji,haka dai ta cigaba da shiri, Ummie ta had’a mata wasu abubuwan da zata b’ukata har miyan kaji tayi mata dan dai y’ar nata tayi farin ciki,Bayan ta shirya ne ta zauna tayi tagumi gaba d’aya sai taji bata son rabuwa da Ummie’n ta, Kaka ne ya shigo gidan ganin halin da take ciki sai ya fara mata nasiha, sannan Ummie ta shigo, ita ma wani iri take ji dauriya kawai take yi,MEENAL na ganin ta, ta rungume ta tare da fashewa da kuka, cikin muryan kuka tace”Ummie na ki gafarce ni idan nayi miki wani abu?”Mai da hawayen ta tayi tace”Babu abin da kikayi min fatana Allah ya sa ki gama karatun Nan lafiya Allah yayi Miki albarka ya kare min ke a duk inda kike”Nan tayi mata nasiha sosai har jikinta yayi sanyi, sannan Kawu Aliyu shi ya rakata har tasha inda ta hau motar Abuja,Bayan ta shigo cikin Abuja ne,tana cikin taxi sai ganin tayi an had’a go slow, fitowa tayi Dan ganin meke faruwa,Wani almajiri ne gurgu ne ga wasu mutane sun tsatsaya ana ba mai motan hak’uri wanda ko bud’e glass d’in motan baiyi ba sai driver ne ke faman yin massifa,K’arasawa MEENAL tayi take tambayar mene ne ya faru,Nan wata tshohuwa ke Mata bayani wai yaron ne yana zai tsalake titi shine Mai motan yazo da gudu ya kwashe shi sai da ya buge shi gashi har yaji ciwo amma Mai motan Sam yace ba ruwan shi sai ma yaron ya biya shi Dan ya bugi wata mota ga yaron Kuma na b’ukatar akai shi hospital Dan yaji ciwo, to duk da driver suke magana akan sai ya Kai yaron hospital,shine yak’i,Cikin mamaki tace”to ina Mai motan?”Wani mutum yace”ai yana ciki azalumin” MEENAL ta nufa motan tare da dukan glass d’in motan da k’arfi tana cewa sai mutumin ya fito,Cikin jin haushin wace ke buga mai glass ya sauke glass d’in,masu karatu ko kun san wane ne, ABBA ne,Kallon shi tayi tace”Alhaji Sam wannan abin da kakeyi ba girman ka bane,ya Kamata ka d’auki yaron nan zuwa hospital gudun Kar wani abu ya same shi”Cikin fushi yace”ke dan uwarki wa kike gaya ma haka ko gidan ku ba manya ne idiot kawai” ya d’aga glass d’in sama,Taji haushin yanda ya zage ta sai dai tana tausaya ma yaron nan, k’ara dukan glass d’in tayi tace”Alhaji ka fito ka Kai yaron nan hospital,ka had’a go slow”Cikin fushi ya fito motan yace”ke wace irin mara tarbiyya ce?”Tace”tarbiyyan da na samu Mai kyau ne yasa har ina iya yin maka magana,ya Kamata kaji tausayin talakawa Dan abin da kakeyi bai dace ba”Nan dai mutane suka tasa shi a gaba sai da ya Kai yaron hospital, sosai Abba yaji haushin yarinyan Dan yace Bata da tarbiyya, MEENAL Kuma ta shiga taxi aka nufi makaranta da ita,NUWAIRA ranar da suka fara lecture taga aminiyar ta taji dad’i Nan sukayi ta hiran yaushe gamo,Haka sukaci gaba da karatu inda duk weekend MEENAL a gidan su NUWAIRA takeyin shi,Mom najin haushin ta Amma ba yanda zatayi,Dad koh yana Jin k’aunar MEENAL a zuciyar shi kamar ita din,jinin shi ce kamar ita d’in *ZURI’A D’AYA* suke,Rana d’aya kwatsam mom ta gano cewa NUWAIRA Bata rabu da KAMAL ba ranta ya b’aci sosai haka tayi ta mata fad’a tace Kuma dole ta rabu shi,dan ko mutuwa zatayi baza ta aura KAMAL ba Dan tafi k’arfin shi,Hankalin MEENAL ba k’aramin tashi yayi ba da taga halin da NUWAIRA take ciki, ji takeyi duk lokacin da NUWAIRA ke cikin bak’in ciki ita ma tana cikin bak’in ciki haka idan farin ciki NUWAIRA ke ciki to ita ma tana ciki,ji takeyi kamar ita d’in jinin tace, haka ta dinga bata hak’uri tana mata nasiha akan tayi ma iyyayen ta biyyaya Kar ta bijire musu,Mik’ewa tsaye tayi tace”do you know what you’re saying,kina nufin in hak’ura da KAMAL never bana Jin zan daina son KAMAL har k’arshen Rayuwa ta”ta fashe da kuka,Cikin lalashi tace”nasan baza kiji dad’i ba amma Ina son kawai kiyi ma iyyayen ki biyyaya ne”Cikin fushi tace”to bazanyi musu ba idan har akan KAMAL ne”ta tashi ta bar bedroom d’in,Washegari da suka shiga makaranta NUWAIRA ta kira KAMAL a waya cewan yazo su had’u a makaranta, ba tare da b’ata lokaci ba yazo, tana ganin shi ta fashe da kuka tana gaya Mai abin da mom tace Kuma ita gaskiya baza ta iya rabuwa da shi ba, hak’uri ya fara Bata yace tunda mom na ganin haka suyi Dan nesa da juna Dan mom taga kamar sun rabu inyaso sai su cigaba da soyyayar su,Cikin kuka tace dama kawai ba sonta yake ba Dan Mai zai ce haka,barin gurin tayi da kuka, MEENAL dake gefe duk tausayin NUWAIRA ya Kamata,KAMAL ne ya k’arasa gurin ta Yana cewa”Dan Allah MEENAL ki taimake Ni ki fahimtar da friend d’in ki,ta fahimci Mai nake nufi”Murmushi tayi Wanda ya k’ara mata kyau tace”karka damu zanyi mata magana Kuma zata fahimci Mai kake nufi,Ni nasan Kuna k’aunar juna baza ku iya rabuwa ba”Yaji dad’in kalaman ta a gaskiya takan burge shi yace”okay nagode sosai naji dad’in maganar ki”Murmushi tayi sukayi sallama ta nufa gurin NUWAIRA dake ta faman kuka a cikin hostel, hak’uri ta fara bata sannan tace ta yarda da abin da KAMAL yace tasan KAMAL ba zai yaudare ta ba,Cikin kuka ta rungume MEENAL tana cewa”MEENAL Ina son KAMAL ki taimake ni Kar in rasa shi”Zuciyar MEENAL na wani irin suya da d’aci dan tun ranar da ta had’u da KAMAL take jin k’aunar shi,sai dai bata son ta cin amanar NUWAIRA wace take son ta tsakanin ta da Allah Kuma tana son NUWAIRA kamar yar’uwan ta, tabbas taji zafi yanda zuciyar ta ke son KAMAL Kuma zatayi k’okari taga ta cire son shi a ranta, *TOH FA*🤔*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *13*~*14**Tun daga* wannan ranar sai ya zama ba ko da yaushe NUWAIRA da KAMAL ke had’uwa ba yayin da FAWAS ke yawan Kai ma MEENAL ziyara, sai dai ya kasa fitowa fili ya gaya mata son da yake mata,Bayan wasu kwanaki ne Ummie ta kawo ma MEENAL ziyara a makaranta, sosai MEENAL taji dad’i sai farin ciki takeyi,sai ga FAWAS yazo Nan suka gaisa da Ummie, har yace shi zai mai data idan zata koma,haka akayi kuwa, lokacin da zata tafi yazo ya d’auke ta, MEENAL kamar zatayi kuka tace ita ma sai ta raka Ummie tunda yau basu da lecture,Nan ta shiga mota FAWAS na tsokanar ta, sai da ya biya da su wani Store mai kyau Dan yayi musu shopping,Shiga sukayi inda suke d’aukan abun da yayi musu duk da Ummie ba son haka Dan tace ya barshi yak’i, MEENAL ce ke d’aukan mata komai, b’angaren performs suka shiga, FAWAS yace ma MEENAL tazo su duba wani abu ta d’aya b’angaren, Nan suka bar Ummie a gurin tana duba wasu performs da tasan NASIR na so, ganin wani turaren shi da yake massifar so na TOUCH ME, Kai hannu tayi zata d’auka yayin da shima ya Kai hannu zai d’auka, hannayen su ne ya tab’a juna wani irin shock sukaji yayin da a lokaci d’aya suka d’ago Kai,Ido cikin Ido sukayi, fuskar da ya Jima Yana son gani, fuskar da ya tafi ya barshi tsawon shekaru goma Sha takwas, ji yakeyi kamar ba ita d’in bace,Yayin da Ummie ta shiga tashin hankali da rud’ani har abada baza ta manta da wannan fuskar ba, tabbas wannan NASIR ne mijinta Kuma mahaifin y’ar ta AMINA, cikin tashin hankali ta juya domin barin gurin, saurin Kiran sannan ta yayi domin tabbatar da cewan ko ita ce, “ZAINAB kece?” abin da ya fad’a kenan,Juyowan da tayi ne ya tabbatar mai da cewan tabbas wannan ZAINAB ce, k’afar tane ya d’auki rawa domin ta rud’e sosai,K’arasawa yayi har gaban ta yace”Ashe akwai ranar da zaki gudu daga gare ni, ZAINAB why yanzu ma tafiya zakiyi ki bar Ni?”Gaba d’aya ta rasa abin da za tace, magana ya k’ara yi yace”Zainab kiyi min magana”Da k’yar tace”Naam”Cikin zak’uwa yace”Zainab Ina abin da Kika tafi min da shi,Ina nufin abin da Kika haifa?”Rasss taji gaban ta ya fad’i sai yanzu ta dawo hayacin ta, d’aurewa tayi tace” abin da na haifa ya rasu”Gaban shine ya fad’i,yayin da ta cigaba da cewa”bayan Bari na gidan ka Ina cikin mota Dan tafiya wani k’auye shine mukayi accident lokacin da aka kaini hospital akayi min aiki aka ciro namiji amma ya rasu” ta shararo k’arya,Jikin shine ya d’auki rawa sai da ya dafe bango cikin tashin hankali yace”Amma meyasa baki dawo kin sanar da mu ba,meyasa zaki tafi ki bar mu cikin tashin hankali da damuwa, yanzu kina wani guri ne Kuma Mai kikeyi anan?” Ya jero Mata tambayoyi lokaci d’aya,Ta rasa mai zata ce mai addu’a takeyi a zuciyar ta Allah yasa Kar MEENAL tazo ta ganta da Nasir da sauri tace”Ni yanzu ba anan nake ba sai anjima”tayi hanyar fita, da sauri yabi ta yana cewa ta bashi number’n ta, duk ta rud’e Nan ta bashi number’n tare da fita da sauri, dafe Kai yayi cikin damuwa ya bar gurin,FAWAS da MEENAL ko wani b’angaren flowers ne kala-kala ya kai ta, gurin ba k’aramin kyau yayi Mata ba, haka ya dinga d’auka Yana bata sai hira sukeyi shi ko yana Jin wani irin k’aunar ta a zuciyar shi, lokacin da suka fito basu tarar da Ummie ba, sai suka nufa gurin mota, ganin ta sukayi ta jingina da mota hankalin ta a tashe,da sauri MEENAL ta k’arasa tana tambayar meya same ta,ganin Kar su zargi wani abu sai ta daure ta cire komai a ranta, tace musu ba komai, nan suka d’auki hanyar k’auye,Har cikin gida suka shiga, inda suka d’an huta suka d’auki hanyar Abuja Dan basu so dare yayi musu,K’arfe 6:00pm suka shiga Abuja direct School ya Kai ta,bayan ya ciro wani zoben gold Mai shegen kyau a jiki an rubuta ANA UHUBIKI,da kalmar larabci yasa mata a yatsan ta yayi bala’in yin mata kyau dama dan ita akayi, duk da Bata san ma’anar bata zoben ba amma taji dad’i sosai har tayi mai godiya nan suka yi sallama ta nufa hostel, murmushi yayi cikin farin ciki ya nufa gida,Ummie ta kira baban ta suka zauna har da Aliyu ta fad’a musu had’uwan ta da NASIR har da k’aryan da tayi mai, da farko fad’a Kaka yayi yace Hakan bai dace ba,da ta fad’a gaskiya Kuma tunda ta bashi number’n ta to tabbas zai neme ta, Kuma lokaci yayi da zata bashi y’ar shi domin gaskiya ta raba mahaifi da y’ar shi, kuka tayi-tayi ita a gaskiya bata son rabuwa da MEENAL gaskiya bata shirya bada MEENAL ba, Kaka yace ai ya rage nata dan a gaskiya ya gaji da goya mata baya akan abin da bai dace ba a matsayin shi na mahaifin ta Kuma Malami,Aliyu ko cewa yayi ya Kamata ta had’a MEENAL da mahaifin ta domin tayi rayuwan talakawa bayan Kuma mahaifin ta Mai kud’i ne ya Kamata yanzu taji dad’in Rayuwa da mahaifin ta, Ummie tace bata yarda ba,Tun bayan da ya koma gida tunanin Zainab da d’an shi da tace ya mutu yakeyi amma Yana ji a jikin shi cewa d’an shi na raye, mom ta lura Yana cikin damuwa ko data tambaye shi bai fad’a Mata komai ba Dan baya son hankalin ta ya tashi,Bayan kwana biyuKullum sai ya kira number’n Zainab amma bata d’aukan wayan shi, haka Kuma Yana had’uwa da MEENAL Yana Jin k’aunar ta a jinin shi,Kuma ita ma yanda yake sonta kamar y’ar shi yasa take son shi kamar mahaifin ta tare da bashi respect na mussaman, B’angaren NUWAIRA suna soyyaya a b’oye ita da KAMAL yayin da shima ta wani b’angaren yake kyautata ma MEENAL Dan tana burge shi halayyen ta kyawawa ne,FAWAS na jin k’aunar MEENAL sosai a cikin zuciyar shi sai dai har yanzu ya kasa fad’a Mata amma Yana kyautata mata da nuna Mata alamun so Wanda ita Kuma bata gane ba, yayin da zuciyar ta ke son KAMAL Wanda tak’i Bari a gane don tana fatan ta daina son shi,Bayan wani lokaciA yau ne su MEENAL suka gama jarabawa inda tayi shirin komawa k’auye, FAWAS da kanshi yazo ya Kai ta,Dan wani irin shak’uwa ne a tsakanin su na mussaman,Lokacin da suka Isa k’auyen haka Ummie tace bazai tafi ba sai ya ci abinci gashi yamma yayi,MEENAL ce ta shirya musu abinci shi da Kaka,Nan suka fara ci Dan Kaka akwai barkwanci ga Wasa da dariya, gaba d’aya Kaka ya gama gano FAWAS Dan yaga sai binta yake da kallon k’auna ga hiran da yake mata kina ji kinsan na soyyaya ne amma duk bata gano ba, Murmushi Kaka yayi yace”yaro in tambaye ka?”Yace”Eh kakan mu inaji”Gyara zama yayi yace”akwai wace kake so ne?”Cikin rud’ewa da mamakin yanda akayi Kaka ya gano shi ya fara in Ina”Eh….. Aa…. uhm… hmm ba wace na…..ke..”katse shi yayi da cewa”Kar ka damu nagane,amma da alama baka sanar ba ko?”Sunkuyar da Kai yayi cikin kunya yace”Aa”Yace”To ya Kamata ka sanar da ita domin ku fahimci juna”Yace”Inshallah”Daga Nan yayi musu sallama ya tafi cike da kewar massoyiyar shi,ta gefe d’aya Kuma mamakin Kaka yakeyi,Bayan kwana biyuDaddy ne ke faman Kiran number’n Ummie Amma Sam Bata d’aga ba, can kawai yaji an d’auka muryan namiji yaji Nan suka gaisa Aliyu yace wake magana Nan Daddy ya fad’a Mai shine, da murna Aliyu yace dama ya shigo d’akin ne yaji ringing d’in waya ita Kuma Ummie ta fita Nan yace ai shine Aliyu,Cikin murna Daddy yace” Dan Allah ka taimake ni ka fad’a min inda kuke, wallahi Ina son had’uwa da Zainab Ina son ta sake bani dama a karo na biyu,duk da jikin na bani abin da ta haifa Yana raye”Ba tare da b’ata lokaci ba Aliyu yayi Mai kwatancen k’auyen Dan shima Yana son yaga MEENAL ta rayu da Mahaifin ta, Daddy yaji dad’i sosai Nan ya shirya ya d’auki hanyar k’auye,Parking yayi a k’ofar gidan,sai ga Aliyu ya fito Nan suka gaisa sannan yaje ya fad’a ma Kaka, fitowa yayi suka gaisa inda Aliyu ya fito da tabarma ya shimfid’a sannan Kaka yaji duk abin da ya faru bayan rabuwar Nasir da Zainab inda baiji dad’i abin da sukace akan sakin Zainab ba Kuma baiji dad’in yanda Zainab ta bar gidan Nasir ba,Hak’uri sosai Daddy ya bama Kaka sannan yace ya shigo cikin gidan su had’u ayi magana har da Ummie,Ba k’aramin mamaki Ummie tayi ba da ganin NASIR, MEENAL ce ta shigo gidan dan dama Ummie ce ta aike ta, ba k’aramin mamaki tayi ba da taga Daddy, shima d’in yayi mamaki sosai,MEENAL tace”Daddy Kai ne a gidan mu?”Cikin mamaki yace”Eh MEENAL Nan gidan ku ne?”Kaka ne ya katse su day cewa”kin san shi ne?”Tace”eh Kaka ai shine Daddy’n NUWAIRA da nake zuwa gidansu”Gaba d’aya sun shiga tashin hankali ba kamar Ummie da tafi su shiga tashin hankali ashe haukan takeyi sun san juna, da sauri taja hannun MEENAL tana cewa”wuce ki shiga cikin d’aki Kar ki kuskura ki fito”Kaka ne ya daka ma Ummie tsawa yace”meyasa zakiyi haka duk wani b’oye-b’oye ya tashi lokaci yayi da za’a San gaskiya Dan bazan sa miki ido kina abin da kika ga dama ba”Cikin tsoro da rud’ewa tace”Aa baba Dan Allah Kar ka fad’a komai”Kaka ne ya jawo hannun MEENAL da na Daddy ya had’a tare da cewa” MEENAL ga mahaifin ki, NASIR ga y’ar ka wace Zainab ta haifa bayan ta bar gidan ka”Gaba d’ayan su d’agowa sukayi tare da kallon Kaka!Ummie ko zama tayi a k’asa dirshan tana girgiza kai!*Muje zuwa masu karatu This is just the beginning of ZURI’A D’AYA**TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *15*~*16**DEDICATED TO MUSAN JUNA O.H.W. & TIMES ⏱ WRITER’S**Ina rok’on Allah ya k’ara muku basira da k’warin ido tare da zak’in hannu, Allah ya k’ara zumunci da k’aunar junan mu baki d’aya, Ameen*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇*RUBUTACEN AL’ AMARI*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇*Aunty AISHA ALI GARKUWA Ina taya ki murnan Kamala litafin ki Allah ya k’ara basira da k’warin ido tare da zak’in hannu*🍇 *Up* *Up* *Up**Ke d’in ta daban ce naki ba irin nasu ba ne a gaskiya kin fad’akar Kuma kin ilmantar da mu a cikin litafin ki,Allah ya Kare ki daga sharin makiyya da mahassada Ameen sai mun ciki a sabon litafin ki*🍇*Allah ya jikan HAMMA UMAR FARUQ Allah ya raya abin da ya bari, UMMUL Allah ya raya ZURI’AR ki baki d’aya, Allah ya bar ki keda HAMMA USMAN dinki*🍇*Nagaishe ku y’an group d’in AISHA ALI GARKUWA Fans tare da RUBUTACEN AL’ AMARI Fans, UMMU BASHEER na k’aunar ku*🍇*Kallon* kaka sukayi gaba d’ayan su cikin rud’ewa, Abba ne yayi k’arfin cewa”Baba da gaske ne kana nufin MEENAL y’a tace amma ai Zainab tace yaron ya rasu?”Kaka yace” babu d’an da ya rasu MEENAL ita ce ‘yar ka, wacce Zainab ta haifa”Cikin rud’ewa da rashin fahimta MEENAL tace” Kaka nifa ban gane maganar ku ba ya za’ayi kace wai Daddy’n NUWAIRA shine mahaifina?” Gurin Ummie ta nufa wace take zaune a k’asa, rik’e hannun ta MEENAL tayi tace”Ummie na ki fad’a min meke faruwa, ba kince mahaifi na ya rasu ba to ya za’ayi Kuma yanzu Kaka yake fad’in haka?”Rushewa da kuka Ummie tayi cikin bak’in ciki, yayin da Kaka yace duk su shigo su zauna ayi magana Dan su fahimci meke faruwa,Kaka ya ganar da su komai,inda Daddy yaji wani irin farin ciki tare da k’aunar y’ar shi MEENAL, cikin kuka MEENAL ta rungume Daddy tana kuka, shafa kanta yayi Yana cewa” Y’a ta ki gafarce ni duk Ni naja komai ban zama namiji tsayayye ba a gida na da har na Bari mace na juya Ni ki yafemin keda mahaifiyar ki”Cikin hawayen farin ciki tace”ba komai naji dad’in had’uwa da Kai mahaifin na” K’ara rik’e ‘yar shi yayi cikin k’auna, yayin da Ummie ke share hawaye,Daddy ne ya d’auki waya ya kira mahaifin shi ya gaya Mai,yayi farin ciki ba kad’an ba, Nan ya kira Hajja ita ma tayi farin ciki tace Kuma ya d’auko su Ummie su zo Abuja, haka ko akayi duk suka shirya Ummie gaba d’aya kunyar had’uw take da Hajja Dan Bata san me zata gaya Mata ba, MEENAL ko tunani take ko yaya Mom zata karb’e ta, amma sai dai Daddy ya fad’a musu suna rik’on NUWAIRA ce ba y’ar shi ba ce, sosai ta tausaya ma NUWAIRA ta so ace yar’uwan ta ce,Ummie ce ta shigo d’akin da MEENAL ke shiryawa tace” MEENAL nasan da k’yar zamu dawo tare Dan nasan mahaifin ki zai rik’e ki ba zai bar min ke ba, ki gafarce ni k’in gaya miki gaskiyan da nayi”Cikin kuka” Ummie na meyasa zaki raba Ni da mahaifina tsawon shekaru goma Sha takwas, meyasa Kika samin a raina cewa Mahaifina ya rasu,meyasa Baki barni na rayu da mahaifi na ba naji dad’in soyyayan shi gare Ni da kulawar shi, duk meyasa….why ….. Ummie….. meyasa?” Kuka ne yaci k’arfin ta.Rungume ta tayi tana cewa”ki yafemin wallahi bana son a raba mu ne banyi hakan dan wani abu ba nayi ne saboda k’aunar da nake Miki kuma nake ma mahaifin ki”K’wace Kan ta tayi tace”please kawai ki k’yale ni” ta fita d’akin da sauri tana share hawaye,Ummie ko kuka ta fashe da shi ganin yanda y’ar ta tak’i yarda da ita lokaci d’aya,Sun Isa Abuja direct gidan Hajja suka tafi, already dama Hajja ta kira mom(Aisha) ta sanar mata, NUWAIRA ko lokacin da Mom ta gaya Mata sai da gaban ta ya fad’i ashe Daddy na da wata Y’a, tun bata gan ta ba taji ta tsane ta tare da wani irin kishi da taji, haka suka nufa gidan Hajja, Abba ko da yaji bai so aka gan su ba tunda su basu da mutunci a cewar shi dan shi fa har yanzu yana Jin tsanar Malam Zakariyya (Kaka),Lokacin da suka shigo parlour’n gidan kowa a razane suka mik’e tsaye,Mom ce ta nufa gurin Zainab cikin zafin nama ta Kai mata wani irin mari ji kuke taaaasssss, a firgice kowa ke kallon su, mom tace”kin cuce mu kin yaudare ni dana San abin da zakiyi kenan da bazan tab’a yarda ki auri Nasir ba wato……”Hajja ce ta katse ta da tsawa tana cewa”kina da hankali, kin san me kikeyi, kuwa duk ba kece Kika jawo komai ba saboda rashin hak’urin ki, duk kowa ta samu guri ta zauna”Ji kuke tsit dan suna shakar Hajja, zama kowa sukayi,inda Kaka da kanshi ya bud’e taro da addu’oi sannan ya fad’a duk abin da ya faru bayan barin Zainab gidan Nasir har zuwa yau,ya nuna musu MEENAL a matsayin yarinyan da Zainab ta haifa wato ‘yar Nasir,Cikin razana NUWAIRA ta mik’e tsaye tana girgiza kai tare da cewa”No it can’t be MEENAL, ban yarda ba hakan ba zai tab’a kasancewa ba, she’s my friend, Aa ba *ZURI’A D’AYA* muke ba” cikin kuka ta bar parlour’n.Yayin da MEENAL ta mik’e tsaye domin ta bi bayanta saurin rik’o hannun ta Mom tayi ta rungume ta tace” welcome back my sweet daughter dama tun ba’a haife ki ba Daddy’n ki ya bani ke halak”MEENAL hawaye kawai takeyi,ta rasa farin ciki zatayi ko bak’in ciki,Ummie ko abin da take gudu ne ya faru wato rayuwar MEENAL a hannun mom,Abba ne ya mik’e tsaye cikin tsanar MEENAL yace”yanzu wannan ita ce Yarinyan wannan marar kunyar, gaskiya ba ku bata tarbiyya ba”tsaki yaja ya fita waje,Duk basu ji dad’in abin da yace ba amma suka share, Nan Hajja taja hannun MEENAL tana farin cikin yanda Zainab tasa sunan k’anwar ta AMINA, Hmm masu karatu ranar MEENAL taga gata da k’auna, Hajja Kuma tayi ma Ummie fad’a akan tafiyan da tayi tace hakan Bai dace ba, Nan dai tayi musu nasiha sai dai Mom bata d’auka ba domin tana Jin zafin Ummie da kishin ta,Daddy ya d’auki MEENAL ya Kai ta gurin iyyayen shi,haka suka dinga murna da yake babban gida ne sosai haka aka dinga gabatar da ita gurin Yan’uwa, sannan Daddy ya Mai da Kaka k’auye Dan Hajja tace a bar mata Ummie ta kwana biyu wurin ta,NUWAIRA ko bayan ta fita parlour’n direct mota ta shiga ta bar gidan, gida ta nufa ta dinga kuka sannan ta kira KAMAL ta fad’a Mai abin da ke faruwa,yayi mamaki sosai sai dai Bai ji dad’in yanda NUWAIRA ta nuna Jin zafin dawowan MEENAL ba ko da ya tambaye ta sai ta fad’a Mai gaskiya cewan ita ba y’ar gidan bace Kuma dole taji haushin dawowan MEENAL gidan Dan tasan sai sun nuna son y’ar su a kan ta, KAMAL ya tausaya mata sosai haka ya dinga lallashin ta da bata hak’uri har ta daina kukan sannan suka yi sallama,*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *19*~*20* *Ganin* shi nayi yayi parking cikin wani madaidaicin gida.hankalin shi a tashe yake gaba d’aya. parlour’n gidan ya shiga cikin tashin hankali, wata mata ce zaune a kujera tayi tagumi da hannun ta, Jin an shigo ba tare da sallama ba yasa ta d’ago kai da sauri,KAMAL ne ya k’arasa gurin ta ya zauna ya dafe kan shi da hannu biyu yayin da yake girgiza kan shi, cikin mamakin abin da ya same shi tace” lafiyan ka kuwa ka shigo ba ko sallama, meke damun ka ne kayi min magana man?”D’agowa yayi idon shi jajazur yace”Mama ban san me zan ce ba, ban san laifin da na aikata ba aka sallame ni a aiki ba” ya k’are cikin fuskar tausayi.Ba K’aramin tashin hankali ita ma ta shiga ba Jin abin da d’an ta fad’a tace” innalillahi wa’ina illaihir-raji’un ka dinga mai-maita wannan kalmar zakaji sanyi a ranka Kuma Allah ubanghiji yasa kasa mu aikin da yafi maka alkhairi” Yace”Ameen” Haka ta dinga mai nasiha da yarda da k’adara Mai kyau da Mara kyau. Can yaji wayan shi na ringing d’auka yayi ganin bak’uwar number. Yana d’agawa abin da yaji shine” nasan kayi mamakin sallaman ka aiki da akayi to wannan k’adan daga cikin aiki na kenan idan ka shigo gona ta”Cikin rashin fahimta yace” Kai wane ne menayi maka a rayuwa da zaka sa a sallame ni daga gurin aiki na?”Dariya yayi can yayi shiru cikin Isa da tak’ama yace” yaro bai san wuta ba sai ya taka, to nine ABBA kakan NUWAIRA, kazo office na ka same ni yanzu muyi magana ko in tarwatsa rayuwar ka” ya k’ara dariya tare da kashe wayan.Ba abun mamaki bane dan yasa anyi mai haka yasan zai iya mai fiye da hakan ma, Nan ya shiga mota ya nufi office d’in ABBA.Yana zaune a kujera sai juyi yakeyi, shiga KAMAL yayi ya zauna kujeren da ke kallon na ABBA, yace”gani nazo nasan maganar ka ba zai wuce kan kud’in Nan ba dai”Dariya Abba yayi can ya d’aure fuska yace” daga yau ina son ka rabu da NUWAIRA ko kaga tashin hankalin da baka tab’a gani ba a rayuwar ka, zan tarwatsa *ZURI’AR* ka in tozar ta su idan har baka rabu da ita ba Kuma duk inda zaka shiga sai ka shiga ka biya ni kud’in da mahaifin ka ya gudu min da shi kai bari in nuna maka wani abu ma” kunna laptop yayi ya nuna ma KAMAL. wa zai gani k’anin shine cikin uniform an d’aure Mai baki da hannun shi, wani k’aton mutum ya cire mai abin da aka rufe mai baki da sauri yaron ya kalla laptop d’in course suna ganin junan su cikin kuka yaron yace” Yaya Yaya kazo ka tafi da ni zasu kashe ni pl…….” maganar ne ta katse lokacin da mutumin Nan ya rufe Mai baki yaron ko sai turjewa yakeyi,Cikin tashin hankali yace” zan zo Jamil in tafi da Kai karkayi kuka ba abin da zai same ka” Abba ne ya rufe laptop d’in Yana cewa” k’adan daga cikin aiki na kenan, kafin gobe zaka kaga wani abin Kuma idan har baka rabu da NUWAIRA ba”Kallon Abba yayi idon shi jajazur yace”kar ayi mai komai ku sake shi, ko da NUWAIRA ita ce autar mata to har abada na rabu da ita daga Rana iri na yau” cikin zafi ya k’are maganar.Dariya Abba yayi yace” hakan kad’ai zai sa ka samu kwanciyar hankali”Mik’ewa tsaye yayi yace” kasa su sake shi yanzu, ni Kuma na bar NUWAIRA”Dariyan mugunta yayi ya d’auki waya yasa aka maida Jamil makarantar shi Dan dama daga can akayi kidnapping d’in shi.Cikin bak’in ciki KAMAL ya bar gurin Yana zuwa makaranta ya d’auki Jamil suka dawo gida. Mama ta shiga tashin hankali lokacin da ta gansu Nan ta fara tambayar Mai ya faru. KAMAL bai b’oye mata komai ba ya fad’a mata. ko k’adan bataji dad’i ba haka dai tayi mai nasiha tace Kuma su barshi da Allah Kuma tace ya fita harkar NUWAIRA tunda zasu iya yin musu komai a kanta, zuciyar shi haka yake mai zafi da rad’ad’i na rashin massoyiyar shi.**********************Kafin Daddy ya fad’a ma Mom maganar auren shi da Ummie har Abba ya gaya mata Kuma yace kar ta yarda. aiko ranar ta shiga tashin hankali, lokacin da Daddy ya dawo aiki da massifa ta tare shi, tun Yana bata hak’uri har ranshi ya b’aci sukayi fad’a sosai ya Kuma tabattar mata da cewa sai anyi auren ko ba da yardan ta ba, haka tayi ta kuka tsabar bak’in ciki da kishi.MEENAL taji dad’in yanda za’ayi auren dan zata cigaba da rayuwa da Ummie’n ta guri d’aya, NUWAIRA ko bata damu ba tunda Babu mai k’aunar ta to ita ma bata k’aunar su Dan damuwar ta ne a gaban ta su k’ara ta can. a cewar ta kenan. A yau ne FAWAS ya shirya cikin riga red and black jeans yayi kyau sosai, direct gidan su MEENAL ya nufa. yana zuwa ya Kira ta a waya da k’yar ta d’auka tace mai tana zuwa. dama tana sanye cikin gown d’in material light purple, gyale kawai tasa black ta d’an fesa perform.Tun daga nesa ta hango shi yayi mata kyau sosai, k’arasawa tayi. murmushi yayi mata mai sanyaya zuciya,Gaishe shi ta fara yi sannan gurin ya d’auki shiru can yace”MEENAL nazo ne inji amsan ki, ina fatan kinyi tunani?”Da k’yar ta iya cewa” tohm da farko ina Mai baka hak’uri akan abin da zan fad’a ma, wato a gaskiya bana son in yaudare ka ko in ci amanar ka, FAWAS ina da Wanda nake so, zuciya ta tajima da son shi, ina rok’on kayi hak’uri ka manta dani ka cire soyayyar da kake min Dan Allah”Wani irin sarawa kan shi yayi ji yayi bazai iya cigaba da tsayuwa ba sai da ya dafe mota wasu irin hawaye ne suka zubo mai masu zafin gaske, MEENAL lokaci d’aya taji wani irin tausayin shi ya kamata ina ma ace ana iya controlling d’in zuciya da tayi controlling d’in zuciyar ta da ta so FAWAS dan dashi ta Dace ba KAMAL ba.Kneeling yayi a gaban ta ya had’a hannun shi guri d’aya irin mai neman alfarman Nan yace” MEENAL ki taimake ni ki amince da soyayya na gare ki, bazan iya rayuwa Babu ke ba, zuciya na yana min wani irin zafi ki taimake ni kar kice ba Kya so na Dan Allah MEENAL na rok’e ki” ya fashe da kuka, (wallahi Nima sai da nayi hawaye).Cikin hawaye tace” kayi hak’uri please” da gudu ta bar gurin tana kuka.FAWAS ya jima a gurin kafin ya iya tashi da k’yar yayi driving zuwa gida, motar ai ko parking da kyau baiyi ba ya shiga parlour,Mommy na Kitchen taji an shigo, tana fitowa taga FAWAS cikin wani irin yanayi na ban tausayi, da sauri ta k’arasa gurin, d’ago kanshi tayi tana tambayar shi meke damun shi, wani irin kuka ya fashe da shi kamar k’aramin yaro ya rungume ta, da k’yar ya iya yin magana yace” Bata so na, why why Mommy? ina son ta amma bata sona”Cike da tausayin shi tace” oh my God who is she? wace ce ita FAWAS, shin akwai macen da zata kalle ka tace bata son ka?, tell me wace ce ita ni Kuma nayi *ALK’AWARI* (my novel) sai na San duk yanda zanyi ka aure ta gaya min wace ce?”Murmushi yayi cikin hawaye yace”no Mommy I want her to love me, ba wai muyi aure tana son wani ba, Mommy zuciya na nayin min zafi” ya d’aura hannun ta a zuciyar shi, bata San lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba cikin tausayin d’an nata Kuma tayi *ALK’AWARI* duk ranar da ta gano wace yake so zata aura mai ko ‘yar wace ce kuwa Dan samun farin cikin d’an nata,Da k’yar ya iya tashi ta rakashi har bedroom d’in shi, sai da taga barci ya d’auke shi sannan ta fita,MEENAL tana shiga gida ta fad’a kan bed tana wani irin kuka, gaba d’aya duniyar wani iri take Jin ta,A kwana a tashi ba wuya, Allah ya kawo mu lokacin d’aurin auren su Daddy, Ranar asabar da missalin k’arfe 2:00pm mutane suka shaida d’aurin auren *ZAINAB* (Ummie) da *NASIR*(Daddy) akan sadaki mafi daraja, ranar duk kowa na farin ciki, banda su Mom da zuciyarta ta cika da kishi Kuma tayi tanadin zuwan Ummie, yayin da Ummie ke cikin farin ciki at least zata k’ara rayuwa da massoyin ta a karo na biyu, Kuma ta shirya yin hak’uri da duk abinda Mom zatayi mata Dan wata rana sai labari,An kawo Ummie gidan Daddy, inda taro ya watse,Bayan sati biyu da yin auren,Mom batayi komai ba a wannan lokacin Dan ta samu musu ido ne Kuma ta Kuma basu time,MEENAL na tashin hankali tana tuna Sam abin da tayi ma FAWAS bai Dace ba, haka Kuma tana tunanin KAMAL Wanda bai San ma tana son shi ba,Yayin da NUWAIRA ke cinyar rashin massoyin ta dan gaba d’aya ta rasa shi, sun daina had’uwa,FAWAS da KAMAL duk suna fama da rashin masoyiyyar su, KAMAL rayuwan shi ya canza suna buk’atar taimako Kuma yak’i nuna ma KAMAL cewa akwai abin da ke damun shi,Dan baya son ya sani,FAWAS dai yayi k’okarin ganin ya manta da MEENAL sai dai ina kamar k’ara mishi son ta akeyi a zuciyar shi,Zaune suke suna hira jefi-jefi dan kowa da abin da ke damun shi, FAWAS da KAMAL kenan aminan juna.*I need your comments👌🏻, idan kunyi comments sosai zanyi muku dayawa gobe inshallah idan Kuma ba kuyi ba shike Nan*🤷🏻♀ *Let’s get going my Fan’s*🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *17*~*18**Driver* ne yayi parking cikin gidan Hajja inda MEENAL ta fito ta shiga parlour’n gidan, da sauri Hajja ta fara mata barka da zuwa, cikin ladabi ta gaishe da Hajja, Ummie ce ta fito daga kitchen da sauri MEENAL ta rungume ta tana cewa”Ummie na ki yafemin nayi nadamar abin da nace miki”Shafa kanta tayi tace”ba komai b’acin rai ne”Nan suka had’u sukayi ta hira, ya rage daga ita sai Ummie, rik’o hannun ta tayi tace”Ummie na Dan Allah zan rok’e ki alfarma guda d’aya ki taimake ni kiyi min shi”Tace”ina Jin ki mene ne shi?”Tace” Ummie na Dan Allah ki aure Daddy na”😰Mik’ewa tsaye tayi tace”are out of your sense?, look maganar nan ta tsaya a nan bana son ki sai ke maimaita shi kinji ni ko?”Cikin marairaicewa tace”haba Ummie na ko dan ni ya kamata kuyi aure, ina son ganin ku tare please Ummie na kar kice A’a”Mik’ewa tsaye tayi ta bar gurin, yayin da MEENAL ke rok’on Allah yasa Ummie’n ta ta amince, Sai dare ta koma gida, Bayan Daddy ya gama dinner ne taje ta same shi a parlour’n shi, inda shi ma ta rok’e shi da ya aure Ummie’n ta, ai kamar ta sosa Mai inda yak’e k’aik’aiyi, yaji kuma dad’in yanda tazo mai da wannan maganar dan har ga Allah Yana son Zainab sosai,bare kuma ga ‘yar su MEENAL, cikin farin ciki yace”don’t worry inshallah zanje in same ta da maganar”Tayi farin ciki sosai tace” yauwa Daddy na I’m proud of you thanks so much”Yaji dad’in ganin yanda tayi farin ciki yace” Allah yayi miki albarka, oya yanzu kije kiyi barci dare nayi”Nan tayi mai sallama ta tafi,The following dayMEENAL na Kitchen tana had’a breakfast sai ga NUWAIRA ta shigo cikin gadara da tak’ama, indomie ta dafa tanayi tana wak’a duk Wai Dan ta ba MEENAL haushi, MEENAL ko ajikinta bai Dame ta ba, haka NUWAIRA duk ta b’ata gurin, ta tafi ta barshi haka, Da missalin k’arfe 8:00pm FAWAS yayi parking a cikin gidan su MEENAL, Kiran ta yayi a waya sai ta fito, tana sanye da Riga da skirt na wani orange less mai kyau, tasa gyale orange a kanta,Tun daga nesa ya hangota ba k’aramin kyau tayi ba, fuskar ta sai shining yakeyi, ga hasken wuta dake k’ara hasko ta, cikin natsuwa ta k’arasa gurin motan shi,Sauko yayi daga saman motan shi yace” tsarki ya tabatta ga Allah Wanda yayi wannan hallitar” Murmushi tayi cikin kunya ta sunkuyar da kan ta, Murmushi shima yayi yace”you look beautiful”Gaishe shi tayi ya amsa cikin farin ciki sannan ta shigar da shi cikin parlour’n bak’i sannan ta kawo mai drinks,Gurin ya d’auki shiru kamar na 5 minutes sannan ya katse shirun da cewa” na jima ina son gaya miki wani abu Wanda yake cikin zuciya na, zan so ki bani time dan in gaya miki”Murmushi tayi tana wasa da zoben hannun ta, saukowa yayi daga kujera ya durk’usa a gaban ta tare da cewa” ko zaki iya fad’a min meyasa har yanzu kike tare da zoben nan?” ya nuna zoben,Tace” please ka zauna tukun sai in gaya maka”Yace”no until you tell what I asked you”Murmushi tayi tana murza zoben hannun ta, tace” Yana min kyau Kuma haka kawai nake son shi”Murmushi yayi cikin farin ciki yace” AMINA”D’ago da kanta tayi cikin mamakin yanda ya Kira sunnan ta dan bai tab’a Kiran ta haka ba Kuma cikin wani irin murya,Cikin sanyin murya mai dad’in sauraro yace” zuciya na ya jima da k’aunar ki tun ranar da na had’u dake nake son ki, amma na kasa fad’a miki *I REALLY LOVE YOU MEENAL*”Mik’ewa tsaye tayi cikin tsananin mamaki dan ko a mafarki bata tab’a tunanin FAWAS zai so ta ba, ba k’aramin tashin hankali ta shiga ba, Cikin tsoro shima ya Mike’ ganin halin da ta shiga yace” Please accept my love for you, MEENAL ina miki son da bazan iya rayuwa Babu ke ba, amma zan Baki lokaci kiyi tunani da kyau”Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mata tace” ban tab’a tunanin cewa zaka so ni ba, I…. really… don’t.. know what to do….” ta k’arasa cikin kuka,Ba k’aramin tashin hankali ya shiga ba yace” no please don’t cry, zuciya na namin wani irin zafi idan kina kuka, ki gafarce ni idan magana na ya b’ata miki rai”Juyawa tayi da sauri ta bar parlour’n, direct bedroom d’in ta ta shiga ta fad’a kan bed tare da fashewa da kuka, yayin da take Jin duniyar gaba d’aya na juya mata, har ga Allah zuciyar ta na son KAMAL gashi Kuma aminin shi FAWAS na son ta, bata San ya zatayi da son KAMAL ba da take fama dashi Wanda shi bai ma San tanayi ba, Da k’yar ya iya driving yaje gida, cikin wani irin yanayi ya shigo parlour’n, Mommy na zaune tana duba wasu takardu, ganin yanda ya shigo cikin wani irin yanayi ya sa ta a cikin damuwa, kwamtar da kanshi yayi a cinyar ta yayin da take tambayar shi lafiya meke damun shi, gaba d’aya ya kasa magana idon shi yayi jajazur, zuciyar mommy ya cika da tausayin d’an nata, tayi-tayi yayi mata magana amma yak’i cewa komai,haka dai tayi ta lalashin shi da bashi hak’uri, har bedroom d’in shi ta rakashi ya kwanta sannan ta fito tana mamakin ko meke damun shi Allah kad’ai ya sani,FAWAS gaba d’aya ya rasa meke damun shi,haka Kuma ya dage da addu’a Allah yasa MEENAL ta amince da shi, ***********************Daddy yaje ya samu Ummie da maganar son a d’aura musu aure ya Kuma nuna mata cewan Yana son ta Kuma he’s serious akan auren su, da farko bata amince ba Dan gaskiya bata San abin da zai had’a ta da Mom ba, amma kusan Koda yaushe sai yazo Kuma ya fad’a ma Hajja ita ma taji dad’i sosai, haka Hajja tasa Ummie a gaba da fad’a Dan Daddy yace tak’i yarda, shine ta amince, Daddy ya samu mahaifin shi ya sanar da shi yayi farin ciki sosai Nan ya aka k’ara neman ma Daddy auren Ummie a karo na biyu,Abba cewa yayi shi Sam bai yarda ba, Hajja bata ji dad’in yanda yace ba Kuma ta nuna Mai tunda mahaifin Ummie na Nan to aure na hannun shi shine zai yanke komai, an samu Kaka inda ya amince,Nan take aka sa ranar aure bayan sati uku,*Kuyi managing wannan please**Ina baku hak’urin jina shiru kwana biyu, gaskiya Thursday and Friday ina zuwa islamiyya bana samun time dan haka ba ko wani Thursday and Friday zan dinga posting ba course bana samun time, nagode sosai da k’aunar ku da kulawar ku gare ni fans thanks ku sani Nima ina k’aunar ku*🌹 *TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *21*~*22* *DEDICATED To ALL MY FAN’S* *Oh my fan’s I’m speechless I don’t even know what to say u make me feel happy, Alhamdulillah naji sauk’i, nagode sosai da addu’oin ku gare ni, masu Bina ta private charts suna gaishe ni nagode sosai wallahi, wayyoo gaskiya Kuna k’auna na, ina rok’on Allah ya bar mu tare, I really appreciate, and ni UMMU BASHEER I love you so much my fan’s, Kuna shagwab’a ni dayawa fa ji nake kamar inyi Mai course I’m happy, sai da ku nake samun k’arfin gwiwa, NUWAIRA and KAMAL tare da MEENAL and FAWAS suna mik’o sak’on gaisuwar su gare ku gaba ki d’ayan ku massoya, thanks again for your love and support, I love you wujiga-wujiga duk wuya duk runtsi ana mugun tare ina nufin irin taren nan*🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *My Aunty Rahmat Nalele ina rok’on Allah ya baki lafiya, kiyi ta suburbud’o Mana SAMAREEN BANA course fan’s gaba d’aya ke suke jira**Sister Maimounath ke d’in ta daban ce wallahi kinfi k’arfin su na fad’i Kuma na k’ara fad’a bana tsoro ehe idan ba bomb ne zai tashi to sai dai ya tashi, Allah ya k’ara miki basira tawan da k’warin ido* *FAWAS* ya lura gaba d’aya friend d’in shi na cikin damuwa, a hankali cikin sanyin murya yace” my friend i know something is bothering you please tell me?”Jikin KAMAL a sanyaye yace” friend you know I won’t hide anything from you”Yace” no ban yarda ba common feel free and talk to me please” Bai b’oye mai komai ba game da raba shin da akayi da NUWAIRA sai dai ya b’oye mai Koran shi aiki da akayi course baya son ya tayar Mai da hankali, ya tausaya Mai course shima yana jinyar rashin masoyiyyar shi before yana cewa soyayya ai shirme ni yinshi wasting of time ne ya d’auki Wanda ke soyayya just like a mad person, but now he realized what actually true love is, Magana ya fara cikin tausayin friend d’in shi yace” na tausaya maka sosai, before I was saying love is useless thing but now I realize what love is, friend Allah yasa ka samu NUWAIRA course I know she’s your happiness” Ya fahimci cewan akwai abin da ke damun FAWAS, Nan ya tambaye shi meke damun shi, amma yak’i fad’a mai sai da k’yar yace” I know idan na fad’a ma you will laugh at me bare kuma I’m rejected by the woman I truly loved” kasa magana yayi dan tuno da abin da ya faru between him and MEENAL.Cikin mamakin abin da ya fad’a yace” don’t tell me wacce kake so bata son ka?” Kamar ya fashe da kuka yace” yeah friend I really love her and I don’t want to lose her yazan yi please?” Lokaci d’aya idon shi ya canza colour zuwa red.Hak’uri tare da lalashin shi ya fara har zuciyar shi yayi sanyi sannan yace” inshallah zan ta yaka da addu’a Allah ya zab’a maka mafi alkhairi a rayuwar ka, but tell me who’s this beautiful woman that you are dying for her?”Dukan wasa ya Kai mai yace” I don’t know, kar ka sani a gaba da tsokana”Ai ko dai bai fad’a mai ba, suka d’an yi hira daga k’arshe FAWAS ya kai KAMAL har gida, *************** **************Cikin dressing d’in ta na Arabian gown black tayi rolling d’in veil akan ta, light make up tayi, amma tayi mugun kyau, cikin sauri-sauri ta sauko downstairs ta nufi dining area inda duk aka had’u ana break fast, gaishe su tayi, sannan ta fara breakfast d’in ta, tunda ta sauko downstairs NUWAIRA take Jin wani irin bala’in haushin ta, mik’ewa tsaye tayi zata bar gurin da sauri Ummie ta rik’o hannun ta tace” Ayya please ki gama breakfast sai ku wuce tunda MEENAL ta shirya”Wani dogon tsaki taja tare da k’wace hannun ta da k’arfi ta bar gurin, dan gaba d’aya haushin Ummie takeji,Girgiza kai Daddy yayi a zuciyar shi cewa yake wannan wani irin tarbiyya ne Aisha ta ba yarinya nan?, tsaki yayi ya bar gurin, Ummie bata ji dad’in abin da NUWAIRA tayi mata ba ita dai Allah ya d’aura mata son yarinyan a zuciyar ta,Mik’ewa tsaye MEENAL tayi tana musu sallama, lokacin da ta fito waje ta tarar da NUWAIRA tsaye a jikin mota ran ta a b’ace yake k’arasawa tayi tace”I’m sorry sister na miki wasting of time”Tsaki taja tace” you are very stupid, don’t pretend to love me as your sister course I will never forget how you betrayed me” Girgiza kai tayi tace” wallahi banyi betraying d’in ki ba believe me, buri na d’aya shine inga mun dawo yanda muke a da please try to understand me”D’aga hannu tayi alamar bata son wani magana, ta shige mota. da sauri driver ya k’araso. MEENAL ta shiga ya wuce da su school. After four hours Cikin gajiya ta k’arasa gurin parking lot d’in course a gajiye take dan lectures d’in yau me zafi ne, cikin riga da wando na shadda white colour yayi kyau sosai ta hango shi. Ko a mafarki bata tab’a tunanin cewa zata gan shi ba.Murmushi ya sakar Mata, k’arasawa tayi tana cewa” are you really the one KAMAL?”Dariya yayi yace”yeah I’m the one, two days bana ganin ki so I decided to come here mu gaisa” ya k’are maganar yana waige-waige alamar yana neman wani abu.Murmushi tayi cikin farin ciki tace” ayya ka kyauta sosai ya aiki ya mama da my little brother”Amsawa yayi cikin jin dad’in yanda ta nuna kulawar ta ga abin da duk duniya bashi da kamar su wato Maman shi da k’annin shi yana son su sosai, Nan suka fara hira suna dariya cikin nishad’i, abin da basu sani ba ashe NUWAIRA na kallon su tun fitowan MEENAL ta fito Kuma ta gansu, zuciyar ta ne ke tafasa tana jin wani irin kishi, abin da yafi bata haushi yanda KAMAL ya nuna kamar bai ma san tana makarantar ba. duk da cewan an raba su. Sallama KAMAL yayi ma MEENAL ya tafi, a lokacin ne NUWAIRA ta iso cikin b’acin rai ko kallon ta batayi ba ta shige mota tana had’a rai,Murmushi kawai MEENAL tayi dan ita gaba d’aya tana cikin farin cikin ganin KAMAL ne.Hmm masu karatu guess what? in taik’aita muku dai kusan Koda yaushe sai KAMAL yazo sun gaisa da MEENAL inda shak’uwa ya shiga tsakanin su. Yayin da a Koda yaushe zuciyar NUWAIRA ke cika da bak’in ciki da kishi mai zafi. gashi tana ganin gaba d’aya kamar KAMAL ya manta da ita ne yana rayuwar shi,Abin da bata sani ba shine. Kullum da sonta yake kwana Kuma yake tashi, plan ya had’a na ganin ta wato kullum zai had’u da MEENAL to yasan tabbas zai gan ta. Shiyasa da ya fara zuwa yake ta waige-waige yana neman ta. tunda an raba shi da ita shi Kuma zaiyi k’okari ya dinga had’uwa da ita ta hanyar MEENAL. Abin da ya lura shine MEENAL ta na da kirki tana son Maman shi k’annin shi. tana kyautata mishi sai ta fara burge shi. Ba wai Yana son ta bane No kawai he likes her behaviors ne. MEENAL ko ji takeyi kamar something is missing in her life. But she don’t know ko mene ne. Haka Kuma tana jin KAMAL a ranta Kuma tafi tausayin shi course yanzu tasan komai a kanshi har abin da ke faruwa tsakanin shi da NUWAIRA dan ya d’auke ta like his sister shine ya fad’a mata damuwar shi. Sai dai yace Mata ya samu wani aiki. Ashe aikin kanikanci yakeyi gareji yake zuwa yayi gyara a biya shi. Wayyo ni ummu basheer na tausaya mai.Tsakanin Mom da Ummie kuwa Babu abin da yake had’a su na shiri, ita dai Ummie zata gaishe amma sai taga dama take amsawa. Dan ma bata da time bata cika Zama a gida ba kullum tana office.**************************** A yau ne suka Kamala karatun su inda suka fito da results mai kyau. Daddy yaji dad’i sosai haka yayi ta sa musu albarka. KAMAL yazo gurin sai dai a b’oye ya ba MEENAL gifts. NUWAIRA ko kamar zatayi hauka ranar tasha kuka.MEENAL ko sai duba wristwatch d’in ta takeyi kamar tana jiran wani abu ji takeyi kamar something else is still missing in her entire life. Har taro ya watse lafiya suka koma gida.Bayan ta shigo bedroom ta cire Kaya sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito sai tunani take Wanda ta rasa na mene ne. Ta gama sa kayya kenan taji anyi banko k’ofa da k’arfi an shigo. D’ago da kan da zatayi wa zata gani. NUWAIRA ce fuskar ta yayi ja alamar tana cikin b’acin rai.Da mamaki MEENAL tace” lafiya NUWAIRA? naga kin shigo ba sallama?”Wani wawan tsaki taja tace” ank’i yin sallaman. nazo ne inyi miki warning domin na riga na gano cewan kina son KAMAL! Kuma KAMAL nawa ne ni kad’ai kinyi k’arya ki raba mu wallahi course we meant for each other” Zaro ido tayi cikin mamakin abin da ta fad’a tace” you are wrong, kinyi mistake ni ba son KAMAL nake ba”Tsawa ta daka mata tace”shut up your dirty mouth, kina tunanin ban Gane ba, let me warn you for the last time, ki fita harkar na ki daina shiga rayuwa ta na tsane ki, na tsane ki a rayuwa ta ina rok’on ki for God sake ki rabu da ni” ta fashe da kuka.Da sauri MEENAL ta Isa gurin ta, rik’o hannun ta tayi tace” ki fahimce ni Dan Allah wallahi ni ina k’aunar ki a matsayin ki na ‘Yar uwa ta, mu *ZURI’A D’AYA* ne”K’wace hannun ta tayi cikin zafi ta Mari MEENAL, da sauri ta fad’i k’asa tare da dafe inda ta mare ta,Cikin hawaye tace” me kike nufi da mu *ZURI’A D’AYA* ne? How comes muka zama *ZURI’A D’AYA* bayan ba jinin mu d’aya ba, na tsane ki MEENAL, I hate you” da gudu ta bar bedroom d’in, Yayin da MEENAL ta rushe da kuka. tana jin wani irin zafi a zuciyar ta course tana jin NUWAIRA kamar sister’n ta. After two weeks Mom ce take sanar da dukan su cewa zasuyi aiki a company d’in ta na manufacturing Kaya, sunyi farin ciki sosai su Daddy ma sun taya su murna. Kuma tunda company na Mom ne tace zasu fara aiki next week. Next week Monday NUWAIRA ce ta shirya cikin riga red and black skirt tayi rolling kanta da black veil sai sunglass da tasa taci heavy make-up, fitowa tayi cikin tafiyar k’asaita,MEENAL ce sanye cikin Arabian gown dark pink colour tayi rolling veil d’in akan ta, heavy make-up tayi ga wani hill shoe pink da handbag da ta sa. cike da natsuwa take saukowa daga upstairs. Kallon ta NUWAIRA tayi taja tsaki. Ummie cikin farin ciki tace”Allah yayi muku albarka Allah yasa ku fara aiki cikin sa’a”Ameen MEENAL tace ita ko NUWAIRA fita tayi a zuciyar ta tace matar nan ta cika shishigi mtwwwssss taja tsaki ta shiga mota. Mom ce da MEENAL suka k’araso tare da shiga motan jefi-jefi suna hira. NUWAIRA ko wani irin zafi takeji. Dan kafin zuwan MEENAL ita da Mom ke hira tana nuna mata so amma yanzu tana ga kamar bata son ta ne, Cikin wani babban gini na bene mai girman gaske driver yayi parking. Fitowa sukayi, tare da shiga ciki. Wani elevator suka shiga inda suka fito a 4th floor. Mai aikata ne duk suka mik’e suna musu barka da zuwa. D’aga musu hannu kawai Mom keyi, cikin farin ciki MEENAL ke amsa gaisuwar su tana murmushi lokaci d’aya sukaji ta burge su. Gurin meeting suka shiga dan kowa sun hallara su Mom kawai ake jira. Tana shigowa duk suka mik’e tare da yin gaisuwa. d’aga musu hannu kawai Mom tayi sannan suka zauna inda su MEENAL suka zauna a kujerun dake kusa da ita.Bayan kamar 5 minutes Mom ta mik’e tsaye ta gabatar musu da yaran ta wato NUWAIRA da MEENAL. tashi suka tsaye tare da gaishe da shugabanin gurin. Sannan suka zauna. Mom ce ta kalle su Nan take ta fad’a musu matsayin su a gurin aiki. Inda MEENAL aka bata PRESIDENT na gurin making Kaya sannan ita Kuma NUWAIRA matsayin VICE PRESIDENT.Duk gurin aka d’au tafi. Ana musu congratulations. Yayin da zuciyar NUWAIRA ke bugawa cikin matsanan cin damuwa da k’yar ta iya daurewa, cikin farin ciki marar missaltuwa MEENAL ke amsawa. Sai flowers ake basu.Mom ce ta nuna musu office d’in su. Na MEENAL na kusa da na NUWAIRA, office d’in yayi bala’in kyau da tsaruwa. Especially na MEENAL course she’s the President. Komai na office d’in ta orange and white ne. Yayin da na NUWAIRA komai Navy blue ne, wow ama sunyi kyau, Wasu ce aka kawo mata su biyar Wanda zasuyi dinga mata wani aikin. Baban cikin su sunan ta *HUSNA* lokaci d’aya MEENAL taji ta kwanta mata a rai. Suma gurin duk sun yaba da kirkin MEENAL. NUWAIRA wata aka kawo mata a matsayin wace zata taimake ta da wani abin sunan ta *Bilkisu* ama ana Kiran ta da BILLY, NUWAIRA k’are ma office d’in kallo tayi ta zauna a kujera tana juyawa can ta mik’e tsaye ta buga table d’in da k’arfi tace” kinyi k’arya ki fini komai hakan ba zai tab’a yuwuwa ba bazan tab’a yarda ba ni NUWAIRA nafi k’arfin ki MEENAL” ta bushe da dariyan mugunta. *TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *23*~*24* *DEDICATED TO SEEMBY LUFF*😘 *Aunty SEEMBY kina fad’akarwa tare da ilimantarwa a cikin litafin ki na SAHR-KHULAYD a gaskiya naji dad’in litafin sosai Allah ya k’ara basira da hazak’a,k’warin ido da laushin hannu Allah yasa kifi haka Allah ya kare ki daga sharin mahassada**MEENAL* ce ta iddar da sallan asubah, direct kitchen ta nufa course tana son tayi duk abin da zatayi da wuri dan bata son tayi late gurin aiki, fere dankali tayi da plantains ta fara frying, bayan ta gama ne sai ga NUWAIRA ta shigo, MEENAL tayi mamakin tashin ta da wuri har ta shigo kitchen.Yamutsa fuska tayi sannan ta d’auka wani cup ta had’a tea. Samun kujera tayi ta zauna sai murmushi take yi. tana gamawa ta fita. Har MEENAL zata fita sai ta tarar da Sauran tea d’in da NUWAIRA ta rage Wanda ta had’a amma ba Wanda tasha ba. Da yake MEENAL idan ta tashi barci sai tasha tea sannan take wanka ta Shir sai a sake breakfast da ita. Zubawa tayi a cup tare da Sha sai da ta shanye sannan ta hau upstairs. Tana shiga bedroom ta fad’a toilet tayi wanka tana cikin shafa mai taji wani irin barci komawa kan bed tayi tana tunanin ko barci lafiya ne haka dan ita idan ta tashi barci to ta tashi kenan Bata komawa, tana zaune taji wani irin mugun barci kawai sai ta fara gyangyad’i can ta kwanta sai barci.NUWAIRA ce ta fito cikin riga brown da wandon jeans duk ya matse ta sai tayi rolling d’in veil ga wani sunglass daya rufe rabin fuskar ta. Straight bedroom d’in MEENAL ta nufa tana dariyan mugunta. Ganin da tayi MEENAL sai barci take ne yasa ta saurin rufe bakin ta kar dariyan da take rik’ewa ya fito cikin zuciyar ta cewa take hmm yarinya k’adan ma Kika gani indai kina shiga harka na. wai har Mom na wani baki matsayin da yafi nawa ko to wallahi bazan yarda ba. Taja tsaki ta bar bedroom d’in. Da missalin k’arfe 10:30 am MEENAL ce ta farka daga barci mai nauyin da ya d’auke. da k’yar ta iya mik’ewa tsaye tana dafa bango. D’agowan da zatayi me zata gani k’arfe 10:30 am. Dafe kanta tayi cikin rud’ewa tace”oh my God what’s happening? daga kawai in shirya sai barci” ai da sauri ta fad’a toilet ta wanke fuskar ta cikin sauri ta fito Arabian gown black tasa da sauri veil d’in ma d’aura shi tayi a kanta. Handbag da takalmi flat shoe duk a hannu ta rik’e su da sauri take saukowa daga upstairs.Ummie ta gani ta fito kitchen da sauri ta fara tambayar ta tace” Ya akayi sai yanzu ai nayi tunanin kin tafi me yasa meki ne wai?”Fita tayi da sauri tana cewa” Ummie na ba time d’in magana I’m late” Dafe kanta tayi tace”oh yarinyan nan ko lafiya a haka ma zata fita” Da sauri driver ya k’araso. Ta shiga yayin da ya tashi motar suka nufa gurin aikin. Ko parking bai gama yi ba ta fito da sauri tana cewa” sorry”Da sauri ta shiga ciki kowa sai ya kalle ta ganin gaba d’aya bata cikin hayyacin ta. Zata shiga office d’in ta kenan sai ga Mom. Tsayawa tayi duk ta rud’e da k’yar ta gaishe da Mom. Bayan ta amsa ne tace” are ok? Ya akayi kinsan yau kuka fara aiki shine zakiyi late. Kar ki manta kece shugaba, ki san lokacin da Zaki dinga zuwa” Tace”sorry wallahi ban San ya akayi nayi late ba I’m very sorry”Juyawa kawai Mom tayi ta bar gurin, da k’yar ta shiga office d’in ta tana tunanin ko ya akayi tayi barci har tayi late, Nan ta fara aikin gaban ta bayan HUSNA ta shigo Dan sectary d’in ta ce. NUWAIRA dake lab’e ta k’ofar ta tana kallon meke faruwa sai farin ciki take tunda tasa MEENAL yin late.Sanye yake cikin suit da alama aiki zai je cikin tafiyar shi mai d’aukan hankalin ‘yan mata ya shigo gurin. Gaba d’aya kowa sai kallon shi suke daga matan har mazan. Wucewa yayi straight office d’in Mom.Tana ganin shi tace” welcome FAWAS sorry mun takura maka ko? gashi Kuma kayi late”Bai ce komai ba ya mik’a mata wani leda babba wanda Mommy’n shi ce tace ya kawo ma Mom, duk da bai so ba sai da tasa shi dole.Yace”Morning”Tace”morning FAWAS kace mata za muyi waya”Yace”okay sai anjima” ya fita.Sauri-sauri ta fito office d’in ta tana tunani ji tayi ta fad’a kan wani abu. Cikin fushi ya ture ta da k’arfi yana Shirin fara mata massifa sai dai Kuma me MEENAL ya gani, rabon da ya ganta tun lokacin da suka had’u d’in nan.Mik’ewa tsaye tayi tana cije lips course taji zafin ture tan da yayi cikin massifa tace” are blind or what da baka ganin han…….” Maganar tane ya katse lokacin da taga FAWAS. Lokaci d’aya taji wani irin farin ciki gaba d’aya ta ma rasa mai za tace she’s very happy. Tace”I’m sorry please”Murmushi yayi kawai ba tare da yace komai ba ya bar gurin. Mamaki tayi yanda baiyi mata magana ba. Sai ta tuna had’uwar su na farko inda har takalmin ta ya tsinke murmushi tayi cikin farin ciki marar missaltuwa.FAWAS gaba d’aya ya cika da farin ciki yau yaga masoyiyyar shi wow he really missed her, dama ya bata time ne ta huta bai son ya cika damun ta, that’s why ya fita harkar ta, but now he’s back again to win her heart inshallah.*Manage this please**TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *25*~*26* *Ina taya ki murnan gama litafinki sister na NI BA ‘YAR KOWA BACE Allah ya k’ara basira Allah yasa muyi amfani da darrusan dake ciki,Muna maraba da zuwan sabon novel d’in ki na BAWAN ALLAH, Allah yasa ki gama lafiya, Ameen**Har ta* koma office tunanin shi takeyi ji takeyi kamar kar su rabu, zuciyar ta tace why?meyasa take jin haka game da FAWAS?bata da mai Bata wannan amsar dole ta hak’ura taci gaba da aikin ta. Ranar haka ta yini cikin wani irin hali da k’yar ta iya aikin. The following dayNUWAIRA ce zaune a office d’in ta abin duniya yayi mata yawa ta rasa ya zatayi da rayuwar ta zuciyar ta na mutuwar son KAMAL amma ta k’arfi an raba su she really don’t know what to do. Kifa kanta tayi akan table har bataji shigowan MEENAL ba. Har sai da ta d’an buga table d’in.Firgigit ta dawo hayyacin ta wani irin mugun kallo ta watsa ma MEENAL tace”uban me ya kawo ki office na?”D’an zaro ido tayi tace”Kai NUWAIRA abin har da zagi ne haka, I’m sorry dama na shigo ne in sanar da ke cewan Mom na neman mu a office d’in ta”Mik’ewa tsaye tayi tace” to dole sai kinzo da kanki wallahi ni na tsani ganin face d’in ki gaba d’aya” taja tsaki ta bar office d’in.Jikin MEENAL a sanyaye ta fito office d’in, HUSNA na kallon ta tasan akwai abin da ya same ta Dan ba haka ta shiga office d’in ba.Da sauri ta fito gurin parking lot tana murmushi, NUWAIRA dake lab’e bayan ta tana son ganin ina zata take sauri. Haba zaro ido tayi lokacin da taga KAMAL suna gaisawa da MEENAL cikin farin ciki. Wani irin bak’in ciki taji,da sauri ta nufa gurin tana zuwa ta wanke MEENAL da wani irin azababben mari, cikin huci ta kalla KAMAL tare da rik’o hannun shi cikin kuka ta fara cewa”what have I done wrong to deserve this? shin ka yarda a raba mu? Ka yarda ka cire soyayyar da kake min a zuciyar ka,uhm tell me what’s happening?”Lokaci d’aya yaji wani irin sabon son ta a zuciyar shi da k’yar ya iya cewa” No kawai ina son kiyi ma iyyayen ki biyayya ne that’s why”Kallon shi tayi tace”look into my eyes and tell me you love me”Idanun su ne ya had’u guri d’aya cikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa suka shiga gaba d’aya sun bar duniyar mu sun shiga na soyayya.MEENAL dake gefe rik’e da gurin da NUWAIRA ta mare ta hawaye ne kawai ke zuban mata, she’s totally speechless, Dan taga ainihin k’aunar dake tsakanin KAMAL da NUWAIRA, lokaci d’aya taji sun bata tausayi Kuma sub burge ta. Gaskiya ita ta hak’ura da cewar tana son KAMAL domin basu dace ba.he only meant for NUWAIRA, ita yanzu ta d’auki KAMAL a matsayin yayan ta ne, murmushi tayi ta bar gurin.KAMAL ne ya fara dawowa hayyacin shi cikin sauri ya k’wace hannun shi gudun kar Mom ta hango su da sauri yace”look NUWAIRA I really love you but bazan iya cigaba da soyayya dake ba kuma kinsan meke faruwa I’m begging you please let’s end it now”Wani irin kuka ne ya k’wace mata da gudu ta bar gurin. Tana Jin wani irin zafi a zuciyar ta.******************************After two weeksGobe ne ranar da su NUWAIRA da MEENAL zasu cika shekaru ashirin da d’aya da haihuwar su.tsakanin NUWAIRA da MEENAL wata d’aya ne. Kawai Mom ta shirya musu BIRTHDAY party domin tayasu farin ciki,duk da Daddy yace kar ta had’a domin a ganin shi wannan ai bidi’a ne amma tace ina ai Sam ba zai yuwu ba dole ta shirya musu BIRTHDAY party. Kawai ya k’yale ta tunda tana da kafiya.Gown masu shegen kyau na mussaman tasa aka shirya musu. Dan kowa ne d’aya zai Kai duba saba’in ga Kuma takalman su hill masu shegen kyau, mussaman ta d’auko Wanda zasuyi musu make-up.Dilka aka Fara musu sanan akayi musu lalle amma ja sai suka fito kamar larabawa. Sannan akayi musu gyaran Kai dayake Allah ya basu gashi Nan aka gyara shi amma ba’a sa relaxer ba, gaba d’aya gashin aka had’a guri d’aya akayi musu donut da shi, gashi anyi inviting d’in mutane dayawa, har ‘yan company d’in su they’re invited, invitations card da aka kawo ma Mommy ne FAWAS ya gani gaba d’aya ya cika da farin ciki dan haka yaje SAHAD STORE ya siyo wani necklace silver me shegen kyau tare da earring d’in shi, *RANAR BIRTHDAY PARTY* 🎂Wata mai yin make up ce ta shigo tayi ma MEENAL wani irin make-up amma light make-up course yafi fito da natural beauty, sannan tasa mata nata gown d’in light pink colour da torch d’in red Yana want irin shining like stars, hill shoe da wallet d’in duk light pink ne, earring kawai na gold aka sa mata. Sannan aka d’auko wani abu kamar butterfly aka sa mata ta bayan gown d’in, akayi mata rolling d’in veil akai Wanda yake kamar net Kuma transparent. Masha Allah nace she’s looking like doll baby. Tayi masifar kyau ba k’adan ba. Ta b’angaren NUWAIRA ma haka ne duk abin da akayi ma MEENAL ita ma haka akayi mata banbancin colours be kawai dan na NUWAIRA komai golden colour ne Kuma ita ansa mata necklace. Wayyo fan’s kar kusu ku ganta tayi massifar kyau,kuyi imagining d’in mace chocolate colour cikin Kaya golen, sannan Kuma mace fara cikin Kaya pink and red, ni dai nasan sun had’u over,A ko’ina ansa balloons an Kuma rubuta sunayen su. *NUWAIRA &AMINA* NUWAIRA ce da MEENAL suka fito a tare shigowa sukayi cikin hall d’in inda yake cike da mutane dayawa.tafiya take cikin k’asaita kamar baza ta taka ba, yayin da MEENAL ke tafiya mai cike da natsuwa, gurin ansa wani irin wuta me colours sai juyawa yakeyi, dai-dai zasu hau high table aka hasko su da wuta tare da zubo musu da red flowers Yana zuba a kansu,Masha Allah kawai mutane ke cewa dan sun had’u over sai suka fito kamar stars, NUWAIRA gaba d’aya ta cika da haushin MEENAL gani take kamar ta fita kyau, zuciyar ta ya cika da kishi mai zafi.Tun lokacin da su MEENAL suka fito FAWAS ke kallon ta domin gaba d’aya tayi wani irin bala’in kyau sosai, haka shima KAMAL yaga Masoyiyyar tashi NUWAIRA tayi Mai kyau dan tare yazo da FAWAS.MEENAL ko murmushi kawai takeyi zuciyar ta fari fes, wani irin kid’a aka sa Yana tashi a hankali wak’ar mai dad’i mai sanyaya zuciya mai sauraro.Mom ce ta fito gurin tare da d’aukar speaker ta gabatar dasu NUWAIRA. Duk gurin aka d’au tafi sannan ta Kiram Daddy ya fito yaje gurin, karb’an speaker’n yayi ya Kira Ummie wacce duk jikin ta yayi sanyi, da k’yar ta k’arasa gurin.Mom ko haushi ne ya cika ta ganin yanda Daddy yake nuna kulawar shi akan Ummie.Duk gurin aka d’au tafi sannan NUWAIRA ta yanka,taba Mom a baki, Koda ta gutsura sai ta had’a hannun ta Dana NUWAIRA taba Daddy shima a baki. Kallon Ummie ba suyi ba. MEENAL na kallon su Kuma bataji dad’i ba.MEENAL ta yanka cake, Ummie’n ta tafara ba sannan Daddy sai Mom habawa duk gurin aka d’au tafi.Daga Nan aka cigaba da yin birthday d’in inda suka samu kyauta sosai, FAWAS yaba MEENAL nashi gift d’in taji dad’i sosai, babban abin da yayi mata dad’i Kuma ya ba kowa mamaki shine kyautar mota Mom taba MEENAL,dank’a Mata key tayi hannun ta, MEENAL ita kanta tayi mamaki, sai farin ciki ake yayin da zuciyar NUWAIRA tayi zafi sosai dan me yasa za’a ba MEENAL mota banda ita abin ya Mata zafi,MEENAL na tsaye ita da KAMAL yana fad’a mata irin son da yake ma NUWAIRA,ita Kuma tace zatayi k’okari taga sun koma sun cigaba da soyayya, kawai sai ganin NUWAIRA sukayi a gaban su tana huci a tunanin ta ko soyayya sukeyi, Cikin d’aga murya tace” sai yaushe Zaki fita harkar na? Wai menayi miki ne a rayuwa MEENAL” sai ga hawaye.Da sauri MEENAL tace” menayi miki ne? ni har yanzu baki gayamin abubuwan dana ke miki ba”Cikin zafi ta fara magana tace” kina son sanin abin da kikayi min ne? To bari in fad’a Miki, kin k’wace min soyayyar da iyaye na ke min,kin k’wace min gatan da ake nuna min har a gurin aiki kin fini matsayi, kin k’wace min KAMAL Kuma kinsan massoyina ne, kin k’wace min komai yanzu har mota aka baki amma ni ba’a bani ba, Wai meya kawo ki cikin rayuwa ta ne? Me kike so game da ni?” Ta fashe da kuka,da sauri KAMAL yayi k’okarin rik’e ta, ta dakatar da shi.Cikin hawaye MEENAL tace” ban k’wace miki komai ba kece kike ganin hakan, ban shigo rayuwar ki ba, sai dai Allah ya k’adara cewa Daddy shine mahaifina, maganar dukiya bai dame ni ba komai kike so zan baki indai nawa ne dan nafi sonki a matsayin ‘yar uwa ta akan dukiya, ki gafarce ni dan Allah ki janye wannan tsanar da kike min ki so ni kamar ‘yar uwa’n ki, NUWAIRA mu *ZURI’A D’AYA* ne”NUWAIRA ba abin da ta tsana irin MEENAL tace su *ZURI’A D’AYA* ne dan ta tsane ta cikin zafi ta k’wace key d’in motar a hannun MEENAL tayi waje da gudu, da sauri ita ma MEENAL tabi bayan ta tana Kiran ta,Dai-dai lokacin da FAWAS ya fito Yana neman ta ganin shima KAMAL ya bi su waje yasa ya fita, Mota ne mai shegen kyau pink colour ‘yar k’arama na mata, cire flowers d’in dake jikin motan NUWAIRA tayi sannan ta bud’e ta shiga ciki, ganin hakan yasa MEENAL ita ma ta shiga tana ba NUWAIRA hak’uri, da gudun gaske NUWAIRA taja motan suka hau kan titi.Cikin razana da rud’ewa FAWAS ya shiga nashi motan tare da KAMAL, suka bi bayan su,Daddy ne dasu Mom suka fito bayan sunga wucewar motocin gaba d’aya hankalin su ba k’aramin tashi yayi ba duk sun rud’e, Daddy ne ya fara kwantar musu da hankali.Gudu sosai NUWAIRA takeyi,yayin da FAWAS yake binsu a baya Yana yin horn alamar su tsaya, sai dai ina NUWAIRA bata saurare shi ba, cikin kuka MEENAL tace” NUWAIRA me kikeyi haka ne so kike mu mutu ne?”Juyowa tayi cikin zafi da d’aga murya tace”eh mu mutu gaba d’aya nafi son mu mutu…..” Bata rufe baki ba kallon gaban ta da zatayi wani irin babban mota ne DAF ta gani a gaban su cikin tsoro da firgici duk sun rud’e sun fita hayyacin su, MEENAL sunan Allah take Kira, cikin ikon Allah NUWAIRA ta kauce ma motan yayin da motan yayi gefen titi ya bugi wani bishiya da k’arfi, duk kansu yayi gaba NUWAIRA ta buga Kai haka ita ma MEENAL, Parking FAWAS yayi cikin tashin hankali shida KAMAL suka nufi motan, da sauri FAWAS ya bud’e murfin motan tare da ciro MEENAL, kwantar da ita yayi a jikin shi gaba d’aya ya fita hayyacin shi especially da yaga jini na zuba ta goshin ta, KAMAL ko gurin NUWAIRA yaje ya rik’e hannun ta da k’yar ta iya bud’e idon ta, ya fito da ita daga ciki, yayin da take Jin wani irin jiri na d’aukar ta,FAWAS d’aukan MEENAL yayi yasa ta a mota sannan su KAMAL suka shiga, inda ya wuce direct hospital,Da sauri aka shiga da MEENAL emergency room, hankalin FAWAS duk ya tashi, Kiran Daddy ne ya shigo wayar shi Yana d’auka ya fad’a mai hospital d’in da suke,Doctor ne ya fito Yana sanar da su cewan Babu abin da ya same ta doguwar Suma tayi sai ciwon da taji a goshin ta shima k’adan ne, sannan aka duba NUWAIRA ba abin da ya same ta, a lokacin ne su Daddy suka shigo gurin,D’akin da aka kwantar da MEENAL suka shiga, ganin ta sukayi tana zaune idon ta biyu, duk sun gode ma Allah da abin ya tsaya iyakar nan,Mom ce ta fito ta samu NUWAIRA a zaune ita da KAMAL,Yana ganin ta ya mik’e ya bar gurin, k’arasowa tayi gaban ta tare da d’aga hannun ta, ta Kai Mata wani irin Mari Mai shegen azaba, da sauri NUWAIRA ta rik’e gurin tana hawaye,Cikin zafi Mom tace”Ashe Zaki iya kashe MEENAL? wannan wani irin tsana kikayi mata ne? Kin samu na Raine ki kamar ‘yar da na haifa Amma yanzu da abin da Zaki saka mana dashi kenan?”Girgiza kai tayi tace”kiyi hak’uri mom bansan ya akayi hakan ya faru ba”Tsawa ta daka mata tace”Yi min shiru idiot kawai Baki da hankali ne? Idan da ace ta mutu wallahi sai nayi shari’a dake stupid, wannan ya Zama last warning da zan Miki domin duk abin da ke faruwa tsakanin ki da MEENAL ina sane” taja tsaki ta bar gurin,Kuka NUWAIRA ta fashe da shi, yau ita Mom ke fad’a ma haka har tana yin mata gori, lalai ya Zama dole ta nema *ZURI’AR TA* tunda har an Fara mata gori sai ta Nemo asalin ta.*TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *27*~*28* *Bayan* doctor ya duba ta yaga babu wani matsala ne akayi discharging d’in su, bayan sun dawo gida Mom ta samu NUWAIRA tace lalai ta tabattar taje ta nema yafiyar MEENAL duk da bata so amma haka dole taje bedroom d’in ta, MEENAL ce kwance kan bed Ummie na fama da ita akan ta tashi tak’i, cike da shagwab’a tace “Nifa Ummie na ba maganin da zan Sha kawai ki barni Kuma ni bana son faten shuwa kan nan ya cika d’aci” Ummie tace” to ai shikenan kinga sai ayi miki allura kawai” Da sauri ta tashi tsoro d’auke a fuskar ta zatayi magana kenan NUWAIRA ta shigo,NUWAIRA a ranta cewa take ina ma zata samu mahaifiyar ta tana bata irin wannan kulawar na mussaman gaskiya da taji dad’i sosai,dan Mom bata mata irin haka. Komai dai take so za’ayi mata amma ba a nuna mata irin wannan kulawar. Jikinta a sanyaye ta zauna a gefen bed d’in cikin fuskar tausayi kamar da gaske tace” I’m sorry about the accident that just happened please kiyi hak’uri duk nice naja hakan ya faru forgive me”Ummie ce tace”haba NUWAIRA dan me Zaki ce haka? Karki manta musulmi Yana yarda da k’adara Mai kyau ko mare kyau, Allah ya k’adara cewa sai hakan ya faru kuma mun gode ma Allah da ba abin da ya same ku,dan haka karki ce komai”Taji dad’in abin da Ummie tace amma duk da haka tana jin haushi dai.MEENAL ko mutuwar zaune tayi ganin ba’a jima ba da NUWAIRA ke cewa sai ta kashe su gaba d’aya, Kai amma da NUWAIRA ta hak’ura da komai ne tayi nadama da tafi kowa Jin dad’i, course bata son yanda take nuna mata. Cikin farin ciki tace”No stop apologizing for what happened, kamar yanda Ummie na tace to haka ne, fata na da buri na mu zama *ZURI’A D’AYA* hope you’ll forgive me too?”Cikin murmushin yak’e tace”why not sweet sister? komai ya wuce inshallah”Ummie ko dariya tayi ta fita tana jin dad’in yanda take ganin su cikin farin ciki. Ummie na fita NUWAIRA ta mik’e taja tsaki tace”do you think that is over? No I said no this is just the beginning of the war” ta bar bedroom d’in.Mamaki da rud’ani ta shiga wannan Kuma wani irin sabon salo ne NUWAIRA ta fito da shi? Lailai da abin da take shiryawa amma ko ma mene ne zata sa mata ido kawai.In the morningCikin kwanciyar hankali take barcin ta kamar a dream taji phone d’in ta na ringing,da k’yar ta iya danna answer tasa a kunnen ta cikin barci tace”hello”Lumshe ido yayi tare da tsotsan lips d’in shi, wani irin yanayi ya shiga na soyayya, yace” ina fatan kina lafiya, ya jikin ki?”Da sauri ta zauna cikin farin cikin jin muryan FAWAS tace” Alhamdulillah ya Mommy?”Murmushi yayi yace”she’s fine, hope ba abin da ke damun ki ko?”Tace”No ba komai headache ne Kuma da sauk’i”Yace”okay dama ina son jin ko ba abin da ke damun ki ne, bye”Murmushi jin dad’i tayi tace”thanks for the care bye”Bai ce komai ba ya kashe wayan, samun kanshi yayi cikin nishad’i gaskiya he really miss her sweet voice. Sati d’aya tayi bata koma aiki ba dan Mom tace tafi so ta samu sauk’i sosai, NUWAIRA ko ba k’aramin haushin MEENAL take ji ba, amma fa a jikin mutane nuna mata so da kulawa takeyi, tun abin naba MEENAL mamaki har ya daina bata mamaki. A cikin satin nan taga kulawa da gata gurin FAWAS, ga wani irin son shi da ya shiga zuciyar ta ji takeyi kamar kar su rabu idan sun had’u. KAMAL kullum yana tare da NUWAIRA a waya Dan sun shirya kansu basa Jin zasu sake rabuwa, wani irin k’auna suke nuna ma junan su.MEENAL ce a office d’in ta tayi shiru da alama tayi nisa cikin tunani,har HUSNA ta shigo bata sani ba har sai da ta d’an buga table d’in sannan ta dawo hayyacin ta.Murmushi HUSNA tayi tana tambayar ta ko lafiya, da farko kamar baza ta fad’a mata ba sai Kuma taga cewan sun shak’u da HUSNA tana da kirki kuma HUSNA matar aure ce har da yaran ta biyu Ilham da Imad, bata b’oye mata komai ba ta fad’a mata.Murmushi HUSNA tayi dan tun Ranar birthday party d’in su ta lura akwai abin da ke tsakanin su, tace” gaskiya naga alamar yanda yake k’aunar ki, ni ina ganin me zai hana ki amince da shi, dan Naga kema kina son shi”Taji dad’in maganar HUSNA dan haka tace” gaskiya nayi kuskure tun farko gashi yanzu ina regretting, HUSNA Allah ya jarabce ni da son FAWAS so mai tsananin gaske wallahi har kunyar shi nake ji”HUSNA tace”yanzu dai abin da zakiyi shine kawai ki amince da soyayyar shi, dan kowa ce mace zatayi burin malakar FAWAS a matsayin miji dan haka ina muku fatan alkhairi” Murmushi tayi tace”nagode sosai da shawarar ki gare ni gaskiya ke d’in k’awa ce ta gari” Nan sukayi d’an hira jefi-jefi sannan kowa ta koma kan aikin ta.A yau ne FAWAS yayi Shirin zuwa gurin MEENAL a karo na biyu domin samun soyayyar ta wannan karon a shirye yake ba gudu ba ja da baya inshallah sai yayi winning heart d’in ta course Yana Mata wani irin so mai wuyar fassaruwa.Cikin riga da wando na shadda navy blue kan shi ba hula sai dai kan nan yaji gyara balarabe sak ya fito. Mommy dake kitchen taji an rungumeta ta baya, juyawa tayi tana cewa” wai kai FAWAS sai yaushe Zaka girma?”Murmushi yayi yace”Mommy kece fa kika ce baki son ace kin tsufa kuma yanzu kince ban girma, I need your prayers”Juyowa tayi tace” ina zaka je ne haka?” Sunkuyar da kai yayi tare da rufe idon shi wai shi a dole yaji kunya yace” wace nake fad’a miki ce, zanje gurin ta, kiyi min addu’a Allah yasa ta amince da ni course I love her Mommy”Murmushi tayi cikin farin ciki dan tana son farin cikin shi dan haka tayi mai addu’a sannan ta d’auko wani perfume mai k’amshin gaske ta fesa mai, sai farin ciki yake, mota ya shiga ya nufa gidan su MEENAL, NUWAIRA na zaune taga FAWAS ya shigo gidan, gaisawa sukayi tana mamakin meya kawo shi gidan Dan babu alamun sak’o ya kawo ma Mom, dama already ya Kira MEENAL ya fad’a mata yana gidan sai kawai ta bud’e mai guests room ya shiga, NUWAIRA ko mamaki take duk yanda akayi akwai wani abu tsakanin Su. Sanye take cikin riga da wrapper skirt na wani Swiss less tayi kyau sosai dan colour d’in ya karb’e ta milk and chocolate colour ne, shigowa parlour’n tayi tana d’auke da tray da juices sai cupcakes, FAWAS na ganin ta yayi sauri ya k’arasa ya karb’a yana mata welcome, ajiyewa yayi kan center table, sannan ya zauna kan kujera dake fuskantar na MEENAL. Gaishe shi tayi cike da natsuwa da kunya, amsawa yayi cikin farin ciki, gurin ya d’auki shiru kusan 5 minutes kafin yayi magana cike da natsuwa yace” MEENAL do you love me?” Lokaci d’aya taji duk ta rud’e dan batayi tunanin wannan question d’in zaiyi mata ba, shiru tayi ta kasa cewa komai har sai da ya k’ara mai-maitawa sannan ta tuna hiran ta da HUSNA da abin da ta fad’a mata.da k’yar tace” Me yasa kace haka?” Murmushi yayi yace” I want to know whether you loved me or you still love that person you’ve said?” Gaba d’aya ta rud’e da k’yar tace” oh that time, nifa ba wanda nake so” ta fad’a cikin shagwab’a. Yaji dad’in yanda tayi magana ji yake kamar ya rungume ta da alama yanzu zai samu guri a cikin zuciyar ta, yace” are you serious? MEENAL na k’ara zuwa a karo na biyu ki taimake ni ki amince da soyayya na gare ki, please I’m begging you I truly love you” Kai bata san irin farin cikin da ta shiga ba, yau rana ce na farin ciki a gare ta, cikin kunya tace” I’m…..” She’s confused she actually don’t know what to say.Kneeling yayi a gaban ta yace” Please accept my love, I love you MEENAL”Rufe fuskar tayi cikin Jin kunya tace” na amince” da sauri ta bar parlour’n cikin jin kunya.Sujudud shukra yayi tsabar farin ciki Alhamdulillah kawai yake cewa, cikin farin ciki ya bar gidan.MEENAL ko saura k’adan ta buge NUWAIRA dake kan stairs, ta shiga bedroom d’in ta da gudu, NUWAIRA ko tsaki taja cikin takaici. A wannan kwanakin wani irin soyayya su MEENAL da FAWAS sukeyi suna k’aunar junan su sosai, kussan ko da yaushe suna tare ko a phone ma suna mak’ale da juna,Tun ba Wanda suka sani har su Ummie suka gane, NUWAIRA tayi mamaki sai dai ta nuna su suka sani, Mommy’n FAWAS ko tafi kowa farin ciki ganin cewa ‘yar aminiyar ta ce, Kuma ta yaba da natsuwar da tarbiyyan MEENAL. Bayan wata biyu After two months NUWAIRA ce kwance a bedroom d’in ta tana wani irin kuka mai tsananin gaske domin Daddy yace duk su fito da Wanda suke so za’ayi musu aure, gashi Mom tak’i bata damar gabatar da KAMAL, MEENAL ko har Daddy’n FAWAS yazo anyi maganar auren, Ummie ce ta shigo bedroom d’in tana tambayar ta meya same ta da farko tak’i fad’a mata sai da tace zata taimake ta idan har tana da buk’ata, Nan NUWAIRA ta fad’a ma Ummie komai game da soyayyar ta da KAMAL da Kuma irin tsanar da su Mom suke nuna mai. Sosai Ummie taji tausayin ta Kuma tace zatayi ma Daddy maganar domin Wanda NUWAIRA ke so zata aura babu takura. NUWAIRA taji dad’in maganar Ummie lokaci d’aya taji tana k’aunar ta sai godiya take mata. Ummie ta samu Daddy da maganar NUWAIRA da KAMAL Kuma shima ya amince yace ba zai mata auren dole ba dan haka yasa ta Kira KAMAL d’in dan yayi magana da shi.Cikin farin ciki NUWAIRA ta fad’a ma KAMAL sai farin ciki suke, ba tare da b’ata lokaci ba KAMAL yaje gurin Daddy inda ya yaba da halin KAMAL Kuma yace ya yarda ya turo magabatan shi domin asa musu Ranar aure da NUWAIRA,Kawun KAMAL Wanda yake matsayin yayan Maman shi shine yaje gurin Daddy shi da wasu aminan shi inda aka tsayar da maganar aure.dan Daddy ya lura mutane ne masu mutunci. A yau ne aka sa ranar d’aurin auren NUWAIRA da KAMAL, sai MEENAL da FAWAS, Nan da wata biyu masu zuwa.*Sorry fan’s kunji ni shiru, I’m very sorry please**TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *29*~*30* *Ina Mai baku hak’urin jina shiru da kukayi, please kuyi min uzzuri, masu min magana ta private chat nagode sosai Allah ya bar zumunci* *Lokacin* da Daddy ya fad’a ma Mom ansa ranar aure harda na NUWAIRA da KAMAL ba k’aramin haushi taji ba tace kuma Bata yarda ba sai dai a fasa Dan NUWAIRA baza ta aure shi ba, Daddy yace shi kuma bata Isa ta maida shi k’aramin mutum ba Dan anriga an gama komai Kuma duk abin da yaran shi suke so shi za’a ayi in har bai kauce ma hanyar addini ba dan bazai yi musu auren dole ba. Sosai Mom taji haushi har Mommy’n FAWAS ta Kira take fad’a mata ita Kuma tace tayi hak’uri kawai ta bar NUWAIRA da Wanda take so, haka Nan ba dan Mom ta hak’ura ba sai dan ba yanda zatayi, NUWAIRA ko ba k’aramin farin ciki tayi ba at least Ummie da Daddy sunyi mata abin da baza ta tab’a mancewa ba dan sun aura mata wanda take so.Tsakanin FAWAS da MEENAL wani irin soyayya sukeyi Mai ban sha’awa duk inda suka shiga sai ance sun dace da juna kuma suna k’aunar junan su, haka NUWAIRA ma da KAMAL sosai suke soyayya dan yanzu har gidan yake zuwa Kuma ba abin da Mom ta Isa tayi Dan Daddy yayi mata warning sosai,Lokaci na gudu sosai dan gashi har Allah ya kawo mu bikin su MEENAL Dan yanzu haka biki saura sati d’aya. An kawo kayan lefen MEENAL, akwati sai goma sai kit, komai na cikin kayan yayi dan Mommy da kanta taje ita da ‘yan uwa’n ta Dubai suka yo siyayya especially Arabian gown sunfi yawa Dan shine dressing d’in ta. Haka ma an kawo lefen NUWAIRA ita ma dai ba laifi sosai kayan yayi dan Daddy’n FAWAS da kanshi ya sa aka had’o ma KAMAL lefe. Already dama Ummie ta dage da gyaran yaran nata tun kusan one month biki, yanzu haka ma sai k’ara shirya su takeyi bare kuma tayi wata k’awa ‘yar Sokoto ai Nan ta dage da gyara su, MEENAL ko har b’uya take dan ta gaji da Shan abubuwa, Ranar Wednesday akayi musu lalle da salon sunyi bala’in kyau kamar ku sace su ku gudu tsabar kyau bare kuma dama tun saura one week ake musu gyaran jiki dasu dilka, fatar su tayi fresh sai shining take kamar ka tab’a jini ya fito, Thursday akayi Mother’s day inda suka yi shiga mai shegen kyau da Swiss less orange and lemon green colour har jakan su da takalman su, wow ranar sunyi kyau ko da angwayen nasu suka gansu sun kasa natsuwa dan ma akwai wata cousin d’in Mommy’n FAWAS sai gadin amare take da k’yar ta bari ranar angwayen suka gansu shima daga nesa. Ranar Friday aka shirya walima akayi wa’azi inda jikin su duk yayi sanyi. Dan basa sun yin bidi’a shiyasa kawai basuyi sauran abubuwan ba. Ranar d’aurin aure Ranar gaba d’aya sunyi shiga cikin wata atamfa red and black anyi mai Stone work gashi sun sha heavy make-up sai shining suke, hmm masu karatu tsayawa fad’a muku yanda amaren suka had’u da yanda taron ya gudana zai sa mu b’ata lokaci sai dai a wannan Ranar gaba d’aya *ZURI’A D’AYA* suna cikin farin ciki marar missaltuwa. Da missalin k’arfe 2:30 pm aka d’aura auren *KAMAL & NUWAIRA* akan sadaki mafi daraja Naira dubu hamsin, sannan aka d’aura auren *FAWAS & AMINA{ MEENAL}* inda suma akan sadaki mafi daraja Naira dubu hamsin, dubamin mutane sun shaida wannan d’aurin auren inda akayi tasa albarka. Angwaye FAWAS DA KAMAL sai farin ciki suke suna murmushi ana ta gaisawa da mutane, Lokacin da su NUWAIRA suka ji an d’aura auren duk sai jikin su yayi sanyi, MEENAL ko har kuka tayi, bayan nan ne aka shirya su cikin wani material mai shegen kyau da tsada pink and blue colour sunyi masifar kyau, shiga dasu gurin Daddy akayi yayi musu nasiha sosai duk jikin su yayi sanyi, d’auko Al-QUR’AN yayi da praying mat(abin salla) ya basu, sukayi godiya sannan aka kai su gurin Mom tayi musu nasiha ita ma duk da tana jin haushin NUWAIRA hakan bai sa taji wani irin ba, da sauri NUWAIRA ta rungume ta tana kuka da k’yar aka raba su,haka ma MEENAL lokacin da Ummie ta gama musu nasiha rik’e ta tayi sosai tace ita ba zata ta tafi ba,da k’yar aka raba su, Straight gurin parking lot aka nufa da su inda kowa ce a ka saka ta a mota aka nufi da su gidan su inda zasuyi rayuwar aure sai kuka sukeyi,nima fa na d’an taya su k’adan. NUWAIRABayan an kaita gidan aka nufa parlour’n Mama da ita sai da aka gaisa taga amarya sannan aka nufa da ita side d’in ta, dan KAMAL yayi wani flat mai kyau ta cikin gidan. Bayan mutane sun watse ya rage sai ita kad’ai shine ta shiga tayi wanka ta shirya cikin wasu nighties masu shegen kyau duk ya bayyana surar jikin ta sannan ta feshe jikin ta da different performs, sai around 9:00pm KAMAL ya shigo gidan inda ya zo da gasashen kaza da yorgurt, sai bayan sunyi sallah ne suka zauna ya dinga Bata a baki shima yana bata har sai da suka k’oshi. Sannan suka yi brush, KAMAL dai duk a rud’e yake, rungume NUWAIRA yayi ya fara aika mata da kiss ta ko’ina, har suka Kai kan bed sannan ya raba ta da kayan jikin ta inda ya fara zuba mata love, a wannan Daren dai Mai afkuwa ya afku ni dai na gudu Dan ba da ni ba, bayan komai yayi dai-dai ne na koma naji ya dinga sa mata albarka, ita ko sai kuka take tana narkewa cikin shagwab’a. FAWAS & MEENAL An Kai ta har gurin Mommy ta sa Mata albarka sannan aka nufa side d’in ta da ita dan daga gefe Daddy’n FAWAS ya Gina mai gida mai kyau sosai gashi komai na cikin gidan iri d’aya ne Daddy yayi masu ita da NUWAIRA, different d’in kawai colours ne, MEENAL Zama tayi ta dinga kuka har sai da kan ta ya fara ciwo, Around 9:00 pm FAWAS ya shigo, har bedroom ya shiga ganin ta yayi ta rufa da blanket sai kuka take, a hankali ya k’arasa gurin tare da jan blanket d’in yana duba ta, cikin dubara ya sauko da ita sannan ya kawo gasashen kaza da yorgurt ya dinga Bata a baki da k’yar take ci sannan ya bata medicine tasha, bayan Nan sukayi alwala sukayi sallah, wani night gown iyakar cinyar ta ya kawo mata tasa, lokacin da tasa sai da ta d’aura hijab a Kai Dan gaskiya kunyar fita take a haka, Pyjamas yasa Yana zaune yana jiran fitowan ta sai ganin ta yayi da zunbulelen hijab, mik’ewa tsaye yayi ya rungume ta cikin dubara ya cire mata hijab d’in ya ajiye a gefe, sauke ajiyar zuciya yayi dan ba k’aramin kyau tayi mai ba, d’aukar ta yayi cak ya kwantar da ita akan bed sannan ya hau, had’a lips d’in shi da nata yayi ya fara kissing d’in ta, duk ya rud’e ya fita hayyacin shi sai romancing d’in ta yake, a haka har ya cire mata kayan, MEENAL ko jin wani sabon salo da ya canza yasa ta fara tsoro tana kuka, amma ina bai ma San tana yi ba, har da yak’ushin shi take da cizo amma bai fasa ba, nida fita nayi Dan ba Dani ba har sister Maimounath na Jan hannuna nace ai ina bazan tsaya ba ita ma sai da na tasa keyar ta,lolx.Nidai sai wurin asubah na dawo, sai Jin kukan MEENAL nakeyi shi Kuma FAWAS sai faman lalashi yake, shida kanshi ya gasa mata jiki sannan ya bar ta tayi wankar tsarki da kan ta. Fitowa tayi daga toilet sai cize lips take dan wani irin azaba take ji, FAWAS na ganin ta yayi sauri ya d’auke ta cak, da kan shi ya shafa Mata mai,tasa Kaya sannan sukayi sallah suka hau gado, FAWAS ya lalubo lips d’in ta yayi Mata kiss tare da rungume ta yana cigaba da sa mata albarka har sukayi barci. *Muje zuwa masu karatu**TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:22 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *31*~*32* *Sister MUNEERA ina taya ki murnan Kamala litafinki mai sunna ITA CE A TAINA Allah ya k’ara basira, gashi yanzu har kin fara wani mai suna NAGA TA KAINA, Allah yasa yanda Kika Fara lafiya ki gama shi lafiya, Ameen* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *Maman Waleed REAL MAI DAMBU CE🥗, kina matuk’ar k’okari a litafin ki na NAMIJI MA YA YARO NE Allah ya kare ki daga sharin mahassada,ina mutakar yin ki irin sosai d’in nan,muje zuwa,kina k’amshi ina bin ki da humra tawan*😊🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 *Hip Hip Hip Hurray* *HAPPY BIRTHDAY ACTION BABY*🎂 *Sister ina taya ki murnan zagayon ranar haihuwar ki Allah ya k’ara tsawon kwana, Allah ya kare ki, UMMU BASHEER wishing you Happy birthday*🎂 *Ga nawa birthday cake d’in manage it please*🎂 *Allah ya k’ara basira da hazak’a a litafin ki na DEEJE DA SANGHAMI*🌹 🌹 🌹 *Washegari da safe* *Lokacin* da gari ya waye ba k’aramin kunyar FAWAS bane ya kamata,dan gaba d’aya kunyar had’a ido take da shi, bayan sunyi breakfast ne taje har gurin Mommy ta gaishe ta cikin kunya. Bayan sati biyuCikin satin nan ansha amarci ta b’angaren duka amaren da angwayen, sannan duk sun koma gurin aikin su, lokacin da MEENAL ta had’u da NUWAIRA ta gaishe ta amma ko amsa mata batayi ba, duk da MEENAL bataji dad’i ba kawai sai ta hak’ura ta share. Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, sosai FAWAS yake nuna ma MEENAL tsantsar k’auna da tarairaya, haka ita ma tana mai ladabi da biyayya kuma tana nuna mai k’auna, yayin da NUWAIRA da KAMAL ko kamar zasu cinye junan su tsabar soyayya. Bayan wata biyu Jan blanket d’in yake tare da jan yatsun k’afan ta a hankali yana cewa”come on my love wake up now, barcin ya isa haka”K’ara shigewa cikin blanket tayi tace”let me sleep please Honey” Da k’yar ya d’auke ta cak ya Kai ta toilet, sai Jin ta tayi cikin ruwa tsundum, da sauri ta bud’e ido tace”please please, ni ka maida ni I’m feeling sleepy kaji honey?” K’okarin cire mata kaya ya fara yana cewa”no you have to wake up, za muyi late a office, oya take your bath?”Fita toilet d’in yayi ita Kuma tayi wanka,ko da ta fito baya bedroom d’in kawai sai ta shirya cikin Arabian gown peach colour, sannan ta fito a parlour ta same shi yana breakfast, cikin shagwab’a ta iso gurin tana cewa”ni nifa nace ka dinga tashi na ina had’a breakfast amma sai ka barni inyi ta barci ina Jin ma sleeping sickness nakeyi”Habawa ai bai san lokacin da ya tuntsire da dariya ba yace” gaskiya wannan barci nake my love ba na lafiya bane, kizo muje Mommy na ta duba min ke, may be na Baki ajiya ne”Turo baki tayi gaba tace”No nak’i d’in, kawai so kake ayi min injection, wait ajiyan me ka bani?” Yace”oya come, zo in fad’a Miki” Tana zuwa kusa da shi ta shak’i k’amshin perfume d’in shi da k’amshin indomie with eggs da yayi taji wani irin amai yazo mata da sauri ta juya ta nufa toilet, da sauri yabi bayan ta cikin rud’ewa, yana zuwa ya tarar sai amai takeyi, rik’e ta yayi yana mata sannu, bayan ta gama ya wanke mata fuskar ta, ya wanke gurin suka fito.Cikin tausayawa yake tambayar ta mene ne ya sata amai? Ita dai bata sani ba dama two days tana jin tashin zuciya sai yau ta samu tayi amai. Fita yayi yaje ya Kira Mommy’n shi, gani yayi har ta fito zata tafi aiki da sauri yace mata MEENAL ba lafiya, sannan suka nufa side d’in shi, Kwance take kan bed wani irin jiri ne ke damun ta da k’yar ta bude idon ta, ganin halin da take ciki yasa Mommy tace su tafi hospital ta da tayi mata test, haka ko akayi suna zuwa aka d’ebi jinin ta da k’yar ta tsaya sai da FAWAS ya ririk’e ta sannan akayi test har Urine sai da akayi test inda suka gano cewa tana d’auke da ciki, habawa ai ba k’aramin farin ciki FAWAS yayi ba, ita ma taji dad’i, sannan suka nufa gida, ai ranar ba aikin da FAWAS yaje Zama yayi a gida ya dinga kula da ita.Bayan sati uku Sosai take samun kulawa ta b’angaren FAWAS da Mommy’n shi, komai take so ake Mata, Zaune take a office d’in ta tana tunanin ko sai yaushe NUWAIRA zata dinga kula ta? HUSNA ce ta shigo ciki suka gaisa inda MEENAL tace” ni Wai HUSNA ina Zan samu tsamiyar biri ne da garin kuka?”Dariya tayi tace”toh fa, ya za’ayi kenan Dan nima ban san inda zan samu ba”Kamar MEENAL zatayi kuka tace” wallahi ina son Sha yanzu ya zanyi? Let me call FAWAS” ta d’auki waya tare da Kiran shi, Yana office Yana aiki yaga call d’in ta da kamar bazai d’auka ba course aiki yayi mai yawa sai ya d’auka, Cikin shagwab’a tace” Honey garin kuka nake son Sha yanzu please” Dafe kan shi yayi yace” oh my God, my love what is garin kuka?” Cikin shagwab’a tace” wani abu ne, ni dai kawai ina son Sha” Cikin lalashi yace”ok don’t worry inshallah Zan sa a Nemo min”Sannan suka yi sallama. Lokacin da ta tashi aiki dai-dai ta fito office taga NUWAIRA ita ma ta fito k’arasawa tayi cikin farin cikin ganin ta dan two days basu had’u ba, sai dai ta lura akwai abin da ke damun ta, da sauri tace”sister what’s wrong with you, naga kin canza min?” Wani irin wawan tsaki taja tace” ban sani ba, kin San dai bana son shishigi koh? Toh ki kiyaye ni” ta wuce abin ta,Gaba d’aya a tare suka fito inda kowa ce taga mijin ta yazo d’aukar ta dan ita ma NUWAIRA ciki take dashi sosai KAMAL ke tarairayar ta da nuna mata k’auna, FAWAS da KAMAL suna jingine da mota suna hira suna jiran fitowan matayen nasu,NUWAIRA ce ta wuce cikin zuciya ta shige mota, ganin halin da take ciki yasa MEENAL ta k’arasa dan ta bata hak’uri, da sauri su KAMAL suka k’arasa dan Jin meke faruwa duk da sun San da cewar basa shiri,Ganin yanda MEENAL ta biyo ta yasa ta fito tare da wanka mata Mari mai shegen azaba,Cikin tashin hankali da rud’ewa FAWAS ya rungume Matar shi yayin da yake Jin haushin NUWAIRA, KAMAL ne ya rik’e hannun NUWAIRA Yana cewa meyasa zatayi haka?Cikin zafi tace” ai na fad’a mata tun farko ta fita harkar na what’s her own business with me? Nace ta k’yale ni ko dole ne sai ta kula ni?”Cikin hawaye MEENAL tace”ba laifin ta bane ko mene ne nina jawo ma kaina dan kawai na d’auke ki a matsayin *ZURI’A D’AYA* muke dake hakan ne zai sa kiyi min haka? Ok Inshallah daga yau na fita harkar ki, that’s final”Cikin zafi tace” kar ma kice *ZURI’AR mu D’AYA* Dan wallahi ni dake ba jinin mu d’aya ba Kuma zanje in binciko ainihin iyaye na” Shiga mota tayi, da sauri KAMAL ya fara basu hak’uri, NUWAIRA ce ta Kira shi ya shiga mota kamar wani golo.Tsananin takaici ya hana FAWAS motsawa daga inda yake, da k’yar yaja hannun MEENAL suka shiga mota Yana Mai lalashin ta.Cikin satin nan NUWAIRA hankalin ta ya kasa kwanciya burin ta kawai tasan su wane ne asalin iyayen ta, haka take sa KAMAL a gaba da kuka shine shima yace zai Taya ta bincike har sai ta gano iyayen ta,Gurin Mom ta nufa tana tambayar ta ko wace ce mahaifiyar ta tana son zatayi bincike ta bata dama Dan tasan su wane ne iyayen ta, ba k’aramin tashin hankali Mom ta shiga ba, da farko bata yarda ba sai da NUWAIRA ta dinga kuka tana rok’on ta sannan ta amince amma fa zufa ne kawai Mom keyi dan ta shiga rud’ani, Cikin hawaye NUWAIRA tace”Mom so nake kawai insan wane ne mahaifina tunda mahaifiyana ta rasu, amma ko Zaki iya fad’a da Zan gano har in Fara bincike?”Cikin rud’ewa tace” k’auyen kura zaki je, Dan naji kamar kafin ta rasu ta fad’i sunan k’auyen Nan”Cikin zafi da tuno da mahaifiyar ta ta rungume Mom,Ita ko Mom ajiyar zuciya ta sauke tana sama NUWAIRA albarka amma da sharad’in kar ta fad’a ma kowa inda zata je. Haka ko akayi NUWAIRA da KAMAL sun shirya tafiya k’auyen kura dake cikin Kano, *Muje zuwa NUWAIRA da KAMAL ina bayan ku domin ganin ainihin ZURI’AR ki, fan’s ku muje zuwa*🏃🏻♀🏃🏻♀🏃🏻♀ *TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:27 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *33*~*34* *Wannan shafin na sadaukar da shine gare ku massoya na, Haske writer’s Asso.fan’s, Aysha Ali garkuwa fan’s, sangartaciyya fan’s and ZURI’A D’AYA fan’s, tare da duk sauran groups d’ina, Thanks for your love and care UMMU BASHEER loves you so much**Ba K’aramin* tashin hankali Mom ta shiga ba tun bayan barin NUWAIRA gidan ta kasa zama sai zagaye bedroom d’in ta take, yayin da zufa kawai takeyi duk da cewar A.C a kunne yake, can dai ta d’auko wayan ta, tare da call d’in wani number. Ana d’auka da sauri tace” ba lafiya nace maka akwai abin da ke faruwa, yanzu kasan halin da nake ciki kuwa? Wait ina son mu had’u first ya za’ayi?” Can tace”okay to shikenan make sure kazo da wuri course bana son wasting of times” A jiye wayan tayi tare da Zama a gefen bed ta fara tunani, shekaru Ashirin da Biyu da suka wuce. Twenty two years ago Shekaru ashirin da biyu da suka shud’eMom tun bayan barin ZAINAB (Ummie) gidan hankalin ta ya kasa kwanciya ji takeyi baza ta iya hak’uri ba dan haka dole taje gidan marayu ta d’auko rainon yaro dan har ga Allah tana k’aunar yara sosai. Ranar tana zaune gurin aiki sai ga Kira ya shigo wayar ta, cikin mamaki ta d’auka ganin bak’uwar number,bayan sun gaisa ne mutumin yace mata shine ALIYU cousin d’in ZAINAB Kuma yasan duk abin da ke faruwa na barin ZAINAB gida, da sauri ta fara tambayar shi ko yasan inda take? Yace shidai gaskiya bai sani ba sai dai yasan da cewar suna tsananin buk’atar haihuwa, dan haka idan har ta amince da shi to zai kawo mata wata jaririya ta raina amma fa da sharad’in zata biya shi kud’i mai tsoka, da sauri tace ta amince domin burin ta taga ta samu abin da zata raina a matsayin abin da ta haifa. Shiyasa lokacin da ya fad’a mata ta amince da sauri, Nan ta fad’a mai su had’u a wani park inda ya same ta sannan ta mik’a mai kud’i mai tsoka ya Kuma bata yarinyan, Nan ta tambaye shi iyayen yarinyan yace ai mahaifiyar ta rasu, tace to kar ya nuna yasan komai akan hakan ita san abin da zata shirya ta fad’a, haka Koh akayi suka rabu inda Mom ta had’a wannan k’aryan cewa ta buge wata da mota, to tun bayan lokacin basu sake had’uwa ba sai da Ummie ta dawo gidan ko da suka had’u basuyi maganar komai ba amma dai tana da number’n shi. To yanzu da NUWAIRA ta tambaye ta duk ta rikice ta rasa yanda zatayi shine ta fad’a mata sunnan wani k’auyen Dan ta rasa Ina zata ce to shine ta tuna da sunan k’auyen Maman Aliyu, Dan tasan ba yanda zatayi ta gano iyayen ta, Wannan kenan Cigaban labariLokacin da suka Isa k’auyen sun rasa ta Ina zasu fara, to duk Wanda suka gani sai su dinga tambayar su ko sun San wata da ta bar gida da tsohon ciki shekaru ashirin da biyu da suka shud’e? Kowa sai suce A’a, wasu ma cewa suke amma basu da hankali, abin da ya wuce shekaru ashirin da biyu suke tambaya lalai basu da hankali. Ranar duk sun gaji gashi har dare basu samu ansa ba kawai KAMAL suka shiga Kano suka kwana a Hotel, washegari suka koma k’auyen.Kusan sati d’aya suna zuwa k’auyen nan amma basu samu wani labari ba, Har sun Fara cire rai sun San da k’yar zasu samu wani labari akan iyayen ta. NUWAIRA ce zaune kan dakalin wani gida duk ta galabaita rabon ta da abinci tun jiya da daddare shima da k’yar KAMAL yasa ta a gaba taci, mik’o mata swan water yayi tasha, tana gama sha sai wani irin amai ya taho mata, da sauri ta farayi a gefe, Wata mata ce ta fito daga gidan, da ta fito taga su NUWAIRA sai taji ta tausaya ma NUWAIRA ganin yanda take amai Nan tace su shiga gidan ta su huta da alama su bak’i ne, Bayan sun shiga sun gaisa ne, NUWAIRA ta huta, shine matar ke tambayar su me ya kawo su k’auyen dan taga su bak’i ne,Nan suka gaya mata abin da ya kawo su, Kuma NUWAIRA ta Bata labarin ta,Girgiza kai tayi cikin mamakin abin da suka ce, tace”Kai gaskiya da wuya ace matar a k’auyen Nan take, kuyi hak’uri gaskiya Dan abin ya shima” Basu ji dad’i ba haka Nan bayan sun huta suka fito Dan tafiya har sun Kai gurin mota matar Nan ta aike wani yaro ya Kira su, da sauri suka dawo Nan take fad’a musu cewa akwai wata kakan ta tsohuwa ce zata iya sanin wani Abu akai Nan suka shiga mota ta Kai su har gidan tsohuwar nan.Suna shiga suka tarar da tsohuwar nan, Nan matar ta gaishe ta, sannan Suma suka gaishe ta, matar ta fad’a ma kakan ta abin da ke tafe da su NUWAIRA, tsohuwar nan ta jinjina musu tace gaskiya ita ba tasan wata da ta bar k’auyen nan da tsohon ciki ba,NUWAIRA kuka ta fara sosai haka KAMAL yayi ta lalashin ta, har sun fito zasu tafi tsohuwar nan ta Kira su tace musu akwai dai wata mata da tazo k’auyen da tsohon ciki har ta haihu, sai dai wancan matar ta bar gidan auren ta ne tazo Nan k’auyen har ta haihu .Cikin tunani NUWAIRA tace to matar mai ta haifa? Sai tsohuwar tace ai ‘YAN BIYU ta haifa Amma tana da wani cousin shine ya raba ‘yan biyun ya tafi da d’aya, dan lokacin da ta haihu bata cikin hayyacin ta, bata san me ta haifa ba ganin hakan ne yasa ‘dan uwa’n nata d’aukar guda d’aya, lokacin da nayi mai magana sai yace min zai Kai ma mahaifin yarinyan tunda ita matar ‘yan biyu ta haifa, nace to ya bari sai ta farfad’o sai suyi magana idan ta yarda Dan ba dad’i ace mace ta haihu bata sani ba a raba ta da abin da ta haifa, sai yace min to ai baya son ta sani Dan bazata yarda ba, Nima ya rok’e ni kar infad’a mata ‘yan biyu ta haifa, duk da banji dad’i ba hakan nan ya tafi da yarinyan, lokacin da matar ta farfad’o na bata yarinyan nace ita ta haifa,Cikin tsanin mamaki duk suka kalle ta, yayin da KAMAL yace “to ita Mai ya kawo su k’auyen? “Tsohuwar tace” ai lokacin shi Aliyu ya kawo matar gidan kakan shi ce wato mahaifiyar Maman shi, to kakan shi aminiya ta ce, dalilin da yasa da ta fara nak’uda aka Kira ni Dan a lokacin ni unguwar zoma ce”Gaba d’aya sunyi mamaki, sai NUWAIRA tace ko zata iya tuna sunan su matar da cousin d’in ta, tace A’a baza ta tuna ba.NUWAIRA ta d’auko wayan ta tare da shiga gallery ta fito da picture d’in Mom ta nuna ma tsohuwar tace”Iya ko kin san wannan?”Girgiza kai tayi tace”A’a”NUWAIRA ta fito da picture d’in Ummie tace”wannan fa ko kin San ta?”K’ura ma picture d’in ido tayi can ta fara sallati tace”wannan ai ZAINAB CE a Ina Kika san ta?”Cikin razana da firgici suka kale ta KAMAL yace”iya Ina Kika san wannan waya fad’a Miki sunan ta?”Tace”ai wannan ita ce matar da nake baku labari yanzu, it’s ce ZAINAB wacce ta haifa ‘yan biyu, ‘dan uwa’n nata ya tafi da d’aya”Mik’ewa tsaye NUWAIRA tayi lokaci d’aya taji wani irin jiri na d’aukar ta, KAMAL ne ya rik’o ta Yana cewa” iya mene ne sunan ‘dan uwa’n matar da Kika ce?” Iya tace” ALIYU shine sunan shi” Zufa ne ya wanke ma NUWAIRA fuskar ta lokaci d’aya, KAMAL cikin rud’ewa yace”kenan NUWAIRA kece yarinyan da Aliyu ya Kai ma Mom ta Raine ki a matsayin marainiya, Kuma Ummie da Daddy sune iyayen ki sannan MEENAL TWINS SISTER d’in ki ce”Girgiza kai ta fara tana hawaye tana cewa”A’a ba zai yuwu ba,No that can’t be true”Nan tsohuwar ta tambaye su meke faruwa, suka fad’a mata komai ita ma tace tabbas haka ne Dan haka suje su tambaye Mom da Aliyu sune zasu tabattar musu da ko su waye iyayen NUWAIRA,Haka ko akayi NUWAIRA da KAMAL suka d’auki hanyar komawa Abuja, *Toh fa kenan NUWAIRA da MEENAL TWINS SISTER ne? Ku biyo ni muje dan sanin gaskiyan zancen* *Shin idan da gaske ne Kuna ganin NUWAIRA zata so MEENAL?* *Idan da gaske ne meyasa ALIYU ya aikata haka?* *To ya zata kasance kenan?**TAKU CE UMMU BASHEER*✍🏻(07/01 5:27 pm) Sis Ummu Bashir: 🌹 *ZURI’A D’AYA*🌹 🌹 { *A story about Relationship, love and Friendship*} *NA**UMMU BASHEER*® *REAL* *PURE MOMENT OF LIFE WRITERS* (We don’nt only entertain and educate,but we touch the heart ❤of reader’s📚)_#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM*#IG PML WRITERS*#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035#http://maryamsbello.blogspot.com *WARNING**Ban yarda a canza min litafi ba, ko ayi min copying yin hakan laifi ne domin nayi litafin nan ne Dan fad’akarwa da nishad’antarwa , duk wace ta canza min zan d’auki mataki dan haka akiyaye**PAGE* *35*~*36* *Shafin k’arshe* *The last page* *The End* *B’angaren* Mom kuwa, bayan ta Kira Aliyu ne yazo suka had’u a wani park, inda duk ta rud’e ta fara tambayar shi cewa ya fad’a mata ko mahaifin NUWAIRA asalin ‘yan Ina ne ? Gaba d’aya sai ya rikice ya kasa amsa mata har ta gaji da tambayar shi ta gano bashi da gaskiya, tace lalai sai ya fad’a mata gaskiya akan NUWAIRA,Cikin rud’ewa da rasa yanda zaiyi yace” maganar gaskiya NUWAIRA da na kawo miki ‘Yar da Ummie ta haifa ne tare da MEENAL” Cikin tashin hankali tace” me kake nufi? Mai kake son cewa?”Cikin dauriya yace” Ina nufin Ummie ‘YAN BIYU ta haifa, NUWAIRA da MEENAL, nine na raba su na d’auki NUWAIRA na kawo miki Dan kawai in samu kud’i Kuma ita ma tayi rayuwa gidan mahaifin ta, kiyi hak’uri na Miki k’arya tun farko” Ba tasan lokacin da ta d’auke shi da wani irin gigitacen Mari ba tace” why do you betrayed us? Me yasa tun farko baka gaya min ba? All this years ka kasa fad’a min gaskiya, gashi can yanzu NUWAIRA ta tafi neman Asalin ta, idan ta gano me kake son inyi da wani idon Zan kalla mutane? Allah ya Isa tsakani na da Kai” tana gama fad’in haka ta bar gurin. Cikin sanyin jiki da nadamar abin da ya aikata ya koma k’auyen su, bai b’oye ma Kaka komai ba ya fad’a mai gaskiya, ai ko dama a gaban mahaifin Aliyu’n ne Nan yayi Mai fad’a sosai yace bai yafe Mai ba tunda ya cuce ‘yar uwa’n shi, haka Aliyu yayi ta basu hak’uri sannan da kanshi yaje har Abuja gidan su Ummie, da farko Mom taji tsoron ganin shi, amma sai duk yace Yana son magana dasu har dasu Hajja.MEENAL ma yayi mata waya yace tazo gidan, gaban ta sai da ya fad’i tana tunanin ko lafiya, FAWAS ne Mai bata hak’uri akan ba komai, Nan suka je. Bayan duk sun taru ne a parlour gaba d’ayan su ya fad’a musu gaskiyan abin da ya faru har d’auke d’ayan jaririyan da yayi na Ummie Wanda ita ce NUWAIRA duk ya fad’a musu!. Cikin tsanin b’acin rai Daddy ya mik’e tsaye ya nuna Mom da yatsa yace”Ashe duk zaman da nake dake na yaudara ne, Ashe kina cin Amana na ne ban sani ba, Dan me yasa zakiyi min k’arya akan NUWAIRA, sai ki fad’a min gaskiya gashi na rayu da ‘YA ta a matsayin marainiya ban tab’a sananin cewa yarinyan da na haifa bane, meyasa rashin samun haihuwa ya rufe miki ido ne? Kin cuce ni ban yafe Miki ba” Gaba d’aya Mom ta rud’e ta rasa mai ke mata dad’i a duniyar. Ummie cikin rashin fahimta tace” ALIYU kayi min bayani da kyau Sam ban gane mai kake nufi ba?”Cikin nadama yace” abin da Kika ji na fad’a gaskiya ne, kiyi hak’uri ki gafarce ni”Mik’ewa tsaye tayi ta Isa inda yake tare da wanka mishi Mari Mai shegen azaba tace” kana hauka ne shin kasan me kake cewa? Kana nufin ‘YAN BIYU na haifa? NUWAIRA da MEENAL sune ‘YAN BIYUN da na haifa? Amma tsawon shekarun Nan ban tab’a sani ba Kuma Muna tare da kai, Ashe Kai macucu ne mayaudari ne Allah ya Isa tsakani na da Kai wallahi bazan tab’a yafe maka ba, akan kud’i ka raba ni da abin da na haifa, ban yafe maka ba, Kuma Allah sai ya saka min abin da kayi min” ta fashe da kuka, Hajja ce ta rungume ta tana mai bata hak’uri.MEENAL ko ta kasa ko motsawa ashe dama NUWAIRA jinin ta ce, shiyasa take matuk’ar k’aunar ta, Ashe mahaifa d’aya suka fito,Ashe su d’in *ZURI’A D’AYA* suke.Cikin hawaye tace” Kawu Aliyu me yasa zaka aikata mana haka Shin dama Dani da NUWAIRA’ YAN BIYU ne? Amma ka kasa sanar da mu? Meyasa zaka aikata wannan d’anyar aikin?Ashe nida NUWAIRA *ZURI’A D’AYA* muke” ta fashe da kuka, FAWAS ne ya rungume ta Yana lalashin ta ko kunyar mutane bayayi, shi dai kawai burin shi ya lalashi matar shi,Jin an bud’e k’ofa ne an shigo yasa duk suka kalla k’ofar, wa zasu gani!? NUWAIRA ce da KAMAL suka shigo.Straight NUWAIRA gurin Mom ta nufa ta rik’e hannun ta tana girgiza ta cikin d’aga murya tace”Yau Ina son ki fad’a min gaskiya, shin a Ina Kika same ni? Aliyu shine Wanda ya baki ni ko har Kika bashi kud’i ko?” Mom duk ta rud’e ta rasa mai zata ce, k’ara girgiza ta NUWAIRA tayi cikin d’aga murya tace”ki amsa min tambaya na, shin Daddy da Ummie sune iyaye na? Shin nida MEENAL ‘YAN BIYU ne? Answer me please”Durk’ushewa tayi a k’asa tare da fashewa da wani irin kuka mai tsananin gaske, da sauri Ummie ta k’arasa gurin ta zata rik’e ta ne, ta tashi cikin b’acin rai tace”No karki kuskura ki tab’a ni duk kece Kika jawo komai ya faru idan da baki bar gidan Daddy na ba da duk hakan bai faru ba, yanzu da ace bandage Nan gidan Aliyu ya kawo ni ba da a Ina Zan rayu? Da ke da shi tare da Mom duk Kun cuce ni kunsa na rayu a gidan mahaifina a matsayin marainiya Kuma ‘Yar rik’o, duk na tsane ku” ta fashe da kuka tare da barin parlour’n da sauri, Gaba d’ayan su basu ji dad’in yanda NUWAIRA tayi ba amma kuma bata da laifi domin tana cikin tsananin b’acin rai tana buk’atar hutu yanzu dan zuciyar ta tayi sanyi, MEENAL ce ta fito waje dai-dai NUWAIRA zata shiga mota ta rungume ta tace”nasan yanzu Zaki San ainihin k’aunar da nake miki na ‘Yar uwa ta mu ‘YAN BIYU ne, kin yarda mu *ZURI’A D’AYA* ne?”NUWAIRA lokaci d’aya taji wani irin k’aunar ‘yar uwa’n ta lokaci d’aya da nadamar abin da take mata a baya cikin hawaye dukan su suka kalla juna tare da sakin murmushi, suka rungume juna.KAMAL da FAWAS da suke tsaye suna kallon su duk sai suka burge su, sunji dad’in yanda suka shirya dan dama tun farko tare suka gansu a matsayin Aminan juna.NUWAIRA murmushi tayi tace”Tun farkon had’uwa na dake nake k’aunar ki, ko abubuwan da nayi ta aikata miki duk kishin ki ne yasa nayi hakan Amma Ina rok’on ki da ki yafemin, na yarda mu *ZURI’A D’AYA* ne mu d’in ‘YAN BIYU ne” duk sukayi murmushi.FAWAS ne ya k’araso yace” TWINS SISTERS idan Kun gama soyayyar sai ku kula mu mazajen ku” Dariya sukayi gaba d’aya cikin k’aunar junan su, suka shiga mota gaba d’aya zuwa gida cikin farin ciki marar missaltuwa. Mom gaba d’aya ta rasa mai ke mata dad’i Daddy ya juya mata ba haka ma Hajja, sai binsu take tana basu hak’uri da k’yar suka hak’ura.Daddy da kanshi yaje har gidan NUWAIRA suka gaisa ya bata hak’urin abin da ya faru ita ma ta bashi hak’uri, sannan sukayi ta hira irin na ‘Ya da mahaifi cikin k’aunar junan su. Ummie ko tana yawan kyautata ma NUWAIRA Dan ta gyara laifin da ta aikata Mata, duk da haka NUWAIRA na fushi da ita kwata-kwata tak’i yarda suyi rayuwa irin na ‘Ya da Mahaifiyar ta, Ummie bata Jin dad’in hakan MEENAL ce ke yawan bata hak’uri tace taba NUWAIRA lokaci zata huce. ***************************** Rayuwa ce mai cike da Jin dad’i sukeyi, yanzu cikin NUWAIRA da MEENAL ya shiga wata na tara. Haihuwa yau ko gobe kuma suna samun kulawa ta b’angaren mazajen su. Yau tun safe MEENAL ke Jin wani irin azababben ciwon mara daurewa kawai takeyi. Har sun kwanta zasuyi barci dan lokacin k’arfe 9:00 pm ne, jawo ta jikin shi yayi tare da rungume ta very tight yana shafa cikin ta cikin k’auna, can taji wani irin azababben ciwo, tayi d’an k’ara dan taji azaba.Da sauri FAWAS ya zauna yana kallon ta yace”me ya same ki, ko haihuwar yazo ne muje hospital?”Daurewa kawai tayi tace”No kawai juyi ne, let’s sleep” Rungume ta yayi tare da had’a lips d’in su guri d’aya ya fara kissing, can taji wani irin ciwo Kuma da sauri ta ture shi ta tashi tsaye, cikin rud’ewa yace”baby Ina Jin fa labour kikeyi please let’s go to hospital”Tana zagaye bedroom d’in tace”nifa ba labour nake ba kayi barci kawai,juyi ne Kuma zai daina” K’in yarda yayi kawai sai ya nufa side d’in Mommy ya Kira ta, ko kafin su zo nak’udan yayi tsanani dan wani irin Nishi takeyi, sai addu’a takeyi.Mommy na shigo taga halin da take ciki tace ai labour ne, FAWAS duk ya rud’e tausayin matar nashi ya kama shi, k’in tafiya yayi duk da Mommy na korar shi yak’i tafiya, Cikin ikon Allah MEENAL Allah ya sauke ta lafiya inda ta haifa ‘YAN BIYU duk maza, Kuma identical twins ne masu kama da baban su Dan komai sak na FAWAS ne, habawa zo kuga murna gurin su ba’a cewa komai.Ranar suna yara suka ci sunan Daddy’n FAWAS da Daddy’n MEENAL, ana Kiran su da AMAN da IMAD, yaran sun ga gata sosai.Washegarin suna NUWAIRA ma ta haihu inda ta haifa ‘YA mace Mai kama da KAMAL, ranar suna yarinya taci sunan NANA AISHA sunan Mom aka sa, ai ko taji dad’i sosai, NUWAIRA tun bayan ta haihu take Jin kunyar had’a ido da Ummie dan tayi nadamar abin da tayi mata, haka Kuma tana jin wani irin k’aunar Ummie a ranta sosai. Bayan tayi arba’in ta rok’e Ummie gafara ta yafe Mata abin da tayi Mata, Nan suka shiga da shiri sosai, Ummie ta had’a kan yaran ta NUWAIRA da MEENAL tana nuna musu k’auna sosai Kuma ita da Mom suna zaman lafiya. *************************** *Ten years later* *Bayan shekaru goma* Wasu kyawawan yara na gani su biyu suna yin basketball, AMAN da IMAD kenan, can sai ga wata yarinya sa’ar su ce ta zo gurin tana wani yamutsa fuska tace” ku dai baku da aikin yi sai basketball, mtttsss Allah ya shirya ku”AMAN ko kallon ta baiyi ba sai IMAD yace” Ke NANA na lura kin raina mu ko mu sa’an ki ne?” Ya fad’a Yana zaro ido.Wata yarinya ce ta k’araso gurin da gudu tana cewa”eh d’in ai ko sa’an mu ne” har da murgud’a Baki. Da gudu IMAD ya fara bin ta suna zagaye gurin Wai sai ya buge ta Yana cewa” ke marar kunya ZEE ko? Ai sai nayi maganin ki yau”Cikin parlour ta shiga tana zuwa ta taga wasu yara su biyu suna wasa ta buge su ta ruga d’aki ta kulle tana dariyan mugunta,IMAD ko tsayawa yayi Yana lalashin yaran ITRAN da JAWAHIR kenan,Can sai ga NUWAIRA da MEENAL sun fito daga bedroom suna tambayar me ya faru, dukan su suna d’auke da tsohon ciki, IMAD ya fad’a musu ai ZEE CE ta duke su ta gudu, Nan MEENAL tace ta bud’e amma tak’i, can sai ga FAWAS da KAMAL sun shigo, Zee na Jin muryan baban ta ta bud’e k’ofar, ta rungume FAWAS tana ma IMAD gwalo. Shi ko hararan ta yayi.MEENAL tace” idan na rik’e ki Zaki sani”KAMAL yace”meye ta Yi ne da za’a rik’e ta? na lura Kuna takura ma Zee d’ina”FAWAS yace”ka bar ni da Mommy’n su nice maganin ta” ya kashe ma MEENAL ido d’aya alamar zamu had’u.Hararan wasa tayi mai, can sai gasu AMAN da NANA sun shigo, Nan sukayi ta hira cikin nishad’i da farin ciki.Bayan MEENAL ta haifa ‘YAN BIYU ne sai ta haifa ZAINAB Wanda taci sunan Ummie, daga Nan ta haifa ITRAN Mai sunan Mommy’n FAWAS,NUWAIRA Kuma bayan NANA ta haifa JAWAHIR, sai cikin da suke d’auke da shi yanzu, FAWAS da kanshi ya gina musu gida shi da KAMAL yanzu gida d’aya suke kowa da side d’in shi,Zaman lafiya sukeyi sosai, da k’aunar junan su, haka Mom da Ummie, suna cikin kwanciyar hankali bare kuma idan aka kawo musu jikokin su ai basu da wani matsala. Ummie ta Gina ma mahaifin ta Kaka gida yayi aure Kuma ta yafe ma ALIYU abin da yayi mata. Abba Kuma yanzu shiri suke sosai shi da Kaka.Sanye take cikin wani night sunyi mata bala’in kyau, ta nufa kan bed inda FAWAS yayi mutuwar zaune Dan ba k’aramin kyau tayi Mai ba, tana zuwa ya rungume ta ya fara kissing d’in ta duk ya rud’e, ita ma ta dage sai maida martani takeyi, ganin sun cire kayan su ne yasa na fito Dan ba Dani ba. Lolx.*Alhamdulillah**Anan na kawo k’arshen litafina Mai suna ZURI’A D’AYA, Ina ma Allah godiya da yasa na Kamala lafiya* *Allah ya yafe min kuskuren da nayi a cikin litafin Nan Allah yasa mutane su gane darasin da yake cikin litafin nan, Allah ya bamu ikon amfani da abin da ke ciki, Ameen* *Massoya na nagode sosai da yanda Kuke k’aunar novels na, Allah ya k’ara zumunci da k’aunar juna,Ina godiya sosai massoyan ZURI’A D’AYA**Muje zuwa sabon novel na Wanda zaizo muku Nan ba da jimawa ba, sai mun sake had’uwa,kar ku Bari a baku labari**TAKU CE UMMU BASHEER MAI K’AUNAR KU*✍🏻🌹Download Zuri’a Ɗaya Littafi Na Ɗaya Complete Hausa Novel